Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata doguwar jacket light brown da gashinsa cikin wani style kamar an barbaza shi wajen goshinsa, k'arya zata yiwa kanta in har tace bai yi kyau ba.

Ya k'ifta idonsa a hankali kafin yace.

"Kin kyauta yau da baki makara ba."

Ya salam! taji kamar ya rad'a mata maganar a cikin kunnenta ne saboda yadda muryar ta fito cike da laziness.

"Bani da lokacin b'atawa yau, idan har ka san zaka sake cewa sai gobe ne, ka fad'a min tun yanzu in juya."

Kamar bai jita ba sai ya turo leda d'aya gaban teburin.

"Kizo ki duba, ina ga kamar na siyo komai daidai, in kuma akwai abinda baiyi ba gobe sai a sake siyowa."

Ba yadda ta iya, haka ta k'araso ciki zuciyarta cike da mamakin me ya siyo, Ledar farko data fara bud'ewa kayan painting ne na kaloli da kuma brushes d'in shafawarsu, ta biyu kuma tarin tarkace ne fal da suka tabbatar mata da abinda kwakwalwarta ke tunani... abubuwan da take so ne gabad'aya a cikin ledar! ma'ana duk abubuwan da suka shafi hobbies d'inta wanda ta rubuta masa jiya.

Ta shiga fiddo su d'aya bayan d'aya zuciyarta na juyawa cike da mamaki, har zuwa kan wata hadaddiyar MP3 dake d'auke da complete karatun alqur'ani... ta tuna cewar ta rubuta harda sauraren alk'ur'ani don hakan ma ya dad'a k'ona ransa, sai gashi da hannunsa yaje ya siyo ya kawo mata.

Ta kasa daure mamakin don haka sai ta d'ago ta kalle shi, ya sake lumshe idonsa kad'an sannan ya gyad'a mata kai.

"Yau zamu fara Maths, ta hanyar da kwakwalwarki zata karb'e shi."

Ya lura bakinta ya k'ulle gabad'aya, ta rasa me zata ce ko kuma abinda ya kamata tace d'in. A daidai wannan lokacin ne kuma wayarsa tayi k'ara, ganin number dake kira yasa ya mik'e da sauri ya nufi can d'aya b'arin library d'in, wajen da dogwayen durowuyin littattafai ke jere.

"Barka da aiki yallab'ai." Ya fad'a muryarsa cike da girmamawa.

Daga d'aya b'angaren wayar aka amsa.

"Barka dai Adam, komai lafiya?"

"Lafiya k'alau, komai yana tafiya daidai."

"Babu wani suspect?"

"Babu ranka ya dad'e daga malaman har d'aliban babu mai zargin wani abu har yanzu."

Da alamun gamsuwa a muryarsa ya sake tambaya.

"Ka kusa gamawa?"

"Duk da ya amince dani a yanzu, wasu abubuwan baya sakin jiki akansu sosai, amma dai a yanzu ma akwai evidence da yawa."

"That's good, kuma babu wata matsala data k'aru?"

Wannan maganar tasa ya juya a hankali ya kalli Fadeelah dake tsaye tana ta juya kayayyakin nan har yanzu, bayanta kawai yake iya gani daga nan, amma zuciyarsa na iya karanto labarin kan fuskarta, musamman daga cikin wad'annan idanun nata...

Sai ya girgiza kansa kawai, ita d'in kamar nauyinsa ce a yanzu ba zai tab'a sanyata cikin lissafinsu ba.

A hankali muryarsa mai taushi tace.

"Babu wata matasala ranka ya dad'e, kuma ina k'okarin kare duk wata hanya da zata fito da cewar ni LAWYER ne!"

*●﹏●*


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

09

(☆_☆)

"Mu fara?"

Muryarsa ta tambaya bayan ya dawo daga wayar daya amsa. Ta juyo da idonta ta kalle shi, me yasa ne wai yau yayi kyau a idanunta?

Har yanzu bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce, don haka sai ta d'aga kanta kawai sanda yaja kujerarsa ya zauna, tana shirin zama a ta gabanta ya tsaida ita ta hanyar d'ago mata zara-zaran yatsun hannunsa.

"Wane irin lenses kike amfani da shi a glass d'inki?"

"Aspheric."

Ya gyad'a kansa a hankali.

"Yana nuna rubutu a juye ne?"

"Kamar yaya?"

"Ina nufin idan nayi rubutu anan, zaki ganshi a daidai daga nan?"

Ta gane me yake nufi amma bata da niyyar magana saboda haka ya nuna mata kujerar dake gefe da d'an allinsa, wadda dama kamar ya tanade ta ne saboda ita. Bayan d'an gajeren tunani taga cewa bata da zab'i saboda haka ta saki kujerar ta zagayo a hankali ta zauna a gefensa.

Sassanyan k'amshin turerensa kuwa ya nemi k'ofofin hancinta yayi masauki, sai ta runtse idonta kad'an jin k'amshin da kwakwalwarta ta yiwa tambari da NASA.

Ya jawo ledar farko mai d'auke da kalolin zane, ya b'are su daga cikin ledojinsu sannan ya d'auko wata farar cardboard paper a gefe.

"Abu na farko da kika fara rubutawa jiya shine kina son zane (painting), don haka dashi zamu fara."

Yanzu da take kusa dashi, sai taji kamar ya lalubi kunnenta ne yana rad'a mata maganar, saboda haka sai ta karkatar da kanta kad'an.

Ya bud'e robobin kaloli guda goma sha biyu.

"Daga 0 zuwa 9, kowacce number zan zana ta da kala daban, sai ki rik'e kalolinsu yadda idan muka fara amsa tambayoyin, kwakwalwarki zata karbi kowacce number da irin kalarta, za'a samu saukin hargitsewarta wajen gane nambobin."

Bata ce komai ba ya cigaba.

"0 - green, 1- blue, 2 - orange, 3- yellow, 4- red, 5-...."

"Kayi d'aga muryarka bana ji sosai."

Ta katse shi. Ya juyo a hankali ya kalleta.

"I'm sorry haka muryana yake, ina damunki ne?"

Kamar yaya yana damunta? yana tunanin muryarsa tana da wani tasiri akanta ne?

Ta girgiza kanta da sauri.

"Ta yaya zaka dame ni, ka cigaba kawai ina jinka."

Bayan ya juya tasa yatsanta d'aya ta k'asan glass d'inta, ta duba kwarmin idonta da tunanin ko kwantsa ya gani a ciki, don ta lura duk sanda zai kalle ta cikin idonta sosai yake kalla kamar mai son lalubo wani abu nasa da ya tab'a rasawa.

Da wata tambaya guda d'aya a topic na farko 'Pythagoras' suka fara, kamar wasa ko wani abu ma majigi, sai gashi a hankali Fadeelah ta fara gane abinda yake yi, saboda yadda yake bin kowanne step na lissafin daki-daki cikin rubutunsa mai tsananin kyau da kuma yadda raunanniyar muryarsa ma ke mata bayanin kamar ana zirara ruwa cikin roba a hankali.

Sannan dad'in dad'awa da taimakon yadda kowacce number ke fitowa cikin nau'in kalarta daban, sanda suka gama tambaya ta farko sai yayi kama da draft d'in zane, ta dinga gani a idanunta yadda zata ja kowacce kala zuwa 'yaruwarta har su had'u su fitar da wani hoton. Lissafin da ake yinsa a aji tana ganinsa kamar wani tashin duniya sai ya zama kamar d'an uwan zanenta a yanzu har taji ta k'agu a tafi wata tambayar don ta samu a sake fitar da wani abun.

Wasa-wasa, a cikin awa guda kawai sai ta suka amsa tambayoyi hud'u, wanda babu wanda bata fahimta ba a cikinsu, Allah ya sani kwarai ta jinjina masa yadda ya iya mata bayanin cikin nutsuwa, sai yanzu ta fahimci zancensa da yace zasu iya gama gabad'aya topics d'in cikin lokaci.

A wannan daren bayan ta gama dukkan harkokinta na ranar, tayi sallah sannan tayi wanka, ta saka wata 'yar k'aramar riga armless iya gwiwa, sannan ta d'ago cardboard paper da ta amsa question guda d'aya da yace in ta koma gida tayi, rana ta farko a rayuwarta data amsa lissafin Maths kuma tayi daidai, don ya rubuta mata final answer a bayan paper yace in har tayi daidai amsar da zata samu kenan, kuma bayan ta dawo gidan ta kasa ko cin abinci sai da ta zauna tayi, haka tayi ta zagaye gidan da murna rik'e da paper su Mami ma na taya ta.

Ta rufe idonta a hankali, sanda fuskarsa ta ranar ta haska a cikin su, tana son kalar brown sosai watakila shi yasa shigarsa ta yau tayi mata kyan da har ta kasa manta ta.

Ta hango yadda gashin idonsa ke kwantawa akan na k'asansa duk sanda yake rubutu, sai kaga kamar ya rufe idon ne gabad'aya. Me ya same ta ne wai? ya kamata tayi wa kanta fad'a, Adam d'in data tsana kamar me shine tun ba'a je koina ba take b'ata lokacinta wajen tunaninsa? don kawai ya koya mata maths ta gane? wannan ma ai shirme ne.

Ta ja tsaki a hankali sannan ta ninke paper ta ta ajiye akan bedside drawer, daidai sanda wayarta dake gefe tayi haske alamun shigowar message.

Memory loss girl kin kwanta?

Ta karanta sak'on da muryar Al'ameen kamar yadda number ta nuna shi ya aiko, a cikin kwana biyu ta fara sabawa da Al'ameen sosai ta hanyar chatting d'in da ta koya ta dalilinsa, don kullum zai aiko mata da text lokacin da zata kwanta wani lokacin ma har da safe kafin tafiyarta makaranta, sai dai bai k'ara zuwa ba don kullum yana gaya mata abubuwan sun masa yawa, don harkar settling d'insu a garin da komai yana hannunsa.

Da murmushi a fuskarta hannayenta suka rubuta.

A'a

Beeem!

Wani sak'on ya shigo a take.

Thank god ban tashe ki ba, kin yini lpya?

Lafiya k'alau. And you?

Dama baki tambaya ba, don nasha wahala sosai yau, in na fara gaya miki zaki tausaya min.

Ta sake wani murmushi sannan ta rubuta.

Me kayi?

Intrested? ya tambaya.

Yes.

Ta tura sak'on da ya haddasa doguwar hira a tsakaninsu, doguwar hirar data shafe ta kuma wanke tunanin Adam a kanta!

***

Adam ya rufe idonsa a hankali yana hasko nata daga ciki, idanun dake hana masa sukuni a kowacce bullowar rana zuwa fad'uwarta, musamman a kowanne dare lokacin da zai zo kwanciya. Ya lullub'e jikinsa da bargo baki d'aya kamar hakan ne zai hana shi tunanin idanun nata kafin bacci ya d'auke shi.

A baya inda zai karanta cewa wani abu zai zo ya dami kwakwalwarsa bayan burin da yake dashi, zai k'aryata koma meye ne kuma yayi sanadin dakatar dashi.

Sai dai sanin gaibu baya hannun d'an adam, a yanzu ya tabbata koda wani zai kawo masa hanyar da zai cire tunaninta daga kansa ba zai tab'a karb'a ba, don watak'ila ya saba koma yana jin dad'in hakan.

A hankali tunaninsa ya gangara can baya zuwa wani lokaci baya kad'an...

*WANI LOKACI BAYA KAD'AN.*

K'arfe takwas da rabi na safiyar ranar talata, had'addiyar motarsa tayi parking cikin jerin gwanon motocin dake harabar ma'aikatar kotun.

Ya d'auki ragowar lemonsa dake gefe yana d'iga saboda rab'ar sanyi ya k'arasa shanye shi sannan ya zare bak'in gilashin dake fuskarsa, kwayar idonsa mai kyau ta haska a cikin d'an karamin mudubin dake gaban motar, gashin kansa a kwance yake cikin style mai kyau yana kyalli sannan yana da saje amma ba mai yawa ba, mai laushi wanda yabi ya kwanta kan fatarsa mai kama da launin chocolate mai haske.

Ba wai fuskar tasa yake kallo ba, a'a tunani ne fal a cikin kansa wanda zuciyarsa ke d'ebewa da tarawa a hankali. A jiya ya gama case d'in da yake aiki akai kuma yayi nasara, yana fatan hakan ya bashi ikon samun hutun watanni ukun da yake nema wanda zai saita rayuwarsa dasu, ya san abu ne mai wuya a yanzu da ba lokacin leave d'insa ba ya samu hakan shi yasa ya dage iya k'okarinsa ba dare ba rana ya had'a evidence d'in da suka bashi damar cinye shari'ar da fatan a dubi nasararsa a bashi wannan damar.

Ya jawo 'yar k'aramar briefcase d'insa dake kan kujerar mai zaman banza sannan ya fita daga motar, ta tsakanin d'inbin motocin dake tsaye a wajen yayi ta kurd'awa har zuwa cikin tamfatsesiyar kotun.

"D'an k'araminsu babbansu kenan!"

Muryar wani abokin aikinsa ta fad'a sanda ya nufi hanyar elevator d'in da zai kaishi ofishinsa.

"Ka san jiya ban zauna ba, ashe an gama case d'in nan kuma kayi nasara, gaskiya Man na taya ka murna kayi k'ok'ari sosai, weldone Steve! "

Ya kirashi da surname d'in da suke kiransa a kotun.

"Thank you Ryan, Nagode sosai."

Ya amsa da muryarsa mai zurfi sanda ya bud'e elavator suka shiga bakid'aya, sai dai kafin k'ofar ta kai ga rufewa wani lawyer mai suna John ya shigo rik'e da files d'insa, bai ko kalle su ba ya nemi waje ya tsaya, lift d'in ya shiga d'agawa.

"Ka san me, zan zo in karb'i clues a wajenka, don ina assisting wani case lowcoast court shigen naka, wa ya sani mu ma muyi nasara in mun bi irin hanyoyin da kayi amfani dasu saboda..."

Ryan ya cigaba da magana lokacin da gravity na lift d'in ke d'aga su sama, sai da hankalin Adam kwata-kwata baya kansa, yana ga mutumin nan dake gabansa hannayensa rik'e da files, haka kurum jikinsa ya bashi wani abu, don mutumin yana d'aya daga cikin 'yan team d'in da suke adawa dashi tun farkon fara aikinsa a wajen wanda yanzu shekara guda kenan.

Zarginsa ya k'ara tabbatuwa lokacin da John d'in ya tsaya a hawan da office d'in shugabansu yake, saboda haka ya sawa zuciyarsa ta yarda cewa dole akwai wani abu da aka shirya masa yau wanda ke shirin faruwa, don ya fahimci cewa an daidaici lokacin zuwansa ne ma aka saka John yazo rik'e da wad'annan files d'in don a nuna masa daga ina koma meye ake shirin k'ulla masan ya fito.

Da kyar ya samu ya tserewa surutun Ryan ya k'arasa cikin office d'in nasa. Kasancewar jiya ya gama case d'insa sai ya zama ba abinda zaiyi yau illa rubuta wasu dokoki da zai turawa wani d'an kasuwa kan sha'anin da ya shafi kasuwanci.

Wajen k'arfe goma ya jawo wayarsa ya danna kiran da kusan kullum yake saman call log na wayarsa, kiran kuma da ya san ba zai tab'a amfanarsa da komai ba.

"Hello, barkan ka dai, kana magana _ne da gidan kula da tsofaffi da masu rauni na garin Leicester a k'asar England."

Ya lumshe idonsa kad'an jin wata sabuwar murya ba ta matar daya saba ji in ya kira ba. A hankali ya amsa.

"Barkanki da aiki, ina neman wata mata ne mai suna Magareth, ance min tana tare daku."

"Haka ne kwarai Magareth tana tare damu, waye kai a wajenta? d'anuwa ne?"

"A'a..." ya amsa abinda yake fad'a kullum, sannan ya cigaba da k'arashen.

"Ina son inyi mata wasu tambayoyi ne game da IYAYENA!"

"Na fahimta amma sai dai kayi hakuri, magareth ta tsufa da yawa kuma tana da lalurar kunne bata iya amfani da yawa, sai da kazo da kanka in har kana son amsar tambayoyinka, zata ji dad'in zuwanka!"

D'ib! ya kashe wayarsa sannan ya koma da baya ya kwanta a jikin kujerar, a kowacce safiya dake fitowa magareth k'ara tsufa take, don haka dole ne yayi k'ok'arin samun lokacin da zai isa gareta kafin ta mutu, damar da yake da ita guda d'aya ta tankwab'e.

Da kyar ya samu ya saita tunaninsa, sannan ya koma kan aikinsa ya cigaba. Da misalin k'arfe sha biyu na wannan ranar kuma ya samu kiran da ya sawa zuciyarsa tsammaninsa, ya samu kiran da ya canja akalar rayuwarsa kamar yadda igiyar ruwa ke tambali da k'aramin jirgi a tsakiyar teku.

"Na taya ka murnar samun nasara akan case d'inka."

Muryar shugaban nasu ta ambata lokacin da yake zaune a kujerar tsallaken teburin bayan ya amsa kiransa.

"Nagode sir." Adam ya fad'a a hankali kamar koyaushe.

"... sannan naga proposal d'inka cewa ka nemi hutu na wata uku ko?"

"Haka ne sir, ina da wani abu mai muhimmanci ne da nake son yi a yanzu."

Sai ya tab'e bakinsa kad'an.

"Amma ka san baka dad'e da karb'ar hutu ba ko?"

"Na sani, shi yasa na nemi hakan a matsayin alfarma."

Shiru ya biyo baya kafin ya sake magana.

"Mu ajiye zancen hutunka a gefe Steve, akwai aikin da shigo yanzu kuma ba wanda ya dace dashi sai kai... saboda haka wannan ba case ne da zaka yi din ra'ayinka ba, case ne da ya zama umarni bama daga ni ba, daga can shugabanmu gabad'aya kuma babu wanda ya isa ya canja shi."

Adam bai ko yi motsi ba balle yayi magana har zuwa lokacin da hannun shugaban ya d'auko wannan file d'in daya gani d'azu a hannun John, a sannan ne yaji zuciyarsa tayi wani irin motsin da shi kad'ai ya san ma'anarsa.

"Case ne akan wani mutumi da ake zargi da kisan kai daga can garin Alaska, an neme shi an rasa sai a yanzu ake tunanin ya gudo daga garin yazo nan ya bud'e sabuwar rayuwa a matsayin malamin makaranta, saboda haka babu hanyar da za'a tabbatar da hakan sai ta 'Private investigation'.

Saboda haka zaka b'ad da kamannika sannan kaje makarantar da yake a matsayin d'alibi, kabi dukkan wasu hanyoyin da zai amince da kai a harkokinsa yadda zaka sami enough evidence d'in da zamu iya tunkararsa, daga nan sai ka dawo kotu ayi handling case d'in."

Saurararsa kawai yake yi amma kwakwalwarsa ta gagara saita maganganun akan layi d'aya, yaje wata makaranta a matsayin d'alibi? ta yaya hakan zai yiwu? ta yaya zai rage shekarunsa? me yasa ma sai shi d'in?

"Saboda kaine mai k'ananan shekaru duk cikin ma'aikatar nan kuma kai ne kad'ai baka tab'a magana da media ba ba ka fara aiki bada dad'ewa ba, babu wanda ya sanka sosai, sannan akwai wanda zai kula da harkar kammaninka a gefe guda, shi zai saita ka akan duk abinda zaka bi ka koma irin yanayin d'aliban makarantar."

Bai yarda da zancen ko kad'an ba, don ya riga ya san su waye suka yi masa cunen wannan aikin, amma kamar yadda shugaban ya fad'a ne a farko ba yadda ya iya dole ne ya amsa, saboda haka ya gyad'a kansa sannan yace.'

"Na fahimta kuma zanyi dukkan k'ok'arina ranka ya dad'e babu matsala, a bani files d'in da kuma sauran abubuwan da zan buk'ata."

Watak'ila ya fahimci cewa dauriya kawai yayi ya fad'i hakan, don maimakon ya amsa sai ya kira sunansa da wani irin amo mai jan hankali.

"Yes sir."

Ya amsa shima cikin malalaciyar muryarsa.

"Idan har kayi nasara a wannan case d'in, na tabbatar maka ni da hannuna zan yi signing cewa a baka leave na shekara guda."

Sai ya d'ago da fuskarsa sosai ya kalle shi, da gaske yake zai nema masa hutu har na tsawon shekara guda? a hankali yaji wani abu kamar sabon k'arfi da kuma son case d'in ya gifta a zuciyarsa, yaji cewa dama zai iya gama aikin a cikin 'yan kwanaki kawai!

"Amma akwai wani hanzari ba gudu ba Steve, mutum da zaka yi binciken akansa, yana da tsananin k'in wannan addinin na musulunci, saboda haka abinda zaka fara yi shine had'a k'ungiyar da zata dinga sukar wannan addinin, ta nan zai fara lura da kai bayan ka shiga k'ungiyarsa ta kwallon k'afa sannan..."

Adam bai san zancen da ya cigaba da yi bayan ya fad'i cewa sai ya zama mai sukar musulunci ba, ubangiji ya sani shi BA MUSULMI bane amma musulunci bai tab'a damunsa ba don ya san abubuwa da yawa game dashi, kuma yana ji a jikinsa cewa ba zai so ya zama mai takurawa mabiyansa ba.

Sai dai mafitar da yake nemarwa kansa tafi k'arfin wannan a lokacin, saboda haka daga wannan lokacin yabi umarninsu ya aske gemu da sajensa, ya barbaza gashinsa da kullum yake a kwance sannan ya shiga bin duk wata hanya da mutumin da aka d'auko ke nuna masa yadda zai koma yaro matashi mai irin shekarun samarin makarantar.

Daga wannan lokacin kuma, k'addarar rayuwarsa ta had'u ta kanannad'e data Fadeelah!

***

"Deelah, saura wad'annan plates d'in na can sama."

Mami ta fad'a lokacin da Fadeelah ta taka can saman kata tana mik'o mata kayayyakin da suka dad'e basu yi amfani dasu ba, kayayyakin data rasa meye amfanin d'ebo sun da ake yi.

Suna kitchen ne gabad'ayansu a ranar Asabar, ita tana d'ebo kayayyakin, Mami kuma tana ware wad'ansu sannan ta mik'awa Zahra dake bakin sink ta shiga wankewa.

Beeem!

Wayarta dake ajiye daga gefen k'afarta akan durowar data taka tayi k'ara alamun shigowar message, ta sunkuyo da kanta daga tsayen sanda k'arfin ganin gilashin idonta ya nuna mata d'an k'aramin hoton fuskar Al'ameen da kuma sak'onsa a gefe.

Dan Allah ki gaya min baki yi fushi ba, I'm so sorry sai yanzu naga message d'inki wallahi.

Tayi murmushi kad'an sannan ta d'aga kanta ta cigaba janyo wasu kofuna, ta tashi ne da safe taga sak'onsa na mata barka da safiya, bayan ta gama breakfast ta tura masa da cewar ta gode ya weekend d'insa? bata ga reply d'insa ba sai yanzu kusan k'arfe d'aya na rana, ta san cewar a yadda ta tambayar ba wai dole ne ya turo mata da amsa ba, amma haka kurum taji zuciyarta ta d'an damu, ta dinga kallon wayarta da jiran message d'insa a duk abun da take yi, har sai da ta kai duk bayan minti d'aya sai tayi bud'e ta, ta duba.

Beeem!

Wani message d'in ya sake shigowa, ta sunkuya fuskarta da sauri.

Please ki min magana mana, I'm sorrryyy!

Wani dad'i ya ratsa ta a take.

"Ga wani green kwali can na toaster mik'o shi."

Mami ta katse tunanin dake shirin faruwa akanta.

"Mami dan Allah kar kice shima wanke shi za'ayi, seriously na gaji Allah."

Zahra ta fad'a tana zare idonta akan kwalin, daga gefen idanun Fadeelah tana ganin yadda Mamin ta gallara mata harara.

"Zaki yi min shiru anan ko kuwa, yaushe rabonki da wanke plates a gidan nan."

Beeem!

K'arar wani message d'in.

Da gaske fushi kika yi?

"Jawo kwalin mana deelah, a hankali."

Sai ta d'aga kanta ta shiga k'ok'arin d'aukowa.

Beeem!

Memory loss girl, you there?

Beeem!

Ki min magana.

Beeem!

Babe?

Sai ta sunkuyo gabad'aya sanda ta mik'awa Mami kwalin, hannunta duk k'ura ta d'auki wayar, Idanunta suka manne akan sak'onsa na k'arshe... *Babe* Ya salam ya Allah! ita fa ya kira da haka, taji wani irin dad'in da bata san dalilinsa ba ya shiga ratsata.

Beeem!

Wani sak'on ya k'aru akan na k'asa.

In kira ki?

Sai ta shiga danna keybord d'in dake k'asa da sauri.

A'a gani nan.

Sai kuma ta k'ara da...

Ina wani aikin ne shi yasa kaji shiru.

Beeem!

You just save a life!

Ta cije k'asan lebb'enta da k'arfi jin hakan.

Beeem!

Kiyi hak'uri, naje wani interview ne shi yasa ban amsa miki da wuri ba.

Sai ta rubuta k'arya irin ta kowacce Mace.

Ba komai fa, ni na manta ma da text d'in.

Beeem!

Aikin me kike yi?

Kitchen.

Beeem!

Mrs chef! hannunki mai albarka ne, shi yasa tun daga nan, naji fingers d'inki na k'amshin curry.

Ba girki nake ba Mr. predictor, gyara ne.

Beeem!

Yayi kyau, na fara koya miki.

Me fa?

Beeem!

The pet names, gashi nima kin fara saka mun suna, wa ya san a ina zamu tsaya...

Murmushinta yayi k'arfin da ya kusan zama dariya.

"Fadeelah, mik'e ki mik'o min kwandon can na gefe."

Mami ta dawo da ita cikin zagayen duniyar da suke daga wadda Al'ameen ke neman kai zuciyarta.

A wannan ranar, komai ya k'ara kala a idanun Fadeelah, duniyar tayi wani haske da kyalli, iska tayi sanyi, korayen bishiyun unguwarsu suka k'ara kyau a ganinta, ta cika da wani irin nishad'in da take ganin kowa ma irinsa yake ji duk saboda zuciyarta da yatsun hannunta na tare da Al'ameen a cikin wayarta.

****

Washegari lahadi, da daddare bayan sun gama cin abincin dare, Daddy ya tara su a falo gabad'aya, ya shaida musu wani abu da basu tab'a zato da tsammani ba, cewar ya nemi aiki a wani asibiti dake Nigeria garin Abuja, (Garinsu Mami) don abubuwa sunyi masa yawa anan ba zai iya affording komai ba, don haka su taya shi da addu'a zuwa wani watan yake sa ran samun bayani daga wajensu.

A lokaci d'aya kwakwalwar Fadeelah ta gaya mata cewar wannan shawarar ta Mami ce, don ba tun yau ba ta fahimci tana zaman cikin turawan nan ne kawai saboda nauyin igiyar aure, amma tunaninta da zancenta a kullum yana mahaifarta, shi yasa tayi amfani da wannan damar ta lallab'a Daddy ya nemi aiki a Nigeria inda take da tabbacin zai samu don Nigeria ba kamar Turai bace da likitoci masu fasaha irin Daddy suka yawaita.

Sai a sannan ta k'ara fahimtar manufar Mami na rage kayan gidan, tunda sun kusa tashi meye amfanin ajiyarsu.

Kamar yadda Iman ta cika gidan da murna wannan daren haka itama nata tunanin ke ta tsallen murna saboda tana ganin kamar komawa Nigeria, zai tallafa wajen warkar da ciwonta da wuri, idan har tana cikin kewayen da zata dinga ganin abubuwan da suka shafi rayuwarta ta baya.

Zahra ce kad'ai taga alamun bata yi farin ciki ko b'acin rai da zancen ba, ita ta tunanin yadda zata siya make-up kit da wasu inner wears da ta gani online take. Amma Farouk ya damu sosai da tunanin zai rabu da abokansa da ya riga ya saba dasu.

A lokacin da tazo kwanciya text d'in Al'ameen na Goodnight ya nuna tar! akan screen d'in wayarta, sai taji kamar wani b'angare na zuciyarta yana fad'a mata ne cewa in har ta koma Nigeria, zata tafi ne ta barshi anan... ta tafi da b'arin zuciya guda d'aya!

Saboda haka a cikin baccinta tayi wani irin mafarki mai d'auke da abubuwa kala-kala! wanda muhimmi shine akwai Al'ameen a cikinsa sai dai d'auke da muryar Adam, ko yaya bud'e baki yayi magana maimakon muryarsa sai taji wannan malalaciyar muryar ta Adam kamar tana busawa ne a hankali cikin kunnenta.

***
*BAYAN NA MUTU!*

©AYSHA SHAFI'EE

*10*

*(☆_☆)*

A cikin kwanakin da Mami ke lissafawa na ragowar lokacin daya rage musu a k'asar turai, abubuwa suka cigaba da gudana bi-da-bi, sababbi da kuma al'amuran yau da kullum na rayuwa. Daga cikin sababbin akwai wata irin shak'uwa mai k'arfi data

Please Login or Register in order to submit comment