Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin zuga shi yake aka kar ya sake ya bawa Khamal auren tilon 'yarsa ga mutumin da bashi da gobe, dan haka kullum abin k'ara kwab'ewa yake.


Dady da Abban Ja'afar ne zaune a falo suna tattaunawa yayinda da Abba sai k'ara zuga Dady yake, ya kalle shi yace " ni dai ina k'ara baka shawara karka sake ka d'auki tilon 'yarka ka bawa mutumin da yake zaman banza jobless, bawai dan Ja'afar d'ana bane, Fateeha bata dace da kowa ba sai Ja'afar shine kad'ai zai jiyar da ita dad'in dake cikin aure, shine zai bata farin ciki da kwanciyar hankali, saboda yafi kowa sanin darajarta kuma duk tsiya shi d'an uwanta ne, kaga kuwa ai ya bare, koba komai wannan had'in zai k'ara dank'on zumuncin mu, kasan wani abu? Abba ya tambayi Dady, kasa magana Dady yayi illa girgiza masa kanshi dayayi, murmushi Abba yayi yace " matuk'ar Khamal bai rabu da Fateeha ba sai na b'atar dashi, kai idan ta kama ma na kashe zan iya kashe wallahi, a hankali zugar Abba ta rink'a tasiri a zuciyar Dady har yaji ya tsani Khamal fiye da komai da kowa.


Bayan tafiyar Dady ne Abba ya shiga gida, Umman Ja'afar dake zaune tana jiyo hirar su hankalinta yayi mugun tashi, ta shiga mummunar damuwa, gabanta sai fad'uwa yake dan taji abinda Abba yace, a haka Abban ya shigo ya same ta, mik'ewa tayi cikin sanyin jiki, ta shiga yi nasiha , " haba Abban Ja'afar, saboda tsabar san kai, wato naka d'an shine kad'ai d'a shi ba d'a bane, wannan wane irin zalunci ne, da rashin tausayi yarinyar nan tace batasan shi, ga wanda take so, shima fa d'a ne kamar naka, kuma shima iyayen sa suna sanshi kamar yanda kake son naka may be ma sunfi k son d'an su, yanzu Alhaji ashe zaka iyaye kisa, wata irin mahauciyar tsawa ya daka mata cikin fushi sai huci yake yace "bana son jin komai daga wannan banza bakin naki, shashasha kawai, banza lusarar mace, ke kin isa ki zaunar dani kina min wa'azi, ke kin isa ki fad'a min abinda ya kamata nayi, ok wato yadda baki sanshi baki damu da damuwar sa ba, nima so kike nayi watse dashi, wallahi badan akan ido kika haife shi da saina ce dan ba d'anki bane,dan haka na riga na gama yanke hukunci kawar da Khamal kowa ya huta " Alhji dan ina fad'a maka gaskiya kake jifana da wad'an nan maganganun, kadai tuna da mutuwa, da ranar tsayuwa, hannu ya d'aga mata kawai saboda ya kasa magana sai hhuci yake tsabar bak'in ciki ya wuce.


Sannu a hankali rayuwa ke tafiya sabuwa suka dinka faruwa suna wucewa, cikin haka ne Khamal ya buga ball d'in k'asa, cikin sa'a da taimakon Ubangiji yaci ball d'in cikin k'ank'an lokaci Khamal ya farayin suna a Nigeria, cikin haka gwamnati ta zab'e a wanda zai jagoranci Nigeria, a worlds cup wanda a yi Saudia a garin Riyadh, aiko murna da farin ciki ba'a magana suman wajen Hajiya da Hamza.


Khamal da Fateeha kuwa sunfi kowa farin ciki dan gani suke nesa tazo kusa, soyayyar su kullum k'ara gaba ji suke kamar su had'eye juna, kullum k'ara shak'uwa suke sunan su, Khamal da Fateeha na tsaye a harabar gida su, sai zuba soyayya suke suna sakarwa juna k'ayataccen murmushi, da tattausan kallo, cike da k'aunar juna, duk wanda ya gansu a haka yasan ko ba'a tamaya ba akwai tsaftacciyar soyayya, Abba da Dady suka fito, cikin zafin rai Dady ya nufe su, da sauri Abba rik'o shi, yace " mai yasa ka cika gagagwa ne, saura k'iris mu kai ga gaci, kai ka b'ata mana plan, ai na riga na gama shirya masa *GADAR ZARE*


Fateeha da Khamal zaune a Shagalin ku restaurant, Oder suka bayan ta abinci da drinks, murmushi d'auke a fuskar kowannensu, Khamal ya kafe ta da ido, iska ta hura masa tace " yadai wannan kallo haka?

Dariya yayi yace " ba dole ba kin san bana gajiya da kallonki, ko a cikin b'akin ciki nake idan na kallonki sai naji na zama freshman, murmushi kawai tayi, suna cin abincin suna hirar soyayya cike da tsantsar so, kowannen su ji yake idan duniya zata tashi bazasu iya rabuwa da junan su, shauk'in k'auna ke fizgar kowannen su, duk wanda ya kalle su yasan ba k'arya akwai true love, sai lumshe ido suke, Ja'afar dake zaune a gefe yana shan coffee, ya sauke idonsa a kansu.


Wani irin mugun kishi ne ya taso masa, zuciyar sa ta shiga bugawa da k'arfi, gabansa yayi muguwar fad'uwa, take yaji k'irjinsa na neman daina aiki, lokaci d'aya ya rud'e ya figa daga hayyacin sa, ya rasa abinda me masa dad'i a duniya, ya rink'a jin zuciyar sa kamar zata kama da wuta, idon shi ya rufe da sauri ya sake bud'ewa, ya sauke su a kansu, bai san sanda ya nufe su ba, yakai wajen 5mtn tsaye a kansu amma basu sani ba kasancewar sun da tafiya wata duniya, cikin zafin rai ya buga table din da suke zaune, a firgice suka mik'e suna kallonsa, wani wawan tsaki taja, ta watsa mishi kallan banza, ta kalli Khamal tace " please have a set my life, don't worry about him, a hasale Ja'afar yace " dama baki daina bin wannan d'an iskan yaron ba, zauna gari banza jobless wanda shi kanshi bai iya ci da kanshi ba balle ke, murmushi Khamal yayi baice komai ba, cikin zafin rai Fateeha tace" wannan shine zab'in rai na, masoyayi na, burin zuciya ta, kai da kake da aikin yi bana sanka bazan kuma tab'a auren ka ta, wai kai wanne irin maye ne jarababbe, nace ban san ka, ko dole ne, ana soyayya dole ne?


Zuciyar Ja'afar ta k'ara yin zafi yaji kamar zai mutu, a harzuk'e yace " dolenki ki aure ni Fateeha matuk'ar kina raye ina raye baki da wani miji daya wuce ni, ya kalli Khamal wanda shiru kawai yayi zuciyar sa sai tafasa take, yace " kai kuma katon banza, matsiyaci zaman uwar me kakewa mutane anan, banza sakarai marar zuciya, uban yarinya yace bazai baka 'yarsa ba, amma dayeke kai maye ne ka nace, " dalla Malam rufewa mutane wannan k'azamin bakin naka, kai har zakayi maganar rashin zuciya, maye kawai wanda baison ciwon kansa ba, zuciyar Khamal ta k'ara hasala ganin yadda Fateeha ke ci masa mutunci akan Khamal, kuma yak'i tanka masa, ya kai hannu zai ci kwalar Khamal, cikin zafin nama Fateeha wacce bak'in ciki yayi mata katutu ta zabga masa zafafan mari,gaba d'aya hankalin jama'ar dake zaune yayo kansu, idonta yayi ja ta nuna masa hannu tace " wallahi koda maza sun k'are babu abinda zanyi dakai, ta nuna masa hanyar fita tace " get out from here, kad'an ya rage numfashin Ja'afar ya fizge tsabar firgicin daya shiga, lokaci ya d'auka yana kallanta da mamakinta, yace " ni kika mara akan wannan jakin matsiyancin, a tsawace tace " get out, da k'arfi babu wanda baiji ta ba, kai ya girgiza ya kalli Khamal yace " zaga ni, murmushi Khamal yayi yace " aini d'an gata ne, dan ina damai shigar min, kaga kuwa idan kana mayyi maka kai baka yi, tsaki Fateeha taja, ta rik'o hannun Khamal, sai da ta taka k'afar Ja'afar sunnan suka fice, suka bashi zuciyar sa kamar zata tarwatse.


Bayan kwana biyu zuciyar Ja'afar ta kasa akan abinda ya faru tsakanin shi da Fateeha, duk yadda yaso ya yakice ta daga zuciyar sa amma ya kasa, gashi idan ya kira ta a waya bata picking, babu abinda yake san gani kamar kyakykyawar fuskarta, ya rasa yadda zanyi, dan haka ya shirya a falo ya zauna kasancewar falon ba kowa, ya aika mai aikinsu ta kira amma fir tak'i zuwa, yayi aiken duniya tak'i zuwa, mik'ewa yayi cikin sanyin jiki zai tafi, Dady ne ya shigo falon ganin Ja'afar yasa shi sakin fara'a, da sauri Ja'afar ya nufe shi, ya gaida shi, ya kalle shi yace " yau she kazo, ko har kun gama da Fateehar ne?


Murmushi Ja'afar yayi yace " yanzu nazo ban iske kowa bane shiyasa zan tafi, Dady yace " zauna bari na shiga ciki na turo maka ita, dad'i Ja'afar yaji dan ko bakomai ya ganta koda zaginsa zatayi, murmushi yayi had'e dayi masa godiya, a d'aki ya same ta yace " kije falo Ja'afar yana jiranki kuma minti 2 na baki, idan ba haka ni da ke ne, ya juya, direct kitchen ta nusa, sob'on (zob'o) da Momy ta had'a ta d'auko, ta nufi inda yake zaune, sanye yake cikin farin boyel da gani sabo ne, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta juye masa zob'on a jiki, da sauri ya mik'e yana kallonta ta kalle shi tace " wai kai wanne irin maye ne marar zuciya, ko dai kare ya d'auke maka ne?


Shiru yayi kawai yana kallonta, karka k'ara zuwa gidan mu idan kuma ka sake ka k'ara dawowa wallahi sai nayi maka abinda yafi haka dan harka mutu bazaka manta ba, murmushi yayi yace " ko k'in k'i ko kin so baki da wani miji daya wuce ni, kallon sa tayi shek'ek'e tace " wallahi matuk'ar Khamal yana raye bazan tab'a auren ka ba, a hasale yace " lalle kuwa Khamal zai mutu koda bai shiryawa mutuwar ba, lokacin barin sa duniya yayi, ke da kanki kikace idan baya raye zaki aure ne kinga kuwa dole ya mutu, ke da kanki kin jawo masa mutuwarsa kusa, bakin ki ya jawowa masoyinki mutuwarsa a kwana kusa daga yau daga wannan lokacin ki fara k'irga kwanakinsa na mutuwa, kin jawo masa bala'i sai saka shi kukan mutuwa, sai yayi tsere da mutuwar sa, sai na k'ulla masa *GADAR ZARE*, sai na ya tsani ratuwarsa, sai tsani duniya da abinda ke cikinta, wallahi hatta ke sai ya tsane ki Fateeha, kwalar rigar sa taci ta zaro idanuwa waje tace " wallahi k'arya kake Ja'afar babu abinda zai same shi sai alkhairi, Allah yana tare da, kuma ka sani komai za'a Khamal bazai tab'a tsana ta ba, kamar yadda nima ko rayuwa ta za'a cire min bazan tab'a rabuwa dashi ba.


Dariya ya tuntsure da ita yace " akan wannan lusarin jakin kike wannan haukan, hannu ta d'aga zata kifa masa mari taji caraf an rik'e hannun ta baya, taji saukar wasu fitananun marika, kuncinta ta rik'e ta juya a firgice Dady ta gane tsaye a matuk'ar hasale sai huci yake, kamar mahaukaci zaki ya fara..........



MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/



16


Ya fara k'ok'arin ball da ita, da sauri Momy ta rik'e shi, cikin b'acin rai tace " karka soma dukan min 'ya akan wani katon banza, kai a ganinka Abban Ja'afar zai iya marin d'ansa ne koda kai ya mara?

shima a fusace yace " wallahi Zainab ki fita daga ido na inba haka ba, ranki zaiyi masifar b'aci, "wani kallo Momy tayi masa murya ta a matuk'ar fusace tace " wallahi muddin ina da rai da lafiya a doron k'asa bazan tab'a bari Fateeha ta rayu cikin bak'in ciki ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwar mu da kai, tana karasa fad'ar haka ta kama hannun Fateeha fuuuuuuuuuuuu suka yi ciki, ranta a b'ace zuciyar ta tamkar zata tarwatse.


Bayansu Dady yabi da wani kallo me cike da alajabi da mamaki a hankali kuma ya maida kallon sa ga Ja'afar dake tsaye yana kallonsu cike da takaici zuciyarsa na masa wani irin tsalle tamkar zata basa masa kirji,
muryar Dady a raunane yace " kayi hak'uri Ja'afar kasan yadda halin mata yake, murmushin yak'e Ja'afar yayi domin shi kad'ai yasan yadda yake jin kansa
kana yace " ba komai Dady, sallama suka yi sannan yabar gidan koda yaje gidansu a matuk'ar haukace ya shiga gidan kai tsaye part d'insa ya nufa ya sona cire kayan jikin sa ya bud'e washing machine ya zuba ya soma sintiri a d'akin yana had'a abubuwan da Fateeha take masa akan wani banza cima kwanace marar aikin yi jobless me zaman banza sosai ya dad'e yana zarya da saka da warwarar yadda zai salwantar da Khamal daga duniya kafin daga baya wata idea tazo masa, dariya ya saki , had'i dayin murmurshin mugunta ya ware hannushi duka yana dariyar samun mafuta had'e da shigewa bathroom.



Bayan kwana biyu tafiya takama Dady zuwa Abuja wanda a kalla zai yi kamar sati kafin ya dawo .



Yayin da a hankali kuma tafiyar Khamal Saudia ke k'ara matsowa wanda kwata kwata Fateeha batason tafiyar tashi dan wani lokacin har kuka take masa, ta rasa dalilin dayasa hanklinta yak'i kwanciya akan tafiyar Khamal bayan farin ciki ya kamata yayi, tun daren jiya sukayi da Khamal zai zo gidan su, ganin mahaifin ta baya gari,
ta shigo dashi har parlour bak'i, bayan Khamal ya shiga cikin wata rantsantsiyar shadda gizna, zama yayi a d'aya daga cikin kujerun dake falon, ya kafeta da ido, yayinda hannunta ke cikin nashi, maganar tafiyarsa yake son mata amman baya son abinda zai tada hankalin ta, itama shi take kallo zuciyarta na wani irin bugawa idan akwai abinda tafi so da k'auna a duniya yana bayan Khamal tana yi masa son da ita kanta bata san yadda zata misalta shi ba, a hankali ya bud'e bakinsa yace " Fateeha next week In sha Allah zanbar k'asar nan dan angama komai na tafiyata saboda... tun kan ya k'arasa magnarsa, hawaye suka cicciko sun fara bin fuskarta, zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri ya rud'e,
kasa magana yayi illa jikinsa daya rungumo ta tsam, ya shiga rarrashin ta yana shafa bayanta muryasa a matuk'ar sanyaye yasoma magana " please Fateeha ki natsu ki kwantar da hankalinki wlh kece karfin tafiyar nan tawa ,kusan sbd ke zanyinta domin cigaban rayuwarmu kin dai ji abinda Dad d'inki yake fad'a akaina, ko bakya son cigabanmu ne?
ya k'arasa maganarsa yana sake k'amk'ameta.. muryarta na rawa tace " nifa..nifa bawai tafiyarka ce banaso ba rashin ganinka daba zan dinga yi bane na wani lokaci shine damuwata amman kamin alkwari duk rintse duk wuya bazaka barni ba bazaka juya min baya ba Khamal ina mugun sonka, rayuwata da komai nawa naka ne mallakinka ne Khamal.



Sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan yace " juya miki baya Fateeha tamkar barazana ce ga rayuwata ina miki son da bazan iya barinki b, a hankali ya soma yawo da hannushi asansar jikinta yana romancing din jikinta yana cigaba da magana cikin rawar murya dake fitowa dakyar daga can k'asan mak'ogwaro " Fateeha am not with out you, you are my everythings.


Jin yadda yake magana dakyar a matuk'ar kasalance ne yasata d'ago kai ta kafe shi da ido, idonsa sun kad'a sunyi ja, har lokacin yana yawo da hannunsa a jikinta, ya kashe mata idonsa d'aya, yakai bakinsa nata ya shiga sucking lips d'inta a tare suka lumshe ido, ta soma k'ok'arin zamewa daga jikinsa sbd ganin yadda yake kokarin rud'a mata jiki da salonsa sake rungumo ta tsam-tsam a jikinshi yayi please Fateeha, ki barni yau kawai naji dumin jikinki, da kyar maganar ke fita, joystic d'insa ta mik'e samb'al ya shiga romancing d'inta, ya zira hannushi cikin rigarta ya soma shafa Brest d'inta yana murzawa , da sauri Fateeha ta yunk'ura zata mik'e, cikin zafin nama ya maida ita, yaci gaba da abinda yake, " please please kawai yake cewa, a hankali ya maida bakinsa cikin nata yana tsota, gaba d'ayansu sun gama fita daga haicinsu, gabansa ne yayi muguwar fad'uwa, idonsa ya bud'e take abinda ke faruwa ya fa'do masa, a hankali ya zame jikinsa daga nata, ya d'an matsa baya, sai da akayi 15 minutes babu wanda yayi magana, kunya duk ta ishe Fateeha sai kunne kai take, ta kasa d'ago kai ta kalle shi.



Murmushi Khamal yayi ganin halin da Fateeha ke ciki, mik'ewa yayi yace " ni zan tafi, ba tare data d'ago kai ta kalle shi ba, tace" Allah ya tsare, " dariya yayi yace " ba rakiya, kasa cewa komai tayi, " ok bakin ya mutu ne, shiru bata bashi amsa ba, " bari nazo na bud'e miki shi, ya nufo ta, aiko da gudu ta mik'e tayi cikin gida, bayan ta yabi da kallo yana murmushi.



Daren ranar gaba d'aya kasa runtsawa Fateeha tayi duk inda ta juya Khamal take gani yayinda a k'asan ranta ta dinga jin wani irin feelings d'insa da tunanin abinda ya wakana a tsakanin su , juyi kawai take akan makeken gadonta tana tunanin Khamal.


A b'angaren Khamal shima hkn ce ta kasance dashi dan kwata-kwata bai runtsa ba tunanin Fateeha da surar jikinta kawai yake a hankali ya maida kanshi k'asa had'e da janyo pillow ya rungume tsam ajikinsa yana jin ina ma tana kusa dashi ina ma tafiyar nan da zai yi tare zasuyi kuma a matsayin mata da miji, da shi kadai yasan irin dadin da zai jiyar daita.


A kwana tashi ba wuya a gurin Allah, gashi yau harta kama ranar tafiyar Khamal Saudia, Hajiya da Hamza sun rakoshi har Airport, Fateeha dake gefen sa kuwa sai faman aikin kuka take, Hajiya da Khamal tana faman lallashinta, sosai Fateeha ke kuka harda shashsheka, Khamal ko duk ya rud'e saboda kukan da Fateehar keyi, magana kawai yake yi da jama'a amma gaba d'aya hankalinsa baya kansu, dakyar Hajiya tasa Fateeha tayi shiru, ana kiran su Khamal Fateeha ta k'ara fashewa da kuka dakyar aka b'anb'are ta daga jikin Khamal, suka shiga jirgi, basu bar Airport d'insa sai da suka ga su Khamal sun d'aga.


Sai wajen k'arfe 3:30 na k'asar Saudia su Khamal suka sauka a babban birnin Saudia Riyadh, jirginsu na sauka suka ga dubban jama'a masu taryansu, ba k'aramin dad'i Khamal yaji ba, take yaji hawaye na k'ok'arin zubo masa, jami'an tsaro sai gadin su suke direct hanyar fita suka nufa, duk suka bi layi a inda ake caje kaya kafin kasamu damar shiga k'asa, duk aka gama caje kayan kowa lafiya, amma me ana bod'e jakar Khamal akaci karo da *KOKEN* babu komai acikin jakar face kayan maye, mamaki ne ya cika mai duba kayan, dan ya tabbatar wa da idonsa gaskiyar abinda yake gani, ya mik'e da sauri cikin rawar jiki, da gudu balaraben ya zagayo ya zazzage kayan Khamal a k'asa, yana zazzage kayan yaga KOKEN fal, aiko da k'arfi yace " arrest him!


Kafin Khamal yayi magana dubbun jami'an tsaro sun zagaye shi da bundigogi, cikin tsoro da firgici da mugun tashin hankali yace " wat!!! Koken kuma a kaya na, kafin ka k'ara maganar yaji wayar sa na ringing, cikin firgice ya d'auki wayar, wata mahauciyar dariya Khamal yaji an tinture da ita, cikin rawar murya Khamal yace " waye kai?


" Gaggawar me kake yi hakan ne d'an uwana, ai dan nasar dakai na kira ka, nine *HAMZA D'AN UWANKA* tab!!!!! ai tashin hankalin da Khamal ya shiga yafi na koyaushe, cikin rawar murya yace " why Bro why, sai kuma ya fashe da mahaukacin kuka shima Hamza kukan yake yace " Yaya tun muna yara kake kwace duk abinda nake da burin mallaka, ka fini sa'a Yaya duk wani abu da nake da burin zama ko mallakarsa sai naga kai kake samu Yaya, tun ina da k'arami nake da burin yin suna a duniya sai gashi tun kafin aje ko'ina Yaya kai kayi sunan, ni ko a unguwar mu babu wanda ya sanni, haka a b'angaren karatu ina so ace nake yin 1st position, sai gashi kai keyi, haka da muka zo University nan ma kayi min zarra, bani da wani burin dayafi na karanci Medicine, amma nan ma na fad'i kai ka samu, sai kuma uwa uba FATEEHA, wacce itace macen dana fi a duniya itace nake hauka akanta, a kanta na kamu da ciwon zuciya, itace komai nawa, farin ciki, jin dad'i kwanciyar hankali na duk suna tattare da ita, amma itama sai gashi a kanta kayi min fintin kau, bata ko san kallo na, kai take so bayan ita d'in rayuwa tace.



Kasan meye next target d'ina? shiru Khamal yayi bayyi magana " hmmmmm Hamza yace sannan yace " zan KASHE HAJIYA dan ita kad'ai ce matsalata a yanzu, bayan nan bani da wata sauran matsala, dan nasan hanyar da zanbi wajen mallakar FATEEHA.


" nasan kai yanzu taka ta k'are, kasan meye hukuncinka? Khamal dai ba baka sai kunne, ya zama mutum mutumi kawai, murmushi Hamza yayi yace " hukuncin kisa ne a kanka, dan ina da tabbacin bazaka tab'a barin Saudia da ranka, domin k'asa ce ta musulci da musulmai masu hulunci da Quran, da Hadith, wad'anda basu kai ka laifi ba bama an yanke musu hukuncin kisa bare kai, da aka kama da laifin safarar muyagun kwayoyi, kaga yanzu bani da sauran mak'iyi balle ciwon kai na gama da matsaloli na, dan Fateeha tasan ta yadda zan biyo mata, sai wata rana d'an uwana sai mun had'u a next world



Wata mahaukaciyar k'ara Khamal yasaka had'i buga wayar da bango ta tarwatse, ya tsugunta ya d'ora hannu aka yana kurma ihu yana kukan mutuwa kamar ransa zai fita.........



MOMYN ZARA
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*




17




D'aya daga cikin 'yan sandan ne ya danna wata 'yar k'ararrawa, ba'afi 2 minutes ba saiga dan dazon motocin police sun zo wajen, kama Khamal sukayi suka danna shi cikin mota, sai da sukayi tafiya takai ta 8hrs sannan suka k'araso Shimesi prison, baban gidan yarin dake k'asar saudiyya kenan, nan aka kai Khamal wanda duk wanda ya aikata babban laifi can ake kaishi.


Sosai Khamal ke kukan mutuwa yana ihu kamar ransa zai fita, yace " haba bros bai kamata kayi min haka ba, bai kamata ka nemi hallaka ni akan mace ba, kai d'an uwana ne na jini, kai kad'ai gare ni, duk duniya bani da kowa sama da kai idan dan Fateeha ce meyasa baka sanar dani ba?

" me yasa baka sanar dani itace wacce kake so ba?

"haba my only blood bros, why Hamza?

ya k'ara fashewa da wani irin mahaukacin kuka mai cin rai da tab'a zuciya.



Hamza ko cikin farin ciki ya kashe wayar ya juya fuskarsa d'auke da murmushi, yana juyawa yayi arba da Hajiya wacce tunda ya fara waya da Khamal take tsaye akanshi tana sauraran sa, babu abinda jikinta keyi sai kerrma, gumi ya gama jik'a mata duk ilarin jiki, kamar wacce akayiwa wanka da ruwa, cikin tsoro da firgice take nuna Hamza da yatsan hannunta bakin ta na rawa tace " Ham...za Ham..za.. kai ne kuwa?

" Kai ne ka yiwa d'an uwan ka uwa d'aya uba d'aya haka, Hamza meka fara sha, ?

"mai ya sameka, meke damun Rayuwarka akan mace Hamza?
, kai ta fara girgizawa cikin tashin hankali tana "' a'a wannan bakai bane Hamza , bakaine ainahin Hamza na ba.
, "Hamzan dana sani na rik'a da hannuna jikana ba haka yake ba, murmushi yayi ya tako a hankali har gabanta ya tsaya ya zuba mata ido kana yace " Ok kinji abinda nace kenan?
, cikin tsawa yace " amma duk da kinji kika tsaya a gaba na kina yimin tamboyin banza da wofi tare da surutan iska cikin kuka Hajiya ta rufe shi da duka tace " Allah ya isa tsakani na dakai, bazan tab'a yafe maka ba, dan ba

Please Login or Register in order to submit comment