Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



بسم الله الرحمن الرحيم



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



3



Filin wasan kwallon k'afa dake garin Holland cike yake tap da d'unbun jama'a, iri iri babu k'abilar bil Adama da babu, ciki wannan filli wasa wanda ya tattara kan bak'aken fata 'yan Africa koma ince in Nigeria,da sauran kasashen duniya. ihun mutane daban daban dake zaune wajen ya cika filin wasan kwallon Yayinda wasu daga 'cikin mutane gurin ke sanye rigar matches rike da flags suna Dagawa sama suna zabga matsanancin ihu alamun Yan team dinsu ne suka samu nasarar cinyewa..


Kyakykyawan saurayin dake gefe zaune ya b'ata rai, in banda tsaki babu abinda yake faman yi,cikin fushi ya cutsa laulausar tafin hannushi 'cikin sumar kansa dake kama data Fulanin asali yana shafawa , cikin harshen Hausa yace " aikin banza kawai sun b'atawa mutane lokaci a banza ashe babu abinda zasu iya.
" wani dake gefen zaune ya lalleshi fuska d'auke da murmushi yace " Assalamu Alaikum, wanda ke zaune rai b'ace ya juyo ahankali ya tsurawa wanda keyi masa sallamar idanu yana kallonsa , had'i da amsa masa sallamar.


D'ayan yace " naji kayi Hausa ne, shine nace bari nayi maka magana d'an uwa, murmushi yayi yace " lalle ko, wani can daga gefe shima yayi dariya yace " sannunku, nima naga 'yan uwa, dariya sukayi su duka,uku d'ayan dake gefe ya taso ahankali cike da takun isa ya mik'a musu hannu yace " am KHAMAL by name , dariya d'ayan yayi yace " ni kuma NASEER, hannu shima d'ayan ya mik'o musu yace " ni kuma ABDUL.


Take Kowanesu yagabatar da kansa, da dan'uwansa wani matsanancin ihun da aka kuma yi ne ya dawo da hanakalin su wajen filin wasan,sosai tsaki still NASEER ya kuma yi ya furzar da iska me zafi Daga bakinsa kana yace "aikin banza, aikin wofi ashe duk dakikai akatara anan dabasu iya koma kawai ana sa mutun bata lokacinsa .
dariya Khamal yayi tare da cewa " haba ai Chelsea k'arshe ce wajen wasa,kwallon duniya Abdul yace " haba dai Chelsea Malam.
kasan dai Amman idan ana maganar manya kwallon wasan duniya Barcelona ba'a mana ko itace kan gaba ?

Naseer dake zaune ya dan zamo kadan Daga kujerarsa yana me juyowa saitin da Abdul yake ya kalleshi yana lumshe idanunshi sannan yace " Barcelona me? Suwaye 'yan wasan ta?


Khamal yayi dariya yace "Barcelona cluv pleyers 1 stegen 2 segi roberto 3 pique 4 basquet 5 samul umtiti 6 ivan rikitic 7 usman denbelle 8 Philip coutinho 9 surez 10 leneal messi 11 jodi alba, kallansa Naseer yayi yace " sannunka, gaskiya kai mayen kallon ball ne,na karshe amma ni nafison Real Madrid, saboda tana da manyan 'yan wasa wayanda suke da kwarewa sosai akan fanin wasa .



Dariya Khamal da Abdul sukayi sosai har da dan buga kafafunsu suka ce " suwaye manyan?


Dariya Naseer yayi yace "Real madrid cluv 1 keylo navers 3 cavejal 3 marcelo 4 sergio ramos 5 rafeal varen 6 casmiro 7 Asensio 8 tony krooss 9 karim benzema 10 luca modric 11 grez bell.


Abdul yace "ai gara kace ma Manchester City, suma suka saka masa dariya, hade ranshi yayi sosai yana cin magani kana yace " wallahi tafi duk sauran yan wasan kwallon da kuke.
dan itama tana da manyan 'yan wasa km kwararu da suka shahara acikin duniya Manchester city cluv 1 ederson 2 neuclas otemendi 3, kyle walker 4 fabian delp 5 ilkey gundigon 6 fernsndinho 7 bernado silver 8 rahem sterling 9 sergio aguero 10 leory sane 11 lapote,



Nan fa musu me karfi ya shiga tsakaninsu kowanne yana kokarin kawo hujoji da cewa nashi ne babba, har sanda aka tashi daga wasan, har waje suka fito tare suna wasa da dariya, tare da exchanging din numbers junansu suka yi, sannan kowa ya nufi gida.


Washe gari tun wajen k'arfe 12:00pm Naseer ya fita wajen motsa jiki, tun baiyi nisa ba yaji ana kwala masa kira, cak ya tsaya ya juyo, dariya yayi yace " Khamal ka fito kenan?


" eh na fito, tare suka ci gaba da tafiya, Khamal ya kalli Nasser yace " halan kaima anan kake ba nisa?


"Eh daga can baya gida na yake, number 12,dariya Naseer yayi yace " kace bamu da nisa, ni ina layin baya number 27,ina nan da matata d'aya da yara 4 mata 2 maza 2, Khamal yace " nima da iyalina mata ta 1 yara 3 biyu maza 1 mace,



Suna hira har suka k'arasa wajen, Abdul suka hango ya dage yana ta motsa jiki, dariya sukayi suka nufeshi, cikin dariya Khamal yace " an dage ana ta faman aiki, halan madam ce bata san k'iba, sai a lokacin ya kula dasu.



Dariya yayi yace " ni Madam d'ita babu ruwan ta, kudai da naku suka koro ku, tunda safe, dariya sukayi gaba d'aya, sai wajen 4:00pm sukayi sallama, har zasu rabu, Khamal ya kalli Abdul yace " a ina gidan ka yake?


" a Jon crescent house number 35,dariya sukayi suka ce" lahh dukkan mu ashe unguwar mu d'aya,batare mun sani ba .
nan suma suka fad'a masa inda gidan su yake, murmushi yayi yace " nima ina da mata 1 da yara biyu mace da namiji.


Sallama sukayiwa juna suka rabu, wajen k'arfe 8:00pm Abdul ya fita kallan wasan Cricket, yana zuwa ya iske Naseer zaune gaba d'aya hankalinsa ya tafi wajen wasan.


Murmushi Abdul yayi yace " tabb kaga sarkin kallo, ajiyar zuciya Naseer yayi .
ya kalli Abdul dake tsaye hannuwasa duka zube cikin aljihun wandonsa yace " oh kai ma kana kallan wasan Cricket?


"Sosai ma, Khamal suka hango can gefe yana ta waya, mik'ewa sukayi gaba d'aya suka nufe shi, yana ganin su ya ajiye wayar ya mik'a musu hannu yana dariya yace " kaga manya a she nan ma kuna lel'owa?



" Sosai ma kuwa inji Naseer dake murmushi,zama sukayi suka maida hankalin su ga wajen wasan



Ba'a tashi ba sai wajen 11:pm, tare suka fito, sallama sukayiwa juna, kowa ya nufi gida.



Ranar asabar da wuri Khamal ya tafi kallon wasan Poly, yana zama saiga Naseer, shima bai dad'e ba saiga Abdul, kallonsu Abdul yayi yace " wai ku ko'ina kuna nan kmr wasu mayyu ?


"Dariya suka kwashe dashi suka ce " ko kuma muce kai ko'ina kana nan kmr wani magnet?

Gabadaya suka kwashe dariya wannan karon tare da tsansar murna sake ganin junansu da hk kawai kowanensu ke jin dan'uwansa 'cikin zuciyarsa .km a duk sanda zasu hadu suna tsintar kanshi 'cikin farinciki.
Bayan an gama wasan Khamal yace " gaskiya ya kamata musan juna fiyye da haka tunda duk Muna tare da matan mu yakama har su mu had'asu domin zumucinmu ya daure .


Murmushi Abdul yayi yace " gaskiya dai ya kamata, Naseer yace " to yanzu tunda unguwar mu d'aya, kamata yayi kowa yaje yaga gidan kowa, inyaso gobe sai mu had'u a gida na, shawarar Naseer aka bi.



Washe gari Abdul da Khamal kowa yazo gidan Naseer da Matar sa da yaran sa, cikin fara'a Zarah ta tari Fateeha da Yasmeen, wanda daman tasan da zuwa agurin mijinta hira sukayi sosai, tamkar sun jima da sanin juna sannan aka zauna a dinning aka ci abinci,yayinda yaran su 'cikin farinciki suke wasa da juna wanda hkn ya faranta ran iyayen .



Tun daga wannan ranar wata irin kwakkywar shak'uwa ma k'arfi ta shiga tsakanin Khamal, Abdul, Naseer haka matayensu da yaran su, sun saba sosai, dan bazaka tab'a tantance yaran su ba, d'an kowa na kowa ne.


Har school d'aya suka maida yaransu domin inganta zumuncinsu kyakykyawar fahimta ce mai k'arfi a tsakanin su, kowa bai da get a gidan kowa.



Khamal ya kalli dubbun manya 'yan jaridan da 'yan gidan TV da sauran masu d'aukar labarai, yace " to kunji farkon yadda muka fara had'uwa, da junanmu har Allah ya dai-daita tsakanin mu, har yau Allah baisa mun tab'a samun sab'ani ko rashin fahimta a tsakanin mu ba, haka ma yaran mu, da matan su.



D'aya daga cikin 'yan jaridan ne yace " Sir to yaakayi kuka had'u da Ammar, Fahad, Zaid?



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:11] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



4


Murmushi Khamal yayi ,sannan ya kalli Ammar yace " to Bissimillah,shima murmushi yayi yace "ok sannan ya fara



" misalin k'arfe 11:00pm na dare a garin Holland, muna tafiya ni da Matata Basma a mota .
ana tsuga matsanancin ruwan sama, Basma tace " Dear kamar hannu naga ana d'aga mana ko?


Ido sosai na k'ara bud'ewa dan ganin ko gaskiya ne, " eh my love kuma kamar mace, " eh macece Basma ta fad'a a dai-dai lokacin da muka k'arasa wajen, mace na gani da tsohon ciki, ga motarta a gaban ta ga dukkan alamu motar ce ta lalace, muna tsayawa Basma ta fito da sautunta ta kama wannan matar dake takawa da kyar ta shigar da ita 'cikin mota, ta rufe ta zaga ta shiga gaba, da kyar matar ta iya bud'e baki tace "motatace tayi faci.
sai a lokacin na lura yarinyar ce wacce bazata wuce sa'ar Basma ba.



" a hankali tace " sunana YASMEEN, "oh Basma tace, sannan tace ni kuma Basma, yanzu ina zamu kaiki ko mu wuce gida dake kawai?


"A'a please ku kaini hospital saboda ina d'an jin ciwo, "ok Basma tace, ta kalli Ammar, gira ya d'aga mata yana murmushi , direct a hospital mafi kusa muka wuce, sai da muka kai 1:00am sannan aka sallame mu Dr ya tabbatar mana da babu wata matsala, daga nan muka wuce gidan mu, da taimakon Basma Yasmeen tayi wanka, ta bata abinci, dai da Yasmeen ta dawo hayyacinta sannan ta fara laliben jakarta.


Kallon ta Basma tayi tace "me kike nema, murmushi tayi tace "jakata, Basma tace " aiko ina tunanin kin barta a mota, " please kozan iya samu aran waya na kira miji na na sanar dashi, inda nake .
dan nasan hankalin sa nacan a matukar tashe, "ok tace had'i da mik'o mata wayarta, kiran Abdul Yasmeen tayi ta shaida masa abinda ya faru, hankalinsa yayi mugun tashi yace " a bashi mai gidan.


Basma ta karb'i wayar ta kaiwa Ammar, da sallama Ammar ya fara magana, cikin tashin hankali Abdul yace " please a wace unguwa kuke? ina son nazo yanzu.


Murmushi Ammar yayi yace " mu muna liver fool stress, amma idan ba damuwa ka fad'a mana inda gidan yake sai mu kawota, dan naga kamar baka cikin nutsuwa, "ok ina gida,


"Yanzu zamu zo da iznin Allah, da Basma aka tafi kai Yasmeen gida, a harabar gidan suka iske Abdul sai safa da marwa yake, yana ganin motarsu ta shigo tun kafin su k'ara sa parking ya k'ara sa da sauri wajen.
Yasmeen ta fito da kyar aiko da sauri Abdul ya rungumeta ajikinshi .
yana sauke naunauyen ajiyar zuciya, gyaran murya Ammar yayi, sai lokacin Abdul ya tuna ashe fa basu kadai ne agurin ba .
sakin Yasmeen yayi tare da nufar inda Ammar yake yana Miko masa sukayi musabaha fuskasa cike da tsansar farinciki taimakon matarsa dasukayi .
sosai yayi masa godiya, sukayi sallama.


Washe gari bayan an gyara motar Ammar yana wajen aiki yayiwa Basma waya yace yanzu bakanike zai kawo mata mota takaiwa Yasmeen, muryarta cike da shagwab'a tace " ni idan Kai wa zai dawo dani?

Murmushi yayi kamar tana kallan sa yace " ok to mu had'u a gidan, lokaci d'aya Basma da Ammar suka k'ara gidan, number Abdul da Yasmeen ta kiya ta bawa Ammar ya kira Abdul, aiko da sauri ya fito da fara'a, ya taresu yana cewa " kwa tsaya daga waje ai ciki zaku shigo, yana maganar yana mik'awa Ammar hannu.

hannunsu rik'e dana juna suka karasa shiga 'cikin gidan a tsaye suka samu Yasmeen a parlor tana jiran shigowar su, da fara'a ta rungume Basma, nan dai aka k'ara jajantawa juna, Ammar ya mik'awa Abdul key d'in motar ya karb'a had'i da sake yi masa godiya.


Sai da suka ci abinci,s sannan Yasmeen ta matsawa Ammar akan ya bar mata Basma sai dare ya biyo ya d'auke.
hakan ko akayi, anan Ammar ya barta suna ta hirar su .
Shi km suka fita tare da Abdul


Tun daga wannan rana zumumci mai k'arfi ya k'ullu tsakani Ammar da Abdul, har Abdul ya had'a Ammar da Khamal da Naseer, ita kuma Yasmeen ta had'a Basma da Zarah da Fateeha, shi kuma Ammar ya had'a Abdul, Naseer, Khamal da Zaid da Fahad, itama Basma ta had'a Yasmeen da Lubnah da Kausar.


Ahankali Ya juyo ya kalli tarin 'yan jaridan dake tsaye yace " to kunji asalin had'uwar mu wanda idan ka duba kasan daga Allah ne, musamman ma yadda duniya ta lalace yanzu ta zama ba yarda da Amana ballanantana uwa uba Gaskiya yanzu.



Kowa a wajen yayi shiru yana ji da sauraro .
Ahankali Al'amern yace " masha Allah ko zamu iya jin labarin ku d'ai-d'ai ?

dukkan su sukayi shiru batare da kowanensu yayi yunkurin cewa komai ba kafin Daga Naseer yace " da dai gaba d'ayan mu mun manta da rayuwar mu ta baya, mu rufe babin abinda yagabata akanmu sbd tunoshi bashi da wani amfani sakamakon rudanin dake tattare acikinsa .wanda muninsa kadai ya isa ya nufar da farin ruhi .... amma babu komai zamu iya baku, domin yazama iznah Ga wasu 'cikin al'uma .. Naseer ya kalli sauran Aminan nasa kana yace " wazai fara acikin mu ?


Abdul yayi sanyayyiyar murmushi me hade da kwalla tausayinsa kanshi take hawaye ya balle masa batare daya shirya hkn ba 'cikin rawar murya yace " bari bari ni na fara, yakarasa fadar hk cikin muryar kuka .
Sannan ahankali ya fara bada labarin sa hawaye Na tsiyaya a idanunshi tamkar ba namiji ba .



*LABARIN ABDUL*


"Ni d'an asalin garin gambe ne a bakin kasuwa gidan mu yake, mu uku kacal iyayen mu suka haifa mace 1, maza 2 gaba d'ayan mu uwarmu d'aya uban mu d'aya, nine babba sai k'anwata wacce a k'alla na bata sama da shekaru goma,a duniya sannan aka haifeta .
sunan ta Ramlat sai d'an autan mu wanda bazai wuce shekara biyar ba, bayan na gama secondary school aka haifeshi, mu ba talakawa bane ba kuma ba masu arziki bane,muna 'cikin rufin asirin ubangiji sannan km Muna gudanar da rayuwarmu farinciki Daga mu har iyayenmu .
Tare da lallab'a rayuwar mu.



Muna da mak'ota wanda a wajen iyayen mu sun wuce mak'ota sun zama kamar 'yan uwa, juna saboda zaman aminci da makotan dake tsakani kan iyayen mu a had'e yake daga maza har mata, tunda muka taso bamu tab'a jin wani abu na rashin dad'i ya shiga tsakanin su ba.ko a tsakaninmu yaransu bbu wani bambanci idan ba'a gaya mutun ba wallahi zai dauka shakikan yan'uwan juna ne ..

Sosai suke zumunci wanda ni tunda Na taso a Haka na gansu km a tunani 'yan uwan mu ne na jini ashe, sam abun ba Haka bane .
sai da na girma ba k'ara wayo sosai sannan na fahimci ba haka bane

, su din makwatamu ne km 'yan asalin kasar niger ne, tunda suka zo neman kudi basu tab'a komawa gida ba.
, mahaifin mu yayi yayi suje suka ki zuwa harya gaji da yi musu nacin zuwa kasarsu ya kyale su, suna da d'an su d'aya mai suna UMAR tun daga kanshi Allah Bai sake basu haihuwa ba.
, wanda a shekaru sa'a nane,muke a haihuwa .
an haife da da kwana 2 shims aka haife shi,muna da shekaru 10 ne, kwatsam ranar da iyaye na bazasu tab'a mantawa ba, domin sun tashi da mummunan labarin Na rashin iyayen Umar.


Suna kwance da dare babbar moatar daf ta kwacewa matuk'inta tayo 'cikin gidan su Umar tabi takan iyayen sa, ta murk'oshesu.
, shi yana gefe yana kwance, Allah bai sa kwanakin sa sun k'are ba, iyaye na sun ji bbu dadi sunyi jimamin mutuwar sunyi kuka har sun gaji,sakamakon rasa makwaftansu da sukayi haka sukayi ta neman danginsu domin sada ummar dasu amma basu samu ba.
Dan ko wanda yasan su Allah Bai Sa sun samu ba . Haka suka gaji da nema da cigiya suka hakura suka rungume umar ajikinsu da tarin tausayin yaron .



Haka suka had'a mu nida Umar suka rik'e komai iri d'aya suke sai mana, idan ko basu da arzikin abu biyu hak'ura suke yi, tunda Umar yako hannun iyaye na bai tab'a kukan maraici ko rashin iyaye ba, .
Sannan ko su iyaye na basu tab'a nuna san kai a tsakanin mu ba sun daukeshi tamkar su suka haifeshi .


Bayan mun gama secondary school ne, iyaye na suka nemi mu ci gaba da karatu kai tsaye na amince wanda hakan shine burina, amma abinda ya bawa kowa mamaki k'in amincewar Umar babu yadda iyaye na basuyi ba akan yacigaba da karatu kmr yadda zanyi amma fir Umar yak'i amincewa acewarsa yafi san yayi hakar kasuwanci.



'Cikin matsanancin damuwa Mahaifina ya kalleshi , yace " to Umar ko gaba karkayi kuka damu .
kayi kuka da kanka,sbd Shi ilimi abu ne me mahimmanci a rayuwar Dan Adam ban hanaka yin kasuwanci ba Amman nafi son ka dan samu illimi me zurfi .
Shi ilimi haske ne a rayuwa ,duk abinda mahaifina yasan zai yi Dan ganin umar ya amince da cigaba da karatu yayi km ya fada masa , babu irin shawarar da iyaye na basu bashi ba amma fir umar yaki amincewa yace shi sam a'a business yake da raayin .
Haka iyayena suka hakura suka barshi ba Dan ransu yaso ba sai Dan basa son matsa masa amatsayinsa Na maraya .


Bayan wasu kwanaki aka damu mahaifina da yawan kawo k'arar Umar jama'a kowa yace Umar yayi masa kaza ko yayiwa 'yarsa kaza.h k
mahaifina yasa me shi yayi masa fad'a sosai .


Amma mu a gidan da kuma kamanni duk inda kake neman mutumin arziki kona kirki Umar yakai, ko mahaifina da yakeyiwa Umar fad'a bawai dan ya yarda bane, dan matuk'ar yarda mun yarda da Umar.



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*


5


Sanu ahankali Cikin ikon Allah na samu gurbin karatuna anan University of Gombe, kullum k'orarin iyayen Mu shine suka inganta rayuwarmu tare da son faranta mana.ni da umar musamman sbd
, muguwar shak'uwar dake tsakanina dashi . dan duk inda ka ganni dole zaka ganshi, komai namu iri d'aya ake mana bbu wani bambanci atsakaninmu shiya wasu suke kiran mu 'yan biyu, babu wani sirri na da Umar bai sani ba.
haka Nina babu wani sirrin sa daban sani ba. Sosai nake matsanancin kaunarsa tare da maidashi tamkar Dan uwana Na jini .yadda nake jin umar acikin raina ko kanina da muka fito ciki guda bana yi masa irin son da nakeyiwa umar ..


Akwai wata yarinya a unguwar mu mai suna Yasmeen k'awar k'anwata tace sosai, sun yi masifar shak'uwa da junan su abin ma har ya wuce tunani, rana d'aya na tsinci kaina da mugun k'aunar Yasmeen amma babu wanda na baiyanawa .
Har Umar, nabar dai bar abin a raina. Ina cigaba da renan soyayyarta acikin zuciyata.


Haka zalika a b'angaren Umar ashe tuni sun tsunduma cikin soyayya shi da tilon k'anwa ta Ramlat, batare da wanda ya sani,b a.
tuni km har soyayya rsu tayi nisa.


"Umar wai bazaka raka ni bane, a 'yan kwanakin nan na rasa me kake yi a gida da dare idan nace kazo mu fita sai ka k'i,.Ko meyasa hk ?


murmushi kawai Umar yayi hade da yatsina fusakarsa yana kallon Abdul kasa kasa kana yace " kawai dai ban san fitar ne.
, nafisan na zauna gida tare da Mama da Baba ina taya su hira.
, kallon sa Abdul yayi da alamar rashin yarda atare dashi da km maganar sa.
" kai dai ka san dalilin dayasa kake kunshe kanka ciki gida yana maganar yana tafiya har dai yakarasa fice Daga gidan gabadaya.


Sakamakon ruwan saman da ake tsulawa yasa Abdul dawowa gida da wuri, yana danna kai 'cikin d'akinsu yaji hirar soyayya tsakanin Umar da Ramlat, d'an b'ata rai Abdul yayi sosai sannan yace " ke tashi ki fita, da fara'a Ramlat tace" Yaya mai ya faru?


"Nace ki fita ko, da sauri Ramlat ta fita,tana mamakin abinda yayanta yayi .
kallon Abdul, Umar yayi yana shafa sumar kanshi , Abdul yayi dariya yace"Ok dama wannan ne da yake hanaka fita kullum ko ?
ka lik'e a gida,kana sacewa kanwata zuciya ko ?
munafiki to Allah ya kamaka.


Dariya shima Umar yayi yace " kodai Allah ya kamamu, "kai da wa?

" ni kai cewar Umar yana dariya, shima Abdul dariya yayi sosai yace " kamar ya ban gane ba.
Kallosa Umar yayi da alamar zolaya ya fara wak'a "Yasmeen abar k'auna ta, dariya Abdul yayi sosai yakai mai duka, suka shiga wasa suna tsokanar junan su, Umar yace " haba d'an uwa har akwai abinda zaka iya b'oye man to ai har na tura mata sak'onka, ta kuma amince, ido Abdul ya zaro waje yace " kai haba?

" Wallahi da gaske nake maka sosai Abdul yaji dad'i had'i da rungome Umar ajikinshi yana yi masa godiya.


Washe gari Baba da Mama, da Umar da Abdul da kuma Ramlat da Auta duk muna zaune a parlor, muna hira Abdul ya kalli Mama yace " Mama d'anki fa ya fad'a soyayya, Ramlat naji haka ta zaro ido da alamar tsoro.
, Mama tayi dariya tace" ikon Allah ina kuma ya samu min sirikar?


Da sauri Umar ya mik'e ya rufewa Abdul baki yana janshi waje, yana dariya, shima Abdul dariya yake, dakyar Abdul ya kwace bakinsa yace " 'yarki ce ai, 'yar gida za'ayi, yana jin na fad'a ya sake ni yayi waje da gudu, Ramlat ma ta mik'e ta shige d'aki, sosai iyayen mu sukayi masifar farin ciki da soyayyar Umar da Ramlat dan su a tunanin su Umar yaran kirki ne, mai nagarta gashi nutsatstse zaifi rik'e musu Ramlat da daraja, shiyasa kowa ya nuna farin cikin sa da amincewarsa.


Soyayya sosai ta k'ara k'arko tsakanin Umar da Ramlat, a b'angaren Abdul da Yasmeen ma haka abin yake soyayyar su, dan kowa ya sani har iyayen su sun sani, dan haka aka tsaida ranar auren Abdul da Yasmeen, Umar da Ramlat da zarar sun k'are Secondary school.


Mummunar rana ta farko dabazan manta da ita arayuwata ba.
, lafiya lau muka ci abinci da Baban mu, mukayi hira yayi mana fad'a sosai akan gaskiya da rikon Amana, da zumunci, sosai yayi mana fad'a daga k'arshe yayi mana addu'a tare da fata na gari a rayuwar

Please Login or Register in order to submit comment