Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikinsa.

"Sister Rabi'a dan Allah taimaka ki tsaida ita." Muryar Nurse d'aya ta fad'a daga bayanta, amma kafin Nurse d'in dake gabanta ta fahimci me suke nufi ta wuce ta da sauri ta nufi hanyar matattakala ta sauka k'asa.

Benen na kallon waiting area don haka tsaf idanunta suka gane mata wanda take nema, Sadiq na tsaye jikin ginin receiptionist d'in wajen yana magana da ita, hannunsa na hagu d'auke da Muhammad.

Bata jira komai ba ta nufi wajen nasa sanda Nurses d'in dake biye da ita su kai ga cimmata, zaune a waiting area, mahaifiyar Sadiq ce da k'annesa mata biyu da kuma wasu daga cikin danginsu duk mata, sai 'yarta Afra dake ta 'yan wasanninta. Kusan awarsu d'aya kenan a wajen saboda tun bayan zuwansu ranar da aka kwantar da ita, aka ce ba wanda zai iya ganinta sai zuwa yau daya kama kwanaki uku.

Mairo duk bata lura dasu ba, don idanu dama hankalinta na kan Sadiq da ya juya bayansa don haka bai ga tahowarta ba, sai Recieptionist d'ince mai suna Amina ta zare idonta cike da mamaki tana kallonta.

"Ai gata nan ma ta fito, har an sallame ta ne?"

A lokaci d'aya ya juyo da tsantar mamaki daidai sanda ta k'araso itama ta shige jikinsa saboda saurin da ta taho dashi.

"Maryam yaushe kika farka?"

"Sadiq mu tafi gida."

Dukkkansu suka yi maganar a tare, kuma lokaci guda. Hakan yasa ya sake saurin tararta.

"Me kika ce?"

"Ikara zaka kaini." Ta fad'a tana kallonsa da idanunta wanda suka kad'a suka yi jawur alamun tana cikin ciwo har a lokacin.

Sadiq yaji duk wani tashin hankalin duniya ya dira cikin kansa a lokaci d'aya sannan mamaki ya k'ulle bakinsa.

"Yallab'ai yi hakuri wallahi fitowa tayi..."

D'aya daga cikin wasu Nurses guda uku da suka iso ta fad'a lokacin da suke kokarin rik'e hannunta, amma ga mamakinsa Mairo bata ko juya ba ta fizge hannunta da wani irin k'arfi da bai tab'a sanin tana dashi ba, a lokacin kuma Muhammad ya kwallara kuka mai d'agawa na alamun gane mahaifiyarsa da yayi, ya shiga mik'o 'yan hannayensa gare ta, amma Mairo bata ko kalle shi ba, idanunta a tsaye ta sake cewa.

"Sadiq gida zaka kai ni." Muryarta na d'auke da wani irin kaushi mai cike da ciwo.

"Subhanallahi, Sadiq me yake faruwa haka?"

Yayar mamansa ta fad'a sanda dukkaninsu suka taso daga waiting area d'in, k'anwarsa Zakkiya ta k'araso da sauri ta karbi Muhd d'in dake ta kuka a hannunsa ta shiga jijjiga shi, amma zillewa kawai yake yana mik'a hannu wajen uwar da yayi kewarta tsawon kwanaki, uwar da bata ma san yanayi ba, don bata kallon kowa a wajen, idonta na kan Sadiq kawai da ta shige cikin jikinsa kuma ta rik'o da kwalar rigarsa har sama, rik'o irin na alamun rok'o.

"Har ta farka? An sallame ta ne?"

Da yawansu suka had'a baki wajen tambaya.

"Wallahi Hajiya ba'a sallame ta ba, farkawa kawai tayi ta fito, kuma tak'i bari a maida ita."

Nurse d'in nan ta fada.

"Sister Nafisa, jeki d'auko Diazepam (allurar saka bacci.)" Nurse Hawwa ta bawa d'ayar umarni.

"Sadiq gida nake son zuwa.." Mairo ta k'ara maimatawa tana jijjga shi, da alamu bata ko fahimtar abinda ke faruwa a bayanta.

"Bari inje in gayawa Dr. Haruna, ina ganin ba zamu iya rik'e ta ba.."

"Bibty gida zani...."

"Me ya same ta haka me ya faru?" Wata likita da tazo wucewa ta tambaya.

"Kana jina? Ka kaini gida..."

"STEMI patient ce kawai ta farka ta fito." Nurse Hawwa ta bata amsa.

"Bibty dan Allah..."

Kwakwalwar Sadiq ta hargitse a lokaci d'aya don ya rasa me zai d'auka ya fara aika mata, magiyar Maryam, kukan Mahammad, hayaniyar Nurse d'in, ko kuma tambayoyin dake ta fitowa daga bakin 'yanuwansa... Yaji ya zama tamkar wani mutum-mutumi ba abinda yake iya fahimta sai yadda hannayen Mairo ke jijjiga kwalar rigarsa da dukkan k'arfin da zata iya.

Bai farga da komai ba, sai sanda wannan Nurses d'in ta dawo d'auke da allurar da aka aiketa, bai san amfaninta ba amma ya tabbata idan ta shiga jikin Mairo zata sa ta k'ara fita daga haiyacinta ne, saboda haka yayi saurin had'eta da cikin jikinsa bakid'aya sannan ya juyar da ita gefe.

Sai hayaniyar ta ragu kowa a wajen ya tsaya kallonsa da mamaki.

"Alhaji, matarka fa bata gama warkewa ba, ba sallamarta akayi ba."

Mai rik'e da allurar ta gaza jinkirin b'oye mamakinta.

"Ba sai kun sallame mu ba Nurse, a barta haka, sauran da kuka yi ma ya isa."

"Ai ba zancen isa bane Yallab'ai, wannan patient dinmu ce a yanzu, kuma ba zai yiwu a bari ka fita da ita ba tare da sallama ba."

"Zamu tafi yanzu?" Muryar Mairo data sake magana, ta nunawa kowa a wajen cewa bata cikin hankalinta, don duk da shorun da akayi baisa ta juyo ta kalli kowa ba.

"Sadiq wai me yake faru ne? Me ya same ku duka biyun?"

A yanzu mahaifiyarsa ce ta fad'i hakan, ganin har yanzu sun gaza fahimtar abinda ke faruwa.

"Mama gida zan take son zuwa."

Kusan a rikici yake don haka baiyi shawara da tunaninsa ba ya fad'i abinda ya rufe su a cikinsa tsawon shekaru.

"Wane gidan, naga duk gamu mun taho."

Ya girgiza kansa yana k'ara kallonta.

"Gida can wajen 'yanuwanta nake nufi."

"Yan'uwa? Yaushe Maryam d'in ta samu 'yanuwa bamu da labari?"

"Pleaseee Bibty..."

"Ba'a dad'e ba, kuma dalilin ciwon nata kenan, shi yasa ta rikice take son tafiya."

"Don darajar ma'aikin Allah Sadiq..." Muryarta rawa take a yanzu, somi-somin kuka hakan ya d'arsa tausayinta a zuciyar duk wanda ke tsaye banda Nurses d'in nan, banda Nurses d'in nan dake hango query da zasu iua amsa in har basu maoda ita gadonta ba.

Daga inda take tsaye, mahaifiyarsa ta tsaya ta kalle ta, a shekarun zamanta kaf da Maryam ba zata iya tuna rana d'aya da ta b'ata mata rai da gangan ba, ita d'in mai tsananin biyayya ce ga mijinta da kuma su, har wasu a danginta na cewa tunda bata da 'yanuwa su ta same su ai dole ne ta rik'e su, saboda haka yadda take tsaye a yanzu ba tare da ta kalli d'aya daga cikinsu ba, kuma ta shige jikin Sadiq d'in da a gaban idonta ko hannunta bata bari ya tab'a, ya tabbatar mata cewar bata cikin haiyacin da zata fahimci komai sab'anin abinda take so.

"Abubakar ka tabbata ba matsala?"

A rayuwarsa kaf! Sadiq ya san sau biyu ne ta taba kiransa da Abubakar, a ranar da ta kira shi a waya yana makaranta ta shaida masa zancen rasuwar mahaifinsa, sai kuma ranar da yaje mata da maganar auren Mairon, saboda haka ya tabbatar da ta fahimci halin da Mairon ke ciki, ta fahimci cewa idan aka maida ita cikin asibitin nan tabbas su dukkansu sun zalunceta.

"Wallahi babu matsala Mama, so take yi kawai ta gansu.."

"Alhaji mu fa ya kamata mu tabbatar muku da hakan ba ku da kanku ba, don haka ku bada ita a maida ta."

Bai ko saurari Nurse d'in ba ya cigaba da kallon Mahaifiyarsa wadda ke k'ara tambayarsa sunan garin 'yanuwan nata.

"Kaje ka kaita Sadiq, amma ku tafi tare da Zakkiyya ta rik'e Muhammad, don ba'a san abinda zai faru ba... Insha Allah zuwa gobe zan turo su Umar su ga me ake ciki."

Wannan izinin na mahaifiyarsa, shi ya haddasa tafiyar da d'ayansu bai shirya mata a yau ba. Don Nurses d'in nan babu yadda suka iya suna gani likitan dake duba ta ya sallame ta da tulin magunguna, saboda yana zuwa shima yaga halin da ake ciki yace ai dole ne ayi mata abinda take so don in ba haka ba zuciyarta zata iya sake bugawa kwatankwacin na da.

A duk abinda ake yi Mairo na rik'e da Sadiq wanda ke ta bata hak'uri da cewa zasu tafi yanzu, don duk tarin jama'ar dake kansu kaf! Shi kad'ai take gane abinda yake cewa.

Kafin a kammala komai d'aya k'anwarsa ta koma gida ta d'ebo musu 'yan kayayyakin sakawa da zasu buk'ata, kuma har a lokacin Mairo bata karbi Muhammad dake ta ihunsa ba har ya gaji yayi baccinsa a bayan Zakkiya, kowa a wajen nan ya tausaya mata don sun shaida cewa da gaske ne bata cikin haiyacinta, in ba haka ba meye zai shafe tausayin dake tsakanin uwa ga d'anta?

A waje biyu kawai suka tsaya kafin su hau kan titin express way, inda Sadiq ya tsaya ya siya musu tulin abinci sai kuma gidan mai da ya cika tankin motarsa taf.

Tunda suka d'auki hanya kuwa, idanun Mairo na kafe akan titi, bata sake cewa komai ba, kuma ko sau d'aya bata juya ta waiwayi su Muhammad dake zaune a baya ba, Shi kansa Sadiq baice da ita komai ba, don abinda ke faruwa a cikin kansa ma ya ishe shi.

Ya riga ya yarda cewa tabbas lokacin rabuwarsa da Mairo ne yazo... Ya kama hanya zai kaita inda baza ta taba dawowa gare shi ba, don ya san babu abinda zai hana ragowar asirin nan kwancewa in har tayi ido biyu da mahaifarta!

***

Akwai wani zane a hannunta irin na 'yan indiya, anyi shi da kalolin bak'i da kuma ja, duk da ba zai iya tuna yaushe a rayuwarsa ya tab'a kallon film d'in india ba, ammma yasha ganin hotunansu kuma hannunsu da irin wannan zanen na flower daya fito d'al akan farar fatarta.

Ya rufe idonsa ya sake yin baya cikin lallausar kujerar falon da yake zaune, a daren jiya baccinsa kad'an ne, don rabin daren ya shafe shi ne wajen rubuce-rubuce na fitar da yadda zaman kotun na farko ya kasance da kuma yadda zai shiryawa na biyu, sannan da yadda tsarin tasa hanyar zai cigaba da tafiya.

Bayan ya gama kuma da yaji baya jin bacci sai ya tashi kawai yayi ta sallolin nafilarsa yana rok'on Allah daya bashi sa'a a shari'ar na, sannan kamar kullum yana neman yafiyarsa kan yadda ya shafe rabin shekarun rayuwarsa yana bauta ga wani abun daban. Sai gashi a yanzu d'an baccin da yake nema kuma ya gagara, kwakwalwarsa tak'i hutun, bayan idanun Fadeelah yanzu ta bud'e wani sabon shafi kuma na tunanin hannayenta da zanen da aka yi musu.

Ya san cewa abun yayi masa kyau ne, amma kuma abu nawa ne yayi masa kyau kuma yake saurin manta shi, me yasa sai komai nata ne zai tsaya a kansa?

Motsin shigowa cikin falon yasa ya bud'e idonsa, Sadiq ne d'auke da ledoji na abincin da yaje siyo musu, yayi zaton ma Awwal ne ya fito, wanda tunda ya biyo Sa'id daga wajen kotun jiya yak'i komawa ya samu d'aki yayi kwanciyarsa.

Yaga alama kamar Sa'id d'in ya damu don da alama Awwal bashi niyyar komawa Ikara kwata-kwata, amma shi bai damu ba don ya san yana da faragar da in mutum talatin daga Babban gida zasu dawo k'ark'ashinsa a yanzu zai iya d'aukar nauyinsu. Ya dad'e da yarda cewa DANGI kowanne iri ne kuwa sune ginshik'in kowanne mutum a duniya.

Sa'id ya shigo ya gaishe shi sannan ya ajiye ledojin akan center table na falon.

"Yaya ina son anjima inje Ikara."

Yaji shi amma sai ya d'anyi shiru yana wani tunanin kafin ya amsa.

"Shi yasa nace maka kamata yayi mu sayi wata motar kawai, guda d'aya tayi kad'an a wannan zirga-zirgar."

A jirgi dukkaninsu suka zo, sai suka biya wani direba ya taho musu da motarsa.

"Yaya in dai ba kyauta zaka yi da ita in mun tashi tafiya ba, ni gani nake yi asarar kud'i ne kawai."

"Kyautar nayi niyyar yi da ita ai, naga Baba yana yawan zuwa cikin Zaria, kaga sai kawai Jamil (d'an kawu Ibrahim d'in) ya dinga kawo shi duk sanda zai zo tunda ya iya driving."

Sa'id ya gyad'a kansa.

"Hakan yayi, zaiji dadi kuma Allah ya saka da alkhairi."

"Ameen." Fatar bakinsa ta furta ba tare da sautin ya fito ba.

Har Sa'id ya mik'e zai shuga ciki ya tsaida shi a ta hanyar kiran sunansa.

"Sai'd ya sunan abun da naga mata suna zanawa a hannunsu?"

Mamaki ya d'an kama shi.

"Yaya wai k'unshi?"

"Sunansa kenan?"

"Eh k'unshi ko lalle suke ce masa."

"Saboda me suke yi?"

"Saboda kwalliyarsu kawai, amma yawanci sai za'a yi bikin aure suka fi yinsa, musamman ita amaryar kusan dole ne ma tayi k'unshi."

...ranar da aka fara bikina ne, komai ya tarwatse, Sadiya ta gan ni sannan Mairo ma tazo nemana, ni kuma ganinsu ya tayar min da ciwo na, ban sake fahimtar komai ba daga hakan sai bayan na farka Mami tace min Al'ameen ya dakatar da d'aurin auren namu saboda halin da nake ciki.

Iya wadannan kalaman nata a lokacin da take bashi labarinta suka gutsiro suka haska cikin kansa, Ya Allah! Ya akayi ya manta da hakan, ya akayi ya manta daga ita har Kawu Ibrahim dasu Mami marik'anta sun shaida masa cewa a ranar da aka fara bikinta wannan hargitsin ya fara? Shine har zai zauna a cikin kansa yana yaba kwalliyar da ta yiwa wani?

Ganin Adam bashi da niyyar sake magana yasa Said ya juya ciki yana tunani me ya had'a k'unshi kuma da zancen wannan shari'ar.

Kusan minti talatin kafin ya iya goge tunanin k'unshin Fadeelah daga kansa, ya mik'e ya bud'a abincin da Sa'id ya ajiye, sai dai lomar farko tunaninsa ya sake hasko masa ita, wane irin abinci take samu a wajen? Zata ma iya cin abinda suka bata tukunna? Ko zata iya ci ya san tashin hankalin da take nad'e cikinsa ba zai barta taci na kirki ba, dole ne ma ta fara ramewa akan sanda ya fara ganinta, sai rufe nasa kawai ya mik'e ya shiga ciki.

Wasa-wasa, tunaninsa ya dinga k'aruwa, duk wani abu daya zo yi sai ya kwatanta shi da halin da Fadeelah ke ciki a lokacin, saboda haka ya rasa sukuni ko kad'an, aikin nasa ma ya kasa k'arasawa, yana jin hirarsu Awwal da Sa'id amma ya kasa cewa komai, daga k'arshe wani yanki na zuciyarsa ya kasa daurewa, ya gaya masa cewar bazai rasa shari'ar nan ba don kawai yaje yaga Fadeelah sau d'aya, shi lauyanta ne yana da damar da ko tsakar dare ya tashi zai iya zuwa yace a fito masa da ita ya ganta.

Saboda haka bai bari wani tunanin ya danne wannan ba, ya tashi ya shirya ya d'auki muk'ullin mota ya fita. Motarsa ce amma ta zama kamar ta Sa'id saboda ko a can Abuja yafi shi amfani da ita, shi yasa bai san abubuwa da yawa a cikinta ba, a yanzu ma yana kunna ta ya hau titi, wak'ar dake cikin Cd da Sa'id d'in ya sanya ta fara playing.

I can be your hero baby..
I can kiss away all the pain..
I will stand by you forever..
You can take my breath away.

Sai ya maida kansa ya jingina da saman kujerar, saboda yadda sautin wak'ar ya karad'e motar a volume d'in da Sa'id ya barshi.

Am I in too deep?
Have I lost my mind?
Well I don't care... You're here tonight!

Adam ya lumshe idanunsa yana kallon titin, ji yake kamar kowanne baiti dashi ake yi!

****

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

(☆_☆)

"Kai inda zaka san duk duniya ba inda munafunci yake tasiri kamar Babban gida, ace wai baturen nan yazo amma kowa haba-haba yake dashi, kai ba zaka ci kowa yana wajen ba sanda aka kafa dandalin Allah ya tsine masa."

Isah d'an gidan Kawu Bashir ya fad'a sanda suke zaune a dakalin dake gaban wani k'aton gida na k'asa bayan maghriba tare da wasu 'yanuwansa da abokansa. Saminu d'an gidan ne ke sayar da rake a wajen saboda haka sai ya zame musu kamar dandali, harda ba siya yazo yi ba sai ya zauna a shiga hira.

"Kud'iii...! Ake gaya maka yaro, kaima kayi kud'i ka gani wallahi har babanka durk'usa maka zai yi, har ka mutu kuwa in kana dasu baza ka taba jin mai zaginka ba." Cewar wani abokinsa.

"To yanzu ma meye ba'ayi ba, shi baban nawa da yazo kaga wani sussunkuyar masa da kai da yake yi, ance fa har zancen shari'ar sai da suka yi dashi."

"Ai shi yasa kullum nake cewa Sa'idu ya haye wallahi, don ance fa yanzu ma aiki yake nema masa a can Abujan." Cewar Saminu yana kankare rakensa.

"Yanzu ai kwa fad'i hakan..." Wani Ibrahim d'an bayan layin ya sako baki.

"Sanda ya dage yana karatunsa, ba daku ake kafa hirar wai shi ya nacewa boko zai je ya dawo ya same ku ba, daya gama ya fara zama a shagon babansa wace irin dariya ce ba'ayi daku anan ba, yanzu ai gashi nan tana kai masa."

"Ni yazu duk ba wannan ba..." Cewar Aminu yana gyara zamansa.

"... Rayuwata ce ta shiga kwale-kwale zuwan mutumin nan wallahi, don tunda yazo Asma'u ta fara canja min fuska, itama ta shiga layin haukan dake tashi a cikin gidan wallahi."

"Haukan me?" Buhari ya tambaya yana gaftarar raken hannunsa.

"Au wai kai baka san me akeyi ba? Lallai an barka a tasha wallahi." Cewar Saminu.

"Dan Allah me yake faruwa?" Ya tambaya da zumud'i.

"Tsaya in fara tambayarka a hankalinka kwana biyun nan baka ga yadda ake bawa Kawu Ibrahim wani girma bane?"

"Eh na lura kuwa don d'azu ma ina ji Ramatu tana cewa 'yarta ko za'a kai masa me?"

"Toh yanzu duk Babban gida, ba zan d'ebe maka kowa ba sai masu yara k'anana, fata suke Kawu Ibrahim ya had'a ya'yansu aure da wannan baturen hatta su 'yanmatan kuwa, duk hankalinsu ya koma kansa don sunga yadda yake jin maganarsa."

"In dai Kawu ne kuwa zasu yi su gama ne, don in baiyi niyyar abu ba, babu mai saka shi."

Kafin d'aya daga cikinsu ya sake cewa wani abun, suka hangi tahowar wata mulmulalliyar mota da tayo full light jan layin kuma daidai saitin Babban gida inda suke zaune.

"Toh 'yan gida sai su shirya ga wani baturen nan."

"Kai haba?" Cewar Isa yana d'ago da kansa.

"Duba da kyau ka gani, duk layin nan ka san ba mai wannan motar kuma ku kad'ai ne ke da 'yanuwa masu irin wannan k'ashin arzik'in."

"To kuma an ta zuwa kenan?" Cewar Saminu yana kallon motar da babu tantama saitinsu ta take tahowa.

"Kut!" Cewar Buhari.

"Allah yasa da gaske kuwa wani baturen ne yanzu in samu wajen zuwa wallahi."

Ya fad'i hakan ne daidai sanda motar ta tsaya gaba kad'an dasu, kuma ba da wani b'ata lokaci ba k'ofar gaba ta mai zaman banza ta bud'e, sannan wata mace ta fito daga ciki.

Hasken kwan lantarki, hasken farin wata da kuma hasken fitilar motar dake gefe ya shaida musu siffar wata kyakkyawar matashiyar mace sanye da dogon hijabi, basu take kallo ba k'ofar Babban gidan dake gefensu nan ta kafe idanunta ba ko k'itawa tana kallo, duk cikinsu ba wanda ya gane ta saboda haka suka sake bin mutumin daya gito daga mazaunin direba da kallo shima.

Sai dai me? Saminu na d'ora idanunsa akan mutumin daya zagayo inda macen ke tsaye wani tunani ya d'arsu, da sauri ya sake maida idonsa kan macen, ai kuwa bai san sanda ya saki raken hannunsa ba sannan bakinsa ya lailayo wani irin zagi.

"Ashe Sadiya da gaske take kenan? Jama'a baku gane ta bane? Mairo ce fa."

"Wace Mairon? Da yawansu suka hada baki wajen tambaya.

"Mairo dai ta gidan man, k'anwata!"

***

Gabanta fad'uwa yake yi a lokacin da dukkan wata ma'anar tsoro ta duniya, likacin da tayi ar ba da tsirawa barandar k'ofar gidansu kuma mahaifarta, barandar kofar gidan waje ne da Babanta yake zama tare da abokansa kullum bayan sallar magriba, wani lokacin har ta fito musu da abincin dare suci anan sannan suyi isha kafin ya shigo gida.

Sai ta motsa kafafunta ta nufi ciki, ba abinda take fahimta na gefenta har ta shiga cikin zaure na farko wanda banda shafen farar k'asa, bai canja ba ko kad'an daga yadda yake, zaure na biyu ma yana nan d'auke da d'akuna guda uku na yayyenta maza a wancan lokacin. ('Yayan Gwaggo lami.)

Daga nan sai k'ofar da zata kai ka cikin gidan, tun kafin ta shiga, kwakwalwarta ta tuno mata da yadda cikin gidan yake, k'aton tsakar gida mai d'auke da bishiyar darbejiya wadda take kamar ruhin gidan don kusan komai a k'ark'ashinta ake yi, sai
daga gefen dama kuma d'akin iyayensu jere cikin layi kowanne ciki da rumfa, dakin Baba da wani store da yake ajiye amfanin gonarsa sune a farko kafin a kai ga nasu inartata, sai daga d'aya bangaren mai kallowa kuma d'akuna biyu ne kowanne falle d'aya, na farko na saukar baki ne sai kuma nata da Baba ya ware mata tun daga sanda ta shiga boarding.

Kicin da makewayi suna daga b'arin hagu na k'aton tsakar gidan sannan kuma garkensu in an zagaya baya.
Sai dai me, tana karya kafarta cikin tsakar gidan, wata irin hayaniya ta daki kunnuwanta, hayaniyar da har ta k'are rayuwar gidan kaf bata taba sanin makamanciyarta ba.

"Na rantse da mahallicina sai dai ayi uw*ar da za'ayi yau a cikin gidan nan amma sai na kwaci hakkina, bashi har wata nawa."

"To ba sai ki kwata ba mu gani, in kin isa ke 'yar halak ce Safiya ki shiga d" akina ki yashe shi tsaf shine zan yadda kin damu da bashinki."

Idanun Mairo suka gane mata mata fal an taru a k'asan wannan darbejiyar sai rik'e mutum biyu akeyi wanda da alama sune masu fadan, bata yi ko sallama ba amma da idon wata daga cikinsu ya hangota sai tace.

"Wa'alaikum salamu shigo."

Jin hakayasa kusan duk suka maida hankalinsu kan k'ofar kafin wata ta sassauta murya tace.

"Larai, kinga dai ga bakuwanan, kiyi wa girman Allah ki hak'ura kar..."

Kalmar Bakuwa ta daki Mairo a tsakar kai, itace bak'uwa? Itace yau ta zama bak'uwa a gidan ubanta?

"Sannu da zuwa Hajiya, Gwaggon kike nema?"

Wata Dattijuwar mace ta fada tana kokarin durkusawa Mairo, sai tayi saurin fakatar da ita ta hanyar cewa.

"Inna Amina nake nema?"

"To fa? Kuma a gidan nan aka kwatanta miki ita?" Cewar wata data k'araso.

Muryarta na shirin rawa tace.

"A gidan nan take, matar gidan ce."

"Ai Amina a gidan nan d'aya ce, kuma watan daya mutu ma suka tashi, tunda taje gida wankan haihuwa bata dawo ba."

"Ita wadda nake nema babba ce."

"To Hajiya anya kuwa nan ne?"

"Sai dai ko a tambayo Gwaggon." Cewar wata matashiya goye da d'a."

"To Inna Saratu fa?"

Matashiyar tayi dariya tace.

"Hajiya ni kad'ai ce Saratu a gidan nan amma ni ba Inna bace."

"Kinga bari dai a kaita wajen Gwaggon, shigo muje Hajiya."

Sai ta taka ta bita ba musu, sauran matan na tsaye sai kallonta suke yi kamar sun ga wani abin mamakin, amma ita ba tasu take yi ba, idonta na kan ginin d'akunan gidan, komai yana nan yadda yake sai k'ara tsufa da yayi, ga tarkace nan a jibge koina, mamaki ya kamata, ta tuno sanda koina yake fes! Sanda zata d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan nan duk girmansa. Kafin ta waiga ta hango k'ofar d'akinta suka sha kwanar da zata kaisu garke.

Sai dai a yanzu ba garken ne a wajen ba, gini ne a tsaye kyam na bulo har da fentinsa kalar ruwan madara.

"Salamu Alaikum, Gwaggo bak'uwa kika yi."

Kubra ta fad'a sanda ta tsaya a k'ofar d'akin.

Numfashin Mairo yayi kokarin zarcewa sanda muryar Gwaggo Lami ta kwararo daga cikin d'akin, gwaggo lami dai data sani Uwargidan mahaifinta.

"Bana son rainin hankali Kubra, wace bak'uwa zanyi a daren nan? In zancen kud'inki ne banda canji."

Da wannan fadan, wannan fad'an dai da kowa ya santa dashi tayi maganar.

"Alqur'anin Allah bakuwa kika yi, lek'o ki ganta." Cewar Kubran.

Kamar ba zata leko ba sai kuma can ta d'age tattararren labulen ta zuro fuskarta, kallo d'aya ta yiwa fuskar Mairo ta mik'e ta fito.

"Ya rabbis samawati wal'ardi! Kar dai Mairon Amina nake gani? Mairo kece? Daga ina? Dama da gaske Sadiya take ta ganki?

Mairo kawai kallonta take yi da mamaki itama, itace dai Gwaggo lamin da ta sani amma tsufa ya kamata fatarta duk ta yamushe sannan jikinta ma ya tsomare.

"Gwaggo nice na dawo, ina Innata take da Inna saratu, na tambaye su sunce basu gane ba."

"Au da kuka had'u da Sadiyan bata shaida miki ba? Ai Amina ta mutu babu dad'ewa da barinki gida, Saratu kuma tana can Kaduna tayi aure."

Mairo ta hadiye yawu mai zafi cikin makogwaronta, abinda Sadiya ta fad'a gaskiya ne kenan, mamarta ta mutu.. Innarta mai tsananin sonta wadda ta raini ta da dukkan kulawa, daidai da rana d'aya bsta taba bari kunya irin ta uwa da d'iyar fari ta shiga tsakaninsu bud'e zuciyarta take ta fad'a mata komai, don ta maida ita kamar k'awa ko kuna k'anwa da bata da ita.

Wani irin kuka da bata shirya masa ba ya faso daga bakinta sannan ta durk'ushe a wajen.

"Au, au... Yanzu kika san ciwon Uwa Mairo? ai na zata dadi soyayyar saurayi tasha gaban

Please Login or Register in order to submit comment