Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon kujerar.

Ta san cewa an tashi daga makaranta ne a lokacin, don haka ba d'alibin da zata gani, amma mai zaman wajen fa? (Librarian) ya kamata ace shi yana zaune akan kujerarsa da take kallo fanko a gefenta.

"Mr. David baya nan."

Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ba don ta san cewa haka take a baya ba, zata ce ya rage sautinsa ne don a d'akin karatu suke. Ta juyo ta sake kallonsa, yana jingine da kujerar da yake kai yana kallonta ta k'asan lumsassun idanunsa. Taji tana son ta waska masa mari yadda zai dad'e bai sake bud'e idanun ba.

Sai kawai ta d'auke nata idon gefe sannan ta k'araso wajen teburin, ba yadda zata yi dole ne ta tsaya wajen mutumin da ada, bata tab'a barin zuciyarta ta yarda cewa ma yana raye.

"Me ya tsaida ke har mintuna goma sha biyar?"

Lallausan turancinsa ya nad'o kalmomin cikin sautinsa, wannan sautin nasa data tsana kamar me. Ya Allah ta tsani komai nasa ma.

"Naje sallah ne."

Muryarta ta fito kai tsaye babu gargada, a wayewar safiyar yau, ta furtawa kanta cewa 'zata iya' yafi sau cikin carbi, sannan ta nunawa su Melisaa dake ta sukar abin dauriyarta da kuma tabbacin cewa zata iya d'in, me yasa sai a gabansa zata k'aryata kanta?

"Na d'auka Sallar bata wuce minti biyar."

Ba tambaya yayi ba, fad'a yayi kamar kamar yana bata tabbaci ne. A cikin shawarar da Melissa ta bata harda cewa tayi k'ok'arin b'oye addininta a gabansa, amma saboda me? ta tambayi zuciyarta, zata yi mu'amala dashi na tsawon lokacin da bata tantance ba kuma a daidai lokacin da sallar azahar ke shiga, toh saboda me zata b'oye kanta bayan ya riga ya san ko ita wace ce?

"Baka da hurumin da zaka yi magana akan addinina, don ba abinda ya kawo ni nan kenan ba."

Abinda ta koya a k'ungiyar 'Musulm Support' sanin hanyoyi ne na yadda zasu kare kansu daga mutane irinsa masu k'alubalantarsu, amma Allah ya sani, ko kad'an zuciyarta bata kwanta da wannan tsarin ba, saboda ta yarda cewa a lokacin da mutum ya nuna tsoronsa, a lokacin hanyoyin da za'a sami galaba akansa ke k'aruwa.

Ga mamakinta sai ya gyad'a kansa a hankali sannan ya nuna mata kujerar gefenta alamun ta zauna. Ta dire jakarta akan table d'in dake tsakanin kujerar da tasa sannan ta zauna.

Ya mik'e zaune sosai.

"Yaya ma kika ce sunanki?"

"Fadeelah."

"Right, leelah..."

"It's Fadeelah." Ta katse shi da sauri.

"Fadlah?"

Sai ta juya idanunta kawai ba tare da ta kalle shi ba tace.

"Ka fad'a kawai yadda zaka iya."

Ya sake gyad'a kansa a hankali sannan ya juya jakarsa d'auko wani abin, sai a lokacin ta kalli fuskarsa sosai, fuskar dake b'oye halayyarsa a idanun mutane, fari ne sosai amma ba irin farin turawa ba Allah kad'ai ya san daga wace k'abila ya fito, dogon gashin idonsa ya kwanta akan na k'asa yabi saitin cikin jakar da kallo.

Zuciyarta ta matse da tunanin suna zaune a waje guda ne kuma suna shak'ar iska d'aya, daga yadda take jin k'amshin turarensa wanda ta haddace a gefen lokarta, k'amshin da tayi wa tambari da NASA.

Ya fito da tarin takardu fal! sannan ya d'ago ya kalleta, sai ta zame idanunta kan jakarta.

"Kafin mu fara komai, in kina da abin cewa, wannan ce damarki."

Kanta yaso ya d'aure, abin cewa kamar me? in ba addu'a yake nufin ta bud'e taron da ita ba ita bata san me yake nufi ba.

"Baki da wani abu da zaki fad'a min?"

Ya sake tambaya a hankali. A can cikin kwakwalwarta ta rubuta cewa dole ne ta sabawa kanta da wannan sautin muryar tasa.

"Abinda zan fad'a maka kamar me? na d'auka nazo nan ne don ka koya min lissafin da ban iya ba, ba don na fad'a maka wani abu ba."

Ta fad'a a lokacin da ta d'ago tana kallonsa ta cikin glass d'in idonta.

"Eh na san abinda ya kawo ki ai, amma ina tunanin kafin mu fara komai akwai wani abu da ya kamata mu fara tattaunawa, don hakan ne kawai zai sa mu san irin hanyar da zamu bi."

Fadeelah ta hard'e hannayenta a kirji, zuciyarta cike da d'acin yadda yake maganarsa hankali a kwance alhalin ita dukkan nata tunanin a dagule yake.

"Bani da wani abu da zan tattauna da kai in ba lissafi ba, saboda haka ko ta wacce hanya ne ma ka bi."

A cikin kanta ta fassara kallon da yake mata da na rainin hankali, kamar yana kallon wata k'aramar yarinyar da bata iya kirga 'one plus one' ba.

Sai ya mik'o mata wata paper da babu komai a jiki, ta karb'a.

"Bari mu gwada wannan hanyar, ki rubuta min sunayen subject guda biyar a wanda na baki friday."

Bata ko kalle shi ba ta zaro biro a cikin jakarta ta shiga rubutu, sai da ta jero su guda ashirin da biyu sannan ta mik'o masa ba tare da ta d'ago da kanta.

"Kinyi k'okari." ya fad'a ganin ta rubuce su duka.

Sai ka fara gyara tunaninka akaina!

"Wanne kike ganin kinfi iyawa a ciki?"

Kamar ta zab'i wasu a cikinsu ta nuna, sai kuma taga meye amfanin zuwanta kenan, saboda haka kai tsaye tace.

"Kowanne ina da matsala dashi."

"Haka na gani a takardunki."

Ta d'ago da kanta lokacin da yake fito da gabad'aya papers d'in ayyukanta na Maths wanda Mr. Hawkins ya tattaro masa, sai ta had'iye yawu sannan ta godewa zuciyarta da bata yi k'arya ba.

"Kin taba tambayar kanki me yasa bakya gane lissafi?"

Tambayar tasa ta d'ago da kanta a lokaci d'aya ta kalle shi, wani abu ya motsa a cikin kanta, kwakwalwarta ta maimata tambayar, Me yasa bata gane lissafi?_ Taji a jikinta cewar tambaya ce da ya kamata ace ta dad'e da yiwa kanta tun farko, me yasa take gane komai amma banda lissafi.

"Bud'a takardunki ki gani."

A hankali tasa hannunta ta janyo papers d'in dake kan table d'in, ta shiga bud'a su d'aya bayan d'aya, a jikin kowacce, a kan kowanne lissafi akwai iya wani waje da aka zagaye da jan biro.

"Duk inda kika ganshi a zagaye daidai kika amsa tambayar, daga k'asan sa ne kika kuskure wani wajen, saboda haka in kin kula zaki ga kowacce tambaya kin amsa rabinta daidai ne, rabi kuma yake fad'ar dake.

Saboda haka dole ne da akwai dalilin da yasa kike gane farkon kowanne lissafi kuma kike fad'uwa k'arshen kowanne."

Tayi shiru tana bin takardun da kallo, ita bata tab'a tunanin tana yin wani abu daidai ma a Maths ba, ta d'auka komai shirme take yi saboda data fara take jin kwakwalwarta ta cushe komai ya d'auke mata.

"Shi yasa na tambayeki idan akwai wani abu da zaki gaya min kafin mu fara."

"Ni bani da wani abun da zan fad'a maka, ban san komai ba."

"Kinga leelah..."

"Its Fadeelah..."

"Na kasa fad'ar hakan, kince zan iya fad'ar yadda zan iya."

Muryarsa da zurfi ta fad'a, sai ta gyad'a kanta kawai ba tare da tace komai ba.

"Idan muka ce zamu fara karatun nan a haka, baza a sami banbanci da yadda kike ganewa a aji ba, idan akwai matsala a abu dole ne sai an magance ta in ba haka ba, baza'a tab'a cigaba ba."

"Kana nufin akwai abinda ke hana ni ganewa kenan?"

"Haka nake nufi, kuma ke kin san kanki, idan kina da wata matsala ko yaya take, say it! zai taimaka miki sosai."

Tayi shiru tana murza yatsunta, bayan matsalar 'Memory loss' d'inta bata san wani abu dake damunta ba, sai dai in har ta bud'e baki a yanzu ta fad'i hakan, ta fad'a masa wani rauninta ne a matsayinsa na mak'iyinta.

Wani abu da baza ta tab'a bari ya faru ba, baza ta tab'a bari yaga gazawarta ta koina ba balle har ya samu damar danganta hakan ga sauran musulmai 'yan uwanta.

"Zan baki lokaci kiyi tunanin sosai, nan da zuwa kwana biyu."

"Kwana biyu?" Ta tambaya da mamaki.

"Subject ashirin da biyu nake dashi a cikin kwanakin da basu fi wata d'aya ba, amma har za'a sami kwana biyun kawai da zan zauna ina tunani?"

Ya cije gefen lebbensa na k'asa yana kallonta da idonsa a lumshe.

"Na fad'a miki baza mu iya fara komai ba sai mun san matsalarki, sauran karatun abu mai sauki ne da zamu iya gama shi in har ba matsalar."

Ta tsani yadda yake amfani da kalmar 'Mu' tsakanin shi da ita, kamar ta sake cewa wani abin sai zuciyarta ta gaya mata ai itama hutun ta ne baza taga fuskarsa har na kwanaki biyu ba, saboda haka ta mik'e tsaye ta d'auki jakarta.

"Ina ga ba amfanin zama na anan kenan."

Da haka ta juya ta fita daga cikin library d'in. Ta isa daidai gate d'in makarantar sanda yazo ya wuce ta cikin motarsa.

***

"Hace tiempo que no te veo!"

(Na dad'e rabon da in ganki)

Direban Bus d'in ya fad'a sanda yake mik'o mata metro-card d'inta bayan ya d'auki kud'insa.

"Abubuwa ne suka d'an min yawa, amma ina nan..." Ta amsa masa cikin harshen turanci sanna ta k'ara da..

"...muchas gracias." Hakan na nufin ta gode sosai.

Sanda ta sauka daga cikin motar, kwakwalwarta na ta aunawa da tarawa ne akan maganar da ya fad'a mata, da ace akwai wani abu dake damunta bayan matsalar kwakwalwarta, da tun farkon zuwanta asibiti Dr. Gibert ya fad'a mata ko kuma a yanzu da take ganin Dr. Florence ta san da hakan.

Ta yaya za'ace don kawai yaga takardunta ne zai yanke hakan, shi kad'ai ransa? kuma har yana fad'in taje tayi shawara ta samo matsalarta, sai yanzu sosai ta fahimci rainin hankali k'arara a cikin zancen.

A baya tayi kokarin goge tunani irin nasu melissa a cikin kanta amma a yanzu kwakwalwarta ta fara gano ingancinsa, dole ne akwai wani dalilin da yasa ya kawo kansa cikin rayuwarta, akwai wata manufarsa daban da yake son cimma, kuma tayi wa kanta alkawari in har da ita yake tunanin amfani yayi koma me yayi niyya to sai dai su rasa damarsu su duka biyun!

Da haka ta k'arasa k'ofar gidan nasu, ta tsaya a barandar ta danna door bell dake gefe.

"Aunty deelah! kin san su waye suka zo?"

Iman ta fad'a da k'arfinta sanda ta wangale k'ofar.

"Su waye?" Ta tambaya sanda ta shigo ciki tana kokarin cire takalminta.

"Aunty Miryama dasu Haneey! Kuma kin san me? wai sun dawo nan gabad'aya."

Gabanta ya fad'i a lokaci d'aya, ta juyo da sauri ta kalleta.

"Nan ina?"

"Nan garin mana, anjima ma zamu je muga sabon gidansu! Dad'i nake ji sosai... Haneey tace tana da games d'in su Moana da yawa kuma har da..."

Daga nan corridor d'in tana iya jiyo muryoyin mutane dake ta tashi daga falo, Aunty Miryamah 'yar uwar daddy ce ta dangin mahaifinsa dake zaune a garin Vegas ita da mijinta Balarabe da kuma 'yayansu guda uku duka mata. Fatimah, Sa'ar Zahra guda d'aya, sai wadda ta girmi Iman Aysha da kuma sa'ar Iman d'in Haneefa.

A farkon zuwanta k'asar nan, lokacin Aunty Miryaman da 'ya'yanta sun zo hutu, matsalar da ta fara samu daga wajenta ne, don ba irin fad'a da maganganun da bata yi ba, akan rik'e ta da Daddyn yace zaiyi, ta dinga ziga Mami Saffiyya da shawara kala-kala akan kar ta yarda da zamanta sai da Daddyn da kansa ya taka mata birki sannan tayi shiru.

Ta fahimci ita macece da bata tab'a son wani ya rab'e ta ita da 'ya'yanta, don duk shirin da suke da Mami Saffiya ma, su Zahra basu cika zuwa gidanta ba don ko sunje d'in ba wata kulawar kirki suke samu ba.

Ta k'arasa cikin falon jikinta a sanyaye sanda Mami Saffiya ke fad'in.

"Har kin dawo deelah, nayi zaton sai nan da awa d'aya."

Aunty Miryaman dake zaune a gefen Mami ta juyo jin hakan, tana sanye cikin doguwar riga bak'a ta abaya, ta had'e girar sama data k'asa kamar mai shirin lailayo zagi.

"Eh, Mami bamu fara ba tukunna sai jibi."

Ta fad'a muryarta a hankali sannan ta tsugunna har k'asa ta gaishe ta.

"Lafiya." Bakinta ya motsa kad'an ba tare da wani sauti ya fito ba, sai ta juya gefen Mami tace.

"Dama har yanzu wannan yarinyar tana nan? kinyi kokari wallahi Saffiya kinyi k'okari!"

A baiyane yake tun da bata tab'a b'oye kiyayyarta ko a gabanta ne kuwa.

Fadeelah na ganin yadda Mami ta d'anyi murmushi alamun bata ji dad'in hakan ba, sai ta mik'e da sauri tayi hanyar d'akinsu amma kafin ta isa kunnenta ya jiyo mata Aunty miryaman na fad'in.

"Kuma har yanzu tana fama da wannan ciwon haukan?"

Ta rufe k'ofar da sauri sanda kowannensu ya d'ago ya kalleta. Zahra da sa'arta Fatima nata danne-danne cikin Ipad dinta yayin da Iman ke nunawa Haneey stickers d'inta na cartoons, d'ayar Aysha na daga can jikin zanenta tana kallo.

"Kin fara lesson d'in?" Zahra ta tambaya lokacin da Fatiman ta maida kanta kan abinda suke yi, ba tun yau ba ta fahimci dukka 'ya'yan halinsu d'aya da mahaifiyarta, Aysha ce kawai mai d'an saukin kai a cikinsu. A baki su 'ya'yan musulmai ne, amma a d'abia da tarbiyya basu da banbanci da 'ya'yan turawa, akwai layi mai kauri tsakaninsu da 'ya'yan Mami.

"A'ah Zahra, sai jibi tukunna."

"Amma ko waye ya raina miki hankali wallahi, zaman da kika yi a banza kenan?"

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, don a yanzu zancen Aunty Miryamah ya shafe na Adam a cikin kanta.

Ta ajiye kayanta sannan ta shiga band'aki tayi wanka, har ta shirya ba wanda ya kula ta a cikin 'ya'yan itama bata bi kansu ba ta saka doguwar riga mai k'aramin hannu sannan ta d'aure gashinta cikin bun.

Har zata fita a haka, ta tuna da Aunty Miryama saboda haka ta d'auko hijaabinta ta zura. Sanda tazo wuce su ta falo, kanta na k'asa saboda haka bata ga irin banzan kallon da Aunty Miryaman tabi ta dashi ba.

Tana shiga kitchen ta cire hijaabin ta fara kokarin had'a tea don haka kawai taji bata sha'awar cin abinci.

"Fadeelah."

Mami ta kira sunanta sanda ta shigo kitchen d'in. Da murmushinta ta juya ta kalle ta.

"Dan Allah kar ki saka zancen Miryamah a kanki ya dame ki, tun farko bata fahimce ki bane amma na tabbata tunda yanzu sun dawo kusa damu komai zai gyaru insha Allah."

"Insha Allah Aunty, ba komai." Ta fad'a da murmushi ba tare da ta tabbatar da abinda ta fad'a ba, don daga yanayin Aunty Miryamah bata tunanin ko tunda aka haife ta suke tare zata tab'a sonta.

A hakali ta juya ta cigaba da kokarin zuba sugar da take yi a cikin madara. Sanda ruwan zafin dake cikin kettle ya tafasa take zubawa, lokacin taji motsi a bayanta, tayi zaton Mami ce saboda haka bata juya ba har ta gama had'a tean ta.

"Uhmm... ina kike ganin zan ajiye wannan?"

Da wani irin sauri ta juyo jin muryar namiji a bayanta.

Ai kuwa karaaf! idanunta suka shiga na cikin wani saurayi daga bakin k'ofar kitchen d'in, yana tsaye hannayensa rik'e da manyan ledojin siyayya. Kallo d'aya tayi masa idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala.

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... sai a lokacin kuma ta tuna irin rigar jikinta sai ta juya baya da sauri ta lalubo hijaabinta ta zura, kanta cike taf da mamakin WAYE SHI kuma me yake yi a tsakiyar kitchen d'insu.

Sai dai muryar Aysha data shigo a lokacin, ta amsa mata dukkan tambayoyin a cikin jimla d'aya.

"Ya Al'ameen kazo inji Mommy zamu tafi yanzu."

Sai k'afafunta suka k'ame cike da tsananin mamaki, wannan d'an Aunty Miryaamah ne? Tayi zaton ai Fatima ce babbar 'yarta, ya akayi bata tab'a ganinshi ba?

Taji k'arar sanda ya ajiye ledojin akan counter kitchen d'in sannan muryarsa ta biyo baya, wata husky murya mai zurfi da kuma kwarjini, wadda ta fito da zallar matsayinsa na namiji.

"I'm sorry, kiyi hakuri na ganki a haka."


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

07

(☆_☆)

Tana tsaye daga bayan wata had'addiyar mota hannayenta rike da ledojin siyayyar nan wad'anda ta rik'o bisa umarnin Mami a lokacin da suka rako su Aunty Miryaman dake shirin tafiya.

"Toh shikenan idan ya dawo zamu yi maganar dashi, kince ma kuna buk'atar wata motar ta kai yara makaranta ko?"

Mami ta fad'a sanda suke cigaba daga tattaunawarsu daga bayan motar nan, wadda a cikinta yaran Aunty Miryamah ne dasu Zahra da zasu je su gano sabon gidan da suka tare.

Yana zaune daga mazaunin direba, ya saita mudubin gefensa yana kallonta tsaye daga gefen su Mamin, headphone ne a kunnensa wanda k'arfensa na sama yabi ya nutse luf! cikin sumar gashin kansa irin ta jinsin larabawa, a karo na biyu data kai idonta cikin mudubin suka had'a ido sai ta koma bayan Mami a hankali ta kare kanta.

A cikin zuciyarsa, tunani ne fal! na son sanin ina Mami ta samo wannan 'yar kamilalliyar budurwar da kuma sanda tazo, tunda shi dai ya san ko a wajen 'yan k'annensa bai tab'a jin zancenta ba duk kuwa da yana yawan ji suna hirar su Zahra, ya k'ank'ance idonsa kad'an yana hango gefen fuskarta ta tsakanin fuskar Mamin data tsaya a bayanta, haka kurum yaji yana da interest na son sanin wacece ita.

"Goben idan kin shigo sai muje mu siyo curtains d'in."

Aunty Miryama ta fad'a sanda ta zagaya can gaba zata shiga motar, har Mami tayi gaba tabi bayanta sai kuma ta juyo tace.

"Deelah wannan a booth za'a saka su... Al'ameen bud'e mata booth d'in."

Aunty Miryama da bata kai ga shiga motar ba ta juyo tabi ledojin hannun Fadeelan da wani irin kallo, kamar tana shawarar fasa amfani da kayan ciki ne tunda hannayen wadda tak'i jini sun tab'a. Har zata yi magana sai fitowar Al'ameen ta katse ta.

"Button d'in yak'i dannuwa daga nan, bari in gani..."

Ya rufe k'ofar motar, ya zagayo baya daidai inda take tsaye, yayi mata murmushi mai nuna alamun sannu sanda ya danna mukullin motar, booth d'in ya shiga d'agawa da kansa. Bata ce komai ta shiga k'ok'arin had'a bakin ledojin don ta saka, sai ya sunkuyo da hannunsa k'asa ya karbi na hannu d'aya, muryarsa mai zurfi kamar maganad'isu ta ratsa cikin kowanne senses na jikinta.

"Ban tab'a ganinki a gidan nan ba... Zan iya tambayar yaushe kika zo?"

K'amshin sassanyan turarensa ya busa a hancinta sai ta sakar masa ledojin cikin hannunsa ba tare da ta shirya ba, haka kurum taji ta takura a gabansa.

"Last year." Kwarjininsa yasa ta amsa hankali ba tare da ta d'ago da kanta ba.

"Fadeelan last year, ya akayi ba wanda ya tab'a fad'a min kinzo?"

Ta d'ago da kanta da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunanta, tunda take bata tab'a jin wanda ya fad'i harafan sunan daidai kuma yayi mata dad'i kamar shi ba, idanunta suka shiga cikin nasa farare tas! sai dai bata yi wani nisa ba muryar Aunty Miryama daga baya ta finciko ta.

"Baza ta iya sawa bane?"

A tsorace ta juyo ta kalli gaban motar, Mami na amsa waya yayin da Aunty Miryaman ke tsaye a jikin k'ofar motar ta had'e girar sama data k'asa tana kallonsu, sai dai shi bai saurareta ba don sake sunkuyowa yayi ya karb'i na d'aya hannun nata ya saka a booth d'in.

Sai ta juya da sauri ta koma hanyar cikin gidan idanunta na kallon yadda tafin hannunta yayi ja saboda nauyin kayan.

"Mommy wacece ita? Baku tab'a fad'a min tazo ba."

Ta jiyo muryarsa sanda yake komawa gaban motar.

Amsar da Aunty Miryaman ta bashi cikin harshen turanci ta daki kunnuwanta ba shiri ta bud'e k'ofar falon ta shige.

"Uwarka ce Al'ameen, dole ai a gaya maka in tazo."

***

"Dan Allah Deelah kar ki saka damuwar Miryama a cikin kanki, kiji da tarin abubuwan da suke gabanki, na gaya miki insha Allah zata fahimce ki tunda sun dawo nan gabad'aya."

Mami ta fad'a sanda ta shigo gidan ta tarar tana wanke plates d'in da akayi amfani dasu.

"Takurawar da ake yiwa musulmai ne a can Vegas yafi yawa akan nan, har wasu mutane sun jefi Aysha a ido sai da aka mata surgery shine mijinta yace gwara su dawo nan garin tunda ko ba komai akwai 'yan uwanta a kusa, shi kuma yana can sai ya samu hutu zai dinga zuwa.

Jiya suka iso kuma unguwar da ya kama musu gida babu nisa daga nan, don haka gobe zamu je gidan gabad'aya zan taya ta siyayyar wasu kayayyakin."

"Wallahi Mami ba komai fa ni ba wai damuwa nake yi ba, na fahimci kawai jininmu ne bai had'u ba kuma zan dinga k'okari ina kaucewa hanyarta insha Allah, saboda haka gobe ma in zaki je ba lallai ne in biki ba."

"Ai ba zai yiwu ba kuma, kema kamar kowa ce a gidan nan don haka baza'a taba ware ki a komai ba, kuma itama ta haka ne zata saba dake. Sannan ki k'ara hakuri akan abinda tace wa Al'ameen d'azu, na san kema baki sanshi ba, shine babban d'anta lokacin da kika zo yana England ne a makaranta."

Da murmushinta tace.

"Mami kuwa sai cewa kike inyi hak'uri kamar wani laifi aka min, wallahi na rantse miki ba komai ni banji wani abu ba."

"Toh Allah yasa, naso su Zahra ma sun bari sai gobe muje gabad'aya, yanzu dole sai sun saka shi ya dawo, wai ina Farouk yaje ne? Al'ameen d'in yana ta tambayarsa."

"Stadium, Ball."

"Haka ne wato yau babu Tahfeez."

Har ta juya zata fita, Fadeelah ta juyo a hankali ta kira sunanta.

"Mami me ya faru da kantin daddy kwanakin baya?"

Sai ta tsaya cak daga bakin k'ofar cike da mamakin yadda akayi zancen da suke b'oyewa ya fito.

"Waya fad'a miki wani abu ya faru deelah? me kika gani?"

"Sau biyu ina jin yana amsa wayar dake ke da alak'a da zancen kantin ne, kuma na san ba haka aka saba ba."

Sai Mami ta lalubo ajiyar zuciya ta d'ora a kirjinta, da farko tayi zaton ko Fadeelan taji tattaunawarsu da Daddy ne a jiya.

"Babu komai ba abinda ya faru, watakila zancen sabon xubin d'in da zasu fara ne yasa yake yawan wayar."

Sanda ta fad'i hakan, Fadeelah na iya hango rashin tabbacin maganar a idonta, sai dai bata son matsawa akan abinda bata yi niyyar gaya mata ba, saboda haka tace.

"Gobe zanje wajen Dr. Florence bayan makaranta."

"Kina da appointment ne?"

"Patients d'inta basa buk'atar appointment, kowa zai iya zuwa bayan ranar data maka fixing."

"Toh kar ki dad'e tunda zamu fita."

A baya duk ranar da tace zata je wajen Dr. Gilbert Mami ko Daddy zasu tambaye ta akan me zata je, amma tunda ta koma wajen Dr. Florence ta kula sun daina hakan, sun yarda cewa a yanzu ciwonta keb'antaccen abu ne da ba kowa ya kamata ta dinga zancen dashi ba.

Itama kuma sai ta godewa Allah da bata tambaya ba, don bata san ta yadda zata yi bayanin cewa zata je tambayar rainin hankalin Adam ne ba.

A wannan daren data zo kwanciya, tunanin hoton fuskar Al'ameen ya cika kanta, ba wai don bata tab'a ganin mai kyau irinsa ba, A'ah.. sai don bata taba ganin mai kyawu da tsarin halittar da yayi mata kwarjini irinsa ba. Ta tabbata da Mahaifinsa yake kama wanda akace balarabe ne don babu abinda ya had'a siffar Aunty Miryaamah data fi kama da turawa da tasa.

Ta jawo wani d'an k'aramin throw pillow ta rungume lokacin da shirun d'akin da duhunsa ya shaida cewa Zahra ma ta ajiye wayarta tayi bacci. Dole ne ma ta goge zancen kwarjini Al'ameen a ranta tunda dai ba abinda hakan zai k'are ta dashi kuma ta riga ta sani baza ta so koda tunaninta ya rab'i duk wani abu daya kasance daga hanyar Aunty Miryama ba, balle kuma jininta.

Ta jero addu'o'inta sannan ta rufe idanunta a hankali, amma sai hoton fuskar Al'ameen ya sake yiwa idanun nata rumfa!

Sai kawai ta d'ora filon a sama ta binne kanta cikinsa.

***

"Maganar Gaskiya ni bana tunanin mutumin nan niyyarsa ta koya miki karatu ce, in ba haka ba me yasa zaice wai kina da wata matsalar dake baki san da ita ba?"

Romilda ta fad'a sanda suke zaune a k'afar benen hanyar classes d'in dake hawa na uku a makarantar inda ba'a fiye wucewa sosai ba, suna k'arasa zana wani format na architecture da aka basu aikinsa.

"Sannan ta yaya ma za'a ce duk tsawon lokacin nan ba wanda ya tab'a fad'a miki hakan daga asibiti sai shi kawai, idan nice ke daga yanzu ba zai k'ara ganina ba."

Melissa ta fad'a kanta na kan zanenta, sai kuma ta d'ago ta tattara dogon gashinta ta tufke shi a baya, saboda yadda yake wa fuskar tata rumfa.

Fadeelah tayi ajiyar zuciya a hankali tana nata zanen, abinda suka fad'a haka ne tunaninta itama,

Please Login or Register in order to submit comment