Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auri d'an fashi, da makami mazinaci, d'an maye ba, saboda komai yana iya faruwa,arayuwa duk ita ma Ramlat bata son auren nasu yanzu kuma bbu komai addini haramun auren d'an giya.


Shiru Mama tayi, Sosai cikin mutuwar jiki tace " Allah ya zab'i abinda yafi alkhairi, " Amin Mama addu'a ya kamata kiyi mana, "addu'a kam kullum akanta ake Abdullahi, murmushi Umar dake labb'e yayi ya girgiza kanshi kawai kwalla takaici na zubo masa a fili yace " na cuci kaina, jin Mama na niyyar fitowa yasa shi saurin barin wajen.


Dayake Abdul Medicine yake karanta, cikin ikon Allah aka tura shi Practical a General hospital din dake Gombe, Allah yasa ya fara practical a sa'a tunda yake aiki bai tab'a samun wata matsala ba, har Allah yasa yayi wata biyu.


ranar wata Monday da wuri Abdul ya tashi ya shirya ya nufi hospital, yana zuwa yaga an kawo wata yarinya a matuk'ar galabaice, za'a shiga da ita Emergency, sai jini ke zuba ta k'asanta,yayinda numfashi ma da kyar take fitarwa tsabar tashin hankali datake ciki bata ko iya magana bata iyawa , da sauri Dr ya kira Abdul akan yazo ya taimaka masa , cikin rawar jini ya shiga,dakin aka kwantar da wannan yarinyar.
Abdul na shiga Dr ya d'age gaban yarinyar, " Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un abinda Abdul ya shiga furtawa kenan yana dauke idanunsa da sauri .


Saboda ganin yadda gaban yarinyar yayi da sauri ya runtse idanushi tare da kansa gefe, sai ji yayi caraf an rik'o masa hannu a d'an tsorace ya bud'e idonsa, yarinyar ya gani rik'e da hannunsa, hawaye na zubo mata,tana dubansa agalabaice bakin da k'asanta jini sai zuba yake, da kyar ta iya bud'e baki tace " sunana Aisha, ina karatu a Government Girls ina SS1, d'an gidan Sanata Sambo ya ganni yace yana sona, nak'i amince masa ballanantana Na kulashi to shine dan nak'i kula shi, suka yi min fyad'e shi da abokan sa, ni 'yar talakawa ce iyaye na basu da wani k'arfi dasu daukar min mataki akan abinda aka min .
dan Allah , ina neman taimako d'aya a wajen ka, ta rik'o hannayan sa duka ta yunk'ura alamun tana son tashi amma ta kasa tashi sai uban jini ne kawai ke fita daga jikinta,.
hannayen damke cikin nasa tace " ka duba School Bag dina nayi video nayi recording komai, dan girman Allah ka yad'a labari nan karka b'oye shi sannan ta fashe da wani irin matsanancin kuka,me ban tausayi da cin rai numfashinta Na sauka ahankali tace " ka d'auke ni tamkar k'anwar pls kayi min alk'awarin zakayi min abinda nasaka tallafa kamin gata , ka tona masa asiri, ta yadda mahaifinsa bazai samu nasarar ci zab'en takarar governor daya tsaya ba, pls kayi min alk'awari tana ta maimaita pls kayi min alk'awari zakayi har numashinta ya tsaya cak alamun mutuwa tayi hannunta still damke cikin nasa.


Mutuwar tsaye Abdul yayi ya kasa koda kwakwkwaran motsi balle yayi magana saboda rik'on datayi masa dakyar likitoci suka kwace hannunta daga 'cikin nasa, shi kansa hawayen tausayin yarinya ke bin kuncinsa yana fitowa daga Emergency yaga iyayenta suna kuka kamar ransu zai fita.


, direct School Bag d'inta ya d'auka ya wuce gida, shi bai ma san me yake yi ba, koda yake tafiya babu abinda yake tunawa sai yarinyar yaddda take kuka
tare da nacewa _ka taimake ni kayi min alk'awari zakayi_.


Yana k'arasawa gida ya zube agaban mahaifiyar sa, sai daya kusan 30 minutes baice mata komai,ba Mama sai tambayarsa take lafiya, Abdul ?

Meyye faru da kai hk ?

amma ina ya kasa magana sai kuka yake yana tuno da yarinyar da irin illar dakayiwa rayuwa hakika maci amana irinsu basu cancin rayuwa a doron kasa ba .kuka yake sosai har shesheka , sai can iya bud'e baki ya fara magana bai b'oyewa Mama komai ba ya kwashe duk abinda ya faru ya zaiyane mata,d dangane da wannan yarinyar .
sosai Mama ta firgita,d a jin lamarin sai da saita kanta sannan tace " kai yanzu meye shawararka? Sannan km meyye abinyi Abdul ?


Kallon Mama yayi sosai kana muryarsa cike da kuka yace " ni bani da wata shawara ko abinyi, Mama ta kalle shi tace " kamar ya?


"Mama nima ban san me zanyi ba, ban san ya'ya zan taimakawa wannan yarinyar da,akazalinta aka yanke mata farinciki rayuwa ta hanyar yi mata fyade murmushi me cin rai da zuciya Mama tayi tare da cewa " karkayi haka Abdul ka tuna hannunta cikin naka ta mutu tana zubd hawayen takaicin abinda akayi mata tana k'ara nanata maka kalmar, bata sanka ba amma tasamu yak'i ni akanka harta yarda dakai ta dank'a maka amana, a hafin hannunka ta mutu tana zubar da hawaye, yanzu idan Ramlat akayiwa haka, kuma fa .
Nasan ita bazakace bakasan abinda zakayi ba nasan kana da hujja yadda zakayi, .....da wani irin mugun sauri Abdul ya d'ago kanshi ya xubawa mama idanunshi yana kallonta cike da jin tsoron kalmar data fito bakinta , .

Ahankali muryarsa Na rawa ya furta sunan Ramlat ....can km yasoma girgiza kanshi yana cigaba da kallon mahaifiyarsa hawaye km Na tsiyaya Daga idanushi murmushi takaici mama ta sake yi tana jin tayi daci da radadin ciwon abinda akayiwa diyar mutane duk da bata ganta ba Amman abun yata ruhinta da gangar jikinta .
Muryarta a sarke tace " ita dayake 'yar uwarka ce ba, shine duk ka frigice kadawo wani mutun abin tausayi , ba lalle sai d'an uwanka na jini kadai zaka iya taimakawa ba arayuwa .
, kamata yayi ka fi taimakon wanda yake da yak'ini akanka fiye da jininka.
, ni dai inda zan baka shawara ka kai gidan jaridu, TV, radio a buga labarin a ko'ina.
Ta yadda za ka samu sauke nauyin da Allah ya d'ora maka. Allah sarki yarinya karama hk abar tausayi ko a wani hali yanzu iyayenta suke ciki ?
Ko yaya zasu ji idan suka samu labarin mutuwarta mama takarasa mgnr zuciyarta cike da alhinin mutuwar yarinyar dabata San kowace ce ba..


Shiru Abdul yayi yana sauraron mahaifiyar tasa, sosai ta k'arayi masa nasiha ta k'ara masa k'arfin gwiwa, a YouTube Abdul ya fara d'ora video daga bisa yakai wa wani abokinsa dake aiki a gidan TV a gaban Abdul aka nuna video had'e dayin bayanin da yarinyar ta sanar dashi, duk da ba Abdul dinne yayi bayanin ba, daga direct gidan jarida ya wuce ya biya aka buga masa labarin.


Bayan kwana biyu labari ya kaiwa sanata Sambo, aiko hnklinsa ba k'aramin tashi yayi,ba.
cikin k'ank'anin lokaci labarin ya yad'a ko'ina duk gidan TV ko radio daka kunna maganar da akeyi kenan, sosai hankalin Sanata ya tashi, saboda hakan yana nufin rugugujewar siyasar shi.


Nan da nan sanata ya kira taron gaggawa, na manyan 'yan siyar sa, ciki kuwa harda Haidar d'an sanata wanda yayiwa Aisha fyad'e bayan kowa ya zauna an natsa Sanata ya kalli Haidar yace " kai ka fad'a min gaskiya kayiwa yarinyar nan fyad'e? kai tsaye Haidar yace " eh Dad, cikin fushi sanata yace " dan ubanka baka da hankali ne bakaga zab'e ya kusa ba, gashi nan sbd da sakarcinka kana neman ka watsar min siyasata danayi shekara da shekaru ina ginawa, ya kai dubansa ga sauran mutane yace " meye shawararku yanzu akai ?


Babban yaronsa yace " gaskiya ranka ya dad'e kar muyi wani motsi yanzu saboda idon jama'a yana kanmu, yaron zamu nemo musa ya k'aryata kansa, yace kud'i aka biyashi dan ya b'ata maka suna kaga daga nan zamu k'ara samun d'aukaka, kowa ya yarda da wannan shawara.


Kasancewar su manya ne a k'asa ba'a wani sha wahala ba, aka samu address d'in, Abdul har gida Sanata Sambo ya aiko aka tafi dashi cikin aminci da kwanciyar hankali, babu wata alama ta wulak'anta duk da dakyar Abdul yaje dan da farko k'in zuwa yayi sai da Mama ta matsa masa, bayan Abdul ya bayyana a gaban Sanata Sambo ne, Sanata ya gabatar masa da buk'atar sa, murmushi Abdul yayi yace " gaskiya bazan iya ba.
Alahakikanin gaskiya acin zarafin yarinyar an cuceta an cuci rayuwarta da iyayenta.
Idan Na amsa bukartaku Na cika muku burinku na rufa muku asiri naje nakaryata abinda yake gsky ne akan siyarsarku ni km meyye hukuncina agurin Allah?
babu yarda Sanata Sambo baiyi da Abdul ba.. amma fir Abdul yak'i amincewa bukartasa sosai Abdul da Sanata Sambo sukayi cacar baki da musayar magana amma ba cikin fad'a, ba Abdul ya zage ba tsoro ballanantana wata fargaba ya dinga gayawa Sanata magana sosai daga k'arshe yace " idan kashe ni zakuyi kuna iyawa amma gaskiya banza iya cin amanar mamaci ba.
, mai yasa d'anka bai yiwa bakin jijiyarsa key ba, ai yasan dakai da km siyarsarku amma yaje ya aikata san ransa.dan kawai yana takamar Ku wasu acikin kasa .
, dan haka wallahi wallahi banza tab'a karya alk'awari dana daukarwa yarinya ba.
Sai naga an durkufar danka gaban koto an yanke masa hukunci daidai da kaifinsa ta yadda ruhin yarinyar nan zai samu salama , yana kaiwa nan ya mik'e tsaye jikinsa a sanyaye yayi waje.yana takaicin masu hali irin Na senata sambo masu fifita harkar siyasarsu akan rayuwarsu wasu ..


Da wani irin kallo Sanata yabi bayan Abdul yana murmushi 'cikin kasan ranshin , yace yaro baisan wuta ba saiya taka,i Dan kasan wata bakasan wata ba zan b'ullo maka ta yadda bazakayi tsammani ba, zan baka mamaki yaro, idan ko har kasa burina .
Na siyatata yak'i cikawa saina saka kuka .idan
har ka tsani kuka, sai na saka yin kukan jini da idanunka Sai Na gigita rayuwarka Na wujijiga duniyarka da farinciknka ta yadda har ka mutu bazaka daina kukan bak'in cikina .....



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



8


Gida Abdul ya wuce Kai tsaye cike da alhinin abinda yashiga tsakanina da senator , yana shiga ya iske Mama a tsakar gida tana shara, tana jin shigowarsa ta mik'e tsaye tana kallonsa tace " yaakayi ?
Ya kukayi da su ne?,tayi masa tmbyr ajere.
Acikin tsanake Abdul ya zayya ne mata komai , shiru Mama tayi na d'an wani lokaci, sannan tace " ni dai Abdul ina jin tsoro kar wani abu ya sameka fa, mutanen nan ba imani gare su ba, akan cikar burinsu babu abinda bazai iya ba.


"Bakomai Mama in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, Allah ya sani dan shi nayi nasan kuma bazai tab'a bari a wulak'anta ba.

Km ma mama kece kika bani kwarin ya km naga duk jikinki Yayi sanyi ?
, jikin Mama a sanyaye tace "to shikennan Allah yabada sa'a Abdullahi, Ubangiji ya tsare min ka, Daga sharrin su Yasa kayi nasara akansu " Amin Ameen Mama,t are da shigewa d'aki.


D'aki ya iske Umar yana sallah, zama yayi yana jiran ya idar, shima ganin Abdul d'in yasa bai ja doguwar sura ba, yana idarwa ya juyo .
Ahankali ya kalli Abdul din yace " bro lafiya dai naganka hk ?


Guntun murmushi Abdul yayi sannan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga kan had'uwar shi da Aisha har zuwa yau din nan da Sanata Sambo ya nemi son ganinsa.
, shiru Umar yayi sosai yana tunani tare da nazarin mgnr , sai kuma yace " gaskiya nima dai ta bakin Mama wallahi tsoro nake ji, bana san su cutar dakai.
, dan idan wani abu ya faru da kai, wallahi bazan tab'a ragawa iri irin su ba, dan sai na fi baya zama terror, sai na addabi ahalinsu gabadaya.


Murmushi sosai Abdul yayi yace " da yardar Allah ma babu abinda zai faru balle na tuna maka jiya, " Allah yasa haka inji cewar Umar.


Tun daga ranar da Sanata Sambo ya had'u da Abdul yaji ya k'ara tsanarsa fiya da koyaushe burinsa kawai yaga ya kawar da Abdul a doron kasa amma ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin saboda kar jama'a su farga.
, saboda ga dukkan alamu Abdul ya tarwatsa masa siyasarsa, shiyasa a yanzu bashi da wani buri daya wuce yaga ya tarwatsa rayuwar Abdul, burinsa kawai yagan shi ya tagayyara, dan haka ya shiga binciken hanyar dazai b'ullowa al'amarin, cikin sa'a kuwa sanata ya samu labarin Umar, yasa akayi masa bincike akan sa sosai, ya samu cikekken bayani akan dangartakar su, da kuma halin Umar na baya, murmushi Sanata Sambo yayi sanda ya samu wannan damar, sannan yace " da d'an gari kan ci gari.


Nan da nan yasa aka nemo masa Umar aka gawo masa shi gabansa, kallansa Sanata Sambo yayi yace " Umar ko? da ido kawai Umar ya bishi baice masa komai ba, Sanata Sambo yaci gaba " d'an fashi, d'an daba, d'an maye, sannan wanda ya makance akan san abun bazai taba samun saba wato Ramlat, d'an niger wanda iyayensa suka mutu, ya taso a hannun mak'otansu.


Tsaki Umar yayi yace " kaga ni ba shirme da b'ata lokaci ne ya kawo ni ba, idan baka da abincewa ni zanyi gaba, dariya Sanata yayi sosai sannan yace " ni ko ke da abincewa, ai abin cewar ne ma yasa ni kiranka, " Ok ina jinka, " nasan halinka, nasan sirrinka, nasan abubuwa da dama akan kawanda kai kanka baka sani ba, nasan baka da wani buri daya wuce na mallakar Ramlat, kuma kasan hakan bazai taba faruwa ba, idan Abdul yana raye, kai Ramlat kake so ni kuma rayuwar Abdul nake so, shiyasa na kiraka dan mu had'a hannu wajen cikar burin mu, saboda idan har Abdul yana raye bazan tab'a samun siyasata ba, haka kai ma bazaka tab'a samun masoyiyarka da Ramlat ba.


Dan hak......... Wata mahaukaciyar tsawa Umar ya dakawa Sanata Sambo wanda yasa shi yin shiru da bakin dole,batare daya dasa aya ba .
Umar ya mik'e tsaye yayiwa Sanata muguwar shak'a yace "wallahi in banda nayiwa Mama da Abdul alk'awarin na daina munayen halayen na da anan take zan murd'e maka wuya na jefar da wulak'antacciyar gawarka.


Saboda nasan ko awajen Allah kai wulak'antacce ne banza kawai wanda bai san darajar amana, halacci da alk'awari ba, iyayen na su mutu tun ina da 6yrs, mutanan nan suka d'auke ni, duk unguwar babu wanda ya kalle ni balle yasan Allah yayi ruwa na, sune ci na, sune sha na, sune sutura ta, sune komai nawa, su sukayi min komai arayuwa babu abinda basuyi min, sun yi min gata, sun rik'e ni kamar d'an cikin su, tunda nake dasu basu tab'a yi min wani abu na b'atanci ba, sannan dan kai jaki ne, jahili, wanda bai san me yake ba kace naci amanar wad'annan mutanan, wallahi Allah ya rufa maka asiri baka same ni sanda nake HORROR ba, da tuni ka tsufa a lahira, yayi jifa da Sanata yayi tafiyar sa, sosai Sanata ya bugu sakamakon jifan da Umar yayi dashi, bayan Umar Sanata Sambo yabi da kallo, yana murmushi bak'in ciki.


Bayan Umar ya koma gida ya samu Mama da Abdul yake sanar dasu yadda sukayi da Sanata Sambo, aiko sosai hankalin Mama yayi masifar tashi, ta kalli Abdul tace " Abdullahi yanzu meye mafita? "addu'a mana Mama, addu'a itace babar mafita, bamu da wani abinyi sai ita, Umar ko sai huci yake yana sauke ajiyar zuciya da k'arfi, an tab'a masa ahalinsa, Mama ta kalle shi tace " lafiya dai Faruk'u, naga kana ta faman huci? shiru yayi bai bata amsa ba, saboda ranshi ya b'aci yake sosai, murmushi tayi ta shafa kansa tace " a dai dinga samawa zuciya salama, ana kwantar da hankali, tashi ka shiga d'aki ka kwanta, baiyi magana ba ya tashi yayi shigewar sa d'aki, Mama tace "Allah ya shige mana gaba, "Amin ya Allah, cewar Abdul.


Ganin irin wulak'anci da Umar yayi masa ga kuma wanda Abdul yayi masa yasa Sanata, k'ara hura wutar fansa a zuciyar sa, gashi yana ji yana gani al'umma tayi masa buye had'e dayi masa zanga-zanga akan dole sai an gurfanar da d'ansa a gaban kotu, haka yanaji yana gani aka kai d'an shi gidan yari, tun daga ranar ya k'uduri niyyar d'aukar fansa fiye da abinda Abdul yayi masa, ya shiga bin duk wata hanya dayasan zata fisheshi.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, ga shi har Ramlat da Yasmeen sunyi candy, kuma cikin nufin Ubangiji ya sake fitowa da Ramlat miji na gani na fad'a, dama hausawa sunce wani hanin ga Allah baiwa ne, kasancewar sunyi candy yasa aka saka bikin babi dad'ewa, sosai aka shiga shirye-shiryen bikin Yasmeen & Abdul, Ramlat & Jamil, sosai Mama da Umar ke farin ciki, Umar ya shige gaba akan komai, duk wata hidama ta bikin shi yake yinta.


Ana gobe d'aurin aure da misalin k'arfe 5:00pm Abdul na zaune abakin masallaci wani yaro da gudu har tuntub'e yake k'afarsa babu takalmi, ya zo gaban Abdul ya tsaya yana ta haki, Abdul na ganin yaron gabansa yayi muguwar fad'uwa ya k'urawa yaron ido ya kasa magana, shima yaron ya kasa cewa Abdul komai, cikin rawar baki Abdul ya kalli yaron yace " lafiya? Shima yaron a tsorace yace " gidan ku ne ke ci da wut...... ai kafin yaron ya k'arasa Abdul ya zunduma a guje koda yaje gaba d'aya gidan ya kama da mahaukaciyar wuta yana ci tako'ina mutane ma sun kasa dusar koda jikin gidan domin taimako duk wanda ya nufi gidan sai kaga ya dawo da gudu yana haki da zarar hucin wuta ya buge shi,mutane jungum acan nesa da gida kowa ya na san ya taimaka amma ba damar yin haka saboda tsoran wuta, saboda yadda take ci ya wuce tunanin mai karatu.



Abdul na zuwa ya fara tambayar ina " Mama ina Ramlat, ina Ja'afar, ina Umar, maganar yake amma kaida ganinsa kasan baya cikin hankalinsa, gaba d'aya Abdul ya gama fita daga hankali sa, kowa ya kasa cewa komai aiko gadan gadan Abdul ya nufi gida, jama'a suka yo ca suka rik'e shi,Abdul yana jiyo Ramlat tana kwala mai kira, haka yana yiyo salatin Mama, da kukan Ja'afar, sosai Ramlat ke kwala mai kira, ihu Abdul yake yi sosai yahau dukun mutane had'e da kiciniyar kwace kansa Daga garesu amma ina sarkin k'arki yafi sarkin yawa Muryar Mama ya jiyo tana cewa " Abdullahi karka zo, kar kazo, ko kai kad'ai ne ka rayu dan ka d'aukar mana fansa.


"Kar kazo Abdullahi, sai yaji Mama ta kwala kiran U.....MAR...................
, sai kuma yaji salatinta daga nan bai kuma jiyo sautin muryar Mama ba sai kukan Ramlat dana ja'afar, dake ta faman ihu da kururuwa , itama har ya daina jiyo ta, sosai Abdul yake hauka a wajen ya haukacewa jama'a, yana ihu yana d'ibar k'asa yana zubawa jikinsa yana wanka da ita, sosai yake ihu yana birgima cikin k'asa, jama'a sai rik'e shi suke.


A firgice Abdul ya mik'e daga kan kujerar dayake zaune yana bada labarinsa, yana kallon sauran abokansa da 'yan jaridan dake d'aukar labarin, fuska cike da hawaye idonsa sosai yayi jawur tamkar an xuba masa garwashi wuta yana kuka kamar ransa zai fita, ya hau buga kansa da bango yana ihu yake cewa " sun kashe min kowa nawa, bani da kowa yanzu bani da wanda zan kira d'an uwana, ko dangi na, zaman dirshan yayi a k'asa yana kukan tuno mutuwa had'i da ihu, yana yarfa hannunsa zambur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko ruwa mai mugun sanyi ya b'alle murfin ya shiga bulbulawa kansa ruwan.


Cikin kuka yake cewa " akan idona gidanmu ya k'on e da mahaifiyata, k'anwata, k'anina duk suka mutu akan ido na ina jiyo ihun su, gaba d'aya hankali 6's STARS ya tashi dukkan su kukan suke babu mai lallashin wani, haka ma 'yan jaridan, da dumbun jama'an dake sauraron labarin kuka suke, suna masu tausayawa Abdul, dukkan su suka mik'e suka nufi Abdul suka rungume shi ajikinsu suna matsanancin kuka, cikin karfin hali Abdul ya goge hawayen sa ya shiga lallashin sauran abokan nasa, sai da komai ya lafa sannan Abdul yaci gaba.


Bayan mutuwar 'yan gidan mu ne na samu tab'in hankali amma ba sosai ba, kwakwalwa ta, ta d'an tab'u, bayan sadakar bakwai aka zo da gungun 'yan sanda aka kama ni akan ana zargi na da kashe 'yan gidan mu, duk da bani da cikekken hankali a lokacin amma nayi mugun mamaki, sosai naci mugun duka wajen 'yan sanda kafin aka gurfanar dani gaban kotu, tambayar duniya alk'ali yayi min amma nak'i magana, kwata-kwata a lokacin bana k'aunar zaman duniya na tsani komai da kowa, nima babban buri na shine na mutu, ganin nak'i magana ne, alk'ali ya fusata har yake neman yanke min hukunci mai tsanani, ganin haka yasa Yasmeen bada shaidar bani da hankali, munafukan da suka k'unlla komai suka k'aryata ta, nan alk'ali ya bada damar aje amin test, sannan a dawo dani..........



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*


9


"Bayan anyi min test aka dawo dani, Doctor ya tabbatarwa da alk'ali ina da tab'in hankali, kwakwalwata ta tab'u wanda hakan ya haifar min da ciwon kai me tsanani ,bayan Dr ya gama yiwa alk'ali bayani sannan ya mik'awa alk'ali takardun .
, alk'ali ya duba sosai kuma ya gamsu, bayanin alk'ali ya gama yan duba dubensa da zaiyi ya yanke min hukunci zama a sabitin mahaukata dake kurkuku (prison) na tsawon shekara biyu, tare da shaidawa jama'ar dake kotun cewa idan na gama shekara biyun babu wani sauran hukunci a kaina kotu ta sake ni.


Daga kotu kai tsaye (Prison) aka wuce dani, Yasmeen nata kuka, nazo na wuce ta gabanta ko kallan inda take banyi ba sbd bana 'cikin natsuwata da haiyacina , bayan an kaini prison, na samu kulawa sosai ban sha wata muguwar wahala ba can , kasancewar ni a hospital din nake.


Ko a gidan yari banida da wani aiki sai kuka, da tunani ahlina dana rasa kona nay ta ihu ina kiran sunan Mama da Ramlat ko Ja'afar da Umar, sosai wani lokacin idan abin ya fad'o masa ko ya tuna yake hauka tuburan, na rame na koje, tsabar tunani da tashin hankali.
gaba d'aya na fita daga hayyacina Sai sambatu iri iri nake a game taskon rayuwa r dana tsinci kaina ciki .
, Na tara k'asumba da gemo, kwata-kwata bana magana idan zaka shekara akaina aka na yi min magana bazai kalle ka bama balle na tanka maka, haka wani lokaci zakajini cikin dare ina ihun Ina buge buge da kira sunan Sanata Sambo ....ka cuceni ka zalinceni karabani da ahlina danafi kauna fiyye da komai ka maidani maraya karfi da yaji mara galihu adoron kasa .

daman Haka fadar gsky zatayi da rayuwata?
Hk son kwatar yanci zatayi sanadin tabarbarwa duniyata da tarwatsa rayuwata ?

Meyasa...?

meyasa zaka min hk ?
Sai km ya fashe da wani matsanancin kuka me tsanani da cin rai tare da taba zuci



BAYAN SHEKARA 2


Cikin ikon Allah Abdul ya fito lafiya lau, ya warke sumul babu abinda ke damunsa, sai matsanancin bak'in ciki da damuwa, da kuma wutar d'aukar fansa dake k'ara ruruwa a

Please Login or Register in order to submit comment