Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa kai kenan, ina zasu je da babu ko sevice d'in waya tsawon wannan kwanakin?

"Ya iyalin taka? Ina fata dai baka sanar da ita ba ko?"

Muryar Kawu Ibrahim ta katse shi, sai ya d'ago ya kalle shi, ya san yana nufin Mami Safiyya ne, don satinta d'aya kenan da komawa Abuja bisa matsawar da 'yanuwanta suka yi, don haka bata da labarin cewa an kai Fadeelah kurkuku, shima sai da Kawu Ibrahim ya kira shi ya gaya masa ne sannan ya nemi hutun sati d'aya ya taho, da cewa Mamin Kano zaije.

Ya girgiza kansa.

"Ban sanar da ita ba, tayi zaton ma ina Kano ba nan ba."

Kafin ya amsa Daddy ya cigaba da cewa.

"Dama kawu wata magana ce ta kawo mu..."

Ya sake cigaba bayan Kawu Ibrahim d'in da sauran sun nuna sauransa.

"... Na san yanzu ba lokacin da ya dace bane, amma su wad'annan kawun nan nawa su suka bada shawarar gwara a sanar daku da wuri tunda yanzu kune da alhakin akan yarinyar nan."

Ga su Kawu Bashir da basu saba da maganar Daddy sosai ba, da kyar suke iya rarrabe kowacce kalma da yake fad'a cikin malkwalalliyar hausar sa da yaren turanci yabi ya nannad'e.

"Ba haka bane Alhaji Ahmad, damu daku duk d'aya ne a yanzu, tunda a baya ma kunyi abinda mu d'in zamu yi."

"Da wannan Alhaji, kuma mun gode da karar, amma shari'a ai ku ta tanadar."

Suka d'anyi murmushi bakid'ayansu sannan Daddy ya cigaba.

"Kawu kun san cewa lokacin da lamarin nan ya faru ana cikin shiryen-shiryen bikin Fadeelah ne ko?"

"Haka ne."

"Toh dani dasu wad'annan 'yanuwan nawa mu muka karb'i auren yarinyar daga wajen Baban yaron wanda yake daga dangin mahaifina, sannan tun bayan dawowata na sanar da kai cewa yaron bai samu damar k'arasowa nan zaria bane saboda ana tsaka da lamarin mahaifinsa ya rasu ya koma can American.."

"Haka ne, haka ne.. Ai kaima sai bayan da ka dawo daga gaisuwar sannan muka had'u."

Daddy ya sake gyara murya sannan yace.

"To gaskiyar abinda ke faruwa shine lokacin da za'a yi auren nan akwai wata 'yar rashin jituwa daga b'angaren mahaifiyar yaron, wadda ni ban san da ita ba sai bayan naje can tukunna sannan ita mahaifiyar tasa ta buk'aci da in zauna wai zuwa ranar aurensa don inyi masa walicci, ni kuma ban gane zancen ba sai na tambayi wane aure kuma bayan wanda muka baro anan Nigeria? A lokacin take gaya min cewa ai ita kwata-kwata bata san da aurensa da Fadeelah ba, ya rufe ta ne shi da mahaifinsa suka shirya komai don ita ta riga ta gama shirye-shiyen aurensa da wata acan."

Kawu Ibrahim da sauran suka shiga gyad'a kai na al'ajabin abin.

"A tak'aice dai Kawu yanzu ita mahaifiyar tasa tak'i yarda kwata-kwata da zancen aurensa da Fadeelah, tak'i yarda ma ta saurare mu, sannan ta hana yaron dawowa tace ma zata sallama shi daga gareta in har baiyi mata biyayya akan abinda take so ba."

"Mhm-mhm!" Muryar Kawu Ibrahim ta fad'a cike da tsantsar mamaki.

"Yanzu Alhaji kana nufin zancen auren ita Bintun babu shi kenan?" Kawu Bashir ya tambaya.

D'aya daga cikin 'yanuwan Daddy yace.

"Abinda muke nufi kenan Alhaji, shi yasa muka ce gwara a sanar daku tun yanzu don ku san me ake ciki."

"Haka ne gaskiya..." Kawu Ibrahim ya amsa.

"... Wannan ba zance ne da za'a barshi a ciki ba, kuma mun fahimci zancenku, wannan kamar ishara ce daga Allah akan yaron ban, uwa ba abin wasa bace da har za'a rufe ta akan babban al'amari irin wannan, watakila ishararsa ce ma tasa wannan al'amarin bai tashi ba sai a lokacin bikin... Allah ya nuna masa cewa albarkar uwa ba k'aramin abu bane.

Kuma ni banga laifin mahaifiyar tasa ba, ya sab'a mata kuma matakin da ta d'auka akansa bai yi tsauri ba, sai dai fatan Allah yasa ya fahimta kuma ya gyara kuskurensa... Bintu ba matarsa bace Allah ya riga ya k'addara, don haka sai dai muyi mata fatan samun wani mijin nagari in har ta wanku daga lamarin nan lafiya."

Magana ance jari ce! Wanda Allah ya bashi kuma ya samu baiwa mad'aukakkiya musamman in hakan ya had'u da kamala, Kawu Ibrahim ya tara dukkan wad'annan abubuwan biyu, shi yasa farat d'aya mutane ke nutsuwa dashi ko a ganin farko. Wad'annan kalaman nasa su suka burge 'yanuwan Daddy game dashi, zuciyarsu ta gaya musu lallai Fadeelah da suke wa kallon kitse a da da kuma yanzu da suka ji cewa danginta ne suka d'aure ta bata cancanci hakan ba... Don Dangin ma suna suka tara!

***

"Kina ganin da gaske ba zaki saurare shi ba?" Aunty Hassana matar Kawu Ibrahim ta tambaya Mairo data idar da sallah a gabanta.

Mairo bata d'ago da fuskarta ba balle ta kalleta, idonta na kan yatsunta tace.

"Aunty dan Allah, wallahi bana k'aunar zancen Sadiq yanzu."

Aunty Hassana ta gyara zamanta tace.

"Ai zancensa wajibi ne yanzu akanki Mairo, na san cewa da ciwo abinda kike ji amma 'ya'yanki nake jiye miki, yanzu ki duba ranar da aka zo da yarinyar nan yadda ta mak'ale a jikinki aka b'are ta da kyar, bar ganin ita yarinya ce kuma 'yarki, wallahi akwai hakki wanda ba lallai ya gogu daga kanki... Musamman na d'an da kika yaye lokacinsa bai kai ba, wallahi ko yana cin abinci Mairo hakkinsa na nan yana bibiyarki.

Sannan ni ban san zamanku da yaron nan ba, amma duk wanda zai ganki ya san baki wahala a gidansa ba, 'yanuwansa har cikin gidan nan sun zo kuma babu alamun akwai rashin jituwa tsakaninku, laifi ne ya riga yayi miki kuma kowanne d'an adam a duniyar nan baya iya shallake abinda Allah ya tsara masa, mijinki yayi nadama Mairo, ki dubi irin wahalar da yake sha a garin nan, daya tafi da ya dawo, bakya ko bari ya ganki. Suma kuma su Kawun naki ban san me suke jira ba, kowa ya zuba miki ido kina zaune da aure a ka, an kasa gaya miki cewa abinda kike yi kuskure ne..."

"Kuskure..." Mairo ta maimaita kalmar, sautin muryarta a hankali.

"... Na dad'e a cikin kuskure Aunty, rabin rayuwata kaf a cikin kuskuren take, 'ya'yan da kike magana ma duk a cikin kuskuren na same su, Sannan shi Sadiq d'in shine abu mafi kuskure daya tab'a faruwa a rayuwata."

Aunty Hassana ta mik'e daga inda take zaune ta k'araso gabanta kan sallayar ta zauna, sai a sannan Mairon ta d'ago ta kalle ta.

"Da gaske ke kika haifi yaran nan kuwa Mairo? Da gaske ke Uwa ce? Kin san yadda uwa ke jin ciwon rabuwa da 'ya'yanta kuwa? Bari in gaya miki kin san dai ba nice matar Kawunku ta farko ba ko? Amma wallahi 'ya'yan marigayiya duk da suka yi aure sai da naji ciwon rabuwa dasu, ina ga wanda ka haifa kuma? Dan Allah Mairo ki lalubo soyayyar uwa ki tausayawa 'ya'yanki, wallahi babu wanda zai hana ki komawa wajen mijinki tunda har yanzu da aurensa akanki."

Hawaye suka gangaro kan fuskar Maryam, ta share su a hankali.

"Yanzu Aunty saboda 'ya'ya sai in zalunci kaina in koma wajen mutumin daya cuce ni?"

"Rayuwar macen kenan Mairo wannan shine kamashon zama macen, kuma ba'a kanki aka fara ba, mata da yawa sun sha sadaukar da farin cikinsu akan 'ya'yansu kuma sai kiga Allah ya baka Rahma ta wani b'angaren."

"Ki duba fa Aunty, saboda shi Bintu tak'i saurarata har yanzu, tun tana yarinya na san ita ba mai rik'e abu a rai bace, shi yasa hankalina yake dad'a tashi, ina tunanin wane irin bak'in ciki taji daya manne tsanata a ranta tun daga wancan lokacin har yanzu, Ga iyayena ma Aunty, duk sun rasu da bak'in cikina a tare dasu, Gwaggo lami tace sanadiyata ma Inna ta kamu da ciwon daya haddasa mutuwarta..."

Ta girgiza kanta da sauri.

"... A zab'ina, bana jin zan tab'a iya yafewa Sadiq balle har na koma gare shi."

Aunty Hassana ta d'an juyar da kanta gefe, yadda Mairo ta kasa fahimtar ta haka itama ta kasa fahimtar irin tunaninta.

Sai dai Allah ya riga ya tsara cewa a wannan ranar dai Mairo zata fara saukowa daga ak'idarta don basu wani dad'e a haka ba suka tsinkayi sallama daga can k'ofar b'angaren.

"Wa'alaikum Salam, Maraba."

Aunty Hassana ta fad'a sanda ta mik'e zuwa k'ofar falon da suke ciki.

"A'ah, wa nake gani haka kamar Saratu? Da gaske ita d'in ce kuwa... maraba ku shigo."

Sunan na 'Saratu' ya amsa a cikin kan Maryam, ta d'ago da idonta da sauri sanda Aunty Hasanah ta bar bakin k'ofar, wata mata ta shigo, sannan wata, sannan kuma mai suna Saratun da zuciyarta ta ayyana mata.

Aunty Saratu!

Aunty Saratunsu dai matar Mahaifinta.

Sa mik'e da sauri har tana tuntub'e da hijabin jikinta, k'afafunta na rawa ta isa gare ta, zuciyarta kuma na bugawa ta kalli fuskar data zama dattijuwa akan ta Aunty Saratun da ta tafi ta bari ta bari a baya.

Ga d'imbin mamakin Mairo sai ji tayi ta jawo ta jikinta ta rungume, sab'anin yadda Bintu ta juya baya sanda ta ganta.

"Ke nazo gani Maryam, ina sauka garin nan aka shaida min kin dawo, ban ko zauna na runtsa ba na taho don in gasgata zancen nan mai kama da mafarki, Alhamdulilahi.. Alhamdulilahi.. Alhamdulilahi! Amina tayi gaskiya, wallahi daman tace min zaki dawo, tace Mairo ba zata tab'a barin mahaifarta har abada ba.. Tace ke d'in mai tsananin biyayya ce da son 'yanuwa, tace k'addarar da Allah ya tsara miki ce tazo da hakan amma wallahi ta yafe miki duniya da lahira. Ni shaida ce Maryam, daga ita har Babanki sai da suka yafe miki kafin su bar duniya!"

Mairo ta rufe idonta a hankali hawaye mai d'umi ya shiga gangarowa kumatunta har yana d'iga kan hijabin da Aunty Saratun ke sanye dashi, ji tayi kamar anja wani gingimemen dutse can gefe an sauke shi daga kanta. Ganin Aunty Saratu a wannan lokacin ya zame mata kamar wani ruwan sama da ya sauko ya wanke rabin matsalolinta a lokacin.

A wannan ranar kuma daga ita har su Kawu Ibrahim suka ji cewar Adam ne yaje har gidan da take aure a can Kaduna, ya labarta mata duk abinda ake ciki na al'amarin Bintu ya kuma nemi alfarmar da tazo ta bada shaida a zaman da za'ayi na gaba.

Kawu Ibrahim ya jinjina kansa cike da mamakin yadda akayi Adam ya iya nemo gidanta har yaje, da gaske ne abinda ya fad'a kenan, Binciken ya tafi, amma to bayan ya bar Kadunan ina ya sake tafiya har tsawon wannan lokacin bai komo ba?

****

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

36

(☆_☆)

"Mami ki saurare ni dan Allah..."

Muryar Al'ameen ta fito ta cikin wayar dake kare a kunnen Mami Safiyya, ta girgiza kanta sannan ta amsa masa cikin yaren turancin da suke magana.

"Wallahi Al'ameen ba zai yiwu ba, Daddy ya d'auki zafi sosai akan maganar nan, yace abinda muka yi babban kuskure ne, sannan ni kaina na san nayi ba daidai ba...na biye maka akan abinda ko a musulunce bai dace ba, don haka kayi hak'uri kawai, Allah yayi iyakar mu'amalarka da Deelah kenan, shi yasa ma komai ya faru kafin akai ga d'aurin Auren.

Kayi wa mahaifiyarka biyayya shi yafi, don kamar yadda yanzu kake da ita kad'ai a duniya haka itama kai kad'ai take dashi, su Aysha mata ne, duk daren dad'ewa zasu yi aure su barta, amma kai zaka zama mai kula da ita har k'arshen rayuwarta, don haka babu wanda zai so ka bijere mata ko ka rab'u da wani abu da baza ta so ba. Uwa tafi k'arfin komai, bayan biyayyar ka ga Allah tata biyayyar ce zata sa ka rabauta a duniya da kuma lahirar saboda haka dan Allah Al'ameen ka hak'ura da Fadeelah, wallahi don ka rasa ta babu abinda zai faru da kai ko ya ragu a rayuwarka.

Rahmar Allah yawa ne da ita, ba sai da Fadeelah kad'ai zaka samu farin ciki ba, na tabbata itama wannan zab'in ta Maminka alkhairi ce a wajenka, wuyar ta a zauna Al'ameen amma na san zaka fahimceta har ta zame maka matar rufin asiri, kai d'in mai kyakkyawar mu'amala ne ba wanda zai zauna da kai ya kasa fahimtarka... Dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka saki ranka ayi auren nan, Fadeelah kuma ka cigaba da taya ta da addu'a an kusa kammala shari'ar kuma muna sa rai zata fito insha Allah."

Bi da bi, kowacce kalma ke shiga kunnen Al'ameen yana jin kamar maimaici ne akan irin maganganun da kowa ke gaya masa.

... Don ka rasa ta babu abinda zai same ka.

Basu san cewa komai ya riga ya same shin ba, komai ya riga ya cakud'e masa, ya riga ya zama kamar d'an adam d'in da aka sassak'a da k'arfe, wanda abin juya shi ke hannun mutane da yawa, ya rasa duk wani emotion balle har yayi iko da kansa.

Kamar komai na rayuwarsa, wannan karon ma mahaifiyarsa tayi jagoranci da hukuncinta, tun yana yaro bata tab'a barinsa yayi abu bisa ra'ayinsa ba, hatta kaya ko abinci bai isa ya zab'a ba sai wanda ta bashi, bayan ya girma kuma bai tab'a son zama lauya ba, burinsa ya karanci harkar Computer, ya iya sarrafata ya fitar da abubuwan zamani daga cikinta amma tace tafi son ya karanci aikin lauya, abinda taso yi kenan a karatunta amma bata sami dama don haka shi yayi... Zai iya rantsuwa bai tab'a sanin ranar da ta barshi ya zab'i wani abu da yake ra'ayinsa ba sai in har abu ya zama dole ne sai shi d'in zaiyi.

Sai a yanzu rana d'aya kawai daya riga ya kai wani minzali da ko a shari'ah zai iya zab'awa kansa abu, don ya bud'i baki ya fad'i ra'ayinsa sai ta sake cewa A'ah, kuma kowa ya amince cewa ya cigaba da binta a haka? Ya lumshe idanunsa a hankali, fad'ar Allah ne cewa babu wata halitta a doron k'asa da zata zama cikakka... Tunda ya taso a rayuwarsa bai ga abinda Allah ya rage shi dashi ba sai wannan.

"Al'ameen kana jina?... Yaushe ne bikin?"

Muryar Mami ta shiga kunnensa, sai ya k'arasa rufe idanunsa gabad'aya kafin ya amsa.

"Tace farkon wani watan mai kamawa."

"Toh Allah ya kaimu, su Zahra zasu zo insha Allah, in da hali ma zan had'a su da wasu cousins d'insu."

Ba wai fatan lokacin yazo yake ba amma jin ta d'ebe kanta yasa yayi saurin tambayar.

"Mami ke fa?"

Ta girgiza kai kamar yana ganinta.

"Da wuya Al'ameen, Miryaamah ta d'auki zafi a lamarin nan, ni kaina ba zan iya kai fuskata gabanta a yanzu ba, mu bari dai zuwa wani lokaci sai inzo in ziyarce ku insha Allah."

'KU' tana nufin shi da Hamida, Hamida a matsayin matarsa... Abinda ya kasa haskowa a cikin kansa har yanzu, ya kasa rusa wannnan mafarkin daya gina a cikin kansa na irin rayuwar da zaiyi shi da Fadeelah.

A yanzu baya iya hango yaya rayuwarsa zata kasance a gaba, don ya san ba zai iya hak'urin rasa Fadeelah ba... Ya rasa ta a farko kuma ya kasa hak'urin!

****

MIMBIRI, 10:15 AM.

K'auyen Mimbiri, wani waje ne dake tsakanin babban birnin tarayya na Abuja da kuma garin Niger, k'auye ne k'arami da ko gwamnati bata san dashi ba saboda babu ko wutar lantarki balle ayi maganar ruwa, hanyar samun ruwansu ta jikin wani k'aton dutse ne dake bayan garin inda yake fitar da tsaftataccen ruwa mai sanyi wanda hakan ya sanyawa mutanen cikinsa d'orarriyar lafiya da kuma kuzari, gine-ginen cikin k'auyen na asalin k'asa ne da azara, k'asar ma ba irin wadda ake sarrafata zuwa bulo ba, don yanayin gidajen nasu babu fasali balle tsari.

Yarensu kuwa Hausa ce amma mai cakud'e da garhariyar yaruka kasancewarsu a tsakiyar garuruwa. Kamar yadda k'auyen yake k'arami, haka mutanen cikinsa basu da yawa, banda gangarawar shekaru ma da suka zo da aurarraki da kuma hayayyafa, a da baifi a k'irge su zuwa 'yan dozinnai ba.

Hanyar zuwa cikinsa bata da kyau, don da kyar aka fitar da ita 'yar siririya ta tsakanin gonaki. A shekarun baya ma babu hanyar, sai da aka yayyanka gonaki daga can hanyar babban titi sannan aka fitar da ita, 'yar k'arama mai cike da gargada wadda duk kyawun abun hawa sai yayi tangad'i akanta.

Babban abin taraddadi a k'auyen Mimbiri shine zuwan Bak'o, abu ne sabo da ba kasafai yake faruwa ba, saboda in har ka hangi wani akan hanyar shigowa k'auyen, to d'aya daga cikin 'yan d'aid'aikun 'yan uwansu ne da suke fita birni yin sayayyar kayan masarufi, ko kuma a wasu lokuta 'yan wani k'auye dake can nesa dasu su shigo cin kasuwarsu, amma shima ba koyaushe ba, duk ranar kasuwa kusan su kad'ai ke cin kasuwarsu saboda k'arancin mutanen kewayen da suka ma san da zamansu.

Sa'id ya juyar da kansa gefe yana mai k'ara sautin wak'ar da yake ji cikin earpiece d'insa, idonsa ya kai kan cajin dake kan wayar, bai ko kai kwata ba, gashi man dake cikin motar tasu ya kusa k'arewa, na cikin boot ma ragowarsa bashi da yawa.

Tun da gari ya waye fatansa shine su sami mutumin nan a yau su koma cikin gari, tsawon kwanaki hud'u kenan rabonsa da sevice d'in waya, ba don yana caji a motar ba ma da wayar ta dad'e da mutuwa. Allah ya sani bai tab'a ganin k'untataccen waje irin k'auyen na Mimbiri ba, tun daga 'yar banzar wahalar da suka sha a daji yaji ya tsani garin, don sunfi k'arfin awanni biyu cikin daji suna karo da dutsuna da kuma busassun shukoki kafin su iso cikinsa, har sai da ya fara tunanin matashin da suka d'auko daga can wani k'auye k'arya yake musu bai san garin ba.

Tun a wancan lokacin kuma ya yarda cewa da gaske ne idan Adam yasa kansa yin abu, to ba k'aramin dalili za'a samu ba da zai canja ra'ayinsa, kwata-kwata bai d'auka da gaske zasu taho har wannan k'auyen neman tsohon da ya bashi labarin ya gani a wajen Habiba ana i-gobe rasuwar Hajiya ba.

Tausayin ganin yadda yake ta fafutuka akan shari'ar ne da kuma ita Bintun da yake hangen za'a datsewa rayuwa yasa ya fad'a masa cewa yaga shigar tsohon wajenta amma ba wai don yana tunanin hakan zaiyi amfani ba, ga mamakinsa kawai sai Adam d'in ya nuna zak'uwarsa wajen k'arin yi masa tambayoyi.

Ya gaya masa iya abinda ya sani cewa ya san tsohon ne kawai ta hanyar wani abokinsa dake siyan magungunan gargajiya a hannunsa...ga k'arin mamakinsa, sai cewa yayi wai ya had'a kayansa zasu yi tafiya. Washegari suka nufi Ikara, yayi sallama dasu Kawu Ibrahim akan zaije bincike ne kuma shi zai raka shi, daga nan suka tafi wajen abokin nasa daya bashi labari, acan yake gaya musu cewa tsohon ya dad'e da barin ikara kuma asalinsa d'an wani kauye ne wai shi Mimbiri a can gaba da birnin tarayya.

Kaduna suka fara tsayawa, inda mamaki ya sake cinye shi ganin yana ta bin wani adireshi a cikin wayarsa har kofar gidan tsohuwar matar mahaifin Bintu, Saratu.

A hanya hira kala-kala ba wadda basu yi ba harda ta shari'ar da ake ciki, amma bai fad'a masa inda zasu ba ko yadda akayi ya samo gidan Saratun.

Bayan sun baro Kaduna, hanyar Abuja a mik'e suka d'auka bayan sun cika motarsu taf! da kuma wasu manyan jarkuna a boot d'in motar da man fetur, a cikin Abujan suka tsaya wani bakery suka siyo tarin kayan cimar fulawa mara saurin lalacewa da fruits da katan-katan na ruwa da lemo kamar masu barin garin.

Tunda suka wuto Abujan kuma suke faman tsayawa k'auyuka-k'auyuka tambayar K'auyen Mimbiri, sai dai tun daga k'auye na biyu da suka yi tambaya aka nuna musu wata hanya data d'auke daga kan titi zuwa cikin daji, tun farko an gaya musu dama k'auyen a ciki yake, sai dai suna isa k'auyen farko a hanyar suka zata shine, ai kuwa mutumin da suka fara tambaya ya shaida musu cewa ai ko rabi na hanyarsa basu kai ba, shi yana can ciki.

Da jagorancin kwatancensa, suka k'ara luluk'awa cikin dajin, kuma tun suna tafiya suna ganin d'aid'akun mutane har ya zama sai sunyi tafiya mai nisa kafin su sake ganin wani k'auyen, kuma daga kowanne k'auye sai ayi ta sake luluk'a su ciki da cewar K'auyen na Mimbirin na gaba, tun suna tafiya service d'in wayarsu na iya kawowa har ya d'auke bakid'aya sannan k'asan motarsu duk yabi ya karkarce saboda yadda suke taka duwatsu da busassun shukoki.

Kwana, d'aya, biyu, har uku, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su sai ko in zasu k'ara mai a motar ko kuma d'aya zai karb'i tuki. Allah ya sani sun wahala kamar a zamanin DA don wani lokacin sai su yini kafin su isa inda za ga mutane su sami ruwa su wanke jiki su canja kayan jikinsu, tun yana k'orafi har ya gaji ya daina don ko kad'an Adam bai damu da wahalar da suke sha ba ko kwazazzababbiyar hanyar da suke bi wadda duk ta karce fenti da kuma k'asan motarsu tsaf!

Sai a rana ta uku sannan suka isa wani k'auye mai suna 'Sauna' inda suka sami jagorancin wani matashi jamilu, suka d'auko shi a bayan motarsu yana musu kwatancen hanya wanda haka sai da suka shafe awanni biyu suna tafiya daga inda suka d'auko shi kafin su isa, amma zai iya rantsewa Adam ko gezau baiyi na alamun nuna gajiya ba, tuk'i kawai yake yana bin umarnin matashin nan daya bararraje yana shak'ar sanyin A.C motar.

Bayan sun iso kuma mutanen garin suka maida su tamkar wasu Dodanni, kowa yaki kula su, kowa yak'i yarda dasu har guduwa yara suke in sun gansu, ba yadda matashin nan baiyi ba don ya fahimtar da wan mahaifinsa dake k'auyen cewa ba cutar dasu zasu yi ba, amma fintinkau kowa yak'i fahimtarsu sai da kyar aka sami k'ungiyar wasu dattijai suka turo wakili daga cikinsu cewa in suna son magana dasu sai da su jira Maigarinsu ya dawo daga gaisuwar jana'iza da yaje wani k'auye.

Haka suka kwana a cikin mota babu mahalukin daya kula su, abin ya bashi mamaki mutuk'a yaga kamar sun koma wani zamani ne dake can baya da wanda suke ciki, Amma Adam bai yi mamakin ba, don cewa yayi duba da yanayin yadda rayuwarsu take, in sun kore su ma basu yi laifi ba.

Ya kalli lokaci bayan ya dawo daga wannan dogon tunanin, k'arfe goma da rabi na safiya! Adam ya tafi dubawa ko Maigarin nasu ya dawo, shi kuma ya zauna gadin motarsu, ya juya bayan motar ya d'ebo dabino da kwakwa da kuma cake, ya had'a dabino da kwakwar yana ci, wak'ar iRobot na tashi a kunnensa.

Kwankwan-kwan! Gilashin gefensa yayi k'ara bayan wani lokaci, da sauri ya zare earpiece d'in ya bud'e k'ofar motar ya fito.

"An aiko mu ne mu tafi da kai, yace ka rufe motar ka biyo mu."

D'aya daga cikin mutane biyun dake tsaye a gansa ya fad'a.

"Shi wa?" Kai tsaye ya tambaya.

"Wanda kuka zo tare dashi, yana can a fadar Maigari."

"Kuka ce baya nan."

"Ya dawo d'azu da asubar fari."

Sa'id ya d'an kallesu su duka biyun, zuciyarsa na son gasgata zancen, yana son d'ebe zargin wani abu a ransa, ganin haka yasa wanda yayi maganar nan ya zura hannunsa a aljihu ya zaro wani agogo ya mik'o masa.

"Yace mu baka wannan."

Ya mik'a hannu ya karba, agogon dake d'aure a hannun Adam ne, ya sake d'agowa ya kalli mutanen, yaga dai babu alamar rashin gaskiya a fuskokinsu amma duk da haka bai yarda dasu ba, sai ya gyad'a kai sannan ya zura agogon cikin aljuhun wandonsa, ya juya ya bud'e motar, ya kashe ta, ya rufe glasses, sannan ya zare muk'ullin, har zai fito wani tunanin ya gifta cikin kansa don haka ya bud'e drawer jikin dashboard, ya zaro wata 'yar k'aramar wuk'a da Adam ke yanka apple da ita ya zura a aljihunsa.

Sai dai bai hango komai da zai iya yi da wuk'ar ba, don fatansa shine zuciyarsa tayi kuskure akansu...

****


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

37

(☆_☆)

Koda minti d'aya, bai tab'a mance k'irgar saura awa nawa kafin rana ta fad'i ba, bai tab'a kuskuren saura kwanaki nawa ya rage zuwa sanda za'a sake zaman shari'ar ba, zuciyarsa tana bugawa ne kamar da sautin motsawar sakanni kawai, D'aya.. Biyu... Uku... Hud'u... Biyar... A haka har a kai kowacce sittin d'in dake nuna minti guda ta ragu a lokacin da ya riga yayi tanadinsu.

Adam ya d'an gyara tsayuwarsa idanunsa k'ir! akan k'ofar gidan da Maigarin yasa aka rako shi da kyar, bai ko damu da yadda k'ofar gidan da kewayenta

Please Login or Register in order to submit comment