Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fahimci sune marik'an Bintun da komai ke faruwa saboda ita.

Idon sa ya juya kan motar 'yan sandan da suka diro rik'e da bindigoginsu, a sannan ne yaga sanda d'aya daga cikin 'yan sandan ya bud'e gaban motar dake rufe da bak'in gilashi, a sannan ne kuma idanunsa suka hango masa Fatima Bintun dake zaune cikin bak'ar jallabiya da bak'in mayafe yafe a kanta.

Ya k'ifta idonsa ya sake bud'ewa amma ya kasa yarda wai Bintun da ya sani a baya yake gani a yanzu, wannan yarinyar dake shafe yinin ranarta a kullum cikin bautar Hajiya, wannan marainiyar data rasa duk wani gata da tallafin duniya bayan rasuwar iyayenta, wannan Bintun dai da ta bar gida da wannan cukurkud'adden hijabin da yayi mata gani na k'arshe a cikinsa.

Ta yaya Sadiya ta iya gane ta a wannan kammanin? Ya san ita fara ce amma wannan farin nata ya zarce na Bintun daya sani, kamannin ma sun fik'e sun zarta na wannan yasasshiyar marainiyar daya sani a Babban gida.

Ba don 'yansandan da kuma su Yahya ba, ya tabbata ba zai shaida cewa wannan ce Bintun da shari'a ke jiran zuwanta ba.

_____

4:06PM.

Ba'a bari Kawu Ibrahim ya samu ganinta ba har saida aka gama duk wasu cike-cike da tsare-tsare wanda Bintun tayi su babu musu kamar injin da aka saita akan hakan, daga nan aka bata cell a cikin kotun kuma aka umarce shi da sai yabi hanyar da mutum ke bi don ganin mai laifi.

A d'akin da ake ganin masu laifin ya zauna sannan mai tsaro guda d'aya ya fito da ita, ta k'araso ta zauna a kujerar dake fuskantarsa yayin da mai tsaron ya koma ya tsaya daga gefe.

Sai a yanzu da yake kusa da ita, sannan yaga kammanin Bintun daya sani a baya, ya d'an tsaya ya kalle ta idanunsa cike taf da alhini, kafin ta gaishe shi da muryarta mai rawa, sai yace.

"Yaya jikin naki? Ance yau aka sallamo ki koh?"

Sautin muryarsa ya dawowa da Fadeelah komai game dashi, zuciyarta ta tare ta kuma goge tsawon wannan lokacin data bar gida, taji a ranta cewa a jiya ne kawai komai ya faru, a jiya ne yazo ya tashe ta tsakar dare yake shaida mata cewa za'a kaita police station da safe, a yau kuma gari ya waye gasu a cikinsa, saboda haka maimakon ta amsa sai tace.

"Kawu kayi hak'uri, rashin mafita ne yasa na gudu na bar gida, amma wallahi bani na kashe Hajiya ba, ban kashe ta ba kuma ba zan tab'a iya kashe ta ba, na fad'a maka tun a wancan lokacin."

"Na sani Bintu, na fahimci komai ba sai kin maimaita ba, don komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci abinda ke gabanmu a yanzu, na samo lauyan da zai kare ki, d'anuwanki ne ma, d'an k'anina Ahmadu da kike ji a baya ana cewa ya b'ata, shine ya nemo mu bayan bakya nan yazo har Babban gida a cikakken lauyansa, munyi maganar dashi kuma zai zo ya ganki gobe insha Allah, ina so ki fad'a masa duk wani abu da zaki iya tunawa don Allah."

Sai ta d'ago da idonta ta kalle shi, har sai an rok'e ta ma? ita da a yanzu take neman duk wata hanyar da zata iya samun nasara akan Habiba da kuma su Kawu D'anjuma, don ta karyata tunaninsu akanta ta kuma nuna musu darajarta na d'iyar 'yar gudun hijirar da suke gudu.

"Kawu, naga Mairo ma a can."

Ya gyad'a kansa sau d'aya.

"Haka Sadiya tace, har ana tunanin tare kuke sai daga baya su Yahya suka ce itama taje nemanki ne a lokacin."

"Wallahi tun bayan tafiyata ban taba ganinta ba sai a ranar da Aunty Sadiyan ta ganni itama."

"Kar ki damu Bintu, zancen Mairo mai sauk'i ne, naki daya had'a da hukuma shine a gabanmu yanzu, amma na san Adam zai yi duk kokarinsa don ganin munyi nasara akansu."

Jimlar sunan Adam ta dawo da wani tunani akanta, tunanin wannan Id card d'in dake cikin purse a kuma k'arkashin kayanta, amma sai tayi saurin ture shi, hakan ba abu ne mai muhimmanci yanzu ba.

"Bintu mutanen da suka rik'e ki masu karamci ne, munyi magana dashi Alhajin kafin yayi tafiyar data kama shi, Allah ya kaiki cikin kyakykawan hannu ki gode masa."

Bakinta yayi nauyi da jin hakan, don ta rasa ta ina ma zata fara gaya masa irin tarin alkhairi da kuma karamcin su Mami.

"Na gansu har su hudu sunzo, kuma sun tabbatar min maigidan ma zai taho da zarar ya dawo."

Sai ta kasa daurewa kawai, bakinta ya shiga furta masa duk wani tarin alkhairin su Mami a gare ta, tun daga ranar da suka kad'eta a mota, har zuwa sanda suke shirin bikin aurenta da jininsu. Hakan ya d'auke su kusan awa d'aya tana zayyane masa duk wani abu daya faru da ita bayan barinta daga cikinsu har zuwa dawowarta yanzu.

Sai bayan daya tafi, mai tsaron nan ya sake rakata cikin cell dinta sannan komai ya dawo mata sabo, duniyar tayi duhu sannan ta had'u ta dunk'ule a cikin idonta, sai kawai ta koma can k'arshen cell d'in ta dukunkune jikinta waje d'aya.

Komai zai kare a d'an kankanin lokaci, komai zai wuce kamar ba'ayi ba, idan nayi bacci a yanzu zan farka inga an kammala komai, kamar yadda duk wani abu daya faru bayan barina daga Babban gida ya shud'e.

Da wannan k'aryar ta lallab'i kanta ta bari magungunan baccin da Mami ta bata kafin a shigo da ita ciki, suka sami damarsu akanta.

_____

WASHEGARI.

08:30AM.

Bayan rabuwarsa da gidan Kawu Ibrahim a lokacin, Adam ya shiga tunanin irin tambayoyin da zai yiwa yarinyar da aka shaida masa sunanta Bintu. Ya riga ya gama tara tulin bayanai akanta daga wajen Sa'id da kuma Kawu Ibrahim d'in daya had'u dashi a yanzu.

Zai iya cewa ya san duk wani bayani game da ita na abinda ya shafi rayuwarta a IKARA, ya san asalinta tun daga tushensa har zuwa kan sanda ta gudu bayan zargin da ake mata, abinda ya rage kawai, shine yaji komai daga bakinta ya kuma san wani abu game da rayuwar da tayi bayan barinta Ikara daga marik'anta wanda Kawu Ibrahim d'in ya tabbatar masa da zai had'u dasu a kotun bayan ya gana da ita.

Ya juyo ya kalli Sa'id dake tuk'a motar da suke ciki, ya fahimci shi gabad'aya al'amarin nan ma baya kansa, harkokinsa kawai yake yi kamar baya cikin dangin da ake wannan rikicin, amma shi bai san me yasa ba, tun daga ranar da Kawu Ibrahim ya kira shi cewar ya koma lauya mai kare yarinyar nan ya kasa samun nutsuwa a zuciyarsa, kullum tunaninsa yana kan shari'ar ne da kuma son ganin an fara ta... Amma shi Sa'id d'in daya san komai ma kuma akayi a gabansa bai damu haka ba.

Idonsa ya koma kan titin sanda suka k'araso bakin gate d'in shiga kotun, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya gayawa kansa cewa 'An fara.'

Sa'id yayi parking a layi na k'arshe daga cikin jerin gwanon motocin dake harabar wajen sannan suka fito bakid'ayansu suka shiga wajen, wani mai tsaro ne ya kaisu har ofishin wanda ya kamata su gani. Adam ya mik'a masa Id card d'insa sannan yace.

"Barka da aiki yallab'ai, suna na Adam Ahmad, nine lauyan da zai kare wadda ake zargi a shari'ar da za'ayi ranar goma sha biyar ga wata, nazo in gan..."

"Kar ka damu na fahimta, dama tun safe take jiranka."

Mutumin ya fad'a sannan ya mayar masa da Id card d'insa.

Adam ya d'an tsaya da mamaki yana kallonsa, Tana jiransa? Waya gaya mata ta jira shi?

"Habu, jeka ka kaisu inda zasu zauna."

Mutumin ya fad'a yana kallon mai tsaron daya rako su.

***

Muryar mai tsaron nan na jiya ce ta yakice Fadeelah daga nauyayyan baccin da take yi, don har aka kwana aka tashi k'arfin magungunan nan da aka bata basu sake ta ba, ta fahimci dama amfaninsu kenan da aka bata daga asibitin, don ta samu isashshen hutu da nutsuwa akanta wanda zai sauk'ak'a ciwonta.

"Kina da Bak'o." Muryarsa ta fad'a sanda yake k'ok'arin bud'e cell din.

Sai ta d'ago da fuskarta daga dandaryar simintin da take kwance sannan ta murza idanunta don son wartsakewa.

Kwakwalwarta ta fahimci bak'o yace, don haka a take ta gane basu Mami bane da take jiran zuwansu, lauyan da Kawu Ibrahim yace mata zai zo ne.

Yaya ma sunansa? Adam ko?

Ta mik'e a hankali jikinta ba kwari sannan tabi bayan mai tsaron zuwa magamar bak'i.

_____

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

28

(☆_☆)

"Inaga bari inje daga waje in jira ka a can."

Sa'id ya fad'a sanda suka fito daga ofishin mutumin nan, Adam ya juyo ya kalle shi.

"Saboda me? Baka son ganinta ne?"

Ya d'aga kafad'unsa kad'an.

"Yaya tunda ta dawo ai zan ganta, akwai wayar da zanyi ne shi yasa."

Sai ya gyad'a masa kai kawai sannan ya bishi da kallo bayan yayi gaba, ko dai Sa'id ma baya goyon bayan shari'ar nan daya karb'a ne? Ba abin mamaki bane hakan tunda mahaifinsa ma yana goyon bayan su Kawu Da'anjuma ne basu ba, ya rasa wace irin k'iyayya ce suke wa yarinyar nan haka.

"Ranka ya dad'e nan zaka shiga, yanzu za'a taho da ita."

Mai tsaron nan da yayi can gaba ya fad'a yana nuna masa wata k'ofa, sai ya maida Id card d'insa dake hannu cikin wallet sannan ya nufi wajen k'ofar, yaji shiga ya samu kujera ya zauna, duk wata kafa ta jikinsa ta shiga aiki a don bai taba jin son haduwa da client d'insa ba a tsawon shekarunsa na aiki kamar yanzu.

Daga d'aya b'angaren d'akin wata k'ofa ta bud'e, wani mai tsaron ya shigo sannan biye dashi ita.

Fadeelah ta kalli koina a d'akin bata ga kowa ba, tayi tunani zata zo ta sami mai neman nata zaune yana jira kamar yadda taga Kawu Ibrahim jiya.

"Yallab'ai gata nan."

Muryar mai tsaron ta musanta tunaninta, sai a sannan idonta ya kai gefe inda wanda aka kira 'yallab'ai' din ke zaune.

Wani irin tsoro ne da fargaba suka haska cikin idanunta lokacin da kwakwalwarta ta shaida mata abinda ta gani... Wane irin magungunan bacci ne haka da baza su sake ta ba har yanzu? Sai ta juya baya da sauri ta murza duka idanunta biyun da duka ragowar k'arfinta, saboda babu ta yadda za'ayi ta yarda da abinda take gani.

Sai dai me? Da ta sake juyowa ba abinda ya canja, idanunta dai wani mutum mai siffar Adam d'in data sani a can America take gani, wannan karon shima ya mik'e tsaye sannan wad'annan lumsassun idanun nasa na nuna mamaki makamancin nata.

Ta girgiza kanta da sauri, wannan mafarki ne ba zai yiwu ba, ta sake juyawa baya ta mutstsika idanunta sannan ta k'ara juyowa... Ya salam! Tayi zaton kwakwalwarta ta warke daga dukkan wani ciwo, in ba haka ba me yasa take nuna mata kammanin Adam har yanzu?

Sai ta tsaya kawai ta kasa gaba ta kasa baya, ta kuma kasa daina kallonsa, kwakwalwarta na bata shawarar cewa ta koma ta k'arasa ragowar baccin dake kanta zata ga komai ya dawo daidai, zata dawo ta tarar da wani mutum a matsayin lauyan nata na gaske.

Abu na farko da Adam ya fara lura shine idanunta, ya tsaida ganinsa akansu cike da tsantsar mamaki, wad'annan idanun da kullum ke manne cikin nasa, idanun daya shiga duk wata gwagwarmayar rayuwarsa kuma ya fito tare dasu, idanun da a lokuta da yawa suka zama abinda ke bashi kwarin gwiwa da juriya, Sannan idanun da bayan shekaru kusan biyu ya cire rai da sake ganinsu... Idanun Fadeelan Washington!

Abinda ya fara fahimta kenan kafin kuma wani mamakin ya dake shi a tsakiyar kansa... Don babu wata kwana-kwana kwakwalwarsa ta saita masa cewa Fadeelan daya sani a America ita ce dai Bintun da yazo gani.

"..a cikin watan nan zamu koma k'asarmu, don haka jarabawar da muke ta wannan tanadin don ita ba zan sami damar yi ba."

Maganar ta a ranar da zasu rabu na karshe suka haska cikin kansa, sannan ta Kawu Ibrahim a d'azu.

... Bayan barinta daga wajen mu, ance tayi kusan shekara biyu a k'asar America tare da marik'an nata kafin su dawo...

Hakan kad'ai ya isa ya fahimtar dashi duk wata amsa da yake nema, amma da mamaki, da mamaki ace duk duniya k'addara Fadeelah kawai ta zabo ta d'ora a wannan muhallin, ya had'iye yawu a mak'ogwaronsa kad'an sannan ya karb'i shawarar da zuciyarsa ta bashi a lokaci guda.

"Ki k'arasa ki zauna." Mai tsaron nan ya fad'a daga gefe ganin bata da niyyar k'arasawa, a nasa tunanin rashin gaskiyarta ne ya sa mata shakka.

Bai daina kallonta kamar yadda itama take kallonsa har sanda ya nuna mata kujerar gabansa alamun ta zauna, sai komai ya canja a idanun Fadeelah, d'akin ya juye mata zuwa library d'in makarantarsu na can washington, taga kamar a lokacin da suke lesson dinsu na Maths ne, banbancin kawai, wancan Adam d'in sanye yake da kaya irin na matasan can da kuma gashinsa a barbarje, wannan kuma farar longsleeve ta k'asan suit ce a jikinsa, gashinsa a kwance kuma a tsare sannan alamu na girma da class sunfi fitowa a wannan na tsayen. Sai ta rufe idonta sannan ta sake bud'ewa, ya Allah! In har shine da gaske ta yaya yazo nan? Waye ya kawo shi? Sannan me yake yi anan d'in?

Sai dai kamar yadda ya samu amsarsa itama ta samu tata da kalaman Kawu Ibrahim na jiya.

...na samo lauyan da zai kare ki, d'anuwanki ne ma, d'an k'anina Ahmadu da kike ji a baya ana cewa ya b'ata, shine ya nemo mu bayan bakya nan yazo har Babban gida a cikakken lauyansa...

Kanta ya sara, ciwonsa kuma ya shiga kokarin dawowa, abun yayi mata yawa, bayan duk wannan ace kuma Adam d'in da ta baro a can America d'anuwanta ne? Kuma shi zai karb'i shari'arta?

Ganin bata da niyyar motsawa, sai shi ya k'araso gabanta ya tsaya, a lokacin k'amshinsa ya ziyarci hancinta, wannan k'amshin da tun a baya ta yiwa tambari da NASA.

"Sunana Adam, nine lauyan da zai kare ki."

Muryarsa tana nan yadda take, mai taushi tana bi ta kan fatar ta a hankali, amma ba hakan ne ya bata mamaki ba, da hausa fa yayi maganar... Da hausa, hausa yarenta, anya Adam d'in data sani ne kuwa?

"Nazo ne inyi miki wasu tambayoyi kafin ranar da za'a fara shari'ar."

Ya sake fada' yana kallonta, me yake nufi? Bai gane ta bane ko me? Ta yaya zai kasa gane ta?

"Zaki iya zama sai muyi maganar?"

Da gaske yake? Da gaske yake ba zai ce ya gane ta ba? Ba zai kira sunanta da leelah ba?

Tabi hannunsa da kallo sanda ya janyo mata wata kujera a gefe, sannan ta dawo da idonta kansa sanda yace.

"Ga waje ki zauna."

Ya Allah! Hausa yake yi har yanzu.. Ta yaya ya iya hausa? Ta kasa yi masa musu saboda haka ta matsa ta zauna, mamaki na cinyeta a kowacce gab'a ta jikinta. Shima ya zauna a wata kujerar yana fuskantar ta.

"Kafin in tambayeki komai, ina son ki sani cewa duk abinda zamu tattauna yanzu taimako zaki yiwa kanki, kuma zai tsaya ne tsakanina dake kawai, amma ina son ki fada min gaskiyar duk abinda zaki iya tunawa a wancan lokacin."

Da turanci yayi maganar yanzu, hakan na nufin ya gane ta kenan? Ya san tana jin turanci, to me yasa ba zai ce ya gane tan ba? Sai kuma kwakwalwarta ta tuna mata da mai tsaron nan dake bayansu, watakila don shi yake yi baya son ya san akwai sanayya a tsakaninsu.

Sai ta yanke shawarar biye masa itama, amma Allah ya sani akwai tarin tambayoyi fal! A bakinta, Me ya faru? Ta yaya yazo nan? Da gaske Id card din nan ke fad'a dama shi lauya ne? To me yaje yi makarantarsu a lokacin? Ya akayi ya zama d'an uwanta kuma yanzu? Ya musulunta kenan? Yaushe ya musulunta...

Ya bud'e wata 'yar k'aramar jotter a hannunsa sannan ya zaro biro yace.

"Zaki iya gaya min wace alak'a ce tsakaninki da Hajiya Balaraba?"

Ta kasa yarda wai da abinda zasu fara kenan, ta kasa yarda ba zai fara gaya mata duk abubuwan da suka faru dashi bayan rabuwarsu ba, sannan ta kasa yarda itama ba zai tambayeta komai ba zasu d'auki yau ne a matsayin had'uwarsu ta farko.

"Hajiya kakata ce wadda ta haifi mahaifina."

Da kowanne harafi, muryarta na shaida ba abinda take son fada kenan ba.

"Ke kika kashe ta?"

"A'a..." Muryarta ta fito da tsantsar yak'ini. "Bani na kashe ta ba."

"Lokacin da take raye akwai rashin jituwa tsakaninku?"

Kai tsaye tace.

"Hajiya bata k'aunar mahaifiyata wanda hakan ne nima ya shafe ni tun tasowata, amma ban ban damu ba saboda ba'a wajenta nake ba sai bayan iyayena sun rasu ne na koma wajenta da zama."

"Saboda bata sonki shi yasa kika kashe ta?"

Sa ta ware dara-daran idanunta akansa cike da mamaki.

"Na gaya maka bani na kashe ta ba, babu wani dalilin da zai sa in kashe ta."

Sai ya koma da baya ya d'an jingina da kujera da yake kai.

"Zaki iya fad'a min wani abu da kika sani game da mutuwar tata?"

Ta gyara zamanta kad'an, sannan ta shiga zayyana masa duk abinda zata iya tunawa a ranar da Hajiya ta rasu, sai dai hakan ba abu ne mai sauki ba, don tana bayanin tana jin tension d'in dake tsakaninsu na k'ara yawa, tana jin ba haka ya kamata ya zancen ya fara zama ba.

Kallonsa kawai take yi da tsantsar mamaki wanda tsaf! Ta san ya fahimci hakan amma ya cigaba da yi mata tambayoyinsa hankali kwance, saboda haka a k'arshe itama ta dake tata zuciyar ta zuba masa ido kawai don taga iya gudun ruwansa, wanda kuma ta gani d'in don har bayan kusan awa d'aya da ya gama tattara duk wasu bayanai da yake nema daga gare ta, bai bada ko alama d'aya da ta sake nuna mata cewa shine Adam d'in data sani a America ba, in ka d'auke wannan k'amshin nasa da sautin muryarsa da baya tab'a canjawa.

Da kowacce kalma data fad'a, Adam ya tace ta tsaf a cikin kansa kuma ya yarda cewa bata da laifi kuma bata wayo, bata da wayo da har yanzu da bata iya gano ainhin wadda tayi kisan ba, sai zargi da take kamar kowa.

"Kin tabbata iyaka abinda kika sani kenan?"

Muryarsa a hankali ta tambayeta bayan kusa awa d'aya yana
tattara bayanan dake fitowa daga bakinta.

Ta d'aga kanta ba tare da kallonsa ba.

"Bintu.."

Muryar tasa ta kira sunan a tsaye, kuma kowanne harafi ya fito dalla-dalla kamar dama ya saba fad'a ne, sai ta d'ago ta kalle shi, idanunta na shaida karyewar da zuciyarta tayi tun daga can k'asa, don a lokacin ta gama tabbatar da cewar da gaske yake ba zai nuna ya santa ba, itama kuma ta yanke shawarar baza ta tab'a fara nuna cewa ta sanshi d'in ba.

"Ina so ki fahimci cewa zanyi dukkan iya kokarina in taimake ki a lamarin nan, amma akwai wata 'yar matsalar da muke da ita a yanzu, wad'anda suka shigar da k'arar nan sun riga sun tanadi isassun hujjojin da in kotu ta gamsu za'a iya yanke miki hukunci a d'an k'ankanin lokaci, shi yasa nake so ki tabbata duk abinda kika gaya min yanzu daidai ne kuma babu k'arya a cikinsa."

Nazarinsa kawai take kuma idanunta basu d'auke daga kansa ba har kusan sakanni talatin kafin tayi magana da wani irin sauti mara amo.

"Kawu Ibrahim yazo nan jiya kuma ya riga ya fad'a min cewa in gaya maka duk abinda na sani dasu zaka yi amfaninka fitar dani daga nan wajen, don haka duk abinda na gaya maka gaskiya ne Lauya, kuma babu wani abu da zan k'ara akai!"

Lokacin da Adam ya koma makwancinsa (Temporary gidan da Sa'id ya kama musu) a ranar, ya tabbatarwa kansa cewa shawarar daya d'aukarwa kansa tayi daidai, ba zai tab'a nunawa kowa cewa ya sa Fadeelah a baya ba, har ita kanta kuwa, in ba haka ba aikinsa ba zai tab'a tafiya daidai ba, zai bari zuciya da kuma feelings d'insa su jagorance shi akan case d'in, ya samu raunin da zai dakushe shi ta wani b'angaren, abinda bai tab'a ba kuma baya son a fara da yanzu, yanzun da yake rik'e da shari'ar da zata nuna yadda alak'ar DANGINSU zata kasance a gaba.

Ya hasko yadda take kallonsa da wad'annan idanun nata masu tasiri akansa, ya san tana cike da mamakin abinda yayi amma kuma yaji dadin yadda itama ta rik'e sanin da tayi masa sannan ta biye masa suka yi komai kamar yadda yake faruwa tsakanin kowanne lauya da client d'insa. A yanzu ya san komai game da ita amma akwai tarin tambayoyin da bakinsa ke son furtawa game da wasu abubuwan da basu shafi case d'in ba.

Yasa hannu ya murd'a ruwan shower dake zuba a kansa ya koma na sanyi kalau, so yake sanyinsa ya k'arfafa shi, ya daskarar da kwakwalwarsa wajen tunaninta amma yak'i yiwuwa, ganinta a yau bayan tsawon lokaci ya bud'e komai, ya fallasawa kansa cewa yayi kewarta a baya, musammam wad'annan idanun nata...

Ya Allah! shi fa ba yaro bane, idan a baya ya bari har zuciyarsa tayi abubuwa irin na matasa to ai komai ya wuce kuma ya canja a yanzu, ya zama cikakken mutum mai d'imbin ayyuka a gabansa, bai kamata ya bari wani shirme ya dame shi ba.

Dole ne ma ya kange zuciyarsa, ba zai k'ara zuwa ganinta ba sai hakan ta kama!

***

A cikin kwanaki hud'u kawai Adam ya tattara duk wasu isassun bayanan da zasu ishe shi ya fara tunkarar shari'ar, sannan bayan duk wasu tare-tsare na kotun ya samu kira daga alkalin da zai jagorancin shari'ar yaje ya had'u dashi da kuma lauyan da su Kawu d'anjuma suka d'auko mai suna Bashir Kutama.

A lokacin ya k'ara fahimtar yadda su Kawu D'anjuma suka d'auki shari'ar nan da zafi, don Bashir Kutama babban lauya ne daya shahara a garuruwa daban-daban na arewacin Nigeria, bai san nawa suka narkar don d'auko shi ba, amma ya san cewa sunyi hakan ne da fushin abinda Kawu Ibrahim yayi musu kuma sun narkar da kud'insu akansa ne da tunanin kwarewarsa zata yi tasiri a shari'ar.

Yaje Ikara har sau biyu, bayan kuma bayan Kawu D'anjuma da yaga canjin fuska daga gare shi, babu wanda yaga wani abu daga wajensa, kowa ya sakar masa fuska sosai, har zancen shari'ar sai da suka yi dasu Kawu Bashir inda anan yaji cewa Kawu D'anjuman ya hana kowa daga Babban gida zuwa wajen Fadeelah.

Hakan ya tabbatar masa da cewa za'a cika a kotun kenan ranar fara shari'ar, don ya san hatta mutanen gari zasu nik'i gari ne su taho har cikin birnin Zariya.

A kusa da kotun da za'ayi shari'ar ya samu wani office mai kyau yayi hayarsa inda zai dinga ganawa da duk mutanen da zasu shafi bincikensa hankali kwance.

Sai dai bayan tsare-tsaren shari'ar, office d'in ya zama kamar wani waje dake kange shi daga komawa wajen Fadeelah, don ranar daya sake komawa kotun ma yayi magana da marik'anta, bai nemi ganinta ba.

Ya sake magana da Kawu Ibrahim, kuma ya k'ara samun duk wani sauran bayanin da yake nema daga gare shi, sai dai kamar yadda ya b'oyewa kansa shima bai shaida masa cewa ya san Fadeelah a America ba.

A daren da ya zama washegari za'a fara shari'ar, Adam ya kasa wani bacci cikakke, tunani fal ke yawo akansa game dayadda komai zai kasance, shari'ar Nigeria daban ce da wadda ya saba a America, yaga hakan akan case biyu daya k'alubalanta bayn dawowarsa, ba daga alk'alan kad'ai ba, mutanen nan suna da wani irin taurin kai da sai sunga abu k'iri da muzuru sannan zasu yarda, amma a America in har akwai shaidu na gaske da suka tabbatar da abu to shari'a zata iya yadda dasu ba sai anja da nisa ba.

Amman Nigeria, sai kowa yaga komai dalla-dalla tukunna, shi yasa tunaninsa ya kasa tsayawa waje d'aya, lalube kawai yake yi a cikin kansa ta yadda zai fito da komai ya baiyana bayan tsawon shekaru da faruwarsa.

Idanunsa biyu tar ya kwana!

***

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

29

(☆_☆)

K'arfe goma na safiyar laraba sha biyar ga wata za'a shiga shari'ar, amma tun kafin takwas mutane suka fara tururuwar zuwa don samun wuri kafin ya cika, 'yan Babban gida kaf matansu da samarin 'yayansu, hannu kawai d'aya zai d'ebe wad'anda basu zo ba, sannan banda 'yanuwa ga jama'ar gari dama wad'anda suka tsinci zancen a titi, kowa yazo cike da zumud'in d'aukar rahoton yadda shari'ar zata kaya, musamman da jita-jita ta zaga koina cewa ai lauyan da zai kare

Please Login or Register in order to submit comment