Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta k'arya ranar da ruwa zai k'arewa d'an kada.


Ta juya ta mayar da kallan ta wajen Zarah dake ta faman kukan zuci, tana zuciyar ta kamar zata tsaga k'irjinta ta fito saboda tsananin bak'in cikin duniya gami da tsananin takaicin rayuwarta, saboda tsananin b'acin rai gaba d'aya jikinta kerrrrrma yake yana rawa, zuciyar ta bugawa da matsanancin k'arfi tana yi mata soya gami zafi, k'irjinta sai suya yake yana mata k'ona yayinda gaba d'aya taji ta tsani rayuwarta da duniyar ma gaba d'aya, Zainab ta kalle ta tun daga k'asa har sama sannan tayi murmushin takaici tace.


" Banza sakarya shashasha, wawiya kawai wacce bata san ciwon kanta da darajar kanta ba balle tasan mutunci da k'imar kanta, kina tare da makashinki amma baki sani ba, kin d'auki so da yarda gami da amanar duniya kin d'ora masa, amma banga laifinki ba dan masana halayar d'an Adam sunce matuk'ar akaga mace ta lik'ewa Namiji awai wani abu a k'asa a b'oye, to ke naki dayake ya fito ya bayyana kansa duniya sani zai iyayiyowa abinda yake miki ne kike jin dad'insa wannan alama ce ta Naseer ya iya wasan sa amana yasan kansa amatsayin sa na cikekken namiji, hakan ya k'ara tabbatar da gaskiyar abinda nake zargi dan gashi saboda tsabar jin dad'in ZINAR dayake yi dake gashi kin biyo shi har gidan dan nasan yanzu kema kinsan dad'in namiji kin ji yadda ake ji shiyasa kika kasa hak'ura ki jure kika biyo shi har gida, JARABABBIYA kawai, HARIJA, MASIK'A MAZINACIYA.



Dady da Momy na zaune akan sofa babu wanda ya motsa balle yayi magana ko yayi k'ok'arin dakatar dasu, a hankali Dady ya mik'e ya kalli Momy yace " tashi muje ciki ko, babu musu Momy ta mik'e tabi bayan sa, dan matuk'ar El-Mustapha yaci gaba da zama a wajen za'ayi b'atacciya dan ranshi yayi masifar b'aci, dan dama yana da bak'ar zuciya zamu iya cewa a wajensa Naseer ya gado zuciya, mutum ne shi mai wasa da dariya, amma kwata-kwata baya d'aukar raini, musamman yadda Mannir ya zubawa matarsa ido take zazzaga rashin mutunci da tsabagen rashin kunga gami da fitsara a gaban idansu amman ya kasa hanata balle yayi k'ok'arin dakatar da ita kodan kunyar idansu, amma ya tsaya yana kallan yadda ta zage take tijara.


Ta juya ta kalli Naseer dake ta faman huci kyamar zaki in banda Zarah ta hana shi da tuni ya sumar da ita day duka, tace " banga laifin ka ba dan kanata rawar kai da rawar k'afa gami rawar jiki kanta, banga laifinka ba dan kana iya rufe ido akanta kayiwa makusanta turaja ka zazzga musu tsantsar rashin mutunci ba, zai iya yiyiwa kai ma kaji abinda baka saba ji a wajen matan banza da aka saba huld'ar banza dasu ba, da sauri ya yunk'ura zayyi kanta cikin hanzari Zarah ta rik'e hannu shi had'i da girgiza masa kanta aalamar a'a, idansa ya runtse da k'arfi saboda tsananin zuciya dan zuciyarsa takai mak'ura, idan Aunty Zainab ne ya sauka akan hannun Zarah dake rik'e dana Naseer tayi murmushi tace " ai basai kunana ba an rigada an sani, gata nan sai kai ta rik'on abokiyar FASIK'ANCIN naka hannu bibbiyu, MAZINATA kawai, banzaye FASIK'AI.



" Haba Momy abinda kike yi fa kwata-kwata bai dace ba, baya cikin tsari da tarbiyya da kike tunk'aho da ita, a gaban Dadyn Dadyn mu, da Momyn Dady kina irin wad'annan abubuwan haba Momy wallahi bai kamata ba, surukan ki ne fa, zaki zubarwa da kanki da Dady da kuma mu kan mu mutunci da k'imar ahalin mu, wannan bake bace Momy, wani shaid'ainin ne ya shiga zuciyar ki yake sarrafa miki ita, dan wannan ba ainahin Momy dana sani bace, please karki bari shaid'an yayi tasiri da k'arfi a zuciyarki da gangar jikinki gami da ruhunki, Momy ki shaid'anin dayake san juya akalar rayuwarki da zuciyar ki daga kyawawan halaye zuwa ga munana hab...... k'au Zainab ta d'auke Ikram da wani gigitaccen mari mai tsananin k'arfin gaske wanda yasa saida ta hantsila da baya, dole yasa Ikram yin shiru badan ta gama fad'ar abinda yake ranta.


A fusace Zainab tace " dan ubanki ni kike gayawa irin wad'annan maganganun ni zaki gayawa abinda ya dace dani, ko abinda ya dace inyi, lalle Ikram kin isa, tunda hantsarki ta kawo ai dole kiyi min rashin kunya da fitsara, ai kin girma zaki iyyin fiye da haka ma zaki iya yin duk yadda ransa ke so, tunda ga 'yar uwarki nan ma ta zab'i nata zab'in, tabi hanyar data ke, yanzu Ikram dama irin wannan tarbiyyar na baki, oh ni dai Zainab na shiga uku naga ta duniya ina ganin bak'in cikin rayuwa dai-dai gwargwado, me nayi ne?


"Wanne laifi na aikatawa Allah dayake jarrabata da iftila'i kala-kala haka, "yanzu ke wannan tarbiyya kikayi, ko kina ganin kinyi dai-dai ko abinda ya dace ne kikayi,, ki tsaya a gaban iyaye na mahaifa na wad'anda suka haife ni kina zazzaga rashin mutunci gami da tsabar rashin kunya da tijara, haba Zainab idan rai fa ya b'aci hankali baya kushewa, haka idan nutsuwa ta gushe tunani ake sawa ya nemo ta, cewar Mannir, murmushi tayi had'i da cewa " ok yanzu na fahimta, na fahimci cewar ni bare a cikin ku yaran dangi zaku yi min, tunda Naseer d'an uwanka ne, Ikram kuma 'yar ka sannan kuma wacce ta nuna Zarah farkar d'an uwanka ce.


A hankali Zarah ta shiga kokawa da nufashinta dake niyyar d'aukewa gaba d'aya saboda tsantsar bak'in ciki da takaici, a hankali taji numfashin nata ya d'auke gaba d'aya yayinda idanta ya fara gani dishi-dishi, daga k'arshe ma ganin nata ya d'auke gaba d'aya dakyar ta fusgo magana ta kira sunan NASEER!!!! da k'arfi, a kid'ime Naseer ya juya indatake, ai a firgice ya k'arasa inda take, dai-dai lokacin data k'ok'arin sulalewa k'asa da sauri ya tare ta kiran sunanta da k'arfi ZARAH!!!! amma ina bata ko motsi, a tsorace Ikram ta nufi saman su Dady ta sanar dasu hankalin da ake ciki.



Hankali a tashe Naseer ya sure ta yayi harabar gidan da ita, a kid'ime yake kwalawa driver kira da k'arfi cikin tashin hankali, shima driven jiki na rawa ya taso, tun daga harabar asibitin yake kwarawa Doctor kira, da gudu Doctor da nursing suka k'araso d'auke da gadan tura marasa lafiya, kasancewar private hospital ne kuma tana buk'atar taimakon gaggawa yasa basu wani tsaya b'ata lokaci ba aka shiga da ita ciki aka fara aiki, a k'ofar d'akin da aka shigar da Zarah Naseer yake ta zarya ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana cikin wannan halin Dady, Momy, da Ikram suka k'araso cikin tashin hankali, tamabayar Naseer Dady yake halin da ake ciki amma ina Naseer ba baka sai kunne, da ido kawai yake binsu.


Wata baturiyyar likita ce, kyakykyawar gaske matshiya dan bazata wuce 35 yrs ba ta fito cikin matsanancin tashin hankali da gudu Naseer ya nufe ta, a kid'ime take masa bayanin, ba haihuwa bace amma ta fara nak'uda, kuma gashi kasancewar tana cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar damuwa ya haifar mata da hawan jini, kuma zuciyar ta ta kumbura sosai, dole sai dai ayi mata aikin gaggawa a curo d'an matuk'ar ana san duk su biyun su rayu, da sauri Naseer yasa hannu aka shiga da Zarah Operation room, Dady Naseer ya rungume had'i da fasa kuka mai cin zuciya.


Ganin za'ayiwa Zarah CS yasa Dady sanar da mahaifinta da kuma amininsa Alhaji Abdullahi, ba'afi 30 minutes ba sai gasu a lokaci d'aya da hanzarinsu, sai da suka nutsu Dady yayi musu bayanin duk abinda ya faru bai b'oye musu komai ba, take zuciyar Alhaji Abdullahi ta shiga tafasa tana azalzala kamar wuta.


Ba'afi 2hrs da shiga da Zarah Operation room d'in ba, aka fito da ita da hanzari Naseer ya nufi har suka k'arasa wani k'ayataccen bedroom, bakin gado Naseer yaje ya zauna had'i da k'ura mata ido yayinda su Dady, Momy, Ikram, Abban Zarah, Alhaji Abdullahi duk suka zagaye bakin gadon suna kallan yadda take bacci, kallo d'aya zakayi mata kasan tana yin baccin ne dole badan ranta ya so ba, kana dubanta kasan tana cikin matsananciyar damuwa.


Babu wanda yafi takan abinda aka haifa balle a tambayi tana ina, dai-dai lokacin Baturiyyar nan mai suna Jennifer ta shigo d'akin d'auke da Baby tana murmushi ta mik'ewa Naseer tana cewa " congratulations Mr cry, Babynka yayi tsananin kama dakai, you an him they're look like twice, da k'arfi k'irjinsa yayi muguwar bugawa, hannun Dady na rawa ya karb'i yaran yakai idansa kan yatsunsa, gaban Dady yayi mummunan fad'uwa ganin CINDO a hannun yaron, sannan ga tsananin kamar da yaron yake yi da Naseer kamar an tsaga kara bakin Dady na rawa yace " yaron yana da CINDO, cikin kerrrrmar jiki ya d'aga rigar Babyn nan ma yaci karo da MARK a gefen cikinsa, Dady bai san sanda yace " still Mark ba, a fili Dady yace " Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un.




MOMYN ZARAH


```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





52




Cikin tsananin firgici had'i da kid'ima Naseer ya mik'e had'i da karb'ar yaron daga hannun Dady yana dubawa, kallo d'aya ya yiwa yaron ya kau dai yana ambaton " Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un, tabbas shi kanshi yasan yana tsananin kama da yaron, a fili yace " ta ya haka ta faru?


Da k'arfi ya runtse idansa jikinsa na tsuma, had'i da muguwar kerrrma duk ilahirin jikinsa rawa yake, yayinda zuciyar ta tsinke, zuciyar sa ta shiga bugawa da tsananin gaske, yayinda k'irjinsa ya shiga yi masa soya, mak'ogwaran sa ya fara d'aci yana yi masa mak'ak'i, yayinda zuciyar sa ta ci gaba da harbawa da tsananin gaske tana tsalle kamar zata tsaga k'irjinsa ta fito, gaba d'aya jikinsa ya d'auki mugun zafi lokaci d'aya , shi kansa yanzu ya fara zargin kansa yana mamakin taya hakan ta faru, had'i tuhumar kansa, shi dai a iya sanin sa bai tab'a kusantar Zarah ba, iyakacinsa d'an shan minti (romance) take yaji ya tsani kansa da kansa, ashe duk wannan abu daya samu Zarah shine sanadi, a hankali ya share hawayen dake zubo masa, ya kasa koda motsa hannunsa dan yasan yanzu bashi da bakin magana balle ya samu abin cewa, dan yasan shi kowa zai zarga.


Shi babban tashin hankali ma ita kanta Zarah, tayaya zai kuma had'a ido da ita bayan tarin yardar daya mishi, d'azu-d'azun nan ta gama fad'ar yadda matsayinsa yake a gunta, yanzu idan ta farka taga yaron nan ya zayyi mai kuma zai ce mata, Alhaji Abdullahi ya mik'e a hankali gami da d'aukar yaron ya k'ura masa ido cike da tsananin tausayawa take hawaye suka fara zuba daga idanuwansa, a hankali ya shiga furta " kai kuma taga k'addarar kenan, haka Allah ya tsara maka, ta wannan hanyar zaka zo duniya, amma Allah yafi mu sanin dalilin dayasa yayi haka, dan Ubangiji baya tab'a yin abu babu dalili, duk abinda kaga Allah yayi to akwai dalilin yinsa, sai dai muyi addu'ar Allah ya kiyaye gaba, kallan Naseer yayi daya zama kamar wani tab'abb'e yace " wanne suna za'a saka masa, idansa ya k'ara runtsewa da k'arfin gaske had'i da furta "Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un, shikenan mai afkuwa ta auko ya yanzu kowa shi yake zargi, bashi da wata mafita, maganar Aunty Zainab ta tabbata.


Sake maimaita masa tambayar Alhaji Abdullahi yayi, kasa magana Naseer, a hankali ya d'ago kai ya kalli Dadynsa yaga shima shi yake kallo yana watsa masa wata uwar harara gami da kallan tuhuma, da sauri ya sunkuyar da kansa k'asa, Dady yace " baka ji ana yi maka magana ne?



Cikin rawar murya Naseer yace " wallahi Dady yaron nan ba d'ana bane, ni bama Zarah kad'ai ba, ni da kowacce mace ma ban tab'a aikata ZINA ba, wallahi Dady ban tab'a sanin wata 'ya mace ba, a matuk'ar hasale Dady yace " to d'an ubanka ne idan ba d'an ka bane? da uban wa yake kama? sannan duk wasu shaidu sun nuna tabbacin yaro nan d'anka ne, ga CINDO sannan ga MARK, kuma kace zaka zo mana da maganar banza, ko akwai wanda kaji ya tuhume, koya yayi maka fad'a? "Dady aje ayi NDA test amma wallahil azim yaron nan ba d'ana bane dan ban tab'a yin zina a rayuwata ba, ran Dady ab'ace ya wanka Naseer kyawawan marika guda hud'u a jere, da sauri Abban Zarah ya rik'e Dady yana cewa " a'a Alhaji duk abin bai kai ga haka ba, shima yana da dama gami da hak'k'in gare kansa, daga b'acin rai yasa ka yanke hukunci cikin fushi wanda daga baya kazo kana danasani, " a fusace Dady ya kalli Abban Zarah yace " wanne danasanin zanyi bayan ga hujja da shaida nan Allah da kansa ya bayyana GASKIYAR AL'AMARI, sannan zaka d'aure masa gindi, dai-dai lokacin da Zarah ta farka tana tari had'i da salati, a hankali ta fara kiran sunan Naseer.


Wani irin razananniyar fad'uwa gaban Naseer yayi jin Zarah ta farka kuma sunansa ta fara kira, da hanzari Naseer ya mik'e ya nufi bakin gadan, a fusace Dady ya ka mishi tsawa yace " karka sake ka k'arasa inda take, a hankali Zarah ta yunk'ura ta mik'e zaune, cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya tace " Dady please let him come to me? ido Dady ya runtse gami da yin tsaki da k'arfi ya kawar da kansa gefe, Naseer na ganin haka da sauri ya nufi Zarah, cikin kuka yace " please Zarah ki sanar dasu bani ne baban yaron nan ba, ki fad'a waye ainahin mahaifin sa, ki gaya musu MEKE B'OYE, dan Allah ki sanar dasu GASKIYAR AL'AMARI da SIRRIN B'OYE please kona fita daga zargi, ke kad'aice kawai duk duniyar zata iya kub'utar dani daga zargi.


Hannunsa ta rik'o cikin nata tana zubar hawaye, tace "wallahi Naseer nima kai na ban san waye uban yaro nan ba, ban ya akayi na samu cikinsa ba, amma ni dai abu d'aya na sani shine nasan bazaka tab'a yimin haka ba, nasan bazaka tab'a iya cutar dani ba, Naseer koda duk duniya zata yarda kai ne mahaifin yaron nan ni bazan tab'a yarda ba, ta rasa mai yasa zuciya ta tak'i yarda da aminta akan cewar kai ne kayi min ciki.


Amma nasan komai daren dad'ewa gaskiya zata bayyana kanta koda bama rai raye mun bar duniya ne, Allah ne ya jarrabe mu daga ni har kai sai dai mu karb'i jarabawarsa hannu bibbiyu muyi addu'a Allah ya bayyana GASKIYAR AL'AMARI, ajiyar zuciya Naseer ya sake da k'arfi gami da k'ara damk'e hannunta cikin nashi yace " Alhamdulillah tunda baki yarda da hakan ba, dama ni tsoro na da fargaba ta d'aya kema karki yarda da abinda mutane suka yarda dashi, sannan karki aminta da abinda duniya zata ce, dan bana san kema ki rink'a yi min wani irin kallo kamar yadda sauran mutane zasu rink'a yimin, karki rink'a yi min kallan mugu, azzalumi wanda ya cuci rayuwarki ya gurb'ata miki daniyaki, ya musanya miki farin ciki da walwalar ki izuwa bak'in ciki da damuwa kuma ya..... jin an banko k'ofar d'akin da k'arfi yasa Naseer yin shiru batare daya k'arasa maganarsa ba.


Zainab ta shigo cikin d'aurewar fuska ta had'e rai sasoi tace " Alhamdulillah, Masha Allah, yau dai anyi walk'iya munga gaskiya, kuma anyi iska munga d'uwawon kaza, GASKIYA AL'AMARI ya fito fili, ABU A DUHU ya bayyana kansa da kansa, yau kuma Naseer me zaka ce? da wanne kalar wasan kwaykwayon zaka kuma rainawa mutane hankali, ga yaro yayi kama da ubansa sak, sannan ga CINDO & MARK, Allah ne ya kawo k'arshen dramar ka Naseer, dubunka ta cika munafuki mak'iyin Allah, mik'ewa Naseer yayi duk da Zarah na k'ok'arin hana shi, amma zuciyar sa taje sama bazai controlling kan sa, daf da daf yaje kusa da ita ta yadda suna ina jiyo bugun zuciyar junan su ya kalle ta ido cikin ido ransa a matuk'ar b'ace zuciyar sa nayi masa ambaliyar wuta gami da k'una yace.


" Yes Zainab yaron can d'ana ne, jini nane halak malak na kuma karb'e shi hannu bibbiyu, babban abin takaicin shine ace ba'a san ubansa ba, to yanzu an san waye ubansa tunda gashi tsaye a gaban ki, kuma ubansa yakai uban daza'a iya nunawa duniya, saboda yakai duk inda wani namiji yakai, kyau, kud'i, ilimi, gata duk ina dasu, mu kalar tamu k'addarar kenan, ke ko ku an san kalar taku k'addarar da zata zo muku a nan gaba, kuma sannan ina miki albishi a yau d'in nan zan auri Zarah, kuma yanzu-yanzu anan ba'a wani waje ba, sannan na karb'i d'anta daga yau ya zama d'ana kuma na saka masa sunan uban rik'on ta mijinki wato MANNIR, hannu yasa a aljihu ya ciro kud'in dashi kansa bai san konawa bane ya risina ya mik'ewa Alhaji Abdullahi yace " ka dubi girman Allah ya aura min Zarah yanzu kuma anan take, da sauri ta d'ago kai ta kalle shi tana hawaye, kallan ta yayi yace " eh Zarah yanzu zan aure ki, in ga wanne d'an iska ko shege ne zai kuma nuna min iko da gadara a kanki, naga wanda ya isa ya kuma tab'aki matuk'ar ina raye, ya juya ka d'auki jaririn yace " daga yau sunansa MANNIR NASEER MUSTAPHA.


Murmushin farin ciki Zarah ta rink'a yi yayinda hawaye ke zubo mata daga idanunta, sosai Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka ji mugun dad'i da tsananin farin ciki ya gauraye musu duka zukatan su, Alhaji Abdullahi ya kalli Abban Zarah yace " kaje waje ka nemo mutane biyar suyi shaidu, sannan ni zanyiwa Naseer waliyyanci, ya kalli Dady dake tsaye yace " kai kuma sai kayiwa 'yar waliyyanci, ba musu Abban Zarah ya mik'e ya fita, zuciyar Aunty Zainab kamar zata fashe saboda tsananin bak'in ciki da takaici, kallan Zainab Naseer yaci gaba dayi ido cikin ido yayi tsaye kawai yana aika mata da silent killer smile, bak'in ciki ya k'ara turnik'e ta, AbbanZarah bai jima ba ya dawo da mutane wajen guda 10,nan take ranar a lokacin aka d'aura auren NASEER MUSTAPHA & FATIMA MUHAMMAD ZARAH.


Cikin nishad'i da fara'a gami da tsananin farin ciki Naseer ya kuma takawa har gaban Aunty Zainab yana murmushi yace " Alhamdulillah suruka ta tunda kinga k'arshen wason kwoykwayo na, kin san sai cikekken namiji mai kafin basira da tunani ne kad'ai dai iya tsara irin wannan wasan kwaykwayon, sannan GASKIYA AL'AMARI, da kike yawan fad'a gashi Allah da kansa ya bayyanar dashi cewar NASEER MUSTAPHA shine mijin Zarah, ABU A DUHU shima ya fito fili cewar NASEER MUSTAPHA shine mahaifin d'an ZARAH MUHAMMAD, sai me kuma kike cewa? ya fad'a yana karkata kai sama alamar tunani, sai kuma yayi murmushi yace " yawwa SIRRIN B'OYE da kuma MEKE B'OYE, hmmmmm suna duk ga sunan kin gani yanzu a gabanki sai kuma idan yaro ya girma yazo gidan kakaninsa cin tuwo ya k'arasa maganar idansa tarrrr cikin nasa yana silent
smile.


Cikin muryar kuka Zarah tace " please Uncle stop is, she is still my Mom like no other, wata gigitacciyar tsawa Zainab ta dakawa Zarah " dallah can rufewa mutane baki, sai bayan da kika bari ya gama fad'ar duk abinda zai fad'a yakai inda yake san kai, ya dasa aya sannan zaki yiwa mutane bariki da hanzari Naseer yasha gabanta yana girgiza mata kai had'i da cewa " no! no! Zainab, shi is now Mrs NASEER not miss Zarah, you have to be understand Mrs Mannir, dai-dai lokacin Mannir ya shigo cikin matsanancin farin ciki da walwala mara misaltuwa had'i da annushuwa direct wajen Zarah ya zarce bai ma lura da wad'anda ke wajen ba, sannu ya shiga yi mata yana shafa kanta had'i da k'ok'arin rungume ta, cak yaji an d'auke hannunsa daga jikin Zarah had'i da cewa " sorry Mr man, wannan ba Zarah'n daka sani da bace, wannan Zarah matar aure ce yanzu, kuma mijinta yana da tsananin kishin matarsa, dan haka don't ever touch her again if not, ya cije lab'ensa na k'asa da k'arfi.


"What cewar Mannir a kid'ime, "yes she is Mrs Naseer, a matuk'ar firgice ya juya yana yiwa mutanen wajen kallan tambaya, sai a sannan Dady yayi magana " yanzu muka d'aura auren Naseer da Zarah, a hargitse Mannir yace " what kamar yaya Dady, "eh kamar dai yadda kake ji, kamar Mannir zayyi kuka yace " but why Dady?


"Saboda Allah ya rigada ya tsara cewar Zarah matar Naseer ce, sannan ka d'auki matarka kubar wajen nan yanzu, tun kafin ran ku ya b'aci, wajen Baby ya nufa yasa hannu ya d'auke shi yayi hanyar fita dashi, tsawa Dady ya daka masa had'i da cewa " ina zaka kai yaron? "zan tabi dashi inda ya dace ne, dan ya samu ingantacciyar tarbiyyar gami da kulawa ta musamman ne, " baka da hankali ne, ya zaka raba yaro da uwarsa, d'ayen jaririn zaka raba da nonon mahaifiyarsa?


"Eh Dady bazan bari su lalata shi kamar yadda suka lalace, murmushi Naseer yayi had'i da nufar inda Mannir yake, cikin tsananin fitsara yake kallan shi k'uri, murmushi yayi masa had'i mik'a masa hannu yace " bani d'a na, k'in bawa Naseer Baby Mannir yayi, da k'arfi Nasser yasa ya b'anb'are hannun Mannir daga jikin Baby ya kwace yaro, cikin tsananin b'acin rai yana ta faman huci kamar zaki, yayi hanyar fita yana cewa " Zainab zo mu tafi, har sun kai bakin k'ofa suka jiyo muryar Alhaji Abdullahi na cewa " Mannir daga yau mun din kasan ba alkhairi zai kawo ka kai da fitsararriyar matarka wajen mu ba karku kiskura ku k'ara zuwa inda muke, bai jiyo ba yayi ficewarsa Zainab ma ta rufa masa baya.


Alhaji Abdullahi ya yiwa yaro hud'uba da sunan da ubansa ya rad'a masa MANNIR, yace a rink'a kiransa da Na'eem, ranar aka sallame su suka koma gida, da farko k'in Zarah k'in shayar da yaron tayi sai da Naseer ya nuna b'acin ransa a fili sannan ta fara Breastfeeding baby, sosai Momy ke kula da Zarah tana yi mata duk abinda ake yiwa wata 'ya mace 'yar gata idan ta haihuwa, kulawa ta musamman Momy ke bawata tana kuma gyara mata jikinta sosai had'i da tsumata da ingantattun magungunan mata, dan tasan muddin ta gama bik'i Naseer bazai tab'a d'aga mata k'afa ba, musamman yadda yake rawar kan nan.


_Hmmmmmm Ashe k'addara ta rigayi fata_


BAYAN WATA BIYU



Sosai Na'eem nake samun kulawa a wajen Momy, yaron yayi kyau yayi b'ul-b'ul dashi kamar d'an larabawa, gwanin ban sha'awa, yayinda Zarah ta tsane tayi kyau, tayi wani so fresh da ita, sai dai kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, kwata-kwata Zarah bata cikin kwanciyar hankali tunda ta rabu da Zainab take cikin tunani da bak'in ciki akan rashin ganinta, gashi yanzu ko wayar bata kiran su, ta had'asu daga ita har Ikram tayi watsi dasu, dan ma Ikram tana matuk'ar k'ok'arin kwantar mata da hankali, haka ma Momy duk wani abu datasan zai faranta ran Zarah shi takeyi dan tana jin mugun tausayinta, tasha zama tayi mata kuka akan k'addarar da Allah ya jarrabe da ita gata yarinyar k'arama wacce har yanzu bata cika 18yr ba, kullum Momy sai ta markad'awa Zarah fruits ta zuba mata pick milk da honey aciki ta had'e ta bata tasha, sannan ga tsumi kala-kala da ingantattun magungunan mata data ta mafan d'irka mata, dana gyaran jiki, fata, breast, aiko cikin k'ank'anin lokaci tayi d'au da ita, tayi mugun kyau da shek'e duk da matsananciyar ramar datayi, dan tana cikin matsananciyar damuwa.


Wajen k'arfe 12:00am na dare Naseer kwance akan bed d'insa sai juyi yake ya kasa runtsawa, haka kawai yaji yana san ganin Zarah dan haka ya mik'e a hankali cikin sand'a ya

Please Login or Register in order to submit comment