Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauri driver ya taso, Hajiya Lailah ta d'aga masa hannu ta dakatar dashi, Ummi a gaban mota yayinda Hajiya Lailah ke driving suka nufi gidan Hajiya Rabi.



Hajiya Rabi na bedroom ita da wata 'yar shilar yarinya da aka kawalinta ya kawo mata suna tsakiyar duniyar sama ta rink'a jiyo muryar Hajiya Lailah sama-sama d'an tsawa tayi da abinda take yi ta saurara sosai taji, daga parlor ta ji muryar Hajiya Lailah na kwala mata kira, guntun tsaki taja had'i da mik'ewa ta kalle yarinyar tace " ki d'an jira ni ina zuwa, a parlor ta iske Hajiya Lailah zaune kusa da Ummi yayinda keta faman lillik'e mata a jiki.


Da wani irin kallo Hajiya Lailah tabi Hajiya Rabi dan daga ganin ta basai ka tambaya ba zaka fahimci a yanayin da take ciki, Hajiya Lailah tayi d'an mugun murmushi na gefen baki tace " ke kuma ke da wa na ganki haka duk a birkice, ko Alhaji ya dawo ne yana gida? take Hajiya Rabi ta kama 'yan kame-kame tana d'an sosa kanta ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali tace " a'a wallahi ko d'aya, kema ai kin san yanzu bazaki same shi a gida ba koda yana gari, murmushi Hajiya Lailah ta kuma sannan tace " to ke waye a gidan? ko kum....... bata k'arasa ba ganin wata k'aramar yarinya kyakykyawar gaske ta fito daga ita sai wani guntun towel a jikinta.


Baki Hajiya Lailah ta saki tana kallan inda yarinyar take, a take kuma taji yawunta ya tsinke da yarinyar, ranta yayi masifar biyawa, inda Hajiya Lailah take kallo nan Hajiya Rabi tabi da kallo dan taga abinda ya d'auke mata hankali haka ta shagala da kallansa, ganin yarinyar ne yasa ta runtse idonta gam had'i da cewa " oh my God! meyasa kika fito ba cewa nayi ki jira ni a bedroom ina zuwa ba? yanzu da wasu ne ma da kin tuna min asiri kin zubar min da mutunci, yanayin kallon da Hajiya Lailah keyiwa yarinyar ne yasa kishi ya kama Ummi take taji zuciyarta kamar zata buga, duk irin yanayin da Hajiya Lailah ta shiga baisa Hajiya Rabi gano cewar ta fad'a sha'awar yarinyar k'arara a idanta ba, a hankali Hajiya Rabi ta k'arasa inda Hajiya Lailah ke zaune ta zauna a kusa da had'i da cewa " wallahi Aminiya ta ba abinda kike zargi bane, kwata-kwata hankalin Hajiya Lailah baya jikinta yana gun yarinyar.


Murmushi Hajiya Lailah tayi had'i mik'ewa ta nufi inda yarinyar take tana cewa " karki damu k'awata daman abinda ya kawo ni wajenki ma kenan, ni da ke yunzu duk jirgi d'aya ne ya kwaso mu, kwaryar sama ce data k'asa, tana maganar amma idonta nakan yarinyar cikin rashin fahimta Hajiya Rabi tace " kamar ya bangane ba? a hankali Hajiya Lailah ta rungume yarinyar tana sauke ajiyar zuciya a fili, hannun yarinyar ta rik'o ta fara tafiya ita, ba musu yarinyar ke binta har ta zaunar da ita akan kujera ita ta zauna gefenta, Hajiya Rabi kuwa baki ta saki tana ganin ikon Allah ganin yadda lokaci d'aya idon Hajiya Lailah ya canja launi daga fari zuwa ja, cikin kishi Ummi ta mik'e tana zunb'urar baki tace " my life zo mu tafi.


"What my life? Hajiya Rabi ta fad'a a firgice, fuskar Hajiya Lailah d'auke da murmushi ta jiyo tace " I'm so sorry sweetie I cant control my feelings, ido Hajiya Rabi ta k'ara zarowa waje had'i da mik'e ta nufi wajen aminiyar tata tace" please explain it 2 me mana k'awata kin barni cikin rashin fahimta, kin sani a duhu, baki Hajiya Lailah takai wuyan yarinyar tana magana " please mana k'awata ki bari na d'an samu nutsuwa, cikin rashin fahimta tace " dan Allah k'awata kiyi min bayani kozan samu nutsuwa, tsaki Hajiya Lailah had'i da cewa " zauna jarababbiya kawai, wannan ai dole Alhaji ya rink'a guduwa dan idan ya shiga hannunki sai buzunsa, kamar wata doluwa Hajiya Rabi ta zauna a gefen ta, nan Hajiya Lailah ta bada labarin duk abinda ya faru tsakaninta da Ummi tun daga farko har k'arshe, ai tun kafin ta k'arasa Hajiya Rabi ta buga wani uba tsalle ya saki ihu had'i da rungumo Hajiya Lailah jikinta.


Cikin matsanciyar murna da farin ciki tace " weldon k'awata kema yanzu kin shigo layi, da kin tsaya kin cutar kanki a banza ki b'atawa kanki lokaci, shi yana can yana hulewarsa da sa'anin 'ya'yanki, hankali Hajiya Lailah ta kalli yarinyar tana yiwa Hajiya Rabi magana " to yanzu yaza'ayi dan gaske yawu na tsinke da wannan 'yar shilar, dariya Hajiya Rabi tace " shegiya ba'a samun ba, d'auke ta ku shiga bedroom dan nima rai na ya biya da wannan kayan ta fad'a tana kallan Ummi da kamar zata fashe saboda tsabar bak'in kishi, murmushi Hajiya Lailah tayi dan gano abinda yake damun Ummi tace " badamuwa na baki aran ta, s ki k'ara mata haske akan harkar dan na lura tana matsanancin kishi.


Ta fad'a tana mik'ewa had'i da rik'o hannun yarinyar suka nufi bedroom, a hankali Hajiya Rabi ta mik'e ta nufi inda Ummi ke zauna ta rik'o hannunta tana murmushi tace " muje ko? ba musu Ummi ta mik'e had'i da rungume Hajiya Rabi suka nufi Bedroom d'in da su Hajiya Lailah suka shiga, Hajiya ta gama yiwa yarinyar zindir itama taji shigowar su Hajiya Rabi da sauri ta yayi abu zata rufe jikinta tace " haba Hajiya Rabi ya haka zaki shigo d'aki bayan kin muna ciki, kaya Hajiya Rabi ta fara cirewa batare data bata amsa ba, sai da tayi tsirara sannan ta nufi Ummi itama hau cire mata kaya sai ta gama cirewa Ummi kaya sannan ta jiyo ta kalli Hajiya Lailah tace " ashe ke k'aramar 'yar bariki ce, au na manta ashe fa farin shiga ce ke, dole sai na d'ora miki karatu had'i da koya miki salon harkar dan haka gaba d'ayan mu zamuyi Lez anan kuwa ya biya buk'atarsa kowa ma'ana 4 in 4.



Tana gama maganar ta nufi kan bed d'in da Ummi, murmushi Hajiya Lailah tayi sannan ta nufi kan bed d'in itama da yarinyar, tun daga wannan rana Hajiya Lailah ta zama cikkekkiyar 'yar mad'igo ma'ana lesbian, duk inda take idonta yana kana mace, ita bata neman maza kamar Hajiya Rabi, mata kawai tasa a gabanta, tuni Hajiya Lailah tayi mugun suna a harkar lesbian dan duk wata 'yar lez tasan da zaman Hajiya Lailah, yanzu zan iya cewa Hajiya Lailah tafi Hajiya Rabi nesa ba kusa ba, ta zama cikekkiyar 'yar duniya wacce duniyar 'yan iska ta san da zamanta, ba'a iya nan Hajiya Lailah ta tsaya ba, har k'asashen k'etare tana iya haurawa tabi mace kai akan Lez babu abinda Hajiya Lailah bazata iyayi ba, matuk'ar ta kyallara ido ta gano macen da take so to ba zaman lafiya dan tana iyayin komai dan ta samu biyan buk'atarta, su Hajiya suna da wani boka mai zaman kansa wanda yake yi musu aikin asiri da sihiri akan mata ko maza, da zarar Hajiya Lailah ta gano mace ta neme ta tak'i yarda zatakaiwa bokan su ita, shi kuma da yake Allah ya ara masa dama sai kaga dayayi aiki yake ci, yarinyar da kanta zata kawo kanta a haukace.


Kai Hajiya Lailah har su Nijar, Ghana take haurawa akan neman asirin mata, shiyasa dataga mace tana so ko ba Lez sai ta yi amfani da ita dan tsafi take yi musu, su Hajiya Lailah da Hajiya Rabi babban click ne dasu na manyan mata masu ji kansu wajen kud'i da hutu wad'anda mazajen su sukayi watse dasu da buk'atansu suka saka harkar siyasa ko kasuwanci a gabansu, click d'insu yayi suna sosai a duniyar iskanci wajen neman mata (lesbian da neman matasan samari) kuma 'ya'yan talawa suke nema masu kwad'ayi da matacciyar zuciya suyi ta sakar musu mak'udan kud'ad'e suna d'aukar su yawan k'asashen duniya suna kashe musu mahaukatan kud'i.


_Wannan kenan, Allah kasa mu dace duniya lahira ka rabamu da matacciyar zuciya, ka tsare mu da fad'awa halaka_


SHEMA'U


Shema'u wacce duniya tafi saninta da Sheemah, 'ya ce ga Hajiya Lailah da Sanata Sambo wanda tun tasuwar ta ta taso da rashin jin magana ga rashin kunya da raina manya bata gata da shegiyar tsiwa, tunda ta taso Allah ya sanya mata san k'awaye da harkar girma takasance mace ce mai san gayu da kwalliya sutura idan bamai tsada ta alfarma ba bata sakawa, haka ta taso da wannan mugayen halayen kasancewar gidan kowa zaman kansa yake yasa babu mai kwab'arta balle ya tsawarta mata ko ayi mata fad'a akan halayen ta dan haka data girma sai abin yayi gaba ya girmama yaci uban nada.


Bayan ta gama secondary school ta nunawa k'awayenta ita aure zatayi, nan fa suka shiga zuga ta suna cewa lalle kamarki mace har mace zakiyi saurin aure bata dakin fantama kin shana kinyi k'ara'i ba, kije gidan wani k'ato yayi ta iko dake ko fita zakiyi sai kin nemi izinin shi, kuma baki shiga University kin waye idonki ya bud'e ba kake wani maganar aure, da wannan suka d'auke hankalin Sheemah tabar maganar aure duk da ta kasance tana masifar son auren kuma ita gata ba ilimin addini ba balle tasan abinda ya dace da ita, gashi tunda taso a rayuwarta bata san dad'in uwa ko uba ba balle ta fad'a musu matsalarta su bata shawara su kuma nemar mata mafita.


Bayan Sheemah ta shiga university ta waye sosai idonta ya bud'e ta zama cikekkiyar karuwa kuma 'yar lesbian





MOMYN ZARAH


[24/01, 07:12] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




36




Haka Sheemah ta taso cikin rashin tarbiyyar balle ganin k'imar na gaba da ita, duk inda kake tunanin Sheemah ta wuce nan domin yarinya ce cikekkiyar mara kunya fitsararriya wacce bata ganin kan kowa da gashi, duk girmanka duk tsofanka da yawan shekarunka Sheemah tana tsefe idonka ta zage ka taita surfa maka ashar, kullum Sheemah bata gidan su tana yawan gida jen k'awaye da yawan bin samari party, dan haka cikin k'ankanin lokaci tayi mugun suna a duniyar shahararrun karuwai.


Sheemah tantiriyar karuwa ce dan duk tsofan namiji matuk'ar zai bata kud'i ba ruwanta zata bashi kanta, irin su Sheemah ne ake kira da RUWAN KASHE GOBARA, dan duk wulak'antar namiji bata jin k'ank'amin sa, haka ma a b'angaren Lez kwata-kwata bata k'in yin amfani da ita koda irin 'yan k'auyen nan ne masu talla a titi, gata idan taga mace ko namijin dayayi mata kamar tayi hauka bata tab'a iya yin controlling kanta, kamar mahaukaciya take zama taita naci duk irin wulk'anci da cin mutuncin dazakayi mata zata iya jurewa harta samu biyan buk'atarta.


Haka a University su duk yawancin lacturer's da students d'in su sunyi sex da ita, dan ita karantun ba damunta yayi ba, dan kwata-kwata bata zaman class, kai duk yadda kuka tunanin iskancin Sheemah ya wuce nan, duk da irin mak'udan kud'ad'an da take kashewa kanta wajen siyan sutura mai tsada, bags & shoes unique, mota da phone sai wanda taga damar rik'ewa amma duk da haka Hajiya Lailah ko Sanata Sambo babu wanda ya tab'a kula balle ya tambaye ta inda take samun kud'in siyan wad'annan kayayyakin.


Da tsakar dare wajen misalin 2:00am wata irin muguwar sha'awa ta tasowa Sheemah gashi ba halin fita saboda dare yayi sosai balle ta fita taje inda za'a biya mata buk'atarta, haka Sheemah tayi ta murk'ususu tana nishi ita kad'ai a d'aki sha'awa ta matsa mata kamar zata kashe ta, a hankali ta mik'e tayi tsirara a d'akin ta haye saman bed ta fara wasa da al'aurarta tana son biyawa kanta buk'ata, amma a banza yadda kasan k'arawa kanta masifar sha'awar take yi, kwanciya tayi had'i da fashewa da wani mahaukacin kuka kamar ranta zai fita, dan Sheemah tayi gadan jarabar tsiya wajen iyayen ta.


Sosai Sheemah ta rink'a jin kamar k'asanta naci da wuta saboda masifar sha'awa, a matuk'ar galabaice ta mik'e ta nufi d'akin Ummi a gigice ta banko k'ofar d'akin ta shiga, akayi sa'a kuwa yau Ummi bata je d'akin Hajiya Lailah kwana ba, saboda sun biyawa juna buk'ata da dare, a razane Ummi ta mik'e saboda jin yadda Sheemah ta banko k'ofar a haukace, cikin tsoro Ummi ta haye can k'uryar gadon ta rakub'e, da sauri Sheemah ta k'arasa inda Ummi take ta rik'o ta cikin wata irin murya dake fita dakyar saboda tsabar jaraba tace " please Ummi ki taimake karna mutu please Ummi, a d'an tsorace Ummi ta zaro tace " mutuwa? dakyar Sheemah ta iya bud'e bakinta tace " eh wallahi matuk'ar baki taimake ni ba mutuwa zanyi, so please help me.


Cikin rashin fahimta Ummi tace " dame zan taimake ki?

"Da kanki Sheemah ta fad'a tana had'e bakinta dana Ummi, ba musu Ummi ta bawa Sheemah had'in kai sosai suka gudanar da masha'ar su, Sheemah tayi matuk'ar mamakin yadda Ummi tayi masifar iya Lez, tun daga wannan rana Sheemah da Ummi suka d'inke sosai, dan sosai Sheemah taji dad'in amfani da Ummi dan haka taji bazata iya rabuwa da ita ba, dayake Ummi tayi masifar iya takunta daga Hajiya Lailah har Sheemah babu wanda yasan tana da alak'a da wani, kwata-kwata bata nuna alamar akwai wani abu a tsakaninta da d'aya a gaban d'ayan, shiyasa daga Hajiya Lailah har Sheemah babu wanda ya tab'a tunanin akwai wani abu a tsakanin su.



_Wannan kenan, ga Sheemah da Ummi an d'inke sannan kuma ga Hajiya Lailah a gefe, koya za'a kare oho_




HAIDAR



Shine d'an Hajiya Lailah da Sanata Sambo na biyu, shima ya kasance kamar Uwarsa da Ubansa da kuma Sheemah, ya kasance cikekken d'an iska mazinaci d'an shaye-shaye bashi da wani aikin yi daya wuce neman mata da shaye-shaye, Haidar d'an maye ne na bugawa a jarida dan shi koyaushe 24hrs a cake yake, gashi duk inda yaga mata idansa na kansu, maye mata ne na sosai, shima ya kasance kamar Sheemah ba ruwansa da zab'in mace da zai kwanta da ita, kodan ya kasance kullum a buge ne oho.


Kai duk inda kake neman saurayin banza d'an iska Haidar ya kai har ya wuce, shima tun tasowarsa ya kasance yaro d'an k'arya ga son matan tsiya, kasancewar ba kwab'a yasa yaci gaba da girma da wannan mummunar d'abi'ar tasa, duk inda yaga mata hankalinsa na kan su, burinsa kawai ya kasance tare da su, ga mugun shaye-shaye dan babu abinda Haidar bai sha, kullum ka shiga d'akinsa a turnuk'e yake da uban hayak'in kayan maye, da kabi hanyar d'akinsa dole ka rufe hanci saboda tsinannan warin kayan shaye-shayen sa, gashi kwata-kwata bai ganin mutumcin mutane dan yanzu zai yaga mutum duk girmansa, dan duk gidan duk gidan tsoran shi ake ji har Hajiya Lailah da Sanata Sambo dan yanzu nan zai keta musu rigar mutunci matuk'ar suka shiga harkarsa, Fahad kawai yake d'an shayi shima saboda yasan bak'ar zuciyar sa ne, dan sai yayi masa matsiyacin duka a banza.



FAHAD


Matashin saurayi mai ji da kud'i da kyau, d'an gayu ajin farko, kwata-kwata shi bai damu da yawan magana ba, duk da shima a farkon rayuwarsa ya kasance mai irin tarbiyyar gidan su, _(nasan kun riga da kun san waye Fahad tun acikin labarin Abdul)_ amma cikin ikon Allah ya shiryu ya dawo mutumin arziki sosai nutsatstse mai cikekkiyar kalama, kwata-kwata sabgar mutane bata dame shi ba dan baya shiga harkar kowa, idan har ka ganshi a waje to wajen aiki zashi ko wajen kallan ball sai wajen motsa jiki dayake zuwa kullum, a wajen shi ne kawai iyayen su suke samun sauk'i shima bayan ya shiryu ne.


Dan ko yaya Sanata Sambo da Hajiya Lailah suka kuskura suka shiga gonar Sheemah ko Haidar sai buzun su, haka dai rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Hajiya Lailah babu wani gyara kullum sai k'ara tab'arb'arewa da watsewa gami da tarwatsewa da gidan keyi, yayinda hakan bak'aramin k'ona zuciyar Fahad yake ba, dan duk cikin su babu wanda bai san bak'ar halayarsa ba, Hajiya Lailah ce kawai har yanzu bai san ainahin wacece ita ba, yana iya kar k'ok'arin sa dan ganin ya gyara gidan da mutane gidan sun dawo normal suna tsaftatacciyar rayuwa mai inganci gami da tsabta amma ina abin ya wuce tunanin sa dan abun ya faskara ya wuce saninsa, lalacewar gidan ya lura da tushe ta samu.


A gefe kuma Hajiya Lailah da K'awata sai abinda yayi gaba dan wolewarsu kawai suke yi, ba ruwansu da tunanin duniya ko sakamako da makoma balle suyi tunanin k'arshen al'amarin, gaba d'aya rayuwar duniya suka saka a gabansu, kullum idon su yana kan 'yan shilan mata da maza 'ya'yan talakawa suna bud'e musu ido da mahaukatan kud'i, yayinda da a gefe d'aya Ummi da Sheemah ke k'ara holewarsu suna kuma shak'uwa da juna kamar hauka, amma kwata-kwata Hajiya Lailah bara lura da abin ke faruwa tsakanin su ba.



Su Kausar an shiga hidimar bikin aminiyarta Ni'ima haik'an dan an shigo satin bikin dan haka kwata-kwata basa samun zama 24hrs suna busy , yau tun da safe da suka tashi suka tafi kasuwa dan k'arasa yin sauran siyyar data rage musu, basu dawo daga kasuwar ba sai yamma lik'is a kuma matuk'ar gajiye, hakan ne ya hana su zuwa k'unshi da kitso suka bari akan sai gobe dan yau sunyi masifar gajiya, tun da aka fara hidimar bikin Kausar ta dawo gidan su Ni'ima anan take yin komai dan har kwana acan take kwana, suna shiga gidan suka zube a parlor had'i da cewa "wash, Umman Ni'ima dake shigowa parlon d'auke da tiran abinci ta aje agaban su tana cewa " ya naji kuna wash ku duka biyun?


Fuska Kausar ta d'an yamotsa cikin shagwab'a tace " wallahi Umma munyi masifar gajiya ne, tun safe fa muke yawan kasuwa duk rana yau da aka kwala a kanmu ta k'are ga muguwar yunwar da muke faman ji, murmushi Umman tayi had'i cewa "tab tun yanzu har kun fara kukan gajiya, to wallahi inzaku zage gwara ma ku zage dan acikin kashi goma baku d'auki ko d'aya ba, Ni'ima data kasa magana saboda wahala ta mik'a hannu dakyar ta jawo abincin gabanta ta fara ci, Kausar ma ta sanya hannu suka fara cin abincin.


Washe gari ma tun da safe suka fice wajen saloon dan Ni'ima bamai san kitso bace shiyasa ta zab'i saloon itako Kausar tace kitso take so, sai da aka gyarawa amarya kansa aka wanke mata k'afa sannan suka wuce gidan kitso, kasancewar Kasar nada yawan gashi kuma k'ananun kitso akayi mata yasa basu dawo gida ba sai magrib, dan ko k'unshi basu samu sunyi ba, kitson Kausar yayi masifar kyau dan 'yan mitsi-mitsi aka yarfa mata irin na 'yan Nijar, akayi mata shuku a tsakiya sai kuma ayi mata na gaba.


Tun da safe yauma suka k'ara ficewa suka nufi gidan k'unshi aiko an yana musu lallan ya zanu mai ja da bak'i yayi masifar kyau, amma ita Kausar saboda kasancewarta bak'a yasa akayi mata red & golden color, suna dawowa suka Ni'ima ta fad'a wanda saboda a ranar ne akeyin dinner kuma gashi har lokacin ya kusa ga masu make up sun su sai faman jiran su ake yi, wata irin fitinanniyar kwalliya aka yiwa su Kausar sun fito sosai sunyi kyau dan Kausar komawa tayi kamar aljana saboda kyau.


Fad'ar had'uwar da wajen bikin yayi b'ata lokaci ne, an kashe kud'i iya kud'i wajen tsara wajen, Ni'ima da Angonta suna zaune a high table yayinda da kid'an police band ke tashi daga gefe, duk inda ka juya Kausar zaka gani tana ta hidima da jama'a sai kyalli take had'i da shek'i tana d'aukar ido kamar gold kusan gaba d'aya hankalin mazan dake wajen na kanta.


Bayan an gama ciye-ciye da shaye-shaye MC ya buk'aci ganin babban k'awar amarya a filin rawa domin ta d'an taka, gaban Kausar ne yayin mugun fad'uwa dan bata tab'a yin rawa a rayuwarta a ba ita kunyar rawa ma take balle yanzu acikin wad'annan dubban jama'a, MC ya k'ara maimaitawa had'i cewa idan bata fito kafin ya irga goma ba to zai sa mata tarar daba ta kud'i wacce tafi rawar, ganin MC har ya kai eight yasata saurin mik'ewa dan bata san wacce irin tara zai saka mata ba gashi yace bata kud'i bace, a hankali ta fara takawa har izuwa filin rawar ta rawa d'an jujjuwa jikinta a hankali, kasancewar Kausar mace ce har mace akwai diri wacce idan tayi taku duk ilahirin jikinta sai ya motsa yasa nan take gaba jikinta ya d'auki sheken, gaba d'aya hall d'in akayi tsit ana kallonta hankalin kowa yayi kanta.


Shurun da Hajiya Rabi taji anyi ne yasata d'ago kanta a hankali, domin ganin abinda yasa mutane shiku, tana d'agowa idonta ya sauka akan Kausar, nan take gabanta yayi mummunar fad'uwa k'irjinta ya buga da k'arfi, take yawon bakinta ya d'auke mak'ogwaronta ya bushe had'i daui mata d'aci, a fili ta furta " wow masha Allah, Ubangiji yayi halitta anan, bata san sanda ta mik'e ta nufi inda Kausar take a filin rawar ba, tana gaf da isa Mc yace " masha Allah muna godiya k'awar amarya Allah yasaka da alkhairi, zaki iya komawa ki zauna, dama kamar jira take dan jinta take kamar akan k'aya da sauri tabar filin rawar bata k'ara koda 1 second bane.


Tsaki Hajiya Rabi tayi gami da cizon yatsa dan taso ta iske Kausar a filin rawar ta fakaice da rawar ta tab'a jikinta, nan take Hajiya Rabi ta shiga neman Kausar ido rufe a hall amma duk inda ta hango Kausar d'in kafin ta k'asa sai ta iske harta bar wajen, sosai Hajiya Rabi ta tada hankalinta akan son yin magana da Kausar amma Allah bai bata ikon yin hakan ba har aka tashi daga dinner d'in haka Hajiya Rabi ta nufi wajen motar ta cike da matsanancin bak'in cikin rashin magana da Kausar, Hajiya Lailah ce ke jansu a mota motar tayi shiru babu mai cewa da kowa k'ala, shirun da Hajiya Lailah taji yayi yawa ne yasa ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " kai gaskiya bikin nan an tsara komai akan tsari abin ya burge ni wallahi, shiru Hajiya Rabi tayi bata ce komai dan gaba d'aya hankalinta baya kan Hajiya Lailah bare tasan me take cewa, tuni ta tsunduma duniyar tunanin Kausar wacce tunda take bata tab'a jin ta kamu da son mace lokaci d'aya haka ba, kai bama ta tab'a son wani mutum kamar yadda take jin son Kausar haka ba, dan sosai Kausar ta gama tafiya da hankalinta da tunaninta burinta kawai ta kasance da yarinyar, take taji zata iya yin komai akan ta mallaki yarinyar koda na tsawon dare d'aya ne, kuma taji zata iya koda abinda ta mallaka kaf ne akan Kausar, had'i da k'udurcewa ranta zanta aikata komai, kuma zata iya rabuwa da kowa akanta.


Hajiya Lailah takai hannu tad'an tab'a kafad'arta had'i da cewa " lafiya kuwa k'awata? nannauyar ajiyar zuciya Hajiya Rabi ta sauke tare yin murmushin k'arfin hali tace " bakomai k'awata kawai dai ina tunanin rayuwa, ta b'oyewa Hajiya Lailah gaskiyar abinda yake damunta dan tasan matuk'ar Hajiya Lailah taga yarinyar itama sai abinda Allah yayi, koda suka k'asara gida sama-sama Hajiya Rabi tayiwa Hajiya Lailah sallama, tana shiga gida ta wuce bedroom d'inta ta fad'a kan bed had'i da lumshe ido ta fad'a tunanin yarinyar.


Washe gari d'aurin aure tuni su Kausar suka gama shirya komai sannan Ni'ima ta shiga wanka tana fitowa aga watsa mata make up mai shegen kyau, har Kausar zata shiga wanka Umman su Ni'ima ta aiko kiran su, sai dyar Kausar ta zame ta dawo d'akinsu dan ta samu tayi wanka ta shirya itama dan har an d'aura

Please Login or Register in order to submit comment