Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinyar ma musamman daga America aka d'auko shi.

Sadiya. Tana daga cikin wannan cincirindon mutanen sai fara'a take sanye da wani leshi irin kwancen data samo a Abuja, wani zaice taron wani abin alkhairi daya same ta ake yi ganin yadda take ta zubar surutu tana k'ara nanata zancen da zata bayar a matsayin shaida daga gare ta.

"Gabana fad'uwa yake Salame, kin tabbatar kuwa da malam yayi aikin nan?"

Habiba data iso wajen bisa tattagowar da Kawu D'anjuma yayi mata ta fad'a tana duban k'awarta Salame.

"Na rantse da kabarin ubana Habi bani da shakka akan malamin nan, ni ban san sau nawa zan gaya miki hakan ba ki yarda, kin riga kin sawa zuciyarki k'ulafucin sai aikin na Kadunan nan ne zai ci, bayan da bakinki kika ce ai ko'ina ma sa'a ake samu kawai."

"Dole inyi shakka Salame, tunda har Kawu D'anjuma nace dake a k'ulle bakinsa daga zancena a lamarin nan bayan ita an kashe tan amma har yanzu yarinya na raye, kuma kina gani yadda aka sa Mudan ya tattago ni har nan a haka."

Ta fad'a tana kallon karyayyiyar k'afarta d'aya da kuma sandan da take dogarawa, a ranar da suka kama hanya zuwa Kaduna ne motar da suka shiga tayi hatsari, kuma wani abu na tsautsayi Salame ta fita babu ko kwarzane yayin da ita ta samu karaya a k'afa harda kuma gocewar k'ashi. Hakan ne yasa ta tattara kud'in da ta dad'e tana tarawa dubu d'ari da hamsin cif! Ta bawa Salame da tayi mata zancen wani sabon bokan da aikinsa ke ci kamar yankan wuka a nan gaba dasu kad'an.

"To me akayi da maza? Yanzu fa za'a fara shari'ar nan ko shiga bamu yi kinji me za'a ce ba, kar kiyi saurin yanke hukunci, don dama saida ya fad'a, aikin kisa da d'aure baki a lokaci d'aya abu ne mai wahala, don haka ki bari mu saurara dai mu gani."

Da wannan zancen Salame ta rufe bakin Habiba daga sake wani k'orafi amma daga ita sai ubangijinta suka san irin fargabar dake dukan zuciyarta.

Lokacin da lauya Bashir Kutama ya iso harabar cikin kotun, wasu ma'aikatan gidan jarida da kuma na rediyo da suka sami labarin abin suka tare shi tun daga wajen motarsa.

Bayan sun sanar dashi abinda ke tafe dasu ne d'aya daga cikin 'yan jaridan ya tambaye shi.

"Yallab'ai me zaka iya gaya mana game da wannan case d'in? Yaya kake ganin shari'ar zata kasance?

Kutama ya kalli camerar da aka saita don d'ukarsa hoto da murmushi sannan yace.

"Wannan shari'a ce mai sauki, a duk case d'in da na tab'a yi ban ma tab'a cin karo da mai sauki wanda komai yake a fili irin wannan ba, saboda haka abinda zan iya cewa shine zamu yi nasara nan da k'ankanin lokaci insha Allah."

"To yallab'ai me zaka iya cewa game da abokin takararka wanda akace kwararre ne tun daga k'asar America."

Ya sake wani murmushin mai kama da dariya sannan yace.

"Kow sarki ne a garinsu, don haka abinda zance fili nan ga mai doki, Allah ya bawa mai rabo sa'a!"

A wannan safiyar ta laraba dai, idanun Adam suka sami abincin da suka yi yunwarsa tsawon kwanaki, don dole ce tasa shi ya sake neman ganin Fadeelah kafin a fara zaman kotun, a cikin kwanaki hud'u kawai, kammaninta sun fara canjawa daga yadda ya ganta da farko, hasken farinta ya ragu sannan idanunta sun fara zurmawa cikin raminsu.

"Ki cire damuwa a ranki, komai zai tafi daidai da yardar Allah, zamu fuskance su kuma zamu yi nasara kinji?"

Babu yadda ya iya dole ya fad'a mata hakan cikin sigar lallashi, don ta fahimci duk irin k'arfin halin mutum akwai taraddadi ranar da zai fara shiga kotu a matsayin wanda ake zargi da kisa.

Bata kalle shi ba tace.

"Habiba tazo?"

Sai ya ya lumshe idonsa yana kallon yadda gashin idonta ya had'e dana k'asansa kamar a rufe suke, hakan ne kad'ai ya bashi damar iya kallonta hankali kwance.

"Kawu Ibrahim yace tazo, amma ban ganta ba."

Sai ta gyad'a kanta kawai alamun ta fahimta, sannan tayi shiru bata k'ara cewa komai ba.

Har ya mik'e tsaye sai kuma ya juyo ya kalle ta yace.

"Ina so ki yarda dani, kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."

Bata d'ago da kanta ba kuma bata ce komai ba haka ya juya ya fita, sannan mai tsaron da ya rako ta ya bata umarnin tashi don ana dab da fara zaman shari'ar a lokacin... Shari'ar data gujewa a baya, shari'ar dake shirin canja akalar rayuwarta.

***

Kotun ta cika ta kuma tunbatsa don har saida aka rufe k'ofa da wasu mutanen a waje. Zaune daga jerin wajen masu saurare, Kawu Ibrahim ne a gaba sai daga gefensa wasu daga cikin 'yan Babban gida masu irin ra'ayinsa a ciki har da Abdullahi daya zo tare dasu Mami, layi biyu bayansu kuma muk'arraban Kawu D'anjuma ne su Yahya, sulaimaman, da sauransu. Su Mami na daga bayansu ita da Aunty Hadiza da kuma Fatima wadda tayi tsuru-tsuru don har ga Allah ta shiga damuwar ganin Fadeelah a wannan matakin. A layi na k'arshe kuma, Nasir abokin aikin Adam ne daga can ma'aikatarsu wanda yazo a daren jiya a matsayin wakilin ma'aikatar.

Daga nan kuma duk mutanen Babban gida ne da kuma cikin Ikara mazansu da matansu kowa da irin abinda ke k'ulle a zuciyarsa.

Daga gaba teburin masu shari'ar kuma lauya Kutama ne zaune a gefensa da wasu k'ananan lauyoyin biyu masu taimaka masa.

Adam na zaune, daga gefensa kuma wani k'aramin lauyan gwamnati ne da kotun ta bashi don ya taimaka masa ta hanyar rubutu mai suna Jabir. Adam sanye yake cikin kaya na kowanne irin lauya amma sai ya fita daban da kowanne lauya dake cikin wajen, saboda yadda kalar hular ta kwanta akan fatarsa ta kuma fito da duk wata ilhama da kwarjininsa.

Zuciyarsa tayi nauyi ta kuma tsaida bugunta na wasu dakikai lokacin da aka shigo da Fadeelah cikin wajen, irin abinda yake gudu kenan gashi ya fara faruwa tun ba'a je koina ba, ina ga kuma ya bari sun fahimci juna?

Alkali Bashir Uba Ali (mai jagorantar shari'ar) ya shigo cikin kotun a daidai wannan lokacin, mai sanarwa ya d'aga muryarsa ya bada umarnin a mik'e da cewar zaman kotu ya fara kuma alk'ali ya zauna.

Bayan zamansa ne kuma, Alkalin yayi gyaran murya yace.

"Za'a iya zama, wannan shari'ar zata fara ne tsakanin masu shigar da k'ara da suka taru akan hakan da kuma wadda ake zargi Bintu Abubakar. Zamu iya farawa."

Bayan kowa ya zauna, Alk'ali ya juya ga Kutama yace.

"Shin masu shigar da k'ara suna da abinda zasu ce?"

Kutama ya mik'e tsaye a take.

"Kwarai ya maigirma mai shari'ah, kamar yadda kowa ya samu labari an shigar da wannan k'arar ne shekaru hud'u da suka wuce bisa zargin yarinyar dake zaune anan Bintu Abubakar wadda a lokacin shekarunta sun kai sha takwas akan kisan kakarta, ta hanyar sanya mata guba a cikin kokon da take dama mata a kullum safiya.

Amma k'arar bata kai ga isa mataki na gaba ba, sai yarinyar ta tsere a washegarin ranar da tayi kisan, anyi nemanta har zuwa garin Kano inda bayan bincike aka tabbatar da inda ta nufa kenan, kuma motar data hau d'in tayi hatsari a lokacin, amma aka samu sab'ani kafin hukuma ta isa ma'aikatan asibitin suka sallameta bisa rashin sanin ainhin dalilin rabuwarta da gida.

Kuma tun daga wannan lokacin bata k'ara waiwayar gida ba, saida a bisa fad'in marik'anta, sunce ta samu gushewar tunani ne a dalilin gatsarin nata wanda babu wata kwakwakwarar shaida data nuna hakan, don a lokacin da aka ganta, da bakinta ta furta cewa ta gane kowa kuma ta san laifin da ake zarginta dashi."

Ya juyo da idonsa kad'an ya kalli Adam fuskarsa d'auke da murmushi.

"Hakan na nuna cewa tana sane da laifinta kenan, kuma tana guje masa ne tsawon wannan lokacin, ya mai girma mai shari'a, akwai tarin hujjojin dake tabbatar da aikatuwar laifin nata wanda zasu zo a gaba kad'an. Nagode."

Ya koma ya zauna, Alkali ya juyo kan Adam dake nazarin komai da dukkan wata kafa ta fuskarsa yace.

"Masu karewa suna da abinda zasu fad'a?"

A hankali Adam ya mik'e tsaye sannan muryarsa mai taushi ta shiga kunnen duk wani mahaluki dake wajen cikin nutsuwa.

"Ya mai shari'a, Bintu bata aikata laifin nan ba, bata kashe kakakarta ba kuma ba kuma bata tab'a samun ra'ayin kashe ta ba, wasu sunyi amfani da damarsu akanta ne sun isar da niyyarsu ta kashe kakar tata, wanda a gaba cikin wannan shari'ar zan fito da hakan insha Allah, saboda haka da muryar adalci nake kira da kar kotu tayi saurin yanke hukunci ga yarinyar da bata da laifin komai."

D'an wannan tak'aitaccen bayanin ya gamsar da Alkalin wanda har haka yasa ya gyad'a kansa sau d'aya sannan ya juya ga Kutama.

"Masu shigar da k'ara zasu cigaba?'

"Kwarai ya mai girma mai shari'a kamar yadda na fad'a a baya, akwai tarin hujjojin da zai sa kowanenmu ya yarda cewa wannan yarinyar dake zaune fuskarta na nuna kammani irin na salihan mutane, kwararriyar mai kisa ce ..."

"K'orafi ya mai shari'a."

Muryar Adam ta katse bayanin kutama.

Alkali ya gyad'a kansa.

"K'orafinka ya karb'u, bai kamata mai zargi ya tabbatar da abinda shari'a bata yanke hukunci akansa ba."

Kutama ya duk'a kansa kad'an sannan yace.

"Ina sanar da kotu cewa akwai hujoji na mutane da kuma abubuwa wanda zasu tabbatar da zargina, amma kafin in fara kawo komai, ina son kotu ta fara da mutanen da kisan ya faru a kewayensu don muji ta bakinsu."

Alkali ya gyad'a kai yana kallonsa.

"Zanso in kira shaida ta farko, Sadiya Muhammad wadda k'anwa ce ga mahaifin ita Bintun da ake zargi da kisan."

Daga cikin masu saurare, Sadiya ta mik'e ta taho wajen tsayuwar masu shaida.

Magatakarda yace. "Ki fad'i sunanki kuma ki fad'i kowacce kalma dalla-dalla don za'a rubuta."

Cikin muryar dake shaida zumud'i Sadiya tace.

"Sunans Sadiya Muhammad, k'anwa ga mahaifin Bintu marigayi. S-a-d-i-y-a M-u-h-a-m-m-a-d.

Kotun ta d'auki shiru a lokacin da ake rantsar da Sadiyan kafin ta k'araso ta tsaya.

"Sadiya ina son ki shaidawa kotu kina da aure ko baki dashi?" Kutama ya fad'a tsaye a gabanta.

"Bani da aure a halin yanzu, amma a baya nayi aure sau biyu na fito."

"A shekarun baya, lokacin da Bintu take tare da Hajiya kina gidan ko bakya nan."

"Ina gidan don ba'a fi shekara da mutuwar aure na ba a sannan."

"Hakan na nufin kin san irin alak'ar dake tsakanin Hajiya da Bintu kenan?"

"Kwarai na sani."

"Zaki iya fada mana wani abun?"

"Tun tasowar Bintu dama bata son Hajiyar mu, bisa tarbiyar da mahaifiyarta ta d'ora ta akai na k'in mu dangin ubanta saboda mun nuna cewa bata da asali sanda aka tashi auro ta, don hakan ko bayan da iyayenta suka mutu rik'onta ya dawo wajen Hajiyar da wannan akidar ta taho a ranta, kuma aka sami akasi Hajiya bata maida ita makarantar bokon da take zuwa ba saboda BABU ta yau da kullum.

Sai wannan abun ma ya k'ara d'arsa tsanar hajiyar a zuciyarta, shi yasa mamakina kad'an ne lokacin da aka ce ta kashe Hajiyar tunda tun a baya dama ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da ita ba."

Fadeelah na daga can gefe idanunta kyam akan Sadiya, tana sauraren yadda take had'a karya da gaskiya waje guda tana tada wani sabon labari.

"Ta wace hanya kuke zargin ta kashe Hajiyar?"

Sadiya ta girgiza kanta.

"Ba zargi muke ba ai ranka ya dad'e, a cikin damun kokonta ta saka mata guba, tunda kowa ya san cewa tunda ta dawo gidan nan itace mai dama mata koko a kowacce safiya."

Kutama ya gyad'a kansa da murmushi yace.

"Kotu ta gode da wannan gudunmawar taki kwarai malama Sadiya."

Sai ya juya b'angaren Adam yace dashi.

"Your witness.."

Adam ya d'anyi shiru idanunsa na nazarin Sadiya daga inda yake kamar zai taso sai kuma ya girgiza kansa yace.

"Bani da tambaya akanta."

Hakan ya bawa kowa mamaki, Alkali ya kalle shi yace

"Baka da tambaya Barrister Adam?"

Ya sake girgiza kansa yace "Babu ya mai shari'a."

Da wani irin murmushi na k'eta kutama ya juya yace.

"Ina so kotu ta bani dama in gabatar da shaidata ta biyu ya mai shari'a."

"Kotu ta baka dama."

Kutama ya juya baya yace.

"Zan so in kira Sule wanda yake d'a ga wan Mahaifin Bintu."

Sule ya mik'e daga cikin mutane ya k'araso gaba, ya fad'i sunansa aka rantsar dashi sannan ya k'araso gaban Kutama.

"Sule, me zaka iya shaidawa kotu game da rasuwar Hajiya?"

Sule ya gyara tsayuwarsa sannan yace.

"A safiyar da Hajiya zata mutu ni ta bawa sak'o cewa in gayawa Bintu ta kai mata kokonta, kuma bayan ta had'a ta kai mata har gubar tayi aiki a jikinta, mu muka fara shiga d'akin dani dasu Salisu, sannan mu muka d'auke ta muka kaita har asibiti inda aka shaida mana cewa guba taci mai k'arfin gaske tayi sanadiyar mutuwar tata."

"Sule, a lokacin da kaje gayawa Bintu ta had'a kokon Hajiya me take yi?"

"Wankin kayanta take yi, kuma wankin ma da kyar ta karbe shi a ranar don har saida nasa baki sannan ta d'iba."

"A baya dama haka take yi?"

Sule ya girgiza kansa.

"Ko kad'an, ana bata zata tashi tayi."

Zuciyar Adam ta tabbatar masa da wani tunani a lokacin.

"Hakan na nufin a ranar bata yi niyyar wankin bane saboda ta riga ta shirya..."

"K'orafi ya mai shari'a." Muryar Adam ta katse kutama.

"Mai zargi yana kokarin bawa mai shaida sabon ra'ayi."

'K'orafi ya karb'u, lauya ya kiyaye."

Kutama ya sunkuyar da kansa sannan ya koma ga Sule.

"Sule a lokacin da kuka shiga d'akin, Bintu tana ciki?"

"Kwarai tana ciki don a gaban gawar ma muka same ta kuma idonta babu alamun tashin hankali balle hawaye."

Sai a lokacin da Sule ya fad'i haka ne sannan Fadeelah ta fahimci ma'anar kalaman Adam na d'azu.

...kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."

Kutama ya juya ga Alk'ali.

"Ina fatan kotu ta fahimci abinda hakan ke nufi, Bintu bata tab'a tunanin cewa wani zai shigo kafin ta tabbatar da mutuwar Hajiya har taje ta fad'a ba, shi yasa suka same ta a wannan yanayin na rashin alhini."

Ya juya ga Salisu yayi masa godiya sannan ya juyo ya kalli Adam yace.

"Your witness..."

A karo na biyu, Adam ya girgiza kansa sannan yace.

"Bani da tambaya akansa."

"Yayi kyau Barrister Adam, Dama gaskiya d'aya ce kuma a koina ba'a iya kalubalantarta."

Wannan maganar tasa kotun ta rud'e da hayaniya jama'a, Kutama ya jira har akasa surutun ya sassauta sannan ya kira shaidansa na gaba. Habiba.

Da kyar ta taso tana dogara sandanta aka rantsar da ita sannan ta tsaya.

"Hajiya Habiba, zaki iya gaya mana meye matsayinki a Babban gida?"

"Na'am?" Muryarta ta amsa a cikin kotun, Kutama ya sake maimaita mata tambayar a hankali.

"Ni matar wan mahaifinta ce."

"Ance mahaifin nata yana da yayye da yawa harda wanda ba uwa d'aya suke ba, shi wanda kike aure yaya alak'arsu take da mahaifin nata?"

"Uwarsu d'aya, shine d'a na biyu a wajen marigayiyar."

Ya gyad'a kansa alamun fahimta.

"Habiba kina a ina safiyar da Hajiya ta rasu?"

"Ina b'angarena ban ma fito da wuri ba sakamakon d'ana k'arami bashi da lafiya a lokacin, sai daga can naji hayaniya na lek'a aka ce dani wai Hajiya ce ta rasu."

"Me kika yi bayan nan?"

"Na tafi can b'angaren Hajiyar inda akace Bintun na can kuma ita ta saka mata guba a kokon data sha."

"Ance a ranar Bintu ta zarge ki da cewar ke kika had'a kokon ba ita ba."

"Wallahi k'arya take min ranka ya dad'e, na gaya maka ma ni ban ma fito da wuri a ranar ba kuma..."

"Kwantar da hankalinki Habiba, ai kowa anan yasa k'arya take miki, so nake kiyi tunani ki gaya mana shin akwai wani abu daya tab'a had'aku ne da har kike ganin zata iya dora miki wannan laifin."

"Eh ranka ya dade kowa ya san Bintu yarinya ce mai rashin kunya, to ni kuma a lokuta da yawa ina yawan kwab'arta akan hakan, kamar yadda dai marigayiya take k'okarin nusar da ita abubuwa a kullum, watakila saboda haka ne bayan ta kashe hajiyan, ni kuma ta nemi d'ora min wannan laifin."

Kutama ya gyada kansa.

"Na fahimta, bayan haknan akwai wani abu da zaki iya k'ara mana game da abinda kika sani?"

Habiba ta girgiza kanta da sauri.

"Allah ya sani ranka ya dad'e, ni ban fiye shiga harkar mutane ba, kowa zai min shaidar hakan, saboda haka ba zan iya cewa komai game da ita ba."

"Na fahimce ki Malama Habiba, na kuma fahimci irin abinda kike ji a yanzu, sharri bashi da dad'i musamman k'azafi irin wannan na kisa. Kotu ta gode sosai da wannan gudunmawar taki."

Ya juya ya kalli Adam.

"Your witness..."

Ga mamakin kowa sai ya mik'e a hankali ya karaso gaban Habiban da zuciyarta ke dukan casa'in- casa'in kamar ta na shirin fasowa daga kirjin nata ne a kowanne lokaci.

"Habiba.."

Yadda ya kira sunanta da wannan malalaciyar muryar tasa yasa wani abu ya tsarga mata har k'asa, taji tana k'okarin sakin fitsari a tsayen da take.

"A yadda rahoton yake babu wanda ya san Hajiya ta rasu har sai da aka kaita asibiti, ta yaya ke daga jin hayaniya kika lek'o akace miki Hajiya ce ta rasu? Sannan waye ya gaya miki?"

Habiba ta tsure ta rasa me zata ce, don ita har ga Allah ta manta ma ta fad'i hakan, to zancen da ba gaskiya ba.

Kotun tayi shiru, kowa ya tsira mata ido jiran amsa, ganin haka yasa kutama ya mik'e da sauri.

"K'orafi ya mai shari'a, Lauya na k'okarin tursasa...

"K'orafi bai karb'u ba."

Alkali ya katse shi tun kafin ma ya k'arasa, sai ya koma ya zauna zuciyarsa cike da haushi. Adam ya lumshe idonsa akan Habiba sannan ya sake cewa.

"Ya akayi kika san Hajiya har ta riga ta rasu a lokacin bayan ba wanda ya fad'a miki ma dalilin mutuwar, sannan waya ya shaida miki cewa ta rasun?"

Habiba bata da mafita sai wata k'aryar saboda haka ta hadiye wani tarin yawu a bakinta sannan tace.

"Ba zan iya tuna waye ya gaya min ba, sannan tunda aka fita da ita kowa ya gane cewa guba aka bata tunda kumfa nata fita ta bakinta."

Ga mamakinta sai ya gyad'a kansa kawai sannan yace.

"Mun gode Habiba."

Ya juya ga Alkali.

"Bani da wata sauran tambaya ya mai shari'ah."

Da haka ya koma ya zauna, Habiba ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi tana godewa wayonta, bata san cewa rami ta hak'awa kanta ba, don Adam ya riga ya gama abinda zaiyi ya d'aure ta da harshenta ba tare da ta sani ba, don yadda shaid'an ke shagaltar da bawa ga ayyukan zunubi ba tare daya farga ba haka Adam ke d'aure mai laifi da harshensa a kotu ba tare daya fahimta ba.

Shaida ta gaba da kutama ya kira Kawu Yahya ne, kamar sauran shima yazo ya gwamutsa k'arya da gaskiyarsa irin yadda suka shirya hakan tun a gida.

"Your witness.." Kutama ya fad'a sanda ya gama dashi amma sai Adam ya girgiza kansa alamun bashi da wata tambayar da zaiyi masa.

Ba sauran jama'ar kotun ba, hatta Fadeelah sai da ta d'ago ta kalle shi a lokacin, idanunta na haska tsantsar mamaki na rashin sanin inda ya dosa, ko kuma ma yana da tabbas cewa ya kama hanyar dosar wani wajen.

"Kotu ta d'age sauraren k'ara nan da ranar sha takwas ga wata, wato kwana uku masu zuwa, sannan kotu ta bada umarni a rik'e Habiba har zuwa sanda shariah zata daidaita."

Alk'ali Bashir Ali, ya shaida hakan sanda zaman kotun yazo k'arshe. Da wani irin sauri Kutama ya mik'e.

"Ya mai girma mai shariah, Habiba bata da laifi...."

"Baka da hurumin k'alubalantar abinda kotu ta yanke Barrister, sannan kuma baka da hurumin k'alubalantar laifin wani!"

Da wannan hukuncin wani mai zak'in murya ya kawo k'arshen zaman ta hanyar d'aga muryarsa yace.

"Koooootuuuuu!"

***

"Me kake yi ne haka Adam? Ka san cewa su Sadiya duk da suka tsaya a wajen nan k'arya suke fad'a, don me yasa su baka k'alubalance su ba?"

Kawu Ibrahim ya tambayi Adam a lokacin da ya same shi daga can bayan harabar wajen bayan yayi iya k'okarinsa wajen gujewa 'yan jarida da kuma tarin mutanen dake tururuwar jin ta bakinsa game da shari'ar. A hankali ya sauke muryarsa k'asa sannan yace.

"Baba, na san duk abinda suka fad'a k'arya ne, amma da ace na tashi na k'alubalance su, da duk cikinsu babu wanda zai bar kotun nan a yau, Habiba ita kad'ai nake hari a lamarin nan, shi yasa ita kad'ai na k'ulle!"

***

Baku tambayi ina Mairo ba, Mairon Bintu, Mairon Sadiq! Ya akayi har aka fara shari'ar nan babu labarinta?

Waye yarda cewa Adam ya kware a aikinsa???😁😁😁

Ina lawyers d'ina? Ya kuga zaman mu na farko?

Sai mun had'u a zama na gaba!


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

(☆_☆)

Mairo ta bud'e idanunta a karo na barkatai, don bata san iya adadin sau nawa tasha bud'e su tana komawa cikin mayen data kasance a cikinsa ba.

Cikin taimakon ubangiji wannan karon sai bata ji irin jirin dake sake maida ita duniyar data fito ba saboda haka ganinta ya tsaya akan wasu Nurses guda biyu dake tsaye a gaban gadon dake fuskantar nata, tun a baya kwakwalwarta ta fahimci a asibiti take, amma bata yi tunanin cewa har a yanzun zata farka ta ganta a cikinsa ba, duk da cewa kuwa ta san abinda ya sameta ya cancanci hakan.

Bugawar zuciya, ba ciwo ne da rana d'aya za'a sallameta ta koma gida ba, amma tsawon kwanaki nawa kenan take nan? Idonta ya juya kan agogon d'akin, k'arfe hud'u da 'yan mituna ya nuna, matsalar shine bata san wace k'arfe hud'un ba ta dare ce ko kuma ta rana? Amma a take kwakwalwarta ta shaida mata cewa idan har k'arfe hud'un dare ne wad'annan Nurses d'in da take gani a tsaye ba lallai ne a same su ba.

Saboda haka ta yunk'ura ta mik'e zaune, tana jin kowacce gab'a ta jikinta tayi mutuk'ar nauyi wanda hakan ke nuna cewa lallai ne ta dad'e a kwance.

"Sister Hawwa, 185 ta farka."

Muryar d'aya daga cikin Nurses ta fad'a sanda ta juyo tana kallon gadon nata dake d'auke da wannan number. A lokaci d'aya suka yo kanta gabad'aya, wadda aka kira da Hawwa ta d'ora bayan hannunta a k'asan wuyanta sannan tace.

"Sannu ya jikin naki?"

"Da alamun sauki, tunda a file dinta babu high blood sugar."

D'ayar ta fad'a, Mairo kallonsu kawai take yi ba tare da ta fahimci me suke cewa ba, don hankalinta yana kan wayar dake hannun wadda aka kira da Hawwa d'in, kamar kuwa ta karanci zuciyarta sai ta ajiye kayan hannunta har da wayar a gefenta ta juya ta shiga tab'a wani monitor dake gefen gadon nata.

Mairo bata jira komai ba tasa hannunta ta d'auki wayar ta danna ta, hasken daya kawo a screen ya nuna mata lokaci da kuma kwanan wata na ranar.

Laraba, sha biyar ga wata.

Kwakwalwarta ta shaida mata hakan a daburce, abin ya d'aure mata kai, taji kamar a cikin mafarki take, don gani tayi kamar jiya ne ta fad'i a band'aki Sadiq ya d'auko ta ya kawo ta asibitin nan cikin mawuyacin hali numfashinta na kakkatsewa... Bayan hakan abinda zata iya tunawa kawai shine an shigar da ita CCU (coronary care unit.) Likitoci da yawa suka taru akanta daga nan akayi mata wata allura da ta janye ta daga cikin tunaninta.

Amma duk da haka yaya za'ace har anyi kwana uku da hakan?

"Kawo wannan mu gani, hannunki akwai allura." D'ayar Nurse d'in ta fada tana kokarin karb'ar wayar hannun nata.

Sai dai ga mamakinta tana karb'ar wayar Mairo tasa d'aya hannunta ta cisge allurar drip d'in dake shiga jikinta, sannan tasa d'ayan kuma ta cisge wayoyin monitor da aka manna a hannunta.

"Ya salam.. Meye haka? Ina zaki?" Ta tambaya da tsananin mamaki ganinta diro daga kan gadon.

Bata ko saurare ta ba, idonta ya shiga bin d'akin da kallo, hijabi ko mayafinta take nema amma sai ta tuna ai daga cikin toilet d'in nan da ta shiga alwala haka Sadiq ya d'auko ta ba mayafi.

"Mijina yana nan?" Ta tambaya tana kallonsu su duka biyun.

"Yana nan, yazo harda sauran 'yanuwanki ma, yanzu ki koma ki zauna zamu kira miki su."

Sai tasa duka hannayenta biyu ta kwance d'ankwalinta ta maida shi yanayin yafe.

"Ina zaki je? Kinga ki dawo ki zau..."

D'aya daga cikinsu tayi kokarin rik'eta amma ta fincike hannunta da karfi ta nufi k'ofa. Ta san sun biyo ta amna hakan bai dame ta ba ta kama hanyar fita waje da iya saurin da zata iya, don sunfi shekara biyar da yin rijista da asibitin, ta riga ta san kowanne lungu da sak'o na

Please Login or Register in order to submit comment