Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Zaid abu d'aya ne shiyasa Zaid kawai ya shiga amma dukda haka muna tare.

Al'amin yace " ina Ammi da Abba suke?


"Duk suna nan a raye dan sune iyayen SIX'S STARS


Sosai jama'a suka jinjina musu akan cin amanar da makusantansu sukayi musu, wasu sai kuka suke, haka dai taro ya watse jama'a nata alhinin duniya da mutanen cikinta, wasu suka ce sun d'auki darasi gami da izzina daga rayuwarsu.


Lokaci d'aya duniya ta d'auka akan LABARIN SIX STARS duk wata tasha dazaka kunna a TV ko radio labarin sukeyi, jama'a sai kuka suke yi suna tausaya musu, nan da nan sunan su ya k'ara shahara a duniya suka k'ara samun d'auka, duk inda kayi sai kaji ana ambatar sunansu.


Yauma kamar kullum SIX STARS ne zaune a parlor wanda ke gidan Abraham suna meeting akan wani business , matan su da yaran su na zagaye da su hankalin kowa nakan abinda akeyi amma banda hankalin Zarah dake kan plasma tana kallon wani film take idanta suka fara zubar da hawaye ba tare data sani ba a hankali kukan nata ya rink'a tsananta harta fashe da kuka ba tare data sani ba, sautin kukan da suka ji ne yasa su daina abinda suke yi suka fuskance ta a hankali BASMA, YASMEEN, FATEEHA, KAUSAR, LUBNA, LINA suka mik'e suka nufe ta zama sukayi gaba d'ayan su a kusa da ita, a hankali Lina ta rungumo ta jikinta suka shiga lallashinta, sai da tayi kukan mai isarta sannan ta hak'ura, cikin badara Kausar ta shiga tambayarta abinda ke damunta cikin muryar kuka tace" film d'in can ne yayi min kama da labarin rayuwa ta hakan ne ya tuna min komai, kuma komai ya dawo min sabo take KAUSAR, BASMA ma suka fashe da kuka domin suma sun tuna da tasu rayuwar.


A hankali su Yasmeen suka shiga lallashin su itako Zarah baki ta bud'e tana kallan su, sai kuma tayi murmushi tace " meya saku kuka kodai kuka nane ya saku kuka?


Cikin kuka Basma da Kausar suka ce "muma mun tuna da tamu rayuwar ne, a hankali kowa ya fara kallan juna Zarah tace " gaskiya ya kamata muma mu bawa juna labarin mu, "gaskiya kam cewar kausar cikin kuka, a hankali mazajen su suka mik'e suka nufi inda suke, Zarah ta kalli Naseer tace " dan Allah ina nemar alfarmar a karo na farko a wajenka akan ka bari na fad'awa 'yan uwna labari na, shiru yayi ya kasa cewa komai, haka ma Kausar da Basma kowacce ta shiga neman izini a wajen mijinta akan bada labarin rayuwarta duk sukayi shiru sai can Naseer ya sauke ajiyar zuciya yace " Bawai na hanaki ki sanarwa da su Lubnah labarinki bane haka kawai sai dan saboda sirrin mu ne, a hankali Khamal yace " what sirri? Au dama akwai wani sauran sirrin da muke b'oyewa juna mufa duniya muka sanarwa da namu sirrin akan abinda ya shafi personal life d'in mu, ashe a junan mu akwai sauran abinda muke b'oyewa juna?


"Cool down Khamal ba haka nake nufi ba ka fahimce ni ma, baka bari na k'arasa fad'ar abinda zan fad'a ba ka katse ni so nake nace amma tunda yanzu mun gama zama d'aya nayi mata izini, cikin zumud'i Zarah ta rungume Naseer tace "thank you so much dear, Basma ma ta kalli Ammar tace " please mana murmushi yace " duk mun baku dama, cikin zumud'i suka rungume junansu suna matsananciyar murna, bayan kowa ya nutsu ya zauna kowa ya bada hankalinsa ga sauraren labarin, cikin farin ciki Zarah tace wazai fara? da sauri Kausar tace "ni, "ok to fara muna jinki


LABARIN KAUSAR



Ban muku Alk'awarin samun labarin su ZARAH, KAUSAR, BASMA ba, dan ban gama yanke hukunci ba, zaku iya ganin ci gaba koyaushe ko kuma bazaku iya gani ba ina nan dai ina shawara, dan ba tabbacin zan ci gaba



MOMYN ZARAH


[22/01, 16:44] ‪+234 803 948 8935‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




34



LABARIN KAUSAR




A salin sunana Kausar Muhmud ni haifaffiyar garin Katsina ce, mumu uku ne a wajen iyayen mu, ni ce babba sai k'anwa ta Meenal da d'an autan mu Zita'ulhaq, wanda tun daga kansa mahaifiyar mu bata kuma samun haihuwa ba, mahaifiya wacce muke kira da Umma ita kad'ai ce a wajen mahaifin mu da muke da Malam, abinda yasa muke kiransa da Malam sai dan kasancewar sa Malami tun tasowarsa kuma haka muka ji kowa na kiransa, Umma da Malam suna zaune lafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali tunda muka taso bamu tab'a ganin ko musu ya shiga tsakanin su ba,daga Umma har Malam mutane ne masu matsanancin hak'uri da kawaici had'i da kara shiyasa suka zaune da kowa lafiya, haka yasa muma yaransa muka taso da hak'uri dan duk cikin mu babu mai kwaramniya balle fad'a ko yawan magana, haka muka taso cike da so da k'aunar junan mu.


Muna zaune ne a unguwar k'ofar k'aura dake cikin garin katsina, k'ofar k'aura tana d'aya daga cikin k'ofofi masu d'unbun tahiri, Malam mahaifin mu ba wani mai arziki bane haka kuma ba talaka bane dan munfi k'arfin duk wasu buk'atun mu tunda muke bamu tab'a neman wani abu mun rasa ba, bamu tab'a rasa ci ko sha ba haka kuma bamu rasa sutura ba, dan Malam yana iyakar k'ok'arinsa wajen magancewa iyalansa buk'atun su ,dan haka muka taso acikin rufin asirin Allah.



Haka ma a b'angaren karatu Malam ya tsaya mana dan kamaranta mai kyau ta 'ya'yan gata yaran manyan masu kud'i mukayi anan garin katsina ALHUDA tun daga primary har secondary school anan mukayi, makaranta ce babba sosai wacce ake koyar karatun boko da Islamic duk d'aliban dazasuyi Candy tare suke yi da saukar Qur'an, lokacin ina SS3 dan har mun fara zana waec examination yayinda Meenal ke SS1 Zita'ulhaq ke JSS 2, ni da Meenal tun tuni mukayi saukar Al'kur'an a islamiyyar mu.


Duk wanda yasan Kausar yasan Ni'ima haka zalika duk wanda yasan Ni'ima yasan Kausar, Ni'ima k'awata tace ta rai da rai mak'otan mu ne su daga gidan su sai gidan su, mun shak'u sosai da Ni'ima tun muna yara tare mukayi primary and secondary school site d'in mu d'aya haka ma islamiyya a tare muke , koyaushe muna tare ko kayan sawa ma irin d'aya muke yi, k'awance mu ne yayi sanadiyyar had'a iyayen mu k'awance.


KAUSAR


Mace ce san kowa k'in wanda ya rasa duk da ba fara bace dan kausar b'ace sosai irin bak'ak'en nan da ake black beauty irin wad'anda sukafi farare da yawa kyau, bata da tsayin gashi sosai dan gashinta iyakacinsa kafad'a amma yana da masifar cika (yawa) gata da d'an k'aramin tsukakken baki mai d'auke da fararen hak'ura sol a jere, Allah ya wadata ta da dadaran idanu farare sol manya dasu masu kamar tana jin bacci sai dogon hancinta siriri, a b'angaren diri kowa ba'a magana dan tana cikar k'irji nonuwanta manya madaidaita d'as dasu, k'ugunta mai fad'i , sai uban hips da tudun d'uwawo irin su ne ake kira da coca cola sharp,kai ko macece tayi arba da k'irar Kausar sai taji wani abu balle kuma d'a Namiji mai GANDA.


Muna da 17yrs muka kammala karatun mu na secondary ni da Ni'ima, dai-dai lokacin ne Allah ya had'a ta da saurayinta Bashir wanda take masifar so da k'aunarsa kamar ranta, Bashir d'an wani hamshak'in mai kud'i ne wanda duniya take damawa dashi, tuni duniya ta dad'e da sanin mahaifin Bashir Alhaji Musa Canji, ganin mugun son da Ni'ima keyiwa Bashir yasa iyayen ta suka nemi daya fito (ya turo iyayen sa) ba'a wani b'ata lokaci ba ya turo iyayensa, kasancewar iyayen Bashir ne yasa ba'a wani tsaya b'ata lokaci ba aka saka ranar biki wata d'aya.


Aiko take muka shiga hidimar biki baji ba gani, kasancewar nice babbar k'awar amarya kuma Aniyarta yasa hidima tayi min yawa bana nan bana can, hmmmmmm rashin sani yafi dare duhu da nasan K'ADDARA TAH tana tattare da bikin aminiyata Ni'ima dabanje ba, dan rana bikin Ni'ima ne silar faruwar komai, silar rugujewar komai gare ni, silar shigata cikin k'unci da taskon ratuwa had'i da matsanancin tashin hankali.



HAJIYA LAILAH


Hajiya Lailah mace ce hamshak'iya kyakykyawar gaske ajin farko, mata d'aya jal a gidan Sanata Sambo, ta kasance tana da yara uku biyu maza d'aya mace, Fahad ne babba sai Haidar sai kuma autar su Shema'u wacce suke kira da Shema, Hajiya Laila macece mai aji ga kud'i da hutu sun ratsata ta had'u iya had'uwa dan ta kowanne fanni kake neman had'ad'd'iyar mace takai harta wuce, gaba d'aya gidan Hajiya Lailah a birkice yake dan kwata-kwata gidan baida tsari bare tarbiyya, kowa harkar gabansa yake babu wanda yasan da zaman wani, kasancewar Alhaji Sambo d'an siyasa mai mak'iya da dama yasa shi b'oyewa duniya iyalinsa ya sanarwa duniya yaransa d'aya shine Fahad sai bayan faruwar labarin Abdul sannan duniya ta san sauran yaransa.


Hajiya Lailah bata nemi komai najin dad'in duniya ta rasa ba sai abu d'aya shine mijinta dan kwata-kwata Sanata Sambo bashi da lokacin ta, harkar siyasar sa kad'ai yasa a gabansa, kullum baya gida wani lokacin ma sai yayi wata d'aya cur baya nan, koda ma yana gari sai ya dama yake biya mata buk'atarta idan tayi masa magana ya rufe ta da fad'a yace ta fiye jaraba,
mijinta Alhaji Sambo ya kasance gagarumin manemin mata ne kamar d'an bunsuru duk inda mata suke idonunshi yana wajen su idan ko kyallara ido yaga mace fa shikenan ba zaman lafiya ya rink'a b'arin kud'in kenan har sai ya cimma burinsa, yayinda matarsa ta gida bata da wani mahimmanci da ita da babu duk d'aya ne a wajensa dan yana samun biyan buk'atarsa a wajen matan banza.


To nasan dai kun riga kun san halin Sanata Sambo tun baya a labarin Abdul ba saina dawo baya ba.


Wannan abu ne kad'ai yake masifar damun Hajiyar Lailah dama gata mace ce ita mai matsananciyar sha'awa, Hajiya Lailah duk ta damu kanta ta rasa nutsuwarta ta shiga tunanin nemarwa kanta mafita, lokaci d'aya ta rame ta fige kallo d'aya zakayi mata kasancewar tana cikin damuwa, ganin ta kasa nemarwa kanta mafita ne yasa ta ta shirya nufi gidan aminiyar Hajiya Rabi, Hajiya ta kasance mace ce 'yar bariki cikekkiya ta bugawa a jarida, ita mijinta wani hamshak'in d'an kasuwa ne , itama haka taita fama da irin matsalar Hajiya Lailah saboda mijinta baya zama kullum yana k'asashen duniya, wannan dalilin ne yasata tsundumawa bariki ta zama cikekkiyar 'yar duniya, ta fara neman yara k'anana maza da mata samari da 'yan mata (Under ages).


Aiko nan da nan Hajiya Rabi tayi k'aurin suna a wajen neman mata da maza matasa, ta daina damuwa da lamuran mijinta ta fita harkarsa ko yana gari ba ruwanta dashi burinta kawai ya sakar mata kud'i ita kuma ta nemi yara k'anana dasu, tana isa gidan Hajiya ta shiga falon da sallamarta da gudu Hajiya Rabi ta taso rungume ta tace " wooo aminiya ta rai da rai kwana biyu shiru, "hmmm Hajiya Lailah tace tana zama akan d'aya daga cikin kujerun a gefenta Hajiya Rabi ta zauna jiki ba kwari dan daga ganin yanayin k'awarta ta tasan da matsala dukda tasan matsalarta bata ce ta Sanata Sambo amma yau in sha Allah ta k'uduri niyyar fad'a mata halin da take ciki da kuma ainahin wacece ita.


Cikin mutuwar jiki Hajiya Rabi tace lafiya k'awata?

"Hmmmm ta kuma cewa had'i da sauke ajiyar zuciya, a hankali Hajiya Lailah ta shiga kwararowa Hajiya Rabi matsalarta ba tare data b'oye mata komai ba, murmushi Hajiya Rabi tayi ta talle ta sannan tace " kin fad'a min wannan matsalar taki ta a irga wacce kema kanki shaida ce duk irin matsalarmu d'aya to ni dai gaskiya na nemarwa kai na mafita, da sauri Hajiya Lailah tace " kai K'awata amma shine koki fad'a min a gudu tare a tsira tare, dan Allah sanar da ni mafitar da kika samu, ba tare da tsoro ko fargabar komai Hajiya ta kalli Hajiya Lailah ido cikin tace " LEZ nake kuma ina neman matasan samari irin wad'anda bazasu wuce 25yrs ba a firgice Hajiya Lailah ta mik'e tsaye had'i da cewa "what?


Mik'ewa Hajiya Rabi tayi tana murmushi tace " yes of course, kunnan ki baijiye miki k'arya ba da gaske nake miki, ni yanzu cikekkiyar 'yar lesbian ce ta bugawa a jarida nan da Hajiya Rabi ta shiga sanar da Hajiya Lailah komai bata b'oye mata komai ba, ta kuma shiga kwad'aita mata abu da dad'insa, ta k'ara da cewa ke a tunaninki su mazajen namu hak'uri suke? to idan ma kina tunanin haka gwara ma ki daina tunda su ba waliyai bane, ke kin san irin buk'atar mijinki, kin fi kowa sani idan ma zai iya jure rashin mace na tsawon wata da watanni, take kwakwalwar Hajiya Lailah ta shiga juyawa tsayawa cak kawai tayi ta k'urawa Hajiya Rabi ido harta dasa aya, batare data ce mata komai ta sab'i jakarta ta fice, bayan ta Hajiya Rabi ta biyo tana kwala mata kira amma tayi mata banza, bata ko juyo ba balle ta amsa mata.


Tsaki Hajiya Rabi tayi ta koma cikin gidan ta zauna had'i da cewa "banza wahalalliya a haka zaki k'are inbaki bawasa bak'in cikin d'a namiji ne zaiyi ajalinki sakaryar wofi, haka dai tai fad'a ita kad'ai tana bambami, can kuma tunanin kar Hajiya Lailah ta tuna mata asiri ya zo ta, wani d'an guntun murmushi tayi had'i cewa " yo tama fad'a mana idan ta tuna min asiri kanta ta tunawa dan duniya ta riga ta sammu tare iyakaci na fututtuke na rufe ido nace tare mukayi, kuma nasan duniya yarda zatayi saboda yadda muke da ita.


To k'alubale anan shine karka yadda kayi abota da mutumin banza, karka sake duniya ta sanka da banzan mutum dan duk abinda yake yi tunani za'ayi kai ma hakan kake koda kuwa ba hakan kake ba, domin Hausawa sunce abokin b'arawo, b'arawo ne, Allah yasa mu dace duniya da lahira.


Bayan Hajiya Lailah ta koma gida ta kasa zaune ta kasa tsaye ta rasa gaba d'aya sukuninta duk inda tayi tunanin maganganun Hajiya Rabi na ranta, tabbas tasan Alhaji Sambo bazai tab'a iyayin hak'urin rashin sex ba harna tsawan wata da watanni, saboda ta riga tasan shi mabuk'aci kenan hakan na nufin manemin mata ne? tayiwa kanta tambayar take wasu abubuwa suka shiga dawo mata, dan a lokutan baya tasha kama shi ire-iren wad'annan laifuka kuma mutane sunsha kawo mata tsegumin irin wannan maganar, tabbas maganar Hajiya Rabi gaskiya ce, dan idan ba gaskiya bace mai yasa Alhaji Sambo ya b'oyewa duniya su?


Haka Hajiya Lailah ta kwana cur tana ta tunanin maganganun Hajiya Rabi dan yadda taga rana haka taga dare, da safe wajen 10:30am ta fito falo bayan ta gama shiryawa ganin bata ga Ummi mai aikinta bane yasa ta nufar d'akinta, Ummi yarinya ce dan bazata wuce 27yrs ba, a hankali Hajiya Lailah ta tura k'ofar d'akin Ummi ta shiga da sallamarta bata iya k'arasa sallamar ba saboda yadda taga Ummi tsirara haihuwar uwarta da ubanta ta fito daga wanka tana shafa mai a jikinta, suman tsaye Hajiya Lailah tayi dan ganin surar Ummi bayya ne a gabanta, take maganar Hajiya Rabi ta kuma fad'o mata rai.


Cak Hajiya Lailah ta tsaya tana kallon Ummi dabama tasan ta shigo ba balle tasan tanayi, Ummi na d'ago kai sukayi ido hud'u da Hajiya Lailah ta cikin madubi, wani uban tsalle ta daka ta fad'a kan gado had'i da jan bed sheet ta rufe jikinta, kasa magana Hajiya Lailah tayi, cikin kasala ta fito ta zauna a parlor, da sauri Ummi ta gama shiryawa ta fito itama, gaban Hajiya Lailah taje ta durk'usa cikin girmamawa tace " Hajiya me kika buk'ata?


Takai wajen 5 minutes sannan ta bud'e baki dakyar tace " breakfast, da sauri Ummi ta mik'e ta nufi kitchen, duk inda tayi idon Hajiya Lailah na kanta bata ko k'iftawa daga d'aya hankalinta yana kan duk inda taga Ummi ta gilma, haka dai gaba d'aya yinin ranar Hajiya Lailah tayi shi sukuku, ta rasa abinda yake yi mata dad'i, idan ta k'urawa Ummi ido batako son ta d'auke idanta daga kanta.


Da daddare wani irin mugun fitinannan ciwon mara ya addabi Hajiya Lailah ya hana ta sakat ta kasa koda zama, in banda murd'awa babu abinda marar ta keyi mata, ga wani uban zafi da k'asanta keyi mata had'i dayi mata zillo kamar zai fad'o, duk da sanyin AC dake d'akin amma gumi duk ya gama jik'a mata jikinta, dukta rikice ta rasa inda zata saka kanta dan dama wani lokacin idan sha'awarta ta tashi haka takeyi mata kamar zata mutu, kwanciya tayi a k'asan capet tana ta murk'ususu, tanaji azaba mai rad'ad'i kamar zata mutu, take maganganun Hajiya Rabi suka shiga dawo mata.


A hankali ta furta " kai ina kozan mutu bazan iya lesbian ba, Allah ya tsare ni da wannan tab'ewa, wannan ai wulak'antacciyar rayuwa ce, take kuma ta tuno yadda taga Ummi zindir ya shiga dawo mata a kwakwalwarta ta shiga tuno k'irar yarinyar, kanta ta fara girgizawa tana cewa "no no no Allah ya kiyaye na aikata lesbian, sai kuma ta fashi da wani irin rikitaccen kuka mai cin rai da k'ona zuciya, " Allah yasa tsakani na dakai Sambo duk abinda na aikata ko nayi kaine sila kai ka sani yin hakan, Allah ya isa bazan tab'a yafe maka ba, ka cuce ni, wani irin mugun murd'awa mararta ta kuma ai da sauri ta saki wani mahaukacin kuka had'i da mik'ewa ta dafe mararta da duka hannayenta biyu.


Bata san sanda ta nufi d'akin Ummi ba, a hankali cikin sand'a ta fara tafiya gudun kar d'aya daga kicin 'ya'yanta su ganta, koda ta zo bakin k'ofar d'akin takai wajen 20 minutes tana tsaye tana zancen zuci had'i dayin saka'a da warwara ganin hakan bazai kai ta bane yasa ta runtse idonta gam had'i da tura k'ofar d'akin Ummi ta shiga......


_Gashi nan ba dan halin ku ba, saboda ina jin kunyar masu bina PC suna rok'o na had'i daban hak'uri akan naci gaba_


_Na hak'ura sosai sannan kuma nayi alfahari da ku da soyayyar da kuke nuna min na hak'ura ne saboda Allah tunda ni ba kowa bace da za'ayi ta had'a ni da Allah ana bani hak'uri na k'i hak'ura, hadith ne ingantacce akan idan anyi maka Kay nuna saboda kai ba jaki bane haka idan an baka hak'uri ka hak'ura saboda kai ba kare bane_




MOMYN ZARAH
[22/01, 16:44] ‪+234 803 948 8935‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*



35



Kwance ta iska Ummi daga ina sai yaloluwar rigar bacci iya cinya, hankalinta kwance tana ta sharar baccinta, cikin had'uwar gaba had'i da tsoro ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana k'arewa Ummi kallo, takai wajen 10 minutes a zaune ta kasa yin komai, cikin k'arfin hali ta mik'e hannunta jikin Ummi ta fara shafo ta, cikin bacci Ummi taji ana tab'a aiko ta farka a firgice had'i da sakin gigitaccen ihu da sauri Hajiya Lailah tasa hannunta ta rufe mata baki gam, a kunnenta ta rad'a mata " Ummi ni ce Hajiya Lailah, ajiyar zuciya Ummin ta sauke da k'arfi had'i da kallon Hajiya Lailah tace " Hajiya kina buk'atar wani abu ne?


Murmushi Hajiya Lailah ta sakar mata had'i da cewa " eh Ummi, cikin alamun tsoro Ummi tace " Hajiya me kike so? cikin sakin fuska Hajiya Lailah tace tsoro nake ji a d'aki na shine nake son kizo muje ki taya ni kwana acan, cikin rashin fahimta Ummi tace " ni kuma Hajiya, ina Sheema? rai Hajiya ta d'an b'ata had'i da mik'ewa tsaye tace " taso mu tafi, yadda Hajiya Lailah ta b'ata ranta ne yasa Ummi bata yi mata musu ba ta mik'e tabi bayanta, suna shiga d'akin Hajiya Lailah ta dannawa k'ofar key, cikin tsoro Ummi ke kallan Hajiya Lailah dan gaba d'aya Ummi a tsorace take da ita.


Cikin kissa irin tasu ta manyan mata Hajiya Lailah ta cire rigar baccin jikinta tayi tsirara ta kwanta akan gado had'i da kallan Ummi dake tsaye sororo tana kallan ikon Allah tace " zo nan Ummi, ba musu ta nufe ta, oil Hajiya Lailah ta mik'awa tace " karb'i ki shafa min a jiki na ko'ina da ina, a firgice Ummi ta d'ago kai ta kalli Hajiya Lailah da alamar tambaya, Hajiya Lailah tace "kamar yadda kika ji nace ko'ina to ina nufin ko'ina, kuma sannan kema kema ki cire kayan jikinki kaf kiyi zindir kamar yadda nayi dan ba'a kwana dani da kaya a jiki.


Sororo Ummi tayi a tsaye hannunta rik'e da oil d'in Hajiya Lailah ta bata ta shafa mata ta kasa koda kwakkwaran motsi saboda tsabar mamaki cikin rashin fahimta Ummi ta kalli Hajiya Lailah tace " kamar ya ban gane ba? "kamar yadda kika ji na gaya miki to haka zakiyi cewar Hajiya Lailah, shiru Ummi, wata mahaukaciyar tsawa Hajiya Lailah ta dakawa had'i cewa " dalla cire kayanki kizo nace, cikin firgici Ummi ta cire kayanta tsaf ta nufi Hajiya Lailah ta fara shafa mata oil d'in a d'an tsorace, Hajiya Lailah ganin bazata samu biyan buk'atarta yadda take so bane yasa ta mik'ewa a hankali ta nufi durowarta ta bud'e ta d'auko bandir d'in 'yan dubu-budu ta mik'awa Ummi, k'in k'arb'a Ummi tayi, murmushi Hajiya Lailah ta kuma yi mata had'i da cewa " karb'e mana, da sauri Ummi ta karb'a Hajiya Lailah ta zauna daf da ita had'i da dafa kafad'arta tace.


" Ummi wannan na baki kyauta ne, ai da sauri Ummi ta zaro ido waje tace " ni Hajiya? Murmushi Hajiya Lailah tayi tace " eh, kuma wannan ba komai ne matuk'ar zakiyi min biyayya ki kuma rik'e min sirri na, zanyi miki komai kike buk'ata zan kuma baki duk abinda kike so zan baki kud'i fiye da wanda na baki yanzu, ai Ummi rud'ewa tayi jin abinda Hajiya Lailah tace " cikin matsanancin farin ciki da murna Ummi tace " aiko Hajiya zanyi biyayya zanyi miki duk abinda kike so matuk'ar zaki rink'a bani irin wad'annan mak'udan kud'in,zanyi miki biyayya zan kasance mai bin umarnin ki a ko'ina ne, kuma in sha Allah bazaki tab'a samu na da fitar da sirrinki ko tuna miki asiri ba.


Murmushin jin dad'i Hajiya Lailah tayi had'i da rungumo Ummi jikinta suka fara gudanar da masha'arsu, sosai Hajiya Lailah ta samu biyan buk'atarta da Ummi, tare suka kwana sai asuba Ummi ta koma d'akinta, bayan gari ya waye Hajiya Lailah take sanarwa Ummi bazata k'ara aikatau ba zata saka a kawo sabuwar 'yar aiki, take Ummi ta canja fuska saboda kishi tace " ni dai Hajiya Allah ki bari zan rink'a aiki na inma kuma dole sai an kawo 'yar aikin to akawo tsohuwa, murmushi Hajiya Lailah tayi had'i da rungumo Ummi jikinta dan ta fahince kishi Ummi take yi, tace " no karki damu sweetie duk yadda kike so haka za'ayi k'are shigewa jikin Hajiya Lailah Ummi tayi, nan ma sai da suka kuma biyawa juna buk'ata sannan Hajiya tacewa Ummi ta shirya zasu je unguwa, sannan ta fita ta nufi d'akin ta tayi wanka ta shirya ta fito parlor, a falo ta iske Ummi harta shirya, suka jera tare suka nufi parking space,

Please Login or Register in order to submit comment