Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da ita, shi kuwa Fahad kasa runtsuwa yayi ya fad'a duniyar tunani, can wajen asuba yaji matsi a hankali ya mik'e zauna tare da kuma kasa kunne cikin sand'a ya rink'a jin takon mutum, cike da mamaki ya mik'e a ransa yace " still, to ko dai Sheemah ce ta kuma dawowa? shi da kanshi ya bawa kansa amsa da cewa a'a nasan bazata dawo ba saboda dukan danayi mata takai 1 month tana jinyarsa, a hankali yace " to waye?


Da k'arfi zuciyar sa ta buga, jin takun na k'ara matsowa yasashi mik'ewa da sauri ya b'uya a bayan k'ofa, dai-dai lokacin da mutum ya shigo d'akin, Fahad dake lab'e yaji an tuntsure da mahaukaciyar dariya had'i da cewa " big brother idan kayi mana shigar sauri wajen aurenta mu kuma zamuyi maka shigar sauri wajen having sex da ita, na dad'e ina mafarkin samun mace irin Kausar komai yaji, ban tab'a tunanin akwai su a duniyar ba sai gashi kwatsam naci karo da ita, yaza'ayi na iya hak'ura da ita batare dana mayar da kwad'ayi na ba, ya fad'a yana k'ok'arin cire rigar jikinsa, a gigice Fahad ya fito daga inda yake b'oya ya kunna light d'in d'akin Haidar ya gani tsaye yana k'ok'arin cire wandonsa.


Cikin firgici Fahad yace " what you again?



Cike da matsanancin mamaki yake kallan Haidar yama rasa me zayyi mishi, ya rasa ta ina zai fara hukunta shi, cikin tsoro Haidar ya kalli Fahad bakinsa na rawa yayinda gaba d'aya jikinsa kerrrrma yake, tsoro da fargaba sun hana shi furta koda kalma d'aya ne, a hankali Fahad ya zauna a bakin gado yayi tagumi da duka hannayensa ya fashe da kuka mai cin rai da k'ona zuciya, cikin kuka yace " a waje ba'a damarmin matata ba sai a gidammu a gidan namu ma 'yan uwana na jini wand'anda muke uwa d'aya uba d'aya dasu, meyasa Haidar duk matan waje, duk matan duniyar nan ka rasa wacce zaka nema sai matata, why! why!! why!!! Haidar ya fad'a a tsawace yana mik'ewa yaci kwalar Haidar yace " meyasa Haidar?


A tsawace cikin d'aga murya yace " nace meyasa Haidar, tsawar da yayi ce ta farkar da Kausar a kid'ima ta mik'e ganin Fahad rik'e da kwalar Haidar yasata fara yiwa kanta tambayoyi da dama, kalaman Fahad data tsinta ne suka sakata fahimtar komai cike da mamaki ta shiga kallan Haidar take hawaye suka shigo zubowa daga idanuwanta cikin tashin hankali ta fara zancen zuci dabata san ma yana fitowa fili ba " wanne irin bahagon gida ne, wanne irin mutane ne acikin gidan nan, irin wannan kurman gidan na shigo da irin wad'annan mutanen zan zauna harna had'a jini dasu, kalaman Kausar ne suka kuma tun zura zuciyar Fahad ya fara dukan Haidar tako'ina yana yi masa mahangurb'a, tun daga bedroom yake dukan Haidar har sai da suka fito farfajiyar gidan.



Wani wawan naushi Fahad ya sakarwa Haidar take ya saki k'ara had'i da sulalewa k'asa yana zubar da jini a matuk'ar gabaice wata irin razananniyar k'ara Kausar ta saki wacce ta kaure daga d'aya gidan hakan yayi sanadiyyar farkawar duk wani mahaluk'i dake cikin gidan da gudu Hajiya Lailah da Sanata Sambo, Ummi da sauran ma'aikatan gidan duk suka fita waje, inda suka iske abinda ke faruwa da sauri Hajiya Lailah da Sanata Sambo suka k'arasa inda suke dai-dai lokacin da Fahad ya shak'i wuyan Haidar, daga Hajiya Lailah har Sanata Sambo suka shiga kiciniyar kwace Haidar daga hannun Fahad amma duk suka kasa, ganin idanuwan Haidar sun kakkafe jikinsa ya saki yasa Kausar yin mahaukacin ihuuuuuuuu had'i da sulalewa k'asa a sume.


Sakin Haidar yayi ya fad'i k'asa timmmmmm ya nufi inda Kausar ke kwance a sume, bayyiwa kowa magana ba duk da tarin tambayoyin da Hajiya Lailah da Sanata Sambo keyi masa a hankali ya sunkuya ya sab'i Kausar ya shige da part d'in su ya rufe k'ofa, da sauri Hajiya Lailah ta nufi inda Haidar ke kwance a sume ta shiga jijjigashi tana kiran sunan shi, ganin baiko matsa bane yasata kwalawa driver suka suka shi a mota suka nufi hospital.


Direct bedroom d'insa ya wuce da Kausar a hankali ya kwantar da ita akan bed ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko, yana watsa mata ta sauke ajiyar zuciya ta fara bud'e idanta, karaf ta had'a ido da Fahad ai sauri ta mik'e tayi baya can k'uryar gado jikinta yana kerrrrma da wani mugun tsoron Fahad take ji tana kallan shine kamar wani monster, murmushi yayi dan ya fahimci tsoransa take ji, a hankali ya d'ago jajayen idanunsa ya zuba mata, kallanta kawai yake da jajayen idanuwansa ya kasa yin komai, yana tunanin meyasa Haidar da Sheemah ke neman keta masa haddi, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume gam ya fasa kuka mai k'ona zuciya, itama fashewa tayi da kukan aka rasa mai rarraahin wani a tsakanin su.


Kasancewa Haidar ya daku sosai yasa likitoci kwantar dashi, sai bayan gama komai sannan Hajiya Lailah ta dawo gida, tabar Ummi a wajensa, bayan ta dawo gida tayi wanka ta fito falo ganin har lokacin Sheemah bata fito daga bedroom bane yasa zuciyar ta yin zafi, cikin zafin rai ta nufi d'akin Sheemah, a harzuk'e ta tura k'ofar d'akin, ganin halin da Sheemah take ciki ne yayi mummunan d'aga mata hankali ta k'arasa inda take da sauri, cikin hanzari ta fito ta kira driver suka d'auki sukayi hospital da ita, itama mawuyacin halin datake cikine yasa dole aka kwantar da ita.



BAYAN SATI D'AYA



Yau jirgin su Hajiya Rabi yayi landing a Nigeria, suna isa gida ko bari batayi ta huta ba ta kira boka jimrau, " sannu da dawowa Hajjaju an dawo lafiya?


A tak'aice tace " Alhamdulillah, ya maganar mu dakai kace in bari sai na dawo Nigeria, to na dawo dariya yayi sannan yace " haba Hajjaju gaggawar mekikeyi ne?


Cike da k'usawa tace " hmmmmm Boka Jimrau dan baka san yadda nake jin yarinyar a raina bane, ina yi mata matsanancin so na bam mamaki, dariya ya kuma yace " kinje gidan k'awarki? "A'a ta bashi amsa, "bakiji labarin babban d'anta yayi aure ba? d'anki taja had'i da cewa naji mana, akwai abinda d'ayan mu zayyi batare da sanin d'ayan ba, "akwai Boka Jimrau yace had'i da cewa ki bari ki huta ki nutsu sannan sai muyi maganar, ta bud'e baki zatayi magana ya dakatar da ita had'i cewa " karki sake kira na har sai kinje gidan Hajiya Lailah, dan babu wani abinda zan iya yi miki har sai kinje gidan tukunna, yana kaiwa nan bai bari tayi magana ba ya kashe wayar, wayar Hajiya Rabi tabi da kallo dan ta kasa fahimtar abinda Boka yake nufi.


Jin yace karta k'ara kira har sai ta je gidan Hajiya Lailah ne yasata mik'ewa da hanzarinta bata ma bari ta huta ba ta nufi gidan.



A parlor ta iske Hajiya Lailah zaune tana kallo amma gaba d'aya hankali ta baya kan kallan dan har yau ba'a sallamo Haidar da Sheemah, da sauri Hajiya Rabi ta k'arasa had'i da rungumar Hajiya Lailah cike da jin dad'i Hajiya Lailah tace " kawata yaushe a gari? shine kikayi min zuwan bazata? dariya Hajiya Lailah tayi had'i da cewa so nake nayi surprising naki, "aiko kinyi cewar Hajiya Lailah, bayan sun gama zantuttukan su, sunci abinci Hajiya Rabi ta kalli Hajiya Lailah tace " ni ko k'awata ina surukar tamu kuma sahibarki abar k'aunarki?


Dariya Hajiya Lailah tayi had'i da rik'o hannun Hajiya Rabi tace " me kike ci na baka na zuba, taso muje ki ganta, da sallama suka shiga part d'in su Kausar inda suka iske ta daga ita sai mini skat black da red half best, tayi peaking gashin kanta da red reborn isan ka kanta kamar 'yar baby tayi masifar kyau halittun jikinta sun k'ara fituwa sosai d'as.


Fuskar Hajiya Lailah d'auke da murmushi ta k'arasa inda Kausar ke zaune ta mik'ar da ita tsaye had'i da rik'e ta kalli Hajiya Rabi dake tsaye kamar mutum mutumi tayi sororo kamar doluwa tace " ga surukata nan.


Wani irin mahaukacin fad'uwa gaban Hajiya Rabi yayi yayinda cikinta ya bada k'uluuuuuuuu, idanuwanta sukayi ja, cikin rawar baki tace "............





MOMYN ZARAH
[26/01, 02:37] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




39




Kausar na zaune a parlor Sheeemah ta shigo fuskarta d'auke da fara'a ta zauna kusa da ita sosai jikinsu ke gogar na juna, a hankali Kausar ta d'an matsa baya had'i dayi mata murmushi tace " ina yini? "lafiya lau amaryar mu, ya kwanan bak'unci "Alhamdulillah Kausar tace, "Yaya yana nan ne? Sheemah ta tambaye ta, " a'a ya fita, cikin dabara Sheemah ta d'ora hannunta akan cinyar Kausar tace " ok dama zuwa nayi na tayaki hira, d'an murmushin yak'e Kausar tayi kawai ba tare data ce kome ba.


A hankali Sheemah ta d'an fara matsawa Kausar cinyarta had'i da janta da hira, sosai abin ya bawa Kausar mamaki, a hankali Kausar ta mik'e gami da kallan Sheemah tace " bari nayi wanka, murmushi Sheemah tayi sannan tace " wanka zakiyi shine kuma bako gayyata? dammmm gaban Kausar yayi muguwar fad'uwa, amma sai ta dake tace " gayya kamar ya? ganin yanayin Kausar yasa Sheemah waskewa tace " jeki wankan nima yunwa nake ji ta fad'a tana mik'ewa, ko kallanta Kausar bata k'arayi ba ta shige bedroom d'inta ta fad'a kan bed.


Wajen 5:00pm Hajiya Lailah ta shigo part d'in su Kausar kai tsaye ta danna kanta bedroom d'in a gaban dressing mirror ta iske Kausar daga ita sai guntun towel tana shiryawa tana ganin Hajiya Lailah ta mik'e da sauri cikin alamun jin kunya, kuwa Hajiya Lailah kuwa ita kad'ai tasan yanayin data tsinci kanta aciki, cikin k'ank'anin lokaci ta firgice ta fita daga hayyacinta, batare data sani ba ta nufi inda Kausar ke tsaya cikin rashin sanin abinda take yi tajawo Kausar jikinta ta rungume gam tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, ita dai Kausar tayi sororo cike da tsananin mamaki, a hankali Hajiya Lailah ta mik'a hannu ta d'auko lotion d'in da Kausar ke shafawa ta shiga shafa mata a jikinta, jin laushi gami da tsantsin fatar Kausar ya sake zauta Hajiya Lailah take ta shiga sambatu " I love you Kausar, I really love you so much with all my heart, take tsoro, fargaba gami da firgici suka dirarwa Kausar in banda rawa babu abinda jikinta keyi.


Ta cikin mirror ta hango Fahad tsaye ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa shima ita yake kallo da alama ma bai sai abinda yakeyi ma dan idonunsa sun kad'a sunyi ja sosai, shi bai ma kula da Hajiya Lailah dake tsogunne a gaban Kausar ba, a hankali Hajiya Lailah ta mik'e tsaye tana k'ok'arin rungume Kausar tana cewa " I really love you so much my baby, karaf ta had'a ido da Fahad, iya tashin hankali, tsoro da fargaba Hajiya Lailah ta shige shi, amma ta dage ta nufe shi tana mai cewa " I love you my baby tana k'arasawa inda yake ta rungumo shi jikinta, hakan da tayi ne yasa Fahad bai fahimci cewar da Kausar take ba, a hankali ta zame jikinta daga nashi tace " I love you son, and I can't life without her, she is my heart, my life and she is apple of my eyes ta fad'a tana jefawa Kausar wani irin gigitaccan kallo, shi Fahad tsaye kawai yana kallan Momyn sa had'i da sakar mata murmushi, kwata-kwata bai fahimci abinda Hajiya Lailah ke nufi ba, dan ko a gigin mutuwa akace masa mahaifiyar sa zata nemi matar sa bazai tab'a yarda ba kowa zai gaya masa a duniya.


Ganin irin kallan da Fahad keyiwa Kausar da kuma yanayinsa dan ko yaro ya kalli Fahad sai ya fahimci yana cikin yanayina buk'atuwa, tasan matuk'ar ta barshi ya kad'aici da Kausar komai yana iya faruwa, dan haka ta rik'o hannunsa tana cewa " son muje kayi lunch, " no Mum bana buk'ata yanzu wanka nake son yi, ci gaba tayi da jansa har suka zo parlor tana k'ok'arin fita dashi ya zame hannunsa yace " Momy dawowa ta kenan daga office ina so nayi wanka na d'an huta.



Fuska ta b'ata sosai ta kallashi sannan tace " ka tuna da alk'awarin daka d'aukar min a ranar auren ku, kallanta yayi shima cike da mamaki yace " Momy dat is impossible, dan gaskiya is possible komai yana iya faruwa, kuma naga ai mata ta ce zan iya yin duk abinda naga dama da ita, wani irin kallo ta watsa masa yaci gaba " Momy ai hannu d'aga masa had'i dayi masa mahaukaciyar tsawa da duk gidan sai da ya amsa, da gudu Kausar ta fita still daga ita sai towel d'in, Hajiya Lailah ta tako har gaban Fahad daf dashi ta yadda suna jiyo numfashin juna ta kalle shi ido cikin ido gami da nuna masa d'an yatsa tace " eh Fahad, Kausar matar ka ce, sannan kana iyayin duk yadda kaso da ita, amma dole ne ka k'aurace mata, wallahi tallahi dole ka bi umarnina matuk'ar kana neman zaman lafiya, Fahad idan ka sake ka kusanci Kausar ban yafe maka ba, da sauri cike da mamaki ya d'ago yace " what mom, she is my wife, " eh kamar yadda kaji haka nake nufi, sakarai kai, ta fad'a tana barin part d'in.


Daga Fahad har Kausar suka bi bayan ta da kallo, a hankali Fahad ya mayar da kallonsa kan Kausar dake tsaye daga ita sai d'an, wani yawun wahala ya had'iya, sannan ya zaune akan sofa had'i da lumshe idanunsa.


Can cikin sulasalin dare (tsakar dare) Kausar na kwance kamar a mafarki taji tana shafata can kuma taji ana tsotsar mata nono gami da shafa mata duk ilahirin jikinta da sauri cikin tsoro ta mik'e tana niyyar fasa ihu, da k'arfi taji an rufe mata bakinta sannan an mayar da ita kan gadon an danne ta sosai aka sakar mata karfi, ta kasa koda kwakkwaran motsi ne, cikin zafin nama aka fisge mata 'yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta ya rage daga ita sai pant dama gata ba gwanar saka bra ba, da karfi taji an yaga pant d'in jikinta gashi an rufe mata baki ba damar yin ihu, ji tayi wani irin mahaucin k'arfi yazo mata, da k'arfi ta zame hannun da aka rufe mata bakinta gami da fasa ihuuuuuuuuu tana kiran Fahad! Fahad!! Fahad!!!, tana kwala k'ara, cikin bacci Fahad ya jiyo ihunta, a sauri ya mik'e daga shi sai gajeran wando (boxer)


A firgice ya shigo d'akin, makunnin wuta ya laluba ya kunna, da sauri ta mik'e ta rungushi had'i da sakar mishi gigitaccan kuka, shima hannu yasa ya matse ta da jikinta sosai, a hankali ya zauna da a bakin gado yana shafa mata kanta sai ya bari hankalinta ya kwanta sannan ya tambaye ta abinda ya faru, cikin kuka da tashin hankali ya fad'a masa abinda ya faru, murmushi yayi yace" tsorata kikayi amma babu wanda zai shigo saboda k'ofar parlor a rufe take, tsayawa tayi cak da kukan ta kalle shi ta kalli kanta sannan ta mayar da kallanta zuwa kan gadon, a hankali ta kalle shi tace" to idan tsorata nayi waye ya ya motsa bed, sannan waye ya yayaga min pant da sleeping dress d'ina?


Shima kallan gadon yayi kawai sannan ya kalli pant da sleeping dress d'inta dake yashe a gefe, sakinta yayi yaje ya d'aga rigar bacci da pant d'in ya ganzu a yage, a hankali ya juya ya nufi parlor aiko da gudu tabi bayansa, handle d'in k'ofar ya kama ya jita a rufe gam, murmushi yayi yace " Kausar kin tsorata ne kawai, ganin duk bayanin dazatayi masa bazai fahimta ba yasa yin shiru, hannunta ya rik'o ya nufi d'akinsa da ita, kallanta yayi yace " ki hau gado ki kwanta, ganin shima ya kwanta a kan gadon yasa ta tsayawa batare dataje ta kwanta ba, ganin ya kashe light yasata nufar gadon da gudu ta shige jikinta sosai ita tama manta ba kaya a jikinta, k'arfi hali kawai Zaid yayi.


Washe gari da wuri Kausar ta tashi ta barshi yana bacci dan daren jiya kwata-kwata bai runtsa ba, yadda yaga rana haka yaga dare, bayan ta gama aikace-aikacen ta, ta kunna turaren wuta, ta fad'a bathroom ta shek'a wankanta, ta fito ta shirya tsaf ta zunbula hijab ta nufi part d'in su Hajiya Lailah da sauri Hajiya Lailah da Sheema suka nufo ta ganin suna niyyar rungume ta yata durk'uwa har k'asa da sauri tace" ina kwana Momy? dan yanzu ita abin nasu ya daina bata mamaki ya koma bata tsoro, murmushi Hajiya Lailah tayi had'i da rik'o ta ta mik'ar da ita tsaye cikin dabara Sheemah ta zaunar akan sofa, Ummi na gefe na kallan yadda uwa da 'ya ke rawar jiki akan surukarsu a fili tace " abin kunya.


Yauma da tsakar dare Kausar na kwance tayi d'ai-d'ai akan bed daga gani kasan tana jin dad'in baccinta a hankali aka shafata tun daga sama har k'asa take taji wani irin dad'i ya mamaye mata duk ilahirin jikinta ta k'ara bajewa, a hankali taji an fara tsotsar breast d'inta ana shafa mata d'ayan, kamar a mafarki taji ana cire mata pant, a hankali ta d'an bud'e idanuwanta dan ita duk a zatonta mafarki take, a hankali ta lumshe idanuwanta, taci gaba da sauke ajiyar zuciya, jin ana tura mata wani a k'asanta yasata saurin bud'e idanta shiru tayi dan tana so ta tabbatar a zahiri ne ko a mafarki, jin ana ci gaba da shafata yasa tsoro ya shegeta lokaci d'aya take ta firgice ta fita daga hayyacinta.


Da k'arfi ta saki wawan ihuu gami da kwalawa Fahad kira a gigice, rik'e hannun wanda yake shafata tayi da k'arfi taci gaba ihuu tana kiran Fahad, ganin Kausar na niyyar tona shi yasa ya ta kifa mata mari gami da hankad'a ta, ta fita da gudu, yana fita Fahad ya shigo a gigice, a haukace ta nufi dai-dai lokacin daya kunnah bedroom light ganin shatin mari a fuskarta ga kuma kumburin da fuskar tayi ne yasa shi nufarta da sauri, da sauri ta ja baya a gigice tace " wallahi ana shigowa d'akina idan waccan karen kace tsorata nayi to yanzu, a matuk'ar firgice take maganar duk ta gigece ta fita daga hankalinta cikin tace " wallahi Allah da gaske nake yi maka, tsayawa yayi kawai yana kallan yanayinta, a hankali ya jawota jikinsa ya matse ta gam, ya shiga lallashinta.


Hajiya Rabi an shiga matsanancin hali akan Kausar, ganin bata da wata mafita ne yasa kiran boka Jimrau, yana d'agawa ya tuntsure da gigitacciyar dariya had'i da cewa "manyan mata masu duniya, ba'a jinku ko ganin ku sai idan kuna da matsala ko buk'ata, murmushi tayi tace " ba haka bane kasan wannan karon Alhaji ya matsa sai da ya tafi dani shiyasa kaji ni shiru, " gaskiya kam amma ai baki manta da abar k'aunarki Kausar ba ko? Murmushi dan idan da sabo sun sabo da hatsabibancin boka Jimrau, yaci gaba da cewa " babu abinda zan iya yi miki a halin yanzu sai idan kin dawo Nigeria kin had'u da Aminiyar ki Hajiya Lailah sai musan abinyi mu nemi mafita, "yanzu babu wani taimakon da zaka iyayi min? "Ke dai ki bari sai kin dawo kawai, sanin boka Jimrau baya musu yasata hak'ura dole ba dan taso hakan ba.


Wajen 11:00pm na dare Kausar na zaune a d'akinta tsoro ya hana ta yin bacci sai juyi take ita kad'ai akan bed gashi ita bata san kwana d'akin Fahad dan takura take yi sosai, gaba d'aya sai ta jita a takure bata iya sakewa, babu yadda bayyi ba akan ta koma kwanan d'akinsa amma fir tak'i, ganin sha biyu saura ya sata mik'ewaa ta kashe light d'in d'akin taja bargo ta rufa, sama-sama bacci ya fara fisgarta, tun kafin baccinta yayi nisa taji an shigo d'akin, take jikinta yasoma kerrrrma tsoro ya dirarmata take k'irjinta ya harba da k'arfi ya shiga ukan uku-uku, a sauri ta yunk'ura cikin zafin nama ta fita daga d'akin da gudu aka bi bayan ta a parlor taji an fizgo had'i da rufe mata bakinta, da k'arfi ta shiga kiciniyar kwace kanta, garin ta kwace kanta bata sani ba ta fad'a kan center table, take kanta ya fashi jini ya shiga zuba bata tsaya bin ta ciwon data ji ba ta mik'e da sauri tabi takan glass d'in daya fashe k'afarta duk ta yanke sai jini ke zuba.


Da hanzari ta k'arasa k'ofar d'akin Fahad, a haukace ta shiga dukan k'ofar tana kuka tana kiran kiran sunan Fahad, a gigice kamar zararriya, duk ta rud'e, ta gama fita daga hayyacinta, a hargitse Fahad ya bud'e k'ofar a haukace ta nufe shi tana ihun kuka ta shiga sambatun da ita kanta bata san me take cewa ba.



Cikin rawar baki" wallahi Allah yauma an kuma shigowa, ka duba ka gani ganin baiko motsa ba yasata fara dukan k'irjinsa a haukace tana ihu gashin kanta duk ya bashe, jikinta sai rawa yake yana kerrma, ganin bata cikin hayyacinta yasa shi rik'o hannuwanta ya rik'e cikin nashi yace " shhhhhhhhh, ya matse ta da jikinta, ita ko sai k'ok'arin kwace kanta take tana ihuuu, sai lokacin ya kula da jinin dake zuba daga goshinta da sauri yace " Subhanallahi Kausar kinji ciwo, ya fad'a yana yawo ta zuwa parlor, turjewa tayi tace " bazan koma parlor ba yana can wallahi bai tafi ba, ganin zata b'ata masa lokaci yasa ya d'auke cak, yayi parlor da ita, yana isa parlor ya tsaya cak ganin k'ofar parlor a bud'e, a hankali ya soma bin ko'ina da kallo yaga centre table a fashe, gashi duk an hargitsa ko'ina alamar anyi kokowa, tabbas yasan yau an shigo, sai yau ya tabbatar da ana shigowa part d'in su, a fili yace " to waye? me aka zo nema, ne aka zo d'auka? meyasa ba'a shiga bedroom d'insa sai na Kausar tabbas yasan akwai wani abu.


A hankali ya zaunar da ita a jikinsa ya rungume ta, yana shafa kanta had'i da buga mata bayanta, a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya tare da ita ya mik'e a jikinsa ya nufi kitchen ya bata ruwan sanyi tasha, sannan ya wuce bedroom ya shirya ya shirya ta suka nufi hospital , ba su dawo ba sai wajen 10:30am aka sallame su, suna dawowa ya dannawa k'ofar part d'in su key, ya wuce da ita bedroom ya zaunar ya koma kitchen ya had'o mata breakfast ya dawo ya bata, sai da taci ta k'oshi sannan ya bada magungunanta ya kai ta bathroom tayi wanka, ya saka mata kaya mara nauyi ya kwantar da ita had'i daja mata blanket.





MOMYN ZARAH
[26/01, 02:37] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




38





Murmushi Hajiya Lailah tayi cike da kissa ta shafo gefen fuskar shi tace " FAHAD ne yake son yin aure dan har munje gidan su yarinyar, baka ga yarinyar ba kyakykyawa gata da hankali da tarbiyyar, da sauri Sanata Sambo yace " what da gaske kikeyi koda wasa kike yi, murmushi ta kuma yi tayi wani farrrr da ido tace " wallahi da gaske nake maka sunanan yarinyar Kausar, cike da murna ya mik'e tsaye da ita a

Please Login or Register in order to submit comment