Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai an fara shirya makirci da tuggu a tsakanin shi da Teemah ta yadda zamu raba kansu mu kawo zargi, kokonto had'i da rashin yadda a tsakanin su, ta haka ne zamu samu damar cika birin mu akan su, "gud ideas sister kin kawo shawara mai kyau, dama ance d'an gari kan ci gari, shi dai Zaid shiru kawai yayi ya k'ura musu ido yana kallonsu, Lubnah tace " zan saka Dady na ya binciko min duk inda suke a fad'in duniyan nan, "ok kira shi ki sanar dashi, ba musu Lubnah ta mik'e ta nufi inda wayarta take, bugu d'aya Dady ya d'aga da sallama a bakinsa ta gaida shi, bayan sun gama gaisawa ne ta shiga kwararo masa bayanin duk abinda yake faruwa, cikin kad'uwa Dady yace " lalle wannan yaron ya cika cikkeken butulu , makiri, kuma maci amana, dole a d'auki mummunan mataki akansa dan hakan yazamo izzina ga 'yan baya masu hali irin nasa, "haka ne Dady shiyasa yanzu ma muke san sanin k'asar dayake, "badamuwa Auta ki bani nan da 1hr zan kira nayi muku bayani bayan na gama dubawa, "ok thanks dad ta fad'i dayi mishi sallama.


'Yan sanda kuwa sai bincike suke haik'an babu dare ba rana dan gano inda Zaid yake sunje gidan shi sun bincika in an out amma babu ko alamar yazo gidan ma, haka ma sunje gidan su nan ma sunyi bincike amma basu samu komai ba, duk ma'aikatan gidan tun tara su sun bincike su amma babu wata kwakkwaran maganar kamawa balle su samu shaida, sosai hankali DSP Hassan yayi mugun tashi saboda a hannunsa case d'in yake, haka ma drivers d'in da suka d'auke shi yayinda za'a kai shi asibiti duk an kama su an tsare su ana ta bincike akan su dan ana zargin da sa hannun su kuma da had'in bakin su Zaid ya gudu ana tunanin ko an basu wasu mak'odan kud'i ne.


Bayan 1hr Dady ya kira Lubnah yake shaida mata cewar Mukhtar da Teemah suna Holland ya kuma fad'a musu ya fara gudanar da kasuwancin sa acan dan this week ma zai bud'e sabon Company a can, godiya tayi masa sannan ta aje wayar ta kalli Abraham da Zaid wanda gaba d'ayan hankalinsu na ganta jira kawai take ta gama wayar tayi musu bayani dan a k'agare suke matuk'a, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta shiga yi musu bayanin da Dady yayi mata, aiko wata uwar zabura Zaid yayi ya mik'e yana huci, jikinsa sai kerrma yake, take zuciyarsa ta shiga buga masa da k'arfin gaske, mak'ogwaransa yayi masa mugun d'aci ya juya ya kalli Abraham yace " duk inda zaka samo mana Visa kayi in just 2 days, da sauri Abraham ya mik'e yace " baka da hankali ne baka san yanayin da ake ciki bane yanzu kasan fa kai ko wanene, to idan ma baka sani ba gwara ka sani you are wanted, ta ko'ina nemanka ake a raye ko mace ka tsaya abi komai hankali, tsawa Zaid ya dakawa Abraham yace " koma meye kuma koma wanne hali zan shiga babu ruwanka kai dai kawai kayi k'ok'arin samo mana visa " you are totally mad Zaid, idan kai baka cikin hayyacin ka ni ina cikin nawa hayyacin, da harzuk'e Zaid ya shak'i Abraham, ganin haka yasa Lubnah saurin mik'ewa tayi wajen Zaid, dakyar ta janye shi, a hankali ta zaunar dashi akan sofa ta mik'e ta nufi fridge ta d'auki masa ruwan sanyi ta bashi ta bawa Abraham , sai da sukayi kusan 15 minutes babu wanda yacewa k'ala.


A hankali Lubnah ta numfasa ta d'ago kai ta kalle sannan tace " da farko matuk'ar kuna san samun nasara a gaba d'ayan rayuwarku sai kun cire wannan zafin zuciyar had'i da rashin jituwa a tsakanin ku, na d'auka iya abinda ya faru yanzu kad'ai ya isheku izzina bama ku ba harga wasu, ta kai dubanta ga Zaid tace " kaifa Mukhtar yayiwa bayanin komai ya kuma ce maka da kuna shiri a tsakanin ku da bai samu nasara ba, gaskiya yanzu ya kamata ace kun san Annabi ya faku, ku had'e kanku ku cire wannan zafin zuciyar dan yazo lokaci ne na zumunci da k'aunar juna ya kamata ace kunyi watsi da duk abinda ya faru a baya, nan dai taitayi musu nasiha mai ratsa jiki da karya zuciya ta kuma rink'a kawo musu misalai had'i da kawo musu Hadisai da ayoyin Quran, sosai ta kashe musu garkuwar jiki, take suka manta da duk abinda ya faru, Zaid ko k'ura mata ido kawai yayi yana kallanta yana kuma ganin baiwar kyau, hankali, nutsuwa, tunani ga kuma tarbiyya, haka nan kawai ya rink'a jin farin ciki, a k'ark'ashen zuciyar sa kuma yana yiwa Allah godiya da samun mace ta gari irin Lubnah.


Bayan komai ya lafa tace " bari na kira Dady in tambaye shi idan ma zayyiyo ko bazayyiyo ba shi zai sanar damu, bayan ta kira Dady tayi masa bayani yace " dole sai Zaid ya canja passport da kuma, amma zayyi duk abinda ya kamata, godiya ta kuma yi masa had'i dayi masa sallama, sannan tayi musu bayani, sannan tace " Abraham ya kaiwa Dady password d'insa dan ita nata yana hannunsa, murmushi yayi mata yace "ok badamuwa in sha Allah yau da daddare zan kai masa, ya fad'a yana mik'ewa, har yakai bakin k'ofar fita unexpected yaji Zaid yace " I'm sorry Brother, a hankali ya juyo ya kalle shi had'i sakar mishi murmushi yace " never mind.


Tun daga lokacin babu wani abu daya k'ara shiga tsakanin Zaid da Abraham sai farin ciki da k'aunar junansu da suke mugun yi kowannen su baya k'aunar yaga ko k'uda ya tab'a masa d'an uwansa,balle kuma su suyiwa junan su, kasancewar Abraham ya kama ya tsare ne ya hana wani abu shiga tsakanin Lubnah da Zaid dan duk inda Zaid yake to Abraham na tare dashi, ga gidan mai tsarin turawa, yayinda da Dadyn Lubnah keta faman k'ok'arin nemar musu Visa dan tafiya Holland, Allah yasa cikin satin aka samu visar ta fita dan haka babu wani b'ata lokaci suka hau shirin tafiya, ranar tafiya Dady ne ya tsara musu komai, shi Zaid yayi shigar larabawa ya saka jallabiyya da hijami yayi shigarsa tsaf su haka ma Lubnah ta saka abaya da tarha (mayafin abaya) had'i da k'attuwa (Nik'ab) ta rufe jikinta tsaf, shi kuma Abraham yayi shigar Pakistan, hakan yasa basu samu matsalar komai ba, har jirginsu yayi landing a Holland.


Kasancewar da tskar dare suka sauka ne yasa su yanke shawarar fara zuwa restaurant kafin su wuce hotel d'in su, suna isa wake cikin za'a suka same taxi driver d'an Nigeria da fara'a ya tare su, ganin shigar da sukayi ne yasa shi yi musu turanci, umarni Abraham ya bashi daya kaisu Nigerian restaurant a hankali ya juyo ya kalle su yace " are you Nigerian? wata uwar harara Zaid ya watsa masa hakan daya gani ne yasa kame bakinsa yayi shiru, dan yanzu kwata-kwata Zaid bashi da yarda, ya daina yarda da mutane.


Murmushi Abraham yayiwa driver yace " yes, but why do you ask? "Because am Nigerian too, "ok Abraham, sai kuma ya juya ya kalle shi yace " your tribe please? murmushi driver yayi sannan yace " am Hausa fulani what about you, dariya Abraham yayi yace " nima haka ya bashi amsa da hausa, aiko da sauri driver ya juyo yace " haba kwata-kwata bakuyi kama da hausawa ba, ko kuma kunzo wajen bikin bud'e a Nigerian Company ne matashin mai kud'in nan wanda ake yiwa lak'abi yaro da kud'i?


Murmushi Abraham yayi yace "wake nan? Driver yace " MUKHTAR yana ambatar sunan Mukhtar take jikin Zaid ya d'auki rawa, ya harzuk'o da sauri Lubnah tasa hannu ta mai dashi had'i dayi masa rad'a a kunne, " Lah aiko kamar kasani wajen taron muka zo ya akayi ka sani? "ai tunda aka saka ranar bud'e company kullum sai munyi bak'i, kuma ma aboki na ne babban yaran sa, da tare muke aikin taxi driver dashi, shine Allah ya taimkesa ya samu aiki a gidan sa, aiko take wani irin mugun farin ciki ya lullub'e su, cikin dabara Abraham yace " kai amma yayi za'a amma nasan yanzu dayake shi ya samu duniya ya manta da kai ko?


Dariya driver yayi yace "nine fa baban abokinsa sanda ma yazo nan garin a waje na ya fara zama, kuma babu yadda bayyi da ni akan zai samar min aiki a gidan ba ni ne naki, "mai yasa? haka nan kawai, ni da nama kusa komawa gida, idan na samu aikin naji dad'i bazan koma Nigeria yanzu ba, " kuma har yanzu kuna gisawa dashi abokin naka bai wutak'anta ba? " A 'a shi ba haka yake ba, mutum ne mai kirki ga tsoran Allah, kwata-kwata ya tsani zalunci da azzalumai, haka dai Abraham yai ta jansa da hira yana kuma bugar cikinsa har suka k'arasa restaurant d'in.


Bayan sun gama cin ya kai su hotel, ya sauke musu kayan su, ya zaro card ya basu yace " duk sanda suke san driver suyi mishi magana, Abraham yana dariya ya karb'a, bayan sunje d'aki sunyi wanka sun shirya Abraham ya same su a d'akin su, a zaune shima zaman yayi sannan ya kalli Zaid yace " ka gani ko da kana neman yi masa wulak'anci, ajiyar zuciya Zaid ya sauke had'i da cewa yanzu meye abinyi ? " to ni dai a shawara ta mu kira shi, shida abokin nasa muyi magana da su, tunda dama Lubnah tace dole sai an samu na jikinsa, "haka ne to amma kai a ganin ka me zamu gaya musu? "Gaskiya cewar Lubnah taci gaba da cewa " ita gaskiya d'aya ce daga ita kuma sai b'ata, idan ka dubi mutumin nan sosai zaka san mutumin kirki ne kuma baka ji abinda yace akan abokin nasa ba, ni dai a ganina mu sanar dasu gaskiya kawai, idan sunga dama su taimake mu, idan kuma sunk'i sai Allah ya dubi gaskiyar da muakayi ya taimake mu, duk sukayi shiru kana daga bisani suka sauke ajiyar zuciya, "ok badamuwa hakan ma yayi cewar Zaid, sannan ya kalli Abraham yace " ka d'auki number sa ajikin card d'insa ka kira shi kace yazo shida abokin nasa, "ok kawai Abraham yace sannan yayi dialing number bayan ya d'auka ne ya sanar da shi suna san ganin su.


Washe gari su Zaid zaune tare da driver da abokinsa, bayan su gama sanar da su komai, sosai suka jinjina al'amarin sannan sukayi musu rantsuwa akan zasu rik'e musu alk'awari zasu kuma basu duk taimakon da su, sannan suka rabu bayan sun gama tsara komai had'i da shirya komai.


Washe gari Ali abokin driver ya samo wata kyakykyawar budurwa ya had'a baki da ita ya sanar mata abinda yake tayi masa, ba musu ta amince, bayan kwana biyu ta kawo masa dukkan abinda ya umarce ta, ya karb'a yana murmushi sannan ya biyata iya adadin kud'in da sukayi akan zai bata yayi mata godiya.


Ranar taron bud'e Nigerian Company hall yacika mak'il da jama'a ciki kuwa harda su Zaid, Abraham, anyi masifar kashe mak'udan kud'i wajen tsara hall da kuma kayan ciye-ciyen dake gaban jama'a dan motsa baki sai da aka gama ciye-ciye sannan mc yayi sanarwar cewa ga uban taro nan da matarsa, take Mukhtar da Teemah suka bayyana sunsha kwalliya da shegun kaga iri d'aya fuskarsu d'auke da murmushi hannunwansu sark'e dana juna, suna shigowa kowa ya mik'e amma banda Zaid da tuni zuciyar sa ta kama da wuta, jama'ar dake wajen suka shiga yi musu tafa, duk inda sukayi masu camera da 'yan sai d'aukar su pics suke, bayan an gama komai, komai ya kamla Teemah da Mukhtar suka shiga ferri car d'in su sukayi gida, a hankali idris (taxi driver) ya take musu baya ya rink'a bin su a baya har suka isa gida, daga Zaid har Abraham ba k'aramin rud'ewa sukayi ba dan ganin irin mahaukacin gidan da su Mukhtar ke ciki, suna tsaye suna kallonsa sanda get d'in ya bud'e kansa, suka shiga gidan, Mukhtar da kanshi ya zagayo ya bud'ewa Teemah k'ofa ya d'auke ta cak yayi ciki da ita, da k'arfi Zaid ya rintse idonsa saboda ganin irin rayuwar farin cikin wad'anda yafi tsana a duniya sama da kowa sukeyi.


A hankali Abraham ya dafa kafad'arsa, tare da bawa idris umarnin ya maida su hotel, tun daga wannan rana su Zaid suka zamewa su Mukhtar inuwa dan duk inda suka shiga suna biye da su a baya, har suka gama sanin sirrin su kaf.


Ranar Sunday Teemah ta shirya zata siyayya a mall ta kalli Mukhtar tace " please dear ka raka ni shopping please yau ma karka ce baka da time, rungumo ta jikinsa yayi yace " am sorry my love ina busy yanzu haka ma, amma in sha Allah next week I promise i will spend all my weekend with you, murmushi yak'e kawai tayi ta mik'e dan idan da sabo ta riga da saba da halin Mukhtar kullum ace mata yana busy yake kwata-kwata baya bata lokacinsa, a halin yanzu bata da wata damuwa data ce na rashin bata lokaci, bata k'ara bi ta kansa ba ta fita abinta, driver ta bawa umarnin ya kaita inda ya saba idan zatayi siyayya, ba musu yaja motar, bayan ta gama siyayyar ta fito ne su Zaid dake lab'e a cikin mota ya umarci Ali dacewa yi sauri gata can, da hanzari Ali ya fita, yayi kamar bai ganta ba, ya nufi k'ofar shiga mall d'in da fara'a fuskar Teemah tace " a'a su Ali ne murmushi yayi mata yace " eh nine amma please kiyi hak'uri dan ban gane mai magana ba, "Fateema ce matar Ogan ka Mukhtar "matarsa kuma ya akayi kika zama matarsa bayan ya gaya min shi bashi da aure?


Da k'arfi k'irjinta ya buga ta kalle shi tace " kamar ya? yace " eh shi da kansa yace "min bashi da aure har nake tambayarsa to ke fa, sai yake ce min ke karuwa ce wacce ke kanki baki san asalinki ba, yana dai taimaka miki ne kawai kafin burinsa ya gama cika akanki harma yake ci min wai kin tab'a kashe mijin ki sunanshi zadi kowa, wai mai zayyi da mace maci amana kamar ki, wasu siraran hawayen ne suka shiga zubowa Teemah a ranta tace tabbas maganar nan daga bakin Mukhtar ta fito saboda duk duniya babu wanda san wad'an nan maganganun sai shi da ita kawai.


Wato shiyasa baya san fita da ita, shiyasa yake yi mata wasu abubuwan data kasa gane kanshi, ganin haka yasa Ali yin kalan tausayi kamar da gaske yace " please ki rufa min asiri karki sanar dashi saboda zai iya korata daga aiki kuma wannan aikin dashi kad'ai na dogara,kuma karki damu in sha Allah zan binciko miki komai, kai kawai ta iya gyad'a masa ta shige mata driver yaja, suna cikin tafiya , motar su Zaid tasha gaban motar su Teemah driver ta ya taka burki da k'arfi k'uuuuuuuuu tsorace Teemah wacce keta faman sharar kwalla ta d'ago kai tana duban gaban ta gabanta ne yayi mugun fad'uwa jikinta ya d'auki rawa a matuk'ar firgice take bin shi da kallo, shima a tsorace ya ya bito daga motar su a d'an firgice jikinsa sai rawa yake alamar tsoro da sauri ya bud'e motar ya figi hannun Teemah da gudu yayi wani uncompleted building da ita.........




MOMYN ZARAH

```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*



31



Idris driver na zuwa uncompleted building d'in da ita ya tsaya cikin alamar tsoro da firgici had'i da mummunan tashin hankali ya fara magana " Hajiya kin tab'a taimako na dan haka bazan tab'a bari ina gani wani mummunan abu ya same ki ba, da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro memory card ya mik'a mata yace " gashi idan kinje gida ki nutsu ki gani kinji duk shirin da Mukhtar keyi a kanki yana ciki, sannan ya k'ara da cewa " a kowanne lokaci kina iya jin ance maki na mutu to ba mutuwar Allah da Annabi bace dan Mukhtar yana neman rayuwata akan wannan memory, yana kaiwa nan bai tsaya ya jira abinda zata ce ba ya fita da gudu a matuk'ar firgice, a tsaye ya barta tana ta zancen zuci yayinda da hawaye sai ambaliya yake yi a fuskarta, dakyar ta iya jan k'afarta zuwa inda mota take ta shiga, koda suka isa gida a parlor ta iske Mukhtar bata tsaya bin ta kansa ba ta shige d'aki had'i da danna key.


Jikinta na rawa ta saka memory a wayarta ta kunna ta fara kallon abinda ke cikin, iyakar tashin hankali kan Teemah ta shige shi, jikinta ya shiga rawa had'i da kerrma cikin tsoro da mummunan tashin hankali taci gaba da kallon video, Mukhtar ta gani tsirarar Allah yana aikata zina da wata zankad'ed'iyar budurwa bayan sun gama aikata masha'arsu budurwar ta kwanta a saman k'irjinsa tana shafo fuskarsa a hankali ta d'aga kai tana duban sa, ido d'aya Mukhtar ya kanne mata yace " ''yan mata ya akayi ne?


Murmushi tayi had'i da yin wani farrr da ido sannan tace " yanzu duk irin soyayyar nan da mukeyi amma bazaka aure ne ba? "Inji wa yace bazan aure ki ba? "gani nayi da ido na ai ba sai an fad'a min Teemah zaka aura ba, "what Mukhtar yace had'i da mik'ewa zaune yana kallanta yace " God forbid na aure ni wallahi ko mata sun k'are a duniya ni kuwa mezanyi da ita, wanne dare ne jemage bai gani ba, tun Teemah tana 14yrs nake kusantarta, haba ke ko abinci ne ai yaci ace ka gaji dashi haka, nayi amfani da ita ne dan cikar burina, dan ni babu abinda bazan iya akan kud'i ba, ke ni in tak'aice miki magana idan ta kama ma na kashe Teemah to tabbas zan kawar da ita daga doran duniya abu mai sauk'in ne na tsinke mata numfashin ta matuk'ar naga zata bani ciwon kai, " a firgice budurwar ta d'ago tana kallan Mukhtar tace " kai my dear yanzu zaka iya kashe Teemah?


Murmushi yayi irin nasu na cikakkun 'yan bariki sannan yace "ke nifa tunda nake a duniya ban tab'a ganin mace irin Teemah, shegiya mahaukaciya kawai ita in banda bata da cikekken hankali yama za'ayi tayi tunanin zan aure ta bayan naga irin abinda tayiwa Zaid ni karan hauka ne ya cije ni zan aure ta, ni ma idan ta samu wani wanda tafi sanshi akayi na abu mafi sauk'i ne tayi min irin abinda tayiwa tsohon mijinta.


"To yanzu meye target d'inka akanta? shiru Mukhtar ya d'anyi sannan ya kalli busurwar yace " kinga dai har yanzu ban bata kasonta ba, ina lallab'a ne dan mu rabu lafiya kin san fa halin karuwai, idan ta gane mai nake nufi da ita komai yana iya faruwa, dan haka nake son tsara komai a hankali, ta yadda bazata tab'a fahimtar komai ba, wani mahaukacin kuka Teemah ta saki had'i da buga wayar da bango aiko take wayar ta tarwatse, durk'ushewa tayi a wajen tana wani irin mahaukacin kuka mai cin rai, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e ta shiga bathroom ta watsa ruwa, ta canja kaya, ta zube a gado ta fara tunanin neman mafita, dan yau Teemah ko parlor bata fito ba balle tabi takan abinci.


Takai 3hrs tana tunanin ta inda zata b'ullowa Mukhtar inda daga k'arshe tunaninta ya tsaya akan ta nemi ABRAHAM, batare da sake tunanin komai ko wani kokonto ba ta mik'e ta nufi parlor inda Mukhtar ke zaune, a zaune ta iske shi a gaban system, k'ok'arin saita kanta ta fara yi kafin ta isa inda yake fuskarta a sake, a hankali ta rungumo shi ta baya ta d'ora hab'arta akan kafad'arsa ta shiga hura masa iska a kunne tana yi masa wani irin salo mai wuyar basarwa, a hankali yasa hannuwansa ya juyo da ita, a d'an firgice ya zaro idonsa waje yace " my life ya haka kuka kikayi meya sameki? Murmushi tayi masa had'i da d'an yamutsa fuska tace " kai na ne kemin mugun ciwo, amma karka damu nasha magani ma, mik'ewa yayi tsaye da ita a hannunsa ya koma kan sofa 3 sitter ya zauna yana kallan cikin kwayar idonta yayinda wutar k'aunarta yake sake roruwa a zuciyar sa, take yaji zai iyayin komai akan Teemah zai kuma rabuwa da kowa akanta, babu koma abinda bazai iya yi ba matuk'ar zai sanya ta cikin farin ciki da kwanciyar hankali.


A hankali ya had'e bakin su ya fara tsotsar bakin ta cikin kwarewa, bakinsa ya zame daga cikin nata yace " dear ince dai bani na saka miki ciwon kan ba ko? murmushi tayi masa batare data ce komai ba, ganin duk ya rikice mata yasa ta mik'ewa da sauri ya k'ara mai da ita jikinsa ya cigaba da rod'a mata jiki, tasan idan ta tsaya bazai tab'a kyale taba sai yayi koda damba ne yasa cewa " please my heart ka kyale ni wallahi bana jin dad'i yau, yanzu ma aran wayarka nazo ka bani in kira layi na, na rasa inda waya ta ta fad'a na nema harma gaji, rinannun idanunsa ya d'ago ya kalle wanda dama idan jarabarsa ta tashi haka yake komawa in few minutes, murya can k'asan mak'ogwaro yace " please ki taimake ni my life wallahi nakai mak'ura wajen buk'atar ki, kin san daga wajen ki ne kad'ai nake samun nutsuwa, ke ce duniya ta, ina sanki fiye da kowa da komai aduniyar nan ta mu, wallahi zan iya yin komai matuk'ar zai saki farin ciki, ido kawai ta k'ura masa a ranta kuma tana jinjina girman munafurci irin na d'a namiji, kai maza munafukai ne duk zaman da zakayi dasu baka isa ka gane inda suka dosa ba, sai dai muyi ta addu'a.


Ganin ta k'ura masa ido kuma da gani zancen zuci take yasa shi hura mata iskar bakinsa a fuska yace " ko ba ki yarda bane ki gwada yanzu ki gani, murmushi yak'e tayi masa, sannan tace "ya za'ayi nak'i yarda bayan na gani da ido na ni ganau ce ba jiyau ba, ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa tsaye, yasa hannuwansa ya sake maida ita jikinsa ya rungume ta tsam a jikinsa yana mai da numfashi sama-sama.


Fuska ta b'ata tace " nace maka fa bani da lafiya kuma ai sai da lafiya ake komai ko? kayi hak'uri man na d'an wani lokaci na ji sauk'i mana, ido ya k'ura mata yana aiyana wani abu a ransa sai kuma yace " ok badamuwa, ya sake ta da sauri ta mik'e had'i da d'aukar wayarsa dake kan center table, tana shiga bedroom d'inta ta danne key sannan ta zauna a bakin gado ta shiga neman number Abraham tana yin searching taga number hannunta na rawa da d'auki number tayi serving sannan tayi delete number daga wayarsa sannan ta mik'e ta mayar mishi da wayar bata ko kalli inda yake ba ta dawo bedroom ta shirya tayi ficewarta.


Sai da ta samu wani k'ayataccen garden ta zauna ta nutsu sannan tayi dialing number Abraham, su Abraham na zaune suna tsara next target d'in su, su basu tab'a tunanin Teemah zata nemi Abraham ba, wayar sa ta fara ringing, ido ya k'urawa number na d'an wani lokaci sannan ya kalli Zaid da Lubnah da su Idris yace " bak'uwar number da sauri Zaid ya zaro ido yana kallo wayar, ya kalli Abraham yace " pick it, wayar na gaf da tsinkewa ya d'auka Teemah najin anyi picking ta d'auke ajiyar zuciya had'i da

Please Login or Register in order to submit comment