Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda tayi aman jini ya nuna mata cikin kuka yace " kin gani ko? saboda tsabar takaici da bak'in cikin ki, ji yadda ta rink'a aman jini, tana kokawa da ranta dan tanaso taci gaba da rayuwa damu, amma kika sata dole ta barmu badan ranta na so ba ya k'ara fashewa da fitinannan kuka.


A razane kamar an tsikare shi ya mik'e tsaye ya kuma damk'ar kanta yayi waje da ita, yana isa parlor yayi jifa da ita a k'asa ya durk'uso da fuskarsa dai-dai fuskarta yace " kin san menene magana ta ta k'arshe da ita, batayi magana ba illa kansa dake tayi, yace wasiyya akan ku keda wancan lusarin mijin naki, ya d'ago da kansa ya k'ara kurma ihuuuuuun mutuwa gaba d'aya idanuwansa sun canja launi, sun tashi daga farare zuwa ja, sai da yayi mai isarsa sannan ya kuma juyowa wajen Zainab a haukace yace " maganar ta ta k'arshe shine in kulan mata da Momynta, in yafewa Dadynta ko d'anta data haifa wanda shine k'arami bata fara ambatan sunanshi ba, sunanki ta fara ambata , dan haka ZAINAB KECE AJALIN ZARAH, ya fad'a da k'arfi.


A haukace Zainab tayi harabar gidan ba d'an kwalli ba takalmi balle hijab, tana ihuuu kamar zararriya, babu wanda ya iya motsi balle ya taro ta sai Mannir da shima jikinsa ya gama yin mugun sanyi, ya bita a rud'e yana kiran sunanta tana gaf da fita daga get d'in gidan ya cimmata, cak ya d'auke ta, tana ihuuuu da zille-zille a parlor ya direta, dai-dai lokacin da Abban Zarah yace " lokacin sallar juma'a yana neman ya wuce, mu hanzarta mu kai ta makwancinta, ba musu duk suka mik'e suna shirin d'aukar gawar Zarah, fitinannan ihuuuu Naseer yayi had'i da rik'e gawar gam.


Yana ihuuuu yana gunji yana kuka, had'i da sambatu, " wallahi babu inda zaku kai min Zarah ta, bata mutu ba, nasan bazata tab'a tafiya tabarni ba, munyiwa junan mu alk'awarurka da dama, kuma nasan Zarah akwai amana da gaskiya bazata tab'a karya min alk'awari na ba, dan Allah Dady ku tausaya min karku rabani da Zarah please, wallahi ina santa ina mata mugun so, wallahi bata mutu ba, dan Allah karku raba mu muna matuk'ar k'aunar junan mu da gaske da kuma zuciya d'aya ya k'arasa maganar cikin mahaukacin kuka.


Sosai aka kama kokawa tuburan muraran da Naseer ya rik'e Zarah gam ya hana a tafi da ita, ya zage ya rink'a tikar hauka muraran, ya zama cikekken mahaucin tuburan, sai da kyar Dady da Abban Zarah da Mannir suka taran masa suka danne shi suka jashi, aka danna shi a d'aki aka rufe, buga k'ofar Naseer ya shiga yi yana ihuuuu kamar zai b'alla k'ofar, ana zuwa za'a kuma d'aukar gawar Zainab ta rik'e gawar gam tana kurma ihu, gaba d'aya jikinta rawa yake yana muguwar tsuma kamar wacce ake kad'awa ganga.


Itama dakyar Mannir ya jata ya danna a d'aki tana ta turjewa tana tik'ar hauka, tana ihuuuu gami da fisge-fisge, Abban Zarah Naseer ya shiga kwalawa kira yana rok'onsa " dan girman Allah Abba ka bud'e naje na bunne Zarah da kai na, ko zuciya ta ta huta, wallahi Abba matuk'ar bani na binne Zarah da kai na, na saka ta a kabari da hannu ba zuciya ta bazata tab'a barin rayuwa ta ta huta ba, bazan tab'a yarda Zarah ta mutu da gaske, kun sanya min kokonto kennan har k'arshen rayuwa ta, dan Allah ku bani wannan damar dan in rayu cikin salama batare da kokonton komai ba, yana bubbuga k'ofar kamar zai b'allata yake maganar.


Ganin maganar da yake tana da matuk'ar mahimmanci da amfani yasa Abba tsayawa a bakin k'ofar d'akin yace " kayi min alk'awarin idan na bud'eka bazaka tab'a yimin hauka ba, da sauri Naseer yace " nayi maka alk'awari Abba, batare da Abba yace komai ba ya bud'e shi, yace " kaje bedroom d'inka ka shirya kazo mutafi muna jiranka a waje, "a shirye nake Abba muje kawai, Abba bai k'ara cewa komai ba ya wuce Naseer yabi bayansa, tunawa da Naseer yayi a daren jiya ya kashe arna kuma bayyi wankan tsarki bane yasa shi cewa Abba bari na dawo, kallansa kawai Abba yayi.


Naseer yana wankan yana kukan bak'in ciki mai sauti, harya gama wankan ya zura kaya ya fito, sanin komai yana iya cakud'ewa ne idan Naseer ya fito yaga gawar Zarah yasa akayi saurin sata a mota kafin ya fito, yana kukan ya shiga mota suka tafi, suka bar Momy da Ikram na kuka, yayinda Zainab ke cikin d'aki kulle tana hauka, a babban masallacin juma'an gidan sarki akayi sallar gawar Zarah Naseer nata kuka har a lokacin yak'i yin shiru, daga nan sukace mak'abartar d'an agungi dake wajen k'ofar Na'isa, kafin suje har anyi ginin kabari, sai da akayi mata addu'a sannan Naseer da Abba suka kama gawar Zarah suka sakata a makwacinta na k'arshe, Dady, Abba na zubar hawaye amma Naseer kuka yake sosai dan ya kasa dannar zuciyar sa, da hannunsa yau yasa Zarahn sa a kabari, dole babu yadda zayyi da kanshi ya mayar da k'asa ya bunne ta.



_Am so sorry fans, da mutuwar Zarah, ina san nayi muku tuni da كل نفس ذائقه الموت, duk mai rai dole mamaci ne, bawai ayita karatun novel na zallar soyayya, hot romance and sex ba, ya kamata a rink'a sirkawa da abinda ya riga ya zama dole kuma yana kan kowa, mu dai fatan mu Allah yayi mana rahama yajik'an mu, ya yafe mana yasa mucika da imani muna masu ambaton اشهد ان لا اله الا الله واشهد ان محمدا عبده ورسوله_


~Wannan kenan~


Tunda aka fito daga mak'abartar Naseer ya d'ora hannu aka ya zunduma ihuuuuuuuuu had'i da rugawa a guje,, ya zage ya zama cikekken mahaukaci ya rink'a hauka tuburan muraran, a kid'ime Dady yayiwa mutanen dake tare dasu magana akan su taimaka masa su kamo Naseer, da gudu wajen mutane 10 suka bi bayansa ciki kuwa harda Mannir, dakyar da jib'in goshi suka samu nasarar kamo Naseer, sai da suka ci uwar dambe sannan yayi matuk'ar basu wahala sannan suka samu nasarar danna shi a mota suka danne shi driver yaja motar.


Koda aka je gida sai da akayi fama sosai sannan aka samu aka saka shi a d'aki aka kulle, fashe-fashe Naseer ya shiga yi a bedroom d'in nasa, duk wani abu daya danganci glass sai da yayi rugu-rugu dashi ya fashe komai dake d'akin, ya rink'a ihuuuuuuu yana hauka gami da matsanancin kuka mai tsananin cin rai, kowa a gidan jikinsa yayi matuk'ar yin sanyi kowa ka gani cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa yake baka jin komai sai sheshshekar kuka, Zainab kuwa itama sai hauka take a d'akin da aka kulle ta tana kuka kamar ranta zai fita tana dukan k'ofar.



Bayan kwana akwai da rasuwar Zarah aka share makoki, kuma tunda aka rufe Zainab da Naseer ba'a bud'e su ba saboda haukan da suke, sai ranar da akayi sharar makoki sannan Alhaji Abdullahi yace a fito da su, ba musu aka bud'e su, duk sun rame sun fita hayyacin su sunyi bak'i sosai kamar ba su ba, Zainab da sauri ta fad'a jikin Abban Zarah ta k'ara sakin hargitsatstsan kuka cike da tsananin nadama cikin kuka tace.


" Abba Zarah ta tafi ta barni, Abba meyasa Zarah tayi min irin wannan hukuncin mai tsananin gaske, dan Allah ka taimake ni ka bata hak'uri kace ta dawo ina tsananin k'aunar ta, duk abinda nayi, nayi ne bisa zafin zuciya, amma yanzu nayi matuk'ar nadama, da danasani, na tuba ya Allah استغفر الله و اتوب اليك na shiga uku ina zan saka kaina da rayuwata, idan laifi nayiwa Allah ya hure ni da irin wannan masifar mai zafi, Allah na tuba, ka yafe min ya Allah, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai tab'a zuciya, take jikin kowa yayi mugun yin sanyi zuciyar kowa ta karye, kowa ya shiga zubar da hawaye, Naseer ko tunda ya fito ya koma gefe ya rakub'e bai kuma cewa k'ala ba, gaba d'aya ya koma miskini kalar tausayi.


Hawaye na zuba daga fuskar Abban Zarah ya shafa kan Zainab yace " wanda ya bamu ita ya kuma fi mu santa ya karb'i abarsa dan alk'awarin Allah baya tashi, babu abinda Zarah tafi buk'ata daga gare mu yanzu sama da addu'a shine kad'ai hanyar da zamu nuna mata tsantsan so da k'aunar da muke mata, muna nan duk zaman jiran namu lokacin komawa ga Allah muke, domin gaba d'ayan mu matafiya ne, komai dad'ewar dazakayi a duniya dole akwai ranar da zaka barta ka amsa kiran mahaliccinka.


" Dan mutuwa bata kwankwasa k'ofa, kuma Allah baya tab'a barin wani dan wani yaji dad'i, idan lokacin mutum yayi ko 1 second baza'a tab'a k'ara masa, a koyaushe, a ko'ina idan lokaci yayi tafiya zamuyi batare da wani b'ata lokaci ba, shin kana ina, me kake aikatawa a dai-dai lokaci nan, wallahi idan tazo aduk yadda kake tafiya zakayi, shiyasa ake san a koyaushe, a ko wanne lokacin mutum ya kasance yana aikata alkhari, ana san d'an Adam ya kasance mai tsoran Allah, mai aikata alkhari a kowacce rana dan yanzu mutuwar bazata ake yi, sai a kwanta dakai ba'a tashi da kai ba, ko'a tashi dakai ba'a kwanta dakai ba, dan haka mu kasance masu tsoran Allah da tunawa da ranar sakamako, mu kyautata mu'amular a tsakaninmu, mu kyautatawa junnanmu zato, mu zamo masu yafiya da afuwa, mu zamo masu zumunci, mu zamo masu duban laifukan kan mu, bana wasunmu ba, mu zamo masu yiwa kanmu hisabi.


Sosai Abban Zarah yayi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga k'arshe Alhaji Abdullahi ma ya k'arba yayi iya yinsa akan yadda da k'addara da jarawar Ubangiji, haka ma Dady yayi iya yinsa, dan gaba d'aya jikin su yayi mugun yin sanyi, sun saduda, cikin ikon Allah sosai zuciyar Naseer tayi sanyi, ya ji sauk'in abinda yake ji, zugi, da rad'ad'in da k'irjinsa yake masa yaji ya ragu sosai, haka ma tafasa, k'ona, azalzala, zafi, k'unci, da zuciyarsa ke masa yaji duk sun gushe, a hankali Naseer ya mik'e ya d'auki Na'eem dake cinyar Mannir ya mik'awa Momy batare dayayi magana ba ya juya ya nufi bedroom d'in sa, kiran sunansa Alhaji Abdullahi yayi " Naseer! tsayawa yayi cak batare daya jiyo ba, " ka yawaita fad'ar

انا لله و انا اليه راجعون
اللهم اجرني في مصيبتي واخلفلي خيرا منها
استغفر الله
سبحان الله والحمد لله والله اكبر
حسبنا الله و نعم الوكيل الحمد لله

" in sha Allah, Allah zaya yaye maka damuwar ka yayi maka maganin damuwar da kake cki, ya ya gusar maka da bak'in cikin dakake ciki, murmushi Naseer yayi masa batare dayace komai ba ya shige bedroom d'in sa, ya kulle.


Addu'a Dady yayi aka shafa, Dady ya kalli Zainab yace " yaushe zaki koma gidan ki? cikin muryar kuka tace " sai anyi sadakar bakwai, "ok kawai Dady yace, Momy dai batace komai ba illa rungume Na'eem datayi a k'irjinta tana hawaye, tana k'ara jin tsananin tausayin yaron a ranta, ranar da daddare Naseer na kwance wajen karfe 1:00am na dare ya kashe gaba d'aya light d'in dake bedroom, ya kwanta rigingine yana kallan sama ya tsunduma duniyar tunani yayinda hawaye ke zubo masa.


A hankali yaji motsi a gefensa, cikin mutuwar jiki ya juya b'angaren dayaji motsin, Zarah ya gani zaune a gefensa sanye da doguwar riga ta atamfa ta saka hijab tana yi mishi murmushi hawaye na zuba daga idanunta zuwa kuncinta, a hankali tasa hannunta, ta shafo fuskarsa, zuwa sajensa, ta cusa hannunta cikin sumar kansa cikin muryar kuka tace " Uncle bakayi min adalci ba, da ma wannan ce irin soyayyar da kake min, kasan bana san b'acin ranka balle har yakai ga kayi kuka, Uncle matuk'ar kana san na kwanta a kabarina cikin salama kayi min alk'awarin baka k'arayin kuka, yana hawaye ya girgiza mata kai, "a'a kayi min magana kace kayi alk'awarin baka k'ara kuka cikin rawar murya yace " nayi miki alk'awarin ban kuma kuka, amma me yasa kika tafi kika barni, murmushi tayi takai masa kiss, lumshe ido Naseer yayi, jin shiru yasa Naseer saurin bud'e ido, ganin wajen yayi ba kowa mik'ewa yayi ya kunna light yaga kwata-kwata ba alamun Zarah, hannu ya d'ora akansa yana shirin kurma ihuuuuuuu sai ya tuna da alk'awarin daya yiwa Zarah, dan haka yayi saurin maida kukan sa ya shiga kukan zuci, ya tabbatarwa da kansa Zarah ta fara yi masa gizo, mik'ewa yayi ya shiga bathroom ya d'auro alwala, yazo ya tada sallah, tun daga ranar Naseer ya daina haukan kuka da ihuuuuuuu ya koma kukan zuci kawai.


Ya zama so silent kamar bashine Naseer d'in da, mai yawan wasa da dariya, mai yawan san barkwanci da yawan tsokana ba, duk ya zama wani iri dashi kwata-kwata baya magana, kullum yana d'akinsa rufe idan kaga ya fito to masallaci zashi, dan ko abinci baya ci, sai Momy ta matsa masa dakyar yake shan tea ko coffee.


Ranar sadakar bakwai Naseer yana kwance a bedroom d'in sa ya rink'a jiyo magana sama-sama, kasancewar baya san hayani ko yawan magana yasa Naseer mik'ewa dan ya sawa kofarsa key, yana kaiwa dai-dai k'ofar ya jiyo maganar Zainab na cewa " Momy duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e Na'eem sama dani, dan Allah Momy ki bani shi, tab!!!! Wata irin muguwar zabura Naseer yayi a sukwane yayi waje bibbiyu yake taka step d'in saboda tsananin sauri.....................



A zafafe ya fisge Na'eem daga hannun Zainab a matuk'ar fusace ya kalleta ido cikin ido yace " lalle Zainab ke cikekkiyar mara kunya ce, fitsararriyar zamani ce, ke yanzu idan kina da kunya da cikekkiyar nutsuwa ko bana raye kyama soma tab'a Na'eem?


"Ko an gaya maki na manta abubuwan da kika yi akan shi, tun kan yazo duniya tun yana cikin mahaifiyarsa, sai yanzu ne zaki nuna so da damuwarki akan sai yanzu zaki kula dashi, ko shima kina san na bak'i rok'onsa ne ki salwantar da rayuwar sa kamar yadda kika salwaantar da rayuwar mahaifiyarsa?


"Ko ke a zantan ki bazai samu labarin kashe masa uwa da kika yi ba?


"Ko kina san wanke laifin ki ne a wajensa dan kar ya girma ya d'au fansa?


"To bari kiji matuk'ar mahaifinsa Naseer Mustapha yana raye sai ya d'au fansa, kuma karki d'auka kinci banza ko rayuwar Zarah ta tafi a banza, dan wallahil azim bazan tab'a barin makasan Zarah su rayu cikin farin ciki da walwala ba.......


Ihuuuunn kuka Zainab ta zunduma had'i dayin kukan kura tayi kan Naseer.........





MOMYN ZARAH


[14/02, 22:00] Atk: Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp



```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





57





Kukan kura tayi,tayi kan Naseer a fusace, murmushi Naseer yayi had'i da gyara tsaiwarshi yana jiran k'arasowarta, cikin zafin nama, Mannir yayi wuf ya tare ta dan yaga shirin da Naseer yayi yana jiran k'arasowarta, fisge-fisge ta fara yi tana son kwace kanta daga rik'on da Mannir yayi mata, amma inaaa yayi mata mugun rik'on da bazata iya kwacewa ba.


K'ara tayi mai k'arfi ta fisge kanta daga jikin Mannir ta durk'ushe k'asa had'i da fasa kuka mai k'arfi, hawaye na zubowa Naseer yace " Zainab kin cuce mu, akan cikin yaron da kike so abaki ki rik'e kikayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa, saboda rashin yadda da k'addara, kuka zage ke da mijinki kukayi mata dukan mutuwa, harda karaya biyu tsabar rashin imani da tausayi, tsabar babu tsoran Allah kwata-kwata a zuciyar ku.


Cikin kuka Zainab ta mik'e ta nufi wajen Momy da Dady duk ta rud'e ta fita daga hayyacinta kwata-kwata babu ko d'igon nutsuwa a tattare da ita, gaba d'aya a kid'ime take, ta zube a gaban su Dady tace "Dan girman Allah Momy kusa baki Naseer ya bar min Na'eem, wallahi nayi mugun yin nadama jikina yayi mugun sanyi, wallahi nayi danasanin abubuwan danayi, kuma Allah zan rik'e shi da amana bisa gaskiya da tsoran Allah, duk duniyar nan babu wanda yafi ni cancanta dana rik'e Na'e...........


"Ke awa? cewar Nasir, a zafafe ya yarfa hannayensa da k'arfi zuciyarsa nayi masa suya gami da rad'ad'i mai zafi, ya kalle ta ido cikin ido yana hawaye yace " ko ke a makashiyar mahaifiyar sa, idan har na bawa wacce tayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa ta rik'e shi banyi masa adalci ba, banyi masa gata ba, nasan idan ya girma sai yaji ya tsane ni, ko ma yasani acikin jerin wad'anda zayyi hukunci.


Tana kuka ta mik'e ta nufi inda Naseer yake cikin matsanancin kuka tace " please Naseer ka bar min Na'eem kona ji sassaucin abinda nake ji a zuciyata, walahi ji nake kamar na mutu dan mutuwar zata fiye min sauk'i da salama akan bak'in halin bak'in cikin danake ciki.


" To ki mutu mana, da uban waye ya hana ki mutuwar, in kin mutu waye zayyi bak'in cikin mutuwarki, mun ma rage mugun iri a doron k'asa, banza wofi kawai.


A hankali ta zube a gabansa bisa kan gwiwowinta (ta durk'usa) tana kuka kamar ranta zai fita, zuciyarta nayi mata suya had'i da k'una tana jin k'irjinta kamar zai tsage zuciyarta ta fito saboda tsabar tsananin zafin take ji a k'irjinta, tace " dan girman Allah Naseer ka bani Na'eem bazan tab'a sawa kayi dana sani ko nadamar bani rik'on shi, please ka bani dama ta k'arshe na gyara kurakurai na, in sha Allah zan sa kayi alfahari da hakan, na nuna mashi so da tsantsar soyayyar kamar yadda kowacce uwa take bawa d'anta, please Naseer.


A matuk'ar fusace Naseer yace " soyayarki ta banza da wofi, Allah yayi wadaran soyayya irin taki, soyayyar mara amfani, wacce da zarar mutum yayi kuskure d'aya kuma koda akan rashin sani ne, bakya bashi uzuri, nan take zaki manta da tarin soyayyar kiyi watsi dashi da lamuransa, daga k'arshe ma ki zama sanadiyyar salwantar rayuwarsa, me za'ayi da irin soyayyarki.


K'ara k'arfin kukanta tayi ta zube a gaban shi tana rok'onshi tana yi mishi magiyar ya bar mata Na'eem, " please Naseer kaji tausayi wallahi ina buk'atar a tausaya min.


Murmushin takaici Naseer yayi yace " Allah ko?


"Ashe ke kina buk'atar a tausaya maki?


"Amma ke kwata-kwata baki jin tausayin wasu, baki jin rok'on su ko kukan su, baki da saurin yafiya, baki tab'a manta laifin ke da akayi miki, amma ke kin iya magiya, kin iya rok'on a tausaya miki, bayan ke baki aikata d'aya daga cikin abinda kike rok'on ayi miki, haka Zarah tayi ta kuka tana baki hak'uri tana neman yafiyarki, tana tsananin buk'atar tausayawa daga wajenki amma kika k'i sauraranta balle ki tausaya mata, ga abinda kikayi ya janyo nan, sai kema ki d'and'ani bak'in cikin inda gaske kikeyi.


"Naseer duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e Na'eem sama dan........


Tun kafin ta k'arasa ya katseta da cewa " sai ni, Zainab sai ni ubansa kuma mahaifinsa na fiki cancanta dana rik'e d'ana, ke kin isa ma ki kalli tsabar ido na kice min duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik'e min d'ana sama dake bayan ina nan a raye.


Da sauri ta mik'e ta nufi wajen Abban Zarah dake tsaye tace " dan Allah kasa baki Naseer yabar min Na'eem naga yana matuk'ar jin maganarka, kafin Abban Zarah yayi magana Naseer yayi saurin cewa.


" Banda a wannan b'angaren, Zainab dama kin hak'ura kin dai na wahalar da kanki wajen rok'on na, da bin mutane akan su sani nabar miki Na'eem, dan wallahi tallahi duk duniya babu wani mahaluk'i daya isa yasani nabar miki ruk'on Na'eem, wallahi ko waye shi, idan ma mutum yasan ina ganin girman sa da mutuncinsa karya sake ya soma saka baki a maganar nan, dan zan iya shafawa ido na toka na zage na tsula rashin mutunci, ke dai dayake kwata-kwata baki data ido sai kiyi tayi.


" Wallahi tallahi, wallahil azim, na rantse miki da girman Allah Zainab ko zaki mutu, bazan tab'a baki Na'eem ba koda zakiyi mushe a gaba na, zan sa k'afa na tsallake mushenki nayi gaba da d'ana, ya juya ya d'auki Na'eem daya ajiye akan sofa, ya nufi bedroom d'in sa.


Cikin kuka Zainab tace " ni ban san me nayi maka a rayuwarka ba, na rasa me nayi maka haka, cak ya tsaya had'i da juyowa ya tako har gabanta ya sunkuyo da fuskarsa saitin tata fuskar yana kallanta ido cikin ido yace " Au tambaya ta ma kike yi, kina nufin baki san abinda ki kayi man ba, lalle Zainab kwakwalwar ki bata aiki, ta samu matsala tunda har kike cewa kin rasa abinda kika yi man, Na'eem dake rungume a k'irjin Naseer ganin ya sunkuyo saitin Zainab ya juyar da fuskarsa daga kallan Zainab ya cusa kansa cikin k'irjin Naseer ya k'ara k'ank'ame Naseer had'i da tsandara kuka.


Ganin abinda Na'eem yayi yasa Naseer dakatar da maganarsa batare daya gama fad'ar abinda yake san fad'a ba, ya mik'e tsaye yana kallan Na'eem, duk ya rud'e ya fita hankalinsa, murmushi Naseer yayi yace " Alhamdulillah Masha Allah, nagodewa Allah, ya kalli Zainab yace " kinga tsantsar k'iyayyar da Na'eem yake miki ko, ko k'aunar kallan fuskar ki baya san yi, ji yadda ya fita daga hayyacinsa saboda kawai na sunkuyo dashi sai tin ki, kin dai gani da idanki, bai girma ba balle kice ni na koya mishi yadda zai tsane ki.


Gaba d'aya jama'ar wajen cike da matsanancin mamaki suke kallan Na'eem suna al'ajabin abinda yaro d'an 6 months yayi, hannu Zainab ta d'ora aka had'i da fashewa da matsanancin kukan bak'in ciki.



K'ara rungume Na'eem Naseer yayi tsam a k'irjinsa yana murmushi hawaye na zuba daga idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya, batare dayace komai ba, ya shige bedroom d'in sa ya rufo k'ofa, anan Zainab ta durkushe tana matsanancin kukan bak'in cikin rayuwa, anan kowa ya barta Alhaji Abdullahi, da Abban Zarah sukayi tafiyar su, Dady da Momy suka haye samansu, sai da dakyar Mannir ya lallab'e ta ta yarda suka tafi gidan su suma.


Tun a parlor Zainab ta zube tana ci gaba da kukanta, shiko Mannir dayake yafi Zainab shiga matsanancin halin damuwa da bak'in ciki shiru kawai yayi ya shige bedroom d'in sa ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower had'i da dafa bango yana tunanin mafita dan shi kansa yasan bazai tab'a iya ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da walwala muddin ba Na'eem a kusa dashi ba, zaman lafiyar sa d'aya, da kwanciyar hankalinsa shine yaga Na'eem a tare dashi, dan shi da kansa yasan tunda yake a duniya bai tab'a san wani abu kamar yadda yake mugun san Na'eem ba, dan idan ya ganshi jikinsa har rawa yake, ga yaron kyakykyawan gaske fari fat kub'ul-kub'ul dashi kamar yaron turawa, muddin aka raba shi da Na'eem dai-dai yake da raba shi da duk wani farin ciki, jin dad'i, walwala, nishad'in sa.


Dan duk duniya a halin yanzu babu abinda Mannir yake so yake kuma k'auna kamar Na'eem yafi san shi fiye da kowa da komai, akan yaron babu abinda bazai iya ba, muddin zai dawo masa da yaron kusa dashi ko meye shi zai iya yin abun komai wahalarsa, tsaki yayi had'i da kaiwa bangon bathroom d'in naushi da hannunsa, take yaji ciwo jini ya fara zuba amma shi ko kad'an bai ji zaifin ciwon ba, dan zafin da zuciyarsa take masa yafi ciwon yi mishi rad'ad'in, babu abinda zuciyar sa keyi masa sai rad'ad'in zafi da k'una, ga wani mahaukacin suya da k'irjinsa keyi masa kamar an zazzaga petroleum an kunna ashana.


Duk iya tunaninsa ya rasa wata mafitar kamawa, yayi-yayi amma babu wani kwakkwaran abin kamawa balle ya samu hanyar da zai kasance da Na'eem farin cikin rayuwarsa,, ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi, sannan ya kashe shower ya fita daga bathroom d'in,

Please Login or Register in order to submit comment