Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bak'in fenti haka?"

Zainab ta shiga yanka wani k'aton tumatir jawur dashi sannan tace.

"Meye abin tausayi anan Ladi, bak'in halin uwa ne fa ta d'auko, ko kin manta yarta Mairo ma guduwa tayi da saurayi tun iyayen na da rai, ai ni wallahi a zaman yarinyar gidan nan har bana son a aiko ta sashena, kinga wannan d'an banzan farin nata da yalolon gashin nan, mayya sak! nake kallonta."

Ladi ta kyalkyale da dariya harda buga cinya sannan tace.

"Allah ya shiryeki Zainab, maita ai ba'a fari take ba."

"Ke dai bar mutum kawai, ai shi yasa a ranar da Hajiya ta mutun nan, na zage iya k'arfina nima na shiga aka jibgeta don wallahi bana d'auke kokonton yawan laulayin yusufa (d'anta na biyu) daga ita ne, don ina dab da haihuwarsa ta dawo gidan nan."

Ta fad'a daidai sanda ta gama yankan tumatirin, sannan ta saka k'aton cokali ta juya shi tsaf komai ya had'e, ta janyo wani k'aramin filas dake gefen tabarmar da suke kai ta d'ebi na maigidanta da yaran da suka tafi makarantar allo sannan ta juyo musu da ragowar suka shiga ci.

Sai dai basu kai ga saka loma ta biyu a bakinsu ba, Salihu babban d'anta ya rugo cikin tsakar gidan sakale da allonsa a hammata.

"Kai don ub*nka haka ake shigowa gidan mutane ba sallama kamar wani kafiri?"

Ta daka masa tsawa lokacin da yaja birki a gaban tabarmarsu.

"Ina sauran suke?" Ta katse rawar zancen da bakinsa ke yi.

"Suna can gindin motar suna kallo."

"Motar wa kuma?"

"Mama, Mama wani balarabe ne yazo daga Makka a cikin wata had'addiyar mota, tun muna addu'ar tashi muka ganshi ya wuto mu, yanzu haka dukka su Kawu sun cika wajen Kawu d'anjuma jingim!"

Ita da Ladi kallonsa kawai suke da mamakin yadda ya rikice haka.

"Wajen Kawu Danjuman yazo?"

"Eh mana, kuma naji su yaya Sule suna fad'in wai d'anuwanmu ne!"

***

"Sule me ya faru ne haka?" Me akeyi?"

Kawu Ibrahim ya tambaya sanda ya shigo gidan shida babban d'ansa Harisu da la'asar lis! Daga zagayen gonakinsa da suka dawo.

Banda tarin yara birjik da suka wuce a k'ofar gida sun yanyame wata mota, yanzu kuma ya shigo gidan yaga kusan duk samarin da ba'a fiye samunsu a wannan lokacin ba suna tsaitsaiye kan hanyar shiga sashen Kawun.

Sule ya d'an sunkuyar da kansa ya gaishe shi sannan yace.

"Kawu bak'o akayi ne daga wata k'asar ina jin, kuma naji su Kawu Sulaiman suna cewa wai d'an gidan Baba Ahmadu ne."

Cak! Bugun zuciyarsa ya tsaya na wasu 'yan dak'k'ai, ya kalle shi sosai sannan ya tambaya.

"Wane Baba Ahmadun?"

"Wanda dai ake bada labarin cewa ya b'ata shekarun baya da ak..."

Ai bai ko tsaya saurarar k'arashen ba ya wuce su duk ya durfafi hanyar sashen Kawu Danjuma. Tun daga adadin takalman dake cire a waje zuciyarsa ta tabbatar masa cewa zancen Sule gaskiya ne, don yaushe rabon da a hudu duk a irin wannan lokacin? Sai ya cire nasa daga gefe shima sannan yasa kai cikin d'akin.

Zai iya cewa kowa na nan, yayyensa dama k'annensa da suka manyanta, irinsa masu uzirin nesa kad'an ne basa nan sannan ga Kawu d'anjuma zaune a tsakiyar shimfidarsa, sai dai duk lura da wannan yazo ne bayan siffar Ahmadu k'aninsa daya hanga zaune a gefen Kawu d'anjuma, Ahmadunsa sak! Kaninsa da duk fad'in babban gida daga shi sai k'anwarsu jummai ne suke uwa d'aya uba d'aya.

Amma wannan da yake gani Fari ne ba bak'i ba, sannan in ka d'ebe lallausar sumar kansa, to ba abinda zai banbanta shi da wancan Ahmadun daya bar gida a irin wannan shekarun.

Kwanan nan zan hutar da kai yaya, kwanan nan zaka manta da wahalar noman nan, sai dai kana zaune ka saka ayi maka, kwanan nan yaya!

Maganar wancan Ahmadun ta dawo cikin kansa tar! Maganar da ita ta zama magana ta k'arshe da ta shiga tsakaninsa da d'anuwansa, don daga wannan ranar Ahmadun yayi b'atan damo daga cikin rayuwarsu gabad'aya, aka neme shi aka rasa.

"Karaso mana Ibrahim, taho kaga ashe bamu sani ba Ahmadu ya mutu ya bar jininsa a duniya."

A hankali Kawu Ibrahim ya k'arasa ya zauna a gefen d'an baturen Ahmadun da yake gani.

"Wannan yayan mahaifinka ne da suke uwa d'aya uba d'aya."

Kawu d'anjuma ya fad'a sanda ya juya yana kallonsa, sai dai yana rufe baki Sa'idu ya d'auka, ya fad'i abinda kawun ya fad'a sak amma da turanci.

"Baya jin hausa Ibrahim sai turanci, yace daga America yazo."

Kawu d'anjuma ya tari mamakin daya nuna akan fuskarsa.

"America kuma Kawu? Shi Ahmadun can yaje ya haife shi?"

"I, nima abinda nace kenan, da mamaki da d'aure kai amma gashi yazo da shaidun da suka nuna shi d'an nasa ne."

"Ko ba shaida Kawu na yarda wannan d'an Ahmadu ne, zan iya tsayawa gaban ko waye kuwa in tabbatar da hakan."

Adam bai san me yace ba, amma sai ya zab'i daidai wannan lokacin ya matso gabansa sannan ya rik'o hannayensa, iya hasashensa ya yarda cewa duk cikin mutanen nan wannan shine madadin mahaifinsa, uwa d'aya uba d'aya yafi k'arfin komai.

Kwalla mai d'umi ta gangaro kan kumatun Kawu Ibrahim, don gani yayi sak! Kamar k'anin nasa ne ya dawo gabansa yake neman gafararsa, sai shima ya damk'e nasa lallausan hannayen da suka shaida cewa ko daga ina yake, bai tashi cikin wahala kamar Ahmadunsa ba.

Tiryan-tiryan, Adam ya zauna ya shaida musu tarihinsa da kuma na iyayensa da yaji daga Magareth, shakka babu sun tausayawa irin rayuwar da d'anuwansu ya tsinci kansa, sannan kuma Adam yasha godiya da jinjina kan kokarin da yayi har ya nemo su bai kyamaci cewa su dangin nasa basu zo a irin wajen daya taso ba.

Kawu Ibrahim shi ya shaida masa sai bayan shekaru biyu da b'acewar Ahmad ne suka sami labari cewa wani aboki ya had'u dashi daya kwad'aita masa sana'ar shigar da kwayoyi k'asashen k'etare da cewar kud'i ake samu masu yawa, kuma daga nan basu k'ara jin labarinsa ba.

Da wannan Adam ya had'a ya fitar da cewar an kama mahaifinsa ne a kokarinsa na shigar da kwayoyin k'asar America kuma aka mik'a shi kurkuku daga nan, tunda kuma k'asa ce da bashi da kowa haka ya zauna har zuwa lokacin da aka zo aka d'ebe su zuwa filin yak'i inda anan ya hadu da mahaifiyarsa.

A wannan ranar Adam yaga k'auna kala-kala ba daga iya mutanen babban gida ba harda sauran gidajen da duk su Kawu suka san akwai wad'anda suka san Ahmadu cewa ga d'ansa ya dawo suzo su ganshi. Ba kowa ke iya magana dashi ba saboda haka har yara haka yayi ta binsu da gaisuwar hannu ba tare da ya damu da banbancin tsaftar jikinsu da nasa ba, Abinci kuwa har daga can bakin layi haka akayi ta aikowa daga gidaje-gidaje cewa na saukar d'an bature ne... Al'ada dai irin ta mutanen da wayewar zamani bata ratsa su sosai ba.

Kuma babu kyankyami balle tunanin wani abu haka Adam yasa hannu ya d'andana abincin mafi yawan kwanukan nan ba tare da ya san sunan yadda aka sarrafa ko abu guda da yake ci ba.

B'angaren Kawu Ibrahim aka shirya masa d'aki guda na musamman ya kwana anan, rana ta farko a rayuwarsa Adam ya kwana cikin rufin wani irin gini da bai taba gani ba, rana ta farko daya kwana a d'akin da babu kyale-kyale irin wanda ya saba sannan rana ta farko daya shigo cikin kabilarsa da bai tab'a gani ba. Sai dai tunda babu sauro kuma akwai fankar dake juyawa da wutar lantarki, sai yayi wani irin bacci da rabon da yayi shi tun zamanin da bai san wanene shi ba, yayi bacci da zuciyarsa sakayau babu wannan nauyin daya saba ji a kodayaushe.

Kamar kullum yau ma babu fashi, abu na k'arshe da ya gifta cikin idanunsa shine nata idon, sai ya lumshe nasa cikin nata a hankali kamar mai son yin magana da ita.

***

Washegari, da tarbar cima ta musamman ya bud'e ido, kayayyaki ne barkatai na duk kayan da suka san zai iya cinsu, saboda haka sai da ya cika cikinsa taf sannan ya shirya ya fita cikin jagorancin Sa'id, da ya zama tafintansa tun jiya.

A falon Kawu Danjuma ya zauna, inda manyan mutane da dama suka yi ta zuwa ana gaya masa cewa suma 'yanuwa da abokan arziki ne na dangin mahaifin nasa, hatta matan cikin Babban gida daga tsofaffinsu har kanana sai da suka zo ganinsa.

Anan ya fahimci cewa asalin 'ya'yan Babban gida wato sauran 'yanuwan mahaifinsa su ashirin da biyu ne, kuma hud'u ne kawai a ciki suka rasu, banda mahaifinsa sauran goma sha bakwai d'in duk suna cikin Babban gida da 'ya'yayensu da kuma tarin jikoki dake tasowa gasu nan birjik!

"A cikin masu rasuwar mata uku ne, kuma suma wasu daga cikin 'ya'yansu suna nan tare damu, wasu sunyi aure, wasu kuma suna can wajen dangin iyayensu maza."

Kawu Ibrahim ya fad'a masa bayan zuwan mutanen ya lafa a ranar, Sa'id na daga gefe yana fassara masa.

"Amma d'aya daga cikinsu ita bata yi aure ba ta rasu, wadda itace k'anwarmu jummai da muke uwa daya uba daya da ita nida mahaifinka, d'ayan kuma magidanci ne k'anninsu Kawu Jamilu d'an gidan Hajiya balaraba dana shaida maka itace ta k'arshe mai rasuwa a cikin matan gidan.

Yana da ma mata uku da 'ya'ya takwas shima, shida duk maza ne babarsu d'aya kuma yanzu haka suna zaune a can gidan nasa, sai kuma mata biyu da suma babarsu d'aya, d'aya matar ita bata haihu dashi ba har ya rasu."

Haka kurum sai Adam ya samu kansa da tambayar ina mata ta biyun da kuma 'ya'yan nata.

"Ita ta rasu tun kafin rasuwarsa 'ya'yan kuma basa nan yanzu haka."

Da wannan Kawu Ibrahim bai k'ara komai akai ba, don tunaninsa bai bashi cewar daga shigowarsa cikinsu ya dace ya fara sanin wasu munanan abubuwan ba. Sai yamma lis! sannan Adam ya samu keb'ewa da Sa'id wanda ya fara sabawa dashi a lokacin, babu wata kwana-kwana ya shaida masa cewa yana son ya musulunta ne... yana son komawa addininsu da kuma na mahaifinsa.

Maganar ta daki Sa'id ya tsaya kawai yana kallonshi, yanzu dama shi ba musulmi bane kenan? Ta yaya to sunansa ya zama Adam? Tabbas ya san a labarinsa ya fad'a musu cewa turawa ne suka raine shi, amma ba shi kad'ai ba ya san har ga Allah duk cikinsu babu wanda ya kawo wannan tunanin akansa. To ta yaya ma zasu yi bayan wannan kamilalliyar siffar tasa na nunawa wasu cewa shi balarabe ne ma.

Babu wani b'ata lokaci ya shaidawa su Kawu Ibrahim, kuma anan cikin falon Kawu D'anjuma aka MUSULUNTAR da Adam, ya koma Adam na gaske don ya zab'i sunansa akan canjin wani tunda ko a musuluncin sunan mai ma'ana ne, daga nan Kawu Ibrahim ya d'ora Sa'id kan alhakin koya masa abubuwan da suka shafi tsarki na musulunci da kuma karatukan daya kamata ya sani a yanzu tunda shima Sa'id da d'an iliminsa.

Cikin kwanaki biyar a garin Ikara, Adam ya sake sosai cikin 'yanuwansa kuma ya san abubuwa da yawa na al'adar bahaushe tsantsa! Watakila rashin sabon wani abu kan takura shi a wasu lokutan, misali ruwan wanka, na sha da kuma harkar d'aukewar wutar lantarki, amma daidai da rana d'aya bai bari hakan ya hauro kan fuskarsa ba, har mamaki Sa'id yake na yadda yake sakewa yaci abincinsu, gashi kuma a cikin kwanaki biyar d'in kawai ya fara iya rik'e wasu kalmomi na hausa.

A sannan ne kuma ya shirya tafiya don bayan zuwansa Nigeria a ranar ya hawo wani jirgin zuwa Kaduna, inda ya kwana d'aya anan washegari kuma ya sayi mota sannan bisa jagorancin wad'ansu, ya d'auko direban tasha ya kawo shi har cikin Ikara.

Saboda haka yanzu zai koma can ABUJA ne inda d'aya daga cikin manyan ma'aikatar da yake aiki dasu a America yayi recommending d'insa zuwa wata k'ungiya irin tasu ta lauyoyi mai zaman kanta anan Abujan. Kawu d'anjuma ne ya bada shawarar cewa sai dai ya tafi tare da Sa'id don ya dinga k'ara wayar dashi akan abubuwan Nigeria da kuma harkar karatun addininsa ma.

Ai kuwa babu wani kokonto Sa'id ya had'a kayansa ya bishi tunda dama ya gama karatunsa anan ABU ta zariya kuma yanzu ba abinda yake sai taya mahaifinsa aiki a shagon awonsa.

Ya tafi ya barsu da d'imbin alkhairi na kud'i yadda hatta k'ananun yara a babban gida sun shaida da zuwan BATURE ADAM!

***

A B U J A

"Kin Amince?" Al'ameen ya tambaya a hankali cikin wayar.

"Me Maminka tace?" Muryar Fadeelah ta biyo bayan wani lokaci.

Yawu ya zarce cikin makogwaronsa, a hankali ya tattara saura ya had'iye sannan ya amsa.

"Da da yanzu ba d'aya bane Fadeelah, idan Mami bata so ki a da ba, yanzu komai ya canja ai, saboda haka karki damu yadda mahaifina ya bada goyon bayansa haka itama bata ce komai ba."

Maganar da nauyi, kuma yarda da ita da wuya, amma zai mata k'arya ne? Zai fadi abinda ba haka ba alhali duk daren dad'ewa dai zata je ta fuskanci Aunty Miryaman?

"Kinyi shiru Fadeelah, ko sai zuciyata ta k'arasa fitowa ne waje gabad'ayanta?"

"To me kake son ince Al'ameen?"

Ya lumshe idanunsa kadan jin yadda ambaton sunansa da muryarta ya ratsa ko'ina a jikinsa.

"Cewa zaki yi na amince da kai Al'ameen kuma ina sonka da dukkan ruhina."

Murmushi ya sub'uce mata, tana murza yatsunta cikin junansu tace.

"Ko ban fad'a ba, hakan ba zai canja komai ba, karka manta fa Daddy har Kano yaje sunyi maganar da 'yanuwan hajiyarsa."

"Wallahi zai canja Fadeelah, zai canja abubuwa da yawa fiye da zatonki, so dan Allah ki fad'a min, ko kin manta irin rabuwar da muka yi ta k'arshe ne kafin barinki America?"

Wallahi bana sonka Al'ameen, kuma bana tunanin zan tab'a sonka!

Maganar baya ta haska tar cikin kanta, lallai d'an adam ba'a bakin komai yake ba kuma baki shi ke yanka wuya, da ace a lokacin da take fadin hakan za'a nuno mata sanda take kokarin yin abubuwan da zata burge shi da kuma yanzu da aka saka ranar aurensu, watakila zata hak'a k'asa ne ta shige don kunya. Shi yasa a kullum yanke hukunci cikin fushi baya tab'a zama alkhairi don ko ka yanke din, a haka hukuncin ubangiji zai zo danne naka, kak'i tsira da komai sai tarin kunya da kuma dana sani!

"Ki fad'a min." Taji muryasa tayi k'asa sosai kamar har sai da numfashinsa ma ya busa akan fatar kunnenta.

"Ina sonka Al'ameen, ina sonka saboda na yarda da kai kuma kaima ka yarda dani a lokacin da ko ni ban yarda da kaina ba, ka bani farin cikin da wani bai tab'a bani irinsa ba, saboda haka duk abinda zance ko na fad'a a baya, k'aryar zuciyata ce wannan."

A hankali Al'ameen ya lumshe idanunsa sannan babu gargada ya fadi kalaman dake azabtar da zuciyarsa a kullum.

"Ban san lokacin da na fara sonki ba Fadeela, watakila babu farko kuma babu k'arshe, kin riga kin zama wani b'agare na jikina kuma ina sonki ba tare da tsoron komai ba ko son samun wani abun, sai don kema ki soni kuma ki bani damar da zamu k'are rayuwarmu tare har abada."

Ta koma da baya ta jingina da allon gadon da take zaune sannan murmushi ya sake subucewa a kumatunta.

"Na baka wannan damar Al'ameen, ka riga ka sameta sai dai fatan Allah ya sada mu da alkhairin dake cikinta."

Bata ko jira ya amsa 'Amin' din ba ta katse kiran da sauri sannan ta janyo filon gefenta, ta rungume shi sannan ta cusa kanta cikinsa dad'i na nukurkusar zuciyarta!

Al'ameen ya sauke wayar daga kunnensa a hankali, tunani biyu na ratsa shi, Farko dad'in kasancewar ya shawo kan Fadeela a yanzu kuma komai zai tafi tsakaninsu. Na biyu ruftawar da zuciyarsa tayi ta bar wani tangamemen rami game da k'aryar da yayi mata, k'aryar da ya san duk daren dad'ewa zata zo ta fahimta, watakila ma ba sai an kai ga daren dad'ewar ba gaskiya zata baiyana kanta.

Amma ya zaiyi ne in ba haka ba? Bari zaiyi komai ya sake cakud'e masa irin farko? Damarsa ta biyu da ya samu ya kankaro da kyar ta sake subuce masa?

Ya mik'e daga zaunen da yake kan kujerar karatu ta cikin d'akinsa ya fad'a toilet. Tun bayan dawowarsa daga Nigeria, har yanzu ba'a d'ora shi kan wani sabon case ba saboda haka yake hutunsa yadda yaga dama, baya ma shiga ma'aikatar tasu da wuri.

Bayan ya fito ne ya shirya cikin wata riga mai dogon hannu kalar ruwan toka da wando bak'i, ya dora wata katuwar jacket akai kalar maroon saboda sanyi da ake surawa cikin garin a lokacin sannan ya sunke kafafunsa cikin safa mai kauri itama.

Al'ameen mai kyau ne, Fadeelah tasha fada... Irin samarin nan ne da ko daga nesa ka hango su cikin tarin mutane zaka ji zuciyarka ta tsaya akansu su kad'ai! Ita kanta mahaifiyarsa babban alfaharinta game dashi na kyawunsa ne. Saboda haka sai ya k'ara haskawa cikin kalar kayan, ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ebi wayoyinsa ya fita zuwa falo don samin abinda zai ci. Allah ya sani yayi kewar girkin Mami da Fadeela kamar me!

"A'a ga Ango fa ya fara kyallinsa tun yanzu."

Muryar wata daga cikin 'yanuwan Mami ta fad'a a sanda ya sanyo k'afa daga corridor zuwa cikin falon.

Zuciyarsa ta sake ruftawa cikin raminta sanda ya d'aga ido ya kalle su, 'yanuwa Mamin tasa ne da yawa a falon sannan ga kaya ma birjik ana ta hayaniya... Hayaniyar shirye-shiye... Shirye-shiryen aurensa da Hamida... Hamida dai 'yar kawar Mami... Mami dake tsakiyar falon a zaune fuskarta cike da farin ciki... Farin cikin ganin komai na tafiyar mata daidai ba tare da ta san me suka yi ba... Abinda suka yi shi da mahaifinsa!

Na zuwa neman Auren Fadeelah har Nigeria da sanya ranar bikinsu kafin ma nata data dad'e tana tanadinsa!

●﹏●

Ga dai Adam a garin Abuja.

Ga Fadeelah a garin Abuja.

Sannan ga mutanen Ikara har biyu, Sa'id da Sadiya mai aikatau a garin Abuja.

Sannan kuma ga shirye-shiryen biki shima a garin Abuja.

Can k'asar turawa kuma ga Al'ameen tsumu-tsumu cikin k'arya da ya rufewa Fadeelah da kuma mahaifiyarsa dake shirin yi masa aure!

Toh me kuke tunani zai zo a gaba?😁

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

*22*

(☆_☆)

BAYAN WATA GUDA

Rayuwa ta cigaba da gangarawa a kowanne b'angare na duniya, abubuwa na faruwa wasu kuma na shud'ewa, mutuwa, haihuwa, arziki, talauci, mulki, nasara, shirye-shirye, cikin wad'annan abubuwan babu d'aya da lokaci ya tsaida su.

A cikin haka ne kuma shirye-shirye da lokacin da su Daddy suka tsayar na auren Fadeelah da Al'ameen ke gabatowa, saboda haka sai ya zama kusan dukkan hidima irinta bikin Aseeya ta dawo kan Aunty Hadiza da kuma Mami wadanda suka tsaya akan abun, banda su ma Fadeelah ta lura kowa nata 'yan shirye shiryensa, babu irin su Zahra dake ta tanadin kaya set-set wanda zasu shiga su fita su kuma gwangwanje kamar yadda suke fad'i.

Sannan su Farouk da Usman ma na shirin had'a Cocktail su da abokanansu a cewarsu Aseeyah bata barsu sunyi komai da bikinta ba, ga Hajiya Amarya ma data ce zata karrama mai sunanta tayi yininta guda a gida, kowa dai nata 'yan shirye-shiryensa banda ita... Ita d'in da take ginshik'i kuma Amaryar bikin.

A kullum ta tashi ta kalli hasken safiya, sai ta tambayi kanta wace irin rayuwa take yi ne? Ita ko a labari bata tab'a jin mutum mai cakud'addiyar k'addara irin tata ba. Misali game da ciwonta, a da bata tab'a barin kwakwalwarta ta yarda cewa ciwonta nakasa ne ba balle har ta nuna raunin da wasu zasu tausaya mata, amma a yanzu hannu biyu tasa ta karb'i cewa kwakwalwarta ba daidai take da ta sauran mutane ba, ita d'in mai lalura ce da abinda ya raba ta da MAHAUKACI kad'an ne.

Saboda in ba rashin hankalin ba ta rasa abinda tunaninta ke janta akansa yanzu, ita fa ta damu da Al'ameen d'in nan har ta bashi hanyar daya sake neman aurenta a karo na biyu, amma a yanzu duk sanda ta gama waya dashi, sai komai ya tsaya mata cak! Ta kasa farin ciki, ta kasa sakewa kuma ta kasa karb'ar al'amarin hannu biyu duk da irin kulawar da yake nuna mata. Mami tace wai hakan ba wani abu bane, wai duk macen da za'ayi bikinta haka take ji, wai shi auren wani abu ne mai girma dake canja rayuwar d'iya mace.

Amma wallahi ita abinda take ji a ranta gani take yafi k'arfin taraddadin aure, ji take kamar mutuwarta ce ke shirin k'arasowa, kamar a kowanne motsawar lokaci zata iya bud'e ido taga mala'ikan d'aukan rai a gabanta ko kuma taji nauyin k'asar kabari akanta.

Bayan haka kuma ga wani azababben k'ulafacin son 'yanuwanta daya fara damunta, wad'annan dai 'yanuwan nata da bata iya tuna ko fuska d'aya a cikinsu, saboda da ace ana samun d'an adam d'in da yake zuwa babu dangi a duniya, da tuni ta dad'e da saka kanta cikin wannan layin.

Amma sanin cewa dole tana dasu d'in ne yake sawa in ta waiga taga Mami nata shirye-shiryen bikin, sai ta hango lokacin na Aseeyah da gabad'ayansu Mamin harda mahaifiyarta ake ta wannan hidimar, amma ita yanzu inda za'a d'auke harkar mutuntaka da kuma kyautatawa babu d'aya a cikinsu da zai mata wannan wahalar.

Da a cikin DANGINTA take fa? Tare da iyayenta wad'anda suka haife ta, ta san ko babu kyautatawar ita hakk'i ce akansu da dole ne su sauke, suna ma tunawa da ita a yanzu? Ko suna ma da rai tukunna? Tunda kafin zamanta ya koma wajen Hajiyar Daddy a wancan lokacin anyi cigiya kamar wanda ya yar da kwabonsa na k'arshe a duniya amma babu wanda yazo yace shi d'anuwanta ne, hakan ne yasa a baya ta cire tunaninsu a ranta ta rungumi rayuwar su Daddy kawai, amma me yasa komai ke shirin dawowa sabo a yanzu? Da irin wannan abun da take ji me ya raba kwakwalwarta da matakin hauka ?

"Kara ta sosai mana a wuyan na gani in ta zauna, kin san ba mai saukowa bace."

Mami ta fad'a tana kallon Fadeelan dake zaune akan stool na gaban mudubi tana rik'e da d'aya daga cikin sark'okin da suka baje akan gadon d'akin, wata 'yar k'aramar riga ce a jikinta dake nuna bata dad'e daga tashi daga bacci ba amma su Mami har sunje siyayya sun dawo.

"Wai tsoron sarkar kike ji ne?" Fatima dake ta fito da wasu daga kwalayensu ta fad'a tana kallon fuskarta ta cikin mudubin.

"Naji kamar tana da nauyi ne." Muryarta ta amsa a hankali.

"To mik'o ta nan tunda kika ce nauyi Deelah na san ba sakawa zaki yi ba."

Ta juyo a hankali ta mik'a mata idonta na kallon sauran kwalayen sark'okin. A satin daya wuce ne Al'ameen ya aikowa Mami da zunzurutun kud'in da bata san wane adadi na miloyoyi suka tsaya a kid'in Nigeria ba da cewar ayi mata siyayyar kaya (lefe kenan) da kuma wani sh'ani na bikin.

Bata san me yasa ba amma haka kurum jikinta yake bata cewa bikin nan ba daidai yake da kowanne ba, akwai wani abu tsakanin Al'ameen da Mami da suke b'oye mata, sai dai bata da hujja ko shaidar menene shi.

"A cikin atamfofin nan akwai wata mai lemon gree da milk ko?" Mami ta tambaya tana kallon Fatima.

"Anya kuwa kamar lemon green da brown ne sai wata mai lemon green kawai koh?"

"A'a gaskiya ni naga mai irin wannan kalar, yaya Hadiza ce fa ta d'auko ta ma ina tunawa."

"Toh bari in duba." Cewar Fatima ta mik'e ta tafi can d'akin Mamin inda kayan suke.

A lokacin ne kuma Fadeelah taga dama ce gareta da zata fad'awa Mamin abinda ke cin ranta.

"Mami."

Ta kira sunan da dukkan dauriyar da take da ita a lokacin.

"Al'ameen har yanzu bai fadi inda zan zauna ba, kunyi maganar dashi ne?"

Zata iya rantsewa wani abu ya gifta cikin idon Mamin kafin ta girgiza kanta tace.

"Bamu yi ba deelah, amma me yasa zaki damu kanki tunda dai ai in an d'aura auren ba zai barki anan ba."

"Mami karatuna nake tunani, so nake in san matsayarsa tun tanzu kafin a koma hutun."

"Fadeelah karatu ba matsala bane, duk inda ya d'auke ki ya kaiki a duniya zaki cigaba da yinsa, nasha gaya miki Al'ameen bashi da matsala ko kad'an, wallahi duk abinda kike so shi zai yi."

"To Mami Aunty Miryaamah fa? Ni fa har yanzu banji kuna zancenta ba, banji ana cewa suma suna nasu shirin ba, sannan shima banda lokacin da yace min

Please Login or Register in order to submit comment