Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa da komai ciki kuwa har da ni kai na,
sai inji ina san na d'auki lokaci mai tsawo rungume da ita a k'irji na,
sosai wutar sha'awar Zarah taci gaba da ruruwa a jikina shaid'an na k'ara ingiza ni,
har nakai limit d'in da bazan iya hak'uri ba, dan har na fara loosing control a kanta lokuta da dama.


Dan haka na fara k'ok'arin neman hanyar da zan cimma burina,
amma na rasa saboda nasan yadda Zainab ke tsananin kula da yaranta da kuma tarbiyyar su,
tana hana kanta bacci sosai dan a dare sai ta lek'a su wajen sau uku,
hakan ya sani k'irk'irar tafiyar k'arya zuwa Paris,
a kid'ime Zainab ta d'ago kai ta kalle shi,
Mannir yace " eh Zainab maganar tafiya ta Paris k'arya ne babu inda naje,
ina nan garin kano zaune a d'aya daga cikin gidaje na,
cikin rawar murya tace " video call d'in da muke yi fa?


Shiru yayi na wani lokaci kafin yace " shima k'arya ne Zainab,
wallpaper ne, nake sawa idan zamuyi video call sai nayi editing,
shine zaku ga kamar ina Paris d'in, ranar da kuka raka ni Airport ma a nan na barku na bi ta k'ofar baya na fita,
ina ganin ku tsaye, kafin ku dawo gidan nayi sauri na dawo na shiga gidan ta k'ofar baya shima dan kar a ganni cikin sa'a kuwa har na shiga na fito babu wanda ya ganni,
duk wani drinks da fruits da ruwan sha nabi duk nayi musu allurar bacci,
dan san idan ba'a sha wani ba dole za'a sha wani,
shima kamar yadda na zata hakance ta kasance dan dana dawo gidan da dare ta b'arauniyar hanya iskewa nayi duk kunyi bacci a parlor,
a hankali nasa hannu na d'auki Zarah nakai ta BQ,
d'an shiru yayi na wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya.



Ya k'ara sakin rikitaccen kuka, cikin kukan yace " a ranar ne komai ya faru,
a ranar ne na cirewa Zarah budurcinta, a ranar na kasance tun daga dare har asuba cike da tsantsar farin ciki na cikar buri na,
da naga irin ciwon dana ji mata nayi muguwar tsorata, amma sai na daure dayake har lokacin maganin baccin bai sake ta ba,
sai nayi amfani da wannan damar na gasa ta sosai da ruwan zafi,
hakan yasa ta samu sauk'i, na mayar mata da kayanta jikinta, kamar yadda suke sannan na mayar da ita cikin gidan ni kuma nabar gidan,
tun daga wannan rana kullum da Zarah nake kwana a BQ sai asuba nake mayar daita cikin gida,
tun daga lokacin na daina jin dad'in kowaccen mace sai ita,
ashe duk abinda ke faruwa akan idon Dauda mai gadi, kuma ashe ya kudiri niyyar ramawa Zarah,
sosai nake samun nutsuwa da gamsuwa da ita, na rink'a jin kamar da a baya ba sex nake ba,
sai yanzu ne nake yin sex, ina cikin wannan hali ne Dady ka kira ni ka sanar da ni maganar auren ta da Naseer,,
iya tashin hankali da kukan bak'in ciki da takaici kam a lokacin nayi su, kamar rai na zai fita,
haka na dawo na daure aka saka ranar bikin su, daga nan sai maganar ciki,
inda na rink'a neman hanyar da zanbi na kawar da Zarah ko Naseer dan ta haka ne kad'ai asiri na zai rufo,
dan nasan muddin Zarah ta haifi abinda ke cikinta na kad'e daga ni har buzu na,
ana cikin haka sai naji Zainab tace ta tab'a kama su suna hot romance da wannan na fakaice,
nima na dage akan shine yayiwa Zarah ciki, data haifi yaron naga yana da cindo da mark sai hankali na ya kuma tashi sosai,
dan nasan asiri na ya tonu ya gama, sai kuma nayi wani tunanin,
dan haka sai na cusawa Zainab tsananin k'iyayyar Naseer a ranta ta hanyar zuga ta akan shi yayiwa Zarah ciki, shine wanda ya b'ata mata tarbiyyar 'yarta, wanda nasan halin Naseer da bak'ar zuciya bazai tab'a d'aukar rai ni ba,
da wannan nayi amfani na kawar da zargin mutane daga kai na.


Ranar da aka d'aura auren Naseer da Zarah, wallahi ji nayi dama ai tashi duniya ranar kowa ya huta,
haka naje d'ayan gidan da nake zama nayi ta hauka ina fashe-fashen glasses,
sannan duk da Zarah tayi aure ban kyale taba ban hak'ura da ita ba,
sai da nabita gidan Dady, ranar naci sa'a Naseer baya d'akin na shiga,
na kashe duk room light, na fara hot romance da ita wanda ita a tunaninta kai ne Naseer,
ta saki jiki sosai da ni dan ta d'auka mijinta ne, tunda a cikin duhu ne, hakan yasa bata gane ni ba ne,,
Ina gaf da shigarta hannunta ya fad'a kan bed side lamp aiko haske ya gauraye d'akin,
nayi saurin kawar da fuskarta ban bari ta ganni ba, na bar d'akin.


Da Zarah ta tashi haihuwa sai Allah ya bata abinda nafi k'aunar samu a duniya sama da komai,
wato d'a Namiji dan Allah ya sani ina matuk'ar san na haifi d'a namiji,
amma Allah bai bani ba, tun daga ranar dana d'ora ido na akan abinda Zarah ta haifa sai Allah ya d'ora min matsanancin so da k'aunar sa,
naji akansa babu abinda bazan iyayi ba, sosai na rink'a jinsa a raina da duk wata gaba dake jiki na,
naji babu abinda nake so a duniya kamar kasancewa tare da yaro na,
har gidan su Dady kawai nake zuwa dan na ganshi,
dan haka na fara tunanin......... ya d'anyi jimmmm had'i da sauke nannauyan ajiyar zuciya.


Sannan yaci gaba " na fara tunanin kashe Naseer ko Zarah,
amma har Zarah ta mutu sannan Naseer ya bar k'asar ban samu na cimma buri na,
lokacin da suka dawo naga yadda Na'eem ya koma sai naji sanshi ya k'aru a raina,
ina shirin d'aukar mataki
Allah ya fara jarabta ta,
ya k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka kamar ransa zai fita.


Wannan bak'in 'kudirin nawa, da mummunar manufa ta akan Zarah yasa ni cewa a raba musu bedroom ita da Ikram,
bayan tun da suka taso tare komai nasu d'aya ne,,
cikin rikitaccen kuka ya k'ara zubewa a gaban Zarah yace " ki dubi girman Allah, da dajarar Annabi ki yafe min,
nasan ban cancanci yafiya daga gare ki ba amma ki dubi.....
bai k'asara ba yaji tauuuuu an kifa mishi mari, yana juyawa yaga Zainab tana huci kamar macijiya,
ya bud'e baki zayyi magana ta k'ara kifa masa wani marin,
sannan taci kwalar rigarsa da duka hanuwanta biyu
ta zaro idanta waje da suka gama yin ja tace,,
tsinannan Allah, munafuki fasik'i, macuci, ka cuce ni ka cuci kanka da rayuwarka,
kayi asarar duniya da lahira,
ashe kai ne bak'in mugun dakayiwa Zarah ciki,
amma dan tsabar rashin imani da tsoran Allah ka zage iya k'arfin ka kayi mata dukan mutuwa har da karaya biyu kayi mata,
dayake kai cikekken tsinanne ne,
wallahi da Allah da mala'iku suna gajiya da tsinewa mutum kai ne mutum na farko dazasu fara gajiya da la'antarsa,
Mannir kasa na tsani kaina da rayuwa ta, kasa ina jin kunyar kai na,
yauce rana ta farko da uwa tayi murna da farin cikin mutuwar 'yarta ta cikinta,
Allah ya taimaki Ikram da bata rayu taji kuma taga wannan mummunan abin kunyar ba.


" Allah ya rufa mata asiri, dan sai ta gwamci mutuwarta da ganin wannan mummunar ranar a rayuwarta,
ranar da zata ga ubanta mahaifi yayiwa k'anwarta da suka sha nono da ita ciki,
mahaifiyarta da mahaifiyar ta suka sha nono d'aya,
yarinyar datake tamkar 'ya a wajenka, wallahi tunda kayiwa Zarah haka zaka iya kusantar 'yarka ta cikinka,
wama ya sani ko itama ka keta mata haddin tunda kai d'an akuya ne,
ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka, hannuwanta tasa ta fara dukan k'irjinsa da iya k'arfinta,
Mannir bai hana ta ba, illa kallanta daya tsaya yana yi hawaye na zubo masa,
sosai take dukansa tana hankad'a shi, tana cewa " ban tab'a dana sanin rayuwa ta da zuwa na duniya ba sai yau,
yau nayi nadamar gaba d'aya rayuwa ta, nayi dana sanin saninka a rayuwa ta,
balle har yakai dana had'a jini dakai, na kuma godewa Allah da yasa babbar alak'ar dake tsakanin mu ta yanke ta hanyar mutuwar Ikram,
baice mata komai ba,
a hankali cikin mutuwar jiki ya rik'e hannuwansa da take dukan k'irjinsa,
da sauri ta kwace hannunta daga nasa ta nuna sa da yatsa tace " daga yau anan take a wannan rana a dai-dai wannan lokacin duk wata alak'a dake tsakani na da kai ta yanke har abada,
daga nan har k'arshen rayuwa ta bana fatan ko burin sake ganinka a rayuwa,
a hankali ya sake ta ya kuma komawa gaban Zarah ya zube ya k'ara fashewa da matsanancin kuka yace " please Zarah ki yaf........


Ganin yadda duk jikinta yake kerrrrma da tsananin rawa yasa shi kasa k'arasawa abinda yayi niyyar fad'a,
a matuk'ar tsorace take kallan sa dan ganin shi take tamkar wani moster,
a razane cike da tsoro take kallansa,
jikinta sai rawa yake yana kerrrma gami da tsuma, kamar wacce taga mutuwarta,
cikin sanyin jiki Mannir ya matso kusa da Zarah had'i da mik'a hannu zai tab'a ta,,
a tsorace tayi saurin ja da baya, hannu ya mik'a zai kai jikinta, tana ganin haka saki rikitacciyar k'ara,
Naseer da tunda Mannir ya fara magana kwakwalsa tayi hook ya kasa cewa komai,
koda motsi ma kasawa yayi mamaki, tsoro da fargaba sun gama cika shi,
gaba d'aya baya cikin hayyacisa da nutsuwarsa,
jin k'arar Zarah ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa,
da sauri ya mik'e yaje inda Zarah ke zaune duk ta k'udundune jikinta saboda tsoro,
Naseer ya tsungunna a gabanta had'i da rungume ta jikinsa,
da sauri ta fad'a jikinsa had'i da k'ank'ame shi sosai, jikinta sai kerrrrma yake yana b'ari,
ga wani uban gumi dake zubo mata, gaba d'aya ta zare, kallo d'aya zakayi mata kasan bata cikin hankalinta.


A hankali Mannir ya kuma mik'a hannu zai tab'a ta, aiko Nasser ya zabura............







MOMYN ZARAH

[3/7, 21:04] hassan tanko: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





75

Cikin mutuwar jiki Naseer ya d'aga masa hannu had'i da matsar da ita gefe,
ba tare da yace masa komai ba,
ita ko duk ta rirrik'e Naseer kamar wacce za'a kashe,
Zainab dake durk'ushe a k'asa tana kuka ta mik'e cikin zafin nama taje gabansa,,
tace " da kake mik'a hannu me zaka kuma yi mata?


Ko..... shiru tayi saboda yadda take jin yanayin jikinta ya canja,
k'irjinta na sama da k'asa da kyar tace " tsakani na da kai Mannir Allah ya isa, Ubangiji yayi mana sakayya ni da Zarah, da Ikram,
a hankali numfashinta datake iyakar k'ok'arin fisgowa ya d'auke gaba d'aya ta zube k'asa a sume,
mik'ewa Naseer yayi da Zarah tsaye a jikinsa, ya fita ba tare daya furta koda kalma d'aya ba,
da sauri Mannir ya bi su suna gaf da barin parlorn ya durk'ushe had'i da rik'o k'afafuwan su,
cikin matsanancin kuka yace " please ku yafe min, idan baku yafe min ba wallahi na shiga uku, yanzu ma kuna ganin yadda Allah yayi dani da rayuwa ta,
a hankaki Nasser ya durk'usa yasa hannunsa ya zame rik'on da Mannir yayiwa k'afuwansu,
Dady da Momy kasa motsi su kayi saboda kunya da tashin hankali,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sauran mutane suka mik'e jiki a sanyaye,
a hankali Abban Zarah ya sunkuya ya sungumi Zainab dake kwance a sume yayi waje da ita ba tare da kowa yayiwa kowa magana ba,
suka fita ko a mota babu wanda yayi magana har suka k'arasa hospital da Zainab.


Da sauri aka karb'e ta aka shigar da ita emergency an d'auki lokaci mai tsayi kafin Doctor ya fito ya sanar da su,
ta samu mutuwar b'arin jiki saboda tsananin tashin hankalin data shiga,
sosai hankalin su yayi masifar tashi, Abban Zarah yayi kuka a b'oye har ya godewa Allah,
bak'in cikinsa biyu na farko halin da Zainab ke ciki,
na biyu abinda mannir yayiwa Zarah,
lalle Mannir ya cika cikkekken maci amana butulu, mugu macuci azzalumi,
amma ba komai shida Allah, tunda gashi nan tun yanzu ya fara girbar abinda ya shuka,
bedroom Nasser yakai Zarah, ya ajiye ta akan bed sannan ya d'auko mata ruwa a fridge ya bata tasha jikinta sai rawa yake yana tsuma, a hankali Naseer ya zauna a kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya rungume ba tare dayace komai ba,
sai ajiyar zuciya da yake ta faman saukewa, ya k'i yin magana ne tun a parlor saboda yasan halinsa da bak'ar zuciya,
muddin yace zayyi magana to komai ma b'aci zaiyi, dan ba'a k'are lafiya ba,
dan haka ya zab'i yayi shirun dan shi ya fiye masa sauk'i.


A gigice Zarah ta d'ago kai ta kalli Naseer tace " dama na fad'a maka Na'eem ba d'anka bane,
ko sau d'aya ban tab'a alak'anta ka dashi ba, kwata-kwata zuciya ta tak'i yarda shi d'anka ne,
dan nasan bazaka tab'a yi min haka ba, ina da cikekken yak'ini akan ka Uncle,
na yarda dakai d'ari bisa d'ari, nasan bazaka tab'a cutar da ni da rayuwa ta ba,
dan Allah Uncle ka d'auke mu bar nan, muma tafi ko'ina ne, Uncle bazan iya ci gaba da zama anan ba,
na tsani garin nan, na tsani kowa da yake ciki, ni kai na ma na tsani kai na,
ganin yadda take magana a burkice duk ta fita daga hayyacinta yasa Naseer mai da ita k'irjinsa ya rungume,
had'i da runtse idansa da k'arfen tsiya, yana shafa kanta,
yana tunanin yadda rayuwa da duniya ta canja,
da yadda mutanen cikin duniya suka zama marasa amana, da alk'awari,
ashe duk yadda kake da mutum yana iya cin amanar ka,
duk kusancinka da d'an Adam da alak'ar dake tsakanin ku yana iya cutar dakai,
to kau idai haka ne duniya da mutum ba abin yarda bane,
Dady da Momy sun kai magrib anan babu wanda iya furta koda kalma d'aya a cikin su,
kowanne yayi jugum yana sak'a abubuwa da dama a ransa,
kiran sallar magrib da akayi ne yasa dukkan su mik'ewa jiki a matuk'ar sanyaye suka bar parlor'n.


Bayan kwana biyu Naseer ya gama duk wani shirin komawar su holland,
dan shi kansa ya tsani Nigeria da abinda ke cikinta jinsa yake kamar acikin wuta,
haka tunda abin ya faru Dady da Momy suke wasan b'oya da Zarah da Naseer dan muguwar kunyar su suke ji,
musamman ma ita Zarah, dan sunfi jin kunyarta akan kowa,
itama tunda abin ya faru bata fito ko parlor ba, kullum tana bedroom tana faman kuka,
ji take dama itace ta mutu ta huta ba Ikram ba, sai yanzu tayiwa Allah godiya da mutuwar Ikram,
dan tasan mutuwarta ta fiye mata data rayu taga tarin abin kunyar da mahaifinta yayi,
babban burinta a duniya bai wuce su bar k'asar ba, kwata-kwata ko yaran ma ta daina shiga harkar su,
ta daina kula su, dan ji take ta tsani kowa da komai, ji take gwamma mutuwa tazo ta d'auke ta,
haka yaran zasu zo su hau kanta su k'araci surutun su amma a banza ko kallan inda suke bata yi,
a parlor Nasser ya iske Dady da Momy zaune kallo d'aya yayi musu ya kauda kansa gefe da bazai iya jurar kallan mahaifansa a cikin matsananciyar damuwa ba,
duk sun rame sosai kamar ba su, duk wannan walwalar dake fuskar su yanzu kwata-kwata babu ita,
sai tulin bak'in ciki da damuwa.


Suma kallansa su kayi cike da tausayawa dan shima yayi muguwar rama acikin kwana biyu kawai,
ya rame ya kod'e sosai, Momy na shirin tashi Naseer yayi saurin cewa " no please Momy ki tsaya bana san ki tafi magana zanyi daku gaba d'aya,
cikin sanyin jiki ta koma ta zauna, sai da Naseer ya d'an numfasa kafin yace,,
" please kuyi min izini ina san barin k'asar nan ni da iyalai na,
zamu d'anyi nesa da nan kafin komai ya lafa, hankula su kwanta,
in yaso sai mu dawo daga baya,
daga Momy har Dady babu wanda yaso haka a ransa amma dan sama musu sauk'i duk suka amince batare da nuna masa alamar komai ba,
zai mik'e Dady yace " kuje kai da Zarah ku dubo Zainab a hospital kafin ku wuce,
cikin sanyin murya Naseer yace " bata da lafiya ne Dady?


Dan shi bai ma san ta fad'i ba a lokacin,
bayani Dady yayi mishi na rashin lafiyar Zainab, aiko sosai hankalin Naseer yayi mugun tashi dan yasan hakan yana da nasaba da tsananin so da k'aunar da Zainab keyiwa Zarah,
haka ma yasan idan Zarah taji abinda yake damun Zainab d'in hankalinta zai k'ara tashi,
amma dai koma meye dole ne suje su dubo ta kafin su wuce, dan ba'a san me Allah zayyi gaba ba,
jiki a sanyaye Naseer ya fita ya shaidawa Zarah ta shirya ita da yaran zasuje hospital,
ba musu ta amsa da to, bata wani b'ata lokaci ba ta fito ita da yaran,
a parlor ta iske Naseer zaune rik'e da Nailah, kallanta Naseer yayi yaga duk ta zama wani iri,
dan ya sani bata cin komai, ko ruwan tea dak'er take sha, shima sai ya matsa mata,
haka ma bata bacci yadda taga rana haka take ganin dare,
bata runtsuwa, tayi bak'i ta rame sosai kamar ba ita ba,
batare dayace mata komai ba ya mik'e yayi waje,
bin bayansa su kayi ita da yaran,
har suka isa asibitin babu wanda yacewa kowa komai a tsakanin su,
sai yaran dake ta faman damun su da surutu,
a harabar asibitin yayi parking ya fito d'auke da Nailah da Noor,
ita dai Zarah bin bayansa kawai take dan bata san wanda bai da lafiya ba,
bata tambaye shi bane dan bata san yawan magana yanzu.


Suna shiga d'akin taga Zainab kwance bata motsi sai na'ura dake aiki,
ko numfashi bata iyawa sai da oxygen,
da k'arfi ta saki k'ara had'i da fashewa da rikitaccen kuka ta fad'a kanta tana jijjiga ta,
cikin kuka ta kalli Naseer tace " Uncle ka taimake ni ka d'auke ni dani da Momy na mubar k'asar nan,
dan Allah mu tafi mubar kowa, ku biyu kad'ai kuka rage min a duniya da nake su,
idan wani abu ya samu d'aya daga cikin ku bazan iya jurewa ba, dan Allah ka taimaka min kar Momy ta mutu,
itama ni kad'ai na rage mata a duniya wacce zata kira tata dan Allah please,
ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka,
kanta Naseer ya shafa had'i da rungumo ta jikinsa,
yama rasa abinda zayyi sai kawai shima ya saki kukan,
dan dama ya dad'e yana rok'on Allah yasa yayi kukan ko zai samu sassauci a zuciyarsa,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake gafe, tsaye sukayi suna kallan su cikin tausayawa,
dan su Naseer basu san da su ba,
sosai da k'arfi Naseer ya rungume Zarah yana rusgar kuka kamar ransa zai fita,
sun ma manta da yaran su dake tsaye,
itama Zarah kukan take sosai tana sambatun da bata san me take cewa ba,,
yaran tsaye sukayi sororo suna kallan Dad & Mom d'in su dake kuka,
a hankaki Na'eem yaje kusa dasu yana share musu hawaye, shima yana kukan,
sai Noor da Nauwaf ma suka nufe su,
gaba d'aya suka saka hannu suna share musu hawaye,
cikin kuka Na'eem yace " Dad nine na saka ka kuka?


Yayi maganar yana nuna kansa,
cak Naseer da Zarah suka tsaida kukan su had'i da zuba masa ido,
a hankali Naseer ya shiga girgiza masa kai alamar a'a,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake tsaye sukayi gyaran murya dan sun lura daba susan suna wajen ba,
da sauri suka d'ago kai ganin Abban Zarah da Alhaji Abdullahi dake tsaye yasa su saurin sakin juna, cike da jin kunya,
sosai suka yiwa su Zarah nasiha mai ratsa jiki da zuciya, wanda a take duk suka ji zuciyoyin su sunyi musu sanyi,
Abban Zarah ya rink'a kawo musu misalai akan Annabawan Allah, da salihan bayi na gari,
ya rink'a jawo musu ayoyin Al-Qur'an,
daga k'arshe kuma ya basu hak'uri on belf of Mannir,
shiru duk sukayi babu wanda yace komai,
sai Naseer daya nemi izinin tafiya da Zainab Holland, batare da gardamar komai ba suka amince.


Washe gari jirgin su ya d'aga zuwa Holland gaba d'ayan su da yaran su, da Zainab,
cikin ikon Allah satin Zainab d'aya a hospital ta farfad'o, sai da har lokacin b'arin jikinta a shanye yake,
dan ko magana bata iyawa, ko zama da gane mutane bata yi,
haka Zarah ta rink'a jinyar ta a hospital, itace wankan ta, itace aikin kashi da fitsarinta,
had'i da sauran aikace-aikace har sukayi wata uku a hospital kafin akan sallamo su daga hospital suka dawo gida,
dan yanzu ba laifi tana iya gane mutane musamman Zarah da Naseer,
kuma tana iya zama a wheelchair, kwata-kwata bata barin 'yan aiki su kula da Zainab ita da kanta ke kula da ita,,
haka rayuwa taita tafiya Zarah na kula da Zainab har Allah yasa ta samu sauk'i garau kamar bata tab'a yin ciwo da jinya ba,
ta warke sosai tayi garau, sai lokacin Zainab ta yarda da maganar hausawa da suke cewa


_" D'A DA DUKIYA BA'A YI MUSU BAK'IN CIKI KO MUGUNTA DAN BA'A SAN MAI MORAR SU BA_


_KUMA BA LALLE D'AN DAKA HAIFA DA CIKIN KA NE ZAI TAIMAKE KA KOYA KULA DA KAI BA,_
_HAKA KOWANNE D'A, D'A NE_


Mannir kam ba'a magana dan dashi da tsumma duk d'aya,
ya yargwale, ya k'ek'ashe, ya bushe yadda kasan ba mutum ba ya koma kamar skeleton,
duk wani hospital daka sani a duniya sun k'i karb'arsa saboda warin da yake yi,
ya gama rub'ewa ya lalace ga al'aurarsa data fara tsutsotsi,
saboda yawan complain d'in da jama'a keyi a kansa na ya dame su da wari yasa human right ta shigo cikin maganar babu yadda zayyi dole yana ji yana gani aka mayar dashi daji aka yi masa gida,
shi kad'ai yake rayuwar sa dan babu wani d'an Adam d'in dazai iya yi masa aiki ko nawa za'a bashi saboda d'oyi,
tun abinda yayiwa Zarah Momy da Dady suka cire hannunsu daga kansa,
suka zuba masa ido, babu wanda ya k'ara kula shi acikin su,
balle su shiga harkarsa,
suka cire duk wani tausayi dake tsakanin d'a da mahaifi suka bar shi da halinsa,
dan sun san abinda yayi ne yake binsa,
koda Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka zowa Dady da maganar Mannir fututtukewa yayi yace babu ruwansa,
kuma duk wanda yasa masa hannu bai yafe ba, dole tasa suma suka kyale shi,
sun san Allah ne da kansa yake hukunta shi abisa cin amanar marainiya dayayi,
sosai Naseer, Zarah, Zainab, Momy da Dady suka koma normal kamar babu wani abu daya tab'a faruwa a rayuwar su,
Zainab ce ta matsa musu akan lalle ya kamata su je Nigeria suga iyayen su,
akan dole Naseer ya nema musu visa,
suka yo Nigeria, sai da suka zo Dady yake sanar musu halin da Mannir yake ciki,
aiko Zarah taita rusgar kuka saboda tausayin sa,
Zainab da Naseer kuwa ko a ajikin su,
yadda kasan ma basu san wanda ake magana akan shi ba,
kwata-kwata babu tausayinsa a zuciyar su,
dole Zarah ta matsawa Zainab da Naseer akan dole sai sunje sun dubo shi,
dakyar ta shawo kansu, suka tafi har su Dady.


Tun daga nesa kafin su k'arasa inda Mannir yake suka fara jiyo d'oyinsa,
kuka Zarah ta k'ara fashewa dashi,
koda suka isa dakyar suka rink'a yin numfashi saboda d'oyin da yake yi,
komai rashin imanin mutum yaga yadda Mannir ya koma dole ne ya tausaya masa,
tsakanin d'a da mahaifi sai Allah take zuciyar Dady da Momy ta karye suka shiga zubar da

Please Login or Register in order to submit comment