Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.*

*BAYAN NA MUTU..!*

*©AYHA SHAFI'EE*

*(☆_☆)*

*Da sunan Allah Mai rahma Mai jin ƙai.*

*SHIMFID'A*

______

Rayuwa.

Mece ce ita?

Nasha tambayar kaina hakan.

Wannan lokacin dake tsakanin haihuwa da mutuwa.

Lokacin da ruhi ke tare da gangan jiki.

Ko kuma lokacin da dukkan wata halitta walau d'an adam, dabba ko tsirai ke iya numfashi.

Dukkan wad'annan bayanai ne na ma'anar rayuwa, amma wani ya tab'a fad'a min cewa rayuwa itace abinda yake faruwa a lokacin da ka shagala cikin harkokin gabanka, itace dukkan gwagwarmaya da k'addarar dake samun Bawa a tsakanin zamansa na duniya da mutuwa, rayuwa itace lokacin da matsaloli suka sa ka kaucewa hanyar layin da zai kai ga nasararka, sannan rayuwa itace ke d'aukanka daga cikin mafarkan da ka shirya a zuciyarka zuwa k'addarar ka dake jira a zahiri.

Amma ni a tawa fahimtar, zan iya fassara rayuwa da wannan motsin dake gefen k'irjinka na hagu, wannan dukan dake sawa ka riski abinda gobe ta tanadar, wannan bugawar dake baka kwarin gwiwar fuskantar abubuwa, sannan wannan kid'an dake sawa ka sami fatan canji a rayuwarka.

Bayan wannan ma'anar ta rayuwa... Meye kuma DANGI? Su waye su? Ka tab'a tunanin cewa DANGI suna da muhimmanci a rayuwar kowanne d'an adam? Ka taba sanin cewa suna da damar da zasu hargitsa su kuma kuntata rayuwarka ba tare da ka iya wani katab'us ba? Sannan ka tab'a tunanin cewa DANGI zasu iya zama silar ajalinka?

Sunana Fatima Bintu, Biyo ni in baka labarin k'alubalen DANGI, har kuwa BAYAN NA MUTU!

****

07:1 AM.

"Allah ya sani, ina sonki Fatima." Muryarsa mai dad'i da zurfi ta fad'a.

Na k'ara sunkuyar da kaina k'asa sanda tarin kunya fal ta cika kumatuna, idanuna na kallon yatsuna da suka kasa tsayawa waje d'aya saboda na san cewa idanunsa na kaina ta yadda ko yaya na d'ago da nawa, zasu had'e ne cikin nasa.

"Na san dukkan halin da kike ciki kuma na san irin ra'ayinki daya banbanta da namu, nayi miki alk'awarin zan tallafa miki ki cimma burinki in har kika bani dama."

Kwalla ta cika idanuna a lokacin da naji hakan, wad'annan kalmomin su na shafe tsawon shekaru biyu a rayuwata ina fatan jin irinsu daga bakin wani a cikin 'yan uwana, koda kuwa mutum d'aya ne da zan samu tallafi daga wajensa.

Zuciyata ta cigaba da bugawa da k'arfin da yasa na kasa gane a cikin zahiri nake koko a mafarki, na kasa yarda cewa tsawon wannan lokacin abinda nake nema zai zo ya same ni a daidai wajen daya tarwatsa rayuwata ta baya, wajen da kullum nake ganinsa kamar kurkuku sab'anin gida da aka san d'an adam yana rayuwa cikin mutunci da girmamawa.

Sai dai dama ance dukkan nasara tana zuwa ne cike da k'alubale dake k'ara mana fahimtar wasu abubuwan, kuma zamana a cikin gidan ya koya min tarin ilimin da yasa na fahimci wani b'angaren mai duhu na rayuwa sab'anin wanda na taso a ciki.

Nayi murmushi a hankali zuciyata na fatan wannan ya zama mafarin wata sabuwar rayuwar da zan fuskanta.

"Ba zan takura ki ba, zan jira har zuwa lokacin da yayi miki, ki bi tunaninki a nutse Fatima."

Ya fad'a sanda shiruna yayi tsawo.

Sai dai kuma zuciyata ta buga da yadda muryarsa ta ambaci sunana a hankali, naji kamar zan iya narkewa cikin gulbi.

"Ke!"

Wata k'atuwar murya a gefe ta janyo ni daga cikin tunani na, na zabura da sauri sanda atamfar rigar da nake wankewa ta sub'uce cikin bokitin kafin in d'aga idona akan siffarsa, Yaya Sule.

Wani kwayan mutum guda d'aya da baya tab'a barin inyi yini guda a rayuwata ba tare da hargitsi ba, a lokuta da yawa da tunani na ke tafiya rubutun wasik'ar jaki, nasha hasko cewa rayuwata a cikin gidan nan zata fi sauk'i in har zai matsa wani wajen, don shi ba mutum ne mai yawan fita ba, saboda haka kusan kullum yana gefen hajiya yana k'ara b'antare ragowar rusashshiyar alak'ar dake tsakaninmu.

"Me kike yi anan?"

Ya tambaya yana kallon bokitin dake gabana.

Me? na zata kana zaune a wajen lokacin da Hajiya ta jefo min tarin kayan wankinta da sanyin safiyar da ba kowa ya gama tashi ba taje inje in wanke.

Naso ace zan iya gaya masa hakan ba tare da na jawowa kaina wani abun ba.

"Kayan Hajiya nake wankewa." Ba yadda na iya, na amsa a hankali.

"Toh tana jiran kokonta in kin gama."

Na gallara wa bayansa harara sannan na janyo wata k'atuwar rigarta mai kama da Buba akan yadda take matseta in ta saka a jikinta, a shekaruna kaf! ban tab'a ganin mace mai k'iba irin Kakata ba.

A lokacin da nake matse kayan ina shanyawa, zuciyata ta shiga tunanin irin fad'an da zan sha inda sai yanzu da na gama zanje in had'a kokon, Allah yaso Aunty Habiba taji tausayina da sassafen nan tace zata had'a nata dana hajiyan sai inje in karb'a in na gama, duk da cewa kuwa abin ya bani mamaki sanda ta tsaya tayi min magana.

"A'ah Bintu kayan wa kike wankewa da sassafen nan?"

"Kayan Hajiya ne." Na amsa bayan na gaishe ta.

Ta d'an tab'e bakinta kad'an. "Ai da an barki sai rana ta d'aga, amma a sanyin nan haka kamar yak'i..."

Dama na san zata fad'i hakan saboda duk da cewar Hajiya surukurarta ce, basa shiri ko kad'an da ita akan wani dalili da ban san shi ba. Har tayi gaba sai kuma ta juyo tace.

"Kin had'a mata kokon safen ne?"

"A'ah, sai na gama tukunna."

"Toh ai kya jawa kanki wani fad'an tunda kafin ki gama wannan wankin ai rana ta d'aga, je ki d'auko filas d'in nata sai had'a nawa da ita, in ki gama kya zo ki karb'a."

Da murnata a lokacin nayi mata godiya sannan na koma b'agaren Hajiya na d'auko filas d'in ba tare da kowa ya ganni ba, ashe hakan shine mabud'in k'addarata!

______

10:30 AM.

"Kin gama dukka?"

Hajiya ta tambaya a lokacin da na shiga cikin d'akin. Tana manne akan tabarmar kabarta dake shimfid'e a tsakiyar d'akin.

"Eh na k'arasa, har na shanya."

Ba kallon fuskarta nake ba, amma ina iya jiyo tasirin hararar da take aiko min a jikina. Na mik'a mata filas d'in kokon dana karb'o daga wajen Aunty Habiba amma bata karb'a, sai ta nuna min k'ashen tabarmarta da sandar dogaronta kamar shi d'in wani abin kyankyami ne basha zata yi ba.

"A ina kika yi shanyar?"

"Bayan d'akin Aunty Sadiya."

"Kinga ki tabbata, ki tabbata ko d'ankwali d'aya bai fad'i ba in ba haka ba sai ki sake wanke su wallahi."

"Ai Hajiya na k'ulle k'asan su ta yadda iska ba zata d'iba ba."

Daga yadda ta kalle ni, na san ba haka taso taji ba, amma duk da haka ta sake manna min wata hararar gargad'in kafin ta kad'a hannunta a iska alamun sallama.

Na mik'e a hankali na nufi wani waje daga can k'arshen d'akin, wajen da ya zama makwanci da wajen zama na tun lokacin da k'addara ta jefo ni rayuwa cikin BABBAN GIDA.

Gidan dake cike taf! da tarin zuri'ata na dangin uba, tarin zuriar da basa tab'a jin k'aina kuma basa k'aunata a dalilin turbar da Hajiya ta d'ora su akai tun farko, na k'in mahaifiyata da kuma ni da 'yar uwata da muke jininta.

Mahaifina shine d'a na shida a wajen Hajiya, kuma yana da tarin k'anne kusan bakwai a k'asansa, a lokacin rayuwarsa, ya auri mata uku kuma yana da 'ya'ya takwas.

Gwaggo Lami itace matarsa ta farko mai 'ya'ya shida dukkansu maza, ita d'in 'yar uwarsa ce da ta zama 'yar k'anwar Hajiya, saboda haka da ita da 'ya'yanta sune mafi soyuwa a cikin zuri'armu.

Amma mahaifiyata da ta kasance d'iya ga 'yan gudun Hijira bata tab'a zama abu mai daraja ba a wajensu, duk kuwa da cewar sun san yarintarta don ta taso ne a gidan maigari kasancewar iyayenta sun rasu tun tana yarinya, kuma sun san halinta na hak'uri da juriya, don ba kowa ke iya rayuwa a gidan maigari tare da azababbun mata da 'ya'yansa ba.

Amma a lokacin da mahaifina ya nuna yana son aurenta, ba irin tashin hankalin da ba ayi ba akan zai auro wadda bata da asali, sai da maigarin yasa baki tukunna sannan suka hak'ura ba don son ransu ba. Bayan shekaru uku da auren ne ta haifi Yayata mai suna Maryam da muke kira da Mairo sannan ni kuma nazo bayan wasu shekaru ukun, a lokacin Baba ya sake aure.

Ya auro 'yar gidan wani attajiri a garin mai suna Saratu, mace mai tsananin kirki data k'arb'i Innata damu 'ya'yanta hannu biyu ta rik'e, don bayan mahaifinmu zan iya cewa duk k'auyen babu wanda ke k'aunar mu sama da ita, munyi zama na aminci tare da ita kafin k'addarar Mairo tazo ta gifta.

Lokacin da Mairo ta kammala karatunta na sakandire ne Baba yace zaiyi mata aure da d'an gidan wansa Ibrahim, abinda ya haifar da rikici a cikin gidanmu da kuma Babban gida a lokacin kenan, su can Babban gida suna fad'an basu yarda da had'in ba saboda shi Ibrahim d'in yana da d'an samunsa a lokacin, a cikin gidanmu kuma Mama da Aunty Saratu na rikicin lallashin Mairo akan ta yiwa Baba biyayya, don sanin kowa ne tana da wani saurayi da take mutuk'ar so wanda ba d'an garinmu bane, aminin mahaifinsa ne kawai a garin yake zuwa wajensa don haka ba wanda ya san aslinsa sosai.

Sai dai alk'alami ya riga ya bushe akan abinda Ubangiji ya tanadar, don Mairo bata saurari shawarar kowa ba, ta sulale ta gudu tare da saurayin nata a wani dare, ba irin nema da cigiyar da ba ayi ba a lokacin, har d'an aminin mahaifin saurayin sai da aka k'ulle a kotu amma ba'a same su ba. Dalilin da ya jawowa Mamana ciwon zuciya kenan wanda ya kaita har kabarinta, don a lokacin da abin ya faru sai ya zama kamar Mairo tayi mata wanka da ruwan bak'in fenti ne bayan d'igon da ake ganinta dashi.

Bayan rasuwarta sai rik'o na ya koma hannun Aunty saratu da tsawon shekara biyu kafin hatsarin mota ya zama sanadin rasuwar Babanmu, a lokacin ne kuma komai ya sake hargitsewa, aka raba gado sannan aka raba ni da Aunty Saratu, don ba yadda bata yi akan a bata ni ba, amma su Hajiya suka k'i yarda, wani zaice suna sona da gaske ne a lokacin, wani zaice suna k'okarin kare 'yancina ne na kar a kaini inda za'a dinga min kallon 'yar karo, sannan wani zaice zasu nuna min tarin gata ne sab'anin tulin bautar da nazo na tarar.

Gwaggo Lami da 'ya'yanta su suka cigaba da zama a gidanmu dake can bayan Babban gida saboda shi kansa gidan ma ya shiga cikin gadon 'ya'yanta maza, wanda ni nawa gadon ban ma san ina yake ba. Dawowata Babban gida ya zama sanadiyar yankewar karatuna na boko da islamiyya saboda Hajiya mai iko kad'ai a gidan a matsayinta na matar Kakanmu guda d'aya data rage tace Mamana ma bata yi ko d'aya daga karatun ba don haka bata ga amfaninsa akaina ba nima.

Nayi kuka da jimami kamar an sake min sabuwar mutuwa a lokacin, don Allah ya sani ina mutuk'ar son makaranta amma ba yadda na iya, haka na cigaba da zama tsawon shekara d'aya da rabi ba wanda ke koya min ko alif, sai tarin bautar da nake yi safe da rana, wanda in na samu d'an lokacin hutu ne kawai zaka ganni zaune a can k'uryar d'akin don ko waje Hajiya bata tab'a barina na fita, sai in shafe wata guda a cikin gida.

Daga inda nake zaune ina wannan tunanin, ina iya ganin yadda Hajiya take shan kokonta a hankali bayan ta zuba shi a kofin murfin filas d'in, navsan cewa da ta gama wani aikin ne zai biyo baya don haka na kishingid'a kad'an na rufe idona, sannan tunanina ta gangara kan mamallakin wannan muryar, wannan sabuwar muryar da ta shigo cikin rayuwata a yanzu take shirin bani sabon fata irin wanda na dad'e ina sak'a mafarkansa a zuciyata.

Sai dai banyi nisa a tunanin ba wani irin tari mai k'arfi yasa na bud'e idanuna na kalli b'angaren da sautin ya taho, abinda na gani yasa zuciyata ta buga sau uku da wani irin k'arfi sannan naji jinin dake jijiyoyina yana zuk'ewa. Hajiya kwance akan tabarmarta ta juyo tana kallona cikin ido yayin da jikinta ke girgizawa da k'arfi!

Bakinta yana fitar da wani irin farin yawu mai kauri sannan hannunta na hagu dunk'ule akan k'irjinta, d'ayan kuma yana baje akan tabarmar rik'e da kofin kokon nan. Na janyo dukkan k'arfin jikina na mik'e da sauri na isa gareta.

"Hajiya....me...me ya sameki?" Muryata ta fito cikin rawa.

Idona yana kallo tana k'ok'arin bud'e bakinta amma ba sautin daya fito illa yawan yawun daya k'aru wajen fitowa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..."

Na fad'a ina rufe bakina da duka hannayena, k'arar bugun zuciyata kamar zai fito waje, Idanunta sai faman k'iftawa da bud'ewa suke yi kwalla na zirarowa daga cikinsu, alamun tana cikin tsananin ciwo.

"Hajiya...Hajiya." Na shiga kiran sunanta da muryar da bata yi kama da tawa ba, amma bata iya amsawa.

Sai na mik'e da sauri na nufi k'ofa, amma wani tunani ya tsaida ni a daidai bakin k'ofar, ina zanje? wa zan kira? me zance ya faru? cewa kawai na bud'e ido na ganta a haka? hankali zai d'auka? ko kuwa wani zai yarda dani?

Na juyo na sake kallonta, idanunta na kallon rufin d'akin a yanzu, sannan fuskarta ta d'ashe, me hakan yake nufi? me ya faru kenan? ko dai alamar.... sai kuma nayi saurin katse kaina ban k'arasa ba, ba zan iya k'arasawa ba.

Na dawo da sauri na sake tsugunnawa a gabanta, a daidai hakan kuma k'arar shigowa b'angaren ta cika kunnuwana, sai na kasa banbance k'arar takun dana bugun zuciyata wanne yafi fitowa fili, Numfashi na ya tsaya cak! sanda murya tayi magana daga bayan labulen.

"Assalamu Alaikum, wannan 'yar tsohuwar tana nan?"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un...!"

A zuciyata nayi niyyar fad'a amma sai naji bakina ya furta hakan da k'arfi. D'agewar labulen d'akin ta nuna min fuskarsu tar! a cikin hasken safiyar, Salisu, Auwal, Sule, Yakubu da kuma wani da ban san sanshi ba. A lokacin ne kuma na tuna da abinda Yaya Sule ya gaya mata jiya dadaddare.

"Salisu yazo gari jiya, watakila gobe ma zai shigo ya gaida ki."

Sai tayi dariya tace.

"Ai kuwa ina maraba da maigidana."

"Me ya same ta? me kika bata?" Yaya Salisun da a lokaci d'aya ya karaso cikin d'akin ya fad'a yana girgiza jikinta.

"Na rantse... Na rantse da Allah ban sani ba kawai bud'e ido nayi na g..."

"Kamar yaya baki sani ba? Tun yaushe take a haka?" Yaya Auwal ya daka min tsawa wadda tasa na zabura zan mik'e tsaye.

"Kawai, Kawai, kawai... bud'e idona nayi na ganta..."

"Ku kamata mu fita da ita!"

Yaya Sa'id ya katse k'ink'inata, suka ciccib'eta gabad'ayansu suka yi waje, ni kuma na cigaba da zama a wajen ba tare da wani katab'us ba, don dukkan tunanina a lokacin ya tattara ne ya rataye a iska. Ba abinda nake iya yi sai kallon kofin kokon nan da kuma farin yawunta dake zube a k'asa.

Me kika bata?

Kalaman Yaya Salisun suka dawo cikin kaina.

Me kuwa na bata banda kokon nan? don in bashi ba na san ba abinda taci sai goronta na sanyin safiya, toh amma ta yaya koko kawai zai b'ata mata ciki haka?

Kafin in sake k'ok'arin wani tunanin, muryoyi suka shiga b'ulb'ulowa cikin d'akin sannan wani hannu ya cakumo ni ta wuyan rigata ya d'agoni sama, sanda kalla sai naga Aunty Sadiya ce bayanta fal da mutane.

"Me ya faru? me kika bawa Hajiya? nace don uw*rki me kika bata?"

"Na rantse da Allah Aunty, Wallahi Allah...."

Wani kyakykyawan mari mai zafi ya katse ni, naji zafinsa yana tafiya cikin kaina sannan a lokaci d'aya ya maida ganina dishi-dishi, na k'ifta idanuna da k'arfi amma ba abinda ya canja.

"Rantsuwa aka tambaye ki? cewa akayi me kika zuba a cikin kokonta?"

Muryar Ramatu ta fito daga wata siffa mai rawa.

Kokonta? Suma tunanin da suke kenan? Da sauri nace.

"Wallahi tallahi ban sani ba, bani ma na had'a kokon ba, Aunty Habiba ce ta had'a da nata, tace zata taya ni da ta ganni ina wanki, tace...."

"Laaahailah ha illallahu..." Muryar Aunty Habiban daga cikin mutanen nan ta katse tawa.

"Yaushe na ganki a safiyar nan bayan tashi na kenan yanzu naji ana hayaniya? ko kuwa wani ya taba ganina ma na damawa Hajiya koko a duk masu dama mata na cikin gidan nan? ba aikinki bane wannan? me nayi miki a duniyar nan Bintu da zaki kira sunana a wannan lamarin?" Sai kawai ta fashe da kuka.

Wani irin sanyi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikina lokacin da na zare idona akanta, duk wata ma'ana ta mamaki da firgita shine halin da nake ciki, kafin inyi wata magana kuma wani marin ya taho daga Aunty Sadiya ya sake maida ganin nawa dishi-dishi.

"Ke kad'ai ce kika tsani Hajiya a gidan nan Bintu, wa zai cutar da ita haka in ba ke ba? Innalillahi wa inna ilahir rajiun...." Sai ta sake ni muka sulale k'asa tare.

Amma Aunty Zainab ta finciko ni kafin in kai k'asa.

"Na rantse da Allah in baki fad'a mana gaskiya ba sai na kashe ki a wajen nan!"

Ta fad'a sanda ta janyo sandan dogoron Hajiya ta shiga dukana kota'ina, zafin dukan farko ya d'auke ni ya zagaya dani cikin duniya, na biyu kuma ya dawo dani cikin d'akin.

"Kar kiyi magana wallahi sai na kashe ki a d'akin nan koda kuwa hakan shine abu na k'arshe da zanyi."

Ta sake fad'a cikin kuka, kuma na tsinci muryoyi da yawa suna goyon bayanta.

"Aunty Sadiya! Aunty Sadiya!" Ba zato muryar umar ta kwararo daga cikin dimbin mutanen da suka shak'e k'ofar d'akin.

"Hajiya ta mutu!" Ya fad'a cikin ihu.

"Ta mutu."

Ya sake fad'a sai dai wannan karon a hankali kamar cikin sheshshek'ar kuka.

A cikin sheshshek'ar muryar tasa, na hango yadda rayuwata take gangarawa cikin bala'i.


________

8:00 PM

Kusan awanni tara kenan da suka shud'e tun bayan da aka tabbatar da rasuwar Hajiya Balaraba, sannan awanni hud'u da gama jana'izar binneta. Ta yaya ta mutu? ance wai an saka guba mai k'arfi ne a cikin kokonta wadda ta kasheta cikin 'yan mintuna k'alilan.

Ta yaya hakan ya faru? Labarin ya gama zagaye kewayen garinmu kaf! cewa nice da alhakin kisan, tare da kawo wasu tarin dalilan da suka maida labarin irin wanda hankali zai d'auka.

Ni kuma fa? ina k'ulle a wani d'aki na b'angaren gidan yayin da zaman makokin ya cigaba da gudana a can b'angaren Hajiya, sai dai kafin a k'ulle ni su Yaya Salisu sunyi min d'an banzan dukan da yasa na fita daga haiyacina, kuma a cikin tarin jama'ar gidan kaf! ba wanda yayi yunk'urin cetona in banda tururuwar 'yan kallon da aka samu wand'anda ke k'ara masu dukan.

Kawu Ibrahim, wan Babana shi kad'ai da ya shigo gidan ya taimakeni, ya rik'e bulalar daga hannun Yaya Salisu sannan ya waska masa mari tare da fad'an cewa bai san bashi da hankali ba sai a lokacin.

Daga nan ya ja ni zuwa b'angaren Babban d'an Hajiya wato Kawu D'anjuma, anan ne na kula cewa gidan ya fara cika da d'imbin mutanen dake tunkud'owa don tabbatar da labarin da yaje musu, ta cikinsu na hango Gwaggo Lami kuma kamar kowa a wajen idanunta cike suke da tsana, wata irin tsana fiye da wadda na saba gani a wajenta tun tasowata.

Sanda muka shiga b'angaren sai Kawu Ibrahim yace in tsaya daga gefe shi kuma ya shiga cikin k'aton d'akin da nake hango maza fal a ciki, na fahimci yawancinsu manyan gidan ne sai kuma wasu 'yan uwa na kusa. Daga inda nake tsaye jikina na d'agawar kuka, ina jiyo muryar Kawu Danjuma yana fad'in wad'anda zasu yiwa gawar wanka in an dawo da ita daga asibiti.

Bayan wani lokaci mai tsawo sai na jiyo muryar Kawu Ibrahim tayi magana ban san me yace ba ko me akace masa, amma lokacin daya fito sai kusan idanun kowa ya biyo bayansa suna kallona, jikina ya shiga b'ari sosai, saboda kallon da kowannensu ke min, kallo ne kamar na tabbacin cewa ni na kashe mahaifiyarsu... zan iya rantsewa naga hakan k'arara.

Daga nan Kawu Ibrahim ya kaini zuwa can b'agarensa ya k'ulle ni a cikin wani d'aki na yaransa k'anana, Ba kowa a gidan don duk wani mahaluki yana b'angaren Hajiya a lokacin.

"Komai zai daidaita insha Allah Bintu, ki zauna anan kafin in dawo."

Ya fad'a kafin ya tafi, ina iya jin sanda ya k'ulle kofar d'akin sannan ya fita. Sai kawai na sulale k'asa naci kuka mai d'imbin yawa har saida hawayen suka k'afe suka daina fitowa sai ajiyar zuciya kawai, sannan kuma wani zazzab'i mai zafi ya rufe ni.

Bayan wani lokaci na kifa kaina a jikin bango tunani da yawa na yawo cikin kaina, nayi-nayi in gano dalilin da yasa Aunty Habiba ta d'ora min wannan mummunan laifin amma na kasa, don kawai ta b'ata rayuwata ne ko kuwa wani abu ya faru tsakaninta da hajiya? duka biyun zai iya zama daidai amma na k'arshen yafi d'aukar hankalina... saboda rashin shirin dake tsakaninsu, amma duk da haka na kasa tunanin wane irin abu ne zai faru tsakaninsu da zai kai Aunty Habiba ga kashe Hajiya? Kashe surukarta? kuma ta binne ni a cikin laifin!

Tsawon zamana a gidan, nayi k'okarin binne komai na karb'i rayuwa a yadda yazo min saboda bani da zab'i, amma abinda ya faru yau ya bud'e dukkan ramukan cikin zuciyata, rushin dake binne ya sake ruruwa ya kama da wuta, kuma ina iya jin yadda yake k'one duk wani sauran fatana daya rage.

Me yasa rayuwata take cike da k'alubale ne?

Me yasa kowa ya tsane ni?

Ta yaya zan iya rayuwa mai kyau a yanzu?

Ya Rabbi!

Na san a duk duniya babu wanda zai yarda dani a wannan al'amarin irin

Please Login or Register in order to submit comment