Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

garinsu kuma babu alamun a dangin hajiyar wani na da niyyar rik'eta, tunda ita d'in ai ba hakkinsu bace.

Wannan yawan tunani da damuwar su suka haddasa mata wani sabon ciwon, kwakwalwarta kuma ta kasa karb'ar shi ta d'ora akan na da, saboda haka sai komai ya sake shafe tunaninta a karo na biyu, ta manta komai ta manta kowa... ba hajiyar ba, ba 'yanuwanta ba, ba Ladin da kullum suke tare ba balle kuma d'an Hajiyar Daddy.

Saboda haka sanda Daddyn ya tashi komawa tare da ita bisa umarnin mahaifinsa, da kyar ta yarda ta bishi can Abuja inda akayi fafutukar sama mata visa sannan suka d'unguma har da matarsa wadda ta karb'eta hannun biyu da kuma 'ya'yansu.

Shekara guda a bak'uwar duniya tare kuma da bak'in mutane kafin ta iya sakin jikinta ta karb'i rayuwar da k'addara ta bata, sai dai har a lokacin bata iya tuna Hajiyar Daddy sosai balle kuma rayuwarta ta baya, ta maida hankalinta kawai ga rayuwa cikin su Mami ta kuma saba dasu, a haka har Daddy ya samo mata malamin lesson a gida, bayan watanni shida tayi jarabawar makarantarsu Faruq kuma ta shiga, makarantar da ta hadu da k'awayenta biyu da kuma Adam, mutum guda d'aya daya kasa barin zuciyarta tsawon wannan lokacin.

Daga nan kuma wata k'addarar ta kawo Al'ameen cikin gwagwarmayar rayuwa da kuma ciwonta, zuciyarta ta bashi dama har suka yi sabon da ko a rayuwarta ta baya bata yi da wani namiji ba. K'addara ta raba su kuma wata k'addarar ta dawo dashi har a yanzu da aure ke shirin shiga tsakaninsu!

Ta tuna komai kuma ta tuna kowa, yanzu abinda ya rage shine ta tashi ta fuskanci k'addarar da ta gujewa tun a farkon lokaci, k'addarar data haddasa faruwar d'inbin abubuwa a rayuwarta, don a yanzu ta banbanta da wannan 'yar k'aramar yarinyar data baro Babban gida cike da tsoron mutanen cikinsa, Tayi wayo kuma duniya ta koya mata cewar rauni baya cikin hanyar nasara.

Dole ne ta tashi don ta fuskanci wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya, idan har sun rufe idonsu daga kawaicin DANGANTAKAR dake tsakaninsu, to itama zata yakice cewa sune wannan DANGIN da tsawon shekaru take masifar son tuna su da komawa cikinsu, ta jawo sanin cewa sune dangin da suka yi sanadiyyar hargitsewar rayuwarta, sune sanadin ciwon data sha wahalarsa kuma sune wad'anda har Innarta ta koma ga ubangiji da bak'in cikinsu a ranta!

Daga yanzu ta tashi daga wannan Fadeelan mai sauk'in kai da rauni, ta koma Bintun ta ta asali, mai dakakkiyar zuciyar da har ta iya barin gida a k'ananun shekaru.

Habiba! Ina Habiba take ne?

"Ina ga kamar ta farka, idanunta na shirin bud'ewa."

Muryar wani akanta data tabbatar likita ne ya fad'a.

Sai tayi murmushi kad'an sannan ta bud'e idanun nata bakid'aya. Ba zata k'ara asarar lokaci ba wajen komawa IKARA!

***

Adam ya bud'e k'ofar office d'insa a hankali sannan ya zare muk'ullin ya shiga ciki. A kwanaki biyu kawai da bai zo aiki ba har kan table d'inshi yayi kura don bai bada spare key wanda za'a dinga shiga ana gyara masa ba, ya yarda cewa office musamman nasa, waje ne dake buk'atar sirri.

Ya ajiye jakar daya shigo da ita sannan yayi amfanin da wayar cikin office din ya kira can reception kan a turo masa mai shara.

Ya matsa ya karkad'e wata kujera dake can jikin k'aton windon office d'in sannan ya zuge labulen jikinsa haske ya shigo ciki, akwai d'an k'aramin tebur na d'ora k'afa a wajen saboda haka ya d'ora labtop d'insa akai sannan ya zauna, ya shiga bin duk bayanan da ya rubuta game da abinda su Kawu yahya suka gaya masa kwanaki biyu da suka wuce.

Ya fahimci komai kuma ya gano hanyar da zai bi komai, zaiyi amfani ne da mutane kawai har ya kai ga evidence d'in da zasu fito da komai d'in, don bayan wad'annan shekarun baya jin kai tsaye zai samu ko tsinke ne da ya danganci lamarin.

Sai dai abu d'aya da bai fahimta ba shine a yadda yaga tsari da kuma had'in kai na Babban gida me yasa zasu kasa yafewa 'yar d'anuwansu wannan laifin? Shi lauya ne ya san muhimmanci da kuma ciwon laifin kisa musamman ace na mahaifiyarsu, ya san kuma ko da d'anuwan nasu ne zasu iya k'in yafe masa suce sai an hukunta shi, amma yarinya k'arama irin haka? Shekaru ashirin da biyu? Me zai sa suk'i yafe mata? Sun kuwa san cewa kashe ta za'ayi in har komai ya tabbata?

Dole ne ma ya sake tuntunb'ar Sa'id, ya fahimci akwai wani abu dashi da Kawu Ibrahim basu gama baiyana masa ba game da Babban gida.

K'ofar Office d'in ta bud'e, wani abokin aikinsa ne ya shigo maimakon mai sharar da yake jira.

"So yau kaga damar shigowa kenan?"

Nasir ya fad'a da murmushi sanda ya k'araso ciki, shima murmushin yayi masa sannan cikin tattausar muryarsa yace.

"Wallahi Nasir, hayaniyar case d'in can ya wahalar dani, shi yasa na nemi hutun kwana biyu wanda da kyar ma aka bani."

Nasir ya nemi waje ya zauna.

"Ai dole ne a baka da kyar, mutane irinku hutunsu kad'an ne Adam, ko jiya na shiga office d'in Haro naga an kawo wani case suna requesting d'inka."

Ya girgiza kansa a hankali.

"Da kamar wuya in karb'a, don ina da wani case din yanzu."

"Anan ne?" Nasir ya tambaya.

Ya sake girgiza kansa.

"Na waje ne, ko kuma ince na gida ne... Daga Family na ne."

"Allah ya taimaka, thou na san ma zaka yi nailing d'insa."

Kafin ya amsa, had'addiyar wayarsa daya nemo a daren jiya ta shiga vibrating a gefen labtop d'insa. Kawu Ibrahim ne saboda haka ya gyara zamansa kad'an sannan ya amsa.

"Kunyi magana dasu Yahyan?"

Kawu Ibrahim d'in ya tambaya bayan 'yar gajeriyar gaisuwar daya bada dama suka yi.

"Eh, Baba sunyi min bayanin komai, munje asibitin ma har sau biyu amma bamu ga yarinyar ba, ance ta shiga cikin d'an k'aramin coma ne, sai dai su marik'an nata muka gani."

"Yawwa, tunda ka fahimci komai yanzu so nake in tambaye ka zaka iya yi min wata alfarma?"

Bai san kalmar alfarmar ba, amma fahimci ma'anarta, ya fahimci yana rok'onsa yayi masa wani abu ne don haka kai tsaye yace.

"Insha Allah Baba, ka fad'i ko meye."

Baya fatan Allah ya kawo ranar da zaiyi koda musu dashi ne kan wani abun balle kuma bijirewa.

"Adamu so nake yi ka juya akan case d'in yarinyar nan, maimakon lauyan masu shigar da k'ara, so nake ka koma lauyan da zai kare ta!"

Adam ya had'iye wani abu da bai san menene ba cikin mak'ogwaronsa, a yanzu ya k'ara tabbatarwa kansa akwai wani abu game da rayuwar yarinyar nan!

***

Al'ameen ya shak'i iska a hankali lokacin da yake kallon waje ta tagar motar da Kamaal ke tuk'awa, zuciyarsa tarawa take da kuma d'ebewa, ya san baiyi amfani da tunaninsa ba ko kad'an wajen tursasa mahaifinsa su b'oyewa wa Maminsa zancen aurensa da Fadeelah.

Gashi a yanzu komai ya cakud'e lokaci na shirin k'ure masa, don ranar da Mami ta sanya na aurensa da Hamida a can na k'ara gabatowa alhali bai cimma komai anan ba. Shi yasa ya kasa d'aukan wayar da tayi ta masa jiya, me zai ce mata? Zaman makokin ne ba'a gama ba alhali mahaifinsa ya koma tuntuni?

Allah kad'ai ya san damuwar da take ciki yanzu na rashin ji daga gareshi, ya maida kansa ya jingina a saman kujerar yana kallon saman motar.

"Wai me kake tunani ne?"

Kamaal ya tambaye shi cikin harshen turanci.

"Abubuwa da yawa." Ya amsa a tak'aice.

"Yau zamu karb'i license d'in nan, sannan na gaya maka shari'ar nan mai sauk'i ce, zamu samu duk evidence d'inmu tunda yarinyar ta aikata ne kafin ta kai shekaru...?"

"Bata aikata ba Kamaal, ni na san Fadeelah bata yi kisan nan ba."

"Sorry, ina nufin suna zarginta da kisan ne a lokacin da shekarunta basu kai sha takwas ba, to komai zai zo mana da sauk'i. Meye sauran damuwarka?"

"Mami." Ya furta sunan tare da furzar da iska daga bakinsa.

"Ban tab'a mata k'arya ba sai yanzu, gani nake ban kyauta ba, na zalunceta, na zalunci duk k'ok'arinta akaina Kamaal."

Kamaal baice komai ba yayi shiru kawai ya cigaba da tuk'insa, don ya san baza'a rufa awa d'aya ba zai zo kuma yana gaya masa cewa zai iya bijirewa kowa akan Fadeelah.

Zuwa can wayar Kamaal d'in tayi k'ara akan dashboard, ya mik'a hannu ya d'auka sannan ya kara ta a kunne sa. Magana d'aya yayi Al'ameen ya fahimci daga can wajen da suke neman license ne, don haka ya juyo ya kalle shi sanda ya ajiye kiran.

"Meye?" Kamaal ya tambaya.

"Dan Allah kar ka raina min hankali Kamaal, just say it!"

Sai yayi murmushi kawai sannan ya juya fuskarsa ya mayar titi.

"An samu license d'in Al'ameen, daga yanzu zaka iya shiga kowacce kotu a Nigeria ka kare Fadeelah."

Maimakon yaji farinciki kamar yadda ya dad'e yana zumud'in hakan, sai yaji yawu ya wuce kwat! cikin mak'ogwaronsa. Ya juyar da kansa a hankali ya mayar kan tagar gefensa, me ya same shi ne wai yau? Meke shirin faruwa dashi.

"Al'ameen." Kamal ya kira sunansa da muryar dake nuna mamaki.

"Muyi sauri Kamal, tunda mun samu license d'in ya kamata in had'u da lawyer wad'ancan 'yanuwan nata, Daddy yace jiya ma sun shiga asibitin nama nan."

Daga haka bai k'ara cewa komai ba, kuma akayi sa'a Kamaal din ma bai sake magana ba wanda hakan yayi masa dad'i don ya fi so a barshi da hargitsin cikin kansa kawai.

Sai dai hakan bai d'ore ba, don wayarsa dake kan cinyarsa ce ta shiga k'ara tana nuna wata sabuwar number ce ta k'asar waje, bai yi tunani sau biyu ba yasa hannu ya danna button d'in amsawa.

Magana d'aya ya gane mai maganar, wani kawunsa ne d'anuwan Maminsa, ma'ana daga dangin su Daddy na can washington kenan, ya gaishe shi cikin girmamawa da kuma taraddadin abinda zai biyo baya.

"Al'ameen tun jiya Maminka nata kira baka d'auka ba. Lafiya dai koh?"

Wane zab'i yake dashi banda k'arya? Saboda haka kai tsaye yace.

"Bana kusa ne amma insha Allah zan kira ta yanzun nan."

"A'ah kar ka kira ta ma, don baza ta iya d'auka ba. Dama mahaifinka ne yake ta rashin lafiya tun jiyan aka kaishi asibiti, yau da safe kuma Allah yayi masa rasuwa, sai dai hakuri Al'ameen mu kuma bishi da Addu'a, ka nemi koda jirgin yawo ne in zai samu ka taho a yau, don gobe za'ayi jana'izarsa."

Sau d'aya kawai zuciyarsa ta buga amma ya tabbata Kamaal dake gefensa yaji k'ararta har cikin kunnuwansa!

***

Habiba ta tafi neman halaka Bintu.

Fadeelah ta shirya tunkarar k'alubalen dake jiranta a Ikara.

Adam zai koma lauyan Bintun da bai gani ba har yanzu?"

Ga license ga kuma rasuwar Mahaifinsa, wanne Al'ameen zai dauka?


BAYAN NA MUTU!

*©AYSHA SHAFI'EE*

*27*

*(☆_☆)*

Daddyna mutum ne mai sauk'in kai Fadeelah, bashi da hayaniya ko kad'an sannan bashi da matsala a komai, wad'annan halayen nasa su suka sa Mami ta samu damar juya gidanmu baki d'aya, amma yanzu girma yazo masa kuma ya dawo gida, don haka abubuwa zasu canja deelah, baki da fargabar komai insha Allah.

Ta tsamo wannan maganar a cikin kanta ne daga d'imbin lokutan da Al'ameen yayi mata maganar mahaifinsa kuma d'aidaiku da zancen ya had'o dana mahaifiyarsa, Bata tab'a ganinsa a zahiri ba amma yasha turo mata hotunansa da kuma nasu tare wanda saboda yawansu har tana ganin ma kamar ta san shi a gasken ne... Ya Allah! Bata san yaya Al'ameen yake ji a yanzu ba, ya rasa mahaifinsa, ya rasa Uba a lokacin da ya d'auki fata da yawa na cigaban rayuwarsa ya d'ora a kansa, ya rasa wani jigo na rayuwa dake d'aga darajar mutum a duniya.

Ta san irin wannan yanayin, don a yanzu da kwakwalwarta ta dawo daidai, ta san cewa a baya ta shige shi na sau d'aya ba, ba kuma sau biyu ba.

"Eh, Daddy ma ya biyo jirgin safe d'azun nan."

Muryar Mami Saffiya ta fad'a cikin wayar da take yi da wata 'yaruwarsu Daddyn dake can washington.

"Anyi jana'izar ne?" Ta sake tambaya cikin wayar.

Kafin Fadeelah ta fahimci amsar da aka bata, hannun Aunty Hadiza ya kamo nata a hankali.

"Deelah, yaya kike jin jikin naki?"

Idanunta na k'asa, don bata fiye son yawan d'ago kanta da take jin kamar bulo guda aka jingine akansa ba tace.

"Aunty da sauk'i, babu ciwon yanzu sai dai kawai nauyin da kan yake min."

"Allah ya sawwake, insha Allah shima zai daina kwanan nan... Ki ajiye duk wata damuwa a ranki kinji? An riga an samu lauyan da zai kare ki, sun yi magana da Daddyn jiya kafin tafiyarsa, watak'ila yanzu kafin a sallame ki ma ya shigo."

Ba tace komai ba, tayi shiru kawai tana k'ifta idanunta, tunda ta farka a daren jiya, ta fahimci hankalinsu Mami gabad'aya a tashe yake kuma suna cike da mutuk'ar tausayinta, basu san cewa ita kuma su take tausayi a yanzu ba, yadda ta d'ora musu tulin d'awaniyarta a baya alhali babu hakkinsu a kanta, sannan a yanzu kuma tana shirin sawa su fuskanci abinda ko a cikin danginsu bai tab'a faruwa ba sai akanta... Ita baren da ta shigo cikinsu. Ta rasa sai zuwa yaushe hargitsin rayuwarta zai barsu su huta.

Ganin bata da niyyar magana yasa Aunty Hadiza ta saki hannunta sannan ta matsa wajen Mami da ta gama wayar.

"Kunyi magana da Baba Habibu?" Ta tambayeta cikin sauti k'asa-k'asa amma duk da haka ta ji ta.

Mami ta d'auke wata guntuwar kwalla da yatsanta d'aya sannan ta amsa.

"Na kira shi d'azu yaya amma yace ba zai sami damar zuwa ba."

Maganar tasa Fadeelah ta dago da kanta da kyar ta kalle ta, saboda haka ne har take hawaye? Toh fisabilillahi meye laifin Baba Habibu anan? Bashi da wata alak'a da ita don me zai kashe ayyukansa ya bisu Zariya akan shari'arta? Ba tun yau ba tasha fahimtar ba'a kullum ne ake samun mutane masu zama da mutum zuciya d'aya irin Mami ba, saboda duba alak'ar fa... 'Yar tsintuwa daga dangin miji zata dinga nunawa kulawa haka?

"... Amma yace yayi magana da wani abokinsa an sama mana gidan da zamu zauna a can din, ya bawa Abdullahi numbersa idan munje zai karbo mukullin."

"To ai ba wani abu bane Safiyya tunda da Abdullahi ma, sannan gashi d'anuwan nata na can ya samo mata lauya insha Allah ina ganin bamu da matsala, tunda shima Daddyn ba zai fi kwana uku ba ai na san."

A duk maganar Aunty Hadiza, abu daya ne ya dauki hankalin Fadeelah, '... d'anuwan nata na can daya samo mata lauya...' Tunaninta ya k'ulle a lokaci d'aya, waye d'anuwanta a Ikara da zai sama mata lauya, dama har akwai wani sauran mai jin k'anta a Babban gida? Kafin ta samu wad'annan amsoshin Mami ta k'araso gare ta, ta zauna a kujerar gefe sannan ta rik'o hannunta d'aya kamar yadda Aunty Hadiza tayi.

"Ya kike ji yanzu?" Muryarta na nuna tsantsar kulawa.

"Da sauki Mami, babu wani ciwo."

Ta gyad'a kanta sannan tace.

"Yaya Hadiza ta tafi kiran Nurse a cire miki allurar."

Sai a sannan ta d'aga kanta taga ledar jinin da ake k'ara mata saura kad'an a ciki, kowanne lokaci daga yanzu, inya k'are nata jinin ne zai fara tafiya cikin ledar.

"Al'ameen yaso ganinki kafin ta tafi deelah, babu yadda ya iya ne amma wallahi yayi iya kokarinsa a cikin kwanaki hud'un nan, har license sai da ya samu na shiga kotu yace zai karb'i shariar taki, wallahi ya damu sosai, dalilin da yasa ya dakatar da d'aurin auren kenan, yace kowacce mace na farin ciki ranar aurenta, bai zai so ke kuma ace ba kya cikin haiyacinki ba a ranar.

"Allah ne bai nufa ba kawai Allah ne bai nufi komai kamar yadda muka tsara ba, wallahi abinda suke zargina k'arya ne Mami, ban kashe kowa ba, ban tab'a..."

"Shhhhhh." Mamin tayi saurin katse ta.

"Kar ki sake fad'a min haka Fadeelah, na san baza kiyi kisan nan ba, kuma na san baki yi ba don haka mu rufe babin nan, mu fuskanci abinda ke gabanmu shine yadda za'a tabbatar da hakan a gaban shari'a. Zaki iya tunawa a cikin 'yan uwan mahaifinki akwai wani..."

Wani wa? Zuciyarta tayi hanzarin tambaya sanda maganar Mamin ta katse, sai dai itama tana d'ago da kanta tata tambayar ta katse sakamakon bud'e k'ofar d'akin da akayi.

Taji kamar an saka adda an sara tsakiyar kanta mai nauyi a lokaci guda, don babu wani makari tayi IDO DA IDO da mutanen Ikara, mutanen da tsawon shekaru suka shafe a cikin tunani da kwakwalwarta, sai a yanzu cikin sati d'aya kawai komai ya baiyana, komai d'in dake barazanar tarwatsa rayuwarta ta biyu.

Kawu Yahya ne a farko, mutumin da a baya zuciyarta ta riga ta manna masa wani tambari da ba zai tab'a rabuwa da siffarsa ba.

"Allah ya yiwa yaya Bukar rasuwa Saratu, Babu yadda muka iya sai hak'uri, yanzu aka shiga da gawarsa Babban gida...

Wannan ranar, wannan ranar da yazo da labarin rasuwar mahaifinta tsaye daga k'ofar d'akin Inna Saratu, wata rana ce da ba zata tab'a gogewa cikin idanunta ba.

Bayan shi, Kawu Sulaiman ne ya shigo wanda shima ba baya bane tun a da wajen nunawa Innarta kiyaiyarsa. Fadeelah taji dad'in yadda Mami tayi shiru bata gaishe dasu ba don ba Mamin kad'ai ba idan har itama suna tunanin samun gaisuwarta ne to zasu dauwama inda suke ne.

"Sannunku." Kawu yahya yaga damar yanke shirun.

"Yauwa sannu." Mami ta amsa a hankali.

"Ke." Muryarsa da kauri ta biyo baya, Fadeelah ta d'ago a hankali ta sake kallonsa don ta san da ita yake.

"Kin gane mu?" Ya tambaya.

Sai ta gyad'a kanta ba tare da ta d'auke idanunta daga cikin nasa ba.

"Na gane ku Kawu Yahya Barka da zuwa."

Bai amsa ba sai ya kalli Kawu Sulaiman yace.

"Ai ni na san k'arya ne ace wai ta manta komai, kuma ita k'arya dama ai ba'a yinta kusa da gida ma balle a gidan..."

Ya dawo idonsa gare ta.

"... Bama zanyi mamaki ba da kin nuna baki sanmu ba, wadda ta tsallake gida tabi duniya meye ba zata aikata ba. Kinga nan..." Ya d'ago wata takarda a hannunsa.

"Sallamarki ce don haka ki shirya komawa tushenki a yau ki girbi abinda kika shuka, insha Allahu yau sai kwanan kotun da za'a bi mana hakkin mahaifiyar mu a cikinta."

Kai tsaye tace.

"Ai dama mun shirya Kawu, zuwanku kawai muke jira."

Watak'ila maganar ta bashi mamaki don saida ya d'an tsaya kamar kwakwalwarsa na gaya masa cewa da kunya ne fad'ar wad'annan maganganun wa yarinya k'arama kamar Bintu sa'ar 'yar cikinsa. Kafin ya sake magana sai wayar hannunsa ta shiga kara don haka yayi amfani da damar ya fita daga d'akin.

"Idan su basu gaya miki ba, to akwai 'yan sanda k'ofar koda zaki sake tunanin guduwa." Cewar Kawu sulaiman kafin shima yabi bayansa.

"Kar ki saurari zancensu dan Allah deelah, ki barsu..."

"Basu da laifi Mami, ina tunanin ko waye a matsayinsu zaiyi hakan, mahaifiyarsu fa suke zargin na kashe, Uwa wadda ta kawo su duniya..."

Sai ta kasa k'arasawa saboda kukan da taji yana shirin kunyata dauriyarta.

"Deelah kin tuna wani a 'yanuwan mahaifinki wai Kawu Ibrahim?"

Ta d'aga kanta a lokaci guda.

"Na tuna kowa ai Mami, shi wa ne a wajen Babana amma ba nahaifiyarsu d'aya ba, a baya shi kad'ai ne mai tausayina a cikinsu, shi kad'ai ne nake samun sauk'i a wajensa."

"To a yanzun ma bai canja ba Fadeela, shi ya kira Daddy yace ya sama miki lauyan da zai kare ki, wallahi baki san yadda hankalina ya kwanta da hakan ba, saboda halayyarsu har tsoro take bani.. Wace irin k'iyayya ce wannan?"

"Mami tun asali basa sonmu dama..."

"Mairo ta riga ta gaya mana komai ba sai kin maimaita ba."

A lokaci d'aya taji azabar cikin kanta ta d'auke, ta d'ago ta kalli Mamin da tsantsar mamaki.

"Mairo?" Ta furta sunan da take jinsa bak'o a wajensa.

"Kwananta uku a asibitin nan Deelah tunda aka kawo ki a waiting area take kwana, sai a jiya ne kafin farkawarki ni da yaya Hadiza muka matsa mata kan taje gida ta d'an kintsa kanta, don baki ga yadda ta fita daga haiyacinta ba daga ita har mijin dake ta zarya..."

Sai ta d'ago da wayarta tana fad'in.

"Tun jiya ma da akace kin farka zan kira ta, Yaya Hadiza tace in kyaleta ta huta don ana fad'a zata taho, amma yanzu gwara a gaya mata tunda tafiya..."

Bata k'arasa ba Fadeelah ta mik'o hannunta dake d'aure da syringe da wani irin sauri ta damk'e wayar Mamin, a lokacin jinin dake cikin ledar ya k'are, k'arfin yadda ta rik'e wayar kuma yasa nata ya koma shiga ciki.

"Kar ki kirata Mami, Dan Allah kar ki kirata, bana son ganinta... Wallahi har duniya ta k'are bana son sake ganinta.

Da tsananin mamaki Mamin ke kallon Fadeelah, ta san Mairo ta gaya musu cewa laifi tayi shi yasa su Kawu Yahyan da suka zo suka k'i kulata, to amma wane irin laifi ne da har a wannan halin ma Fadeelan da suke uwa d'aya uba d'aya zata juya mata baya?

Wai wani irin DANGI ne su Fadeelah haka?

______

3:43 PM.

Kawu Ibrahim na tsaye a harabar Babbar kotun cikin birnin Zariya yana tsumayin isowar motocin su Yahya da suka fad'a masa cewa suna dab da shigowa cikin garin. Sai dai daga lokacin da suka yi wayar zuwa yanzu yaci ace sun iso, amma bai sani ba ko Yahyan k'arya yake masa tunda zuwa yanzu ya san sun samu labari abinda yayi daga wajen Kawu D'anjuman da suke bin umarninsa.

Ya jingina da wata mota dake ajiye a harabar wajen sanda kwakwalwarsa ta shiga tariyo masa maganganun Kawu D'anjuma lokacin da ya sake tunkararsa da zancen ya taimaka a janye shari'ar.

Ban yi mamaki ba da ka k'ara samuna da wannan zancen Ibrahim, Hajiya uwa ce a wajenka amma iya baki kawai, yau da ace ita ta tsugunna ta haife ka wallahi wannan tunanin ba zai tab'a zuwa kanka ba, amma baka san ciwonta ba balle ka san na mutuwarta.

Kai kaso ka auri uwar yarinyar nan tun kafin Abubakar marigayi yazo mana da zancenta, shi yasa baka tab'a ganin aibunta balle na 'ya'yan, shi yasa a baya har kayi kokarin had'a d'anka aure da 'yarta, ba don yarinyar ta nuna halinsu na 'yan tsintuwa ta gudu ba da yanzu yaro yana nan ka had'a shi baragurbi.

Sannan banyi tunanin cewa har zance mai girma irin wannan na kisan uwa a garemu zai zo ka d'auko tsohuwar soyayyarka ka d'ora akansa ba, ko ka manta Aminar ta mutu ne Ibrahim? Idan don ita kake duk wad'annan abubuwan to yanzu bata nan, ya kamata ka bud'e idonka ka bari gaskiya tayi halinta, don gara ma ka sani, yau idan Sadiya da muke uwa d'aya ake zargi da kashe Hajiya, wallahi sai na saka an gurfanar da ita a kotu balle wannan yarinyar."

Ba zai manta kallon da Kawu Danjuman ya bishi dashi ba lokacin da ya furta.

"Na fahimci dukkan kalamanka Kawu, kuma banga laifinka ko kad'an ba don ra'ayinka ne, sai dai abinda zance shine ayi hakuri don Adamu ba zai samu damar karb'ar shari'arku ba, na riga na bashi umarnin cewa ya kare Bintu!"

Ba zai manta idanun Kawu D'anjuma a lokacin ba, ba zai manta kallon dake fitowa daga cikinsu ba, don sawa suka yi yaji kamar yasa gatari ne ya raba Babban gida b'ari biyu, ya d'auki wani b'arin daban da nasu, amma bai damu ba, don in har yayi iya k'ok'arinsa wajen kare Bintu koda kuwa babu nasara ya san cewa bai bagarar da yardar da yayansa marigayi ya bashi akan iyalansa ba, ya san kuma ko ba komai, bai bari jinin Amina ya wulak'anta a duniya ba.

Bayan k'arasowar su Yahya, a yanzu jiran Adam ne kawai ya rage masa, wanda ya bashi tabbacin cewa gobe da safe shima zai biyo jirgi ya taho tare da Sa'id, don sai ya k'arasa wani cike-cike da k'ungiyar da yake aiki ne sannan zai, Tunaninsa ya katse, sanda jerin motoci guda biyu suka shigo harabar kotun, ta ukunsu k'atuwar jeep ce ta 'yan sanda wanda ya tabbata a ciki Bintu take.

Motocin suka tsaya a gefe guda na wajen sannan mutane suka shiga fitowa daga cikinsu, ta farko wata tsohuwar golf ce dasu Yahyan ke ciki, wanda saurin fitowarsu ya shaida gajiya da kuma takurar da suka sha a cikinta, ta biyun kuma wata mulmulalliyar mota ce k'irar da Kawu Ibrahim d'in bai taba gani ba rufe ruf! Cikin gilashin dake shaida ni'imar Ac dake cikinta, mata biyu ne suka fito daga baya, sai namiji d'aya da kuma wata matashiyar budurwa daga gaba. Ba sai wani ya gaya masa ba

Please Login or Register in order to submit comment