Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya Lailah a d'aki suka rufe, Sanata Sambo ya fita waje yana waya, mijin Hajiya Rabi ya kira yace " komai yake yazo gidan shi yanzu shida matarsa yana fad'a bai jira abinda zai ce ba ya kashe wayar, direct wajen limamin unguwar ya nufa, ya sanar dashi halin da ake ciki, limamin yace bakomai zai kira mutane 5 mu had'u zasu zo in sha Allah bayan sallar la'asar


A tare malaman da su Hajiya Rabi suka shigo lokaci d'aya, da sauri Alhaji mijin Hajiya Rabi ya k'arasa inda Sanata Sambo ke magana da malaman,Hajiya Rabi kuwa tunda taji kiran gabanta keta fad'uwa yana dukan uku-uku ta rasa mai yasa kwata-kwata hankalinta yak'i kwanciya, hannu Alhaji ya fara mik'awa masa suka gaisa, umarni Sanata Sambo yayi musu dasu shiga gidan gaba d'aya.


Fahad na inda yake ko motsawa bayyi ba yadda Sanata Sambo ya fita ya barshi haka ya dawo ya iske shi acikin mawuyacin hali, yayinda Kausar ta mannashi da k'irjinta tana zubar da hawaye, murmushin k'eta Hajiya Rabi tayi ganin halin da Fahad ke ci ya tabbatar mata da hak'onta ya cimma ruwa, bayan duk sun zauna a babban parlor Sanata Sambo ya umarci Sheemah da Haidar akan su fito da Momyn su, cikin mutuwar jiki suka mik'e, Hajiya Lailah na rik'e a hannunsu suka shigo parlor tana fisge-fisge da sambatu tana ci gaba da fad'ar abubuwan da sukayi ita da Hajiya Rabi,a razane Hajiya Rabi ta mik'e tace " Haukacewa Hajiya Lailah tayi?


Ai Hajiya Lailah nayi arba da Hajiya Rabi tayi kukan kura tayi kanta a haukace, kasa motsawa daga inda take tayi, sai su Haidar ne suka tare ta da sauri, dakyar sukayi controlling d'inta sannan malaman suka fara aikin su, Fahad ya kasa komai sai binsu da ido kawai da yakeyi kamar zararre, sai aka d'auki lokaci mai tsayi ana addu'a da karatun Qur'an sannan aka samu bak'in aljanin yayi magana inda yayi banin turo shi akayi ya shiga tsakanin Fahad da Kausar ya hana su kwanciyar aure, bayan sunne ya koma jikin Hajiya Lailah, dakyar aka samu ya fita daga jikin ta ta dawo hayyacinta bayan tayi attishawa sau uku, had'i dayin kallamatus shahada, shi kuma aljanin ya koma jikin Boka Jimrau bayan yayiwa Malaman bayanin idan ya koma jikin Boka Jimrau bazai tab'a fita har abada, zai kasance a cikin hauka har ranar mutuwarsa.


Sai da ta dawo hayyacinta sosai sannan ta fara bin ko'ina na parlor da kallo cikin rashin fahimta, ajiyar zuciya d'aya daga cikin malaman ya sauke had'i da cewa " Alhamdulillah ta dawo hayyacinta yanzu tana cikin hankali da nutsuwarta, a hankali Sanata Sambo ya kalli Ummi yace " maimaita abinda kikace d'azo, cikin kuka Ummi bayanin komai a gaban Hajiya Rabi da mijinta da sauran jama'ar dake wajen, kuka Hajiya Rabi ta fasa had'i da mik'ewa tsaye tace " ni zakiyiwa sharri Ummi, me nayi miki a raywarki ta duniya da kike nemana da wannan mugun sharrin? tsakani na dake Allah ya isa bazan tab'a yafe miki ba, ta k'arasa maganar tana matse-matsen hawayen munafurci.


Haqaye na zubowa Hajiya Lailah ta fara magana batare data kalli inda Hajiya Rabi take ba " a'a Rabi lokaci yayi daya kamata mu fara girbar abinda muka shuka, lokaci yayi daya kamata mu san me mukeyi mu dawo cikin hayaci da hankalin mu,, muna yara da mazajen auren da sune sanadiyyar jefamu cikin hakala, karki k'aryata Ummi domin duk abinda ta fad'a gaskiya ne, babu k'arya ko sharri aciki sai ma wasu abubuwan data rage wanda ita bata sani ba, amma ke kin san da hakan kuma nima na sani ta k'arasa maganar tana kallan Hajiya Rabi tana zubar da hawaye, tsayawa cak Hajiya Rabi tayi ta rasa abinda keyi mata dad'i a duniya.


Hajiya taci gaba " duk abinda kikaga Ubangiji yayi to akwai dalili dan Allah baya tab'a yin abu babu dalili, haka duk wanda kikaga yana aikata laifi irin namu asirinsa ya tuno ya kunya a idon duniya ya tuzarta d'aya, Allah yayi hakan ne dan yana san sa da rahamarsa, ma'ana dan mutum ya shiryu ya nutsu ya tuba ya koma ga Allah, amma duk wanda kikaga yana aikata laifi amma asirinsa bai tuno ba, bai kuma tuba ya koma ga Allah ba wannan Allah ya barshi, ya kuma rufa mana asiri ne har sai izuwa ranar sakamako sannan zai girbi abinda ya shuka, ya kunya a ranar lahira, wanda mu bazaso hakan ba, dan gwamma kunyar duniya sau 1000 akan ta lahira, duk wannan abu daya faru kece sila, kinga gaba kika k'ara ganin wani zai tunawa wani asiri dan yana aikata mummunan aiki kya hana shi, saboda tsakanin sa da mahaliccinsa ya kuma fiki sani amma ya rufa masa asiri, saboda duk wanda zai aikata laifi b'oya yake a inda yasan babu mai ganinsa saboda shida kansa yasan ba abu mai kyau zai aikata ba, mazinata da 'yan lesbian da sauran manyan laifuka sai sun shiga d'aki sun rufe suke aitawa, wasu sai cikin dare ma, haka Annabi yace " idan kaga wani bawa yana aikata aiki irin na 'yan wuta (sab'o) karka muzantashi (zagi) ko kayi saurin yanke masa hukunci dan kai ma Allah yana iya jarrabarka da irin tashi jarabawar dan jarawace.


Hajiya Lailah ta kwashe duk labarin komai ta bayyana tunda farko har k'arshe da duk irin aiyukan da suke aikatawa ta k'arashe maganar tana kuka, jikin Hajiya Rabi yayi mugun yin sanyi dan haka ta taka izuwa gaban Hajiya Lailah ta durk'usa cikin kuka tace " gaskiya ne Kawata nayi nadama nima, ta juya ta kalli sauran jama'ar dake wajen tace " duk abinda Ummi da Lailah suka fad'a gaskiya ne, amma Lailah bata neman maza mata kawai take nema nike had'a maza da mata.



Da k'arfi Alhaji ya runtse idansa yana jin zuciyar sa kamar zata fashe, yayinda Sanata Sambo yake jin kamar ya mutu saboda takaici, cikin takaici da nadama Sanata Sambo yace " idan kuma kuna da laifi, amma muna da laifi dan babu manyan masu laifi kamar ni da kai Alhaji da kuma sauran mutane masu irin halin mu, da farko duk namijin daya auri mace yasan yanayinta wajen jima'i shin mai hak'uri ce ko akasin haka, ni dai duk mun san yanayin matan mu amma mukayi watsi da buk'atar su, muka fita waje suna holewar mu da sa'anin 'ya'yan mu, abinda muka aikata a rayuwar mu ne muka fara tsintarsa tun yanzu, ni 'ya guda d'aya tak mace a duniya amma ta zama KARUWA saboda abinda nake aikatawa da 'ya 'yan wasu, kai kuma matarka ta sunnah wasu mazan ke amfani da ita saboda kai ma aikata hakan da matan wasu, domin suma matan da mukayi amfani dasu sun kasance 'ya'yan wasu, matan wasu sannan k'ananan wasu, na d'auka kud'i, abinci, da sauran kayan more rayuwa sune farin cikin iyali idan ka basu shikenan basu da wata sauran buk'ata a duniya, ashe ba haka bane, babban abinda zaka basu shine, ilimin addini su san waye Allah, su san musulci da dokokinsa, ka basu ingantacciyar tarbiyya ka kula dasu da lamuran su, Alhaji munyi kuskure a rayuwar mu ta duniya, mun tafka babban kuskuren da har mu koma ga mahaliccin mu yana bibiyarmu sai dai muyi ta istagfari ya k'arashe maganar yana matsanancin kuka.


Alhaji yasa magana yayi illa hawaye kawai dake zubo masa, Liman ne yayi gyaran murya yace" gaskiyar maganarka Sanata Sambo saboda mafi yawan matan da suke neman maza da aure su ko suke lesbian laifin mazan sune, kad'an daga cikin sune kwad'ayi da san abin duniya yake kai su, idan matan suna da zunubi to kuma mazan kuna dashi saboda kukuke sakin matanku da yaranku kamar dadbobi, ba tare da kunna bincikar aiyukan su ba, yanzu duniya ta lalace domin maza da yawan basa neman mata marasa aure sai masu aure, kuji tsoran Allah, ku tuna komai nisan jefa k'asa zai dawo, duk dad'ewar da zakuyi a duniya dole sai kun mutu kunje kun sameshi, ku dai na watsi da matayenku da 'ya'yayanku, Allah yace" duk wanda baya kishin iyalinsa bazai shiga aljanna ba, sannan Allah yace " duk wanda yayi zina da 'yar wani sai anyi da tasa, idan bai da 'ya ayi da matarsa, idan bai da mata ayi da k'anwarsa idan bai da k'anwa ayi da mahaifiyarsa.


Cikin kuka Fahad yace " tabbas haka ne Malam domin alk'awarin Allah baya tashi, ni nasan ba wani abu ne ke bibiyata ba sai alhakin Aisha, yarinyar danayiwa fad'e har hakan yayi sanadiyyar mutuwarta, nasan hakk'in Aisha yayi ta bibiyar rayuwa ta kenan, nasan bazan tab'a zama lafiya a duniya ba, gashi tun a duniya na fara ganin iftila'i dan wannan babbar masifa ce, ace mahaifiyarka, k'anwarka da k'aninka su rink'a neman su kwanta da matarka ta aure, Allah ne ya nunamin ishara tun a duniya, idan ni bare nayi amfani da Aisha to gashi mahaifiya ta, da k'anena suna neman mata ta, kuma babu k'azantar data fi wannan, kamar yadda yace, Allah yace " duk wani yayi zina da 'yar wani sai anyi da tasa, ko matarsa, k'anwarsa da mahaifiyarsa, to gashi ni dai na gani da ido na anyi zina da k'anwa ta, anyi da mahaifiya ta, matata dana k'ara 24hrs da anyi da ita, saura 'yata ta cikina kad'ai ya rage, cikin kuka yace " dama nasan Allah bazai tab'a yafe min hakkin Aisha kuda na tuba ba, ya k'ara fashewa da matsanancin kuka yana cewa " Allah na tuba, ya Ubangiji ka yafe min, Allah kai kace kana san mutane masu tuba.


Gaba d'aya wajen kowa ka gani waye yake zubarwa cikin matsanancin bak'in ciki, a hankali Santa Sambo yace " ba kai kad'ai ne keda laifi ba nima ina da laifi domin nayi zina da 'ya'yan wasu, shiyasa nima akayi da tawa 'yar da mata ta, Alhaji ya kasa cewa komai sai hawaye kawai dayake zubarwa saboda bak'in ciki da takaicin rayuwarsa shi kansa yasan ya tsula tsiya a duniya gashi tun kan aje ko'ina ya fara girbar kayansa, bai tab'a nadamar abinda ya aikata ba sai yau.


Liman ya kalli su Hajiya Lailah dake ta kuka yace " sannan kuma matan dakun san laifin da kuke aikatawa da irin azabar da Allah ya tanadarwa mataye masu irin halinku da kun dai na, kun tuba kun koma ga Allah, sosai malaman nan sukayi musu nasiha mai ratsa jiki, jini da jijiya, ya fad'a musu irin azabar da Allah ya tanadarwa masu laifi irin nasu, daga k'arshe yace " Allah gafurur rahim ne shi mai yafiya ne a koda yaushe, ku yawaita istigfari da hailala had'i da salatin Annabi, kuyi tuba da zuciya d'aya irin wanda Allah keso, sannan ku nisanci sab'o da masu aikatashi, ya juya wajen su Sanata Sambo yace " wannan ya isheku izna daku damasu hali irin naku, kuma sai kuyi ta istigfari ku tuba zuwa ga Allah, ku jawo iyalin ku jikinku, ku kula dasu da lamuransu, ya maida kallansa ga Fahad yace " karka ce Allah bazai tab'a yafe maka ba domin shi mai yawan yafiya da rahama ne, ka tuba irin yadda Allah keso, kaje ka biya diyyar Aisha, sannan ka ruk'i iyayen ta yafiya, sannan kaima ka yawaita istigfari.


Daga k'arshe ya rufe taro da addu'a suka fita, bayan sun fitane Alhaji ya nunfasa yace " Sanata ina da shawara, da sauri Santa Sambo yace " wacce irin shawara? "tunda duk mun gane kuranmu mun tuba mai zai hana mu had'a Sheemah da Farouk d'an waje na aure juma'ar nan mai zuwa, da sauri Sanata Sambo yace " kai Masha Allah amma ka jawo shawara mai kyau, amma kana ganin zai yarda? "mai zai hana ya yarda shi aka san me yake aikatawa, sannan Haidar ma ya fita da matar da yake so a had'a ayi auren lokaci d'aya, cikin sanyin jiki Haidar yace " ni bani da zab'i, na baku zab'i, murmushi Sanata Sambo yayi yace "zan nema maka auren k'anwar Kausar MEENAL, da sauri Fahad ya d'auko yana kallan Kausar dan yaga reaction d'in da zatayi, aiko a firgice ta d'ago kai tana kallan Sanata Sambo a hankali ta mayar da kallan ga Fahad wanda shima ita yake kallo, "Alhamdulillah Alhaji yace daga nan aka sallami kowa.


Da sauri Kausar tabar wajen tana shiga part d'inta ta wuce bedroom ta fad'a kan had'i sakin kuka tana cewa " wallahi bazan tab'a bari Meenal ta shigo wannan baud'ad'an gidan ba, ni dai da Allah yasa K'ADDARA TAH ce hakan to na karb'e ta, tun da ta shigo shima ya shigo ya zauna a kusa da ita batare data sani ba, jin abinda Kausar tace yasashi sake fashewa da matsanancin kuka, kukan shi data jine a kusa da ita ne yasata d'agowa, ganin yadda yake kuka kamar k'aramin yasa zuciyarta karaya, cikin kuka Fahad yace " nasani Kausar, damma Allah yasa ke mai hak'uri ce shiyasa, amma ki sani ina sanki ina miki mugun son da ba kowanne namiji ne yake yiwa mace irinsa ba, tun ranar dana fara d'ora idona akanki Allah ya jarrabeni da muguwar k'aunarki, da sauri Kausar ta tsaya kukanta cak had'i kallansa a razane ganin yadda tayi ne yasashi yacewa " yes Kausar I LOVE MADLY & DEADLY, I LOVE YOU SO MUCH WITH ALL MY HEART & EVER END.


Koda ke zaki iya rabuwa dani saboda wannan dalilin ki sani ni komai za'ayi, koda bakin bindiga bazan tab'a iya rabuwa dake ba, a hankali ya zame yayi kneel down yana kuka yace " please Kausar karkice zaki rabu dani idan kika rabu dani mutuwa bazan iya ci gaba da rayuwa, wallahi ko yanzu abin yayi min yawa ni kunyarki ma nakeji akan abubuwan nan, gaba d'aya jikin Kausar yayi mugun sanyi, tausayin mijinta ya kamata, tasan yanzu ne zata nuna masa ita mace ta gari ce, yanzu ya kamata su raba bak'in cikin sa tare, a wannan lokacin ne ya kamata ta jawo shi jikinta ta kula da mijinta ta rarrashe ni ta bashi kulawa, tasan yanzu idan ta nuna masa damuwarta abin zayyi masa yawa ya kamata ya samu sauk'i da sassauci daga gurinta, a hankali ta rungume shi tana kuka itama, cikin kuka tace " I love you too, i love you so much, goge hawayenta tayi sannan ta shiga rarrashinsa tana baashi hak'uri, tana nuna masa wannan jarabawa ce yayi k'ok'arin cin tasa jarabawar, sa da taga hankalinsa ya kwanta sannan ta mik'e tace " bari naje nayi mana girki, jawo ta jikinsa ya kuma yace "a 'a nafisan najiki a jiki na, cikin shagwab'a tace " ni dai bana san na barka da yunwa karka ulcer ta kamamin kai, murmushi yayi yace " idan ina tare dake yunwarma bazata zo ba, zata kuma yin magana yayi saurin had'e bakin su.


Washe gari Fahad da Kausar suka je gidan su Aisha, dakyar iyayenta suka yafe masa sannan yayi musu alkhairi mai yawa bayan ya biya diyyarta ya had'a musu da 5 million, cikin farin ciki suka dawo gida dan ji yayi kamar an sauke masa dala da gwauran dutse daga kansa, daga nan direct gidan su Kausar suka wuce, suka yini anan iyayen ta suke sanar mata su Sanata Sambo sunzo neman auren Meenal murmushi had'i dayi musu addu'ar sanya alkhairi, daga nan suka wuce gidan Ni'ima wacce take d'auke da cikinta cikin murna suka tari juna, basu baro gidan ba sai 10:10pm.


Ranar juma'a aka d'aura auren Sheemah da Farouk Meenal da Haidar, amare suka tare a gidajensu, yayinda Fahad ya giniwa iyayen Kausar makeken gida ginin zamani, Haidar kuma ya bawa Malam jari mai yawa had'i sabuwar mota, Sanata Sambo yakai iyayen su Kausar Hajji da Umara.



BAYAN SHEKARA BIYU


Tun daga wannan rana su Hajiya Lailah suka shiryu suka daina duk wasu mugayen aiyukan da suke yi, suka tuba tsakanin su da Allah suka shiga yin azumi da istigfari suna aiyukan alkhairi a duniya domin neman yafiyar mahaliccinsu, haka ma Alhaji da Sanata Sambo sun daina komai sun nutse sun maida hankulansu kan iyalansu kun koma ga Allah sosai basu da wani aiki taimakawa al'umma da dukiyar su suna istigfari, sosai tsoran Allah ya shiga zuciyoyinsu, haka ma Sheemah da Haidar.


Allah ya bawa Kausar haihuwar yaronta d'aya sai da tana d'auke da wani tsohon cikin, Ni'ima kuwa tana da yara biyu mace da namiji, yayinda Meenal keda yarinyarta mace mai sunan Kausar, bayan Abdul ya dawo hutu Nigeria da Yasmeen da yaransu daya tashi komawa Holland Fahad da Kausar suka bisu dan acan ta haifi d'iyarta mace.


A hankali Kausar ta kalli Basma da Zarah tace " to kunji labari na, ajiyar zuciya suka sauke dukansu suka kasa cewa komai saboda duk tsiya Hajiya Lailah mahaifiyar Fahad ce kuma dole suyi masa kara, cikin mutuwar jiki Basma ta kalli Zarah tace " Bismillah, a hankali Zarah ta kalli Naseer yayi mata alama da eh, gyaran murya tayi had'i da sauke ajiyar zuciya sannan ta fara.



LABARIN ZARAH



MOMYN ZARAH
[29/01, 11:44] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*



44



*LABARIN ZARAH!!!*



cikekken sunana Fatima Muhammad, ana kira da ZARAH ne kasancewar sunan mahaifiyata aka mayarmin, mu 'yan asalin garin Daura, amma ni haifaffiyar garin kano ce, mahaifina Alhaji Muhammad Daura cikekken mutum ne kamili mai ingantacciyar nutsuwa da kamala dattijo ne mai nagarta, wanda asali kasuwanci da neman nakai ne yasa ya baro tushensa, danginsa da iyayensa ya shigo garin kano, a lokacin yana d'an matashin sauri dan bazai wuce shekaru sha takwas ba, dan a lokacin yana ji k'arfi na samartaka da k'uruciya ya shigo garin kano, cikin ikon Allah yasa ya shigo garin kano da k'afar dama dan Allah ya had'ashi da wani attajirin mai kud'i d'an kasuwa Alhaji Abdullahi, d'an kasuwa ne shahararre a zamanin sa, mahaifina ya fara zama yaron gidan Alhaji Abdullahi kamar Almajiri, yana yi musu aikace-aikace gami da aike, a hankali Mahaifina ya fara shiga ran mutanan gidan yana k'ara samun kusanci dasu kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana.


Dan duk aiken da zakayiwa mahaifina ko aikin da zaka sakashi zayyi maka shine bisa gaskiya da amana, hakan yasa lokaci d'aya ya samu shiga sosai a gidan da zuciyar Alhaji Abdullahi, ya wuce duk sauran ma'aikatan gidan, Alhaji Abdullahi ya kasance mutum ne nagari kamili mai yawan kyauta gami da adalci gashi kwata-kwata bashi da mugunta balle bak'in ciki hakan yasa Allah yake k'ara bashi nasara akan dukkan harkok'insa, Alhaji Abdullahi yana da matar aure d'aya tal tunta ladan noma, suna yara biyar biyu mata uku maza, Fatima wacce itace 'ya ta biyu a cikin yaransa jininsu ya had'u sosai da mahaifina dukda tana k'aramar yarinya sosai a lokacin da bazata wuce shekaru biyar ba, gaskiya da amanar da mahaifina ya rik'e itace silar d'aukakarshi zuwa babban matsayi a rayuwa, nagartarsa da Alhaji Abdullahi ya gani ne yasa ya mayarda dashi kasuwa wajen kasuwacinsa, lokaci d'aya kasuwanci ya k'ara hab'aka yana ci gaba hakan bak'aramin k'ara d'aukaka darajar mahaifina yayi a wajen Alhaji Abdullahi ba har zuwa wajen abokansa da jama'ar gari dan duk inda Alhaji Abdullahi ya zauna bashi da wata magana sai ta gaskiya da amaar yaronsa Muhammad, sosai Alhaji Abdullahi ya aminta da mahaifina harta kai daya d'orashi akan harkokin kasuwancin sa sosai saboda babu kyashi a zuciyar Alhaji Abdullahi ko takurawa, sosai ya d'agawa mahaifina k'afa ta yadda idan aka fita saro kaya shima zai samu nashi.



Bayan kamar shekaru bakwai kasuwanci ya hab'aka sosai dan yanzu idan aka saro kaya zama akeyi ayi lissafi a raba ribar duk yawanta gida uku anan take Alhaji Abdullahi zai d'auki kaso biyu cikin uku ya bawa mahaifina kaso d'ayan, kafin wani lokaci mahaifina ya fara amsa sunansa shima da kansa ya soma shahara, bai tsaya wasa da almubazaranci ba ya soma tanadarwa kansa kadarori da k'ara fad'ad'a kasuwancimsa, duk wata harkar kasuwanci data samu koda badaga b'angaren Alhaji Abdullahi bane sai mahaifina ya sanar dashi yayi masa tayinta, saboda mahaifina mai sa'a ne, idan kuma akayi harkar sai Allah yasa a dace a samu riba mai tsoka, hakan ya kuma k'arawa Alhaji Abdullahi so da k'aunar mahaifina a zuciyar sa, babu wanda Alhaji Abdullahi ya yarda dash gida da waj sama da mahaifina.


Alhaji Abdullahi da kansa ya fara sh'awar mahaifina ya zauna kusa dashi har abada, dan haka da kansa yayiwa mahaifina maganar ya kamata ya samu gida ya siya ya dawo da iyayensa da k'annansa kusa dashi suma ya bud'a musu su samu na kansu dan nan gaba da zarar an k'ara wasu shekaru nauyin zayyi mishi yawa, kuma shim ya kamata ya fara k'ok'arin mallakar mallakar gidan zama nashi na kansa, ba musu mahaifina ya amince,kasancewar akwai kud'i a kasa yasa batare da b'ata wani lokaci ba aka fara neman fili anan kusa da Alhaji Abdullahi, cikin sa'a a kasamu wani makekken fili gari guda zan za'ayi iyayin primary school, take aka siyi filin aka fara gina matafaren estate, dan so yake yayi family hause babba sosai.


Yayinda daga b'angaren d'aya sabo da shak'uwa ya fara kid'ewa yana komawa soyayya mai k'arfi tsakanin mahaifina da kuma Fatima 'yar Alhaji Abdullahi, ana cikin haka Allah ya k'ara bawa matar Alhaji Abdullahi k'aruwar haihuwar d'iya mace aka saka mata suna ZAINAB, yayinda tuni an fara gina katafaren filin mahaifina harma an kusa gamawa dan sosai ake yin ginin ba wani b'ata lokaci, b'angaren iyayensa aka fara gamawa dan haka yaje har Daura ya sanar dasu cewa nan da sati d'aya zasu koma kano da zama gaba , kin amincewa sukayi da farko, sai dakyar Abban mu ya shawo kansu suka amince, sati na zagayowa shi da kanshi yazo ya z'auke, sunyi murna da farin ciki sosai ganin makeken gidan ga kyau da had'uwa.


Bayan iyayensa sun dawo ba'a jima ba aka gama ginin gidan kaf kusan part 16 ne a gidan banda filin ball da filin wasa dana motsa jiki, ganin an gama gidan yasa yiwa Alhaji Abdullahi maganar Fatima wanda dama shi tuni yasan da maganar ba tare da wani b'ata lokaci ba akayi biki aka kai mahaifiyata gidan ta.



Duk wani burin duniya mahaifina ya d'auka ya d'ora shi akan matarsa Fatima bashi da wani burin dayafi ya faranta mata ranta duk wani da take so matuk'ar baifi k'arfinsa ba yana yi mata shi, sosai yake bata kulawa, shekara biyu da auren su amma ko b'ari Mamana bata tab'a abin ya dame su sosai amma Abba na ya danne tashi damuwar yana rarrashin Mama na, sunje asibitoci da dama amma duk inda sukaje maganar d'aya ce lafiya lau Allah ne dai bai kawo lokaci ba, ganin halin da Mama na ke ciki yasa Abba na rok'ar sirikinsa Alhaji Abdullahi akan a basu Zainab , ba musu Alhaji Abdullahi ya amince dan babu abinda Abba na zai tambaya a hannunsa ya iya hana shi matuk'ar yana dashi, Zainab nada 2yrs ta koma hannun yayarta mahaifiyata, tun daga ranar Mamana bata k'ara bak'in ciki ko damuwa akan rashin haihuwa ba, dan ta d'auki Zainab k'anwarta kamar 'yarta ta cikinta.


Ana cikin haka Fatima da kakata mahaifiyar Mamana da Alhaji Abdullahi suka dame Abba na akan dole sai ya k'ara aure dan kar ganin Fatima 'yar su ce yasa shi kuma ya cuci kansa, amma fir yak'i ganin haka yasa Fatima fara yi masa akan dole sai ya k'ara aure amma fafur yak'i dole suka hak'ura suka kyale shi.



BAYAN SHEKARU 14



Duk wanna tsayin shekarun Allah bai bawa Mama na haihuwa ba kai ko b'ari bata tab'a yi ba, hakan yasa Alhaji Abdullahi da Kakata suka matsawa mahaifiya akan dole fa wannan lokacin yayi aure ko yak'i ko yasa, dole tasa Abba nah ya yarda badan yaso ba dan shima iyayensa sun matsa masa akan dole

Please Login or Register in order to submit comment