Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rik'e tana ihuuu, sai da kyar aka b'amb'are daga jikinta aka shigar da ita emergency.


Shak'ar wuyan Mannir yayi yana ihuuu, kwata-kwata baya cikin hayyacinsa da nutsuwarsa ya gama fita daga hankalinsa, ya shak'e shi iya k'arfinsa yana cewa " wallahi idan Zarah ta mutu kai ma sai ka bita, matuk'ar ina raye bazan bar makashin Zarah yaci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai dai nima a kashe ni, kakarin mutuwa Mannir ya shigayi yana kokawar kwace kansa amma ya kasa, Dady da Momy na zaune babu wanda yayi yunk'urin komai balle yayi magana, sai Abban Zarah ne yaje yana k'ok'arin kwace shi, amma ina ya kasa, wani gigitaccen mari Abba ya yarfawa Naseer, a kid'ime Naseer ya saki Mannir yayi kan Abban, ganin Abba ne yasa shi sakinsa da sauri yana yarfa hannu.


Ya durk'ushe a wajen yana kukan mutuwa, gaba d'aya wajen kowa tunanin wannan wanne irin ne Naseer yake yiwa Zarah, duk anyi jugum-jugum a k'ofar emergency room d'in, babu mai cewa k'ala, illa Naseer dake ta faman hawaye yana jin zuciyar sa kamar zata buga.


Iya wuya kam Zarah tasha kamar zata mutu dan sai da ta gwammaci mutuwarta akan ci gaba da rayuwarta, su kan su Doctors d'in sai da suka sha bak'ar wahala kafin su samu numfashinta ya dawo dai-dai, su kansu sun tausaya mata ganin irin bak'ar wuyar dataci, sai akayi 3hrs sannan aka fito da ita, da sauri Naseer ya mik'e ya nufi gadan da ake turata a ciki, yana binsu a baya har suka mayar da ita d'akinta, da sauri Naseer ya k'arasa bakin gadon ya zauna ya rik'o hannunta cikin nasa, kowa ya tsaya cak yana kallan ikon Allah, Doctor ya sauke ajiyar zuciya yace " jininta ne ya hau sosai, kuma tana cikin matsananciyar damuwa ayi k'ok'ari arink'a kwantar mata da hanklinta da zuciyarta nagaf da tab'uwa.


A hankali Zainab taje bakin gadon ta shafa kan Zarah tana hawaye, zuciyarta nayi matuk'ar k'una da tafasa, tana jin k'irjinta kamar zai fashe saboda tsananin zafin dayake yi mata, ita kanta tasan tana tsannin k'aunar Zarah, amma dole tayi nisa da ita, mayar da kallanta tayi wajen Mannir tace " muje, cikin muryar kuka ta kalli Ikram tace " ki tsaya kiyi jinyar 'yar uwarki har ranar za'a sallameta zan sa driver ya kawo miki kayanki da duk abinda kike buk'ata kinji, cikin sanyin jiki Ikram tace " to Momy, dan tana tsananin san Zarah itama a ranta fiye da tunanin.


Harta kai bakin k'ofa ta juyo ta kuma kallan Ikram tace " karki anyi haka kice zakiyiwa Zarah wani abu marar kyau, idan har naji kona gani nida kai na zan kashe ki wallahi, dan har yau har gobe Zarah tananan a zuciyata daram kamar da babu abinda ya ragu dan Zarah bata da uwa sama da ni Zainab ta fad'a kallan saitin Naseer, kuma har bada baza'a tab'a canjawa tuwo suna ba, murmushi Ikram tayi tace " haba Momy yanzu har kina tunanin zan iya yiwa wani abu mummuna, duk duniya fa bani da 'yar uwa ko d'an uwa kamar ta, tare muka taso kamar twice muka sha nono d'aya, Momy Duk duniya Zarah bata da kamar mu muna bamu da wanda yafita duk wanda yake tak'amar yana santa ko sanin ciwonta a bayan mu yake Momy dan munfi kowa sanin zafinta.


Tun daga ranar Momy, Ikram da Naseer ke jinyar Zarah, sai dai ita Momy bata kwana anan da dare take tafiya tabar Ikram da Naseer su kwana da ita, sai da Dady da Abban Zarah suka matsawa Naseer sannan yake tafiya da safe ya dawo da yamma, amma dole ce ta sashi hakan badan yaso ba, tun daga ranar Zainab bata kuma zuwa ba, sai dai kullum sai ta kira wajen sau 10 ta tambayi jikin Zarah, shiko Mannir dama ya gama course d'in daya kai shi Paris dan haka tunda ya dawo bai koma ba, shi Mannir kullum sai yaje asibitin sau biyu da safe idan ya fito zai tafi office sai biya yaga jikin nata haka ma da daddare, amma ko kallansa Naseer bayayi, har gwara Momy da Dady suna amsa masa gaisuwarsa sama-sama, haka kullum Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sai sun zo.


Iya bak'ar wahala kam Zarah na shantashanta dan sau biyu ana fasa kukan mutuwarta, Allah sarki yarinya k'arama amma ta had'u da k'addara mai girman gaske, kullum cikin matsanancin kukan bak'in ciki take da takaicin rayuwarta, duk tayi bak'i ta rame ta lalace kamar ba Zarah ba, kwata-kwata tak'i sausautawa zuciyar ta, Naseer da Ikram na iya bakin k'ok'arin su wajen d'ebe mata kewa da gusar mata da damuwa, yayinda a hankali cikinta keci gaba da girma yana k'ara fituwa kullum yana yawan yi mata motsi wani lokacin ma ko bacci take idan ya motsa sai ta farka.


A haka har akayi wata biyu, jikinta kam yanzu sai dai muce Alhamdulillah, kasancewar akwa ingantacciyar kulawa ta warke, dan har an cire mata d'aurin k'afarta dana hannunta, hannun ya warke sumul sosai, duk inda Mannir yaji mata ciwo ta ya warke babu taso ko d'aya illa k'afarta da har yanzu da saura dan kwata-kwata bata iya taka ta, doctor yace next week za'a fara koya mata tafiya da abin koya tafiya, sab'anin hannun daya warke sosai kamar bata tab'a karyewa a hannun ba dan ko tabo babu babu abinda bata iyawa da hannunta kamar dai yadda ta saba a baya.


Haka ma a b'angaren damuwa ta d'an rage kad'an dan zamu iya cewa ba laifin tunda yanzu tana samu tayi hira dasu Momy, Ikram, musamman kuma Naseer data sawa ranta duk duniya babu mai santa kamar shi, ta rage kukan da take yawan yi sab'anin da, da'indai bacci ba bacci takeyi ba to tana cikin aikin kuka 24hrs, amma yanzu har murmushi take yi sosai.


A hankali jikin Zarah yaci gaba da samun sauk'i sosai, yayinda Naseer ke koya mata tafiya, hankali cikin ikon Allah yanzu tana iya tafiya da sandar ita kad'ai batare da an rik'e ta ba, tana iya yin komai da kanta har zuwa tailed da bathroom tayi wanka ko kashi tayi sallah, yanzu babu abinda akeyi mata da kanta take komai, haka ma abinci tana ci sosai kasancewar cikin jikinta mai sa cin abinci sosai ne, dan yanzu cikin Zarah yana da wata bakwai.



Yau ma kamar kullum Naseer na zaune a gefen Zarah, Momy nakan sallaya, Ikram na kallan wani a MBC Bollywood ta tattara hankalinta gaba d'aya wajen kallanta, Naseer ya kalli Zarah yana murmushi yace " yanzu kina da 3 months a asibitin nan, gashi doctor yace " zaki kai har nan da next month, anya bazaki gaji bakuwa, da naso na matsa masa dole sai ya sallame ki, saboda na fuskanci kun k'usa da zaman hospital, martanin murmushin ta mayar masa had'i da cewa " ku baku gani da d'awainiya dani ba sai ni zan gaji da zaman asibitin, zune ya kamata ku gaji da wahala dani ai, da sauri ya d'ora hannunshi akan lips d'inta had'i cewa " shhhhhhhhhh karna kuma jin kince muna zamu gaji dake ko muna wahala dake kinji ko?


Kai ta d'aga masa alamar eh, cikin sanyi murya tace " uncle kayi hak'uri idan na b'ata maka ban kumawa, murmushi yayi had'i da jan hancinta yace " ai baki laifin a wajen Uncle d'inki, dariya tayi tace " ina godiya Uncle, haka dai sukayi ta hira cikin jin dad'i da annashu yayinda gaba d'aya hankalin Momy na kansu, tana satar kallan su.


BAYAN WATA D'AYA


Kwanci tashi asarar mai rai, rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, yau watan Zarah hud'u cif-cif a asibiti tana jinya yayinda cikinta ke da wata takwas, ta warke sumul babu abinda yake damunta, ko ciwon kai bata ji, tana cikin k'oshin tafiya sai dai d'an abinda ba'a rasa ba namai juna biyu musamman kuma mai tsohon cikin wata takwas yama shiga wata na tara, lafiya lau take tafiyarta kamar da bata ko d'ingishi, haka jikinta babu tabo ko kwarzane, ta dawo normal kamar da, yadda kasan ba itace tasha jinya har ta wata hud'u ba, cikin ikon Allah Zarah ta dawo kamar da, sai dai har lokacin tana cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa gami da takaicin duniya musamman idan ta kalli cikin jikinta ta tuna yau ita ke d'auke da cikin shege kuma cikin shegen ma wanda ba'a san uban sa balle asalinsa ba, sai taji gaba d'aya ta tsani kanta da duniyar gaba d'aya.


Tun tana jin kunya tana b'oye-b'oyen cikin harta gaji ta daina ma, tunda shi ciki d'an duma ne da kansa yake bayyana kansa, ta d'auki damuwar duniya ta d'orawa kanta tayi mugun bak'i ta rame, har zuciyarta ma ta k'ek'ashe ta bushe rak'ayau ta daina kuka sai na zuci dan su kansu hawayen sun bushe, sun k'afe sun gaji da zubowa.


D'aukar da takardar sallama Doctor ya shigo yana fara'a ya mik'awa Naseer yace " yau dai mun sallamar maka MATARKA mun huta da rigimarka sai kuma an dawo mana haihuwa, dan su ma'aikatan asibitin tsammanin su Naseer mijin Zarah ne, satar kallan Zarah Naseer yayi dan yaga reaction d'inta aka ci sa'a kuwa itama shi take kallo had'i da zaro ida waje kamar zasu fad'i k'asa.


Murmushi Naseer yayi had'i cewa " ah wallahi kun huta fa, Doctor ya kalli Zara yace " to maman biyu Allah ya raba lafiya, sai kinzo haihuwa murmushin yak'e Zarah batare datace komai ba, Dady, Momy, Mannir, Alhaji Abdullahi, Abban Zarah, Ikram duk suna wajen, gaba d'aya suka fito wajen harabar motoci Zarah tayi tsaye ta rasa wacce zata shiga dan tana tsoran karta yiwa Naseer laifi, dan tasan halinsa.


Kuma ma bata isa ta nufi motar Mannir batare da izinin Naseer ko Dady ba, su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suna tsaye suna kallan ikon Allah, suna so suga hukuncin da Dady zai yanke, kallan Zarah Dady yayi yace " ki shiga motar Naseer, ya kalli Naseer yace " ka kawo ta gida na, da hanzari Mannir yace " Dady na d'auka gida zan wuce dasu, wata muguwar harara Dady ya watsawa Mannir data hana shi k'ara cewa komai, da sauri Ikram tace " Dady nima Zarah zanbi, "ok jeki shiga motar Naseer ku taho tare, cewar Dady yana shiga mota had'i da bawa driver umarnin tafiya.


Sosai hukuncin Dady yayiwa su Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dad'i har ran su, bare kuma oga Naseer da ji yayi kamar Dady ya mallaka masa duniyar gaba d'aya saboda tsananin farin ciki da jin dad'i, Naseer bai wuce dasu Zarah gida kai tsaye ba sai da ya biya dasu yawo sosai dan d'ebewa Zarah kewar zaman datayi a hospital, kuma yasanta da shegen san yawon tsiya, bai mayar dasu gida ba sai dare shima lura da yayi Zarah ta gaji kasancewarta mai tsohon ciki, sun tarar Momy da kanta tayi girki ta shirya dinning batare data saka 'yan aiki sunyi mata ba, acwarta na tarar Zarah ne, bedroom d'aya Momy ta basu ita da Ikram dan tasan idan aka warewa Zarah bedroom ita kad'ai Naseer damunta zayyi ya hanata sakewa, amma idan yana ganin idan Ikram zai rink'a rage wani abun kodan ita badan su ba, tunda ta lura yana d'an jin kunyar Ikram d'in.


Sai da sukayi wanda da sallah sannan suka fito falo suka tarar da Momy, Naseer, Dady gaba d'aya su ake jira aci abinci Momy tace bamai ci sai Zarah tazo dan ita tayi girkin,cikin shagwab'a Naseer yace " kai Momy ni da Dady ba duk yunwa muke ji, murmushi tayi had'i da cewa " to sai ka tashi ai gata nan ta fito, dariya yayi yana kallan Zarah yace " yau Momy tayi mana horan yunwa saboda ke, ta hana mu cin abinci wai sai kin zo, murmushi kawai tayi batare datace komai ba, Momy tace " to Bissimillah, gaba d'aya suka nufi dining table, cikin kwanciyar hankali suke cin abincin su yayinda Naseer keta aikin tsokanar Zarah yana janta da hira, tana bashi amsa sama-sama.


Mannir na komawa gida Aunty Zainab ta tare shi da sauri dan ta k'agu taji yadda takaya, murmushi had'i da tallabo fuskarta ya zaunar da ita akan sofa shima ya zauna a kusa da ita, idansa cikin nata yake kallan ta, cikin mutuwar jiki ya girgiza mata kai, da sauri tace " ban fahimta ba please ka bud'e baki kayi min bayani yadda zan gane, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace " an sallami Zarah yau daga hospital kuma ta warke sumul kamar bata tab'a yin ciwo ba, da hanzari tace " tana ina ya ban gan ku tare ba?


Cikin mutuwar jiki yace " Dady ya hana ta biyo ni, dan ko kallanta bayyi ba balle ya saurari ni, daga nan ya kwashe duk yadda sukayi da Dady ya fad'a mata, a hankali tace " cikin ya zube ko yana jikinta har yanzu? sai da yayi d'an jimmmmm kafin yace " Zainab ina cikin zashi, yanan mana a jikinta sai ma girma dayayi sosai, dan ina tunanin ma ta kusa haihuwa, dak'arfi da runtse idanuwanta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da k'arfi yayinda k'irjinta yayi mata mugun nauyi, Mannir zai sake magana tayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu.


Ita kanta tasan yanzu kwata-kwata bata k'aunar ganin Zarah, ta rasa meyasa take jin ta tsane ta a ranta, saboda bazata iya ganinta d'auke da cikin shege ba yasa har Zarah ta gama zamanta a hospital bata tab'a zuwa dan zuciyarta bazata iya jurewa hakan ba.


Kullum kuma koyaushe Naseer na tare da Zarah 24hrs yana tare da ita baya matsawa konan dacan musamman ma yanzu da cikinta ya shiga watan haihuwa, dan yanzu jiran haihuwa suke ko yaushe, cikinta ya tsufa sosai ta zama, zama dakyar tashi dakyar, kullum Naseer yana kusa da ita baya matsawa konan da can, dan ko fita zayyi tare dasu yake fita, kuma kullum sai ya raba dare a d'akin su kafin ya tafi, haka da asubar fari yake zuwa duba su, sosai Momy da Dady ke bata kulawa tamkar 'yar cikin su da suka tsugunna suka haifa, a b'angaren Mannir ma kullum sai yazo gidan sau biyu ganin Zarah, sosai Zarah kejin dad'in zuwansa, dan ta saki jiki dashi sosai kamar da, bata tab'a nuna masa wani abu ko fuska na cewar yayi mata laifi ba, asalima itake bala'in jin kunyar sa, idan bai zo ba har waya take masa ta tambaye dalili.


Kullum yazo sai ta tambaye shi Momyn ta, dan sosai take kewar Zainab, tana san ganinta dan dai babu yadda zatayi ne, tasan duk ranar data furta haka rai ran Naseer da Dady yayi masifar b'aci, sosai take yiwa Mannir kukan tana san ganin Momynta, duk sanda yazo sai rok'e shi akan ya bawa Zainab hak'uri dan tasan har yanzu fishi take da ita, babu yadda Mannir bayyi akan Zainab taje taga Zarah ko sau d'aya ne ba amma tak'i.


Yau ma kamar kullum Mannir ya gama shirinsa tsaf zai je duba Zarah, yazo zai wuce ta parlor Zainab tace " ina zaka haka kake ta sauri? "zani duba 'ya ta ne, ga mamakinsa sai yaji tace " zani da sauri ya kalli inda take, bata saurare shi ba, taje ta sako hijab ta iske shi a parlor tace " muje ko?, batare daya ce komai ba ya wuce tana binshi a waya.


A parlor suka iske Momy, Dady, Naseer da Zarah, Ikram zaune, jin sallamar Mannir yasa Zarah mik'ewa dakyar tana cewa " Dady yau ma Momy bata zo ba ko, har yanzu tana fushi dani akan abinda ni kai na ban san asalinsa ba ko? tayi maganar hawaye na zubo mata, har lokacin Zarah na masifar son Mannir da Zainab, kuma ko sau d'aya bata tab'a ganin laifin d'ayan su ba, tana jin su a ranta kamar a baya dan babu abinda ya ragu daga san da take yi musu, kuma tana d'aukar su a matsayin iyayenta, data kallansu a matsayin duk duniya bata da kamar su, hab'arta Mannir ya kama ya d'ago kanta yana murmushi yayinda yake yi mata nuni da bakin k'ofar parlor.


Zainab ta hango tsaye tana kallanta idanta yana zubar da hawaye da sauri Zarah ta saki Mannir ta nufi Zainab tana tafiyar dakyar, tana k'arasawa ta rungume Zainab had'i da sakin rikitaccen kuka mai ban tausayi, tana cewa " Momy kiyi hak'uri ki yafe min wallahi nima ban san asalin cikin nan na jikina ba, Momy har rantsuwa nayi miki da Qur'an dan ki yarda dani amma har yanzu kin k'i yafe min balle ki fahimce ni, Momy kin san fushin iyaye ba k'aramin bala'i bane ga rayuwar d'a, Naseer yayi dan har a lokacin babu wanda yake yiwa magana tsakanin Mannir da Zainab, yana k'ok'arin mik'ewa yaji Zainab cikin kuka tace " bazan tab'a yafewa masik'in da yayi miki cikin nan ba wallahi ko waye shi tayi maganar tana kallan Naseer, murmushi had'i da girgiza kansa ya mik'e yayi shigewarsa d'aki a hankali Zainab ta b'anb'are Zarah daga jikinta niyyar yi mata magana tayi arba da turtsetsen cikin Zarah wanda kwata-kwata bata lura dashi ba sai lokacin, take taji zuciyar ta tayi mata bak'i k'irin k'irjinta ya fara yi mata zafi yana tafasa yayinda mak'ogwaronta ya shiga yi mata k'una take taji tsanar Zarah ta sake dirar mata zuciyar ta, da sauri ta hankad'ata baya, Zarah tayi baya taga-taga zata fad'i Naseer yayi saurin tare ta,take idanuwanta sukajyi jajir kamar gauta cikin zafin rai ta nuna Zarah da yatsanta tace " Allah ya isa tsakani dake Zarah, bazan tab'a yafe miki ba, kin cuce ni kin tozarta ni a idan duniya kin wulak'antar da duk tarbiyyar dana baki.


A matuk'ar hasale, zuciyar sa nayi masa tururin zafi gami da rad'ad'i cikin k'onar zuciya ya je daf da Zainab ta yadda suna iya jiyo numfashin juna ya d'aga hannu zai yarfa mata mari yaji anyi sauri rik'e masa hannu ta baya yana juyawa yaga Zarah a matuk'ar hasale tana kalan shi ido cikin ido babu alamar tsoro ko fargaba a zuciye cikin matsanancin b'acin ta. d'aga hannunta ta.................




MOMYN ZARAH


```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




51




Ta nuna shi da d'an yatsanta cikin kakkausar murya tace " karka soma, karka fara, a gaba na ka marar min uwa, sannan ka saran zanci gaba da huld'a dakai ko ganin mutuncinka, Naseer bari kaji idan ma baka sani gwara sani duk duniyar nan bani da kamarsu bani da wanda suka fisu a waje na, duk wanda yake so a bayan su yake, haka duk wani mahaluk'i dake duniya dazan so kona saba dasu a bayan su.


" Har yau har gobe suna nan a matsayin su babu abinda ya canja ko ya ragu daga yadda suke a zuciya sai ma abinda ya k'aru, har wa yau ina kallan su da mutunci da k'ima had'i da darajar da ba kowanne d'an Adam nake gani da ita ba, har kullum, ina nan ina ci gaba da kallan su a matsayin iyaye na, kuma har k'arshen rayuwata zanci gaba da yi musu wannan kallan, duk abinda ya faru a tsakani ko zai faru nan gaba babu ruwanka, kar ka kuma shiga, su kashe ni in sun so.


" Ni nayi musu laifi na kuma cancan duk wani hukunci daga gare su a matsayina na 'yar su, sannan na cancanci fiye da haka a yadda suke kalla na a matsayin MAZINACIYA (My new novel) masik'a suna iya yin min hukunci mai tsananin gaske san ran su, tun ABU A DUHU (my upcoming novel) ne, babu wanda GASKIYAR AL'AMARI (my novel ) balle yayi min adalci.


" Idan suna ganin irin tarbiyyar da suka bani kenan, suna iya yi min komai tunda duk abinda zanyi musu dan su fahince ni su kuma yarda nayi musu, har rantsuwa nayi musu da mafi girma da darajar littafi Qur'an, amma sunk'i gaskata ni, duk duniya bani da kamar su sune mutane na farko daya kamata su fahince ni su kuma gaskata ni, amma sunyi watsi dani da lamura na, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai cin rai kai daga jin sa kasan kuka bak'in ciki da takaicin rayuwa ne, Naseer zayyi magana tayi saurin dakatar dashi tace " please Uncle karka ce komai, bana san ka shiga tsakanin dan kana da baban matsayi a waje na, wanda idan ka d'auke Momy da Dady bani da tamkarka.


Wani irin sanyin dad'i Naseer yaji ya ziyarci duk wata gab'a dake jikinsa, a hankali ya fara jin duk wani k'unci da bak'in cikin dayake ciki ya fara gushewa yana rikid'ewa izuwa farin matsanancin farin ciki marar misaltuwa, murmushi yayi yana kallan fuskar Zarah da ita shi take kalla ido cikin ido, yace " da gaske Zarah ina da wani matsayi da daban a wajen ki, sansayan murmushi ta sakar masa had'i da lumshe idanuwanta dake zubar hawaye ta bud'e su sauke su akan shi tace " Uncle bama a waje na kad'ai ba har ga zuciya ta da rayuwata duka kana da babban matsayi na musamman, kai ka zame min tamkar d'an uwan da muke ciki d'aya uwa d'aya uba d'aya, ka maye min gurbin wad'anda na rasa, sannan ya sanya farin ciki marar misaltuwa ga rayuwata, ka maye min gurbin bak'in ciki da damuwar dake ciki da farin ciki.


Naseer ka so ni a lokacin da kowa ya k'ini, ya tausaya min a lokacin dana rasa tausayawar kowa, ka yarda dani alaokacin kowa yak'i yarda da aminta da ni, a tsayawa rayuwata a lokacin dana rasa gata, ka zame min uwa da ubana lokacin da suka guje ni, ka kusance ni a lokacin da duk duniya ke guduna, lokacin da wad'anda nafi so nafi kusa dasu suka k'i ni, Naseer zame zan iya saka maka, wallahi da ina da ikon cire zuciya ta da rai na dana dad'e da cirewa na mallaka maka su kyauta, dariya Zainab ta tuntsere da ita tana tafa hannu, cikin isa da tak'ama ta tako har gaban su tace.


"Weldon Mr Naseer and Mrs Zarah Naseer Mustapha, gaskiya kun matuk'ar iya wasa kwaikwayo, da tsantsar rainin hankali sannan da wasa da zukutan al'umma, kun yi matuk'ar rainawa kanku hankali, idan zaku iya yin wasa da zukatan mutane kusa su raunana izuwa gare ku to ku sani banda Zainab Muhammad (da sunan Abban Zarah take amfani shiyasa tace Muhammad sab'anin tace Abdullahi ) domin ni kasan kai na ina da wayo da hankali gami da lura, na dad'e da wucewa da tunaninku balle sanin ku, sannan nasan ainahin kalar ku, nasan su waye ku, bayan ka d'irka mata ciki kazo kana rainawa duniya da mutanen cikinta masu k'aramar kwakwalwa irinka tunani.


" Kana wani pretending kamar mutumin kirki kai wai ga na Allah, mazinaci fasik'i kawai, Naseer koda kowa bazai yarda da cewar cikin dake jikin Zarah naka bane, kai kan kasani cewar ni nasan cikin naka ne, sannan koda duniya zata yarda da wannan wasan kwaykwayon naka kasan ni tar kuma k'arrr nake kallanka, ko da ita Zarah bata sani ba bakuma ta yarda cikin jikinta naka bane, amma akwai lokaci na nan zuwa wanda da kansa zai tabbatar mana da GASKIYAR AL'AMARI, ABU A DUHU ya fito fili, SIRRIN B'OYE ya bayyana kowa gani ya sani.



" Sannan sai muga ta wasan kwaykwayo kuma ko naga a lokacin wanne wasa kuma zaka juya, inga ta inda zaka kuma b'ullo da tsabagen tsagwaron rainin hankalinka, duk wani mahaluk'i dake duniyar nan matuk'ar yasan EL-MUSTAPHA FAMILY yasa koyaya aka had'a jini dasu sai mutu yayi CINDO gami da MARK a gefen cikinsa ina nan ina jiran lokaci da kuma ranar da ABU A DUHU zayya bayyana, sai muga

Please Login or Register in order to submit comment