Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai shiga sha takwas amma baya tab'a k'orafi."

Faruq dake gaba ya d'ago da kansa daga danna wayar da yake yi, ya gallara mata harara ta mudubin gefe. Daddy ya cigaba da cewa.

"..Ba zai yiwu ba, ke yarinya ce har yanzu."

Ta turo bakinta cikin b'acin rai sannan a hankali tace.

"Banda yanzu, nima daidai nake da kowa."

Fadeelah kad'ai ta san me hakan yake nufi, don ita da Mami kad'ai suka gane tana murnar mensturation d'inta na farko ne ranar da ta had'a walima ita da k'awayenta.

Makarantarsu aka fara zuwa suka sauka ita da Faruq, Zahra ta dawo gaba a lokaci d'aya, ta saita mudubin gaba tana k'ok'arin fito da gashinta ta cikin nad'in hijaab d'inta, Iman na baya hankalinta ya tafi duniyar chocolate d'in da take sha.

"Sai na ganki." Kawai Faruq yace, ya rataya jakarsa ya nufi cikin makarantar kamar ita d'in wani wajen zata daban.

Tabi bayansa ta cikin d'imbin d'aliban d'in dake ta harkokinsu da niyyar zuwa lokarta ta duba ajin da take dashi, don har yanzu time table d'inta hargitse mata yake.

Tana ta sauri ta lalubo paper daga cikin tarin litattafanta, don Allah ya sani bata son ta had'u dashi balle shi ya ganta ma, ta san tabbas zata ga wani abun da zai b'ata ranta a sanyin safiyar da bata fara saka komai akanta ba, me yasa ne ma k'addara ta had'a number lokarta kusa da tasa ne? me yasa bata nesanta shi da ita ba kamar yadda take hangensa a baya?

Ta zaro paper ta kalla, tana da English yanzu ita kad'ai, anjima History tare da Melissa, sai commerce gabad'aya da k'awayenta biyun Romilda da Melissa... Arrgh! tana da Maths ma yau, Babban abin tsoronta kuma Babban abinda bata ganewa a makarantar, kwakwalwarta toshewa take da an fara taji kanta ya fara ciwo, kamar lokacin da mutum ke son tuna wani abu da bai tab'a saninsa ba.

Duk da hayaniyar cikin hall d'in na sauran students dake wucewa sai da taji sanda ya tsaya ta gefenta da kuma sanda k'amshin turarensa ya ziyarci hancinta... Ranta ya b'aci a lokaci d'aya, zata iya rantsewa ba ranar da zata zo wajen lokar nan bata had'u dashi ba, dalilin da yasa ta tsani ajiye wani abu nata mai amfani a ciki kenan.

Da k'arfi, ta banka k'ofar locker sannan ta juya da niyyar barin wajen, sai dai wasu tarin fastocin dake fad'owa daga cikin locker tasa suka sata tsayawa, kuma idonta ya kai kan rubutun jikinsu kafin tayi tunanin tsallakewa.

*Back up you terrorists!...Muslim sucks!"*

(B'atanci game da Musulmai.)

●﹏●

FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.

BAYAN NA MUTU..!

*©AYHA SHAFI'EE*

*02*

*(☆_☆)*

Idan mutum ya duba ma'anar tsana a shafin yanar gizo, za'a fassara maka kalmar ne da lokacin da tsananin k'iyaiyar wani abu ko wani ya d'arsu a zuciyarka saboda wasu dalilai na rayuwa dake sa mutum cikin fushi, fushin da zai ta yad'uwa yana fito da tsiron wasu laifukan da zasu dad'a habb'aka tsanar.

Kuma in dai har tsanar tayi masauki, to komai kankantar abu zai dinga k'ara ta ne, balle kuma babban abu, babban abu irin wanda Fadeelah ta gani a wajen mutumin da ta tsana yanzu a rayuwarta. Shima kuma ya tsani ire-irenta saboda suna saka hijaab, suna sallah, suna azumi, sannan basa cin fiye da rabi na kalar abincinsu... ko kuma a saukak'e kawai ace saboda su d'in Musulmai ne!

A lokacin da ta k'addara ta kawo ta k'asar America ana dab! da fara zab'e na sauyin Shugaban k'asa ne, kuma takurar da akewa musulmai ko kad'an bata kai haka ba sai a yanzu da canji yazo na sabon d'an takarar daya lashe zab'en, canjin daya tab'a kowa, kuma ya tab'a rayuwar duk wani musulmi dake cikin k'asar America.

Saboda tun kafin hawansa ya fito kiri-kiri ya nuna kiyaiyarsa ga Musulmai ya kuma dad'a k'arfafawa wanda suke da akida irin tasa hakan, sai ya zama musulmai suna fuskantar tozarci a fili kuma har ta kai ma ana shirin hana wasu musulman dake waje shigowa k'asar.

Kuma suma kamar kowanne musulmi a k'asar suna fuskantar wannan k'alubalen don a kwanakin baya har wasu sun daki Zahra a cikin motar makaranta saboda ta saka baki wajen hirar siyasar sabon shugaban k'asar da akeyi. Gashi kuma a satin daya wuce an kori Mami Saffiyya daga wajen aiki saboda tace ba zata bi ka'idar sabuwar shigar da suka sanya na cire hijaab ba.

Allah ya sani komai nata YA MUTU a baya, amma zuciyarta na rik'e da son addininta, tana mutuk'ar samun nutsuwa a cikinsa, don ta tabbata ba zuwanta gurin likita ko magani ne ya tallafi kwalwalwarta a baya ba, k'arfin imanin da take dashi game da addininta ne.

Sai gashi a yanzu da cikin makarantar nan ya zama waje d'aya da take iya sakewa bayan cikin gidansu shima za'a takura ta a cikinta. Mutumin da a yanzu ta tsana fiye da kowa a makarantar yana cikin kungiyar dake shirin datse walwalarta. Don me yasa kuwa baza ta damu ba?

"Toh don me yasa zaki damun?"

Romilda ta fad'a daga gefenta tana tauna sandwich d'inta cikin baki, Suna zaune a cafteria ne bayan fitowarsu daga class na uku a ranar, commerce.

"Naga dai bamu kad'ai ne musulmai a makarantar nan ba, saboda haka bamu kad'ai zasu takurawa ba."

Ta fad'a cikin turancinta mai cakud'e da yaren Spanish. Fadeelah ta juyo ta kalle ta.

"Shine matsalar, don kawai bamu kadai za'a takurawa ba sai kice kar mu damu? bamu san me suka shirya ba? ba mu san k'ank'anta ko yawansa ba da zamu ce ba zai shafe mu sosai ba."

Melissa dake tsallaken teburin da suke zaune ta gyara zaman dogon gashinta zuwa bayan kunne sannan tace.

"Deelah, kome suke shiryawa ni na san hukumar makaranta bata san da zaman k'ungiyarsu ba, don haka za'a taka musu birki da zarar sun fara."

Turancinta a kwance yake fita ba irin na Fadeela dake a warware kona Romilda mai cakud'e da yarenta ba, don ita haifaffiyar baturiyar America ce kuma ba musulma ba, amma duk da haka k'awancensu na tafiya daidai kasancewarta mai saukin kai da kuma fahimta.

Fadeelah ta buga kanta cikin hannayenta tare da yin ajiyar zuciya.

"Kamata yayi kawai ace na yaga fastocin nan a lokacin da na gansu."

Romilda ta girgiza kanta.

"A'ah Deelah, a dai yanzu gwara da baki fara ba, gwara da baki yi abinda zai sa ya fara lura dake ba balle har mu shiga cikin lists d'insu don ko kin yaga zasu sake yin wasu ne."

Ta sake yin ajiyar zuciyar tana d'ago da kanta. Ta san cewa shi bai santa ba, baima tab'a lura da ita ba a cikin d'imbin matan da suke cikin makarantar, Amma ita zuciyarta ta dad'e tana bidirin tsanarsa, tsana irin wadda d'an adam ke yiwa annoba!

"Kin je kiran Mr. Hawkins kuwa?" Romilda ta katse shirunta, a hankali ta girgiza kai.

"Me ya faru?" Mellisa ta tambaya.

"Faduwa nake yi a komai na Math, makina yayi k'asa da yawa. " Ta bata amsa muryarta a hankali.

"I'm sorry, ya kamata ki same shi gaskiya, ki gaya masa irin ciwon kwakwalwarki na san zai baki wani aikin ne da zai d'ago ki."

"Zanje." Ta amsa.

"Insha Allah." Ta k'ara akai.

"Mun tab'a zancensa bai zo ba kuwa..."

Muryar Romilda tasa ta wulk'ita da idonta gefe kuma a lokaci d'aya hoton fuskarsa ta shigo cikin ganinta.

Adam Steve, Saurayin da yafi kowanne tashe da d'aukaka a makarantar saboda dalilai biyu, fasahar kwakwalwarsa da kuma tsananin kyawunsa wanda ya had'e cikin kammani irin na Africa da kuma mutanen k'asar Turkey, tsananin kyawun da ya jawo masa girman kai da kuma tarin d'abi'u na d'agawa wanda baya hana d'aukacin matan makarantar suji kamar su bauta masa don kawai ya kula su.

Yana tafe rik'e da lemo cikin wani taku na tak'ama da kuma Izza, Dylan babban abokinsa na d'auke da tray din abinci a gefensa yana masa magana, amma shi in banda lemon ba komai a hannunsa don ba wanda zai iya bada shaidar ranar da aka ga yaci wani abu a makarantar, kafin a ganshi a cafteria d'in ma aiki ne.

Tana iya ganin yadda yawanci fuskokin mata ke binsa da kallo kamar yaune rana ta farko da ya shigo makarantar, da kuma yadda wasu ke cije lebbensu kamar suna hana kansu ihu ne saboda mahaukaciyar kwakwalwarsu na gaya musu cewa shine k'arshen burinsu.

Sai dai duk wannan hank'oron nasu yana bajewa ne a iska, Adam bai tab'a kula d'aya daga cikinsu ba kamar yadda aka san duk wani saurayi mai irin qualities d'insa nayi, mata da yawa sun sha yarfa kansu wajen masa shishshigi don baya tab'a damuwa da kowa sai tarin abokansa da suke harkar karatu tare, mutane sunce yana da wani bak'in tarihi ne game da mata, amma abinda fadeelah ta sani shine bak'in tarihinsa bai hana shi yad'a tozarci ga addininta ba.

"Inaga ina da abinyi fiye da zama anan." Ta fad'a tana d'aukan jaka da wayarta ta bar teburin.

"Baki ci abincin ba..."

"Bana jin yunwa, sai na ganku a aji."

Daga cikin cafteria a mik'e office d'in Malamin Maths d'insu ta nufa, Mr. Hawkins.

"Ina ganin ya kamata ki samu wanda zai dinga koya miki wani karatun daban a gida, makin ki ya b'aci da yawa, in zaki cigaba a haka bana tunanin zaki iya kaiwa gejin da ake nema wajen cigaba zuwa wani ajin."

Zuciyarta ta buga a cikin ramin k'irjinta, ta yaya zata maimata ajin da take tsawon shekara guda, ta yaya ma zata kalli Daddy tace masa rashin k'ok'arinta ya kai har ta maimaita aji?

"Zanyi iya k'okarina sir, zan dage in dinga ganewa, watakila in ka bani wani aikin naje nayi zan samu k'arin makin."

"Yaudarar kai kenan, ina fada miki ne ya kamata ki nemi malamin da zai dinga miki wani karatun a gida, sai ki iya samun maki mai kyau nan gaba amma a haka, ba zaki iya kaiwa inda ake so ba."

Ta d'anyi shiru tana murza 'yan yatsunta, ita ta san Daddy ba zai iya d'auko mata wani malami ba a yanzu. Kuma ta san in har ta amsawa Mr. Hawkins to ta yaudari kanta ne ta guntulewa kanta samun wata hanyar da zai iya kawowa ta taimake ta, saboda haka tace.

"Kayi hakuri sir, Babana ba zai iya d'auko min wani malami a yanzu ba."

"Saboda me?"

Yayi tambayar da zuciyarta ta san zata biyo baya, sai dai har ta bud'e baki zata yi magana k'ofar office d'in ta bud'e bayan bugu d'aya kawai da akayi.

"Ance kana kirana... sir?"

A cikin sakan d'aya kawai tunaninta ya tsaya cak!

Don a cikin sakan d'ayan kawai wannan muryar ta shiga kunnenta, muryar wanda ta tsani had'uwa dashi, wanda zuciyarta ke gudunsa kamar irin gudun da bawa ke yiwa Shaid'an. Me ya kawo shi nan kuma bayan ta yiwa kanta katanga dashi daga cafteria? Sai kawai ta d'auki jakarta tace da mr. Hawkins ta gode sannan tayi hanyar k'ofa.

Ta rik'e numfashinta sanda tazo gifta shi, ko kad'an bata k'aunar ta shak'i kamshin turarensa wanda ta haddace shi a gefen lokarta.

Sai dai abinda bata sani ba shine alkalami ya riga ya bushe akan k'addararsu, Office d'in Mr. Hawkins shi ya zama jigon mafarin k'addarar dake jiransu a gaba!

****

"Bayan duka kuma abin ya kai har ga zagi? Daddy ya kamata muje makarantar nan, ba zan zauna kowa ya dinga takura musu don kawai wani dan isk** shugaban k'asar su ya basu damar...

Mami Saffiyya ta fad'a cikin fad'a tana ajiye bowl din miyar dankali akan dining table inda suka taru gabad'ayansu suke cin abincin dare.

"Kar ki k'arasa, yaran nan suna jinki." Daddy ya fad'a yana tauna abincinsa.

Zahra wadda ke zaune a gefensa, ita ta gama k'orafi akan wani d'an ajinsu dake zaginta, amma kamar ba akanta ake maganar ba, hankalinta ya tafi wajen raba abincinta da nikak'ken naman da aka had'a.

"Da gaske nake, bana tunanin shirunmu zai sa rashin mutuncin nasu ya ragu. " Ta sake fad'a sanda taja kujerarta ta kusa da Fadeelah ta zauna.

"Kana jin me nake fad'a kuwa?"

"Kowacce kalma, amma ba inda za kije, dole ne mu k'ara hakuri don makarantar yara ce k'anana, ba zai yiwu muje fad'a dasu ba, in har abun ya k'ara yawa ne sai ayi reporting."

Ba haka taso ba amma ba yadda zata yi, sai ta miko masa plate d'in salad tana fadin.

"Amma dai ko kiran malaminsu ne ya kamata ayi, don su san ba tsoronsu muke ji ba."

"Karki damu, abincin nan yayi dadi da yawa... Kin iya girki.!"

Sai murmushin dad'i ya maye gurbin fushinta.

Fadeelah na zaune a gefenta tana tauna abincinta a hankali, tunani take a cikin kanta in har yara k'anana zasu fara nuna kiyaiyarsu ga yara irinsu musulmai, me yasa take ganin hakan ba zai faru a makarantarsu ba? zuciyarta ta cika da d'aci sanda fuskar Adam ta shigo cikin tunaninta, wani mutum guda d'aya da ta tsana fiye da kowa, bata sani ba ko a rayuwarta ta baya akwai wanda ta tsana irin hakan, amma BAYAN TA MUTU, shine halitta na farko da taji bata sonsa, kuma bata sonsa har cikin zuciyarta.

"Do you know what the boy even said...?" Muryar Iman ta fad'a cikin kunnenta.

"Iman, Hausa!" Mami Saffiya ta katse ta.

"Cewa mata fa yayi 'Black' ba wani abu ba."

Abin ya bawa Fadeelah dariya, don daga yadda Zahra ta gama fadar yaron na zaginta wani zaice babbar magana ce.

"Kwalliyar me kika yi da daddaren nan?" Mami wadda sai yanzu ta lura da fuskar Zahra ta fad'a.

"Ba na hana ki saka wad'annan abubuwan a fuskarki ba..?"

Fadeelah ta kalli fuskar Zahran, bata san wane fad'a Mami zata yi ba da taga yadda ta yiwa gashinta d'azu Allah yaso taji shawararta ta canja shi.

"Mami dan Allah kwalliya fa ba haramun bace, so nake kawai inyi kyau."

"Kina da kyanki ba sai kinyi kwalliya ba Mamana, kawai kin matsu kiyi saurin girma ne."

Daddy ya fad'a daidai sanda Faruq ya sauko daga stairs.

"Yaya!" Iman ta kira sunansa da murnarta tana kallonsa, ya k'araso ya gaida iyayensa a hankali sannan ya zauna kusa da Iman.

"How's my sweetheart" Ya fad'a yana hargitsa gashinta. Mami ta miko masa plate d'in shinkafa ya gyad'a kansa alamun godiya. Daddy ya kalli Fadeelah.

"Dr. Gilbert ya kirani yace kinje wajensa kwana biyu da suka wuce, wai zancen kina fama da mafarkai da yawa."

"Eh Daddy." Fadeelah ta amsa a hankali.

"Amma ba wani abu bane yayi sauki yanzu." Ta k'ara akai amma duk da haka tana iya jin idanunsa na kallonta.

"Da gaske nake Daddy I'm fine."

"Amma baki tab'a zuwa wajensa ke kad'ai ba, kin tabbata ba wani abu?" Mami ta tambaya cikin tausayawa.

"Sannan bata fad'awa kowa zata je ba." Zahra tace tana juya idanunta.

Mami ta gallara mata harara wadda kowa ya san wata hanyar tace ta cewa 'Dake ake magana?'

"Wallahi ba komai naji sauki." Fadeelah ta fad'a a hankali tana cusa wata lomar cikin bakinta.

Sai dai ita kanta ta san k'arya takewa kanta. Ciwonta yayi sauki a baya amma daga lokacin da ta fara irin wannan mafarkan, kwakwalwarta da duk wani abu mai hankali a jikinta na gaya mata cewa wani Babban al'amari na shirin faruwa da ita!

***

BAYAN KWANAKI BIYU.

Fastocin nan suka shiga yawo a makarantarsu Fadeelah, kuma hakan ya karb'u a wajen d'aliban makarantar sosai don k'ungiyar su Adam ta cigaba da printing wasu ana mannawa a koina na cikin makarantar, koina kuma ya had'a harda cikin toilets na mata da maza, ya zamana babu inda wani musulmi zai juya a makarantar bai ga kalmar b'atanci ga musulunci ba, ko kuma a dinga kiransu da sigar tsokana ana dariya.

Wasu sun damu wasu kuma basu d'auki abin da zafi ba, a cewarsu ai babu hannun hukumar makaranta don haka abin ba zai d'ore ba.

Saboda a lokacin ma malamai sun fara tsawatarwa wad'anda ke hassasa abun. Fadeelah tafi kowa takura ba don komai ba sai don ciwon kwakwalwarta, kwakwalwarta da bata iya jure duk wani abu da zai takurata komai k'ank'antarsa kuwa. Dalilin da yasa har a lokacin ta cigaba da fad'uwa ayyukan lissafi kenan, wanda a yanzu ta riga ta gayawa Mr. Hawkins cewa baza ta iya samun extra malami ba saboda Daddy yana iya kokarinsa wajen managing rayuwarsu ne, don har a lokacin Mami Saffiya bata samu aiki ba.

Tsanar da take wa Adam ta k'ara yawa a ranta, saboda ta yarda cewa tunda ta fad'o cikin sabuwar rayuwarta, wannan shine hargitsi mafi muni daya tab'a faruwa da ita, Ashe ko kusa ba hakan bane, mafi hargitsin rayuwarta ya fara ne a wata ranar laraba da daddare.

A ranar sun dawo daga wajen wanki tana jera kayansu cikin wardrobe ita da Iman dake taya ta ninkewa, Su Mami gabad'aya suna falo.

"Jiya na karanta wani labari a tablet d'in Zahra." Iman ta fad'a daga kan gado inda take ninkin, ita kuma tana zarya tsakanin gadon tana d'iban kayan.

"Labarin 'yan Nigeria ne, akan wata yarinya da bata jin magana sosai, tayi ta rigima da mutane da kuma 'yan gidansu, sunanta wai 'BINTU'"

A lokaci d'aya Fadeelah ta tsaya tsakiyar d'akin, bata ce komai ba kuma bata taya Iman dariyar da take yi ba, tarin mafarkan da take yi masu d'auke da sunan Bintu suka haska a cikin kanta lokaci guda, Tunaninta ya hargitse a take ta shiga jin alamun muryoyin dake binta a mafarkin suna kiranta da sunan Bintu.

A take kuma wani b'arin na kwakwalwarta ya shiga bugawa da sauri, sannan fuskoki suka shiga haskawa cikin kanta kuma suna d'aukewa a lokaci d'aya.

"Na san suna Bintu." Ta fad'a a hankali.

"A ina?" Iman ta tambaya.

"A cikin mafarkina."

Ta amsa tana juyowa a hankali rik'e da kayan data d'iba.

"Ni ban tab'a sanin wata Bintu ba, kuma na san dai duk wanda kika sani mun san shi."

Bata amsa ba saboda wani irin azababben ciwo da kanta ya shiga sara mata.

"Me ya faru?" Iman ta tambaya. "Me ya same ki?"

Bata amsa ba, don baza ta iya amsawar ba, ciwon kwakwalwarta ne ya tashi kamar yadda yake yi a d'aid'aikun lokuta, hankalinta ya gushe ya zamana babu maraba tsakaninta da mahaukaci.

Zuciyarta na bugawa ta fara bugawa da k'arfi kamar zata faso ta fito daga kirjin nata sannan kanta ya cigaba da sarawa kamar ana buga mata guduma, yayi nauyi, ya kuma yi zafi, taji babu abinda take bukata kamar wani yasa wuka ya sare mata shi.

Hankalinta yayi nisa da tunaninta, kamar yadda yake faruwa a irin hakan, saboda haka b'arin zuciyarta mara hankalin ya bata shawarar tayi gudu kawai ko zata sami sauki, ba tare da wani tunanin ba kuwa ta matsa wajen windon d'akin, ta bud'e shi sannan ta dira waje, tabi ta bayan gidan ta tsallake 'yar k'aramar katangar data zagaye gidan sannan ta shiga gudu kan titin unguwar, gudu take da dukkan zuciyarta amma babu abinda yayi sauki game da ciwon kan.

Taji tana son tayi ihu, tayi gudu har sai numfashinta ya k'are, ta dinga bin iskar tana wuce mutanen dake wucewa ta kan titin, motoci, gine-gine, ta fita daga unguwarsu ta fad'a wata, ta iso cikin wani park ta mik'e cikinsa, duhun bishiyun ya dinga gizo a idanunta.

Bata san ina zata ba, fatanta kawai yawan gudun ya tsayar da azabar dake faruwa a kanta.

****

Adam yana zuwa cikin park d'inne a duk lokacin da kwakwalwarsa ta hargitse, ciwonsa ya tashi. Yana zuwa ne don samun nutsuwar da zai saita tunaninsa ya koma, walau da rana ko da daddare duk sanda ciwon nasa ya tashi.

Sai dai wannan karon shigowarsa kenan, idanunsa suka hango masa abinda ya sashi tsantsar mamaki, bai san kammaninta sosai ba amma ya tabbata itace, ita d'in da ya gani a office d'in Mr. Hawkins kwanakin baya.

Sai dai shigarta ta yanzu da wancan lokacin ta banbanta, a baya jikinta a rufe yake sannan fuskarta lullub'e take da mayafin dake nuna shaidar addininta, a yanzu k'aramar riga ce a jikinta sannan gashinta a kwance yana tashi cikin iskar!

Bai santa ba, amma tabbas ya san a lokacin wani abu ba daidai yake tare da ita ba, kuma tana buk'atar taimako, daga yadda take lulawa ma cikin duhun wajen daya tabbata bata san ina ne ba. Sai kawai ya ajiye jakar hannunsa yabi bayanta!

●﹏●

_Wane irin ciwon kwakwalwa Fadeelah take dashi?_

_Wane irin ciwo ne da Adam?_

_Wace irin k'addara ce ke shirin had'asu?_


BAYAN NA MUTU!

(☆_☆)

03

K'arar jiniyar motar Amblunce ita ta wuce gudun da yake yi zuwa cikin duhun bishiyun da yarinyar ta shiga, kuma kafin ya k'arasa motar ta tsaya sannan ya hangi tarin mutane sun fito daga cikinta, kowannensu yayi cikin bishiyun ba tare da sun damu su rufe k'ofofin motar ba.

Sai yaja birki ya tsaya daga inda yake, tunda taimakon da yafi nasa ya riga shi isa gareta. Cikin abinda baifi minti d'aya ba sai gasu sun dawo d'auke da ita a kwance jikin kafad'ar d'aya daga cikin mazan biyu, yayin da d'aya ke rik'e da waya yana magana, daga inda yake tsaye yana iya hango tashin hankali k'arara akan fuskarsa.

Sauran mutanen suka shiga k'okarin fito da gadon dake bayan motar Amblunce d'in don a d'ora ta akai. Sai a lokacin ya lura da kayan jikinta sosai, tana kwance a kafad'ar mutumin sanye da 'yar k'aramar riga mai hannun vest, gashinta ya kwanta kan kafad'unta. Haka kurum sai yaji ba dad'i, yadda ya ganta a makaranta ta rufe jikinta ya san a hankalinta baza ta so wani ya ganta a hakan ba.

Yana kallo suka rufe motar sannan suka yi hanyar fita cikin sauri har a lokacin mutumin nan dake zaune a gaban motar nata waya cikin rud'ewa, idonsa yabi fitilin motar har suka b'acewa ganinsa.

A zuciyarsa, yayi fatan ta samu sauki.

***

Muryoyin suna fita a hankali ne a kusa da ita sosai, kamar kuma sun dad'e suna maganar amma sai a lokacin hankalinta ya fahimci me suke cewa.

"Ban san ya akayi na kasa fahimtar taje retrival stage ba, yanayin mu'amalarta da komai yana nuna har yanzu tana kokarin fahimtar kewayenta ne..."

Muryar farko ta fad'a, mai zurfi da kuma nauyi. Namiji ne ta tabbata.

" ...abin da mamaki ace har tayi kwarin da zata fara re-accessing past d'inta." a lokacin taji kamar zata iya tuna sunan mai muryar amma d'ayar data shigo ta katse ta.

"It's a good sign, hakan ya nuna kwakwalwarta na da k'arfin da zata iya warkewa ne a d'an kankanin lokaci."

Mace ce wannan mai siririn sauti kamar an fik'e shi.

"Ba kowa ne kuma ke experiencing creative reimagination a farkon mataki irin haka ba, dole ne ta fita daga haiyacinta."
Namijin ya sake fad'a.

"Zata samu sauki na tabbata, tana da karfin hali.. tayi kokarin kwantar da ciwonta a baya, har ta iya shiga cikin mutane, so wannan ma zata k'ok'arta na sani."

Akwai wani k'arshe a cikin muryarta sanda ta fad'i hakan, (Fata! Hope.) Zuciyarta ta bashi suna cikin harshen turancin da suke magana.

K'arar motsin injinan dake zagaye da ita suka shiga kunnenta kafin Namijin ya sake magana.

"Zuwa yaushe zata iya farkawa?" Muryarsa ta tambaya cikin damuwa.

"Duk lokacin da jikinta ya shirya, ta shiga cikin halin da ita kad'ai zata iya fassara shi, jikinta yana buk'atar ya karb'i komai tukunna kafin ta iya fahimtar wasu abubuwan."

Shiru ya biyo baya daga nan, don haka a cikin wannan shirun Fadeelah ta bud'e zuciyarta zuwa hasashen inda take. Asibiti ne ta tabbata kuma muryar farko ta Namijin nan tayi mata kama da Dr. Gilbert, amma mamakinta shine me yasa ta tsinci damuwa irin wadda ta daina gani a wajensa? tayi zaton matsalarta tafi k'arfinsa da har ya daina d'orawa kansa damuwa akanta.

Ta biyun kuma tabbata Dr. Florence ce, wata babbar likita da ba kowa ke iya ganinta a asibitin ba sai in har cutar mutum tayi k'arfi da yawa, kenan abinda ya faru da ita har yayi k'arfin da Dr. Florence ce zata iya dubata? Bata fahimci komai a cikin zancensu ba amma ta san dole ne bayan farkawarta tayi magana akan abinda ya same ta don haka dole ne ta shirya, ta san amsar da zata bawa dukkan tambayoyin dake jiranta, tayi ajiyar zuciya a hankali, k'arar monitor d'in dake gefe ya shaida cewa yayi registering hakan.

Tsoro ya shige ta kad'an don ta san in har zata nemo abinda Dr. Florence zata tambaya dole ne ta dawo da abinda ya faru cikin kanta, abinda ya sanya ta fita daga haiyacinta, tunaninta ya dulmiya cikin kanta, a yanzu bata iya hasaso komai sosai, abinda ya faru na shirin b'acewa daga cikin kanta, kamar yadda mutum ke hasashen mafarki bayan ya farka.

Ta sake yin ajiyar zuciya a hankali... monitor dake gefe ya sake shaida cewa ya d'auki hakan. Tunaninta ya nutsa cikin kanta, ta shiga lalube cikin duk wani tunani daya tab'a zama a kanta, wad'anda ta

Please Login or Register in order to submit comment