Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'arya,
na wani lokacin kafin ya bayya saboda wani dalili,
da k'arfi Naseer ya sauke ajiyar zuciya da har sai da su Dady sukaji sautinta, a ransa yace lalle babba babba ne, wanda kuma ya rigaka zuwa duniya dole ya fika sanin takan rayuwa,
a fili kuma yace " to kuma Dady har asaka mutum a kabari?


" Sosai ma kuwa, long sleep injection ake yiwa mutum, cewar Dady ya k'arasa maganar yana kallan Naseer,
murmushin yak'e Naseer yayi sannan yace " to amma Dady kai kana ganin hakan zata iya faruwa da Zarah?


Dady ya bud'e baki zayyi magana yaran suka fito da gudu, daga bedroom d'in Ikram,
jikin Zarah suka fad'a suna cewa " we missed you sweet Mom, kafin
Zarah tayi magana Dady yace " they are her niece and they call her Sweet Mom,
da sauri Naseer yace " eh Dady haka suka ji Na'eem na kiranta, kuma sunfi zama a gidan mu fiye da gidan su shiyasa suke kiran mu,
sweet Mom & sweet Dad,
Noor tace " sweet Dad Aunty tayi mana wanka,
cikin rashin fahimtar wacece Aunty ya kalli Momy,
murmushi Momy tayi had'i da cewa " oh Ikram suke nufi, da sauri Zarah ta d'ago idanuwanta,
Naseer yace " tana nan ne?


"Eh tana nan tun bayan mutuwar Zarah take fushi da iyayen tak'i zuwa gidan ko sau d'aya,
ko nan suka zo iyakacinta dasu gaisuwa, ko parlor bata fitowa kullum tana bedroom,
rana d'ai-d'ai ne bata kukan rashin 'yar uwarta Zarah,
ta hanawa kanta duk wani jin dad'i ta takure kanta,
tayi maganar idanta yana kan Zarah,
shiru kawai Zarah tayi, dan ita kad'ai tasan me take ji a zuciyarta,
Naseer yace " to su iyayen nata fa?


Ajiyar zuciya Momy ta sauke cike da jimami tace " hmmm Naseer ai idan kaga Zainab yanzu sai kayi mata kuka,
ta goje, ta kod'e, ta rame, ta k'ek'ashe, tayi muguwar rama,
tun bayan mutuwar da Zarah da tafiyarka da Na'eem ta shiga mummunan tashin hankali had'i da matsananciyar damuwa,
har hawan jini ta kamu dashi, tanan yau da lafiya gobe ba lafiya,
baka ga yadda ta koma, ta takura kanta da rayuwarta had'i da k'untata duniyarta, ta hana kanta farin ciki da walwala,
tana ta azabtar da kanta, ta hanawa kanta jin dad'in duniya,
kuma tana cikin k'uncin rayuwa,
Momy tayi maganar cikin mutuwar jiki, idanta nakan Zarah,
aiko take Zarah taji hankalinta yayi mugun tashi, jikinta ya d'auki rawa da kerrma,
launin idanuwanta suka canja daga farare zuwa ja,
ta rink'a jin zafi gami da k'una a k'irjinta yayinda zuciyarta take tafasa, mak'ogwaranta na tiriri saboda jin halin da Momynta Zainab ke ciki,
Naseer ko baki ya tab'a had'i da cewa " hisabi ta fara yiwa kanta kenan?


Jin abinda yace yasa Zarah yunk'urawa zata tashi,
da sauri Naseer yasa hannunsa ya danne hannunta batare daya kalle ta ba,
dole tasa Zarah ta zauna, amma Allah kad'ai yasan zugi da azabar da zuciyar ta keyi mata.


Washe gari jikin Zainab yayi d'an sauk'i yasa Mannir cewa Zainab ta tashi suje gida kar su Dady suyi fushi dasu kan basu je taryar Naseer ba,
da farko k'in zuwa tayi sai da Mannir yace mata kodan Na'eem ai taje,
jin abinda yace yasata mik'ewa zumbur had'i da surar hijabinta tayi gaba,
murmushi Mannir yayi sannan yabi bayanta,
tunda suka nufi gidan gabanta yake muguwar fad'uwa had'i da bugawa da tsananin k'arfin gaske,
suna shiga harabar gidan gabanta ya kuma fad'uwa da k'arfi,
koda sukayi parking kasa fitowa tayi, tayi shiru a mota tana sauraren yadda k'irjinta ke bugawa da k'arfi,
har sai da Mannir yayi mata magana sannan ta fito cikin sanyin jiki, suka shiga main parlor gidan.


A parlor ta iske yaran suna wasa, da sauri ta k'arasa inda suke had'i da rungume Na'eem gamm a jikinta had'i da sakin kuka,
tana d'aga kai ta hango Naseer yana k'ok'arin barin wajen, da sauri ta mik'e had'i da nufar wajen,
tsaiwarsa Naseer ya gyara yana jiran ta k'oraso dan dakowacce tazo yana dai-dai da ita,
tana zuwa ta rungume shi had'i da sakin rikitaccen kuka mai cin rai tana cewa " Naseer I made a mistake, I'll never forgive me self, ever Naseer,
munyi rashin da har abada bavzamu tab'a mayar da kamar shi ba,
na cuci kai na, nayiwa kai na illar da har in mutu bazan manta ba,
Ikram dake bedroom jin maganar Momynta yasa ta fitowa,
yadda take kuka ya tab'a zuciyar Ikram sosai, ta fara zubar da kwalla batare data sani ba,
Naseer ji yayi zuciyar sa tayi mugun yin sanyi har yaji mugun tausayinta ya shige shi,
a hankali ya cireta daga jikinsa ya zuba mata ido, sai lokacin ya kula da yadda ta koma,
tayi mugun bak'i ta rame, kamar wacce ta shekara tana jinyar HIV & blood cancer,
gaba d'aya ta yarkwale ta lalace,
ji yayi duk wannan zafin zuciyar da k'iyayyar da yake yi mata sun gushe,
lokaci d'aya kuma tsananin tausayinta ya mamaye duk wata gab'a da jijiya had'i da gangar jikinsa,
a hankali ya shiga goge mata hawayen dake zubowa yana girgiza mata kansa alamar ta daina,
dai-dai lokacin idan Ikram ya sauka akan Zarah dake shigowa part din,
ji tayi kanta yayi dum durum dum,
cikin tsananin tashin hankali bakinta na wara tace " Z... A... R... A... H!!! had'i da sulalewa k'asa sumammiya,
da sauri Zainab ta juya had'i da sauke idanta akan ZARAH............





MOMYN ZARAH

```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_



~NA~



*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh



*GARGAD'I*


```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```



~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*



*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*






71





Zarah dake k'arasa shigowa cikin parlor ta tsaya cak had'i da zubawa Zainab idanuwanta,,
idan Zainab nakan Zarah ta fara takowa zuwa gare ta, batare data bi takan Ikram dake kwance a k'asa a sume ba,
k'afa tasa ta tsallake Ikram dake gabanta kan hanyar zuwa wajan Zarah,
kowa a parlor'n baki ya bud'e yana ganin ikon Allah yadda Zainab tasa k'afa ta tsalleke 'yarta ta cikinta dake sume batare data kula ta ba ta nufi wajen Zarah,
a gigice Naseer yayi inda fridge yake ya bud'e ya d'auko ruwa yana zuwa gaban Ikram ya shek'a mata batare da wani b'ata lokaci ba,
ajiyar zuciya ta saki had'i da kiran sunan Zarah da k'arfi "Zarah!!!!,,
bata jira ta gama dawowa hayyacinta ba ta mik'e tana tangad'i ta nufi inda Zarah ke tsaye k'emm kamar an dasa ta,
tana isa ta rungume ta had'i da fasa rikitaccan kuka mai tsananin cin rai,
a hankali Zainab dake tsaye a gaban Zarah ta kafe ta da ido kawai batare da tace komai ba,,
tasa hannu ta raba Zarah da Ikram.


Cikin kerrmar jiki Zainab tasa hannu tana shafa fuskar Zarah zuwa jikinta tana zubar da hawaye,
cikin muryar kuka tace " Zarah ta dama nasan ba mutuwa kikayi ba,
dan kwata-kwata jikina bai tab'a bani kin mutu ba,,
rai na bai tab'a bani kin tafi kin barni har abada ba,,
jikina ya dad'e yana bani tabbas zaki dawo komai daran dad'ewa,
duk ta gigice ta fita daga hayyacinta, kallo d'aya zakayi mata kasan bata cikin nutsuwarta,
kamar mahaukaciya ta juya wajen Mannir dake tsaye tun shigowarsu ya kasa kwakkwaran motsi balle yayi magana,
saboda tsabar rud'ewa, da ido kawai yake bin kowa dake parlor'n,
a kid'ime ta kalle shi tace " ka gani ko?


" Dama nasha fad'a maka jiki na yana bani Zarah zata dawo,
jikina yana bani Zarah ba mutuwa tayi ba, dan nasan bazata tab'a tafiya ta bar Momynta cikin k'uncin rayuwa ba,
amma kake min kallon wata mahauciya ko tab'abb'iya, to gashi ka gani da idanka,
duk abinda zai samu d'a uwa tana ji a jikinta ko Allah ya nuna mata a mafarkinta,
amma ko d'aya banji kona gani ba akan mutuwar Zarah,
maganar take yi amma kamar saban kamun hauka.


Dady dake tsaye a gefe yace " Zainab wannan ba Zarahnki bace,
wannan sunanta LINAH, indian ce kuma itace sabuwar matar Naseer,
a kid'ime Zainab ta juya tana yiwa Dady wani irin kallo,
sannan ta juya ta kalli Naseer tayi mishi kallan few seconds kafin ta mayar da kallanta kan Zarah,
" Zarah!!! ta kira sunanta cikin tashin hankali, kasa amsawa Zarah tayi, illa kallan Zainab kawai da takeyi kwallah na zubo mata,
saboda yadda taga Zainab ta lalace ta yargwale, duk a dalilinta,
yanzu ma gashi ta kuma nunawa duniya a karo na biyu tafi santa,,
fiye da 'yar cikinta, duk da bata da tabbacin itace amma tasa k'afa ta tsallake 'yarta dake sume,
jibi yadda ta nakasa rayuwarta, take azabtar da kanta da kuma zuciyarta,
duk saboda ita, wannan wanne irin mugun so Zainab keyi mata ne haka,
da harta fi san ta akan rayuwarta da duniyar, da kuma fari ciki da walwalarta,
ita Zainab ma bak'in yayi mata yawa ta kasa kukan fili sai na zuci,
dan tuni hawayen idanta suka k'afe, idanta ya bushe kwata-kwata ma ta daina kuka dan ta rigada ta saba dashi,
murmushin yak'e Zainab tayi sannan ta mayarda kallanta ga Dady da Momy tace.


"Hmmmm Dady na yarda wannan Linah ce ba Zarah ba, amma ina da abubuwan da zan fad'a kafin nan,
da farko shekarar Naseer hud'u a Holland ana fama dashi akan yayi aure amma yak'i,
rana d'aya kwatsam sai ya kira ku a waya yace " ya samu matar da zai aura,
bayan kamar 3days ya kuma kira a waya yace washe gari yake san a d'aura auren kuma a Holland d'in,
Dady a lokacin da Mannir ya tambaye dalilin dayasa ka aminta da'a d'aura auren acan,
ce masa kayi saboda kaji muryar matar da Naseer d'in yake so ya aura a gidan,
ko ba haka akayi ba?


Shiru Dady yayi yana kallanta, yana san jin k'arshen maganarta,
d'an gun murmushi tayi sannan tace " abin tambayar anan yaushe mutumin da ake fama dashi yayi aure yak'i, ya samu matar da yake so,
kuma a cikin 3days ya yarda ya amince da ita,
har suka fahinci juna, bayan kowa yasan bayan Zarah Naseer bai tab'a san wata 'ya mace ba,
bai tab'a yin budurwa ba sai ita, bai tab'a tsayawa da wata mace ba sai ita,
kuma kowa yasan Naseer da k'abilanci, mutumin da baya sa kayan wata k'asar ko wani yaren sai kayan k'asarsa kuma yarensa shine zai iya auran wata k'abilar?


" Dady kai da bakinka kace bayan kaje Holland da 2 months kayi fama da Naseer akan yayi aure kodan Na'eem amma yak'i daga k'arshe sai ce maka yayi shida aure har abada,
dan Zarah ce kad'ai macen da yake so, ita kad'ai zai iya zaman aure da ita,
amma sai gashi bayan wata biyu ya kira ka yace ya samu mata zayyi aure,,
d'an shiru tayi, sannan ta kalli su Noor dake wasa a harabar gidan,
sannan ta mayar da kallanta wajen Dady tace " wad'an nan yaran waye?


Da sauri Momy ta fad'a musu kamar yadda Zarah da Naseer suka sanar da su,,
murmushi Zainab ta kuma yi a karo na biyu sannan tace,,
"hmmm Momy kun manta sanda Zarah ta mutu da ciki a jikinta na wata uku?


Gaban Momy da Dady yayi muguwar fad'uwa,
da sauri Momy ta kalli Naseer suka had'a ido kafin dukkan su su mayar da kallan su ga Zainab,
Zainab taci gaba da magana " kuma kallo d'aya za'a yiwa yaran asan sun had'a jini daku,
ta fad'a tana kallan su Dady da Momy dake tsaye kamar mutum-mutumi,
sai a lokacin su Dady suka zubawa yaran ido sukayi musu kallan k'urulla,,
a nan take Momy ta gano tsananin kamar da Nouwaf keyi da Dady,,
haka ma Dady ya gano tsakanin kamar da Noor keyi da Momy,
Zainab tayi gutun murmushi sannan ta juya wajen Noor da Nouwaf ta durk'usa a gabansu tana musu murmushi,,
cikin sanyin murya Zainab tace " ya sunanku?
dariya Noor tayi sannan tace " ni sunana Noor shi kuma Nouwaf ta fad'a tana nuna Nouwaf,,
murmushi Zainab ta kuma yi tana yi musu wasa, cikin dabara tace " i mean your real name,
your school name, kai tsaye Nouwaf yace " my name is MUSTAPHA NASER,
ita kuma Noor tace " MARYAM NASEER.


Murmushi Zainab ta kuma sannan tace gaba " wow that is wonderful name,
sunnan Dady da Momy tayi maganar tana mik'ewa tsaye idanta na kallan Zarah,
mayar da kallanta tayi wajen Dady tace "wannan Zarah ce akwai dai abinda ke binne a k'asa, tayi maganar da k'arfi tana nuna Zarah batare data kalle ta ba,
a hankali Zainab ta taka zuwa gaban Zarah tana kallanta ido cikin ido,
da sauri Zarah ta mayar da kanta k'asa dan bazata iya jure kallan Zainab a irin wannan yanayin data ke ci ba,
Zainab tace " Zarah zan miki magana ta k'arshe, daga wannan maganar bazan k'ara yi miki magana ba,
ba kuma zan k'ara shiga rayuwarki ko duniyarki ba,
tunda naga kin fi san hakan, kin fi san na koma gefe, baki san na rink'a shigar miki rayuwa, hakan yafi miki dad'i da sanya ki ciki farin ciki,
this is the last time da zanyi miki magana,
idan har kika b'oye min gaskiya kika fad'a man k'arya,
d'an shiru Zainab tayi kafin tasa hannu ta d'ago kan Zarah tasaka idanta cikin nata,
tace " nafi san ki kalli ido na idan zaki bani amsar tambayar dazan miki,
sannan ta d'aga murya tace " Zarah na had'a ki da girman Allah,
na rok'e k'i da darajar mahaliccinki ki sanar damu gaskiyar al'amari da abinda ke b'oye,
ke ZARAH ce ko LINAH?


A hankali Zarah ta kalli Naseer, tana zubar da hawaye,
shima hawayen yake zubarwa dan tunda yaga yadda Zainab ta koma yaji zuciyarsa tayi rauni ta karye,
a hankali ya d'aga mata kai alamar "eh,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi , muryar ta rawa tace " M... O... M... Y,
had'i da fad'awa jikin Zainab ta fashe da rikitaccan kuka,
itama Zainab kukan tasa gami da k'ara rungume Zarah gammm a jikinta,
da sauri Ikram ta ma ta rungume su ta baya,
Mannir na tsaye ya kasa koda kwakkwaran motsi balle ya iya yin magana,saboda tsananin mamaki da al'ajabi,
sai da suka d'ade a haka kafin Zainab ta zame jikinta daga nasu tana kallan Zarah,
cikin kuka tace " why Zarah, meyasa zakiyi min irin wannan horan mai tsakanin gaske?
cikin kuka Zarah tace" please kiran Alhajin sama (Alhaji Abdullahi), da Abba nah,
da sauran Family kice su zo nan, a gaban su nake san sanar da komai,
jikin Zainab na rawa ta kira Abban Zarah tace yazo da duk 'yan gidan sa,
sannan ta kira Alhajin Sama shima ta sanar dashi.


Bayan duk kowa ya hallara a parlor'n ne Zarah da Naseer had'i da yaran su suka fito,
da sauri duk jama'ar wajen suka mik'e tsaye had'i da zuba musu ido,
banda Dady, Momy, Mannir, Ikram, Zainab
dake zaune ko motsi ba suyi ba,
Alhaji Abdullahi ya kalli Zarah da Naseer sannan ya kalli yaran,
kafin ya mayar da kallan ga Dady, zayyi magana Dady yayi saurin cewa " kayi hak'uri ka zauna wannan shine dalilin taron,
muma so muke muji abinda ke faruwa wanda mu bamu sani ba,
cikin mutuwar jiki kowa ya zauna, sannan Zarah ta shiga basu labarin abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
kafin Naseer shima ya d'ora akan abinda ya sani,
shiru kowa yayi a parlor'n yana sauraren su har suka dasa aya,
kowa ka gani yayi jigum yana jimamin abin,
cikin kuka Zarah ta durk'usa a gaban su bisa gwiwowinta,
ta fashe da mahaukacin kuka tana rok'onsu yafiya,
murmushi Alhaji Abdullahi yayi sannan ya shafa kanta yace " bakomai Fatima,
Allah yayi miki albarki dake da zuri'arki baki d'aya,
ya sanya albarka a rayuwarku,
sai da tabi kowa dake parlor'n ta fashi hak'uri had'i da neman yafiyar kowa,
kowa ya yafe mata har Ikram, kafin daga baya Abbanta yace " ita kuma wannan 'yar afiruwar ya sunanta yayi maganar cike da tsokana yana kallan Nailah,
Murmushi tayi sannan tace " Zainab amma muna kiranta da NAILAH,
da sauri Zainab ta d'ago tana kallan Naseer da Zarah, tana zubar da hawaye a tare suka d'aga mata kai alamar eh,
dan kawar da abin Abban Zarah yace " haba ashe shiyasa naganta 'yar magezuwa,
dariya Mannir yayi sannan yace " kai Abba Zainab d'in ce 'yar magezuwa,
kai dai kawai kaga saban jini shine ka tuna jiya,
gaba d'aya aka saka dariya,
sosai akayi wasa da dariya kafin su Alhaji Abdullahi su tafi.


Fir Zainab tak'i tafiya sai da tasa Na'eem da Nouwaf & Noor agaba suka tafi,
ganin an kwashe yaran yasa Ikram cewa itama zata bisu, fir itama tak'i zama gidan, wai bazata bar Momy ta kwashe mata 'ya'ya ta tafi dasu ita kad'ai ba,
hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Mannir ba dan yasan yanzu rayuwar su zata dawo normal kamar da cike da farin ciki da walwala.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin farin ciki, babu wani sauran bak'in ciki da damuwa a Familyn su.


Cikin bacci Mannir ya rink'a jin wani mugun ciwo a buret d'insa,
ya rink'a jin kamar zata tsinke,
yadda kasan tana ci da wuta haka yake ji,
tsananin azaba ne ya farkar dashi a gigice, da sauri ya mik'e had'i da cire wondansa, yayi bathroom da gudu,
ganin yadda joy stick d'insa ta koma ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba,
dan ta kumbura simtin, tayi jajir, har penis ('ya'yan marena) sun koma red colour,
ga wani irin azaba da zugin da suke masa ji yake kamar zai mutu,
haka Mannir ya kwana bai runtsa ba yadda yaga rana haka yaga dare,
saboda azabar ciwo, a hankali wasa-wasa ciwon ya fara cin k'arfinsa yana girma, ga azabar na k'ara tsananata.


BAYAN WATA UKU


Sosai ciwon yayi mugun cin jikin Mannir batare daya sanarwa da kowa ba,
shi kad'ai yasan halin dayake ciki,
gashi kullum kwanan duniya ciwon k'ara gaba yake, azabarsa na k'aruwa, dan rabashi da bacci a rayuwarsa har ya manta dan kwara-kwata ciwon baya barinsa yana bacci,
gashi yanzu azzakarinsa da 'ya'yan marainansa sunyi wani mugun girma sunyi luhu-luhu,
sai b'oyewa yake dan babu wanda yasan halin dayake ciki,
Zainab tayi mitar k'in kwanciyar aure da ba yayi da ita har ta gaji,
tayi fushi da zuciya akan hak'k'inta dabaya bata, dan raban ma da su kwana a daki d'aya har ta manta, balle maganar sex,
tun tana damuwa harta dangana, ta zuba masa ido,
sannu a hankali ciwon ya fara zubar da wani irin ruwa mai d'oyi da wari sosai,
dan ko wucewa yayi ta gabanka zaka ji warin ciwon,
wani lokacin yana bedroom d'insa amma warin har parlor,
Zainab da Ikram sunyi neman abinda ke wannan mugun d'oyin har sun gaji dan su a tunanin su mushe ne,
b'era ko wani abinne ya mutu.


Haka ciwon yayi ta cin jikin Mannir, yana b'oyewa har ciwon ya girmama sosai,
azabarsa ta k'aru ga wari da ruwan gembo da ciwon keyi,
wani lokacin ji yake kamar ya kashe kansa saboda azaba,
ji yake kamar ana hura masa wuta, haka yake ji,
ganin ciwon bana k'are bane yasa shi tafiya hospital ganin Doctor,
bayan an gama yi masa gwaje-gwaje da scanning Doctor ya kira shi office d'insa,
jiki a mace Mannir yayi tsaye dan baya iya zama matuk'ar ya zauna yanzu ruwan ciwon zai b'ata wajen,,
ya kuma cika wajen da wari, cikin sanyin jiki Doctor ya fara yi masa bayanin ciwon,,
"Mr Mannir kayi hak'uri da abinda zan gaya maka dan gaskiya ciwonka babban ciwo ne,
kayi hak'uri ka dangana ka yarda da k'addara mai k'yau ko marar kyau,
saurin katse shi Mannir yayi ta hanyar d'aga masa hannu yace " please ka tsagaita maganar ka, ka sanar dani meke faruwa,
ajiyar zuciya Doctor yayi sannan yace " PENIS CANCER (cutar gwaiwa) ke damunka,
kuma tayi bala'in cin k'arfinka ta kama jikinka sosai ta yadda ba lalle magani kad'ai yayi aiki ba,
Inaga sai mun had'a da theater & surgery,
wata irin muguwar fad'uwa gaban Mannir yayi, lokaci d'aya jikinsa ya d'auki rawa da kerrrma,
batare daya cewa Doctor komai ba ya juya ya fita,
da sauri Doctor ya mik'e ya biyoshi da gudu yana yi mishi magana amma ko kallansa Mannir bayyi ba.


Yana isa gida ya zube a parlor had'i da fasa rikitaccan kuka,
da gudu Zainab da Ikram suka fito daga bedroom, ganin abinda ke faruwa yasa hankalin su mugun shi,
dan sun tabbatar mummunan abu ne ya faru, a tare suka shiga tambayar sa abinda ke faruwa,
in banda kuka babu abinda Mannir keyi ko magana ya kasa yi, ganin haka yasa Zainab kama hannunsa ta yi bedroom dashi,
cikin kuka yace " Zainab na mutu na gama yawo, na tashi daga aiki,
dakyar Zainab ta rarrashe ya sanar da ita abinda ke damunta,
cikin tashin hankali ta sake shi tayi baya cikin kid'ima,
wani irin kuka Mannir ya k'ara fashewa dashi, kafin ya mik'e ya cire wandonsa ya nuna mata,
da sauri ta rufe idanta ganin yadda buret d'insa ta koma,
ta zama k'atuwa ga girma da ruwan d'oyin data ke zubarwa, kalarta ma ya canja ta koma red,
daurewa Zainab tayi ta matso kusa dashi tace " tun yaushe kake cikin wannan halin?


" Wata uku ya bata amsa, "amma shine baka tab'a sanar dani ba?


Shiru yayi batare dayace komai ba, dakyar Zainab ta rarrashe ta shawo kansa, tasa shi yayi wanka, tace " ka huta yau, gobe sai muje mu sanar dasu Dady halin da ake ciki,
dan wannan ba abun b'oyewa bane, kuma addu'ar iyaye tana da matuk'ar tasiri,
kai ya d'aga mata batare da yayi magana ba,
itama murmushi tayi ta fita, a parlor ta iske Ikram ta kasa zaune ko tsaye, sai safa da marwa take tana jiran fitowarta,
tana ganin Zainab tayi wajenta da sauri tana tambayar ta abinda ke faruwa,
murmushin k'arfin hali Zainab tayi sannan tace " mata asarar mak'udan k'udad'e yayi,
ta fad'a tana barin wajen, dan tasan Ikram da tambayar tsiya,
bayanta Ikram tabi da kallo dan tasan akwai dai wani abun,
Zainab na shiga bedroom d'inta tasa key, had'i da sakin gigitaccen kuka,
haka taita rusgar kuka har aka kira sallar ishsha sannan ta mik'e dakyar saboda kukan datayi ya saukar mata da matsanancin ciwon kai da zazzab'i,
wanka ta farayi ta shirya sannan tayi sallah, ta fita parlor,
a parlor ta iske yaran da Ikram zaune akan dinning suna cin abinci, suna ganinta suka mik'e da sauri suka rungume ta,
itama rungume su tayi tana sakar musu murmushin yak'e,
Na'eem ne yace " Momy mike damunki, baki da lafiya?


Yayi maganar yana d'ora hannunsa akan wutanta, dariya tayi tace " babu abinda ke damuna bacci nayi,
Ikram dake kallanta ta kalla, saurin kawar da kanta tayi,
abinci ta zuba a plate ta nufi bedroom d'in Mannir,
dakyar ya d'an ci kad'an, sosai Zainab taci gaba da rarrashin Mannir tana k'ara kwantar masa da hankali,
Parlor ta dawo ta iske har Ikram ta gama shirya yaran sun kwanta,
kitchen ta shiga ta had'a tea tasha sannan tasha magani, ta shiga bedroom d'inta,
sai wajen 10:00pm sannan ta koma bedroom d'in Mannir,
dan tasan matuk'ar bata kusa dashi tunane-tunane zaiyi tayi,
yazo kuma ya sake kamuwa da wani ciwon bayan wannan,
ta kuma tabbatar bazai yi bacci ba,
a tsaye ta iske shi, yana zaga bedroom d'in, hannunshi ta kama had'i da kwanta dashi akan bed,
ta rungume shi had'i da ja musu bargo,
zayyi magana tayi saurin had'e bakinsu waje d'aya.


Wajen k'arfe 2:30am na dare Mannir yaji k'arar harbin bindiga,
a tsorace ya mik'e ya lek'a ta window aiko idansa ya sauka akan wasu maka-makan k'atti magaka gato,
su bakwai, cikin firgici da kid'ima ya fara tashin Zainab daga bacci,
tana dud'e idanta yace " 'yan fashi, a

Please Login or Register in order to submit comment