Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba yayi saurin shan gaban ta da motar ya faka ya fito tana tsaye fuskar ta a hade Kamar had'ari,


"My Aunty wannan fushin fa? Kizo mutafi ina zakije da kafa? Bansani ba don ALLAH ka bani hanya in wuce ka koma wurin karuwar ka gata can tana jiranka,


" na shiga uku ni Abdullah so Ake sai zuciya ta ta buga hankalin ki zai kwanta nidai ki taimake ni ki saki ranki mu tafi don ALLAH,

Bazan jeba ka matsa min a hanya ka koma kaci gaba da hirar ka kawai nasan dama ka dade a cikin muguwar harkar shiyasa har kake ganin kayi balagar da zakace ni kake so,


Ta nunashi da yatsaya " kar ka kuma KUSKUREN cewa wai ni kake so ranka zai baci ni ba irin waccen bace jikin shi na rawa ya fara kokarin riko hannun ta,

.don ALLAH ki saurare ni Wallahi ba budurwa ta bace impact ranar da kika fara ganin mu nima Aranar na fara ganin ta Wallahi bansan ta ba ya karasa maganar kamar zaiyi kuka,


Taji mugun sanyi a cikin zuciyar ta har wata y'ar Karamar Ajiyar zuciya ta sauke ta dan kauce kadan zata wuce ya rike hannun ta "Aunty please"


Ki shiga mota mutafi, "ka sakar min hannu kaga mutane na kallon mu ko,

To ki shiga ko Wallahi in d'auke ki in saka ki A mota,

Tasan halin shi bawai kunya ce da shi ba yasata yin baya ta bude motar ta shiga batareda ta rufe ba ta zauna Abinta,


Murmushi kawai yayi ya koma gefen ta ya rufe murfin sannan ya dawo gefen driver ya zauna " tank's Aunty na,


Dauke kanta kawai tayi ta mayar gefen titi,

Tafiya sukeyi batareda sunce wa juna komai ba sai shi dake d'an kallon ta ta gefen ido time to time yana Sakin murmushi,


Domin jin shi yake cikin nishad'i sosai " sun danyi nisa kadan ta fara lumshe idanun ta ta kwantar da kanta kadan nan take bacci barawo ya tafi da ita saboda rashin baccin da batayi ba daren jiya,


Driving yakeyi Amma gaba daya idanun shi na kanta yana kallon kyakkyawar fuskar ta,


Har suka shiga Zaria tana baccin ta saida ya faka motar sannan ya juyo gaba daya yana fuskantar ta ya dora hannun shi a kan fuskar ta ya fara yawo dashi har kan lips dinta da ke sheki ta dan motsa bakinta kadan da ya bashi damar ganin dimple dinta da ya d'an lob'a Ahankali ya matsa da fuskar shi zuwa ga tata

.yayi mata kiss kadan a saman lips dinta sannan ya manna mata wani a gefen chick's dinta


Ahankali ta fara bude idanun ta domin jin kamar ana shafa mata jiki tayi saurin zabura ta zauna da kyau tareda watsa mai mugun kallo ta fara gyara zaman mayafinta


Me kakeyi haka?

"Na d'an tsotsi bakin my wife to be ne,

Ta zaro ido tareda shafa lips dinta Abdul banason rashin kunyar ka fa,

" Hmm Aunty na kenan kema fa kinaso kawai kinki ki bada Kaine Abinda harda kara riko min baki kikeyi Aduk lokacin da na fara kissing dinki'


Bude motar kawai tayi ta fito batareda ta saurare shi ba domin taga kullum sabon iskanci yake karowa da kuma rashin kunya,



"Ta kalli kofar gidan su taga irin gyaran da yakesha ko ina ya fito tsaf bakamar lokacin da Ake turuwar zuwa siyan Abinci ba,


Da gudun ta ta karasa cikin gidan " kakus kakus ina kike nayi ke warki ta fada falon tareda fadawa saman jikinta,


"Ni yau naga y'a karya ni zakiyi da kika fadomin akan jiki da manyan cinyoyin nan naki ke ni dagani ta d'an tureta kadan,


" wato Hajiya yanzu bakya sona ko? Bawani nan keda kikabi ubanki kika manta dani,

Hajiya ni na isa in manta dake "to naji ga Angon ji nan tunda kin shigo kamar wata Yarinyar goye bakya ko jin kunya,.


Sulaiman dake zaune tun Shigowar ta ya zuba mata idanu yana musu dariya,


Ahankali ta saita kanta ta kalle shi sai Alokacin ma ta tuna da maganar shi a waya tayi saurin daure fuska ta kalli Hajiya,


" kuje can dakin Abdullahi toh tunda ta zo ke kuma ki shirya ma Angon naki Abinsha dama bai dade da zuwa ba kika iso,


Da saurin shi ya mike ya fita domin ya kagara su d'an kebe domin ya nuna mata irin farin cikin da yakeyi a zahiri,

Yana fita ta kalli Hajiya " Wai ni Bangane ba Hajiya waye Angon nawa?

Sulaiman mana' ai kina tafiya saiga iyayen shi sunzo ya fadamin kin Riga kin Amince shiyasa kawai na kira Jafaru yazo ya karbesu shida Abokin shi mahaifin ki ma sai bayan sun wuce nayi mai bayani,


Amma Hajiya ni nafada miki ina sonshi tsakani da ALLAH? Baza ku tanbaye ni ba kuji ta bakina? Sai kace wata kaza daga ganin mutane zaku Amshi gai suwa to ni Wallahi banason shi'


Wasa kikeyi yarinya kuma bazaki mayarda mu kananan mutane ba tun farko saida na yi miki magana idan bakyason shi ki sallame shi sai yanzu zaki kawomin zancen banza to idan har bakyason shi sai kije kisamu babanki Jafaru bani ba ehem,


Ta janyo wata yar Karamar Leda ta kunce ta zaro kudi wa inda Akalla zasuyi dubu hamsin " gasu kudin gaisuwar ki ne ki gani'

Ga kwalayen biskit dasu sweet can ta nunamata wasu irin kwalaye a gefe da sunkai kusan biyar,.

Wasu irin hawaye ne suka wanke mata fuska ta kalli Hajiya " Yanzu saboda ALLAH neman kai kikeyi dani Hajiya? Dazaki yi saurin yanke min hukunci?


Jikin Hajiya yayi sanyi domin sai yanzu ita kanta ta fara data sanin karbar kudin gaisuwar Abinka da jika da kaka nan da nan ta janyo ta zuwa jikinta ta fara lallashin ta,.


'Kiyi hakuri Ummu kiyi Addu'ar ALLAH yasa shine mafi Alkhairi agareki kinji ki kwantar da hankalin ki kinji?


Hawaye kawai takeyi domin tama rasa wane irin tunani zatayi ta mike kawai ta fada dakin ta tareda sa kuka mai tsuma zuciya sai yanzu take gane cewa ta cutar da zuciyar ta da ta Amince tun farko ta y'ar da da Abdullah da ba haka ba wai shin menene illar Auren karamin yaron?


Ko ta manta da Annabin mu (S.A.W)ma yayi Auren fari da Matar da ta girmeshi kuma baza wara sai ita da ba wani girman shi tayi ba tazarar shekara daya ce tak a tsakanin su,


"Ummu kifito kinbar shi a waje yanata jiranki. Taji Hajiya na magana'


" Tayi kok'arin share hawayen ta ta mike tareda daukar katon hijabi ta saka ta fito domin dole ne ma ta sanar da shi Gaskiya domin ita Sam bazata iya Auren shi ba,


Abdullah kuwa ya dade Azaune a cikin motar yana faman murmushi kiran wayar shi da Dadyn shi yayi ne ya sakashi dawowa cikin hayya cin shi ,


Yana d'auka yace " kasa meni a GRA yanzu nasan ka shigo garin,


Juya kan motar shi kawai yayi ya nufi gidan su,

.tundaga harabar gidan yakejin hargagin Momyn shi ga security ta ko ins ya faka ya fito Ak ne ya fara ganin shi ya taso da sauri " welcome sir'


Tank you Ak, ya bude kofar ya shiga tana ganin shi ta karaso da sauri ta tareshi,


"We're have you been my son?


Abdullah ka fada ma Momyn ka inda kaje tunda ka tafi kullum sai ta karanta min hauka a gidan nan akan cewar ni ne na boye ka


Kuma ina son yin magana dakai yanzu " ya dan rungume ta kadan ya bata fake a kunci sannan ya kalleta

Momy am fine stop worrying your self am not a small kid any more

"Why shouldn't I worried Jeff u are not picking up my call ta fada cike da damuwa

Abinka da uwa nan da nan yaji tausayin ta ya d'an kara rungume ta tareda bata baki da kuma yi mata bayanin cewar aiki sukeyi na company a KD karta damu ,

Ya d'an raba jikinshi da nata ya nufi Dadyn shi ya zauna gab dashi,


Abdullah"

Yes Dady" inaso kamar yadda na fada maka a baya inaso inkara mai maita maka' ka dauki kaddarar ka ka hakura da Ummu Ruman nariga na tsayar mata da miji har mun karbi gaisuwa kuma baza a dauki lokaci ba za ayi zancen Auren,


Inaso ka natsu yanzu da Angama Gina companin ka zan Gina ma Asibitin ka a duk inda kake bukata zan nemo maka kwararrun likitoci da zakuyi aiki tare kaji ko?


Gaba daya Jinshi daukewa yayi har ma da ganin shi atake batareda yasan me Dadyn shi yake fada ma tun lokacin da ya furta zancen Auren Ummu Ruman saidai kawai ganin shi yayi ya sulale ya zube akasan Capet sharab kamar gawa,

Wani irin ihu Momyn shi ta sanya tareda nufoshi da gudu tana kururuwa........✍



*_Akwai matsala fa fan's anya wannan hukun cin zai haifar da da mai ido kuwa ? Muje dai zuwa my fan's_*

*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_love & Destiny_


_Written by Fenerh_


✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.
✍✍✍✍✍✍✍✍


*Jumu'at Kareem to All my family and friends*

_All the praises and thanks be to ALLAH who has sent down to his slave (Muhammad) S.A.W the book (Qur'an)and not has not placed there in any crookedness._
*(Suratul Al khaf)*





πŸ…Ώβž‘1⃣9⃣

Sun gama shiga tashin hankali ganin gudan jinin su akwance kamar gawa ,

Ihun Momy ne ya janyo hankalin su Ak suka shigo da gudu domin ganin meke faruwa?


Ak ne yayi gaggawar neman Likitan dake kula da shi suka ciccibe shi zuwa dakin shi,

Likita na zuwa ya fara bashi taimako gaba daya iyayen sun shiga tashin hankali,



Dakyar Likitan ya samu numfashin shi ya dai daita Amma yana bude idanun shi ya sanya musu kuka mai mugun ciwo da kuma taba zuciya,


Ba Abinda yake fada sai " please Dady ka taimake ni kar in rasa farin Cikina da kuma Rayuwa ta ina son Ruman kunsani kar Kuyi gangan cin raba mu itama tana sona,


Abinda yake ta mai mai tawa kenan yana gursheken kuka,


Momy tayi saurin rike shi domin ita Sam bata San kukan me yakeyi ba ta kalli uban'


"J tell me what is happening?

Cikin masifa shima ya juya harshe ya fara zazzaga mata masifa


Kifita acikin wannan maganar Tara sannan ki gargadi d'an ki ya kiyayeni this time Around bazan dauki abinda zai bata wa iyaye na rai ba bazan kuma Aikata KUSKUREN da na Aikata a farko ba


Na fada mishi ya hakura da Umma Ruman don haka koda Ace zan rasa shi bazan taba bin son zuciya ta ba,

Cikin daurewar kai ta kara tanbayar shi waye Ummu kuma

Ahankali ya war ware mata komai ya kuma kara da cewa

Ummu jini na ce y'ar kanwata uwa daya uba daya yar d'an uwana da muke d'an wa da d'an k'ani don haka dole abi umarnina,


" Ina so in gyara KUSKURE NA na kin yima iyayena biyayya banaso ya Aikata irin laifin da na Aikata Abaya na sabawa umarnin iyaye,

Na samu ci gaba na Auri Matar da nakeso Amma kullum banida kwanciyar hankali sai yanzu da na nemi yafiyar iyaye na suka hakura zaizo ya bata min komai to bai iyasa ba,


Sannan Ummu da su Hajiya zasu dawo nan gidan domin inaso Agyara gidan gaba daya don haka idan kinsan bazaki iya yima iyayena biyayya ba to kibar min gidana ki koma Abuja ko ki bar kasar gaba daya ki koma taku couse this is my country,


Ya koma kan Abdullah da yayi shiru dole da kukan da yakeyi ya kalle shi " a baya rokon ka nakeyi Abdullah Amma yanzu umarni zanbaka ka fita hanyar Ruman Aure zanyi mata da w'anda takeso kuma idan har ka kuskura iyaye na suka San da wannan maganar Wallahi bazan yafe maka ba,


"Idan ka kuma furtawa koda wani kanason Ummu zaka hadu da fushi na Ummu Ruman bata sonka tanada w'anda takeso ka barta ta Auri zabin ranta na fada maka,

Ya wuce fuu ya fice cikin fushi yana fita security dinshi suka taso ya fada mota ya bar gidan,

Momyn shi tayi saurin karasa wa ta rungume shi tasanya kuka " Am sory my son is All my faults please forgive me,

Kukan ma ya ki fitowa yanzu sai zuciyar shi da ke mishi suya kamar ana soyata yau Dady ne keson rabashi da numfashin shi domin yanaji Ajikin shi Ummu itace rayuwar shi yana rasata numfashin shi zai tsaya,


Shiyasan duk laifin Ruman ne don da Ace ta Amince mai ba Wanda zai raba su Amma ina tasa taurin kai,


Bakomai ya barwa ALLAH duk da yasan rayuwar shi bazata taba yin kyau ba idan har bata tare dashi,


Ruman kuwa tunda tafito tafara baza idanu tana mai neman shi domin ko motar shi bata gani ba a wajen,


"Toh ina yaje kuma gaba daya hankalin ta yaki kwanciya tama manta da wani Doctor Sulaiman dake tsaye yana binta da kallo kamar wani maye,


Ya karaso kusa da ita " Hajiya ta ai gani nan a gabanki ko me kike nema?


Tayi saurin kallon shi ta dan ya tsine fuska " kani na da muka zo dashi yanzu nake dubawa ko ka ganshi ?


Aa banga kowa ba koda na fito nan, OK ta dan matsa kusa dashi ta kalle shi tanaso ta hango aibun shi amma bata ga komai ba domin Sulaiman ya cika cikakken namijin da duk wata mace zataso kasan cewa da shi amma kash zuciyar ta na wurin karamin yaron da take rainawa da farko,


Har yayi surutun shi ya gama hankalin baya tare dashi da kanshi ya Ankare " Hajiya Ummu da gani Agajiye kike don haka bari inbarki kije ki huta nima Kaduna nakeso in shiga domin inaso infara shiri da wuri akan maganar Auren mu,


Gabanta ta mugun bugawa tayi saurin kallon shi so takeyi ta bude baki ta fada mai ita bazata Aure shi ba Amma bakinta ya mata nauyi takasa furta koda kalma daya,

A haka har suka rabu batareda ta ce mai komai ba,


Hawaye ne masu zagin gaske ke bin kuncin ta wannan Auren na shirin kaita ga kabarin ta batareda ta shirya mutuwa ba domin ita sai yanzu ne ma tasan tana mutuwar son d'an uwanta rasashi kamar rasa wani sashi ne na jikinta,


Tana shiga cikin gidan dakin shi ta tura ta shiga " ko ina nan kamar y'an da ta barshi don tun kafin taje Kaduna kullum sai ta gyara shi da Alama ma ko shigowa baiyiba,

Kan katifar shi ta nufa ta fada tareda sanya kuka mai karfi saboda tasan ba w'anda zai jita

Najama kaina waini Jan Aji gashi nan Jan Ajina zai kaini ya baro zan tafka mugun KUSKUREN da zai kaini da kushe wata haka tayi ta kukanta har ta gode ALLAH,

Ganin ba wata mafita kawai ta fito ta daura Alwala ta nufi dakinta domin sauke farayi


Ko Abinci kasa ci tayi tana Alla Alla gari yawaye taje school ta samu kawayen ta ko zata samu sassaucin Abinda ke da munta A zuciya,



Zuwan kawunta ya sanya taji mugun dad'i a zuciyar ta mu samman da ya fada musu zai kwashe su A yau ya mayar dasu can gidan har ma dasu magaji ya tanadar musu inda zasu zauna kafin a gama gyaran gidajen su gaba daya


Tafi kowa farin ciki domin tana saran ganin shi a koda yaushe idan har tana cikin gidan su Hajiya ce dai take so ta kwafsa musu


Jafaru da ka barmu kawai idan an gama gyaran gefe daya mukoma dayan basai mun takura muku ba kasan idan har ni na y'ar da matarka fa baturiya kuma suma su magajin ba y'arda zasuyi ba,


"Inna don ALLAH ki sa baki nasan da kinyi wa baba magana zai Amince innan mu kuwa kinsan bazata ki bin umarnin shi ba kiyi hakuri ki Amince don ALLAH,


Toh shi kenan kaje idan mun gama magana Anjima sai kasa driver yazo ya kwashe mu kafin nan ma mun d'an tattara Abubuwan mu masu Amfani,

" Inna basai kun kwashi wasu kayaba na tanadar muku komai a can,

"Au kace sai da ka gama tsarin ka sannan ka fada mana ko? Dariya kawai yayi ya shafa kanshi sannan ya ce Amma idan ba damuwa inaso muje tareda Ummu Ruman yanzu,


Aa ni na isa in hanaka daukar y'ar ka ai gata nan kuje ALLAH yayi Albarka ya kuma shirya ku da dukkan zuriar ku baki daya, ya Amsa da Ameen,



Ummu kuwa jakar ta kawai ta d'auka d ta dawo da ita batareda ta nemi komai ba sai kuma system din shi dake dakinta ta saka ta cikin hijabin ta ta bishi tareda Sallamar Hajiya,


A sauka lafiya tunda kinzama ta maula kowa ya gara shi wancan ya kwasa shi kuma wannan ya dawo ya kwasa aje ALLAH ya rabaki da sharrin baturiya,


Dariya kawai tayi don tasan halin Hajiya da mita ta wuce domin ita damuwar ta ma kawai ta isheta,


Tunda suka fito security duk suka taso ya karbi makullin mota daya a hannun Ak,

Ku jira iyaye na idan sun shirya ku kawosu GRA,

Abinda kawai ya fada kenan cikin bada umarni sannan ya ce" Ummu shiga mota mutafi


Saida suka d'an yi tafiya sannan ya faka motar shi a gefen titi ya kalle ta "Ummu" ta Amsa cike da jin kunya tareda dukar da kanta kasa kadan,


Nasan tun zuwan Abdullah Nigeria yake takura miki duk da nasan cewa soyayyar da yake miki kaddara ce da ta Afka mai tun yana karami tunma bai sanki ba bai taba ganin ki ba tun baisan cewa ke jinin shi bace, nasani Abdullah yana miki mugun so nasan komai nida mahaifiyar shi Amma hakan ba zai sa intauye miki y'an ci ba na hanaki zabin ranki shiyasa nayi gaggawar karbar masu neman Auren ki,


Ki kwantar da hankalin ki Abdullah indai ni na haife shi ba zai kuma damun Rayuwar ki ba har ki yi Auren ki da w'anda kikeso, yanzu haka na baro shi ba lafiya don haka kar wani Abu ya daga miki hankali ALLAH yayi miki Albarka,



"Wayyo ALLAH na shine abinda ya fara fitowa a cikin zuciyar ta " Yanzu me Dady yake nufi?

Ya datse soyayyar da Abdullah yake mun a daidai lokacin da nafi bukatar kulawar shi a dai dai lokacin da nakejin bazan iya Rayuwa babu shi ba nashiga uku na,

Wani irin zufa ne ke tsiyaya ta cikin hijabin ta har zuwa tafin kafarta har suka isa kofar gidan hankalin ta baya jikinta saida ya ce Ummu kifito munzo gidan,

Tayi saurin kallon tafkeken gidan kamar A kasar turawa tundaga kofar gate din da suka shiga har zuwa harabar gidan da kuma gefen lambun mai dauke da kayan itatuwan marmari kala kala kamar wani gidan gona,


Ya yi gaba tareda cewa muje" bata kara tsinkewa ba saida suka isa bakin kofar glass din da saida ya sa hannun shi ta bude sannan suka shiga,

Badon tana cikin damuwa ba ba Abinda zai hanata kauyanci Ace irin wannan gida kamar baza a mutu ba kai jama'a


_A Zaria nefa wannan ginin ba kano ba 😁_.


Tun shigar ta take baza idanu ko ina tana karewa Aljannar duniya kallo a Gaskiya sai yanzu ne ma ta kara sakan kan cewa da Al amarin soyayyar da Abdullah yake nuna mata w'anda ke cikin irin wannan daular Amma ya hakura ya zauna a irin gidan su saboda kawai so"


Ita kuwa wane irin shirme ne ta tafka da ta kasa fahimtar hakan tunfarko

Soyayya Gaskiya ce idan ba don so ba ita tasan cewa Abdullah yayi mata nisa duk da kasan cewar shi d'an uwanta na jini,



Dady ne da kanshi ya nuna mata wani daki dake cikin katon falon,

Ga dakin ki nan Ummu idan Akwai Abinda kike bukata kiyi magana Ak na nan Akwai kuma mata masu kula da Aikin gidan,

Ta Amsa da toh sannan ta shiga ciki tareda tunanin me zai faru da su a cikin wannan gidan..........✍

_Allah yasa muji Alkhairi y'an uwa fatan kowa yana cikin koshin lfy Allah ya sada mu da Alkhairi n dake cikin wannan rana ta jumu'a Ameen_



_Taku har kullum_


*Matar Soja*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*KUSKURE NAπŸ™†*
_Love & Destiny_



_Written by Fenerh_


✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.
✍✍✍✍

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*_Aslm yan uwa Kuyi min Afuwa da KUSKUREN number da nayi a last post dina instead of insa 18 nasa 19 Don haka zancigaba da hakan kawai na gode_*


πŸ…Ώβž‘2⃣0⃣

Tunda ta shiga cikin dakin zuciyar ta taki natsuwa, shi kawai take murad'in gani A idanun ta,


Nan take wata zuciyar ta Bata shawarr fitowa ta d'an duba ko zata ganshi,


Ta fito falon Amma ta rasa wace kofa zatabi saboda kofofi ne birjik a cikin falon kar taje ta shiga inda bai kamata ba,


Ganin Shigowar wata y'ar budurwa dauke da tray da ya sanya ta saurin yimata magana'


Cikin halshen turance ta gai sheda Ruman tareda girma mawa "Ma'am do you need something?


Tayi saurin Am sawa domin tama rasa ta ina zata fara,


budurwar tayi saurin cewa" Ok Am coming let me take this to the young master....


Cewa kawai tayi ta tafi ta samu kujera A falon ta zauna tareda bin bayan yarin yar da kallo har ta shige cikin wani daki,

Har ta dawo ta na nan a zaune tarasa meke mata dad'i A zuciyar ta,

Ta tanbaye ta me take bukata? " just leav it' ta furta a hankali

Har kusan magrib tana zaune ba tareda ta samu mafita ba

Su Hajiya ma sun zo an basu wasu dakuna can ta baya domin sunki y'arda Sam su zauna ta cikin gidan " tunda Akwai dakuna ba dole mu zo kuma mu takura kuba


Ruman ma taso ta zauna da su Dady ya hana yace ita ta zauna Abinta a cikin,

Ya wadata su da kaya na more Rayuwa Abinci kala kala suturu Alhmdulillah domin sun gama tsara komai da d'an uwan shi ko wannen su kok'arin faranta wa iyayen su rai kawai sukuyi kuma sunyi matukar farin ciki da hakan


Ruman kuwa har wayewar gari bata sashi a ida nun ta ba shi ma kanshi bai San mai yake faruwa ba duk da jikin shi yayi sauki Amma Akwai ciwo mai girma a cikin zuciyar shi


"Shiya sa Sam baya kaunar fitowa sallar ma a cikin dakin yake yinta


Sai da ta gama shirin zuwa makaranta ta tuna da cewa ta na kusa da Kawarta yanzu ita jiya Sam ta manta da cewa tana kusa da Hajara,


Wayar ta ta nema ta fara kiranta tana d'auka tace mata" kina ina ne?

School din fa? Yanzu zantafi, kibiyo ki dauke ni ina unguwar ku tunjiya,

Wani irin ihu ta sanya domin tasan inda zatazo har ta kwana " Wayyo dad'i gani nan zuwa yanzu kuwa kawata,


Ta datse kiran tana mai dariyar Haukar hajara, break fast din ma da aka kawo mata kasa ci tayi domin ita kadai tasan irin halin da zuciyar ta take ciki,


Saida ta fito sannan ta shiga wurin su Hajiya ta samesu Zaune har da Dady cikin farin ciki sai hirar su sukeyi ta durkusa har kasa ta gaida kakan nin ta,


Tareda Dady "Ummu zaki wuce ? "Eh Dady " ok nayiwa driver magana da zai rika kaiki don haka yana jiranki a waje idan kinfita tace to nagode Dady"


Suka bita da Addu'a ta fita ,

"Hajiya ta kalle shi " Jafaru wai ni ina Matar taka take ne? Munzo tunjiya amma ko tazo ta gai shemu idan taki zuwa gidan mu na talaka to mu gamu a gidan ta sai tazo mugaisa ko,


Duk'ar da kanshi yayi cike da jin kunya " Inna bata gari ne tana Abuja'

"ALLAH ya kyauta to dukan su suka Amsa da Ameen,


Tana fitowa Driver ya taso da sauri " Hajiya muje ko? Kafin ma tayi magana hajara ta iso "kabari kawai zamu tafi da kawa ta'


Ya ce " Adawo lafiya ta Amsa da Ameen tareda shigewa motar suka tafi,


"Kawata ya banga young crush dinki ba? Ta kalle ta cikin damuwa tareda war ware mata dukkan matsalar da take ciki'


" kuma tunjiya da nazo ban ganshi ba " Wallahi ina cikin damuwa kirji na har zafi yake mun tsabar tunani da kuma tulin damuwar dake cikin rai na,


Hajara ta matukar tausaya wa kawarta " a Gaskiya Queen tun farko ke kika ja koma meye da kin bashi hadin kai da duk haka bai faru ba,

Toh yanzu ki fadawa Hajiya mana, " kinsan y'an da Hajiya ke son Doctor kuwa?


Ni yanzu menene mafita ki fadamin gaba daya na kasa sarrafa kwakwal wata, nidai mafita daya ce kawai ki fadawa Hajiya,


Bazan iyaba Abin da nauyi ince mata wai kanina

Please Login or Register in order to submit comment