Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanke farcensa yace wai bai iya ba sai kin dawo zaki yanke masa."

Tayi kokarin maida kwallarta sanda yarinyar ke tambaya.

"Momy yaushe zaki dawo? Zaki dawo?"

Har kusan yamma Muhammad bai yarda yazo wajenta ba, harkarsa kawai yake kuma duk wanda zai d'auke shi zai yarda amma banda ita, zuciyarta duk tabi ta cunkushe sannan Aunty Hassanah kuma tayi ta binta da kallon 'Me na gaya miki?'

Sauk'in da ta samu d'aya ne da su Zakkiyan suka tashi tafiya anan suka barsu da yake dama da kayansu aka zo, kuma kamar lokutan baya Sadiq bai nemi ganinta ba haka su Aunty Rabi ma basu yi mata zancensa ba, gaisuwar da suka zo don ita kawai suka yi suka tafi.

Afrah na mak'ale da ita duk inda tayi, amma Muhammad a wajen Aunty Hassanah ya kwana don daga baya Fadeelah ma k'in yarda da ita yayi, watakila ya gano kammanin ta da mahaifiyar data wullar dashi ne.

Washegari Juma'a Saminu yazo mata da wani labari bakinsa a washe kamar gonar auduga, cewar a jiya Kawu Ibrahim yayi magana da Sadiq har kuma yace dashi yazo wani satin ranar laraba tare iyayensa. Mami bata gaya musu ranar da Kawu Ibrahim yace suma su zo ba, amma bayan ta shaidawa Fadeelah, sai dukkaninsu suka yarda cewa rana d'aya ne da sanda su Sadiq zasu zo.

Zatonsu ya kara tabbata ne da daddare lokacin da Aunty Hassanah ta dawo daga b'angaren iyayen Said, tace dasu mahaifiyar Said d'in tayi waya dashi yace mata da jibi zasu zo amma Kawu Ibrahim yace su zauna jikin Adam ya k'ara warwarewa tukunna ranar laraba sai su zo.

Haka kowannensu ya kwana a ranar da tunanin wane irin taro za'ayi RANAR LARABA?

***

LARABA, TA BAWA RANAR SA'A!

Adam ya gyara zamansa kad'an ya jawo hannun rigar Said dake gefensa, sannan ya mik'a wuyansa saitin fuskarsa yace.

"Nawa ka ciro a Atm d'in?"

"Dubu d'ari kamar yadda kace, wai kud'in meye?"

"Ban sani ba, jiya ne ya kira ni a waya yace in taho da 50k."

Har Said zai sake magana magana k'ofar falon ta Kawu D'anjuma ta bud'e, mata suka fara shigowa d'aya bayan d'aya suna zama a d'aya b'angare na d'akin, idan har Adam zai iya rik'ewa to a b'angaren da suke zaune, kusan duk wani namiji babba daya mallaki hankalinsa a Babban gida yana wajen. Bai rayu tare dasu ba amma zai iya tabbatar da cewar ba'a tab'a irin wannan zaman daya had'a da kowa da kowa a gidan ba har kuwa da mata.

Kawu Ibrahim ya riga ya gaya masa cewa zama za'ayi na gidan gabad'aya saboda haka tun da suka taho a hanya daman ya shirya samun hayaniyar mutane, ilai kuwa abinda ya tarar kenan, da wad'anda suka je duba shi asibiti dama wad'anda basu sami damar zuwa ba haka suka yanyameshi kowa na fad'in yaya ya k'ara ji da kuma fad'in cewa ya rame.

Ya kai hannu ya tab'a wuyansa kad'an, shi kansa ya san ya rame don zazzab'in da yayi mai zafi ne, kwana biyu baya cikin haiyacinsa bacci kawai yake yi a k'asan allurorin da ake masa, bayan ya farka kuma jikisa yayi nauyi da yawa don haka ya rasa k'arfi mai yawan da har yanzu bai dawo daidai ba.

Ya d'ago da idonsa ya sauke akan k'ofar da matan keta shigowa ciki, jiran shigowar Fadeelah kawai yake don ko bayan ya farfad'o daga tasa rashin lafiyar, tunani yake idan nata idanun sun farfad'o, so yake yaga ta koma daidai kamar yadda take a baya, so yake tayi jinyar zuciyarta a d'an k'ank'anin lokaci ta kuma warke, baya fatan ace ta rik'e komai a ranta don in har ta cigaba da wahalar da kanta, shima zai cigaba da wahala ne da tunanin halin da take ciki.

Daga bayan yayarta Maryam, Fadeelan kuwa ta shigo sanye da wani dogon hijabi kalar coffee daya rufe jikinta ruf! in banda fuskarta data haska cikin duhunsa. Fatansa ya karb'u sanda suka had'a ido... Ya hango wani kyalli da rabon daya ganshi a idanun nata tun sanda suka rabu a America sannan kuma kalarsu ma ta daidaita, sai kawai ya samu kansa da yi mata wani guntun murmushi, labari mai dad'i shine itama ta mayar masa kafin ta nemi waje ta zauna.

Fadeelah ta sunkuyar da kanta k'asa bayan ta zauna, rabonta da shigowa d'akin nan tun zamanin baya a wannan ranar data canja akalar rayuwarta, ranar data gudu daga Babban gida, ranar da Kawu Ibrahim ya ceto ta daga hannun su Salisu dake mata dukan mutuwa, sannan ranar da a cikin d'akin nan dai kowa ke mata kallon wadda ta kashe mahaifiyarsu.

Bayan gyara da d'akin ya samu babancin wancan lokacin da yau shine... A yau ita d'in wankakkiya ce mai 'yanci, babu wanda ya isa yayi mata kallon raini balle har a sami mai d'aga hannu akanta, haka kuma gaskiya ta fito ta wanke ta tas daga zargin kisan da aka d'ora mata. Ta rufe idonta a hankali sanda muryar Kawu D'anjuma ke umartar Kawu Bashir daya bud'e taron da addu'a... Gani take kamar a yau ne komai ya faru, kamar a safiyar yau Hajiya ta rasu kuma a yau d'in aka gano cewa Sule ne ya kashe ta ba ita ba. Tabbas tsakanin hak'uri da rashinsa d'an tak'in kad'an ne!

Sai ta sunkuyar da kanta a hankali tsakiyar cinyoyinta, bata son wani ya hango kyallin kwallar dake shirin taruwa a idonta, don ta fahimci kusan kowa hankalinsa na kanta. Ta gefen idonsa Adam ya hango sanda ta sunkuyar da kanta fatansa wani tunanin take ba kuka ba, ya cigaba da kallonta har lokacin da aka shafa addu'ar, a sannan ya lura da yawa daga cikin matan sun tsura masa ido ne kuma sun san Fadeelan yake kallo, don haka yayi saurin sunkuyar da kansa ya koma kallon k'afarsa dake tankwashe.

Kawu Bashir ne ya fara magana akan zumunci da kuma muhimmancin 'yanuwantaka, yayi bayani mai tsaho kafin Kawu Danjuma ya karb'a, sai dai mafi yawan bayaninsa na neman yafiya ne kan abinda yayi, kuma ko a muryarsa kowa zai fahimci cewa da gasken ne yayi nadama, kalamansa na k'arshe da suka yiwa Adam dad'i sune inda yace.

"DANGi sune cikar zatin duk wani d'an adam a doron k'asa, sune wad'anda suke karb'ar mutum a kowanne irin yanayi na rayuwa, a cikinsu ne mutum ke samun tallafi da tausayawa koda kuwa duniya ta juya masa baya, amma mafi yawancinmu sai muka manta hakan, muka bari k'iyayyar da ba gaira ba dalili ta rinjaye mu muka cutar da yarinyar da bata da alhakin komai alhalin mai laifin yana cikinmu babu wanda ya tab'a zarginsa. Don haka ina fatan wannan ya zama darasi a garemu kuma ina rok'on duk wanda muka d'auki alhakinsa da ya yafe mana don darajar ma'aikin Allah."

Daga nan ya jinjinawa Adam kan irin namijin k'okarin da yayi wajen baiyana gaskiya sannan shima ya rok'e shi da ya yafe masa akan wahalar daya bashi. Hakan ya bud'e k'ofa ga su Kawu Yahya da sauran muk'arrabansa suma suka shoga neman yafiyarsa. Ya wulkita idonsa kad'an tsakanin fuskokin da yake kalla, hankalinsa ya kwanta ganin Fadeelah ta d'ago kanta har tana magana da yayarta.

Bayan nan Kawu Ibrahim ya gabatar da marik'an Fadeelah ga jama'ar gidan, Kawu Danjuma yayi musu godiya sosai game da jinjina musu kan bajintar da suka yi. Bayan haka Kawu Ibrahim yaso a tattauna matsalar Mairo amma a lokacin mijin nata da 'yanuwansa basu kai ga k'arasowa ba don haka ya yanke shawarar tafiya ga abinda suka riga suka gama shawararsa. Ya kalli Daddy wanda ke zaune a hagun Kawu D'anjuma yace.

"Bayan wannan al'amarin ya natsa, dani 'yanuwana munyi shawara cewa a halin yanzu kai kafi cancanta da a kira ka da mahaifin Bintu, domin kai ka wahala da ita kuma kai ka d'auki duk wata d'awainiyarta, irin d'awainiyar da mu da muke 'yanuwan mahaifinta na jini ba muyi ba. Don haka bisa shawarar da muka yanke a yanzu zamu nemi aurenta ne daga hannunka."

Kamar yadda madannin 'Pause' ke tsaida duk wani abu walau mai rai ko mara rai a cikin video, haka duniyar Fadeelah ta tsaya cak! Lokacin da taji hakan, ta juyo daga sauraren maganar Mairo ta kalli Kawu Ibrahim daga inda take.... Zancen neman aure yake? Aurenta kuma? Dawa?

Wad'annan tambayoyin su suka dira a zukatan duk wasu mazaunan d'akin banda iya wad'anda Kawu Ibrahim ya tattauna zancen dasu. Shi kansa Daddy tambayar daya bud'e baki yayi kenan.

"Aure kuma Kawu? Auren Fadeelan?"

Kawu Bashir ne ya amsa masa wannan karon.

"Haka muke nufi Alhaji, in baka manta ba kun fad'a mana cewa ana tsaka da aurenta ne wannan al'amarin ya faru, kuma bayan haka kazo da 'yanuwanka ka gaya mana akasin da aka samu daga baya cewa auren ba zai yiwu ba, don haka muka yanke shawarar cewa a yanzu gwara ace ta tafi gidan mijinta ba wai don mun raina kulawarta karkashinka ba, a'a sai don dukkanmu munyi hasashen cewa hakan zaifi wajen wanke zuciyarta daga wannan al'amarin."

Fadeelah bata san sanda ta mik'a hannunta ta damk'e na Mami Saffiya dake d'aya gefenta ba, don gani take hakan ne kawai zai sa ta gane cewar ba'a tunaninta komai yake faruwa ba.

Daddy ya gyara zamansa kad'an sannan yace.

"Nagode da wannan matsayin kuma nima na goyi bayan shawararku don haka a shirye nake da ko YANZU in baku auren Fadeelah."

Babu b'ata lokaci kuwa muryar Kawu Ibrahim ta fad'i abinda ya girgiza tunanin mafi yawan mutanen d'akin.

"Idan haka ne, to a yanzun ina nemawa d'ana ADAM izinin auren 'yarka FADEELAH!!"

Idan ka d'auke su Kawu Danjuma da suka riga suka san zancen, a wannan lokacin kaftanin mutanen d'akin nan yanayin reaction d'in mutanen cikinsa iri d'aya ne sai dai na wasu yafi na wasu amma banda Sa'id, wanda yayi wani murmushi mai fad'i sannan ya juya ya kalli Adam d'in dake zaune a gefensa baki a bud'e kamar mutumin da aka sassak'a.

Sai yanzu ya fahimci kud'in da ya ciro a Atm na menene!

----

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

41

(☆_☆)

BAYAN SATI BIYU, ABUJA

GIDAN MAMI SAFIYYA.

F A D E E L A H

.... Yau Amarya sunanki daina tsabar kuka_
Kin riga kin shiga k'ungiya ta manyan mata

Daga yau baki da izini da bin 'yanmata
Zaki bar Baba da Inna don dalilin aure
Zaki k'aura daga garesu don dalilin aure

Tunda ansa miki lalle, daga yau kin girma
Duniya komai naki lokaci ne na wani Gimbiya!

Fadeelah na sanye cikin wata doguwar riga kalar ja yayin da wata mace k'abila ke tsaye a kanta tana mata kitso cikin wani style mitsi-mitsi, Afrah na zaune daga gefensu rike da kwalbar mai wadda ake shafawa tsakanin kitson tana surutunta, tana shafawa a nata gashin itama. Fadeelah ta rufe idonta a hankali tana k'ok'arin maida kwallar dake shirin fitowa daga idonta, inda za'a barta ta fad'i gaskiya kuma a saurareta, rok'o zata yi a cire wak'ar nan don ba abinda take k'ara mata sai sake dulmiyar da zuciyarta... Sake dulmiyar da zuciyarta kan zagayen halin da take ciki.

Yau sati biyu kenan da d'aurin aurenta kuma yau d'in ake shirin d'auke ta daga gabansu Mami. Ta dad'e da zama matar aure tun daga wannan larabar da akayi taro a Babban gida, don a la'asar d'in ranar su Kawu Ibrahim suka d'aura aurenta da Adam a masallacin unguwar ba tare da tuntub'ar d'aya daga cikinsu ba, kuma har cikin d'akin Aunty Hassanah Mami ta kawo mata sadakinta dubu d'ari cif ta nad'e su cikin tafin hannunta.

Tayi kuka sosai a wannan ranar, don kowanne aure yana da nasaba ne da abubuwa da dama tun kafin faruwarsa har zuwa yinsa d'in, amma ita babu d'aya data had'a da Adam don haka gani kawai tayi kamar su Daddy sunyi kyauta da ita ne. Sai dai in ka d'auke 'yan k'alilan mutanen cikin Babban gida da suka saka ran Kawu Ibrahim zai had'a Adam da 'ya'yansu, kowa ya nuna murnarsa a wannan ranar ta yadda babu wanda zai shigo gidan a lokacin yayi tunanin cewa ba'a dad'e da mutuwa a cikinsa ba.

Hakazalika a daren wannan ranar, tasha tarin nasihohin daga mutane da yawa dake nuna jin dad'i da farin cikinsu, nasihohin da suka yi barazanar tsinka duk wani irin tunaninta akan auren, Kawu Ibrahim yace.

"...Wannan auren dana yi miki Bintu, riba biyu zai zame miki a rayuwa, ina ganin abinda daga ke har shi ba kwa hangowa a yanzu sai kun zauna da juna tukunna, Allah ne shaidata ina k'okarin gyara rayuwarki ne kan tafarki mai inganci, don haka a wannan lokacin babu abinda ya dace dake sai auren, don duk dad'in rayuwar da zaki samu a gaba ba zai rufe miki wani bak'in cikin ba, amma in har kina zaune ne a k'ak'ashin inuwar aure, wannan rahamar kad'ai zata yaye miki abubuwa da dama..."

Daddy yace.

"Abinda iyayenki suka yanke daidai ne Fadeelah, kuma kar kiga cewa nima ban tambayi ra'ayinki ba na biye musu, na san kina da hakki kan a nemi izininki tukunna, amma nayi abinda na san koda na tambaye kin ba zaki kunyata ni bane, na san ba zaki tab'a cewa A'ah ba Fadeelah, don haka ina miki fatan alkhairi a wannan sabuwar rayuwar da zaki fara..."

Kawu Bashir yace.

"...Adam shi yafi kowa dacewa dake Bintu, shi ya san duk wata matsalarki da kuma irin halin da kika shiga, don haka zaifi tausaya miki akan duk wanda zamu had'a ki dashi sab'anin shi d'in, mun hango wani abu ne da daga ke har shi ba zaku tab'a ganinsa a yanzu ba.."

Kawu Danjuma yace.

"... Koda kin yafe min Bintu na san ni mai laifi ne a wajenki har abada, amma ina so ki sani cewa sanda Kawunki yazo min da wannan shawarar na had'a ki aure da Adamu naji dad'i mutuk'a sosai, naji kamar ana shirin yin gyara ne ga katangar da nayi yunk'urin rusawa a baya, don wallahi har cikin raina na yarda aurenki da Adamu babban ginshik'i ne da zai gyara zumuncin DANGINMU.."

Bayan wad'annan, akwai maganganun maganganun mutane da yawa da suka cakude akanta, a yanzu ba zata iya rarrabe kowannensu ba saboda kusan duk suna tafiya ne cikin siga d'aya, fatan alkhairi da kuma yak'inin cewa Aurenta da Adam ba matsala bane.

"Wai ba zaki fito bane tun d'azu muke zaune a mota, usman sai mita yake"

Muryar Rahma wadda ta lek'o cikin d'akin ta katse tunaninta tana kallon Asiya dake zaune a gefen gado tana shayar da 'yar jaririyarta Hanan. Ta haihu ne a lokacin tana cikin rud'anin shari'ah don haka ba wanda ya gaya mata sai da ta dawo kawai ta ganta da baby.

"To ba sai ya tashi sama yana mitar ba ub*n 'yan azalzala, wallahi sai Hanan ta gama zan fito kuma ku tafi ku gani."

Cewar Asiyan, zasu je kai kaya ne can gidan da za'a kaita tare dasu Aunty Hassanah wad'anda su sun dad'e da tafiya ita kuma ta tsayar da motarsu ta dawo ciki saboda kukan da yarinyar ta dame ta dashi. Rahma bata ko jira k'arashen maganarta ba ta juya fuu! tana fad'in.

"Tabd'ijan, to wallahi kuwa baza mu jira ba, mu mun tafi kya samu me kawo ki."

"Kar Allah yasa ku jira ni d'in dangin masifaffu." Taja tsaki sannan ta kalli Fadeelah tace.

"Yaya Saifuddeen ya d'ebowa kansa wallahi, nan da 'yan watanni rayuwarsa na cikin kwale-kwale."

Bata san lokacin da tayi murmushi ba don a irin wannan lokacin hirarsu Asiya ce kawai ke tuna mata cewa akwai murmushi a duniya musamman ace Fatima na nan, don su bidirinsu kawai suke kamar wancan lokacin bikin nata, tayi kewar su Zahra ma, wad'anda har yanzu ke Washington tun bayan bikin Al'ameen basu dawo ba, tayi kewar shige da ficensu da kuma tarin k'awayensu masu iyayi kamar yadda suka gaiyato su a wancan lokacin.

Wancan lokacin da take shirin zama matar Al'ameen... Lokacin da duk tarin jama'ar da suka zo babu wani DANGINTA, kowa bare ne da bata had'a ko d'igon jini dashi ba, amma abain dad'in yanzu shibe ita d'in mai 'yanci ce, a yau itama ta zama kamar Asiya lokacin bikinta, tana cikin danginta ta kowanne b'angare, banbancin kawai shine a yanzu ba lallai duka nata dangin tsakani da Allah suka zo taya murna ba, amma duk da haka dai sune DANGINTA kuma sai da sunansu zata samu duk wata d'aukaka da nasarar duniya.

A k'aidar yadda aka tsayar, babu wani biki da za'ayi duba da halin da ta fito daga ciki da kuma rasuwar Sadiya da ba'ayi ko arba'in ba, don haka a yau d'in asabar kawai kaita za'ayi, Sai dai ance wai gidan biki baya b'uya don duk da ba wani taro ake ba amma gidan na Mami a cike yake da mutanen da ba wanda ya san yaushe aka gaiyato su, don hatta wasu daga cikin 'yan Babban gida sun zo duk kuwa da tazarar dake tsakanin Abuja da Zariyan.

Aunty Saratu tazo daga Kaduna sati guda daya wuce kuma tun daga lokacin suke ta zirga-zirgar yi mata kafi a gidan da Adam ya bayar tare da Mami da kuma su Aunty Hadiza.

K'ofar d'akin ta bud'e, Mairo ta shigo biye da ita 'ya'an Aunty Hassana ne su biyu, tayi kyau sosai cikin wasu kaya kalar Maroon. suka shiga jidon wasu manyan ledoji dake cike da kayan kitchen zuwa waje.

"Akwai wata motar da zata tafi yanzu ne?"

Asiya ta tambayeta.

"A'a, pick-up ce zata d'auki wannan, bake su Rahma suke jira mota ba?"

"Ai sunyi tafiyarsu, yanzu ta lek'o tace baza su jira ni ba."

Mairo tayi murmushi tace.

"Kawai fad'a miki tayi, amma su usman d'in ma Mami ta aike su gidan Hajiya Amarya yanzu, sai sunje sun dawo sannan zaku tafi."

Fadeelah tayi murmushi sanda Asiya tayi kwafa tana fad'in.

"Zata san ni zata yiwa burga kuwa."

Mairo ta juyo ta kalle ta tace.

"Au kun kusa gamawa ma, bari na d'auko miki kayanki sai ki shirya kawai, gasu Jamila can sun zo suna tambayarki."

"Su waye su Jamila?"

"Jamilan kika manta? Matar Yaya Salisu fa(wansu, d'an wajen gwaggo lami.) Ita da kishiyarta ne da kuma matan 'ya'yan gwaggo Ramatu, yanzu suka sauka."

Sai ta gyad'a kanta kawai don har yanzu Mairo ta fita gane mutane, don ta fita wayo a lokacin da duk suka bar gida, sannan ga matsalar ciwon kwakwalwar da tayi ma, har yanzu ba kowa take ganewa ba.

"Momy zanci abinci." Afra ta fad'a kafin ta sami damar cewa wani abun.

"Okay zauna nan, yanzu zan kawo miki."

Cewar mairon da murmushi akan fuskarta sanda d'auki wata leda tabi bayan 'ya'yan Aunty Hassanan. Sai dai duk da murmushin nata, Fadeelah na iya hango wani abu kamar alhini a can k'asan idanun nata.

A halin yanzu labarinsu kusan d'aya ne, ciwonsu iri d'aya ne kuma suna shiga cikinsa ne daki-daki, zata iya rantsewa tana iya jin abinda Mairon ke ji a zuciyarta don itama a wannan lokacin irinsa take ji.... Daga yau rayuwarsu zata cigaba ne tare da mazan da suka zama kamar k'alubale a gare su.

A waccan ranar da aka d'aura aurenta ne Sadiq yazo tare da k'annen mahaifinsa maza kuma anyi zama mai tsaho tsakaninsu dasu Kawu Ibrahim harma da Mairon kanta, bata san me aka tattauna ba don a lokacin bata cikin nutsuwa amma dai an kawo k'arshen komai da cewar Mairon zata koma d'akinta, don haka Kawu Ibrahim ya bata damar zab'ar ranar komawar tata wanda ya kama a yau Asabar d'in da itama zata bar su Mami.

Banbancinsu kawai shine tunda suka dawo Sadiq ke zarya zuwa gidan yana neman shawo kan Mairo, yayin da ita kuma tun bayan dawowar tasu, sau d'aya tasa idonta a cikin na Adam, ranar da yazo ya tarwatsa duk wani ragowar kuzarin data fara samu a zuciyarta...

Shi kad'ai yazo a ranar, banda Sa'id da ya zama kamar k'anin Mami a yanzu saboda komai da ya shafi Adam d'in shi ake nema akai. A lokacin data same shi a falon Daddy inda aka sauke shi, 'Yan k'ananan fitilun ceiling na tsakiya ne kawai a kunne don haka a lokacin d'akin yayi duhu har ana iya ganin hasken wayar da yake dannawa akan fuskarsa... Ta fitar da numfashi a hankali lokacin da ta zauna a gabansa kuma hancinta ya zuk'o mata wannan k'amshin da ta dad'e da yiwa tambari da NASA.

A speaker ya amsa wata gajeriyar wayar Sa'id kafin su gaisa don haka ta sami damar kallonsa sosai, Ba ranar ta fara ganinsa cikin dogwayen kaya ba, amma ranar ta fara ganinsa cikin dogwayen kayan masu kalar sky blue, ya sanya hula sannan har a lokacin gashinsa a taje yake, yak'i ya barbaza shi irin na Adam d'in da ta sani a America... Waye ne yace lokaci baya gudu? Waye kuma ke tantama da faruwar al'amarin Allah cikin d'an lokaci? Kamar 'yan kwanakin baya ne fa kad'an take gabansa yana koya mata karatu a matsayin wani bare, yau sai gashi a wasu matakai masu girma har guda biyu, na d'an uwa da kuma mijinta!

Sai dai ba wad'annan abubuwan ne masu amfani ba, abinda ya fara gaya mata a lokacin shi yafi komai muhimmanci a wajenta, sunanta ya kira, ainihin sunan daya fara saninta dashi.

"Fadeelah."

Bata san lokacin da ta d'ago ta ware idonta a kansa ba da tsananin mamaki, sai dai meye abin mamakin, ita fa ta nemi hakan a wajensa tun ranar da zasu rabu don tsaf da maganar da suka yi a can baya ta dawo cikin kanta.

"... ina fatan zuwa lokacin da zamu sake had'uwa ka ka koyi harda yadda ake fad'in sunana."

Amma mai yasa bai fad'a ba tuntuni sai yanzu?

Da muryarsa mai taushi ya bata amsar da tambayarta.

"I'm sorry Fadeelah, kiyi hakuri tsawon lokacin da muka had'u ban nuna cewa na sanki ba, nayi hakan ne saboda yanayin aikina, case d'inki babba ne da bai kamata na bari wani abu yayi distracting d'ina ba, ko su Kawu Ibrahim ban sanar dasu komai ba, sai bayan da aka k'are shari'ar tukunna na fad'a musu."

Iya wad'annan kalaman kawai da zai iya fad'arsu cikin layi uku su suka dad'e suna sata tunanin kwana da kwanaki, taji kamar ta tambaye shi wane irin yanayin aiki ne da zai hana shi fad'a mata hakan kawai amma sai ta cakud'a yatsunta cikin juna wajen kokarin saita kanta kafin tace.

"Me yasa zaka bani hak'uri akan abinda ba laifi ba, nima na fahimci kana da uziri shi yasa ban ce komai ba, beside wannan ma ya wuce, kamata yayi mu fuskanci abinda ke gaba yanzu."

Saura kad'an ta mari kanta, me yasa zata fad'i hakan, ai sai yayi tunanin ko tana da wata manufa ne akan auren nasu. Ta cije lebb'enta sannan ta shak'i iskar dake d'auke da k'amshinsa ko zata samu sassauci.

Ya nisa kad'an sannan yace.

"Nima abinda ya kawo ni kenan."

Sai ta gyad'a kanta jin ta samu tallafi, Abinda ya kawo shi kenan ba ita kad'aice take wannan tunani ba, amma tsaya? Me ye abinda ya kawo shin?

Ya cigaba da cewa.

"Na san daga ke har ni komai yazo mana ne babu zato, kuma a yanzu muna cikin wani hali da babu abinda zamu iya yi akai, amma ba zan takura ki ba kamar yadda aka takura ki yanzu, zuwa lokacin da komai zai daidaita I promise to set you free... Zan barki ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kike so insha Allah."

Cewa yayi zai barta bayan wani lokaci, yana nufin auren ba dad'ewa zaiyi ba tunda ba aure ne dasu duk biyun ke da ra'ayi ba, idan an d'aura bada yardarsu ba su zasu iya kwance shi da kansu! Nasa ra'ayin kenan, irin tunanin da yake yi kenan a lokacin da ita take zagaye da mutanen dake hango mata d'orewar rayuwa tare dashi.

Su Kawu Ibrahim, sun yanke shawarar had'a ta dashi ne don suna ganin cewa auren ne kawai zai iya wanke zuciyarta daga irin uk'ubar data fuskanta kuma shi yafi kowa dacewa da ita sannan hakan zai gyara zumuncinsu, amma sai a lokacin kwakwalwarta ta fahimci tunaninta da nasa shigen d'aya ne banbancin kawai shine a yayin da ita take ganin kamar anyi kyauta da ita, shi kuma gani yake kamar an bashi ita ne a matsayin ladan wahalar da yasha... kuma baya buk'atar hakan!

Tun daga wannan ranar kuma bata sake ganinsa ba amma sun rabu ne lafiya kalau don bata nuna masa komai ba ta bari suka rabu akan hakan. To me zata ce masa bayan ita kanta bata san me take ji game da auren ba da kuma shi kansa, ta san dai ba wai bata sonsa bane balle kuma ace ta tsane shi, don in har ta fad'i hakan ma za'a iya bata wani

Please Login or Register in order to submit comment