Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'akin da aka kwantar da Hamza, ya iske shi yana bacci da alama allurar bacci sukayi masa.


Kiran Fateeha yayi ya shaida mata halin da ciki, muryarta yaji kamar tana kuka, a hankali yace " my heart lafiya? " daurewa tayi ta k'ak'aro murmushin karfin hali kamar yana kallonta tace " lafiya lau my life, d'an hira sukayi tace masa zatayi sallah, bayan ya kashe wayar ne tabi wayar da kallo ta saki sabon kuka.


Bayan kwana biyu
Sosai gidan Alhaji Nasir ya shiga mummunan tashin hankali, dan kwata-kwata Momy ta fita harkarsa bata sakar mishi fuska, haka ma a b'angaren Fateeha kullum tana d'aki bata fitowa kullum tana d'aki tana aikin kuka, tun Alhaji Nasir baya damuwa har abin ya fara damunsa ganin gidan sa na shirin rugujewa, dan haka ya kira Fateeha da Momy yace su sameshi a samansa.


Sa sallama suka shiga, guri d'aya suka zauna, kallon d'aya yayi musu ya gauda kai ganin duk sun fita hayyacin su musamman Fateeha tayi muguwar rama, bayan sun zauna yayi gyaran murya ya kalle ta yace " duk akan Khamal ne wannan abun yake faruwa? shiru sukayi babu wanda ya bashi amsa, ya kalli Fateeha yace " kice masa gobe yazo ina san magana dashi, "to kawai tace, ya kalle ta yace " tashi kije, tare suka mik'e har Momy ita tana shirin fita, da sauri yace " Zainab banda ke, cak ta tsaya, sai da Fateeha ta fita sannan ya taso da kansa ya rungume ta, ta baya ya shiga aikin lallashi.


Khamal kuwa bayan kwana biyun da Dr yace za'a sallame su aka sallame su, Alhamdulillah za'a ce don jiki yayi sauk'i saboda sosai Khamal yake kwantar mishi da hankali, yana k'ara masa k'arfin gwiwa akan in sha Allah zai taimaka masa dan ganin ya sami abin k'aunar sa, bayan sun dawo da Magrib Fateeha ta kira shi take shaida masa kiran da Dady yake masa.


Sosai sukayi waya cike da so da k'aunar junansu yayin da kowannen su yake ji idan duniya zata tashi bazai iya rabuwa da d'ayan ba, duk irin son da sukeyiwa junan su, Hamza ya sani dan duk abinda ya faru a tsakanin su yana sanar dashi, wani lokacin ma a gaban sa suke waya har yasa hand free, dan haka Hamza yasan mugun son da Khamal ke yiwa Fateeha.


Washe gari da misalin k'arfen 8:00pm na dare Khamal ya shirya cikin wani yadi mai bala'in kyau ya nufi gidan su Fateeha, ita ce tayi mishi iso wajen Dady, bayan sun gama gaisawa ne, ya kalli Fateeha yace " bamu waje, ba musu ta mik'e ta fita, kallon sa Dady yace " waye kai? cikin ladabi Khamal yace " sunana Khamal Ahmad, muna zaune ne a unguwar rimi, mu biyu iyayen mu suka haifa, cikin kallon wulak'anci Dady ya kalle shi yace " su waye iyayen na ka? Murmushi Khamal yayi yace " Maraya ne ni tun muna yara iyayen mu suka rasu, a hannun kakar mu muka taso.


"Ok, kana aiki ne, ko kuma karatu kake? " eh to, nagama karatu service ma zan tafi, amma bana wani aiki ko sana'a, a fusace Dady yace " idan na fahimce ka kana nufin kai zauna gari banza, baka da aikin yi ko sana'a amma a haka kake tunnin zan d'auki 'yata in baka, kana zaman banza a gari, kana zauna a matsayin zauna gari banza, kai kan ka har yanzu ba'a yaye ka ba, kakarka ita keyi maka komai ciki kuwa harda acikin ci dazaka ci, da sururar daza ka saka, sai dai kabi wannan kango yau, gobe kabi wannan majalisar, kaima ci da kai ake, cikin sanyin jiki Khamal yace " ba wannan ne abin dafi muhimmanci ba, abinda yafi mahimmanci wanne irin farin farin ciki zan bawa Fateeha a rayuwarta, wacce irin kulawa zan bata, amma in sha Allah zanyi k'orari na neman aiki, tsawa Dady ya daka masa ya balbale shi da bala'i ya zage yayi tayi masa masifa da yana gaya masa bak'ak'en maganganu, masu k'ona zuciya, daga k'arshe yace masa " get out of house nonsense, fuska cike da hawaye Khamal ya fita zuciyarsa kamar zata tsaga k'irjinsa ya fito, idonsa yayi ja, bibbiyu yake gani dakyar yakai kansa gida, don ko takan Fateeha baibi ba..............



MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*


14


A falo yayi zaman dirshan yasa kuka kamar wani k'aramin yaro, sautin kukan sa Hajiya da Hamza suka ji suka fito, " subhanallahi Yaya lafiya meke faruwa? jajayen idonsa ya d'ago ya zubawa Hajiya da Hamza ya kasa koda furta kalma d'aya, sosai hankalin Hamza yayi mugun tashi, Hajiya tayiwa Khamal tambayar duniya amma yak'i magana sai faman aikin kuka yake.



Hakan ne yasa Hamza fashewa da matsanancin kuka, cikin kuka yace " Yaya duk duniya bamu da kowa daya wuce mu ukun nan, mu kad'ai mu kad'ai muka mallaki junan mu, Yaya idan baka fad'a mana damuwarka ba wazaka sanarwa, Yaya please ka sanar damu matsalarka tun kan mu shiga fiye da damuwarka.


Kallon Hamza Khamal yayi, cikin kuka yace " Bro wai yau ni ake kira da cima zaune, k'aton banza, wanda har yanzu ba'a yaye shi ba, ya k'ara fashewa da wani kuka yace " wai bani da aikin yi sai yawon majalisa,.
nine zauna gari banza, yadda yake kukan ne ya bawa Hajiya tausayi itama ta fashe da kuka ta rungume shi tana tambayarsa waya jefe shi da wad'annan bak'ak'en maganganun, cikin kuka ya sanar da Hajiya da Hamza duk abinda ya faru tsakaninsa da Dadyn Fateeha, bai b'oye musu komai ba, cikin kuka Hamza ya rungume Hajiya da Khamal, yace " Yaya kayi hak'uri in sha Allah wata rana sai labari.


" Nasani Bro, Khamal ya fad'a yana gogewa Hamza da Hajiya hawayensu, sosai su Hamza suka lallashi Khamal, sai da suka kwantar mishi da hankali sosai, har suka saka shi dariya, cikin barkwanci Hamza ya mik'e yace " Yaya banci abince ba kai nake jira ka dawo ka bani a baki, nace Hajiya ta bani tace wai nayi girma, shine na bari ka dawo ka bani dan nasan Yaya na bazaice nayi girma ba ko?


Dariya Khamal yace " ah ina ni ina cewa Bro yayi girma ai da kaina ma zan d'anko na baka abakin, ya fad'a yana shirin mik'ewa, da sauri Hmaza ya mik'e yace " a'a Yaya ni zan d'auko kuma na baka a biki, Hajiya na kallonsu tana dariya, a baki Hamza ya rink'a bawa Khamal abincin har ya k'oshi, haka suke tun suna yara, duk wanda yayi fushi to ranar a baki za'a bashi abinci, gidan ya taso cikin farin ciki da walwala.



Fateeha kuwa da taji ne yasata komawa part Dady, bata iske kowa ba a falon, dan haka da sauri ta koma d'akinta dan ta kira Khamal a waya, ta kira shi ya kai sau 30 amma bai d'aga ba, iyakar tashi hankalin Fateeha ta tashiga sosai, don tasan tabbas ba lafiya,ba hankalinta duk yak'i kwanciya, gabanta sai fad'uwa, yake .
Allah .
Allah kawai take gari ya waye, dan ko bacci ta kasa.


Washe gari kowa a falo ya iske Fateeha tana ta faman jiran fitowar Dady, dan ko kayan jikin ta bata canja ba, duk wanda ya ganta yasan bata cikin nutsuwarta, kwana tayi tana kiran Khamal amma yak'i picking, zama ma gagarar ta yayi ta mik'e tana ta kai kawo a falo, tana cikin hakan taji motsin saukkowar Dady, ido ta k'urawa step d'in, Dady yana d'ora idonsa akan Fateeha ya murtuke fuska wai dan kar tayi masa maganar Khamal.


Sosai ya b'ata rai, a dining table ya zauna ko kallon inda take bayyi ba, ga mamakinsa ko zama bai k'ara yi ba, balle akai ga cin abinci, bata ko gaidashi ba cikin murya mai rauni yaji tace " Dady ya kukayi da Khamal ne please?


Face ya k'ara b'atawa yayi kamar baiji abinda tace ba, hankali kwance yake break fast d'insa, duk abinda ke faruwa Momy tana gani kuma tanaji, sai da ya kammala komai ya mik'e zai fita ta kuma cewa " Dady please I need to knew what is going on btwn you an him, kallonta yayi face ba walwala yace " nayi mishi tambayoyi kamar yadda ya kowanne uba yake yi, amma ni ban gamsu dashi ba dan bashi da Qualities d'in da zan iya bashi auren 'yata, dan gaskiya banza iya bawa marar sana'a, zauna gari banza wanda shi kansa har yanzu d'aukar nauyinsa ake a gidan su auren 'ya ta ba, dan bazan sai da akuya ta dawo tana cimin danga ba.


Hannu Fateeha ta d'ora a kai ta kurma uban ihu ta zube a wajen sumammiya, k'afa Dady yasa ya tsallake ta ya fice, a gigice Momy tayo kanta tana kuka, jijjiga ta tashiga yi amma shiru, da gudun maseefa ta nufi fridge ta d'auko ruwan sanyi ta zuba mata, ajiyar zuciya mai k'arfi Fateeha ta sauke, a hankali ta bud'e idonta ta zuba su akan Momy dake faman kuka.


Dady na fita ya kira Abban Ja'afar ya sanar dashi duk abinda ya faru tun daga zuwan Khamal har zuwa yanzu da Fateeha ta suma, dariya Abba yayi yace " kaima kayi wauta, daka sani ka kyale su, da mu kuma sai mu b'ullo masa ta inda bai tab'a tsammani ba, amma duk da haka ka kyale ni dashi zan b'atar dashi b'at, kar ka kuma yi musu maganar, " to kawai Dady yace had'i da kashe wayar.


Tun bayan faruwa al'amarin nan Khamal bai k'ara d'agawa Fateeha waya ba, tayi kiran harta gaji text kuwa a rana sai tayi masa sau 20 a rana amma ba reply babu irin hak'urin da bata bashi ba amma shi,kwata kwata ko ajikinshi dan haka duk ta sukurkurce ta fita daga hayyacinta kwata-kwata ma ta daina fitowa daga bedroom d'inta ta daina shiga harkar kowa, kullum tana d'aki tana ta aikin kuka, ganin haka yasa Momy zuwa d'akin ta same ta, a kwance ta iske ta tana kuka, cikin sanyin jiki ta k'ara kusa da ita ta zauna, " Fateeha Momy ta kira sunanta, "na'am ta amsa amma bata jiyo ba, hannu Momy tasa ta jawo ta jikinta, ta rungume,ta aiko tana jin Momy ta saki wani rin kuka mai sauti da taba zuciya.


A hankali Momy ta shiga shafa bayanta, tace " kiyi hak'uri Fateeha matuk'ar ina raye bazan tab'a bari a aura miki wanda baki so ba , in sha Allah Khamal ne mijinki, shi zaki aura koda kuwa zan rasa raina, rungume Momy Fateeha ta k'arayi cikin kuka tace " please Momy ki taimake ni, wallahi shi kad'ai nake so, idan na rasa shi mutu zanyi Momy, bana san Ja'afar, " karki damu kinji Fateeha.


Da dare Dady da kansa yazo ya sanar da Momy ta kira masa Fateeha ga Ja'afar nan yazo yana san ganinta, ko kallon inda yake batayi ta balle ta bashi amsa, yakai 10mnts a tsaye a kanta yana yi mata magana amma ko ta nuna tasan ma yana wajen batayi ba, d'akin Fateeha ya nufa da kansa, kuka ya iske ta tanayi, bai kalle ta back yace " ki je falon k'asa Ja'afar na jiranki, kuma na baki 5 mnt ki fito, " wallahi babu inda Fateeha zata fita, yaji sautin muryar Momy na magana a bayan sa, a fusace ya juyo, amma yana kallonta yayi shiru dan tunda yake da ita bai tab'a tsananin fushi a tare da ita irin yau ba,
ido cikin ido Momy take kallansa tace " Nasiru tunda mukayi aure ban tab'ayi maka musu kona bijerewa umarninka ba, amma tabbas akan maganar Fateeha ina gaf da rabuwa dakai, dan wallahi matuk'ar kace zaka aura mata wanda bata so zama na dakai yazo k'arshe.


Kallon ta kawai yake da mamaki dan a iya saninsa ko had'a ido dashi Zainab bata iyawa ba, balle harta gaya masa bak'ar magana, taci gaba da cewa " shi akan farin cikin d'ansa da kuma kwanciyar hankalin iyalinsa yake komai, amma kai ka rufe ido, ta wuce ta kama hannun Fateeha suka fita daga d'akin suka barshi.


Da gudu Hamza ya biyo Khamal, sosai Khamal da Hamza ke guje-guje acikin gidan tun daga falo har d'aki da tsakar gida, Hajiya na kallonsu tana dariya, dan ta riga ta saba da halinsu tun suna yara haka suke kuma har yanzu basu daina, Ba wani lokacin sai Khamal yayi nisa da waya da Fateeha Hamza ya zagayo ta bayansa ya warce wayar ya zuba da gudu haka zasuyita zagaye gidan da falon, hannun Hamza Khamal ya kama suka fita waje suna dariya, haka dai suke rayuwar su cikin farin ciki, da kwanciyar hankali.


Babu yadda Fateeha batayi dan su had'o da Khamal ba amma yak'i, ko school d'in ma ya daina shiga tunda dama ya gama dan ita kawai yake shiga, da wuri Fateeha ta shirya tayiwa Momy sallama, ta tafi school, direct department d'insu ta wuce,.
tasha wuya matuk'a kafin ta samu wanda ya san gidan, ta lallab'eshi akan ya raka ta gidan, har k'ofar gidan ya kaita sannan ya juya, da sallama a bakinta ta shiga, gidan babu kowa sai Hajiya, har k'asa ta durk'usa ta gaida Hajiya, da fara'a a fuskar Hajiya ta amsa dukda bata santa ba, Bayan Hajiya ta kaita falo, ta kawo mata ruwa, a hankali Fateeha ta kalli Hajiya tace " Mama kece Maman Khamal dan Fateeha bata tab'a sanin Khamal maraya bane, murmushi Hajiya tayi sannan tace " yarinya ban gane ki ba, sunkuyar da kai Fateeha tayi tace " Fateeha ce, sosai Hajiya tayi mamaki tace " Fateehar Khamal? Murmushi Fateeha tayi ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da 'yan yatsunta, sosai Fateeha taji dad'i a ranta yadda Hajiyar Khamal ta santa, ta k'ara tabbatarwa kanta Khamal yana santa, tunda gashi har a gidan su an santa.


Mamaki ne ya kama Hajiya ganin kyan Fateeha, kyakykyawa ce ajin farko kamar aljana, gata da kunya ga ladabi da hankali, sosai Hajiya taji ta kamu da k'aunar Fateeha, lokaci d'aya taji tana san had'a zuri'a da yarinyar, murmushi Hajiya tayi tace " masha Allah sannunki da zuwa amaryata, amma yasan da zuwanki ne?


A hankali Fateeha ta d'ago idonta tace " a'a, na rasa mai nayi mishi idan na kira shi baya d'agawa, dan Allah Mama idan ya sanar dake wani abu daya faru ki sanar dani please, Hajiya bata b'oye mata komai ba, ta sanar da Fateeha duk abinda Dady yayiwa Khamal, sosai Fateeha ta razana, tace " Dady ne yayiwa Khamal haka? Hajiya ta k'ara da cewa " Khamal maraya ne, bashi da uwa ko uba, su biyu iyayensu suka haifa, ni Kakar su ce ta wajen uba, ni na haifiyar Abban su, daga shi har k'aninsa babu wanda yasan dad'in iyaye, shi Khamal yana da 3yrs iyayen sa suka rasu, shi kuma Hamza yana da 1yrs, basu san kowa nasu ba sani.



Tausayi Khamal da Hamza suka ya kama Fateeha, kuka tasa sosai, kamar ranta zai fita take kuka tace " Hajiya ban tab'a sanin Khamal maraya bane, bai tab'a sanar dani ba,dariya Khamal da Hamza suka jiyo, a tare suka shigo falon sai dariya suke, Hamza na ganin Fateeha yace " Alhamdulillah, ya nufe ta gadan-gadan dan Fateeha ita ce wacce yake haukan so, Fateeha ce wacce Hamza yake so akanta ne ya kamu da ciwon zuciya, yana ganinta yayi tunanin ko Fateeha tazo amsar soyayyarsa ne, ya d'auka ko tazo amincewa dashi ne, dan haka da sauri ya nufe ta yana murmushi, itama Fateeha ta mik'e ta nufe su, shi Hamza a tunaninsa ko wajen sa ta nufo, itako Fateeha bata ma ta lura da wani Hamza ba, hawaye na zuba a idonta tana kuma murmushi ta kalli Khamal tace " why why, mai yasa ka barni wannan hukuncin yayi min tsauri I love you, Hamza na hawayen farin ciki ya bud'i baki yace " I lov....... kafin ya k'arasa yaji Khamal yace " don't ever say u love me Fateeha, I hate you I don't want you in my life, just go, please live from my side, sandarewa Hamza yayi a wajen ya kasa kwakwaran motsi, cikin matsancin kuka tace " wallahi Khamal ina sanka, kai ne rayuwata, bazan iya rayuwa babu kai ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi.



" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai Hamza ke maimaitawa, wani iri juwa yake gani take idonsa suka fara ganin bibbiyu kuma dishi-dishi, numfashinsa ya d'auke,cak k'irjinsa ya fara bugawa da k'arfi, jiri ya fara d'ibansa, a hankali idonsa yake rufewa har ya dai na gani, d'if numfashinsa ya d'auke.............



MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*


15


Da kyar da taimakon Allah Hamza ya samu ya fizgo numfashinsa, a hankali a hankali yake bud'e idonsa harya samu yayi controlling kansa, dan baya son koda wasa Khamal ya fuskanci akwai wani abu tsakanin sa da Fateeha, ya daure ya doje yayi kamar ba wani abu, amma acan k'ark'ashin zuciyar sa ji yake kamar ya mutu da sauri k'irjinsa ke bugawa, mak'ogwaron sa ya bushe bakinsa ya rinka yi masa d'aci.



Itako Fateeha bama tasan Allah yayi ruwansa ba, gaba d'aya hankalinta yana kan Khamal, kwata-kwata bata cikin nutsuwar ta, sosai ta matsa daf dashi ta yadda kowannen su yana iya jiyo numfashin juna cikin sanyin murya tace " please Khamal karka barni, kai kanka kasan ina sanka, karka d'ora min laifin daba nawa ba, ya d'an matsa baya kad'an yana aika mata wani irin kallo, yace " kinga please ki tafi gida, kai ta shiga girgiza masa cikin kuka tace " a'a Khamal please karka barni, bazan iya jure rashin ka ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi, ni kaina bansan ina yi maka wannan mugun son ba sai yanzu, Khamal kaine ruhi ne, idan ka barni tamkar ka tafi da rahi nane kabar gangar jiki na.



" Tunda nake ban tab'a yiwa iyaye na musu ko gardama na sai akanka duk abinda suka umarce bana yi musu gardama hakan ne ma yasa Dady ya yanke ranar aure na ba tare daya shawarce ni ba, cikin muguwar razana Khamal ya d'ago kai ka kalle ta, aiko karaf suka had'a ido, alama tayi masa da idonta na eh, taci gaba da cewa amma a kanka na kunya Dady na tubure nace a'a, akan ka nak'i yi masa biyayya, na bijire masa, yanzu haka Dady ko magana baya man, a kanka farin ciki da kwanciyar hanklin da iyaye na suka gina shekara da shekaru ke neman gujewa dan yanzu haka Momy da Dady neman rabuwa suke.


" Ashe duk tarin maganganun dakake fad'a min ba gaskiya, kasha fad'a min nice rauwarka, nice farin cikin ka, nice duniyarka, kace duk runtsi duk bazaka tab'a rabuwa da ni ba, Idan kasan baka sona mai yasa kace kana so, idan kasan bazaka iya rayuwa dani ba mai yasa ka koyamin yadda bazan iya rayuwa ba kai ba, idan kasan bazaka d'orewa so na ba mai yasa zaka koyar dani yadda zan soka, mai yasa Khamal mai yasa ta durk'usa a k'asa ta fashe da kula mai cin rai.


A matsayi na na mace mai kunya, daraja, k'ima, da Allah yayi min, na yarda jan aji na, na tako har gidan ku, amma duk da haka bazaka hak'ura ba, kai wanne irin mutum ne marar adalci wanda kansa kawai ya sani, baka damu da damuwar wani ba, taka damuwar kawai ka sani, wacce irin zuciya kake da ita mai kafiya marar yafiya.


Jikin Khamal yayi mugun yin sanyi, zuciyar sa ta harba da k'arfi, yayin da yake jin santa na k'ara ratsa ko'ina na jikinsa yana bin kowacce jijiya ta jikinsa yana bin jininsa, ya runtse idanunwa da gam, k'aunarta na fizgarsa zuwa gare ta.


Hamza ko zama yayi kamar ba mutum ya, ya sandare a waje d'aya, babu abinda zuciyar keyi sai bugawa, k'irjinsa nayi masa zafi, ji yake kamar ya mutu, dakyar yake iya controlling kansa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata tsage, a gaban idon sa macen dayafi fiye da kowacce mace a duniya ke kukan son Yayar sa uwa d'aya uba d'aya, wanda duk duniya bashi da kamar sa, a hankali ya share siririn hawayen daya zubo masa.


Hajiya dake tsaye tana kallonsu, tausayin su ya cika mata zuciya, cikin sanyin jiki ta tako har inda Fateeha ke durkushe tana kuka, a hankali ta d'ago ta, takai ta kujera ta zauna ta shiga lallashinta had'i da bata hak'uri, a hankali Khamal ya tako ya durk'usa a gaban kujerar da Fateeha ke zaune, Hajiya ta shiga yi musu fad'a daga k'arshe ta zarce dayi musu nasiha, sosai nasihar Hajiya tayi tasiri a jikinsu, a hankali ya rik'o hannunwanta ya k'ura mata ido ya langwab'ar da kai yace " am sorry my life, murmushi tayi ta kama kumatunsa tace " bakai ne yace zaka iya rabuwa dani ba, " dariya yayi yace " wallahi pretending ne, ba gaskiya bane, dariya Hajiya tayi ta mik'e tace " ja'irai.


Mik'ewa Khamal yayi ya rik'o hannun Hamza ya kawo shi gaban Fateeha yace " my cweet ga brother na, mama da Baban mu d'aya, mu biyu iyayen mu suka haifa, Hajiya kuma grandpa d'inmu ce, ita ta rik'e mu tun bayan rasuwar iyayen mu, bamu san kowa na mu sai ita, ya kalli Hamza yace " Bro ga my heart, sai lokacin Fateeha ta kula da Hamza aiko da k'arfi k'irjinta ya buga, cikin seconds ta shiga tension, da sauri Hamza yayi mata signs ya girgiza mata kai, alamar a'a, da sauri yace " yau dai Allah yayi naga amaryar mu, ya kalli Khamal yace " kai Yaya ka iya zab'e she is very beautiful, murmushi tayi tace " nagode irin wannan kod'awar haka.



A dining Hajiya ta shirya musu abinci, suka ci, cikin raha da wasa da dariya kamar babu abinda ya faru, komai ya wuce an zama normal kamar babu abinda ya faru, da Fateeha zata tafi Hajiya ta had'a mata kayayyaki dakyar ta karb'a had'i dayi mata godiya, Khamal ya raka ta.


Washe gari har gida Hamza yaje wajen Fateeha bayan ta fito sun gaisa yace " please Fateeha ki manta da batun soyayyar danazo miki da ita, a baya, saboda matuk'ar Khamal yasan kece wacce nake so ko sama da k'asa zata had'e Khamal baizai tab'a auren ki ba, nasan kece rayuwar Khamal shine tako rayuwar, shi kad'ai kike so, ke kad'ai yake so, nasan bazaku tab'a kasancewa cikin farin ciki da walwala ba matuk'ar bakwa tare, ina son Yaya na akan shi zan iya komai, murmushi tayi tace " bakomai Hamza, gabansa ne ya fad'i dan yau ne rana ta farko da Fateeha ta fad'i sunansa, ji yayi kamar tafi kowa iya furta sunansa, murmushin yak'e yayi yace " not Hamza bro, ok, murmushi tayi tace " ok.


Kwata-kwata Khamal bashi da kwanciyar hankali burin shi kawai ya samu aiki, kullum acikin neman aiki yake dan ya sawa ranshi bazai tab'a k'ara taka gidan su Fateeha da niyyar neman auren ta ba har sai yana da abinyi, saboda yace koda zasu kai 10yrs a haka shida ita bazai tab'a auren ta sai yana da madagara.


Babu yadda Fateeha tabayi ba dan ganin ta shawo kan Dady amma ina ya riga yayi nisa, abun yaci tura, sakamakon zuga dayake samu daga wajen Abban Ja'afar domin ba k'aramin ingiza shi yake yi ba, kullum

Please Login or Register in order to submit comment