Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hula, hunnan sa manne da agogo, sosai yayi mata kyau, sosai taji dad'in ganinsa, b'ata face tayi, ta kauda kai had'i dayin tsaki, murmushi yayi, ya kafe mashin d'in yazo kusa da ita ya zauna, mik'ewa tayi ta fara tafiya, murmushi ya kuma yi sannan ya mik'e ya hau mashin d'insa a gabanta yaje ya tsaya yace " mu tafi ko?


Kallansa tayi tace " ce maka akayi kai nake jira? "A'a yace, please ki hau mu tafi, kinga yamma tayi, tafiyar ta taci gaba da tafiya, binta ya rink'a yi yana daga kan mashin d'in, sai da lallab'a ta sosai sannan ta hau ya kaita gida, sosai Khamal yayi mamakin ganin gidan su, saboda babban gida ne, da gane kasan 'yar masu hali ce, sauka tayi bata ce masa komai ta shige gida, da sauri ya kalle ta yace " haba ke kuwa ya ba godiya, juyowa tayi ta sakar masa k'ayataccen murmushi, suman tsaye Khamal, harta shege gida bai sani ba.



*MOMYN ZARA*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



12


Da yamma Khamal ya shirya ya d'au fitinannan wanka ya nufi gidan su Fateeha a bakin get yayi faki ya kwankwasa mai gadi ya lek'o yace " lafiya Malam? " lafiya dan Allah yimin magana da Fateeha, kallansa mai gadin yayi cike da mamaki yace " kunyi da ita zaka zo ne? "Eh cewar Khamal, " ita Fateeha ce da kanta ta baka izinin? Cike da k'osawa Khamal yace " nace maka eh, kai mai gadin ya jinjina sannan yace " ikon Allah, da mamaki Khamal ya kalle shi yace " ya akayi ne?


Murmushi mai gadin yayi yace " abin ne ya bani mamaki, " mamaki kuma? cewar Khamal, " eh kasancewar yau ne rana ta farko dana ga hakan, dan kwata-kwata Fateeha bata kula samari, tun Fateeha tana yarinya nake aiki a nan gidan amma ban tab'a ganin wanda yazo yace yana sallama da ita ba sai kai yau.


Murmushin jin dad'i Khamal yayi yace " Alhamdulillah, da sallama ya shiga falon ya iske Fateeha da Momy zaune suna aikin kallon, tare suka amsa masa sallamar tasa, Hajiya k'arama ana sallama dake, ido ta zaro tace " ni? Momy ko saboda tsabar mamaki ta kasa cewa komai, dan tasan halin Fateeha duk wanda yace yana santa tsiyatsiya suke rabuwa, da kallon Fateeha kawai take da Mamaki, Fateeha tace " je kace bata zuwa, har mai gadi yayi nisa sai tunaninta ya bata Kodai Khamal ne?


Aiko bata san sanda ta kwala mai kira ba, tace " ce ne waye? Dawowa yayi yace " wai yace " Khamal ne, bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cike da murna tace " shigo dashi d'akin bak'i, murmushi mai gadi yayi dan yasan bata isa tak'i amincewa Khamal ba, dan duk tak'amar kyan da takeyi Khamal ya fita, mai aikin su ta kira ta sata ta kaiwa Khamal ruwa da lemo.


Ita dai Momy shiru tayi tan kallon ikon Allah, aranta kuwa cewa take wannan wanne mai sa'ar ne? d'aki ta koma ta shirya cikin riga da zani na atamfa, ta shafa farar hoda da lip glo, ta saka takalmi da mayafi 2 match ta feshe ilahirin jikinta da perfumes, ta nufi falo cike da farin ciki, da d'okin ganin sa, ita dai Momy ido kawai ta zuba, tana ganin ikon Allah.


A zaune ta same shi, da sallama ta shiga, a d'aya daga cikin kujerun ta zauna, kallon ta yayi his face with smile, yace " kinyi kyau, face ta ya mutsa tace " wannan itace kalmarka mafi tsada? murmushi yayi dan ya fahimci Fateeha ba k'aramar 'yar rainin hankali bace, hira suka d'an tab'a sama-sama tana yi tana bashi amsar rainin hankali, dakyar ta bashi phone number ta, harta kai bakin k'ofa zata fita yace " ya b aki bani amsa ta ba, juyowa tayi tana d'an yamotsa fuska tace " amsar me? "nace I love you, but u didn't reply me, tsaki ta d'an ja ta fita, mik'ewa yayi yana murmushi ya fita, k'ofar dayaga ta shiga yabi da kallo yana 'yar dariya, a hankali ta da fuskarta ta sakar mishi murmushi, dariya yayi mata yana cusa hannunsa cikin sumar kansa.


A hankali ta motsa bakinta tace " I love you too, sai tin zuciyar sa ya dafe yana yi mata dariya marar sauti, haka kowannensu ya koma gida cike da farin ciki, da dare bayan ya gama duk abinda ya saba kan ya kwanta, sannan yayi dialing number ta, sai da yayi mata 2miss call, sannan ta d'aga, " waye abinda ta fara cewa kenan, murmushi yayi mai sauti yace " ur hubby, " what my hubby? ni bana da wani hubby, please waye? " ok Khamal ne, " wanne Khamal kenan, ni ban san wani Khamal ba, sai da ta gama raina masa hankali, sannan suka tsunduma hirar soyayya, ranar kowannen su yayi kwanan farin ciki.

Washe gari bayan sun tashi daga lactures, a gajiye likis ta fito tana ta had'a hanya, a gabanta yayi parking fuskarsa d'auke da murmushi yace " mu tafi ko? ba k'aramin kyau yayi mata ba dan haka bata san sanda ta sakar mishi murmushi ba, ba musu ta hau, suka tafi, a k'ofar gida ya sauke ta, sai da suka d'an tab'a hira sannan ta shiga gida, tun daga harabar gidan su take jiyo hirar mutane a falo, da sallama ta shiga falon Dady ta gani tare da Ja'afar d'an aminin Dady, ya dad'e baya Nigeria, a Malaysia yake karatun, lokacin dayake Nigeria he is her Best friend, da har iyayen su suna expecting soyayya suke, wacce ita a zaton Fateeha shak'uwa ce kawai ace shi a b'angaren sa, bahagon so yake yiwa Fateeha tun suna yara yake mata mugun so, da sauri ya mik'e ya nufe ta da murna, itama cikin farin ciki tace " Ja'afar yau she ka dawo? " yau dawowa ta kenan ko abinci ban ci ba nace bari na zo naga my Fatee nasan yanzu ta girma, cikin shagwab'a tace " amma shene ko ka gaya min, " sorry my Fatee so nake nayi surprising naki ne, " to yanzu nasan dai baka ci komai ba, ban some minutes in sha na d'an watsa ruwa, nayi sallah na fito sai na girka maka best food dinka, Dady ko baki har kunne sai fara'a yake, " ok yace, da sauri ta shige d'aki.



Wacece Fateeha

'Ya ce ga Alhaji Nasir, tsohon soja ne dan har ya kai matsayin mojor general kafin yayi retired, Hajiya Zainab ita kad'ai ce matar sa auren zumunci iyayen su suka yi musu, Hajiya Zainab macece mai hak'uri da kawaici, Alhaji Nasir mutum ne mai zafi yana da fad'a da kafiya, Fateeha ita ce kad'ai 'yar sa suka haifa, bayan ita Allah bai k'ara basu haihuwa ba, dan haka ta taso cikin gata da kulawa, amma duk da haka sun bata cikekkiyar tarbiyya, hakan bai sa sun saketa ko sun barta ta sangarce ba.


Daf da magrib Fateeha ta fito daga d'aki tace " bari nayi sauri na d'an sama maka wani abun ko, tasowa yayi ya nufe ta yana dariya yace " no ki raka ni restaurant kawai, naga lokaci ya k'ure, " haba Jafy ka kadawo yau d'in amma ka ci abincin restaurant? " eh bakomai yunwa nake ji sosai muje kawai gobe sai kiyi min girkin kinji please, " ok tace ta shiga d'aki ta d'auko hijab ta zira suka tafi, da kallo Dady yabi su yana murmushi yace " Allah ya nuna mana lokaci, " Hmmmm Momy tace.


A round about Khamal ya gansu danja ta tsaida su, gabansa ne ya fad'i, nan da nan yaji wani mugun kishi ya taso masa musamman yadda ya gansu tana zaune a gaban mota yayi dashi kuma yake zaune a mazaunin driver gaba d'aya ya karkata hankalinsa gare ta, sai dariya suke, danja na fasu hannu yabi bayan su, a Food Palace Ja'afar yayi parking, ya zagaya ya bud'e mata murfin motar, suka jera suka shiga, duk abinda ke faruwa akan idon Khamal, in banda tafasa babu abinda zuciyar sa keyi, parking shima yayi ya shiga a zaune ya hango su, gurinsu ya nufa d'aya daga cikin kujerun wajen yaja ya zauna ya sakar mata wani fitinan nan murmushi.


Ido ta zaru tana kallonsa, alama tayi masa daya tashi, dariya yayi yace " ai da kika kira ni a waya kikace mu had'u anan nayi mamaki kasancewar a gida muka saba had'uwa, ya k'arashe magana yana kashe mata ido d'aya, zatayi magana service din gurin yazo ya fara gabatar musu da abinda suka bada Oder, gyaran murya Ja'afar yayi,.
Shima Khamal yayi kamar bai san yana zaune ba.


Kallon Ja'afar Khamal yayi ya mik'a masa hannu fuska d'auke da fara'a yace " sorry ban lura da kai ba, kasan idan ina tare da my heart mantawa nake da kai na ma, shima fuska d'auke da dariya yace " gaskiya kam, murmushi tayi tace " Khamal wannan cousin d'ina ne sunan shi Ja'afar, ta kalli Ja'afar tace " wannan ne Khamal, shagwab'e face Khamal yayi yace " baki gaya masa waye ni ba, ta bud'e baki zatayi magana yayi sauri ya tare dan yasan tana iya bada shi yace " bari kawai basai kin wahalar min da bakin ba zan gaya mishi ya kalli Ja'afar yace " nine mijinta wanda zata aura very soon in sha Allah, yak'e Ja'afar yayi yace " masha Allah, sanin halinta ne yasa shi mik'ewa tun kafin ta kunya ta shi, ya rik'o hannunta a hankali yayi mishi kiss, ya kashe mata ido d'aya, yayi kamar yayi mata rad'a a kunne sannan yace " I love you too sweetheart, yayi saurin ficewa, itako mamaki ne ya hanata cewa komai.


Tasan tsabar kishi ne ke yawo da Khamal shine yasa shi yin hakan, kasa cin abincin Ja'afar yayi, ko a mota sama-sama sukayi hira, a falo suka tarar da Momy da Dady zaune, kusa da Dady Ja'afar ya zauna, ya kasa cewa komai Dady ne ya lura da yanayinsa dan haka yace " lafiya dai, kaci abincin? " eh Dady dan har Khamal ma ya yazo, " waye kuma Khamal? cewar Dady " nima ban san shi ba, Fateeha ce tayi masa waya ya same mu acan, sai sannan Dady ya gane dalilin canjawar Ja'afar murmushi yayi sannan ya kalli Fateeha yace " waye shi? Dariya tayi tace " Dady wani ne kawai ta fad'a tana mik'ewa, shiru Dady yayi baice mata komai ba, ta shige d'aki tabar Ja'afar anan yana ta faman kumbure-kumbure.


Sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta rink'a shiga tsananin Fateeha da Khamal, had'i da muguwar shak'uwa, sosai suke mugun son junan su, ji suke kamar d'ayan su bazai iya rayuwa babu d'aya ba, kullum suna tare, idan ko suna gida to suna tare a waya, sunyiwa junansu mummunan sabo da juna, yayi da Ja'afar ke ta haukan son Fateeha dan ji yake kamar yayi hauka, sosai ya fara fita daga hankalinsa, kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa, duk ya zama wane iri iyayensa sun kasa gane kansa, haka ma a b'angaren Hamza kwata-kwata yarinyar da yake so tak'i kula shi, yayi yin duniya amma taki bashi koda fuska ce, duk ya rud'e ya shiga matsanciyar damuwa ya rame yayi bak'i ya gode, ko abinci baya iya ci, sosai Khamal ya shiga cikin muguwar damuwa saboda halin da Hamza yake ciki, gashi yak'i nuna masa yarinyar.


Hatta Hajiya kakarsu tana cikin damuwa sakamakon ganin Hamza cikin muguwar damuwa, duk sun tada hankalin su, sosai Khamal ke kwantar mishi da hankali had'i da fad'a masa in sha Allah zai mallaketa.


Ganin irin mawuyacin halin da Ja'afar ke cikine yasa iyayen sa tsare shi a d'aki, ganin a koyaushe suna iya rasa shi, da gaf yake da jefa kansa a halaka, Umman sa ta zauna kusa dashi tana shafa kansa, Abban sa yana gefe a zaune, Abban sa ya kalle shi yace " Son meke damunka ne, munyi munyi ka sanar damu damuwarka amma kak'i bayan kasan duk duniya babu wani mahaluk'i daya cancanci sanin matsalarka sama damu, ka sanar mana idan muna da abinda zamu taimaka maka zamuyi iya k'ok'arin mu dan ganin mun magance maka matsalarka, shiru yayi baice komai ba, a hankali Ummansa ta shiga lallashinsa, tana k'ara kwantar mishi da hankali had'i dayi mushi magiya akan ya sanar dasu damuwar shi, shiru yayi yana tuna sanda Fateeha take fad'a masa irin mugun son da take yiwa Khamal har ce mishi tayi idan ta rasa Khamal tasan rayuwarta bata da wani amfani bayan lokaci kad'an zata bar duniya.


Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tuna irin maganganun Fateeha akan haukan son da take yiwa Khamal, gashi kuma iyayen sa sun saka shi gaba akan sai ya sanar dasu damuwar shi, yasan kuma idan bai sanar dasu ba, ran su zai iya b'aci, ba kuma zasu jure ganin sa cikin wannan yanayin ba, suna iya shiga matsala, dan haka ya yanke shawarar sanar dasu, a hankali ya furta " Fateeha ce damuwata, cikin zubar hawaye yake magana " wallahi Abba ina mugun son ta, akanta zan iyayin komai, zan iya mutuwa saboda da ita wallahi Umma da in rasa ta gwamma na rasa komai ciki kuwa harda rayuwa ta, sosai yake kuka yana sambatu akan Fateeha wanda shi baima san yanayi ba, murmushi Abbansa yayi yace " da akan wannan ka tsaya kana damun kanka?

"Karka damu kaji Son Dadyn ta ya dad'e dayi min maganar mu had'a ku aure nine nace kar muyi muku haka mu bare sai mun dai-daita kanku, da shi yaso ma tun kana Malaysia ayi auren, "Abba me yasa kak'i daka sani daka bari anyi, kanshi Umman shi ta shafa tace " kwantar da hankalinka Son koyan zuma lokaci bai k'ure ba, ko gobe kake son a d'aura auren ku za'a d'aura, " eh wallahi Umma na yarda a d'aura goben ma, maganar yake amma kwata-kwata baya cikin hayyacin sa, " don Allah Umma ina nema na rasa ta, ta fara mugun son wani, nan ya kwashe komai dake tsakanin Khamal da Fateeha ya sanar dasu " karka damu kaji Son wallahi koda zan k'arar da abinda na mallaka a duniya zan k'arar dan ganin farin cikin ka da walwalarka sun dawo, wallahi zanyi komai dan ganin ka mallake ta kaji Son, karka damu, maza tashi kaje kayi wanka kazo dining muna jiranka, " please ku taimaka Abba, " nace karka damu gobe iyanzu Fateeha tana a matsayin matarka kaji, ya mik'e ya shiga bathroom, suka bishi da kallo cike da tausayawa, Abba ya kalli Umma yace " wallahi bazan tab'a bari nayi asarar tilon d'a na ba, ko kisa ne ya kama nayi zanyi, saboda farin cikin sa.........



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*


13



Da mamaki Umman Ja'afar ke Abban tace " Alhaji komai fa kace? "Eh kamar yadda kikaji nace komai to ina nufin komai, cikin sanyin jiki tace " Allah ya kyauta, a fusace yace " Amin ya fita, da daddare Abba ya shirya, ya kalli Umma dake zaune a gefe yace " zani wajen Alhaji Nasir kan maganar yaran nan, " Allah yasa a dace tace, " zama a dace, ya fice, kasancewar tun da rana ya sanar da Dadyn Fateeha zuwan sa, hakan ne yasa Dady sanin da zuwan nasa, dan haka bai fita ko'ina ba ya tsaya jiran abokin nasa.


A harajar gidan Abba yayi parking, waya ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Nasir ya sanar dashi zuwansa, fuskarsa cike da fara'a ya fito tarbar abikin nasa, juna suka rungume cike da murnar ganin juna, a falo suka zauna, bayan sun gama gaisawa ne Abba ya sanar da Alhaji Nasir dalilin zuwansa, cikin farin ciki Alhaji Nadir yace " Alhamdulillah dama na dad'e ina da burin ganin mun had'a yaran mu auren, Allah ya sani ina da mafarkin hakan a raina, in sha Allah babu wata matsala, na amince na yarda na bawa Ja'afar auren 'yata Fateeha, ai ko bani kai mai d'aurawa Fateeha aure ne da wanda kaga dama.


Shima Abba cikin murna yace " to Alhamdulillah dama nasan baza'a samu wata matsala ba, amma gaskiya kar abin yaja lokaci nan da sati biyu ayi bikin kawai mu huta, " badamuwa in sha Allah, cikin fargaba Abba yace " wani hanzari ba gudu ba, " to lafiya cewar Alhaji nasir, " eh to lafiya sai dai ba lau ba, " ya kayi Alhaji Nasir ya kum tambayar sa, " shi Ja'afar ya sanar da ni cewar akwai wanda yake zuwa wajen ita Fateeha.


Shiru Alhaji Nasir yayi sai can kuma yace " kai gaskiya ban sani ba, amma zan bincika naji koma meye, tattaunawa suka k'arayi daga basani sukayiwa juna sallama har bakin mota Dady ya rako Abba, sannan Abba yaja motarsa ya tafi, cike da murna Dady ya nufi wajen Momy, a zaune ya iske ta ita kad'ai a falonta, kusa da ita ya zauna ya fara sanar da ita dalilin zuwan Abba,ya kuma shaida mata har sun yanke rana nan da 2weeks, shiru tayi bata ce komai ba, sai kuma ya k'ara da cewa " amma shi Ja'afar yace kamar akwai mai zuwa wajenta ko?


Shiru ta kuma yi tana d'an nazari sai daga basani tace " nima dai bani da tabbas amma ina tsammanin haka, " kamar ya baki da tabbas kuma kina tsammani a matsayinki na uwa, wacce kike zaune waje d'aya da ita, ke ya kamata kefi kowa sani, hakkin kine kula da lamuranta, shiru dai tayi bata ce komai ba, haka ya gama zuba masifarsa ya tashi ya tafi, da kallo kawai ta bishi dan inda sabo ta saba da halinsa.



Washe gari da yamma lik'is Khamal ya sauke Fateeha a k'ofar gidan su, Dady na sama yana kallon su, sai suka kusan 1hr a tsaye suna hira cikin so da k'aunar junansu sai dariya suke, kowa ya gansu a haka yasan akwai mugun soyayya a wajen ba k'arya, sallama Khamal yayi mata ya tafi ita kuma ta shiga gida, bayan tayi wanka tayi sallah, ta falo dan wata muguwar yunwa take ji, Momy ta hango zaune a dining ita da Dady nufar wajen tayi ta zaune bayan tayi sallama ta gaida iyayen nata.


Fuska babu yabo babu fallasa Dady ya amsa mata, itako Momy fuska a sake ta amsa mata, abincin suke ci babu mai yiwa wani magana, sai da ya kammala ya mik'e, ya kalli Fateeha yace " idan kin gama ina son maga dake, ya wuce bai jira amsata ba.


Kallon Momy tayi tace " lafiya Mom, naga Dady ya canja duk ya zama wani iri? " hmmm nima ban sani ba idan kinje kyaji, sama-sama ta gama cin abincin, d'akinta ta nufa kasancewar an kira sallar magrib, sai da kammal komai sannan ta nufi saman Dadyn, da sallama a bakin ta ta shiga d'akin, kansa nakan jarida bai d'ago ya kalle ta ba yace " kira min Momyn ki, " to ta tace, ta mik'e ta tafi kiran Momyn tare suka shigo, kusa da Momy Fateeha ta zauna.


Kallonta yayi yace " waye wannan wanda naganku d'azu tare? , murmushi tayi tace " sunansa Khamal, "d'an ina ne, kuma su waye iyayen sa, sannan meye alak'arku dashi? babu wani tsoro ko fargaba a tare da ita tace " a unguwar rimi yake, sannan a school d'in yake, amma shi ya gama, service ma zashi, amma ban san su waye iayens ba, ido ya k'ura mata yace " nace meye alak'arku? shiru tayi nad'an wani lokaci, a hankali ta furta soyayya muke, " kina sanshi? ba tare da wani b'ata lokaci ba tace " eh Dady.


" Momynki bata fad'a miki na dad'e dayi miki miji ba? " what! ta fad'a a razane, cikin tashin hankali tace " miji Dady? " Eh na dad'e da bawa Ja'afar ke, "wanne Ja'afar d'in ta fad'a ciki razana, " Ja'afar dai wanda kika sani, jiya ma Abbansa yazo muka saka ranar auren ku nan da 2 weeks, wani mahaukacin kuka tasa tace " wallahi Dady bana san shi, Khamal nake so, Khamal ne rayuwa ta idan kuka raba ni Khamal wallahi Dady mutuwa zanyi, shine rayuwa , shi kad'ai nake so, wallahi da in auri Ja'afar gwara na mutu ba aure, Khamal ne........ wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata yace " ke kin isa ince ga abinda zakiyi kice a'a, wallahi ko kin k'i ko kin so Ja'afar ne mijinki, sai dai ki mutu, cikin kuka tace " to wallahi Dady kuna gaf da sarani, dan wallahi sai dai ya auri gawata, wasu mahaukatan marika ya zuba mata, wallahi sai dai ki mutu, kuka ta k'ara fashewa dashi tayi waje da gudu, sai da Momy ta tabbatar Fateeha ta tafi sannan ta mik'e ta kalli Dady tace.


"Zan iya jurar komai amma banda bazan iya jure tauyewa Fateeha hakkin ta, duk wani hali naka na jure shi shekara da shekaru, amma akan wannan wallahi duk inda za'aje sai dai aje, shi akan farin cikin d'an yake komai amma kai ka zab'i musmugunawa rayuwar tilon 'yarka akan farin cikin d'an wani, tsawa ya dakawa Momy ya kalle ta ido cikin ido idonja sun canja zuwa ha, ya nuna mata hannu yace " wallahi kome zakuyi sai dai kuyi, amma nagama yanke hukunci, yayi shigewarsa d'aki.


Tana komawa d'aki ta shige ta rufe k'ofa, ta fad'a gado ta saki sabin kuka mai cin rai,Abban Ja'afar kuwa yana komawa gida, ya sanar da Ja'afar da Umman sa, ihu Ja'afar ya saka ya daka uban tsalle ya rungume Abban yana yi masa godiya, yayi d'aki da gudu ya fad'a kan bed, yana murna da farin ciki, ya rungume filo yata sak'e-sak'e yana sakin murmushi.


Khamal na komawa gida ya iske mummunan tashin hankali, dan Hamza ne yake ta suma had'i da aman jini guda, yana sandarewa kamar zai mutu, cikin Firgici ya k'arasa inda Hajiya ta rungume Hamza tana ta faman kuka, yana ganin Khamal ya saki kuka ya kalle shi yace " Yaya tace bata so na, wai tana da wanda take so kuka shi zata aura, wai shine rayuwarta, wallahi Yaya idan ban same ta ba mutuwa zanyi, rayuwata tana cikin had'ari Yaya, ita ce rayuwata, itace farin ciki na, ya k'arasa maganar yana mik'awa Khamal hannu yayin da bakinsa keta bulbulal da jini guda guda.


Kuka sosai Khamal ya saka ya rasa meke yi mai dad'i a rayuwarsa, baiyi magana ba ya sangumi Hamza yayi asibiti dashi a hanya ma sosai Hamza ke kuka yana sambatu, shima Khamal kukan yake har ya k'arasa dashi hospital, da saurki aka karb'e shi aka shigar dashi emergency, a k'ofar emergency room d'in Khamal ya tsaya sai zarya yake yana zubar hawaye, sai da akayi 1hr sannan Dr ya fito.


Kallon Khamal yayi yace " muje office, a hanzarce yabi yabansa, bayan sun shiga ya nunawa Khamal wajen zama yace " bismillah, zama yayi jiki ba kwari, kallon sa Dr yayi yace " gaskiya rayuwar Hamza tana cikin matsala dan zuciyarsa tayi mugun tab'owa, yana cikin matsanciyar damuwa, ya kamata ku kula dashi sosai, amma zai kwana biyu anan idan komai ya dai-daita zamu sallame shi, ga wad'annan magungunan ka siya, bayan ya siyo maganin ne ya dawo

Please Login or Register in order to submit comment