Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu.
, ya shiga d'aki, da sallar asuba ma shiya tashe mu tare muka tafi masallaci, amma hukuncin Ubangiji yafi k'arfin wasa, da misalin k'arfe 7:00am najiyo kukan Maman mu tana kiran mu, da gudu muka fito muka iske ta a tsakar gida.


Sosai Mama take kuka ta kasa magana da hannu take nuna mana d'akin Baban mu dukkan mu muka shiga da gudu har Ramlat, Allahu Akbar rai yayi halinsa su Baba an riga mu tafiya gidan gaskiya.


Sosai mutuwar mahaifin mu ta girgiza mu, haka muna ji muna gani akayi masa wanka aka kaishi gidan shi na gaskiya, duk wanda yaga Umar yasan yashiga mugun taahin hankali wanda daga k'arshe mu muka dawo muna lallashin shi, sosai mutuwar Baba ta shigi Umar, gaba d'ayan mu jikin mu yayi mugun yin sanyi, kasancewar Abdul karatu yake bashi da wata sana'a,nauyin gidan gaba d'aya ya koma hannun Umar, kusan komai shi yake yi a gidan, har nauyin karatu na shiya d'auka yake yi.



Kwanci tashi babu wuya awajen Allah har Baba yakai wata biyar da rasuwa Mama ta fita daga takaba, cikin ikon Allah kud'in Baba ya fito dayake bamu da 'yan uba, shiyasa ba'ayi maganar rabaon gado ba, d'akin Baba aka fasa ta waje aka bud'e babban shago (shop) sosai muke ciniki dan duk unguwar babu shago kamar kamarsa, dan haka nauyi yabar kan Umar.

Sosai na maida hankali na kan karatu na yayin da soyayya ta da Yasmeen ke k'ara zurfi, sosai rayuwa ta canja mana saboda har yanzu mutuwar Baba bata gama sakin mu ba, duk da kasancewar mun yarda da k'addara, mun karb'eta da hannu biyu.


Haka dai rayuwa tayi ta tafiya yayinda ta ko wanne fanni aka damu mahaifiyarmu da kawo k'arar Umar sosai fiyye da da, wasu ma har cewa sukayi yana shaye-shaye da bin 'yan daba daga k'arshema aka ce yana fashi da makami sosai abin yake bani dariya a duk sanda aka danganta Umar da wad'an nan halaye, a fannin Mamanmu kuma sosai abin ya fara damunta, yayinda Umar ke kuka sosai kamar ransa zai fita.
, a d'aki na samu Umar yana ta faman kuka, a hankali na durk'usa a gabansa na shiga lallashin sa, amma ina na kasa, tashi nayi naje na kira Maman mu, itama jikinta a sanyaye ta shigo d'akin, a gabansa ta zauna ta jawo shi jikinta ta rungume itama ta shiga kukan.


Cikin kuka Umar yace " Mama kodan anga ni ba d'anku bane ansan bani da kowa sai ku shiyasa ake min, sharria .
sannan idan yau kuka ce kun barni na shiga uku, Ina zan saka kaina bani da wasu dangi ko iyaye da suka wuce ku, ban san kowa ba sai ku, a hannunku na girma kunfi kowa sanin halina ku zaku gayawa duniya waye Umar d'inku.
, dan Allah Mama karku bari maganganun mutane suyi tasiri a zucikataku , harku watsar dani, Mama karki fushi dani dan fushin uwa ba k'aramin masifa bace ga rayuwar d'a ba, dan Allah Mama karku yarda wallahi Allah sharri suke yi min, ga Abdul nan duk inda zamu tare muke zuwa yafi kowa sani na da hali Na .


Cikin kuka Mama ta k'ara rungume Umar ajikinta tace " kaima kamar Abdul kake a waje na,umar daga yau karna k'ara jin kace baka da iyaye ko dangi balle harka k'ara cewa baka da dangi, mu mune komai naka a rayuwa, kana da iyaye dan mune iyayenka kana da dangi dan dangi mu sune naka, kana da 'yan uwa dan Abdul, Ramlat, Ja'afar sune 'yan uwanka.


Rungume Mama ya k'arayi sosai yana kuka yace " nagode Mamana nagode sosai Allah yabar zumunci Allah ya bani ikon saka muku da mafi girman alkhairi, dafa shi Abdul yayi ta baya yace" tsakanin mu ba godiya, mun riga mun zama tsintsiya mad'aurinmu d'aya.
, gabadaya sukayi dariya had'i da rungume junansu cikin farin ciki da k'aunar junan su.


Amma sai me?


Washe gari da safe tun 8:00am na shirya domin ina da lactures, bamu fito ba sai 6:20pm a matuk'ar gajiye muke lik'is, ga yunwa ga ba mota, ganin karna b'atawa kai na lokaci yasani yankar hanya nabi ta gefen gari, kasancewar yamma tayi sosai ina fara tafiya magrib tayi, ga tsakanin gidan mu da makaranta akwai Dan tazara sosai, nasan kafin na k'arasa anyi isha'i, ina cikin tafiya duhun dare ya farayi, me zan gani a gaba, cikin firgici na zaro ido na, tabbas ido na ba k'arya yake min ba, abinda nagani gaske ne ba karya ba .
Take ban san sanda kwalla ta fara zubarmin ba, dan in tabbatar na matsa kusa dasu sosai, daga gefe na d'an rakub'e ta yadda zan rik'a jiyo maganar su.



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*



6



Umar na gani tsakiyar rik'ak'un 'yan daba suna ta shaye-shaye shi Umar hannunsa ma rik'e da kwalbar giya, wani daga cikin su naga ya kalli Umar yace " Oga, a fili na maimaita Oga, a raina nace yanzu ashe iskancin Umar da ake fad'a da gaske har ya wuce tunanin mutane, yanzu Umar d'in mu ma shine Oga? nayi kaina tambayar.


Ina cikin tunanin naji wanda yace Oga yaci gaba da magana " Oga kaga gidan Alhajin Sama da mukaje fashi sun samu ta sosai, shege mutumin nan kullum yana kukan babu ashe k'arya yake, mak'udan kud'i ne jibge a gidan sa, wata mahaukaciyar dariya Umar yayi irinta mashaya yace " yo ai irinsu suna da yawa ka manta sanda muka tare hanyar kano, nawa muka samo?


Wani daga cikin su yace " ai Oga munyi fashi da yawa wanda mu kanmu bazamu iya lissafa su ba, ni bama zan iya tuna wanda kake maganar ba, dariya Umar ya k'arayi yace " aikai k'aramar kwanya gare ka, shiyasa baka saurin gane abubuwa, ni na rasa ma yadda ka dad'e kana shaye-shaye amma ba hau bola ba, gaba d'ayan su suka tuntsure da dariya irin ta mashaya.


" Oga wai ni 'yan idan ku har yanzu basu farga dakai bane?

Dariya Umar yayi yace " an fad'a maka kowa ma sakarai ne irinka, aini duk abinda zanyi da tunani nake yinsa, kuma kaga tun muna Jss 2 da Abdul na fara shaye-shaye da haura gatangar mutane ba, d'ayan yace " da lab'e a lungu ana latsawa mata nono, dariya Umar ya k'arayi yace " shege ashe ba manta ba.


"Ah haba Oga yaza'ayi na manta, ni wallahi abin ma har mamaki yake bani, wai ku kwana ku tashi da Abdul amma bai tab'a gane munanan halayenka ba, dariya Umar yayi yace " kuma wani lokacin har a gidan nake cakewa ta ba, saboda fa na samu damar fashi da makami nak'i yin jami'a, dan nafi samun sakewa, " hmmmmm gaskiya Oga kai shege ne gaka marar imani, wallahi ban tab'a ganin mutum marar imani irin ka ba, to wai ita Ramlat da gaske kana santa, kuma tsakanin ka da Allah aurenta zakayi?idan ba aurenta zakayi ba muma ka bamu mud'an tab'......


Wata muguwar shak'a Umar yayiwa yaran ya hau dokan sa tako ina yana dukan nasa yace " idan ina shirmen mu karka k'ara sako min ahalina, dangina ko 'yan uwana bana kisa amma akan su zan iya kashe mutum har lahira saboda sune ni, kuma koda wasa idan na k'ara jin sunan Ramlat a bakin ka wallahi saina gorje maka shi, saboda ita rayuwata ce itace duniya duk abinda kaga inayi dan ita nakeyi, wallahi akan Ramlat zan iyayin komai cikin kuwa harda salwantar da rayuwata akan Ramlat bank'i kowa ya mutu ba, ita nake so, itace Uwa ta kuma itace Uba na, ban d'au kowa nawa ba sai ita ina mata mahaucin so, duk wanda yanemi rabani da ita to tamkar ya d'aukowa kansa hitila ne, yana kaiwa nan yayi jifa da yaran yana huci kamar Lion, yace ita ba irin sauran matan banza da muke bi bace, ita sarauniya tace.


Abdul dake lab'e a ransa yace " wallahi ko Ramlat zata mutu ba aure bazan tab'a bari ta auri Umar ba, ya fito daga inda yake lab'e yayi gida, ba k'aramin tashin hankali Abdul yashiga saboda munanan aiyunkan dayaji d'an uwansa Umar na aikatawa, yana komawa gida direct dakin su ya wuce ya rufe kansa a d'aki ya saki kuka ya manta da yunwar da yake ji balle gajiya, a fili yake magana cikin kuka " Umar ka ha'ince mu ka cuce mu, Allah ya sani ba irin tarbiyyar da iyayen mu suka bamu ba kenan, duk munayan halaye ka had'a ZINA, FASHI, SHAYE-SHAYE, MUNAFURCI, YAUDARA, K'ARYA, ka yaudare mu, sannan kaci amanar mu, kai mak'aryaci ne, a haka zan d'auki tilon k'anwata in baka, daga bakin k'ofar d'akin Mama ta tsaya tana sauraron Abdul.


Duk maganar da Abdul yakeyi cikin kuka Mama najinsa, a hankali cikin rawar murya tace " Abdullahi bud'e k'ofar, ba musu ya tashi ya bud'e mata k'ofa, ta shigo tana shigowa ta k'ura masa ido sai kuma ya kuma fashewa da kuka, ya rungumeta a hankali Mama ta zaunar dashi, ta d'ago kansa tace " fad'a min meye faru?

Bai b'oyewa Mama komai Ramlat dake lab'e jikin window ta saka kuka, a hankali Abdul ya mik'e yaje har inda take ya rik'o ta zaunar kusa da Mama ya kuma kwashe komai ya fad'a musu bai rage komai ba, daga Mama har Ramlat kuka suke sosai, haka ma Abdul, saboda ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba, sosai abin ya girgiza su, cikin kuka Mama tace " iya yarda mun yarda da Umar mun bashi amana, koda ake zuwa ake yawo k'arar sa bamu tab'a yarda ba, haka mahaifinku ma har ya rasu bai yarda a aiyukan da ake danganta Umar dashi ba, mai yasa Umar zaiyi mana haka mai muka rage shi arayuwarsa ko so yake yaja mana zagin da zargin duniya.


Ta k'ara fashewa da kuka, "Allah ya sani irin rik'o da tarbiyyar danayi muku ita nayiwa Umar koda wasa ban tab'a banbanta tsakanin ku ba, amma mai yasa zi zab'i irin wannan mummunar rayuwar, a hankali Ramlat ta shiga gogewa mahaifiyyar su hawaye, Abdul ya kalli Ramlat yace " wannan rayuwar ki ce zab'i ya rage nake ko kiwa kanki gata ko sab'anin haka, ki tuna yau idan ni da Mama muna raye gobe bama nan, kiyi k'ok'ari ki zab'awa yaranki uba na gari, ni dai gaskiya Ramlat ban amince ki auri Umar ba, kwari ki samu wani can ki aura, koda zan rasa rayuwata bazan tab'a yarda ki auri d'an fashi, mazina, d'an shaye-shaye ba, bazan tab'a bari ki lalata rayuwarki ba.


Rungume Abdul tayi cikin kuka tace " wallahi Yaya koda maza sun k'are bazan tab'a auren Umar ba, bana sanshi na tsane shi, Umar mugune, Yaya nayi maka alk'awarin bazan tab'a auren Umar ba koda kuwa baka raye, sosai ya rungumeta, Mama najin su ta kasa koda furta kalma d'aya.


Ana haka Umar ya shigo d'auke da sallama a bakin sa hannunsa rik'e da carbi, ya shiga d'akin yarda ya gansu babu kuma wanda ya amsa masa sallama, da wani irin kallo da Abdul ke jefa masa ne yasashi shan jinin jikinsa, yakai dubansa ga Mama yaga ta k'ura masa ido tana zubar hawaye kamar mai san gano wani abu, ya kalli Ramlat yaga ta duk'ar da kanta k'asa ita kukan take, a bakin k'ofar d'akin ya tsaya ya kasa shiga, duk ya tsargu yasha jinin jikinsa, cikin rawar murya Mama tace " zo ka samu guri ka zauna muyi magana, sosai jikinsa ya k'ara mutuwa, cikin rashin kwarin jiki ya koma can gefe ya zauna.


Mama ta kalli Abdul tace " maimaita abinda ka fad'a min yanzu, tas Abdul ya k'ara kwashe komai ya kuma fad'a, dammmmmm!!!! gaban Umar yayi muguwar fad'uwa, ba k'aramar tsorata yayi ya shiga mummunan tashin hankali babu abinda gabansa yayi sai dukan uku uku, a firgice a kuma razane yake sauraron Abdul harya gama jawabinsa, a zuciyar sa yace " tab yaufa ruwa ya k'arewa d'an kada, amma dayake d'an duniya ne sai kawai ya fashe da kuka kamar ransa zai fita.


" Mama Abdul dan girman Allah kuyi hakuri, wallahi nima ba'a san raina na tsinci kai na da kuma rayuwar danake ciki ba, nasan banyiwa kai na daku adalci ba, Mama nasan na watsar da tarin kuma ingantacciyar tarbiyyar da kika bani, da rarrafe ya rarrafo gabanta ya dafa k'afafuwanta yana kuka yace " wallahi Mama kunyar had'a ido nakeyi daku, naci amanar ku, na yaudare ku, na cuci kai na, wallahi duk hukuncin da kuka yanke a kaina zan karb'e shi hannu bibbiyu, dan Allah Mama kiyi hak'uri ki yafe mana, nayi alk'awari zan daina duk munanan halaye na zan zama mutumin kirki kamar yadda kike so wallahi Mama, ya juya wajen Abdul yace" please kayi hak'uri wallahi damuwa da bak'in ciki ne ya jefa ni wannan mummunar rayuwar amma in sha Allah na daina.


Cikin kuka Mama tace " wacce irin damuwa da bak'in ciki ne wannan da har zaka salwantar da tarbiyyar dana Baja, wacce irin damuwa ce dabazaka zameni a matsayin mahaifiyar ka ka fad'a min ba, wanne irin bak'in ciki ne da bazaka iya samun d'an uwanka kuma amininka ka fad'a masa ba.


Umar ka bani mamaki, kasa na kasa ganin kaina a matsayin cikekkiyar uwa, wacce zata iya amsa sunanta uwa a ko'ina a gaban kowaye, kasa na raina tarbiyyar dana baku, kasa naga gazawata, Umar na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kai na da kuma 'yan uwanka, haba Umar mai yasa haka? ta fad'a tana matsanancin kuka, gaba d'ayan su kukan suke Abdul ya kalle shi yace " kaji dad'i kasa mahaifiyar ka, da 'yan uwanka wallahi Umar inda ba da ido na naganka ba, na kuma ji da kunne ba dako kashe ni za'ayi bazan tab'a yarda ba, idan ko wani ne ya tare ni ya fad'an wallahi sai inda k'arfi na ya k'are, cikin kuka Umar ya mik'e yace " shikenan tunda ba wanda zai karb'i uzurina, zan fita daga rayuwarku, zan koma can gefe naci gaba da rayuwa bana san na zame muku matsala, amma duk inda zani ku sani zuciyar Umar na tare daku, har abada zaici gaba da amsa sunan d'an ku kuma d'an uwanku, Umar na kune kuma yana k'aunar ku, ya mik'e zai fita wani wawan mari yaji an sauke masa har hud'u.



Mama ta k'ara d'aga hannu zata sake marinsa yayi saurin rik'e hannunta yace " Mama karki ji ciwo, idan zaki dage ni madoki ya kamata ki samu, wallahi Mama ki ko kashe ni zakiyi bazan tab'a yi miki musu ba, ya fita ya samu icca ya mik'a mata yace " mama ki dake ni idan hakan ne zai sama miki sauk'i a zuciyar ki, ki dake ni Mama ya k'arasa maganar yana kuka ya rik'o hannunta, yarda iccan tayi ta rungume shi tana kuma.


" mai yasa kake tunanin barin mu, ashe zaka iya barin mu, zaka iyayin rayuwa cikin farin ciki ba tare damu ba?

"A'a Mama zan yi nesa daku ne zan samawa zuciyar ku sauk'i, amma wallahi nasan bani da sauran jin dad'i idan bana tare daku, "daga yau kome zai faru karka k'ara k'ok'arin barin mu, mu naka ne kai namu ne har abada.


Dariya yayi yana hawaye yace " in sha Allah Mama, ta baya ya mik'awa Abdul hannu ya kauda kai, kallon Mama Umar yayi yace " Abdul har yanzu bai huce ba, fushi yake dani, Mama ta kama hannunshi takai shi har gaban Abdul, Umar na zuwa ya rungume Abdul yana kuka yace " kayi hak'uri d'an uwana, in sha nadai na, sosai Abdul ya rumgume shi yace " laifinka d'aya ne na barin mu da kake k'ok'arin yi, laifin barin mu har yafi wanda ya aikata.


Gaba d'aya sukayi dariya amma banda Ramlat wacce a lokaci d'aya taji ta tsani Umar bata ko k'aunar ganin shi, tana yi masa kallon wani Monster ne, ya lura da yanayin Ramlat dan haka ya mik'e ya nufi inda take zaune ya durk'usa a gabanta, yace " please kiyi hak'uri ban kumawa, ko kallansa batayi ba tace " kama kuma mana ni ina ruwa na.


Wata muguwar fad'uwar fad'uwa gaban Umar yayi dan ba k'aramin so yake yiwa Ramlat ba, dan shi gani yake kamar itace rayuwarsa, akanta yana iyayin komai, " please kiyi hak'uri ma..... bata bari ya k'arasa ba ta d'aga masa hannu tace" please ka rabu dani, ka fita harka ta da rayuwa ta please, dariya yayi dan shi a tunaninsa b'acin rai ne yasa ta haka yace " bakomai idan kin huce mayi magana, " na huce me?

"Aini na gama magana wallahi Allah ko maza sun k'are bazan tab'a auren ka ba Umar, wallahi koda kuwa zan mutu ba aure, wallahi dana yi rayuwa dakai a matsayin miji gwamma na mutu, wata k'ara Umar ya saki ya mik'e ya dafe kansa da duka hannunsa biyu, ya nufi Abdul, wanda shi hakan da Ramlat tayi bak'aramin dad'i yayi masa ba, ransa yake godewa Allah a haukace Umar ya kalli Abdul yace " kaji me take cewa?

Murmushi Abdul yayi yace " naji kuma hakan ya faranta min rai, wallahi nima koda zan rasa raina bazan tab'a bari Ramlat ta auri d'an fashi ba, hakan ma zai fiye mana kwanciyar hankali kowa ya fita waje ya nema yayi auren sa kawai.



Zumbur Umar ya mik'e ya saki wata mahaukaciyar dariya yace "...........



*MOMYN ZARAH*
[21/01, 04:11] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_


~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*



Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```




~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*


7


" wallahi k'arya kikeyi kina sons kamar yadda nake san ki, bazaki iya rayuwa ba ni, Ramlat ta bud'e baki zatayi magana, Abdul ya mik'e ya dafa kafad'afar Umar yace " kayi hak'uri kaje waje ka nemo mata, itama taje waje ta nemo miji, Mama ta kalli Abdul tace " me yasa, cikin fushi yace " haba Mama kina jin halinsa fa , wallahi wallahi Allah bazan tab'a yarda Ramlat ta auri Umar ba, koda zan kuwa zan rasa rai na.


Murmushi Ramlat tayi tace " nagode Yayana ina alfahari dakai nagodewa Allah daya bani kai a matsayin wa, murmushi Mama tayi tace "Allah ya shige mana gaba ya zaba mana mafi alkhairi, gaba dayan su suka ce "Amin.


A gaban Mama Umar ya durk'usa yace " nayi alk'awari akan duk hukuncin da kuka yanke akaina zan kasance mai yi muku biyayya, kuma inshallahu zanyi bibiyya agareku km zan nesanta kai na da Ramlat zan koma mata ainahin wa, zan kuma kasance mai kare mata mutuncinta a ko ina.


Tun daga ranar Umar ya koma mutun kirki sannan mutum kwarai baya tab'a sakewa ya rabu da Abdul, haka zalika kuma aka daina kawo k'arar sa, kowa ya koma yabansa, idan har ba masallaci ba babu abinda yake fitar dashi daga gidan idan Abdul baya nan, haka kuma a b'angaren Ramlat bai kuma nufarta da wata maganar soyayya kota aure ta ba, ya d'auke ta ne a matsayin k'anwarshi, yanzu babu wata alak'a a tsakanin su, yayinda Abdul da Yasmeen suke cigaba soyayyar su.


Gida ya zamana basu da wata matsala a rayuwar su, a na cikin haka wani saurayi ya fitowa Ramlat, Umar yaje ya samu ya gabatar da buk'atar sa, Umar da kanshi ya kawo shi wajen Mama da Abdul duk sun yaba da saurayin, haka ma a b'angaren Ramlat, cikin k'ank'anin lokaci soyayya mai k'arfi tashiga tsakaninsu, dan haka su Abdul suka nemi yaron ya turo iyayensa, ba'a wani b'ata lokaci ba aka saka rana.


Ranar asabar Ramlat ta tashi da mummunan labarin mutuwar saurayinta sakamakon had'arin mota, sosai mutuwar ta shege ta, duk dangi da 'yan uwa sun tausaya mata, sosai jikinta yayi mugun sanyi, Umar ne yake lallashinta had'i da kwantar mata da hankali.


Bayan wata d'aya wani abokin Abdul da suke karatu a jami'a yazo gidan yaga Ramlat,din take ya tsinci kansa da fad'awa tarkon sonta, aiko sosai Abdul da Mama suka ji dad'i, haka ma Umar dan a cewarsa idan Ramlat tayi aure shima zaifi yi, sosai suka fad'a soyayya da idris, shima ba'a wani b'ata lokaci ba aka saka rana, hankali kwance suke gudanar da soyayyar su.


K'addara ta rigayi fata, da sassafe aka kira Abdul ake shaida masa mutuwar, Idris sakamakon matsanancin ciwon cikin dayayi fama dashi jiya da dare, sosai hankalin Ramlat yayi masifar tashi, ta razana sosai, saboda a daren jiyan har 10:00 suna tare, wannan karan kowa ya tausaya mata musamman ma Umar.


Tun daga kan Idris Ramlat tace bazata k'arayin soyayya ba, ta hak'ura ta maida hankalinta gaba daya kan karatun ta dan yanzu ta shiga SS 3,ana cikin wannan yanayin ne wani Malamin su ya takura mata da maganar aure, harta ya gabatar da kansa a gaban iyayenta, fafur Ramlat tak'i yarda acewarta kar shima ya mutu a camfa ta.


Sosai 'yan gidan su suka tausaya mata, an d'auki lokaci sosai kafin Malam ya shawo kan Ramlat dakyar da taimakon Yasmeen, sama-sama take kula shi, saboda gaba d'aya a tsorace take, cikin ikon Allah Malam ya gabatar da iyayen sa, had'i da neman alfarmar ayi auren kafin tayi Candy ta k'arasa a gidansa, babu musu su Abdul suka amince, ba'a saka lokaci mai tsayi ba, aka fara shirye-shiryen biki.


Ana saura sati d'aya biki aka tashi da mutuwar Malam, mutuwar data gigita hankulan jama'a, sosai hankalin su Abdul yayi masifar tashi,fad'ar tashin hankalin da Ramlat ta shiga ma b'ata lokaci ne, dan tayi masifar girgiza da razana, sosai ta firgita, ta zaman wata sukuku kamar marar hankali, ba taci bata sha, lokaci d'aya ta rame sosai, ta maida kanta zaman d'aki, koyaushe rana d'aki tana faman aikin kuka, sosai su Abdul suka tausaya mata, musamman Umar, dashi kusan koyaushe yana tare da ita yana lallashinta, da bata hak'uri had'i da nuna mata yarda da k'addara.


BAYAN WANI LOKACI



Bayan hakula sun d'an lafa komai ya fara zama normal, amma har a lokacin Ramlat tana cikin damuwa dan kallo d'aya zakayi mata kasan hakan, Abdul na d'aki Mama ta shigo ta samu guri ta zauna, daina abinda yakeyi yayi ya maida gaba d'aya hankalinsa kanta, Mama tace " Abdul shawara ce nake san muyi akan yaran nan, " cikin ladabi Abdul yace " to Mama akan me kennan?


Umar dake shigowa ya tsaya cak yana sauraran su,da km abinda zasu tautauna akai Mama ta numfasa kana tace " kaga yadda Allah ya nuna lamarinsa da ikonsa akan Ramlat ko, duk wanda ya fito da sunan neman aurenta sai rabo ya kashe shi, cikin rashin fahimta Abdul yace " rabo kuma Mama rabon me?


Murmushi tayi irin Nasu Na manya sannan tace " zai iyayuwa rabon a tsakanin su yake, duba da yadda duk wanda ya fito sai ya mutu, ina Allah ya riga ya tsara Ramlat matar Umar ce, Allah yayi shine mijinta, kasan wani baya auren matar wani haka kuma wani baya haihuwar d'an wani, dan haka nake ganin karmu matsa dayawa kawai mu barsu suyi aure tare da binsu da fatan alkhari .


Shiru Abdul yayi na wani lokaci yana tunani da saka da warwara akan zance mahaifiyarsa kafin Daga bisani can ya nisa yana sauke naunauyen ajiyar zuciya yace " gaskiya Mama indai ina raye bazan tab'a bari Umar ya auri Ramlat ba, sai dai idan nima rabon ya kashe ni, idan na mutu sai suyi auren su, Mama ya za'ayi muna ganin kashi da rana mu taka, duk da Umar ya kasance dolen mu ne, amma gaskiya bazan iya bari Ramlat ta

Please Login or Register in order to submit comment