Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaji k'addarar wani kalar jarabawar wani kai sai kayi sujjada ka godewa Allah saboda taka ba komai bace,
kuma haka suke ci gaba da rayuwar su suna ci masu godewa mahaliccin su,
kai ma kazama d'aya daga cikin masu godewa Allah a duk hali da yanayin rayuwar da ka tsinci kanka please,
kar ka zama d'aya daga cikin masu yiwa Allah butulci dan ya jarrabe imanin ka,
ni dai abu d'aya na sani shine duk abinda kaga Allah yayi,
to akwai dalilin yinsa dan Allah baya tab'a yin abu babu dalili.


Wani irin mugun tausayinsu ne ya kama Dady da Momy, a hankali Dady yaje inda suke,
ya dafa kafad'ar su had'i da rad'awa Naseer ka kai su gida,
ba musu Naseer ya kama hannun Mannir yana yima Zarah alama data kamo Zainab,
tun da suka shiga mota babu mai yiwa wani magana har suka isa gida,
suna isa harabar tun kafin motar ta gama tsayawa Zainab ta bud'e ta fito da gudu tayi cikin gida,
jikin Mannir a sanyaye shima ya fito yabi bayanta,
Zarah tana k'ok'arin bin bayan su Naseer yayi saurin rik'o ta had'i da cewa "ina zaki?


Cikin muryar kuka tace " binsu cikin gidan zanyi,
kai ya girgiza mata had'i da cewa "no ki bar su suna b'ukatar privacy,
batare data kuma cewa komai ba ta koma ta zauna tana share hawayen dake zubo mata,
ganin yadda take zubar da hawaye yasa hankalin Naseer yayi masifar tashi,
dan bak'aramin d'aga masa hankali kukan nata yake ba,
yana jin kukan ta har cikin k'ok'on ransa da zuciyarsa,
a hankali Naseer ya jawo ta jikinsa ya rungume, yana shafa kanta,
abinka dama damai jiran kad'an sai ta k'ara faahewa da kukan,
yana san ya rarrashe ta amma bai san ta ina zai soma magana ba,
bai san mai zai ce mata ba, shi kan shi zuciyarsa a karya take,
cikin kuka Zarah tace " mu kuma irin tamu k'adarar kenan haihuwar shegun yara,
ni na fara haifa yanzu gashi nan Momy da Ikram ma,
yanzu haka zamuyi ta haihuwar 'ya'yan zina?


Wani irin mugun b'acin rai Naseer yaji, take kalar idansa ta canja ta koma red,
gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa da kerrrna,
cikin matsanancin b'acin rai Naseer yayi ma motar key ya fige ta a guje yayi waje,
yadda yake tsala gudu yasa Zarah d'ago kai ta kalle,
ganin yadda idansa da yanayinsa suka canza yasa ta fahimtar ransa ya b'aci abinka dama damai bak'ar zuciya,
yana d'ago ido karaf suka had'a ido da ita, saurin d'auke idansa yayi daga kanta,
cikin sanyin murya Zarah tace " please kayi hak'uri idan na b'ata maka rai,
murmushi yayi mata batare daya ce komai ya mayar da kansa wajen tuk'i.


Zainab na shiga gidan direct bedroom d'inta ta wuce ta fad'a kan bed,
had'i da sakin kukan bak'in ciki, jikin Mannir a sanyaye ya shigo d'akin,
tsayawa yayi had'i da rungume hannunsa a k'irjinsa yana hawaye,
cikin muryar kuka Zainab tace " abinda muka shafe shekara da shekaru muna nema bamu samu ba amma sai gashi lokaci d'aya k'addara ta bamu,
a k'alla munkai 18yrs muna rok'on Allah akan ya bamu haihuwa,,
Allah bai nufa ba, bai bamu ba amma..... sai kuma tayi shiru dan batasan abinda zata ce ba,
tsaye kawai yayi yana kallanta ya rasa abinda zaice.


Sai da Ikram tayi wata guda cur a hospital sannan aka sallame ta lokacin cikin ta yakai wata biyar,
gidan Dady ta koma, yayinda da Zarah keta aikin lallab'ata ta rarrashinta had'i da bata hak'uri,
tana kuma k'ara nuna mata ta yarda da k'addara,
to Alhamdulillah dan Ikram akwai tawakkali da dangana,
ta d'auki k'addararta ta runguma hannu bibbiyu,
tana rayuwarta kamar ba komai,
yadda kasan bata cikin d'umbin b'akin ciki mai tarin yawa da nadamar rayuwa,
yayinda Zainab da Mannir suke cikin k'unci da matsanancin bak'in ciki,
kullum cikin kuka suke,
Mannir ya shigo bedroom d'in Zainab ya iske ta kwance tana aikin kuka,
a hankali ya tsuguma a bakin gadon, dan yanzu baya iya zama saboda ciwon dake jikinsa,
"Zainab ya kira sunanta cikin sanyin murya,
bata d'ago ba amma ta tsaida kukanta,
magana yaci gaba da yi " yanzu Zainab bazaki hak'ura ki d'auki k'addara ba, bazaki sakawa zuciyar ki salama da dangana ba?


" Ki duba Ikram 'yarki ta cikin ki yadda ta yarda da tata k'addarar amma ke da girmaki da komai sai abu kike irin na yara,
kamar wara k'aramar yarinya,
cikin kuka Zainab tace " wannan dalilin ne yasa ni nake kukan,
Ikram yarinya ce k'arama bata san ciwon kanta ba har yanzu,
amma ni tsofai-tsofai dani har da jikoki a ganni da ciki,
cikin ma na shege, haba Mannir taya za'ayi hankalina ya kwanta na samu nutsuwa dan Allah?


"Ni wallahi na gwamci mutuwa ta da wannan bak'ar rayuwar,
cikin kuka ta d'aga hannu sama tace " ya Allah ya Ubangijin al'arshe, ya Ubangijin sammai da k'assai Allah na rok'e dan darajar fiyayyan halitta ka kawo sadaniyyar rabuwata da cikin nan,
Allah idan abinda nayiwa Zarah ne Allah na tuba, Allah dan darajar fiyayyan halitta ka rabani da cikin nan kar ka bani ikon haihuwar sa ya Ubangiji ta k'arasa maganar cikin kuka,
can k'asan mak'ogwaro Mannir yace " Amin,
sosai Mannir ya rarrashe ta ya bata hak'uri, sannan ya lallab'a ta shiga wanka shi kuma ya koma parlor,
bayan Zainab ta gama wankan tazo fitowa tana taka step santsin tail ya kwashe ta,
tayi sama sannan ta fad'o akan cikin, wata irin gigitacciyar k'ara ta saki had'i da zubewa k'asa a sume,
da guda Mannir dake parlor ya nufo bedroom d'in, a kid'ime ya sure ta yayi hospital da ita,
da sauri Nurses suka karb'e ta suka yi Emergency da ita,
sai da akayi wajen 2hrs sannan Doctor ya fito,
da sauri Mannir ya tare shi yana tambayarsa abinda ke faruwa,
d'an b'ata fuska Doctor d'in yayi kafin yace " I'm so sorry cikin dake jikinta ya zube har ma munyi mata wankin ciki,
suman tsaye Mannir yayi saboda tsananin murna da farin ciki,
Doctor dayaga haka tsammanin sa ko shock Mannir yayi saboda bak'in ciki,
a hankali ya dafa kafad'arsa had'i da cewa " am so sorry, ga d'akin da aka kai ta can yayi maganar yana nuna masa wani d'aki,
da sauri Mannir ya shiga d'akin, ido biyu ya samu Zainab, yana isa gareta ya rungume had'i da fad'in " Alhamdulillah Allah maji rok'on bawan sane, Allah ya amshi addu'ar mu,
murmushi Zainab tayi ,
sosai sukayi farin ciki da zamubewa cikin,
sai dare Mannir ya sanarwa Dady da Momy, Naseer Zainab na hospital kuma cikin ya zube har ma anyi mata wankin ciki,
kowa yayi murna da zubewar cikin musamman Zarah da Ikram.


Haka dai rayuwa taita tafiya har cikin Ikram ya shiga watan haihuwa,
duk wanda ya ganta yasan ta canja gaba d'aya kamanninta sun sauya ta zama wata iri kalar tausayi,
kullum cikin addu'a take Allah ya raba ta da abinda ke cikinta lafiya dan wani irin yanayi take ji a jikinta,
jikinta yana bata kamar lokacin ta yayi, kamar bazata rayu da abinda zata haifa,
tun da cikin Ikram ya shiga watan haihuwa Zarah ta koma kwana a bedroom d'in ta,
kuma iya k'ok'arin ta wajen kwantar mata da hankali,
yayinda ciwo ya gama cin jikin Mannir sosai har ya kai ga ya kwantar dashi,
gaba d'aya al'aurarsa ta gama rub'ewa,
babu yadda bayyi da Zainab ta koma gidan su momy ko gidan su,
amma fir tak'i tace idan mutuwa ce sai dai tazo ta d'auke su tare,
amma matsawar yana raye bata tab'a barinsa duk irin mawuyacin halin dazai shiga,
tana tare dashi rai da rai mutuwa ce kawai zata raba su,
saboda warin da Mannir yake yi duk ma'aikatan gidan sun gudu,
har sabon mai gadi da su kayi ya kasa zama dan warin yana kaiwa har bakin get,
yanzu idan babu kowa daga shi sai matarsa Zainab.


Cikin dare Ikram ta tashi da matsananciyar nak'uda ganin ta fara zubar da jini yasa tayi muguwar tsorata,
a kid'ime ta tada Zarah daga bacci, itama Zarah tana farkawa taga jini hankalinta yayi mugun tashi,
da gudu ta fita daga bedroom d'in tama mantataga ita sai rigar bacci kanta ko d'an kwalli babu,
tun daga parlor take kwalawa Naseer kira,
duk gidan suka fito a kid'ime da gudu Dady da Naseer su kayi bedroom d'in,
da sauri Dady ya sungumi Ikram yayi habarar gidan wajen motor park,
Zarah na niyyar fita harabar gidan a haka Naseer yayi sauri rik'o ya danna a bedroom yace " baki da hankaline ji fa a yadda kike amma kina k'ok'arin fita a haka,
sai loakcin ta tuna a yadda take, da sauri ta canja kayan jikinta ta zura doguwar rigar atamfa,
ta sungumi Nailah tayi waje da gudu har tana tuntub'e zata fad'i,
cikin zafin nama Naseer ya rik'e ta had'i cewa " control mana Mrs Naseer,
Naseer ya ja motar, tun a mota Dady ya kira Mannir da Zainab ya sanar dasu,
suma cikin tashin hankali suka nufo asibitin.


Ana shiga da Ikram Emergency Doctor ya fito da hanzarinsa,
dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka k'araso,
kallan su Doctor yayi yace " Babyn a bakin mahaifa yake dole sai dai ayi mata CS a ciro abinda ke cikinta,
yayi maganar yana mik'a musu takadar dasu saka hannu,
kasa karb'ar paper Mannir yayi sai Dady ne ya amsa yayi signing,
da hanzari Doctor ya amsa ya koma ciki,
sai da akayi a k'alla 4hrs akafin Doctor ya fito,
sunan zaune a bakin theater room suna ta zarya masu addu'a nayi,
suna ganin Doctor Naseer yayi saurin mik'ewa ya tare shi,
ya bud'e baki zayyi magana Nurse ta fita da Baby a hannunta tana tsala kuka,
da sauri Zarah ta mik'e ta amshi Babyn,
murmushi Doctor yayi sannan yace " anyi aikin cikin sa'a ga Baby girl nan an samu,
Baby fara sol mai kama da Ikram sak kamar an tsaga kara,
sai kuka take tana wawure-wawuren nono, tana kai hannu bakin ta,
murmushi Zarah tayi tana kallon Babyn hawaye na zubo mata,
Nurse d'ince tace " muje na kai ku d'akin da aka kai mamanta,
daga bakin tagar d'akin ta nuna musu ita kuma ta koma,
jiki a sanyaye suka shiga suka iske Ikram tana bacci,
Momy ta mik'a hannu ta amshi Baby, ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " ikon Allah,
a hankali ta mik'ewa Dady Babyn addu'a Dady yayi mata sannan ya mik'e ma Zainab,
kamar bazata amsa ba, zai kuma ta karb'a, ido ta k'ura mata tana ganin tsananin kamar yarinyar da Ikram sosai,
da yadda kasan lokacin da Ikram tana jaririya, take taji hawaye ya taru a idanta ,
da sauri ta mik'ewa Mannir dake tsaye,
hannunsa na rawa ya amsa shima yayi mata addu'a.


A hankali Ikram ta bud'e idanta ta fara bin jama'ar dake d'akin da kallo,
hannu ta mik'ewa Zarah da sauri Zarah ta k'arasa bakin gadon, had'i da mik'a mata Babyn,
murmushin k'arfin hali Ikram tayi sannan ta amshi Babyn,
ta k'ura mata ido na wani lokaci kafin tace " Allah ya isan mu tsakanin mu da mahaifinki daya samar dake ta wannan hanyar,
Allah yayi mana sakayya ni dake daya kasance d'an fashi,
Allah ya shiryar dake a bisa turba ta gaskiya, Allah ya baki ikon gane gaskiya,
gaskiya ce ya kuma baki ikon binta,
Allah ya baki ikon gane k'arya,
k'arya ce ya kuma baki ikon kauce mata,
Allah yasa kina cikin salihan bayi wad'anda Annabi zayyi alfahari dasu ranar alk'iya,
Allah yayi miki albarka ya sanya haske a rayuwarki ya tsareki daga dukkan abin k'i,
a hankali ta mik'ewa Zarah Babyn had'i da cewa gata ki kula min da ita,
bazan ce na baki ita amana ba, dan nasan zaki kula da ita kamar yadda zaki kula da rayuwar yaranki,
dan girman Allah kar wanda ya sanar da ita asalinta da kuma hanyar da aka same ta,
ku dai sanar da ita Mamanta ta rasu kodan ta rink'a yi min addu'a,
a hankali ta juya wajen Naseer tayi mishi murmushi tace " Uncle nasan zaku kular min da ita sosai, kuma nagode Allah yasaka muku da alkhairi, yabar zumunci,
ta juya wajen Zainab da Mannir tana murmushi tace " Momy, Dady please ku yafe min idan nayi muku wani laifi koda akan rashin sani ne,
ina matuk'ar san ku, ina san ganin ku cikin farin ciki, ta kalli Momy da Dadyn Naseer tace " grandfa please kuma ku yafe min,
kuma dukkan ku kular da Baby na dan Allah,
ta k'arasa maganar tana hawaye.


Kowa ka gani a d'akin jikinsa yayi mugun yin sanyi,
Zainab, Mannir, Zarah sai kuka suke,
a hankali Zarah da Zainab suka fad'a jikin Ikram, Zainab tace " ya kika magana irin haka kamar wacce zata bar duniya please ki dai na bada wasiyya keda kanki zaki raini 'yar ki,
murmushin k'arfin hali Ikram ta kuma yi,
tace " na sani Momy mutuwa zanyi,
a hankali Mannir ya tako gabanta yasa hannu yana shafa kanta hawaye na zuba daga idansa yace " bazaki mutu ba Ikram,
kanta ta d'aga a hankali ta kalle shi tayi mishi murmushi tace " please ni dai Dady kona mutu kar kuyi min kuka,
kar ku d'aga hankalin ku dan Allah.


Ta bud'e baki zata kuma magana, ta fara tari sai jini kafin kace me idanuwanta sun kakkafe,
da gudu Mannir da Zainab suka fita kiran Doctor,
Dady da Momy, Naseer da Zarah suka rirrik'e ta suna kiran sunanta,
a hankali Ikram tayi kalmar shahada,
kafin jikinta ya saki, ido Naseer ya runtse da k'arfi had'i da ja baya a kid'ime,
Dady yasa hannu ya rufe mata idanuwanta dake kallan sama tana murmushi,
a gigice Zarah tace " Dady meke faruwa?


Cikin rawar baki yace " ta rasu,
wata irin k'ara Zarah tayi had'i da sulalewa k'asa sumammiya,
dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka dawo daga kiran Doctor,
da sauri Doctor ya k'arasa yayi 'yan dube-dubensa,
ganin ta mutu yasa shi ja mata bed shirt ya rufe ta, cikin mutuwar jiki,
wani mahaukacin kuka Zainab ta saka tana jijjiga Ikram had'i da kiran sunanta,
taimakon gaggawa aka bawa Zarah,
sannan ta farfad'o cikin matsanancin kuka,
Mannir yayi kuka sosai kamar ransa zai fita,
yana ji yana gani aka shirya Ikram aka kaita makwancinta,
yayinda Zarah ke rungume da Babyn tana faman kukan,
bayan andawo daga kai Ikram Naseer yayiwa Babyn hudubaa da sunan Mamanta Hafsat ana kiranta IKRAM d'in,
sosai Mannir ya shiga dawo hankali shi yayi mugun nadama,
ranar sadakar bayan an gama zaman makoki,
yace yana san magana da Abban Zarah, Naseer, Zainab, Alhaji Abdullahi, Momyn sa da Dadynsa.


A babban parlor'n gidan dake sama aka hallara, yayinda Mannir keta aikin kukan cike da matsananciyar nadama,
bayan duk kowa ya zauna akayi shiru ana jiran Mannir, ganin bashi da niyyar magana ne yasa Dady cewa " Mannir kayi magana ka tara mutane kuma kayi shiru kak'i cewa komai,
a hankali Mannir ya mik'e yaje gaban Zarah ya zube, ya durk'usa ya kasa cewa komai sai kukan dayake kamar ransa zai fita,
Momy tace " Mannir kayi magana mana,
kasa magana yayi illa kallan Zarah da yaci gaba dayi yana kuka,
tsawa Dady ya daka masa cikin b'acin rai yace " karka mai da mutane sakarkaru mana,
idan bazakayi magana ba mu tashi,
still shiru Mannir yayi yana ci gaba da kallan Zarah yana kuka,
tsaki Dady yayi ya mik'e a fusace yana k'ok'arin barin wajen,
da sauri Mannir yace " kayi hak'uri Dady zanyi magana,
komawa Dady yayi ya zauna cike da tausayin Mannir,
k'ara fashewa Mannir yayi da kuka mai tsanani,
yana kallan Zarah, cikin kuka yace ".............





MOMYN ZARAH


```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*






74





Cikin matsanancin kuka yace " please.... sai kuma yayi shiru, ya kasa cewa komai,
sosai Dady ya hasala, cikin b'acin rai Dady ya daka mishi tsawa had'iwa cewa " Mannir karka kuma bari na kuma yin magana,
bai kalli inda Dady yake ba, ya kalli Zarah cikin ido na kamar seconds 15 sannan ya duk'ar da kansa k'asa,
ita dai Zarah shiru tayi tana kallansa batare data ce komai ba, duk ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari,
k'asa da kai Mannir ya k'ara,sannan cikin rawar muryar yace " nasan duk wad'an nan abubuwan da suke samu na a rayuwa yana da nasaba da abinda nayi miki ne,
na tabbatar iftila'in da suke fad'a min, ni da iyali nasaboda ke ne Zarah,
dan nasan babu wani abu da nayi marar kyau a rayuwata da Allah zai azabtar dani,
azabtarwa mai tsanani face abinda nayi miki, kuma wallahi nasan kad'an na gani, ban ga komai ba, matuk'ar ban rok'ek'i yafiya ba,
wannan ya tabbatar min da yanzu tun a duniya ake yin hisabi ba sai anje ko'ina ba (lahira),
idan kayi abin alkhairi tun a duniya zaka gani, haka ma idan kayi sharran,
saboda abinda ni kad'ai nayi miki, iyalai na sai had'uwa suke da iftila,
a gaban ido na akayiwa matata da 'yata fyad'e, kuma duk suka d'auki ciki,
Ikram ta haifi shege kamar yadda kema kika haifa,saboda kema 'yar wani ce, kuma matar wani ce, k'anwar wani ce,
yayar wani ce, sannan mahaifiyar wani ce,
sannan daga k'arshe ta mutu kamar yadda na buk'ata akan ki,
tabbas zancen Allah baya tashi dayace " duk wanda yayi ZINA da 'yar wani, sai shima anyi da 'yarsa
idan kuma bashi da 'ya ayi da matarsa,
idan bashi da mata ayi da mahaifiyarsa,
idan bashi da mahaifiya sai anyi da k'anwarsa,
saboda itama wacce yayi da ita matar wani ce, 'yar wani ce, mahaifiyar wani ce, sannan k'anwar wani ce.


Cikin rawar muryar Zainab tace " Mannir me... me.... ka...ke....nu...fi?


Tayi maganar idanta tarrr akansa,
murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, kai da ganin murmushin kasan na tsananin b'akin ciki ne,
mai cike da tsantsar nadamar rayuwa,
Zainab ta bud'e baki zata kuma yin magana yayi saurin cewa " please Zainab kiyi shiru, har in kai inda nake san na kai, nasan idan nakai inda k'arshen magana ta zaki fahimci abinda nake nufi,
cikin sanyin murya Zainab tace " amma..... bai bari ta k'arasa ba ya d'aga mata hannu had'i da cewa " please Zainab yau rana ce ta jin kunya a gare ni, rana ce ta wulank'anta!, tozarta sannan ta k'ank'anta,
da in bari naji kunyar lahira, na kuma ci gaba da tsintar abinda na shuka gwara na fad'a koda duk duniya zasu k'i ni,
su kuma juya min baya, Zainab kiyi hak'uri nasan nayi miki laifi mai girman gaske wanda nasan da matuk'ar wuya ki yafe min,
cikin sanyin murya yace " na aikata laifi mai girma, mai matuk'ar munin gaske.


A tsorace Dady yace " what Mannir, me ka aikata haka?


K'ara k'ask'antar da kansa yayi a gaban Zarah yana kuka yace " please Zarah ki dubi girman Allah ki yafe min,
ki tuna ko Allah ma muna yi masa laifi amma ya yafe mana,
Zarah idan baki yafe min ba, wallahi na shiga uku na rink'a ganin bala'i kala-kala kenan har k'arshen rayuwa ta,
cikin tsawa Dady yace " wai uban me ka aikata mata da kake rok'onta yafiya?


Da k'arfi Mannir yace " saboda NA'EEM D'ANA NE, BA D'AN NASEER BA,
I'm his biological father,
gaba d'aya parlorn mik'ewa sukayi tsaye amma banda Zainab data kasa motsi saboda tsananin firgici da kid'ima,
haka ma Zarah bata iya mik'ewa ba, saboda tashin hankalin data shiga,
cikin rawar murya Zarah tace " Dady kasan me kake cewa kuwa?


" Eh Zarah nasan me nake cewa, kuma ni ne kad'ai nasan gaskiyar al'amari,
da sauri Zainab ta mik'e ta nufi inda yake cikin matsanancin tashin hankali tace " Mannir baka cikin hankali ka,
wallahi baka cikin hayyaci da nutsuwarka, kwata-kwata baka san abinda kake cewa ba,
zafin ciwon dake jikinka ya fara tab'a maka kwakwalwa,
ya fara haukata ka,,
a hankali yasa hannu ya zame ruk'on data yiwa rigarsa had'i da cewa " lafiya ta lau Zainab,
babu wani zafin ciwo ko gushewar hankali a tattare dani,
balle lalacewar kwakwalwa,
ki koma ki zauna yanzu zan warware miki zare da abawa,
ya k'arasa maganar hawaye na zuboasa,
ya bud'e baki zai kuma yin magana yaji tauuuuuuuuuu tassssssss,
Dady ya kifa mishi gigitattun marika, wanda sai da suka saka Mannir hantsilawa,
cikin matsanancin b'acin rai Dady ya nuna shi da hannu yace " yaushe ka fara shaye-shaye?
da har zaka tara mu kana yi mana maganar banza,
a cikin mu akwai sa'anka, da zaka tara mu kana yi mana zancen banza zancen wofi,
shege d'an iska sakarai shashasha,
hawayen dake zuba masa yasa hannu ya goge kafin yace " Dady bana shan komai, ba kuma zancen banza nake ba,
wallahi tallahi Dady gaskiya nake fad'a muku,
na gwammaci karb'ar kowanne irin hukunci tun a duniya, kafin na mutu na had'u mahaliccina,
Momy da Naseer ido kawai suka zuba masa batare da sun iya cewa komai ba,
Abban Zarah kuwa kai ya duk'ar k'asa yana sak'a abubuwa da yawa a ransa,
gyaran murya mahaifin Abban Zarah yayi sannan yace " kowa ya koma ya zauna,
ba musu kowa ya koma ya zaune da yake duk ya girmewa kowa a wajen nesa ba kusa ba,
sai da kowa ya zauna sannan ya mayar da kallansa ga Mannir yace " fad'a mana ta ya akayi Na'eem ya zama d'anka,
d'an shiru Mannir yayi kafin yace.


" Tun Zarah na yarinya k'arama Allah ya jarrabe ni da mugun santa,
amma so ba irin wanda kuka san ina yi mata shi ba, so irin na masoya, so irin na aure shi nake yiwa Zarah,
na dad'e ina dakon so da tsatsan soyayyarta, wanda ban tabbatarwa kai na da santa nake da gaske ba,
sai lokacin da Naseer ma ya fara santa, lokacin da Zainab tazo min da maganar na shiga tashin hankali iya tashin hankaki,
amma na danne na kuma b'oye ainahin abinda yake rai na game da ita,
dan gudun abinda zaije ya dawo, nayi iya yina dan ganin na cire ta a raina saboda nasaba mai k'arfi dake tsakaninta da Zainab,
da farko Zainab k'anwar mahaifiyar Zarah ce uwa d'aya uba d'aya,
kuma mahaifiyar Zarah ita ta rik'e ta, Zainab kamar 'ya take a wajen Maman Zarah,
na biyu Zainab ita ta rik'i Zarah ta shayar da ita tare da 'ya ta,
haka ma Zarah 'ya ce a wajen Zainab,
amma hakan baiyuyu ba, na kasa cire ta a raina,
ganin babu ta yadda za'ayi aure yayi tsakani na da Zarah yasa shaid'an da zuciya suka fara k'issima min abubuwa da dama akanta.


Abinda na fara ainawa a raina shine matuk'ar bazan auri Zarah ba to kowaye zai aure ta bazai tab'a samuta cikekkiyar budurwa ba,
dan ni nafi kowa cancanta dana amshi budurcinta, tun daga ranar danayi wannan tunanin zuciya ta da shaid'an ya fara kwad'aita min ita,
suna fito min da zallar kyau daga na jikinta harta fuskarta,
musamman ma surar jikinta, take idanuwa na suka rufe ruf, na daina ganin kowacce mace a matsayin mace sai Zarah,
naji babu abinda nake so sai na kasancewa da ita, babban burina a lokacin bai wuce na kwanta da ita ba (sex),,
lokuta da dama idan na dawo daga office saboda Zarah ta rungume ni nake tsayawa daga bakin k'ofa na bud'e musu hannu ita da Ikram,
dan idan Zarah ta rungume ni wani irin mugun shocking nake ji a duk ilahirin jikina,
ina jin shauk'i na shigata ta ko'ina, ta kowanne b'angare na jikina,
idan ta rungume ni, take nake mantawa da

Please Login or Register in order to submit comment