Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raye zaka rik'e min Zarah hannu bibbiyu bisa amana da gaskiya.


" Ashe ba haka bane, na yaudari kai na danayi saurin yarda dakai Naseer, ta k'ara fashewa da matsanancin kuka, idansa Naseer ya runtse da k'arfi yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, k'irjinsa nayi masa wanirin zafi, mak'ogwaronsa yayi masa mugun d'aci, gaba d'aya jikinsa rawa yake yana tsuma, shi kansa yasan babu abinda zai fitar dashi daga zargin yiwa Zarah ciki har sai idan ita Zarah ta farka ta fad'i wanda yayi mata cikin sannan zai fita daga zargi daga wajen kowa dan yasan a halin yanzu bashi da mafita ko abincewa, da gudu Zainab tayi hanyar fita cikin zafin nama Abba ya rik'o ta, kallo d'aya zakayi mata kasan kwata-kwata bata cikin hayyacin ta.


A firgice tace " Abba ka kyale ni taje wajenta ta fad'a min wani tsinannan ne yayi mata ciki please Abba, tayi magana tana k'ok'arin kwacewa, kanta Abban ya shafa had'i da had'iye abinda yake ji yace " a'a Zainab ki bari sai kin ji sauk'in jikinki tukunna, "Abba babu abinda yake damuwa na lafiya k'alau, kwanciyar hankali na d'aya ku kai ni wajen Zarah, kanta ya shafa ba tare daya ce komai ba, sai ya lallab'a ta Doctor yasa mata drip da yaya mata allurar bacci.


Ana ranar Dady ya kira Mannir yace duk abinda yake yi ya dawo gida, dan ba lafiya, washe gari jirginsu yayi landing a airport d'in AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT, hankalinsa a tashe yayi gidan inda ya tarar da Ikram kawai, ya tambaye ta abinda ke faruwa, kasancewar batasan abinda k'e faruwa ba tace masa Zarah ce ba lafiya dan iya abinda ta sani kenan, sai da yaje asibiti yaga Zainab ma ba lafiya.


Tunda Naseer ya koma gida ya shige bedroom d'in sa ya rufe yake ta rusa kuka, yak'i bud'ewa yak'i ci yak'i sha babu yadda Dady da Momy basuyi akan ya bud'e k'ofar ba amma yak'i, kuka kawai yake tuburan baji ba gani, babban bak'insa yadda aka lalatawa Zarah rayuwarta.


Duk budurin da akeyi Zarah batasa ni ba, dan bata san wainar da ake toyawa ba.



Sai da su Aunty Zainab sukayi sati d'aya a sabitin sannan aka sallame su, Zarah ta warke sumul babu abinda yake damunta , haka ma Zainab ta warke sai da batayiwa kowa magana tun da abin ya faru burinta kawai taga Zarah.


Suna shiga gidan ita da Mannir suka tarar da Zarah da Ikram a parlor da gudu Zarah ta nufu Aunty Zainab tana" Momy I really misses you so much, Mannir shima dabe san meke faruwa ba yayi tsaye yana murmushi, a zabure Aunty Zainab tayi kan Zarah ta shak'e ta, wani irin mugun duka ta ko'ina ta shiga yi mata tana kuka, da sauri Mannir ya k'arasa inda take ya kwace Zarah.


"Lafiyarki kuwa Zainab kike mata irin wannan dukan me tayi miki?


Cikin kuka tace " Mannir ka bani ita ta sanar dani uban da yayi mata cikin jikinta, a kid'ime Mannir yace " what! Ciki Zarahn? "Eh mannir Zarah CIKIN SHEGE TAYI ta d'auko mana magana da abin kunya.


"Kin san abinda kike cewa kuwa?


Jakarta ta bud'e ta ciro d'auko gaba d'aya test d'in asibitin dataje, ta had'a da scanning duka ta mik'a masa hannunsa na rawa ya karb'a ya zauna akan kujera yana dubawa, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yake ta maimaitawa bai san sanda takardun suka zube k'asa ba, Zarah da tunda taji maganar ciki jikinta ke kerrrrrrma ta durk'usa had'i da d'aukar takardun tana dubawa, wani irin mahaukacin ihu ta saki had'i da zubewa k'asa a sume, a matuk'ar zuciye Mannir ya mik'e ya zage iyakar k'arfinsa ya shiga kasar mata mahaukatan naushi da duka tako'ina, take ya had'a mahangurb'a, dukan dayake mata ne ya farfad'o da ita daga suman datayi.


Sosai Mannir ke dukan Zarah, amma Zainab na tsaye ko gezau batayi, ita Zarah tama kasa kuka saboda gaba d'aya ba'a cikin hayyacinta take ba, ba zafin dukan tafi ji ba, zafin da zuciyar ta take yi mata shi tafi ji, kanta Mannir ya kama ya gwara da bango wanda sai da yayi sanadiyyar d'aukewa numfashinta.


Fad'uwa a k'asa a sume jini na zuba ta bakinta da hanvinta, fuskarta ta kumbura sumtum, gaba d'aya Mannir ya gaba sab'a mata kamanni, duk da suman datayi amma hakan baisa Mannir tausaya mata ya kyaleta ba, dukan nata yaci gaba dayi kamar mahaukacin zaki, dukan daya sumar da Zarah haka dukan ne ya farfad'o da ita.


Sai ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta, anan ta zube tana mayar da numfashi sama-sama saboda wahala ta kasa tashi, jikinta duk a fashe, cikin kuka Ikram tazo ta ja ta bedroom taKaita kan bed ta kwantar ta sata gaba tana kuka.



A hankali Zarah ta d'ago kumburar kanta ta da jajayen idanta ta kalli Ikram dakyar ta iya bud'e bakin tace " Ikram da gaske ciki ne dani?


Kai Ikram ta d'aga mata hawaye na zubo mata alamar "eh, ido Zarah ta lumshe tana ambaton " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, had'i da shafo cikin ta, aiko wutsil taji ya motsa, a hankali ta bud'e idanta tana sauraran yadda Babyn ke motsawa sosai a cikinta, hakan ne ya k'ara tabbatar mata akwai d'a acikin cikinta, ita dai tasan ba'a tab'a samun ciki sai an kwanta da d'a namiji (sex) dan ta karanta a addini da kuma biology, ita kuma a iya saninta babu wani namiji daya tab'a saninta 'ya mace ko ya kusance ta, balle harta samu ciki, sai dai idan saka mata akayi dan ta tabbatar bata tab'a samun ciki haka nan ba, haka Zarah ya kwana cur bako gyangyad'i balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, har gari waye, haka ma Aunty Zainab da Mannir babu wanda ya iya runtsa, balle kuma Oga Naseer.


Da sassafe Aunty Zainab ta shiga d'akin Zarah ta tarar da kwance cikin bargo tana ta kakkarwar sanyi, Ikram na gefenta, tsaye tayi a kanta tana kallanta cike da muguwar tsana dan yanzu kwata-kwata bata k'aunar ganin Zarah tace " Zarah ki sanar dani uban da yayi miki cikin nan, cikin kusa Zarah tace " wallahi Allah Momy ban san waye ba, nima ganin cikin kawai nayi a jiki na, wasu fitunannun marika ta watsawa Zarah wanda yasata hantsilawa cikin fushi tace " karki k'ara kirana Momy ni ban haifi MAZINACIYA ba, tsayar da kukanta Zarah tayi ta k'ura mata ido kawai, had'i da maimaita sunan da Momy ta kira ta MAZINACIYA!!! , a hankali tace " Momy wallahi nima ba mazinaciya bace, na rantse da girman Allah ban tab'a aikata laifin ZINA ba, K'ADDARA TAH ce haka.


Cikin zafin rai Aunty Zainab tace "cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, dakyar Zarah ta yunk'ura ta mik'e, dakyar ta take taka k'afarta, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa na rantse da girman Qur'an dake kai na bansan wanda yayi min ciki nan ba, ban kuma tab'a aikata zina ba.



Jikin Aunty Zainab yayi mugu mugun yin sanyi, gaba d'aya jikinta ya saki, zuciyar ta daina yi mata zafi da tafarsa dake ji, tasan Zarah tana da cikekken ilimin addinin islama, tana kuma da nutuwa da hankali tasan bazata tab'a rantse mata da Qur'an akan k'arya ba, a harzuk'u Mannir ya k'arasa shigowa d'akin dan dama yana tsaye yana kallan duk abinda ke faruwa, bai jira wata-wata ba hau dukanta tak'o ina baji ba gani, ya zage yadda zai daki k'aton gardi namiji d'an uwansa yayi ta kai mata naushi da kutufo a ko'ina, cikin rashin imani da tausayawa.


Ya rink'a gwara kanta da bango, yana d'aga ta sama yana jefarwa har sai da ta daina numfashi da motsi amma bai dai na dukanta ba, wata irin razananniyar k'ara Ikram ta fasa had'i da fita da gudu tayi wajen wayar Zarah, da sauri dayi dialing number Naseer, da kamar bazai d'aga sai kuma yayi picking ganin number Zarah ce, a gigice tace " Uncle kazo da sauri Momy da Dady zasu kashe Zarah, kayi sauri please karta mutu, a gigice ya fito da gudu yayi habar gidan dai-dai lokacin da Momy da Dadynsa ke yin parking sun dawo daga unguwa, ganin yadda Naseer ya fisgi motar a haukace sun san ba lafiya ba, dan haka suka rufa mishi baya.


Yana yin parking bai jira motar ta gama tsayawa ba ya fito yayi cikin gidan a haukace, a gefen motar sa su Dady sukayi parking suma suka fito suka nufi cikin gidan.


Naseer na shiga gidan ya jiyo ihun Ikram a bedroom d'in Zarah a hanzarce ya nufi can ya shaga kai tsaye dai-dai lokacin da Mannir ya shak'eta yana cewa " mu zaki rainawa hankali, kin tab'a ganin inda akayi cikin haka nan ko a ruwa ake sha, idanuwanta suka firfitu waje gaba d'ayansu suka kakke numfashinta ya tsaya..........



MOMYN ZARAH


[03/02, 20:53] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*




49




A haukace Naseer ya k'asa wajen yasa hannu ya fisge Zarah daga hannun Mannir ya kalle shi ido cikin ido yace " wallahi duk abinda ya same ta bazan tab'a yarda ba sai nayi shari'a dakai, tsabar baka da imani ka zage iya k'arfinka da Allah ya baka a matsayinka na namiji kayiwa mutum wannan mummunan dukan sai kace ka samu dabba.


Murmushi Mannir had'i da cewa " ai dole kaci haka tunda ka lallab'a ka d'urwa 'yar mutane ciki, shege munafuki mazinaci, masik'i kawai, abinda dama damai bak'ar zuciya, gadan-gadan Naseer yayi kan Mannir dai-dai lokacin da iyayen nasu ke k'arasowa, tsawa Dady ya dakawa Naseer had'i cewa " stop! Karka soma ina ruwanka da shiga tsakanin su ba tare ka gansu ba, yayi mata duk abinda zai iya, idan ma kashe ta zayyi gashi nan gata, tunda bashi da hankali yaga idan hukuma zata kyale shi, yayi maganar yana kallan Mannir dake ta faman huci.


Aunty Zainab dake tsaye tunda aka fara abin bata motsa ba sai taga Naseer ya sumgumi Zarah yana niyyar yin waje da ita, da sauri tasha gabansa tana jefansa da kallan tsana tace " ina kuma zaka kaita? bayan ka riga da ka gama lalata, kallanta yayi ido cikin ido yace " kamar yayafa?


"Ni zaka kalli ido na kace min kamar yayafa? sau nawa ina kama da ita, a zabure Dady ya juyo yana kallan ta yace " Zainab mekike kice?


Hawayen fuskarta ta fara sharewa sannan tace " eh Dady gashi nan ku tambaye shi idan k'arya nake masa, wallahi sau uku ina kamashi yana romancing d'inta, kafin Dady yayi magana Naseer yace " da kika ganni ina romancing d'inta, kin ganni a kanta ne? ko kuma kin tab'a kamani akan ruwan cikinta ina sex da ita ya fad'a idansa cikin nata, dama Naseer akwai bak'ar zuciya, ganin ransa yayi masifar b'aci kuma sun san idan ransa ya b'aci haka idonsa rufewa yake yana iyayin komai yasa kuwa yin shiru, a hankali ya sunkuya ya sab'i Zarah a kafad'a yayi waje, Dady da Momy suka bi bayansa.


Amma kafin su iske shi ya figi motar a 360, da sauri suka shiga mota suka bi bayansa, a k'ofar wani had'add'e private hospital yayi parking, da hanzarinsa ya fito ya shiga cikin hospital d'in bai jima suka fito da Doctor da nursing, kai tsaye emergency aka wuce da Zarah, tsaye Naseer yayi a k'ofar emergency room d'in yana safa da marwa, a haka su Dady suka k'araso, da sauri suka nufe shi, Dady yace " ya ake ciki ne?


Naseer ya bud'e baki zayyi magana Doctor ya fito a gigice da sauri Naseer ya tare shi, Doctor yace " ina mijinta? batare da fargabar komai ba Naseer yace " nine?


" accident d'in data samu gaskiya ya munana dan harda karaya biyu, a razane Naseer yace " what!!! KARAYA!!! a d'an tsorace doctor yace " eh k'afa da hannu, zaman dirshan Naseer yayi a wajen a k'asa ya fasa gigitaccen kuka, Kallan sa Doctor kawai yake yana mamakin namiji kamar Naseer amma da karyayyar.


```Ni ko nace hmmmmm Doctor baka san so bane```


Sosai zuciyar Dady da Momy ta karaya, a hankali Dady ya cewa Doctor " kuyi duk abinda ya kamata kawai, ku d'orata, "ok doctor kawai yace ya juya ya koma cikin Emergency room, a hankali Dady ya durk'usa a gaban Naseer ya rungumo shi jikinsa yana lallashi yayinda Momy ke shafa kansa, a zuciyar Dady yana jinjina tsantsan rashin imani irin na Mannir, cikin kuka Naseer yace " Dady kana jin Doctor ma cewa had'ari ta samu dan shi a tunanin sa accident ne, babu wanda zayyi tsammanin wannan duka ne, Dady Mannir kwata-kwata bashi da imani, baya ganin akwai ciki a jikinta idan wani abu ya same ta fa, wallahi Momy bazan yarda ba sai nayi shari'a dashi kona rama mata, daga Momy har Dady babu wanda yace k'ala.


Wayar Dady ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ya sanar dasu halin da ake ciki, basu jima ba suka k'araso tare, cikin mummunan tashin hankali, anan Dadyn Naseer yayi musu bayanin duk abinda ya faru batare daya b'oye musu komai ba, sosai zuciyar Abban Zarah ta sosu, amman ya daure ya b'oye bai bari ko fuskarsa ta nuna ba, balle a gane yaji zafin abin, Alhaji Abdullahi ne ya harzuk'a ya rufe idonsa yayi ta zazzaga ruwan bala'i san ransa.



Sai da akayi a k'alla 5 hrs sannan aka fito da Zarah jiki duk nad'e da bandeji, da hanzari su Naseer suka mik'e suka bayan su, wani shegen d'aki aka kaita mai shegen kyau da k'ayatuwa babu abinda babu harda kitchen da bathroom & toilet, a bakin gadon kusa da ita Naseer ya zauna had'i da k'ura mata ido hawaye na zuba, sosai al'amarin ya bawa duk jama'ar dake wajen tausayi, wajen 11:00pm na dare Dady ya kalli Momy da Naseer yace su fito su tafi, amma bud'ar bakin Naseer yace " in tafi ina?



Juyowa Dady yayi yana kallansa dan yasan dama za'a rina, fuska d'aure had'i cewa amma kasan dai bazai yiyu ka kwana nan ba ko? "ni fa Dady babu inda zani nabar Zarah, haba sai kace dai marar gata da galihu bayan wannan mahaucin dukan sannan atafi a barta babu wanda ya lura da halin datake ciki ga ciki a jikinta, a hasale Dady yace " to idan ma za'ayi jinyar tata kasan dai baka d'aya daga cikin jerin wad'anda suka dace ko?


" please Dady kayi hak'uri amma babu inda zani, babu yadda Dady, Momy, Alhaji Abdullahi da Abban Zarah basuyi akan Naseer ya tashi ya tafi ba amma fafur yak'i ko motsi, dayaga an dame shi ma sai cewa yayi " wai me kuke gudu ne bayan mai afkuwa ta afku duk abinda kuke tsoran karrya faru ya rigada ya faru, dan ni babu inda zani, sanin Naseer na kafiya tun yana yaro yasa Momy cewa " shikenan kuje ni zan kwana dasu, sosai Abban Zarah da Alhaji Abdullahi sukaji dad'in karar da Momy tayi, dan haka suka shiga yi musu godiya " lah bakomai an riga an zama d'aya, Momy tacewa Dady " ka bawa driver barguna da pillows ya kawo min, Dady yace " to muje mana ki d'auko duk abinda ya kamata inyaso sai na dawo dake, ba musu ta mik'e tabi bayansa.


Zarah najin k'arar rufe k'ofa ta bud'e idanta dan ta dad'e da farkawa kunya ce kawai ta hana ta bud'e idanta, duk budurin da akayi da Naseer akan kunanta, hawaye na zubo mata ta k'ura masa ido had'i da kiran sunansa a hankali " Uncle!!, a hanzarce ya juya yana kanta shima hawaye na zubo masa, dakyar ta bud'i baki tace " wallahi Allah Uncle ban san yadda akayi na samu ciki ba, please ka yarda dani, Allah yadda kuka ga cikin nan a jikina haka nima na ganshi, wallahi Allah Uncle ban tab'a sanin wani d'a namiji ba, ban tab'a aikata zina ba, har rantsewa su Momy da Dady da Qur'an nayi amma sunk'i yarda dani ta fashe da matsanancin kuka.


Shima kukan yake ya kasa cewa komai, "Uncle jibi irin dukan da Dady yayi min, Momy har kira na da MAZINACIYA (My up coming novel) tayi, kowa yak'i ya yarda dani, babu mai yi min uzuri, laifi na kowa yake dabuwa, nasan kai kowa yake zargi amma ni ban tab'a ji a raina ko sau d'aya zakayi min haka ba, na rasa mai yasa kwata-kwata zuciya ta tak'i zarginka, Uncle karka d'ai kawai a rage min a masu so na, na baya dan Allah Uncle karka guje ni, please ka yarda dani wannan ABU A DUHU (Next novel d'ina in sha Allah) yake, daga ni har kai babu wanda yasan MEKE B'OYE (shi kuma upper novel d'ina) har yanzu babu wanda yasan GASKIYAR AL'AMARI (Next upper novel d'ina) balle kuma duniya tasan SIRRIN B'OYE (My new novel).


A hankali yasa hannu yana share mata hawayen dake zubo mata yace " karki damu Zarah, nima na rasa me yasa har yanzu zuciya tak'i ganin laifinki ko sau d'aya ba, wallahi na yarda dake 100% kuma ina tare dake d'ari bisa d'ari, cikin rawar murya tace " thank you Uncle, thank you so much, duk duniya a halin yanzu bani da sama dakai, bani da masoyi na gaskiya mai k'aunata tsakani da Allah sama dakai.


_Ni ko nace hmmmmm Zarah kenan baki daddara ba kenan har yanzu_


Goshinsa ya d'ora akan nata suna kuka babu mai lallashin wani, Momy dake tsaye tana kallansu tun d'azu batare dasun sani ba, ta share hawayenta sai a lokacin ta samu sausauci a zuciyarta, d'an gyaran murya sannan tayi sallama, da sauri Zarah ta rufe idanta.


Cikin tausayawa Momy ta k'arasa inda suke ta zauna a kusa da had'i cewa " ki bud'e idanki Fatima dan duk naji mai kuka ce, banbi Dady ba ganin dare yayi yace zai bawa driver ya kawo min, dan haka naji maganarki tun daga farko har k'arshe, a hankali Zarah ta bud'e idanta ta sauke su akan Momy yayinda hawaye keta faman ambaliya a fuskarta tace " wallahi Allah Momy ban san yadda akayi cikin nan ya shiga jikina ba, ban san mafarin abun ba illa BAK'IN GANI (still my novel) danayi, hawayen Momy ta goge mata karki damu Zarah, na yarda dake kuma nayi miki alk'awarin ina tare dake akoyaushe ko'ina, murmushin yak'e wanda yafi kuka ciwo Zarah tayi, Momy tace " karki sake ki damu karki saka komai a ranki balle ki jawowa kanki ciwo kinji, kiyi hak'uri kowanne d'an Adam da irin k'addararsa, sosai Momy ta kwantarwa da Zarah hankali sannan ta kira doctor ya dubata aka bata magungunanta.


Sannan Momy ta bata light food tad'anci d'an mitsitsi shima ba'a san ranta sai da Momy da Naseer suka matsa mata dakyar taci, , a b'angaren Aunty Zainab kuwa kwata-kwata bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare dan bacci k'aurace mata yayi, haka ma Mannir dan shi safa da marwa ma yayi tayi a d'akin har gari ya waye.


Washe gari da sassafe Zainab da Mannir, Ikram suka tafi gidan su Momy dan jin yadda Zarah ta kwana, dan ita Zainab tun da Zarah ta rantse mata da Qur'an kwata-kwata ta daina ganin laifinta ta karkata gaba d'aya laifin ta d'orawa Naseer dan tasan idan ba shi babu mai d'urkawa Zarah ciki, shine suke kullum kuma koyaushe, Mannir dai baya nan balle ta zarge shi dan yanzu 4 months 2 weeks kenan baya k'asar.


Suna isa harabar gidan Dady na fitowa d'auke da kwandon breakfast, ya gansu sarai amma ya d'auke kansa ya shiga mota had'i da yiwa driver alamar ya taho, da sauri Mannir ya nufe shi yana yi masa magana amma Dady ko kallan inda suke bayyi ba balle ya amsa masa ya bawa driver umarni daja motar.


Da hanzari Mannir ya koma cikin motar yana yiwa Zainab alama data shiga, ya figi motar ya rufawa Dady baya, acan Dady ya iske Alhaji Abdullahi da Abban Zarah ana ta drama da Naseer ya tafi gida yayi wanka ya shirya ya dawo amman yak'i, su Dady suna gaisawa Mannir da Zainab shigo d'akin, a hasale Naseer ya mik'e zai zuba tijara Dady yayi saurin hanashi, Mannir na niyyar nufar gadan Zarah Dady yayi saurin dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu, Zainab tsaye tayi k'em ganin mummunan halin da Zarah ke ciki duk jikinta nad'e da bandeji har fuskarta ga k'afarta da hannunta d'aya a sak'ale duk da k'arafa alamar d'ori , sosai Zainab ke kuka cike da tsananin tausayin Zarah.


Mannir yace " please Dady ka barni na ganta wallahi tun jiya muke neman asubitin da kuke, daga ni har Zainab hankalin mu a matuk'ar tashi yake dukkan mu babu wanda ya runtsa.


A hasale Dady yace " kuna san nata ne kai da matarka zaku had'a kai kuyi mata wannan mugun dukan da har Doctors suna tsammanin accident ne, babu wanda yayi tunanin wannan duka ne harda karaya biyu.


"Karaya fa Dady Mannir ya fad'a a razane yana zaro ido, " baka da gani ne ko baka da ido ne ko dazaka shiko part d'in bakaga an saka Orthopedic ba, " dan Allah kayi hak'uri wallahi ban.... bai kai ga k'arasa maganar ba suka jiyo ihun Naseer, duk suka kalle shi,, da gudu ya nufi gadan Zarah yana kwala mata kira Zarah!!! gaba d'ayan suka kalli wajen, jini ne fitowa Zarah ta baki ta hanci data kunnenta, idanuwanta gaba d'aya sun kakkafe bak'in ya d'auke sai iya farin kawai, jikinta ya sandare, sai kaf-kaf datake kamar mai farfad'iya.


A haukace Naseer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan Doctor da k'arfi duk ya fita daga cikin hayyacinsa, nutsuwarsa ta gushi ihuuuu kawai yake yana kuka, hannunsa Zarah ta rik'o da d'ayan hannunta mai lafiya dakyar tace " Naseer, yau ne rana ta farko data ambaci real name d'insa a razane ya d'ago yana kallanta ido cikin ido yana kuka kamar ransa zai fita, murmushin k'arfin hali tayi masa tace " nagode sosai da soyyayyar daka nuna min, dazan rayu dana yi maka..... bata k'arasa ba ta fara aman jini gunduwa-gunduwa dakyar ta tallafo fuskarsa tana murmushi tace " uncle mutuwa zanyi, please ka daina kuka, na baka amanar Momy na Ikram ka kular min dasu yadda zaka kula da kanka, ka yafewa Dady na please karka rik'e shi a ransa.


Hannunsa da rik'e tana zabure-zabure can kusan tayi salati jikinsa ya saki........




MOMYN ZARAH
[03/02, 20:53] Hassan Atk: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*





50




Da k'arfi Naseer ya kira sunanta yana jijjiga ta ZARAH!!!!!, a haukace yake kwalawa likita kira iya k'arfinsa yana ihuuuun hauka, a wajen Aunty Zainab ta zube a k'asa akan gwiwoyinta tana hawaye amma ta kasa kukan, a razane Mannir ya fita yana kwalawa Doctor kira a matuk'ar firgice, da sauri Doctor da Nursing suka shigo, gam Naseer

Please Login or Register in order to submit comment