Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin wannan tarbiyyar na baka ba.


Dariya yayi yace " da kinji nace ki yafe min ne, Hajiya tace" kaci amanar mu Hamza, ka yaudare mu, ka munafurce mu, kai mugu ne mai fuska biyu mai mugun nufi a zuciyarsa, azzalumi, in sha Allahu amanar mu daka ci bata ta tab'a barinka ka rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba.
"kuma alfarmar Ubangiji ko Khamal yana raye ko baya raye baza ka tab'a mallakar Fateeha ba, matuk'ar ina raye in sha Allah bazan tab'a bari Fateeha ta zama matarka ba.


A zuciye Hamza yayo kanta ya shak'e mata wuya yana gurnani yace" aiko lalle zaki mutu, kinyi ganganci Hajiya, dan duk wanda ya nemi yimin katanga wajen cikar buri na, to zan kawar dashi, daga doron k'asa batare da shakka ko tsoro ba.
Hajiya ta shiga haure-haure da shure-shure tana kokuwa da Hamza amma ina, bai sake ta ba sai da yaga ta daina motsi da numfashi alamar rai ya fita.


Gaba d'aya Idonta duk sun firfito waje,sunyi tulu tulu alamun shan wahala numfashin ta ya d'auke, ya wurgar da ita gefe, ya tsugunna a gabanta yana dariyar mugunta yace " sai ki hana ni mallakarta, shima yana hanyar biyo ki, gawarta ya d'auka yakai kan gadonta ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya lullub'e ta kamar mai bacci, shi kuma ya nufi d'akisa ya kwanta yana tunanin abinyi.


Cikin 2hrs labarin Khamal ya bazu a ko'ina a cikin kasashen duniya duk tashar daka kunna zancen akeyi, Aljazira, BBC, CNN, da sauran tashoshi, aiko nan da nan labarin ya cika Nigeria, Dadyn Fateeha na zaune a falo Abba ya kira shi yace " su kunna BBC ba musu Dady ya sauko falon k'asa inda Fateeha da Momy ke zaune suna hira, a hankali ya d'auki remote ya kunna TV, aiko pic d'in Khamal ya bayyana a jikin plasma, da sauri Fateeha ta mik'e tsaye jikinta na rawa ganin an rubuta Breaking news, (Nigerian baller he is an criminal ) live aka shiga nuna sanda aka kama koken a kayansa, har zuwa inda aka kai shi prison, wata mahaukaciyar k'ara Fateeha tasa ta zube a k'asa sumammiya.
cikin firgici Dady da Momy suka yi kanta, da gudu Momy ta d'auko ruwa tashiga zuba amma babu alamar motsi, aiko da sauri Dady ya sungume ta yayi mota, da gudu Momy tabi bayansu, suna shiga hospital direct emergency aka wuce da ita, Doctors sun kai 5 a kanta amma a banza, sai da Fateeha tayi 10hrs a hospital sannan ta farfad'o tana ihu, da sauri Momy da Dady sukayi kanta cikin kuka tace " wallahi Momy he is not criminal, k'arya suke yi masa sharri ne, nasan halinsa, bazai taba aika haka ba. .....ta fashe da wani irin mahaukacin kuka Momy ki taimake ni wlh sherri aka masa nasan Khamal d'ina bazai taba aikata mugun aiki irin wanna ba.
shafa kanta Momy ta shiga yi, tana rarrashinta, rungume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya, kusa da ita Dady ya zauna cikin sanyin jiki, jajayen idonta ta d'ago tana kallonsa tace" ka gani ko Dady?
Kaga abinda kaja ko, a sanadinka Khamal zai rasa rayuwarsa, mai yasa Dady, ta k'ara fashewa da wani sabon kuka, hawayen masu zafi ke tsiyayo mata.

Jikin Dady a matuk'ar sanyaye ya jawo ta jikinsa ya rungumeta yace " kiyi hak'uri Mama na, ba laifi na bane k'addararsa ce haka, in sha Allah zai fito, cikin kuka tace" Dady kana ji fa, sunce kashe shi zasuyi, " karki damu Mama na in sha Allah I will try my best, kinji, Momy dake zaune a gefe tana kallonsu hawayen tausayin tilon 'yarta na zubo mata.

Umman Ja'afar ko tunda taji abinda ya faru hankalinta yak'i kwanciya dan har ga Allah su Abba Ja'afar take zargi,
cikin tashin hankali ta nufi d'akin Abba tana kai kanta zata shiga tajiyo hirar Abba da Ja'afar, cikin sanyin jiki Abba yace " gaskiya na tausayawa yaron nan dan nasan bazai iya aikata irin wannan laifin ba, shima Ja'afar cikin sanyin jikin yace " nima bana tunanin zai iya aikata haka, dan gaskiya yaron yana da hankali da nutsuwa ina ganin dai ya had'u ne kawai da sharrin mak'iya, Abba yace " to sai dai mu taya shi da addu'a, Umma dake tsaye ta juya cikin mutuwar jiki.


Washe gari tunda sassafe Hamza ya fito k'ofar gida yana kukan mutuwa yana ihu da kururuwa yana d'ibar k'asa yana zubawa a jikinsa, mutane suka taru fal a kansa, suna tambayar shi lafiya, cikin kuka yace " sakamakon abinda ya samu Khamal zuciyar Hajiya ta buga, harta mutu ma, aiko ' yan unguwa sun girgiza da jin mutuwar Hajiya dan sun san macece mai kyawawan halaye, sunyi kuma masifar tausayawa Hamza dan sun san bashi da kowa sai Khamal da Hajiya gashi kuma duk babu su, bayan anyiwa Hajiya wanka da sutura dakyar aka raba Hamza da gawarta dan bori ya hauyiwa jama'a baza'a fita daita ba yana kuka yana kari .


Kwanan Fateeha d'aya aka sallamo ta daga asibiti, tana dawowa ta shirya ta fita batare data bari kowa ya ganta ba, dan tasan idan aka ganta baza'a bari ta fita a halin da take ciki ba.
direct gidan su Khamal ta wuce, Fateeha na shiga ana k'ok'arin fitowa da gawar Hajiya Hamza nata ihu da birgima, ai Hmaza na ganin Fateeha ya k'ara fashewa da kuka yana birgima, ya tubure, a slow Fateeha ta k'arasa shiga idan,tsayawa kawai Fateeha tayi ta k'urawa Hamza ido.


Ido Hamza ya zuba mata yace " Fateeha bani da kowa yanzu ba Yaya Khamal ga Hajiya ma ta tafi ta barni a dai-dai lokacin dana fi buk'atarta, sai lokacin Fateeha ta fahimci mai ke faruwa, durk'ushewa tayi a wajen ta shiga kuka kamar ranta zai fita, ba k'aramin tashi hankalin Hamza yayi ba ganin Fateeha na kuka, a hankali ya tsaida kukansa ya rarrafa zuwa gabanta, ya shiga lallashinta.


Dakyar Hamza ya shawo kanta tayi shiru, sai bayan magrib Hamza ya maida ita gida, had'i da k'ara bata hak'uri, bayan sati biyu da mutuwar Hajiya Hamza yayi sweeping sim card d'in Khamal, sai da ya dawo gida ya nutsu sannan ya turawa Fateeha text


_Slm, ya kike ya gida hope kina lafiya, please my dear bana san ki sawa ranki damuwar komai, dan nasan zuwa yanzu kin samu labarin k'addarar data fad'a mana, ina mai bak'in cikin sanar dake cewa an yanke min hukuncin kisa, nan da 2weeks please don't feel sad my heart, u know I really love you, please karki damarmin kanki, idan kika bari wani mummunan abu ya sameki akan wannan abunda daya faru, har abada bazan tab'a yafewa kaina ba, zamu rink'a exchanging text har zuwa nan da 2 weeks, amma banda waya saboda akwai risk_


Yana gamawa ya turawa Fateeha,, Fateeha na kwance taji k'arar shigowar text, a hankali ta jawo wayar ta duba, kamar a mafarki taga number Khamal aiko da sauri ta mik'e, a gaggauce ta shiga karanta text d'in, tana gamawa ta fashe da wani iri kuka, jikinta na kirrma ta rubata mishi reply, haka Fateeha da Hamza suka dinga yin exchanging text tsakaninsu a zuwan Khamal ne.


Khamal ko a prison bashi da wani aiki saina kuka, da surutai ya zama kamar wani mahaukaci ko tab'abb'e, yayi bak'i ya rame, ya koma kamar ba shi ba, kullum yana cikin kuka, ranar Friday Khamal na zaune yana ta faman kuka, yaji an dafa shi ta baya a hankali Khamal ya jiyo, wani mutum ya gani wanda a k'alla zai kai 40yrs ba murmushi mutumin yayiwa Khamal yace " ni sunana Ayuba,naga kana ta kuka ne kuma naji kana yin yaren hausa hakan ne ya tabbar min kai d'an Nigeria ne, ko?

Ko sake kallan inda Ayuba yake Khamal baiyi ba, saboda ji yake ya tsani komai da kowa a duniyar nan , Ayuba yayi maganar duniya amma Khamal yak'i amsa masa, dole tasa Ayuba ya hak'ura ya tafi, wajen k'arfe tara na dare Ayuba ya dawo wajen Khamal,dan tunda ya ganshi yaji tausayinsa ya shige shi, ganin sa yayi a dunk'ule a waje d'aya yana ta rawar sanyi, da sauri Ayuba ya k'arasa wajen yana "fadin Subhanallah lafiyar ka kuwa, kana neman kashe kanka a banza,?
Ayuba ya rik'o Khamal da sauri Khamal ya fizge hannunsa yace " malam lafiya? dan Allah ka kyale ni,
"ka rabu dani ka barni da bala'in dayake damuna, murmushi Ayuba yayi yace " Yaro ba'a wulak'anta mutum kaji kodan gaba, dan baka san darajar da Allah yayi masa ba, ka sani ni zan iya fitar dakai daga cikin wannan damuwar dakake ciki.
, ka sani ko hanyar fitarka daga cikin bala'in yana hannun na, bai kamata kayi haka ba, gashi dai da ganinka ka fito ne daga gidan tarbiyya da mutunci da bakayi kama da mutumin banza ba , ka tsaya na taimake ka, ya fad'a yana k'okarin rik'o hannun Khamal a karo na biyu.


Khamal bayyi k'ok'arin hana shi ba, saboda jikinsa daya mutu, Ayuba na tab'a Khamal yace " Subhanallah ai bakama da lafiya, tashi muje hospital d'in dake cikin prison, ya fad'a yana jan hannun Khamal ba tare daya jira amsarsa ba, bayan sunje an gama duba Khamal aka bashi magunguna akayi masa allurai, Ayuba ya wuce dashi yayi wanka ya canja kaya sannan ya matsa mishi ya bashi abinci yaci dakyar dan sai da Ayuba yayi da gaske sannan Khamal yaci abincin yasha maganin.


Tun daga ranar Ayuba da Khamal suka zama abokai sosai, dan Ayuba sananne ne a prison babu wanda bai san shi ba, sosai Ayuba ke d'aukewa Khamal kewa da damuwa dan ya kasance mutum ne me barkwanci da wasa da dariya, sosai suka saba da juna, Khamal da Ayuba zaune bayan Khamal ya gama bashi labarin sa, dan sosai Ayuba ya matsawa Khamal akan sai ya bashi labarinsa, dakyar dai ya shawo kan Khamal ya bashi labarin, sosai Ayuba ya jinjina al'amarin, ya kuma tausayawa Khamal, amma fa Ayuba yayi bala'in tsorata da firgici.
daya ji laifin da akama Khamal dashi dan yasan idan duk duniya gatansa ne sai sun datse mishi kai.


Tsoratar da Ayuba yayi harta fito fili Khamal ya gane, Khamal yace " ya naga duk ka tsorata haka? Yak'e Ayuba yayi yace " bakomai yana k'ok'arin mik'ewa tsaye, murmushi Khamal yayi yana maida Ayuba zaune yace " nasani kashe ni zasu yi, da sauri Ayuba ya d'ago kai kwalla na son zubo mishi, dariya Khamal yayi yace " please karkayi min haka mana, karka karya min zuciya, duk wanda kaga ya mutu kwanansa ne suka k'are, idan idan da rabon shan ruwa a gaba zan sha, kaga ni gaya min naka labarin, Khamal yace dan ya kawar da wancan maganar.


Murmushi Ayuba yayi dan ya gane mai Khamal yake nufi, yace " haifaffen garin Sokoto, zama ne ya kawo ni saudiyya ni da matata da yara na, ' yata wani labarabe ya sace yakai gidan sa sukayi ta cinta shida abokanan sa, harta mutu, sun zo yarda gawar tata ne wani Bahaushe ya gansu, ya d'auki number su, bayan kwanaki aka gane nine mahaifinta aka zo har gida aka sanar dani abinda ke faruwa munyi kuka sosai nida matata, nakai shi k'ara koto to kasan ni mazaunin k'asar ne kawai su kuma cikakkun 'yan k'asa ne, dan haka akak'i yi musu komai bayan ga shaidu ga hujjoji amma aka danne gaskiya daga k'arshema aka ce sharri nayi musu, dan haka aka kaine gidan prison kasancewar bani da galihu, bayan nayi wata 3 na fito, bak'in ciki ya sani nabi shi ainahin wanda ya sace ya fara kaita gidan nasu, na kashe shi.


Na fito da kwana biyu na kashe shi dan haka zargi ya hau kai na, babu irin binciken da basuyi ba amma basu samu kwakwkwarar hujja ba, kasancewar zargi ne kawai yasa aka kawo ni nan aka ajiye ni yau 5yrs kenan, amma tuni iyalina sun koma gida Nigeria, ajiyar zuciya Khamal yayi yace " tab kai kenan da Kake da hujja bare ni da aka kama k'uru-k'uru, Allah dai ya shige mana gana kawai zamu ce.


Fateeha da Hamza sai zabga soyayya ake ta text ita a tunaninta Khamal ne, ana gobe satin biyun da Hamza ya cewa Fateeha za'a tafi yanke mishi hukuncin kisa ya kira ta, ringing d'aya ta d'auka, sak irin muryar Khamal yayi yace " hello my life kuka Fateeha ta fashe dashi yace " haba my love ya zakiyi min haka, dakayar Hamza ya samu Fateeha ta yi magana saboda kukan dayaci k'arfinta,, sosai sukayi magana ya kwantar mata da hankali, ya rarrashe ta, daga k'arshe yace " please dear ina neman wata alfarma a wajenki, cikin rawar murya tace " fad'i koma meye nayi alk'awarin zanyi maka shi koma meye, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan cikin matsanancin kuka yace " please dear ki auri Hamza, dammm gabanta ya buga yashiga dukan uku uku kukanta ya tsaya cak yaci gaba da cewa Hajiya ta yaba da hankalinki da tunaninki, shiyasa take da burin had'a zuri'a dake.
pls my heart duk da bata raye muyi mata wannan alfarmar, sosai ya shiga rok'onta akan ta yarda ta auri Hamza, yace" wannan kad'ai zakiyi min na mutu cikin farin ciki,sannan km ruhina yasamu salama pls dear ki yarda ki auri d'an uwa na ni da shi duk d'aya ne, pls wannan kad'ai zakiyi min ki tabbatar min da kina so na, sai daya sha wuya sannan Fateeha ta amince, cikin kuka tace " kayi magana dashi Hamzan?


"Eh na kira shi, nayi mishi bayani shima da farko k'in yarda yayi sai dakyar ya yarda yace amma naji ta bakinki tukunna, munyi dashi gobe zai kiraki sai kuyi magana, cikin kuka tace " dan kai zan auri Hamza dan a soyayya akwai sadaukarwa, ta k'ara fashewa da kuka, ranar Fateeha tayi kukan da tunda tazo duniya bata tab'a yinshi ba, dakyar sukayi sallama.


Hamza kuwa ranar kasa bacci yayi dan murna, tunda daga ranar Hamza da Fateeha suka dai-dai ta kansu amma ita sama-sama take kula shi, dan harga Allah bata wani jin son Hamza a zuciyarta bata tab'a jin d'igon son shi, atare daita ba ita kanta ta rasa dalili kwata-kwata ta tsani ta ganta dashi a tsaye shi kuma gashi da naci tsiya , haka dai har magana takai gun iyaye sosai jikin Dady yayi sanyi yayi kuma danasanin abinda ya aikata da farko,.
dan haka babu wata-wata kawai ya amince, aka saka rana, amma Fateeha dole ce kawai ta sata yarda da Hamza, ba'a wani saka lokaci mai tsayi ba wata 1 kawai aka saka.


A kwana atashi ba wuya agurin Allah yau gashi har ana saura kwana 5 d'aurin auren Fateeha da Hamza, gidan Hajiya Hamza ya gyara dan anan zai ajiye Fateeha, sai shirye-shiryen biki ake ita ko Fateeha ko a kanta.


Khamal da Ayuba zaune suna hira, Ayuba ya kalli Khamal yace " wai kai baka da kowa ne ban tab'a jin kace zakayi waya ba, da sauri Khamal ya d'ago idanunshi yana kallon Ayuba yace " dama da waya anan ne, murmushi Ayuba yayi yace " sosai ma, ai koni ina da ita sai dai matsalar bani da caja kuma ga ba caji, da sauri Khamal yace " OMG amma shine baka tab'a gaya man ba, kaga ni duk ba wannan ba, yanzu ya za'ayi nayi magana, shiru Ayuba yayi yace " ni dai tawa sai Friday, za'a kawo min caja, amma zo muje wajen wani abokina.


Ba tare da b'ata lokaci ba aka bawa Khamal waya, Ayuba ya kalle shi yace " kayi wayarka ba damuwa idan ma kwana zakayi kana iyawa, take your time friend, number Fateeha ya fara kira, da kamar bazata d'aga ba, ganin number Saudi Arabia yasa ta saurin d'agawa, tace " hello ido Khamal ya lumshe hawaye na zuba daga idonsa, murya can k'asan mak'ogwaro yace " my heart gabanta ne yayi muguwar fad'uwa numfashinta ya nemi d'aukewa jikinta ya dauki rawa.. ........



MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(united we stand and succed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)_




Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*



18



Numfashinta ya nemi d'aukewa cak... saboda rud'anin sautin muryar daya doki dodon kunneta cikin rawar murya ta bud'e bakinta dake rawa tace" my life kai ne?

Shima cikin rawar murya yace" eh nine my heart, ya kike, ya su Momy da Dady?
" duk muna lafiya, kai ya kake?
Murmushin k'arfin hali yayi yace " Alhamdulillah, am sorry dear ban samu waya bane shiyasa kika ga ban kira ba sai yau, kuka ta fashe mishi dashi, da k'arfi Khamal ya runtse idonsa saboda bak'in cikin daya taso masa, babu abinda Khamal ya tsana kamar b'acin ran Fateeha, balle har yakai ga ta koka, sosai Fateeha ke kuka, cikin kuka tace " am sorry ya dear bazan iya cika maka alk'awarin dana d'aukar maka ba , bana san sa, bazan iya auren sa ba, bana jin zan iya rayuwa da wani d'a namiji a matsayin miji in ba kai ba, kai kad'ai nake so, kai ne rayuwa ta, kaine duniyata wallahi na yarda zan jira ka komai tsayen lokacin, amma Allah bazan iya AUREN dan'uwanka HAMZA ba kamar yadda kace .


Da sauri ya bud'e idonsa dake rufe, gaban sa yayi masifar fad'uwa, kansa ya juye ya kasa fahimtar abinda Fateeha ke nufi, kalmarta ta k'arshe kawai yake maimaitawa _bazan iya auren dan'uwanka Hamza ba_ to me hakan ke nufi?
, bai k'arasa tunanin dayake yi ba yaji tace" wai ni za'a d'aurawa aure nan da kwana 5 kuma bada kai ba, I cant my love, I can't, am sorry, cikin rashin fahimta yace " Fateeha ban gane mai kike nufi ba, ban fahimta ba kin sani a duhu, waye zaiyi auren nan da kwana 5?


Cak ta tsayar da kukanta ta cire wayar daga kunnenta ta k'urawa wayar ido, jin Khamal nata "hello hello yasa ta mayar da wayar kunnenta tace " wai waye, bada Khamal nake waya bane?


"Eh nine mana my heart, please kiyi min bayani yadda zan gane ban fahimci zance ki ba, itama cikin rashin fahimta tace " kamar ya baka gane abinda nake nufi ba, ba da kai muke exchanging text ta layinka na Nigeria ba? " Eh bani bane ya akayi? "What!!? Fateeha tace da k'arfi, you means badai kai mukayi magana ba, ba kaine kace na auri Hamza ba?



Cikin firgici da matsanancin tashin hankali yace " ni! yaushe? kinga please ki nutsu ki dawo cikin haiyacinki kiyi man bayani yadda zan gane, aiko Fateeha ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, daga k'arshe tace " this coming Saturday za'a d'aura mana aure, tab tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, nan take Khamal ya canja kamanni, idonsa sukayi ja, hankalinsa yayi mugun tashi, jikinsa ya d'auki rawa in bada huci babu abinda yake fitarwa, ita kanta Fateeha ta fahimci hakan dan tana jiyo hucinsa, ta cikin wayar .
Cikin rawar murya tace " my life kana nufin duk wannan shirin Hamza ne?


Dakyar ya iya bud'e baki ya bata labarin abinda Hamza yayi masa, yace " koken d'in da aka kamani da ita a kaya na shine shi ya saka min a kaya na, ya fad'a mata duk yadda sukayi da Hamza, kuka Fateeha ta fashe dashi, saboda mamaki itama kasa magana tayi, Khamal yace " Fateeha, gabanta ne ya fad'i dan indai taji Khamal ya kira ta da real name d'inta ba lafiya ba, yaci gaba da cewa " mai yasa zaki munafurce ni, mai yasa baki sanar dani gaskiyar abinda ke tsakaninki da Hamza ba? Cikin mamaki Fateeha tace " kamar ya ban sanar dakai abinda ke tsakanin mu ba, me ke tsakani na dashi, koya ce maka akwai wani abu a tsananin mu ne?


Shiru Khamal yayi baice komai ba, taci gaba da cewa ni dai abinda na sani shine, yayi tayi min nacin yana so na, yasha zuwa gidan mu, yasha rok'ona akan na so shi, ni kuma na fad'a masa ina da wanda nake so, a lokacin ban san alak'ar dake tsakanin ku ba, bayan na sani kuma shine ya hanani na sanar maka, ta fad'a masa zuwan da Hamza yayi gidan su, da yadda sukayi, duk cikin matsanancin kuka Fateeha ke magana.



Ajiyar zuciya Khamal ya sauke da karfin gaske kana yace " lalle Hamza ya cika makiri maci amanar dan'uwa , wallahi tunda nazo k'asarnan banyi magana da kowa ba, sai shi ranar daya kira ni ya sanar dani shine yasa min koken a kaya na, cikin tashin hankali Fateeha tace " baka san ma Hajiya ta mutu ba kenan?



"What Khamal yace da k'arfi, ya fashe da wani irin mahaukacin kuka ya dunk'ule hannushi ya naushi bango da karfi yace shikenan " ya kashe ta, ya kashe min ita dama yace sai ya kashe ta, Hamza ka cuce ni, wallahi kozan yafe maka komai banda jinin Hajiya , bazan tab'a yafe maka abinda kayiwa Hajiya ba, Allah ya isa tsakanin mu dakai, macuci, mugu, azzalumi, maci amana, mayaudari, mak'aryaci, ya k'ara fashewa da wani mahaukacin kuka, fisge wayar Ayuba yayi ya kashe, tuburan Khamal ya haukace agurin ya rink'a wani irin ihu yana hauka, ya fita daga hankalinsa, nutsuwarsa tabar jikinsa, Ayuba ya tusa shi gaba yana yi masa nasiha yana bashi shawarwari, har ya samu ya dawo cikin hayyacinsa.



Fateeha na ganin an kashe wayar, tayi wurgi da wayarta, ta fita da gudu a falo sukayi karo da Momy da Dady da sauri Momy ta rik'e ta ganin gaba d'aya bata cikin nutsuwarta, kuka Fateeha take tana sambatu, a hankali Momy ta zaunar da ita, ta d'auko ruwan sanyi tabata tasha, sai da ta bari tad'an nutsu sannan ta kalle tace " mai ya faru? duk abinda ya faru tsakanin su da Khamal ta fad'awa Momy da Dady, sosai suka shiga cikin mummunan tashin hankali, Momy ta kalle shi tace " please Alhaji kayi wani abu akai mana, ajiyar zuciyar Dady ya sauke yace" tunani nake ta inda zan fara ne.


Cikin kuka Fateeha ta zube a gaban Dadyn ta tace " please Dady ka taimaka mana idan na rasa shi mutuwa zanyi please ta k'arashe maganar hawaye na bin fuskarta, cikin sanyin jiki ya kalli Fateeha yace " karki damu in sha zanyi iya k'ok'arina.


Bayan kwana biyu Dady ya samu Fateeha har dakinta a gefen gadon ya zauna, ya kalle ta yace " kin nunuwa Hamza akwai wani abu?
kai ta girgiza masa alamar a'a, ajiyar zuciya ya sauke yace " yawwa gud girl, yanzu abinda za'ayi ki kira shi yazo gidan nan yau, dan nayi magana da commissioner of police, mun gama tsara komai, amma dole sai Hamza ya shigo hannu za'a iya fitar da Khamal, jikinta na kirma ta d'auki wayarta ta shiga kiran Hamza, bugu d'aya ya d'aga, sai da ta saita kanta sannan tayi k'asa da murya tace " hello my love, kusan fad'uwa Hamza yayi kasancewar yau ne rana ta farko daya ji makamanciyar wannan kalmar daga wajen Fateeha, da sauri yace " hello my everything, tace " please ina san na ganka ne, cikin zumud'i yace " yanzu ko sai anjima, " ah yanzu mana cewar Fateeha, da sauri ya mik'e yana cewa "OK gani nan zuwa.


Da sauri Dady ya kira police d'in da suke magana yace " sun gama tsara komai, dan yana hanya " yes sir cewar police d'in, ya kalli Fateeha yace " ki shigo dashi har

Please Login or Register in order to submit comment