Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowannensu zai iya tsintar kansa a ciki, damuwarta d'aya ce, wane irin kallo su suke mata?

Ta juyar da kanta gefe a hankali ta kalli fuskarta a jikin bak'in fentin motar, dishi-dishi inuwar fuskar me kawai ya fito don haka bata san wane irin yanayi ke jiki ba, wane irin yanayi ne ya sauka a jikinta tun daga lokacin da wani mutum ya shigo cikin d'an k'aramin cell d'inta a wata safiya.

"Kece Bintu Abubakar?"

"Eh." Ta amsa daga can k'asa inda take tsugunne.

"Bisa umarnin da aka yanke jiya a wannan koton za'a maida ke cikin kurkuku sai lokutan da za'a zauna shari'arki sannan za'a dinga kawo ki nan."

Maganar ta fito kamar a mafarki, ta kasa bada ma'ana a cikin kanta... Wai za'a kaita kurkuku, ta yaya za'a kaita kurkuku? Wata mace sanye da kayan masu tsaro da suka shigo tare ta nufo inda take ta mik'ar da ita, al'amarin yayi mata girma a cikn kanta, taji bangwayen cell d'in suna shirin had'ewa da ita.

"Ke kad'ai kin isa bama buk'atar tarkacenki."

Mutumin ya sake fad'a yana kallon ledar kayayyakinta dake ajiye a gefe, matar ta shiga k'ok'arin saka mata ankwa, tunaninta ya sake kwancewa, ta fahimci a sannan yake nufin za'a tafi da ita.

"Saboda me za'a kaini prison? Me yasa baza'a barni anan har a k'arasa shari'ar ba? Laifin me akace na sake yi?"

Ta jero tambayoyin tana kallonsa da dukkan wata ma'anar rud'ani.

"Hajiya laifin da ake zarginki dai shine, kuma ai ke kin ma dad'e anan akan wasu, k'aidar kotun nan zama in ya wuce biyu kurkuku ake tura mitum saboda bamu da waje da yawa, amma ke wajen zama biyar fa akayi akanki kina nan.."

Ya fad'a yana kallon cikin folder dake rik'e a hannunsa, zama biyar! Zama biyar d'in da lauyansu Kawu danjuma ya gama fito da duk shaidunsa, Wannan kalmar kad'ai ita fahimtar da ita cewa da akwai ayar tambaya akan wannan hukuncin, in ba haka ba me yasa sai da Adam baya nan hakan zai faru?

"Lauya na ya sani? Kun fad'awa 'yanuwana?"

Yayi wani guntun murmurshi.

"Koto ce ke da hakki akanki yanzu Hajiya ba wai 'yanuwanki ba, don haka in sun zo zasu sani, sannan lauyanki dole a gaya masa mana in ya dawo, don ina zai dinga samunki in ba can ba."

Matar ta gama saka mata ankwar sannan ta cafki saman hannunta alamun ta fara tafiya, sai ta juya ta sake kallonsa.

"Dan Allah malam ka ara min wayarka inyi kira minti d'aya dan Allah."

Guntun murmushinsa ya karu a sannan.

"Hajiya da alama kin manta matsayinki anan ne, waya gaya miki kina damar 'yancin kira? Sannan ko za'a barki ai sai da sharad'ai, ba wai in baki waya kamar a titi ba."

Ta sake girgiza kai ta a kallonsa.

"Dan Allah minti d'aya kawai zan kira 'yanuwana."

Ya girgiza kansa shima.

"Na gaya miki za'a sanar da 'yanuwanki..."

Ya kalli matar dake rik'e da ita.

"Hadiza, ja ta muje."

Kafin ta sake wata magana matar taja hannunta zuwa wajen cell d'in, ta wata doguwar hanyar daban da inda ake bi da ita ganin bak'i suka bi, don haka idonta ya gane mata tarin cells a jere kowanne cunkushe da mutane hud'u ko sama da haka, akwai na mata daban da kuma na maza, ashe da mutane da yawa a wajen bata sani ba? Wani irin kokari Kawu sulaiman yayi har aka bata wannan cell d'in ita kad'ai ba tare da kowa ba? ihu da maganganu suka yi ta fitowa daga kowanne cell da suke wucewa.

"Yallab'ai an sallame ta ne?..."

"Oga mu kuma fa? Ya za'ayi ne?"

"Baby, prison za'a kaiki, zan zo in fitar dake..."

Rikicewarta bata bari ta fahimci dukkan abinda suke cewa ba. Wannan bak'ar motar rufaffiya na jira a harabar kotun sanda suka fita, ta juya ta sake kallon mutumin.

"Dan Allah yallab'ai ka taimaka min in kira 'yanuwana dan Allah."

Bata san wane irin tunani ne ya canja ra'ayinsa ba, don tsayawa kawai yayi ya d'an kalleta na wani lokaci sannan yace.

"Okay, amma minti d'ayan kawai da kika ce, Hadiza juyo da ita."

Ya fad'i hakan ne don kar sauran securites d'in dake can jikin motar su hango su, ya zaro wata 'yar k'aramar waya daga aljihunsa ya mik'o mata.

Sai dai tana karb'ar wayar, wani tunanin ya dirar mata... Wa zata kira? Daddy zata kira ta gaya masa har Mami taji hankalinta ya k'ara tashi ko kuma Kawu Ibrahim zata k'ara rikitawa ta gaya masa komai ya cigaba da cakud'ewa? Me zai yi a yanzun da Adam baya nan? Wa zai zo ma ya tunkara?

Adam kad'ai shine wanda ya kamata ta kira, shi kad'ai ne zai iya wani abin a yanzu amma baya nan kuma bata da numbersa kamar yadda ta tabbatar wannan karamin ma'aikacin ma bashi da ita, in har za'a samu sai a wajen manya irinsu Kutama ko wanda shari'ar tata ta shafe su, ta juya a hankali ta kalli motar dake tsaye ana shigar da wasu matan ciki, sannan mutumin dake tsaye a gabanta yana jiran wayarsa... Babu wannan lokacin, sai ta girgiza kanta kawai sannan ta mik'a masa wayar.

"Na fasa, na gode."

Tafiyar cikin motar mik'ak'iya ce da bata da niyyar k'arewa, ga zafin injin bodin da suke zaune ga kuma warin man fetur wanda ya had'e dana jikin matan dake gefenta, amma Fadeelah bata damu da hakan ba, ta riga ta d'auke tunaninta dama kwakwalwarta baki d'aya daga cikin motar, ta tafi can wani lokaci baya, wasu zamaninnika da suka shud'e....

Tana zaune Inna saratu na yi mata kitso a tsakar gidansu, bata kai shekaru goma ba a lokacin, yayin da innarta ke ta zarya tsakanin kicin da inda suke alamun girki take yi, Mairo ta shigo rik'e da alqur'ani, ta tashi ta tafi da gudu ta rungumeta, kin siyo min yaya? Kin siyo? Ta tambaya tana tsalle a gabanta, Mairo tace ba'a samu ba Bintu mai siyarwar bata zo ba... Mairo! Inna saratu ta kira sunanta daga can inda take zaune, sai tayi murmushi sannan ta zaro wasu kayan wasa na k'asa daga cikin hijabinta...

Tana tsaye a cikin ofishin Principal d'in makarantarsu na primary, Yarinyar tana da mutuk'ar k'okari Alhaji, Principal d'in ke fad'awa Babanta dake zaune a kujerar gabansa, Shi yasa muka ce ba sai tayi aji na biyar ba daga na hud'un ma zata iya yin jarabawar shiga sakandire, Babanta ya juyo ya kalle ta fuskarsa d'auke da murmushi na alfahari...

Suna tafe ita da Mairo akan wata hanya da babu mutane sosai, Tsaya anan ina zuwa, Mairo ta fad'a sannan tayi gaba, tabi inda ta nufa da kallo, wani saurayi ne tsaye sanye da fararen kaya, hasken yammacin ya haska manyan kyau na fuskarsa, da isar Mairo gabansa ya mik'o hannayensa duka biyun ya kamo nata, sai ta juya bayanta da sauri ga barin kallonsu...

Tana lek'e ta tagar d'akin Mairo, Mairo na zaune a gefen katifarta tana rusar kuka yayin da jamila k'awarta ke rarrashinta a gefe, Na san yaya Aliyu yana da kirki kuma yana da halaye masu kyau amma wallahi Jamila bana sonsa a matsayin mijina Sadiq kad'ai nake so, Jamila ta kalle ta sannan tace, Baki tsane shi ba kenan?, Mairo ta girgiza kanta, Ban tsane shi ba, matsayin da ake k'ok'arin bashi a rayuwata kawai na tsana...

Tana kwance a wani d'aki mai cike da mutane, hawaye na bin fuskarta yana jik'a filon da take kwance, hannunta na hagu d'aure da allurar k'arin ruwa, daga can gefe Inna saratu ce zaune a tsakiyar 'yanuwanta tana ta hawaye wasu na rarrashinta, wasu daga cikin mutanen d'akin suma kuka suke yi, wasu na jan carbi yayin da wasu ke karatun alqur'ani, wata tsohuwa ta shigo ta tsugunna a gaban Inna Saratu muryarta na rawa tace, sai hak'uri Saratu ki d'auki dangana irin ta mai sunanki uwargida a gun khalilullahi... Abubakar ya tafi (Babanta), yabi Amina (Innarta) muma duk nan jiranta muke....

Har Sule ne zai saka ki aiki ki kasa yi masa sauri? Hajiya Babba ke fad'a yayin da take tsugunne a gabanta, Ki zauna lak'aki magariba ta tarad dake saboda baki so yi ba? To kuwa yau baki da abinci dare, yadda kika kwana jiya haka yau ma zaki kwana in yaso yunwar ta kashe ki...

Tana tsugunne gaban Hajiya Babba sanda jikinta ke girgizawa bakinta na fitar da wannan farar kumfar, sannan idanunta a zare tana kallonta, kallo irin na zargi da mamaki...

Tana kwance a dandaryar kwaltar titi, wani azababben ciwo na amsawa a cikin kanta, jini na zuba ta hancinta, daga can gabanta wata k'aramar yarinya ce kwance cikin jini, rigarta ta yayyage sannan naman cinyarta na wani gefe ya zaftare, ta tuno sanda maman yarinyar ke biya mata addu'a a farkon tashin motarsu, _subhaanal-lathee sakhkhara lanaa haathaa.._ Wasu mutane suka zo suka durk'usa gaban yarinyar, d'aya daga cikinsu ya tambaya, Tana da rai? Yanzu muka kai mahaifiyarta waccan motar ta rasu! Idanunta suka rufe a hankali ta koma cikin nata ciwon...

Tana zaune cikin falon Hajiyar Daddy, suna tsintar wake ita da Ladi, Hajiyar na daga kujera tana cin wani dambun zogale da ladi tayi tana ta santi, Anya ladi ba zamu cire mangwaron tsakar gidan nan a dasa zogale ba kuwa? Kar fa rani yazo mu rasa inda zamu samu, Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya...

Mami Safiyya na tsaye daga cikin wani had'adden filin shak'atawa tana kiranta, Deelah sauke ta haka ku taho muci abinci, ta juya ta kalli Iman da take turawa a lilon, Aunty deelah sau d'aya dan Allah, Iman tayi magiya, bata saurareta ba ta d'ago ta cak daga kan lilon tana dariya tana k'okarin sauka suka nufi wajensu Mami Safiyya, Daddy, Faruk da Zahra da suka zagaye wasu tarin kwanuka akan dardumar dake wajen...

Tana tare da Al'ameen, a cikin wani kanti na siyar da litattafai, ya zagayo ta bayanta ya zuro mata wani littafi daya bud'a cikinsa, Akwai wannan sunan a wanda kike nema? Ya tambayeta, ta girgiza kanta tace Judy ne sunan macen, sai ya rufe shi ya juya wata kantar neman wani, idanunta suka bishi da kallo, yana da kyau, mata nawa ne zasu so kasancewa dashi a wannan lokacin? Sai kuma kunyar kanta ta kama ta, ta juya ta cigaba da bincika kantar dake gabanta...

Tana zaune a cikin d'akin karatun makarantarsu, suna lesson ita da Adam, da kaloli suke amfani a ranar saboda haka ta nutsu a cikin aikin daya bata tana tayi, ta d'ago da kanta taga ya tsura mata ido, Me ya faru? Ta tambaye shi, baice komai ba kawai ya ya lumshe ido sannan ya d'ora yatsansa d'aya akan kumatunsa, ta d'ago da screen d'in wayarta ta kalli fuskarta, wata koriyar kala ce ta shafi a gefen kumatunta, sai ta juya da sauri ta zaro tissue a jakarta ta shiga gogewa...

Tana tare dasu Fateemah, Rahma da wasu tarin k'awayensu a cikin d'akin Aseeyah ranar da aka kaita, Rahma ta bud'e labulen tagar d'akin ta hango can wajen gate, To Asee da fatan kin shirya ga Ango nan tafe, Aseeyah ta d'ago da fuskarta tace, Ya k'araso mana, shiri na yaushe kuma? Suka kyalkyale da dariya bakid'ayansu...

Tana zaune a gaban Daddy, yana yi mata nasihar dake shaida cewa ya bada aurenta ga Al'ameen, kuka take yi, na farin ciki da kuma bak'in cikin cewa rayuwarta zata d'ore ba tare da sanin Danginta ba...

Tana zaune ranar bikinta da Al'ameen, lokacin da Mc ke kiran su Zahra filin rawa, lokacin da Sadiya ta tunkud'o Mairo tsakiyar rumfar da take zaune... Lokacin da rayuwarta juya, ta gangara sannan ta tankad'a gab'ar ramin da a yanzu take tunkararsa.

Ta lumshe idanunta a hankali sannan ta bud'e su tar! Akan gefen zanin matar dake fuskantarta... in har duk wad'annan abubuwan sun faru da ita a rayuwarta ta baya, me ya rage zai tsorata ta kuma a yanzu? Ta san cewa tabbas wannan wani sharrin ne daga su Kawu Danjuma tunda har bata ga Habiba tare dasu ba, amma tun lokacin da ta farka a asibiti ta yiwa kanta alkawarin dake zuciyarta ga dukkan wani k'alubale daga gare su, ta rantse zata fuskance su a matsayin wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya.

Ta rufe idanunta gaba daya sanda motar taja ta tsaya sannan rugugin bud'e gate d'in KURKUKUN daga can waje ya cika kunnuwansu.

Barka da zuwa Fadeelah.

Ta yiwa kanta gaisuwar da babu mai yi mata.

****

"Muna da dokoki anan..."

Muryar wata k'atuwar mata ta karad'e d'akin da aka tsayar dasu bayan shigarsu cikin kurkukun.

"... Kuma dole ne kowaccenku ta kiyaye su walau dad'ewa zaku yi a wajen nan ko kuma akasin hakan, bayan dokoki akwai ayyuka da muke rabawa kala-kala kuma dole ne kowannenku yabi su don mu zamu gaya muku yadda zaku yi komai anan, sanda zaku tashi, sanda zaku yi aiki, sanda zaku ci abinci sannan sanda zaku kwanta. Ba'a tashin hankali a wajen nan, duk wadda tayi mana taurin kai zata fuskanci hukunci mai tsananin da zata gwammace kashe ta akayi a maimakonsa."

Yadda take magana idanunta a tsaitsaye da kuma sautin muryarta ya tsorata wasu da yawa daga cikin matan amma banda Fadeelah, ta riga ta saba had'uwa da mutane masu irin wannan siffar na baiyana tsana k'arara daga kowanne b'angare na rayuwarta.

Wasu matron biyu ne suka tafi dasu cikin wani gini daga nan, aka kaisu wajen da aka d'auki jinin kowaccensu don tantance lafiyarsu, bayan nan kuma dukkansu aka auna fitsarinsu don ganin inda akwai mai ciki.

Daga nan a mik'e hanyar wasu band'akuna a jere aka kaisu.

"Akwai sabulu a ciki kowacce ta wanke jikinta sannan karku maida kayan dake jikinku, akwai zannuwa a gefe daga ciki."

D'aya daga cikin matron d'in ta fad'a sanda mutum bakwai suka shiga cikin kowanne toilet d'aya. Daga inda suke tsaye Fadeelah na hango k'afafun kowacce daga cikin matan kasancewar k'ofar bata kai har k'asa ba, hakan yasa ake iya ganin fasashshen simintin dake cikin kowanne band'aki, yayi ramuka wanda kowanne bak'in ruwa ya taru cikinsa.

Zuciyarta ta tashi a lokaci guda taji tana shirin yin amai, sannan wani abu ya shiga zarya a tafin k'afarta saboda tsananin kyankyami, anya zata iya zama anan kuwa? Me yasa bata tambayi mutumin nan ko za'a iya samun number Adam ba?

"Ina da magana dan Allah..."

Muryar wata mata a bayan Fadeelah tayi magana.

"...inaga ni ba sai nayi wankan.."

Bata k'arasa ba d'aya daga cikin Matron d'in nan ta buga mata wani bak'in sanda dake hannunta a fuska, matar ta dafe gefen fuskarta yayin da jini ya fara fitowa daga hancinta.

Matron d'in ta lailayo wani zagi ta rafka mata sannan tace.

"Mu ke da iko daku yanzu ba ra'ayin kanku ba saboda haka kar ki kuskura ki sake magana idan ba'a tambayeki abu ba, gargad'i ne ga kuma dukkanku."

Tana rufe baki idonta ya kai kan Fadeelah, ta nuna ta da sandan hannunta tace.

"In kika kuskura kika yi mana amai anan sai naci uw*rki."

"Ku fito! Lokaci yayi!" Daya Matron d'in ta kwalla wa na ciki kira. Ba b'ata lokaci kowannensu ya fito rufe da wani yamusashshen zani, Fadeelah ta had'iye yawun cikin bakinta sannan tabi layin matan dake shiga band'akin.

Bayan kowannensu ya fito suka shiga wata k'ofa daga nan wajen inda k'aton d'aki ne mai cike da buhunhuna na kaya, wata k'atuwar mace ce a wajen kamar Matron d'in farko da suka fara gani, ta kintaci yanayin kowaccensu sannan ta shiga mik'o musu uniform na kurkukun mai kalar ruwan toka, kowacce kala biyu, sannan pant, da brassier, slippers, da kuma man shafawa roba d'aya.

Bayan sun shirya aka raba su gida biyu, anan Fadeelah ta fahimci a cikin su goma sha takwas, su biyar ne kawai ba'a yanke musu hukunci ba amma duk sauran da adadin watanni ko shekarun da zasu yi akansu.

Su da ba'a yanke musu hukunci ba d'aki daban aka kaisu inda wani mutumi ya d'auki hoton passport d'insu ya lik'a a jikin forms d'insu da aka kawo daga can kotun.

_Shikenan! Ta kafa tarihin da har abada ba zai goge a rayuwarta ba!_

A cikin su biyar d'innan Fadeelah taga harda wannan 'yar k'aramar yarinyar data gani a mota, ta daina kukan da take d'azu, da alama tayi ne har zuciyarta ta k'ek'ashe don idonta a tsaye yake kyam! Tanabin fuk umarnin da aka bata kamar inji.

A lokacin da aka gama komai aka sake had'e su da sauran, sai aka raba su gurin wasu matron shida, kowacce Matron aka bata mutum uku.

"Daga gobe za'a raba ku b'angare-b'angare na kalar ayyukan da zaku yi, yanzu za'a raba muku cell kuma nan zai zama wajen kwananku daga yau."

A sannan ne Fadeelah ta had'a ido da wannan yarinyar, sanda matron d'in da aka basu taja su zuwa wata hanya daban da inda su suke, Fadeelah bata san me yasa ba, amma ta hango wani zurfi a idon yarinyar makamancin nata, ta had'iye yawu a hankali sannan ta juya tabi tasu Matron d'in, bata sani ba ko zata sake ganinta.

Babu kowa a harabar wajen har suka shiga wani dogon gini mai d'auke da tambarin *'Block G'* wata irin hayaniya ta shiga kunnensu a lokacin da Matron d'in ta bud'e k'ofar wajen, Fadeelah ta juya kowanne b'angare na hall d'in ta kalli d'imbin fuskokin dake lek'owa daga kowanne cell, dukkaninsu mata ne sanye da uniform irin na jikinta da kuma sauran mata biyun da aka shigo dasu tare, bayan hayaniyar wani abu kamar tsami ko wari ya ziyarci hancinsu, Fadeelah taji cikinta ya juya aman d'azu na shirin dawo mata, anya bata yi kuskuren k'in kiran su Mami ba ko Kawu Sulaiman? Ta yaya zata fara zama anan?

Taji kamar a cikin ruwa take tafiya lokacin da suke wuce tarin cells da maganganun matan dake lek'owa daga cikinsu, kwakwalwarta ta riga ta rufe a lokacin don haka bata iya fahimtar komai ba sai fito kawai dake fitowa daga kusan kowanne cell.

Matron d'in ta bud'e wani cell daga b'arin hagu.

"Shiga." Tace da Fadeelah da kuma d'aya daga matan.

Gabanta ya fad'i sanda matar ta shiga, ta d'an tsaya kad'an kafin tabi bayanta, garam! K'ofar ta rufe, Matron d'in tayi gaba tare da d'ayar matar.

Kunnen Fadeelah ya amsa sautin k'arara rufewar k'ofar kamar wani abu dake gaya mata cewa sake fitarta zuwa duniyar waje abu ne mai wuya.

Fuskoki hud'u da suka juyo suka zuba musu ido yasa ta fahimci kowanne cell mutum shida ne, duk kuwa da cewar bashi da girma, wasu siraran gadajen k'arfe guda uku k'anana sai toilet na tsugunne daga can gefe inda aka kare rabinsa da katako, akwai kan famfo a samansa, amma babu alamun ruwa don warin daya gauraye iskar d'akin ta tabbata daga shi ne, Ya ilahi! Watak'ila dai mafarki take yi! Bai dace ta tsinci kanta a irin wannan wajrn ba.

"'Yanmata biyu a rana d'aya."

Muryar wata mace ta shaida mata cewa a tsakiyar zahiri take! Babbar mace ce a jiki da kuma shekaru tana zaune daga kan gadonta tana kallo su, hak'oran cikin bakinta data washe sune kad'ai abu mai haskawa a fuskarta, a saman gadon kuma wata 'yar siririyar ce da fuskarta ke nuna alamun k'abila don ga bille nan rad'au fuskarta.

Sauran matan biyun suna zaune a k'asan sauran gadajen suna kallonsu, ko kuma tace mace d'aya kawai, wadda ta zame hannun rigarta d'aya tana shan iska, amma ta bayanta babu marabar kammaninta dana maza, jikinta mai tsawo ne da girma sannan babu wani alamun tsari irin na jikin mace, komai nata ihun fad'i yake yi.

Ta katse nazarinta ta hanyar washe bakinta sannan tace.

"Barkanku da zuwa, bak'inmu."

Fadeelah ta lumshe idanunta cike da rud'ani.

Ashe da mai yi mata Barka da zuwa.

***


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

34

(☆_☆)

Watak'ila tafi minti biyu a tsaye tana kallon 'yan kananan kwarukan dake layi suna bin gefen yamusashshiyar katifar da aka nuna mata a matsayin gadonta, sama ne amma bashi da maraba da k'asa don tsalle d'aya kawai mutum zai yi ya haye.

"Mun gama gaisawa da 'yaruwarki, ke yaya sunanki?"

Wannan mai siffar mazan ta fad'a sanda ta tsaya a gefen gadon. Kallo d'aya kawai Fadeelah tayi mata sannan ta fad'i sunan dake rubuce jikin form d'inta.

"Bintu."

Ba zata tab'a bari wajen nan ya amsa sunan Fadeelah ba, Fadeelah mai wankakkiyar zuciyar ce da ko k'uda bai tab'a mata sharri ba, zata kare martabar wannan sunan daga samun gurbi a k'azamin waje irin wannan, duk kuwa da cewar sunan ya fara sulalewa daga gareta, Bintu ta riga ta dawo tayi kane-kane da komai na rayuwarta... Banda su Mami da kuma Adam da ta sani a America watakila da ita kanta ma ta fara manta cewa ta tab'a zama Fadeelan.

"Sunana Kenken..." Matar ta cigaba sannan ta juya ta nuna d'ayar nan mai cirarriyar hannun riga.

"Waccan sunanta Gheto..." Sai ta nuna wannan Babbar da har yanzu ke kallon Fadeelah tana washe baki.

"Wannan itace shugabarmu a d'akin nan, sunanta Lalita, sannan Zazu..." Ta nuna mai kama da k'abilar nan ta saman gado.

Yanayin fuskar Fadeelah ya shaidawa Kenken cewa sunayen basu bada ma'ana a kwakwalwarta ba, saboda haka tayi wani karkataccen murmushi wanda daga gani ta saba yinsa sannan tace.

"Ba sunayenmu na gaskiya bane, inkiya ce muke kiran kanmu da ita don mu manta da rayuwarmu ta waje, duk wanda kika gani a wajen nan yana da sabon suna don haka kema kwanan nan zaki samu naki, "

Bata ce komai ba Kenken ta cigaba da cewa.

"Karki damu kowa anan ya shiga irin halin da kike ji zaki ware nan da lokaci kad'an, kin riga kin shigo cikinmu yanzu, zamu zama 'yanuwa kuma abokai mu taimaka miki ki fara sabuwar rayuwa, ki manta da komai ki kuma samu duk irin dad'in da kika baro a waje."

Ta k'arashe da murmushi tana k'ok'arin dafa kafad'unta, amma sai ta matsa baya da sauri sannan ta juyar da kanta, haka kurum zuciyarta bata amince da kenken ba ko d'aya daga cikin sauran 'yanuwanta.

Hakan da tayi kuma bai b'ata ran matar mai kama da maza ba, sai ma murmushi da ta sake yi sannan ta d'auke hannunta daga iska.

"Kar ki damu Binbi, muna da isashshen lokaci ai."

Taji sunan da ta kira ta, amma bata so ma ta yardarwa kanta cewa ta jin, saboda haka ba tare da ta k'ara kallon kowaccensu ba ta janyo katifar kan gadon ta karkad'e ta. Zan zauna zuwa wani lokaci,ta ayyana a ranta. Zata daurewa zama da mutanen nan kafin lokacin da za'a sanar dasu Kawu Ibrahim yazo yasa a bata cell ita kad'ai, Kafin kuma dawowar Adam yazo ya fitar da ita gabad'aya.

A lokacin wata iska ta kad'o ta tsakanin k'arafan k'ofar cell d'in, wani tsami ya taho ya kuma kwaso warin toilet d'in cikin cell d'in ya baza shi a iska, Fadeelah ta saka duka hannayenta biyu ta rufe hancinta da bakinta, don ta raba kanta da warin don kuma ta hana kanta ihun dake shirin fasowa daga k'irjinta.

"Wai baki da lafiya ne?" Muryar wadda Kenken ta kira da Zazu ta tambaya daga saman gadonta.

Bata bata amsa ba, haka bata juya ba har saida ta tabbatar ta kwantar da kukan dake neman 'yancinsa sannan ta maida katifar ta hau gadon, ta d'ora kanta akan kayan da aka bata sannan ta duk'ule duka jikinta.

Ta daurewa abubuwa da yawa a baya, don haka wannan ma zata daure masa.

Zata daure.

Zata daure.

***

Bayan kwana biyu.

Ba mafarki bane, tunani ne kawai cikin bacci, don babu abu d'aya da ya canja na wancan lokacin.

A wannan d'akin ne....

Cikin kotun da suka baro, inda d'aurarru ke ganawa da baki, Lokacin da Adam ke bacci a gabanta....

Wani irin tausayinsa ne ya dirar mata a sannan, don bayan sajen da taga ya tara, wannan baccin shine abu na biyu daya tabbatar mata cewa baya samun isashshen hutu a kwanakin nan... Duk saboda shari'arta.

Ta lumshe idanunta a hankali tana cigaba da kallonsa.

Shine wanda ta tsana a wancan lokacin da zuciyarta bata fahimce shi ba.

Shine wanda bata ko son inuwarsa da tata su kasance waje d'aya.

Sannan shine wanda a baya take ganin kamar yana rik'e da makamin tarwatsa rayuwarta.

Sai dai wannan bayan ta riga ta wuce, ta dad'e da shud'ewa tun farkon lokacin da k'addarar koyon karatu ta had'a su, wani b'ari na zuciyarta ya bud'e har ta fahimci b'oyayyun halayen da yake binnewa a bayan fuskarsa... Wannan fuskar dake gigita d'aukacin matan makarantarsu tana saka musu yardar cewa shine k'ololuwar duk wani fatansu.

Ta sake lumshe idonta tana kallon yadda yake baccinsa tsakani da Allah, zuciyarta cike take da hasashen wace irin k'addara ce ta cillo shi Nigeria kuma kan hanyarta.

Ta cije gefen lebb'enta kad'an tana hasko ma'anar K'addara a cikin kanta... Hukuncin Allah ne da babu tunanin wani d'an adam d'in da ya isa ya

Please Login or Register in order to submit comment