Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ciki, dan haka da hanzarinsa ya gyara mata kwanciya had'i da hawa kan ruwan cikinta, ya danna sandar girmarsa cikin k'asanta sid'if ta shige dan Allah ya yiwa Zarah ruwan ni'ima, jinshi a ciki ya k'ara masa kaimi, ya zage yayi ta kashe arna, yana sama da k'asa akan ruwan cikinta, yama pumping, sai da yayi muguwar dad'ewa akanta sannan yayi releasing.


A kanta yaci gaba da kwanciya yana hutawa, sai da yayi wajen 10 minutes akan ruwan cikinta batare daya d'aga ta ba, suna ta faman mayar da lumfashi had'i da sauke ajiyar zuciya, a hankali Naseer ya mirgina gefen ta ya kwanta, yasa hannu ya jawo ta jikinsa ya matse ta da k'irjinsa yaja musu blanket iya cibiyar su, yana shafa kanta, ajiyar zuciya Zarah ta sauke a hankali cikin sassanyar murya tace " Uncle ina san muyi wata magana dakai please, numfashi ya sauke sannan yace " ok ina jinki, sai da ta d'anyi jummmmm sannan tace " Uncle naji ranar nan kace duk wanda yazo duniya ta wannan hanyar yazo ko? "eh, " to Uncle dole sai ta wannan hanyar kad'ai yake ake samun ciki da Baby, batare da ya kawo komai a ransa ba yace " yes.


Cikin rawar murya tace " kenan kana nufin har Na'eem ma ta wannan hanyar yazo, dole sai da akayi sex sannan aka same shi? gaban sa ne yayi muguwar fad'uwa, dan shi bai tab'a tunanin inda maganar tata ta dosa kenan ba, dan da ya san wannan tambayar zata yi mishi daya ce a'a, kallanta yayi cike da matsanancin mamaki, yaga duk ta koma kalar tausayi, k'ara jeho masa tambayar tayi, da k'arfi Naseer ya lumshe idansa, ya rasa mai zaice mata, ganin yayi shiru, yak'i cewa komai, yasa Zarah fahimtar amsar "eh ne, a hankali Zarah tasa hannu tana shafa kwantaccen gashin k'irjinsa, cikin rawar murya irinta masu kuka tace " Uncle na rasa mai yasa har yau nak'i yarda kai ne mahaifin Na'eem, zuciya ta da ruhi na sunk'i aminta, sunk'i gaskatawa gami yarda cewar kai ne ainahin mahaifinsa.


" na rasa mai yasa har yau nake kokonto akan hakan, kwata-kwata zuciya ta tak'i yarda, nayi-nayi na yarda na amince ko sau d'aya ne na danganta ka dashi amma zuciya ta tak'i yarda na rasa mai yasa, saboda na tabbatar Uncle bazaka tab'a yi min haka ba, bazaka iya cutar da ni ba, bazaka iya wulak'anta min duniya ta ba, bazaka iya gigita rayuwa ta ba, bazata tab'a kawar min da farin ciki na ba, ka sanya ni cikin bak'in ciki da k'unar zuciya ba, Uncle na yarda dakai sosai, na yarda dakai fiye da yadda na yarda na kai, I trust you 100%, ta k'arasa maganar cikin kuka, kanta kawai ya shafa ya kasa cewa komai, cikin kukan ta kuma cewa " please Uncle kayi min magana, ka fahimtar dani GASKIYAR AL'AMARI.


Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya shafa kanta cikin sanyin murya yace " ni kuma na rasa mai yasa tun ranar danaga Na'eem nasan cewa d'ana ne, jini na ne, Zarah k'addara ta riga fata, sai dai kawai muyi addu'a, dan Allah Zarah karki kuma tada maganar nan, dan kwata-kwata bana k'aunar Na'eem ya girma yasa cewa shi shige ne, zata kuma magana yayi saurin had'e bakin su, tun daga wannan ranar Naseer ke satar hanya yazo bedroom d'in Zarah ya kashe arna, wani lokacin ma anan yake kwana sai an kira sallar asuba yake komawa bedroom d'in sa.



BAYAN WATA UKU


Har lokacin Zarah tana cikin matsananciyar damuwa a zuciyarta, gaba d'aya hankalinta yana kan Momynta Zainab, kullum da matsanancin tunaninta da kewarta take a ranta, kusan kullum sai tayi kukan bak'in ciki da takaici, tana dai dannewa ne ta barwa ranta saboda idan Momy da Naseer suka fahimta bazasu tab'a jin dad'i ba dan suna iya ganin duk abinda suke yi, da iya k'ok'arin da suke akanta ta raina, yayinda Na'eem yayi wayo sosai ya girma dan yanzu yana da kusan 6 months har ya fara rarrafe sai shegiyar b'anar tsiya, kwata-kwata baya jin magana, gashi da wayo dan da yaga yayi b'arna a waje zai rarrafa ya gudu wajen Ikram ko Momy, yayinda mugun san Na'eem yake k'ara shiga zuciyar kowa a gidan musamman Abban sa Naseer, yana mugun san Na'eem sosai,haka ma Momy, Dady, Ikram, Zarah ce ma bata wani damu dashi sosai ba, shiyasa shima kwata-kwata baya zuwa wajenta sai dai wajen Momy da Ikram ko Dady, idan ko Naseer yana gida baya tab'a yarda da kowa sai Abbansa, dan agaban uban kowa Naseer zagewa yake yi ya nunawa d'ansa so da kulawa.


A b'angaren su Aunty Zainab kuwa rayuwa suke cikin matsanancin bak'in ciki da damuwa, dan gidan yayi musu shiru, ba motsin kowa sab'anin da dasuke cikin kwaramniyyar Zarah da Ikram, musamman Zainab dan idan Mannir ya tafi aiki sai gidan yayi mata girma, ta rasa inda zata saka kanta da rayuwarta taji kamar tayi hauka, tasha zama tayi kuka kamar ranta zai fita.


Haka ma b'angaren Mannir tun ranar daya d'ora idansa akan d'an Zarah da Naseer Allah ya jarrabe shi da mugun so da matsananciyar k'aunar Na'eem, dan shi yanzu kwata-kwata bashi da wata damuwa ko matsala data wuce ta Na'eem, shi kansa ya rasa wanne irin so yake yiwa yaron, gaba d'aya baya cikin nutsuwa da hankalinsa, duk ya shiga damuwa ya rame, ga shi Dady ya hana shi zuwa gidan, balle ya rink'a ganinsa yana jin dad'i, duk ya lalace, kullum cikin tunanin Na'eem yake, ya d'orawa kansa tension, gaba d'aya san da yakewa Zarah sai ya koma kan Na'eem.



BAK'AR RANA



Ranar alhamis da tsakar daren juma'a da misalin k'arfe 3:20am Zarah ta farka da wani matsanancin ciwon k'irji, ta rink'a ji kamar zata mutu, Allah ya rufa asiri Naseer yau ma ya yiyo satar hanya yazo, dafe k'irjin tayi tana kakari, sai kuma ta fara shek'a aman jini ganin jinin ne yayi bala'in tsora ta, a kid'ime ta fara tashin Naseer, a hankali ya bud'e idansa, ganin halin da Zarah ke ciki ne yayi masifar d'aga masa hankali, cikin tashin hankali ya duro daga kan gadon, lokacin harta galabaita ta fara fita daga hayyacin ta, cikin matsanancin firgici ya d'auke yayi harabar gidan yana kwalawa Ikram kira.


A firgice duk 'yan gidan suka fito Momy, Dady, Ikram, shi Naseer yama manta daga shi sai boxer, a kid'eme suka k'araso wajen ganin Zarah a sume ga jini yana fita ta baki da hancinta yayi masifar firgita su, da sauri suka k'arasa wajen, Dady ya karb'i Zarah yacewa Naseer " maza jeka saka kayan ka, da gudu Naseer yayi d'akin, jallabiya da 3 quarter kawai ya zira ya fito.


Dady ne ke jan motar dan yasan Naseer bazai iya jan Motar ba, Naseer na baya rungume da Zarah, Ikram ma na baya tana ta faman kuka, Momy na gaba, tun kafin Dady ya k'arasa yin parking Naseer ya bud'e k'ofar motar ya fito ya sungumi Zarah yayi cikin asibitin da ita da gudu cikin matsanancin tashin hankali yake kwalawa Doctor kira.


Da hanzari suka nursing suka karb'i Zarah suka d'orata a gadon mara lafiya da sauri Doctor Jennifer (baturiyar nan) ta fito zata shiga emergency da Zarah, caraf Zarah ta rik'o hannun Naseer tana hawaye tace " Uncle jiki na yana bani bazan tashi ba mutuwa zanyi, dan haka zan fad'a maka abinda ban tab'a fad'a maka ba, I LOVE YOU NASEER, I REALLY LOVE YOU SO MUCH, I LOVE YOU MORE MOST, I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, gaba d'aya zuciya ta da ni kai na naka ne Naseer, ina sanka fiye da yadda nake san kai na da rayuwata, ba mutuwar da zanyi shine bak'in ciki na ba, babban bak'in ciki na shine zan tafi na barka kai kad'ai, cikin maraici, please ka kularmin da Momy na, ka yafewa Dady na abinda yayi maka, na baka amanar Ikram da Na'eem, please ku dawo kamar da kai dasu Momy, ka yafe musu, kace ni ma na yafe musu suma su yafe min, kai ma ka ya yafe min, in banda kuka babu abinda Naseer keyi, ya rik'e hannayenta gam cikin nashi, ya kasa koda furta kalma d'aya, kai kawai yake girgiza mata.


" I love you ta kuma fad'a hawaye na zubo mata, ta bud'i baki zata kuma magana jini yayi tsartuwa daga bakinta da hancinta, numfashinta ya d'auke da sauri Jennifer ta saka mata oxygen ta bawa nursing umarnin shiga da ita emergency room.


A nan Naseer ya durk'ushe yana gurza kuka iya k'arfinsa, jikin kowa agun yayi mugun yin sanyi, Ikram ma sai kuka take yi, ba'afi 20 minutes da shiga da Zarah emergency room ba, Jennifer ta fito cikin matsanancin tashin hankali, da sauri Naseer ya mik'e had'i da nufarta, bakinta na rawa tace " she is pregnant for 3 months, cak Naseer ya tsaida kukansa yace " ciki?


"Yes of course, she is pregnant, cikin mamaki Naseer yace " for 3 months? kafin ta bashi amsa wata nurse ta fito a firgice ta kira ta, da sauri tabi bayan ta, wajen 15 minutes ta fito cikin sanyin jiki muryarta na rawa tace " she is dead.


" what? Cewar Ikram, wani Doctor ne ya fito daga emergency room d'in cikin sanyin murya yace " sai dai muyi hak'uri, wanda yafi mu sonta, ya kuma bamu aronta ya kira ta izuwa gare shi, Allah ya karb'i rayuwar kayansa, ALLAH YAYIWA ZARAH MUHAMMAD RASUWA...........




Bana editing novels d'ina so nasan akwai typing errors da yawa




MOMYN ZARAH


Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp





```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





55





A haukace Naseer ya mik'e yace " waye ya mutum? please karku ce min Zarah, dafa shi Doctor d'in yayi had'i da cewa " am sorry, zuciyarta ce ta buga, cikin tashin hankali Momy ta kalli Doctor, batare datace komai ba, tun daga nan Naseer bai kuma cewa komai ba, ya koma ya zauna kamar wani sakarai, ganin an fito da Zarah daga emergency room fuskarta da jikinta rufe da farin k'yalle yasa Ikram d'ora hannu aka had'i da karma uban ihu ta sulale k'asa sumammiya, da sauri nursing sukayi kanta suka shiga bata taimakon gaggawa, Dady na hawaye ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi murya Dady na rawa yace " Assalamu Alaikum, jin yanayin muryarsa yasa Alhaji Abdullahi dake kishingid'e saurin tashi zaune, ba tare daya amsa sallmar ba yace.


" El-Mustapha lafiya kuwa naji ka haka?


Da kyar Dady ya daure yace " Allah ya yiywa Zarah rasuwa, cikin mummunan tashin hankali ya mik'e tsaye yana cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin rawar murya yace " kuna ina yanzu?


" Muna asibiti amma yanzu zamu karb'i gawarta mu koma gida, "ka sanar da iyayen nata?


" No ban sanarwa da kowa illa kai dana sanar yanzu, " to shikenan mu had'u a gidan, a rud'e Alhaji Abdullahi ya mik'e yana sanarwa da Kakar Zarah, tana jin rasuwar Zarah ta fasa kuka, yana fituwa harabar gidan ya fara kwalawa driver kira kamar zai tashi sama, ana tafiya yana yiwa driver magana akan ya k'ara taka motar dan shi gani yake kamar ba tuk'in yake ba, a d'imauce Alhaji Abdullahi ya kira Abban Zarah yace su had'u yanzu a gidan El-Mustapha.


Duk wasu k'adoji da ake bi wajen karb'ar gawa Dady ne yayi aka basu gawar Zarah suka nufi gida da ita, har lokacin Naseer yayi jigum kamar wani tab'ab'b'e koda za'a shiga mota sai Momy ta rik'o hannunsa ta shigar dashi.


Haka kawai Abban Zarah yaci gabansa na muguwar fad'uwa, kwata-kwata hankacinsa yak'i kwanciya, tsoro da fargaba sun dirar masa a cikin k'ank'anin lokaci, dan haka ya kasa tuk'in yasa driver ya tuk'a shi.


A mota Dady ya kira Mannir yace masa duk abinda yake yi ya bashi nan da 10 minutes su had'u a gida dashi da Zainab su zo yanzu, a tare Dady da Alhaji Abdullahi, Abban Zarah suka isa gidan, ana yin parking Naseer ya fito sukuku ya shige bedroom d'insa ya rufe, yayi zaman dirshan a k'asa, ya kasa yin komai dan kwakwalwarsa ta daina aiki, shi bai ma san waye shi ba, da gudu Ikram ta fito ta fad'a jikin Alhaji Abdullahi tana gunjin kuka, fito da gawar Zarah akayi daga cikin mota aka shigar da ita main parlor gidan, shi dai Abban Zarah tsaye yayi cikin mutuwar dan har yanzu bai san takamai-mai abinda ke faruwa ba.


Cike da matsanancin farin ciki Mannir ya shigo gidan yana d'okin ganin Na'eem, Zainab ko sai cika take matsewa, tun daga harabar gidan take jiyo ihuuuu Ikram tana kuka, da sauri Mannir da Zainab suka k'arasa shiga gidan cikin matsanancin firgici, da sauri Ikram ta saki jikin Alhaji Abdullahi tayi wajen Zainab tana kuka tace " shikenan Momy Zarah ta tafi ta barmu, Momy ZARAH TA MUTU!!!.


Wai tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, saboda tsabar rud'ewar da Zainab tayi rufe Ikram tayi da duka hannu bibbiyu kamar zata kashe ta tana cewa" uban ki ne ya kashe ta, dakyar aka kwaci Ikram daga hannun duk ta rud'e ta fita hayyacinta.


Shiko Mannir k'amewa yayi a tsaye ya kasa kwakkwaran motsi, a hankali Alhaji Abdullahi ya kama hannun Zainab ya kai ta har gaban gawar Zarah dake kwance yace " gata nan ki bud'eta ki gani da idonki dan ki tabbatarwa da kanki, hannun Zainab na kerrrrrrma idanta na duk ya firfito waje tasa hannunta dake rawa ta yaye farin k'yallen da aka rufe fuskar Zarah dashi, da sauri ta runtse idanuwanta had'i da had'iyar yawu k'uttttttt.


A hankali ta sauke idanta akan gawar Zarah, a haukace Zainab tayi baya da sauri had'i dayin zaman dab'aro a k'asa ta d'ora hannu aka ta kurrrrrrma uban ihuuu, a d'imauce take girgiza kanta hawaye na zuba tana cewa " wallahi k'arya ne Zarah bata mutu ba, duk wanda yace min Zarah ta ta mutu sai na kashe shi.


A kid'ime ta mik'e ta nufi wajen Dady tace " Dady please ka dawo min Zarah ta, ina tsananin buk'atar ta, idan ta mutu ta barni nima mutuwa zanyi, wallahi ina matuk'ar san Zarah sosai, har cikin rai na da zuciya ta kullum sai nayi kukan bak'in cikinta a kusa dani, dan girman Allah ku tashe ta, ganin Dady bayyi magana bane tasa ta nufar Alhaji Abdullahi tana k'ugin mutuwa tace " please Abba ka taimaki rayuwa ta ka dawomin da Zarah ta da..........


Wani gigitaccen mari Alhaji Abdullahi ya kifawa Zainab, cikin k'onar zuciya yana zubar hawaye ya kalle ta yace ", kina san nata ne kika yi watsi da ita da lamuranta, dan Allah ya d'ura mata k'addara, wacce ke kanki yaki fi k'arfin Allah ya jarrabeki da irinta ba, wanda nasan idan ke Allah ya jarraba da irin k'addarar daya jarrabi Zarah da ita Fatima mahaifiyar Zarah bazata tab'a yin watsi dake da rayuwarki ki ba.


" Wallahi nasan mahaifiyar zata bazata tab'a yi miki abinda kikayiwa tilon 'yarta ba, nasan koda duk duniya zata juya miki baya ta k'i ki Fatima bazata tab'a juya miki baya tak'i ba, koda za'a zare mata rai, zata iya rabuwa da kowa akanki, tasha hawala akanki, tayi wahala dake iya rayuwarta tayi miki duk abinda uwa take yiwa 'yarta, ko sau d'aya bata tab'a kallan ki a matsayi k'anwarta ba, tana d'aukarki ne a matsayin 'yar cikinta, amma ke tilon 'yarta guda d'aya tak data mutu ta bari bari in kasa yi mata irin rik'on data yi miki, kin wulak'antar da ita da rayuwarta, alhalin nasan da Ikram Allah yayiwa wannan jarabawar dabaki mata abinda kikayiwa Zarah ba.


"Mahaifinta cikekken mutum ne wanda ya isa a kira shi d'an halak, kuma asalin bafulatani na kwarai, tun da ake abin nan yayi muku kara ke da mijinki bai tab'a yin ko tari ba, bayan nasan yana jin abin har cikin ransa da k'ok'on zuciyar sa, yana dai d'auke kai ne kawai, har dukan mutuwa kukayiwa 'yarsa , da karaya biyu, amma ko kallan banza bayyi muku ba, bayan kema a matsayin 'ya kike a wajensa, yana da ikon hukunta kamar yadda kuka hukunta Zarah, tak'amarku dai kun rik'e Zarah kuke ganin kuna da k'arfin iko akan ta, to kamar yadda kuka rik'e masa 'yarsa haka shima ya rik'e ki, duk gata da so da kike tak'amar kinyiwa Zarah haka shima yayi miki, kuma bashine ya baki rik'on Zarah da kansa ba, ke da kanki kika nema wanda a lokacin ma kara yayi miki kawai ya baki dan bai so rabuwa da 'yar sa a lokacin ba, amma haka ya daure ya baki ita.


Saboda kara irin ta shi, dan ko a mutanen da ba kowa ne zayyi irin karar da yayi ba, kuma tunda ya baki ita bai tab'a nuna miki komai ko a fuskarsa ba, amma ku kun taru kun azabtar mishi da 'ya, daga k'arshe ma kunyi sanadin barinta duniya, kina tsammanin Fatima zatayi farin ciki da muguwar sakayyar da kika mata ya k'arasa maganar yana hawaye, cikin muryar kuka yace " na zuba muku ido ne dan naga ko zaku gane abinda kukeyi ba dai-dai ne kuskure ne, ku gane kuranku amma ina kun riga da kunyi nisa, ni wallahi kunyar Muhammad nake ji, da sauri Abban dake kuka tun lokacin da Ikram tace Zarah ta mutu, sosai yake kukan bak'in ciki da takaicin karar da yayiwa wad'anda kwata-kwata basu san kara da kawai ba yace.


" A'a Alhaji har abada babu wannan a tsakanin mu, kuskure ne mu duka munyi sai dai a kiyaye gaba, Zainab dake tsaye ta zube akan gawarar Zarah had'i da d'ora hannu aka ta zunduma iban ihuuuu ta na birgima tana cewa " wayyyyyyyo ni Zainab na shiga uku naga ta kaina ina zan sa rai da rayuwata, naga taskon rayuwa gami k'angin duniya, sosai Zainab take bori had'i da zunduma uban ihuuuu.


Cikin rawar murya Dady yace " duk mai faruwa dai ta riga da ta faru aikin gama ya gama, yanzu muyi gaggawa kamar yadda Allah yace mu kaita makwancinta, Alhaji Abdullahi yace " a shirya ta kafin sallar juma'a sai ayi jana'izarta a masallacin juma'a bayan an idar da sallar juma'a, cikin k'anganin lokaci akayi mata wanka aka shirya ta tsaf cikin likkafani a bisa koyarwar sunnah, Alhaji Abdullahi yace " a kira mijinta, d'an jummmm Dady yayi dan yasan akwai tashin a kiran Naseer shi inda san ranshi ne a barshi kawai a yadda yayi hocking d'inan, k'ara maimaita maganar Alhaji Abdullahi yayi a karo na biyu, cikin mutuwar jiki ya nufi bedroom d'in Naseer, acan k'uryar gado ya had'a kai da gwiwa kawai ya rasa meke faruwa.


Hannunsa Dady ya rik'o batare dayace masa komai ba, aiko ba musu Naseer ya biyo Dady kamar sakarai ko dolo, haka suka isa parlor kamar rak'umi da akala, Alhaji Abdullahi ya nuna masa gawar Zarah dake rungume a jikin Zainab yace " kayiwa matarka addu'a.


A hankali Naseer yabi inda Alhaji Abdullahi ya nuna masa da kallo, maganganun da Zainab keyi rungume da Zarah ne suka dawo dashi cikin hayyacinsa, Zainab cikin kuka ke cewa " ina sanki Zarah, dan Allah ki dawo karki tafi ki barmu please, wallahi ina miki mugun so, meye zakiyi nesa damu, meyasa ta har abada ba dawowa Zarah meyasa zaki MUTU!!!.


Sai a lokacin Naseer ya tuna abinda Doctor yace masa " ALLAH YAYIWA ZARAH MUHAMMAD RASUWA, a hankali ya juya inda inda yake jiyo gunjin kuka Ikram ya juya kalli Abban Zarah yaga shima kukun yake, a hankali ya rink'a bin jama'ar wajen yana kallonsu, yaga kowa kuka yake ya juya ya kalli gawar Zarah dake kwance cikin linkafani tab!!!! tashin hankali wanda ba'a sa mara rana, wani irin mahaukacin gigitaccen fitinannan uban ihuuuuu Naseer ya baki iya iya k'arfinsa ya kurma had'i da dafe fuskarsa da tafin hannusa ya durk'ushe wajen yana kurma gigitaccen Ihuuuuuuuuuuuuu kamar ransa zai fita.



Hannu yasa yana cizgar gashin kansa yana yakushin fuskarsa, yana ci gaba da sakin fitinannan ihuuuu, a haukace yaje wajen gawar Zarah ya d'aga ta ya rungume gam a k'irjinsa yana kuka yake cewa " mai yasa zakiyi min mai yasa zaki tafi ki barni, bayan kin yi min alk'awarin kasancewa dani har rai da mutuwa, mun gama tsara rayuwarmu, mun tsara yadda zamu rayu da yaran mu cikin farin ciki, mai yasa Zarah ya k'ara fashewa da mahaukacin kuka, dai-dai lokacin Na'eem ya tashi daga bacci had'i da tsandara k'ara, a kid'eme Naseer ya nufe shi ya d'aushi ya kawo shi kan gawar Zarah yana nuna masa yace " please Na'eem kacewa Momynka ta tashi karta tafi tabar mu cikin maraici da kad'ai, gaba d'aya Naseer ya fita fit daga hayyacinsa ya koma cikekken mahauci, cikin rashin nutsuwa yake yin komai, sai a lokacin hankalin Mannir dake tsaye kamar mutum mutumi dan ya gazayin komai, tsaye kawai yake yana zubar da hawayen bak'in ciki daka kallan shi kasan yana cikin tsantsan nadamar rayuwa, hankalinsa ya kai ga Na'eem dake ta faman rusa kuka yana laluben nonon Zarah.


Cikin tsananin bak'in cikin rayuwa Mannir ya fasa kuka dan ya kasa controlling kansa, gaba d'aya wajen tausayin Naseer da Na'emm ya mamaye musu zuciya da duk ilahirin jikinsu, tuni Zainab ta yada hijab da d'an kwalli babu abinda ya rage a jikinta sai doguwar riga, duk ta zare ta d'imauce ta fita daga hayyacinta, a firgice ta mik'e ta nufi Naseer tasa hannu tana k'ok'arin kwace Na'eem daga gareshi, d'ago jajayen idanuwansa da suka gama rinewa yayi ya kalle ta, ganin Zainab ce tsaye a gabansa tana k'ok'arin kwace Na'eem yasa shi tuna duk abubuwan data yiwa Zarah.


Aiko cikin zafin rai ya mik'e ya kifa mata lafiyayyen marika guda biyu kyawawan masu k'arfin gaske wanda sai da suka sakata bajewa wanwar a k'asa,, ya damk' i wuyanta yace " kinsan me yayi sanadiyyar mutuwar Zarah?



A haukace yace " mata ciwon zuciya, ya nuna saitin zuciyarsa yace mata " zuciyarta ce ta buga, wanda kece sanadiyyar faruwar hakan, Zainab, Zarah bata da wata matsala ko damuwa balle bak'in ciki sai naki, kullum sai tayi kukan rashinki a kusa da ita da kuma kewarki, kallo d'aya zaga yiwa Zarah kasan tana cikin matsananciyar damuwa, duk iya k'ok'arin dake nake naga na sanya ta cikin farin ciki da walwala amma a banza saboda tunaninki, duk iya k'ok'ari na akan naga Zarah ta rayu cikin farin ciki amma sai da kika wargaza min burina KIKA YI AJALIN ZARAH.


A firgice ta kalle shi cikin alamun tambaya amma ta kasa furta koda kalma d'aya, kallanta yake shima yace " yes ZAINAB KECE SANADIYYAR MUTUWAR ZARAH, saboda da bakiyi abinda kika yi ba da bata mutu ba, da kin yarda da k'addara, kin kuma d'auki k'addara kin fauwalawa Allah komai da hakan bata faruwa ba, da kin rungume ta kin saurare ta, kinyi mata gata kin zame mata uwa ta gari da batayi kukan bak'in ciki har ciwon zuciya ya kamata ba, da kin yarda da rantsuwar data miki da Qur'an da kin jata ajikinki kin nuna mata so da kulawa Zainab kin cuce mu.


Wani mahaucin kukan ya kuma saki, cikin rashin nutsuwa Naseer yasa hannu ya damk'i k'afarta ya fara janta a k'asa.............






MOMYN ZARAH


Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/Hauwa-A-Usman-Jiddarh-Novels-310316182944006/?referrer=whatsapp




```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





56





Ya fara janta a k'asa har bedroom d'in Zarah

Please Login or Register in order to submit comment