Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da 'yan uwanta, gashi mijinta yana da kud'i sosai amma bata da taimako, ko 'ya'yanta ma haka suke, Shi yasa a abubuwa da yawa kowa ma mantawa yake dasu.

Maza sun fi yawa a jikokin gidan, hud'u ne suka yi aure, uku 'ya'yan Baba Habibu sai d'aya d'an Mama Balaraba sannan mace d'aya Maryam da ita kad'aice tayi aure a cikin matan.

***

Lokacin da Fadeelah ta sauka k'asa da niyyar zuwa kitchen, Su Mami na zaune su shida a falo suna hira, da Haj. Saddika matar Baba Sani, kasancewar ita a gidan b'angarensu yake sai Mama Balaraba, Aunty Hadiza da kuma Aunty iyami, sai 'yar tsohuwa Hajiya Amarya.

Ranar Asabar ce, kuma kamar kowanne k'arshen mako a sabon tsarin da aka fara su Mami na zuwa gidan mahaifiyar tasu ne gabad'aya da 'ya'yansu don sada zumunci, sai dai kusan matan ne kawai suke zama, don mazan ko sun zo, 'yan mintuna kad'an ne kawai zasu tafi harkokinsu, Baba habibu ne kad'ai wani lokacin zai kai har magariba yana zaune ana hira, sai dai yau baya nan yayi tafiya Lagos.

Kafin Fadeelah ta shiga kitchen tana jiyo dariyar da suke tayi wa Mami Safiyya kan wani abu data fad'a, har Aunty iyami na cewa anya baza su tattara su koma k'asarsu ba kuwa don wai ko su Faruq ma har yanzu basa iya fad'ar wani abin a hausa.

A cikinsu gabad'aya, daga Mama Balaraba sai matar Baba Habibu sune kad'ai basa sakar mata fuska sosai, amma su Aunty Hadiza babu ruwansu sun karb'eta kamar yadda Mami ta karbeta cikin rayuwarsu da farko, musamman Hajiya Amarya, yadda take mata baya banbantuwa dana jikokinta ko kad'an, kuma kullum ta ganta sai ta tuna da mai sunan da aka saka mata... k'anwar hajiyan Daddy, wadda taji a bakinta cewar hatsari tayi ana dab da bikinta ta rasu.

A kitchen d'in, ta tarar da Saifudden d'an gidan Baba Habibu yana sirka lemo da ruwa, bata tab'a ganin mutum mara son sanyi irinsa ba amma duk da haka kullum cikin mura yake, watakila yanzu babu lemon ne sai a fridge shi kuma yaga ba zai iya hak'ura ba, ta gaishe shi a hankali sannan ya matsa mata ta d'auki ruwan, har taje bakin k'ofa ya tsaida ita cikin dusashiyar muryarsa ta alamun mai mura.

"Rahma tana nan?"

Ta d'aga kanta.

"Eh, tana nan."

Yayi shiru kamar zai bata sak'o sai kuma yace.

"Shikenan kawai."

***

Sanda ta fito daga kitchen d'in, ta tsinci muryar Abdullahi, d'an gidan kawu Isma'il yana magana zaune a gabansu Hajiya, su Zahra, Sameera da Sahla na gefensa kowaccensu fuskarsu tasha kwalliya d'al da ita ga kayayyaki da takardu kamar na certificate a hannunsu.

"Wallahi fa Mama, kawai Nasir ne yace inzo muje zai d'auko mamanshi daga wajen bikin yaye wasu masu koyon kwalliya da akayi wanda har da k'anwarsa a ciki, shine fa muna zuwa naga yaran nan a wajen wai suma har dasu aka yaye, sai d'aukan hotuna ake yi dasu, wai ita Zahra ma har wata kyauta aka bata don tafi su sanin wasu tips d'in kwalliyar. Ashe har watansu biyu suna zuwa babu wanda ya sani."

Cikin tsananin fushi Mami Safiyya ta kalle su tace.

"Waye ya baku kud'in da kuka je kuka biya su?"

Zahra tafi su sanin halin Mami, don haka kai tsaye tace.

"Abbansu Sahla muka tambaya."

"Ai dama wallahi sai da na kawo a raina, in ba Abba ba wa zai basu kud'in nan."

Cewar Aunty Hadiza, don sarai ta san halin mijinta wajen shagwab'a yara.

"Yanzu Audullahi tunda kaga wajen, d'aukarsu ka maida su kuce musu ba'a san sun biya daga gida ba, su maido muku da kud'in."

"Hajiya kud'i fa sun riga sun tafi tunda har an gama ba mai dawo dasu, sannan dan girman Allah sunana Abdullahi, haba dan Allah."

Haj. Saddika tace.

"Babana kaima ka san fa haka ta iya fad'a ba yadda zaka yi."

Yace.

"Wa? Hajiya a da kenan, amma ranar da kunne na ni da Salim muka ji tace Abdullahi sak!, don baya nan ne da ya tabbatar muku wallahi."

"Ai dama akwai randa za'ayi sa'a ta fadi hakan." cewar Mama Balaraba.

"Kai ku kyale ni dashi nace Audullahin, je ka kaini kotun k'oli a tsire ni."

"To ba gwara kai bama tana k'arasawa..." cewar Aunty iyami.

"Abdul da take kira da Auduwa fa."

Sai dukkaninsu suka kyalkyale da dariya har da su Zahran da aka tasa a gaba da farko.

***

Wata ranar Laraba, Farkon azumin watan Ramadan kuma ana saura kwana biyu dawowar Daddy daga Washington, Rahma da Fatima suka zo gidan Mami da niyyar d'aukar Fadeelah suje siyayyar kayan Sallah wanda Baba Habibu ya ba basu kudi gabada'ya har da ita, wannan itace sallarsu da zasu yi ta farko a Nigeria, bayan zuwansu.

"Wai har wata siyayya ake yi da yawa? ni nayi zaton kayan da za'a saka ranar idi ne kawai."

"A k'auyenku na k'asar turawa kenan, anan garin activities ake had'awa har sai kin gaji, don ma bamu da sarki ne da kinga hawan doki na kwana da kwanaki."

"Eh acan ma ana activities d'in amma baya wuce ranar idi dai."

Fatima tace.

"Dan Allah ku taso mu tafi ko zamu samu mu dawo da wuri, wallahi azumin yau da d'an wuya."

Bayan sun gama siyayyar a cikin wani katafaren shago da Abdul da Faruq suka kaisu, suka iso wajen biyan kud'i inda daga bayan cashier akan rataye 'yan alawowi da kuma magazines ko 'yan riguna don k'arin talla, anan idanun Fadeelah suka hango mata wata magazine guda d'aya ta fashion daga gefe ajiye cikin wani rack, hoton wani kyakkyawan saurayi ne a ciki mai kama da tsantsar jinsin shuwa ko fulani, amma ba wai kammaninsa ne suka d'auki hankalinta ba, A'ah gashinsa, style d'in gashinsa yadda ya kwanto gaban goshinsa a barbaje... sak! irin yadda Adam ke yiwa gashinsa ne.

Adam. Wani halitta guda d'aya da har yau zuciyarta ta kasa manta shi balle alkhairinsa, tayi kokarin shafe duk wani abu na rayuwar washington dan ta bud'e sabon shafi na rayuwar da take ganin itace tata, ciki kuwa harda k'awayenta su Melissa da bata biye hirarsu a social media, sai dai lokaci zuwa lokaci su gaisa kawai, balle kuma 'yan uwan Daddy na can da dama ba wani sabawa dasu tayi ba.

Sai dai mutum guda biyu ne kawai manne cikin tunaninta, Al'ameen da duk sanda taga su Rahma tare da samarinsu musamman in suna waya sai ta tuna shi a wannan kwanakin da suka shafe tare kullum mak'ale a waya cikin wata guda d'ayan nan tal!, ko kuma duk sanda wani abu ya bata dariya sai zuciyarta ta hasko mata hotonsa, don shine mutum na farko daya fara koya mata wata hanyar nishad'in ta daban a sabuwar rayuwarta.

Amma Adam zata iya cewa kusan kullum yana mak'ale ne cikin ranta, Allah ya sani a cikin shekara guda data rabu dashi ba zata ce ga wata rana data zo har ta fad'i bata ga wani abun daya tuna mata dashi ba, kai wani lokacin hatta ta cikin reflection d'in cokali kawai sa ta hango fuskarsa a ciki, tun abin na damunta har dai tazo ta yarda cewa, kirkin da yayi mata ne kawai ya manne tunaninsa a cikin ranta.

Sau da yawa sai tayi tunanin cewa zai iya nemanta a wancan layin da a yanzu ba zaiyi amfani a k'asar nan ba, amma kuma sai taga me zai nemeta yace? abinda ya had'a dasu ya riga yazo k'arshe kuma for crying out loud har yanzu shi ba musulmi bane, ina wannan ragowar tsanar da bata gama fita daga ranta ba?

"Muje Deelah.."

Rahma ta katse tunaninta sanda ta mik'o mata wasu daga cikin ledojin da aka d'ura kayansu. Ta karb'a sanda idonta ya sake kallon magazine d'in, fuskar Adam ta haska a maimakon ta kai, da wannan lumsassun idanun nasa yana kallonta.

"Kun san Allah, wata shekarar sai dai ku nemi mai kawo ku siyayya, don ba zai yiwu kuzo ku shanya mu a mota wajen awa guda a banza ba."

Abdul mai bin Rahma ya fad'a sanda suka koma wajen motar.

"Toh uban 'yan mita, shi Faruq dake tuk'in ma baiyi magana ba sai kai." Cewar Fatima, Rahama tace.

"Rabu dashi wata shekarar ma ina zai ganmu, sai dai ya kai 'yan matansa, yayi jiran banzan nan gaske."

"Ai gwara wannan, dama ni na matsu a senda ku wallahi, in banda aike ba abinda kuka sani, ku dai kawai azo ayi muku."

Sun gama saka kayan a booth suna shirin shiga motar amma zuciyar Fadeelah ta kasa nutsuwa, hango magazine d'in nan kawai take yi tana ganin kamar Adam ne zata tafi ta barshi a baya.

Suka shiga motar, farouq ya tayar, yaja suka bar harabar parking lot d'in, zuciyarta ta tsinke, idonta ya hango mata ranar da suka yi sallama da Adam, sai ta kasa daurewa.

"Faruq dan Allah ku tsaya, nayi mantuwa ban siyo wani abin ba."

"Me kika manta?" Rahma ta tambaya.

"Wannan mayafin da Asiya tace a d'auko mata? mun siyo ai."

"A'ah, wata magazine ce naga wani abu da zan duba a ciki, bari inyi sauri."

Bata ko bari Faruq ya juya ba, ta fita daga motar, ta shiga ratsawa ta tsakanin motocin dake jere a wajen har hanyar data sada ta da k'ofar shagon ta baya, ta dinga wuce mutane akan benen daya kaita hawa na uku, ta k'arasa wajen inda ake biyan kud'in nan... Sai dai me?

Wajen da magazine d'in take fanko, babu ita ba alamarta sai sauran gasu nan rututu!

"Dan Allah wata magazine da na gani yanzu a wajen nan nake nema."

Mutumin ya kalli wajen data nuna sannan yace.

"Yanzun nan aka siye ta wallahi, ina tunanin ma kin had'u da matar da ta siya a hanya."

"Ya salam! Babu wata kuma?"

"Babu irinta gaskiya, amma ga wasu na fashion d'in nan..."

"A ina kake ganin zan sami irinta?" Ta katse shi da sauri.

"Kai, kusan ta wata shida baya ce fa, ta dad'e ne anan ba'a siya bane da sai ince ki duba k'asa ko wasu shagunan, amma yanzu da wuya gaskiya ki same ta wannan watan, sai dai kamfanin amma..."

Bata tsaya jin k'arshen zancen ba, ta bazama k'asa hawa na biyu, ta tambayi cashier d'in nan shima yace mata Babu, haka tayi ta bi waje-waje cikin shagon nan amma babu alamun magazine d'in nan mai irin gashin Adam. Daga k'arshe ta koma wajen cashier ta tambaye shi yanayin matar data siya, ya zaiyana mata cike da mamakin me zata yi da magazine d'in haka.

Sai da ta tambaya sannan itama taga shirmenta, matar fa ta riga ta gama siyan kayanta ta tafi, a ina zata ganta? Haka ta koma wajen su Rahma da suka fara mamakin dad'ewarta da nauyin zuciya.

Sanda tazo kwanciya a wannan daren data k'ara hasko hoton magazine d'in a idonta, da sanda ta juya baya ta tafi ta barta, da sanda ta juya bayan sunyi sallama da Adam ta tafi ta barshi tsaye a jikin motarsa, sai taji wani abu mai kama da kwalla ta cika idanunta!

***

BAYAN SATI DAYA.

A lokacin an shigar tsakiyar azumin Ramadan Daddy ya dawo, wata ranar Lahadi ce da daddare bayan ansha ruwa Faruq da Abdul da yanzu suka zama direbobin k'arfi da yaji suka je suka d'auko shi, su a can airpot d'in ma suka sha ruwa saboda sai da suka jira saukar jirgin tukunna.

Gidan ya rud'e da murna sanda ya shigo su faruq suka biyo bayansa da kaya. Iman ta d'ane shi tana ta ihu yayin da bakin Mami ya kasa rufuwa, shima murna yake sosai don hatta Zahra sai da ya d'aga ta har sama, a cikin sati uku kawai sunyi kewarsa kamar shekara uku.

"Naga wannan abin a hanya na siyo miki."

Muryar Faruq ta fad'a daga gefen Fadeelah sanda ya shigo janye da wani akwati da bana Daddy bane.

"Wanne?"

"Kadaya yake ko me?"

Ta zare idonta da sauri, ta gane kad'anya yake nufi, wani abu da take mutuk'ar so tun daga ranar data fara shansa a wajen Hajiya Amarya.

"Da gaske kake Faruq?"

"Allah kuwa, yana mota bari in ajiye wannan in d'auko miki."

Ai tana jin yace mota tabi ta bayansa da sauri ta fita daga falon, yadda suka yi parking motar a harabar gidan tana fuskantar ta ne, don haka taga booth daga baya a d'age amma bata damu da tunanin me yasa ba'a rufe shiba, ganin ma sauran kofofin motar duk a bud'e suke.

Ta san Abdul ne yayi driving don haka ta gefen kujerar mai zaman banza ta zagaya ta bud'a, ilai kuwa, sai ga kad'anya fal a ciki wata yellow leda, ranta yayi fari k'al a take, sai dai kuma a taken farin cikin nata ya rugurguje har garinsa, tsantsar mamaki ya maye gurbinsa!

Taji sanda aka sauke booth d'in motar, sai dai kafin ta iya juyawa wannan muryar ta shiga cikin kowacce jijiya dake amfani da harkar sauti a jikinta.

"Hello, memory loss girl!"

Wannan husky muryar ce mai cike da tarin kwarjini.

A hankali ta juya gefe, cikin kallo d'aya idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala fiye da wanda ta sani a baya!

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... ta biya hakan ta kuma tuno da tsohuwar haddar da ta yiwa kammanin Al'ameen!

●﹏●

Waye ya hango k'addarar data fara a shafin nan?😀



BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

13

(☆_☆)

"Jiya Daddy yake gaya min naji haushin maganar sosai Miryam, ace muna zaune a gari amma har Al'ameen zai zo ya bi wasu abokanan aikinsa su sauka a hotel? ko bamu da guri ne ai sai haka."

Mami ta fad'a a safiyar washegarin da Al'ameen ya kwana a gidan, suna cikin kitchen ita da Fadeelah a lokacin suna had'a abincin karin safe, yayin da sauran 'yan gidan ke can kowa na fafutukar shiryawarsa.

Ta cikin wayar muryar Aunty Miryama tace.

"Ai ba wani abu bane Saffiya da baku d'orawa kanku d'awainiya ba wallahi, watak'ila shi sai yafi sakewa ma acan."

Daga yanayin fuskar Mami bata ji dad'in maganar ba, amma sai ta daure tayi murmushi kad'an kafin tace.

"Da nan d'in da can duk d'aya ne ai babu takura Miryaam, shima kuma na san zai so..."

Fadeela ta d'auke hankalinta daga kan saurarenta ta juya wainar kwai ta k'arshe da take soyawa sannan ta kwashe ta a cikin plate. Daga daren jiya zuwa yau bata san me take ji a ranta ba, watakila abu biyun da suka damu zuciyarta ne suka had'u suka zuk'e duk wani emotion d'in da take dashi, kuma ta karb'i hakan hannu biyu don ita kanta a yanzu bata da tabbacin abinda take ji.

Har yanzu akwai wani nauyi a gefen zuciyarta tun daga ranar data rasa wannan magazine d'in mai irin gashin Adam, nauyin daya zama kamar wani abu daya k'ara ingiza tunaninsa a ranta, har ya kai ta binciko takardun lesson d'insu don kawai kullum ta kalli rubutunsa, wannan tsantsareren rubutun da kamar buga shi akayi tsabar tsaruwarsa daki-daki, ta dad'e da fahimtar cewa komai nasa a tsare yake cikin nutsuwa, kamar wannan muryar tasa da in yana magana dole ne ko waye ma ya saurare shi.

Yanzu kuma ga zuwan Al'ameen, wani mutum da tayi kokarin yakicewa daga zuciyarta a baya, ta daurewa kanta ta hana shi yin tasiri a rayuwarta har zuwa lokacin da take ganin sun nesanta da juna, ashe k'addara ta tanadi wata hanyar, don ta d'auki wannan zuwan nasa a matsayin k'addara duk da cewa aikin gabansa ne ya kawo shi... k'addarar da take tunanin zata saita ta a yanzu da iya kokarinta.

Ta jera dukkan abinda ta gama soyawa a tray sannan ta fita dasu falo, Tv a kunne take tana nuna labaran BBC yayin da Daddy ke zaune a kujerar dake fuskantarta, a gefensa Al'ameen ne shirye cikin wata hadaddiyar gray suit kamar an auna ta a jikinsa, ya fito a kamanninsa na matashin lauya, hasken safiyar ya haska mata kyawun fuskarta da bata gani gabad'aya a daren jiya ba, kyawun fuskar daya rud'e ta a baya ta fad'a tarkonsa cikin wannan watan guda d'aya!

Magana suke yi da alamu mai muhimmanci, don ya sunkuyar da kansa kad'an yana kallon Daddyn, amma fitowarta yasa ya wulkito da idonsa ya kalle ta tsaye daga kofar kitchen d'in, sai ta juya da sauri ta nufi dining ta ajiye tray d'in sannan ta koma, haushin kanta taji sosai yadda ya kamata tana kallonsa.

"Deelah, fito da dankalin daga cikin fryer nan."

Mami ta fad'a har a lokacin tana waya, sanda ta koma falon babu kowa don haka ta shiga jera warmers d'in data d'auko a gefen sauran kayan kan tebur d'in.

Motsin tsayuwarsa a kusa da ita taji ba tare da taji sanda ya taho ba, ta rufe idonta a hankali had'e da guntuwar addu'a don bayan gaisuwar jiya, bata so ko kad'an wata magana a kusa ta k'ara had'a su, sai dai ga mamakinta bai ko kalleta ba wata 'yar guntuwar sannuki da aiki' kawai yace sannan ya jawo kujera d'aya ya zauna ya fara k'ok'arin d'aukan plate.

"Aunty deelah, ga spoon d'ina nan baki saka ba."

Muryar Iman ta katse ta sanda ta fito sanye cikin uniform d'inta, saboda haka bata amsa masa ba ta ajiye cokalin Iman daga cikin na hannunta sannan ta koma kicin, sanda ta kawo plate d'in Daddy ta k'ara juyawa ne muryarsa ta katse ta.

"Uhm, Fadeelah..."

Zuciyarta ta buga da nauyi, ya Allah! wai ta manta ne cewa ya iya fad'ar sunanta haka? bata juyo ba yace.

"In akwai tea bag na lemon ki taho min dashi dan Allah."

"Baza'a rasa ba kam, ki duba cupboard d'in can gefe daga sama."

Mami ta sake katse amsawarta sanda ta k'araso ta ajiye k'arin wani flask na ruwan zafi, Iman ta juyar da kai game da kokarin tab'e dogon hancinta.

"Mami k'amshin man suya kike yi da yawa."

Bata san me Mamin tace ba, amma tana jiyo dariyarsu daga kitchen d'in har da Al'ameen, wannan dariyar tasa da ada take saka ta nishadi kamar me.

K'arfe bakwai dai-dai sanda kowa ya fito aka zauna cin abincin, Al'ameen yana ta hirarsa da dariya musamman shi da Faruq wanda ke ta bashi labarin abubuwa da ya sani yanzu a Nigeria, har Zahra itama ta shiga hirar tana gaya masa cewa ita kanta yanzu da za'a koma America to banda ita, Sai dai yadda ka san Allah bai halicci Fadeelah dake zaune a tsallaken kujerarsa ba, haka bai ko kalle ta ba, balle yayi mata magana.

Wanda kuma saboda son zuciya, sai rashin kulatan yasa taji ba dad'i kad'an, son zuciya mana! in ba son zuciya ba ta manta abinda tayi ne? ta manta abinda tayi shekara guda data wuce? ta manta abinda tayi masa a tsakiyar makarantarsu?

Fadeelah ki tsaya ki saurare ni dan Allah, I want to talk to you, kin hana ni ganinki tsawon lokaci... kin san yadda nake ji kuwa?

Babu maganar data rage tsakaninmu, na gaya maka kayi hakuri ba zai yiwu ba.

Komai ya riga ya yiwu Fadeelah, saboda na riga na fara sonki kuma na san ke ma kina sona, saboda haka ki bani damar da zan nuna miki duk wad'annan dalilan naki na shirme ne basu isa su tsaida mu ba.

Ta rufe locker data d'ebo litattafanta sannan ta kalle shi, yana tsaye dab! da ita yadda litattafan ne kawai suka yiwa jikinsa da nata katanga, sai ta matsa baya kad'an.

Ni a wajena babu shirme a cikinsu Al'ameen, in kana tunanin kwakwalwata tana da matsala ne shi yasa ka fad'i hakan...

Ya katseta ta cikin d'imbin hayaniyar d'aliban dake wucewa a bayansu.

Kin san ba haka nake nufi ba Fadeelah, abu mai muhimmanci anan shine muna son junanmu, me yasa zamu wahalar da kanmu...

Ban fad'a maka ina sonka ba Al'ameen.

Da na san bakya sona babu abinda zai sa in damu kaina tsawon lokacin nan, kuma har na biyo ki nan...

Fargabarta d'aya a lokacin kar su Melissa su k'araso su gansu tare, don tunda ta yanke duk wata alak'arta dashi bata son k'arin wasu mutane a rayuwarta su san dashi.

Bana sonka Al'ameen, idan baka yarda da abinda na fad'a a baya ba, ka gayawa zuciyarka wannan ka fita daga rayuwata.

Maganar ta dake shi, amma sai yayi murmushi kad'an sannan yace.

Kinyi kokari, kin fad'i abinda ni ba zan tab'a iyawa ba, duk don ki cutar da kanki...

Haushi ya fara kamata, me yasa ne wai ba zai fahimce ta ba? ta d'ago da idonta ta kalle shi.

Hanyar lafiya nake kokarin nemowa kaina Al'ameen, kaine yanzu kake kokarin cutar dani ta hanyar da zaka amfani kanka kai kad'ai.

Kamar yaya?

Zuciyarka ta gaya maka tana sona, saboda haka kana k'okarin bata abinda kake so ne kawai ba tare da tunanin halin da ni zan shiga ba.

Na gaya miki...

Baka gaya min komai ba Al'ameen sai son zuciyarka kuma na fahimce ka sarai saboda haka nima ka fahimce ni ka fita daga rayuwata, na fad'a maka bana sonka kuma bana sonka a cikin rayuwata.

Tayi maganar ne da k'arfi cikin hasala kuma da harshen turanci, saboda haka mafi yawanci d'aliban dake baya da kuma gefensu suka juyo suka kalle su sannan wasu suka fara dariya, wannan dariyar ita ta keta zuciyar Al'ameen gutsi-gutsi, ransa ya b'aci, yaji ya muzanta a tsakiyar yaran da kowannensu bai kai sa'an k'aninsa mai bi masa ba, da ace yana dashi d'in kenan, sannan wata irin kunyar kansa ta kamashi a gaban 'yar k'aramar Fadeelan da shashashar zuciyarsa ta jawo masa raini a wajenta.

Abinda ta fad'a a gaba shi yayi sanadin guntule alak'arsu tun daga wancan lokacin.

Idonta na kallon cikin nasa tace.

Wallahi bana sonka Al'ameen, kuma bana tunanin zan tab'a sonka!

***

"Ranar ashirin ga watan september a shekaru biyar da suka wuce kamfaninku yasa hannu akan yarjejeniyar had'in kai tsakaninku da kamfanin Dibbons P.C dake America a birnin Washington. Daga cikin k'aidojin yarjejeniyar akwai dokar data had'a da cewar zaku dinga turo 40% na ribarku a kowacce shekara.

A shekaru biyun farko da suka biyo baya kun aika da ribar, amma daga nan kowacce shekara sai ku kawo uziri na matsalolin da kuke fuskanta da suke hana ku samun wata kwakkwarar riba, don haka a yanzu kamfanin ya turo mu, mu ma'aikatansa da kuma wasu daga cikin lauyoyin kamfanin don mu tabbatar da dukkanin hujjojin da kuke bayarwa kuma muga komai da idon mu."

Mark Bowden, d'aya daga cikin ma'aikatan da Al'ameen yazo yiwa kamfaninsu aiki ya fad'a yana kallon jerin mutanen d'aya kamfanin da suka zo bincike akansu k'asar Nigeria. A yanzu farkon fara aikinsa dole ne ya rik'e matsayin Solicitor (lauya mai bincike a waje) kafin ya kai matsayin Barrister da zai dinga aiki tare da organization kawai, kamar yadda tsarin ma'aikatarsu yake.

Fatansa ma shine ya had'a biyu, ya rik'e muk'amin da ba kowa ke iya rikewa ba wato matsayin Solicitor da kuma Barrister kamar wani kwararren lauyan daya gani abokin kamal, duk da b'angaren da yake da nasa yasha banban amma yana fatan shima ya iya kawo hakan cikin aikinsa.

Matashi ne kamar shi, amma yana da wani irin k'ok'ari da hazak'a da yawan ma'aikatu irin nasu na lauyoyi suka san dashi, a d'an iya sanin da yayi masa daga nesa zai iya cewa shine role model d'insa a yanzu, ya yardarwa kansa cewa yana son zama irin ADAM STEVE a aikinsa, don shi d'in daban ne a cikin lauyoyi masu irin matakinsa.

A lokacin wata mace daga cikin mutanen d'aya kamfanin ta mik'e don yin bayanin dake cikin file d'in hannunta, ya kalli mayafin data yafa, irin kalarsa Fadeelah ta d'aura a kanta yau sak! tayi wani d'auri mai kyau yana reto a gefe d'aya.

Yaja tsaki a k'asan numfashinsa, shi ya san har yanzu bai yarda da zuciyarsa akanta ba, shi yasa tun farko baiyi niyyar sauka a gidan ba sanda aka had'a har da sunansa a masu tafiyar, amma zuwan Daddy ya tsaya akan cewar babu hotel d'in da zaije ya sauka alhali suna gari d'aya.

Fatansa d'aya ne a yanzu, kar yawan ganinta a kullum yasa alkawarin daya d'aukowa mahaifiyarsa ya kwance, don kamar yadda Fadeelah ta fad'a masa a baya ne, haka itama ta biya masa kuma tasa ya haddace cewar...

Abinda yake tunani tsakaninsu ba zai tab'a faruwa ba!

Saboda haka a yanzu yana yin komai ne bisa tsarin da ta kafa masa tun lokacin da taji Daddy ya kafe sai a gidansu zai sauka, yana bin duk maganganunta d'aya bayan d'aya.

Matsalar shine... bai tabbatar in hakan zai d'ore ba.

***

"Gobe zamu je sayayya dasu Sahla." Zahra ta fad'a da yamma tana tsaye a gaban mudubi tana taje gashinta."

"Me zaku siyo?" Iman ta tambaya daga k'asan gado inda ta baje litattafanta tana homework.

"Kayan da zamu yi decoration na class party mana,

Please Login or Register in order to submit comment