Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sa'id sun sha d'imbin godiya a wannan ranar da addu'a da kuma fatan alkhairi, kowa ya yarda cewa zuwansa cikinsu alkhairi ne mai d'imbin yawa, don duk yawan jama'ar babban gida babu wanda za'a d'ebe da zai ce bai tab'a samun alkhairinsa ba, shi kad'ai ne amma kuma yana da hannaye da yawa, yasha d'imbin godiyar da in har tana yawa a wannan ranar za'ace tayi, don tun yana iya amsawa har ya zama sai murmushi kawai yake yi.

Fadeelah na iya hango yadda yake lumshe idanunsa daga inda take zaune rik'e da Muhammad da yayi bacci a kafad'unta, yadda kyallin idanunsa ke tafiya tare da murmushin.

A cikin 'yan watannin nan rayuwarta ta canja, ta samu wani irin farin ciki da bata san dad'insa ba sai a yanzu, Adam ya cike rayuwarta da soyayyarsa, ya nuna mata kala-kala na ma'anar kulawa ta yadda ko a murmushinsa idanunsa na gaya mata cewa yana son ta, tana ganin wata gaskiya a cikinsu kullum dake sawa ta yarda cewa ba zai tab'a rabuwa da ita ba, idan kuwa ya rik'e hannunta tana k'ara yarda cewa tana cikin kulawarsa ne kuma har abada ba zai tab'a bari ta fad'i ba.

Zata yini tana jin maganganun mutane amma duk lokacin da take tare dashi, kewayenta nutsewa yake cikin wani ruwa mai zurfi, bata tab'a iya fahimtar komai sai shi kawai da kuma al'amarinsa, wanda itama a yanzu ta koya don bata shakkar nuna masa nata b'angaren k'aunar, rayuwarsu tana tafiya daidai manne da wani malik'i daya had'e zuciyoyinsu guri d'aya.

Zuwa can yamma bayan komai ya natsa an kammala taron ne ta samu wayar Mami.

"Mami tun safe nake ta kira shiru, d'azu kuma hayaniya ta hana ni sake gwadawa."

"Yi hakuri Deelah, naje makarantarsu Iman ne zancen lesson d'inta, ya kowa da kowa? Munyi waya ai da Aunty Saratu jiya take ce min bakya gida lokacin."

"Ina jin sanda muka je cikin gari ne, dama tambayarki zanyi kayan k'amshin na nawa za'a siyo?"

"Na 3 thousand ma ya isa, sannan idan zaki iya a taho min da daddawa ta 1 thousand."

Sarai ta san me Mamin take nufi da idan zata iya, tana nufin idan warinta ba zai takura ta ba kenan, don Mami ce ta farko duk duniya data fara ganewa tana da ciki kafin ma ita kanta, kuma tun daga wannan lokacin kulawar da take mata ta ninku akan da.

"Insha Allah Mami za'a taho da ita. Yauwa dan Allah ki gayawa Zahra tayi wa mai k'unshin magana idan mun dawo jibi zamu je."

"Au yanzu baku hak'ura da wannan k'unshin ba, tunda baku samu ba har anyi taron an gama ba sai ku bari sai wani lokaci ba."

Sai ta girgiza kai kamar Mamin na kallonta tace.

"A'a Mami dan Allah, zamu je dai."

A yadda Adam ya kwallafa ransa tayi k'unshin nan ta yaya zata iya ce masa ta fasa? Watakila Mami ta fahimci zancen nata ne shi yasa suka yi sallama akan hakan ba tare da ta sake cewa komai ba, kuma kafin Mamin ta kashe, tana iya jiyo muryar Iman wadda ke kwalo mata ihun 'Aunt deelah yaushe zaki dawo?'_ Taso sunyi magana don alkawari Iman d'in a mata cewa zata zo tayi mata weekend in ta dawo, karo na farko kenan da Mami zata barta tazo sa kwana don koyaushe sai dai suzo suyi mata yini kawai su tafi.

Da daddare bayan komai ya tsagaita ne text d'in Adam ya shigo wayarta.

"Babeğim (Turkish; My baby) zan iya ganinki dan Allah?"

Dama kiranshi take jira don ta san halinsa sarai ba lallai ne yaci abinci a wannan hayaniyar ba, don haka ta d'auki ledar takeaway-takeway na abincin data tanadar masa tace da Mairo wadda ke k'okarin yiwa su Afrah wankan kwanciya tana zuwa, so samu ne ace itama tayi wankan kafin ta fita, amma ta san Adam ba hakurin jiranta zai yi ba.

Babu mutane sosai a k'ofar gidan amma duk da haka motar tasa na daga can gaba hanyar wata kwana da mutane basu fiye zama ba. Sai da ta k'arasa sannan ta fahimci motar Sa'id ce bak'a wuluk mai d'auke da tinted glass a jikin tagogin, tayi kokarin bud'e k'ofar gaba amma taji ta a rufe gam saboda haka ta dawo ta bud'e baya.

Sanyin AC da kuma tsadadden k'amshin nan nasa suka fara yi mata maraba kafin siffarsa, da alama daga can guest inn d'in da suka sauka yake don yayi wanka ya canja manyan kayan daya yini dasu zuwa wani 3-quater wando sak irin socin sojoji da kuma bakar T-shirt mai laushi data kama jikinsa, Ya Allah! Ita kam tun kayan rana ne a jikinta.

Kansa a jingine yake saman kujerar ya rufe idanunsa, kuma bai bud'e su ba har bayan shigowarta, a haka ya amsa sallamar da tayi.

A lokaci guda ta fahimci akwai abinda ke damunsa, ba dai gajiya bace don ta san wannan d'an taron kawai ba zai jijjiga shi ba.

"Daga wani waje kake ne?" Ta tambaya jin bashi da alamun magana. Yayi murmushin jin muryarta kafin yace.

"Eh na koma masauki nayi wanka ne."

"Kaci abinci?"

Sai ya d'ago da kansa a lokacin ya kalle ta, amma bayan kyakkkwar fuskar ta har yanzu akwai wani jan haske da yake gani a gefen idonsa. Irin hasken da tunda yake sau d'aya ya tab'a ganinsa a rayuwarsa, watanni biyu da suka wuce, lokacin da sab'anin farko ya shiga tsakaninsa da Fadeelah.

Ranar da yana duba hotunan wayarta ya tsinci wani hoton ta tare da Al'ameen, sun d'auka ne a cikin wani library cikin sigar selfie, dukkaninsu na dariya yayin da Fadeelah ke kallon camerar amma shi ya juya yana kallonta, yana kallonta... Irin kallon da shima yake mata in yan tare da ita, a wannan ranar kwanan wayar nan ya kare don fasa ta yayi har batirinta.

Tun da yake a rayuwarsa bai taba tunanin Al'ameen d'in Fadeelah shine Al'ameen d'in da shima ya sani a America ba, duk da ba wani sabo suka yi ba amma zai iya cewa sun had'u kusan sau biyar ta hanya abokinsa Kamal daya taimaka masa a baya game da binciken asalinsa, a wancan lokacin zuciyarsa ta kwanta da Al'ameen ne kasancewarsa sabon lauya mai kokarin cimma burinsa, amma a yanzu hoton fuskarsa a k'one yake zuwa idanunsa a kullum.

Kuskuren da zuciyarsa tayi a wancan lokacin shine na kasa rik'e fushinsa har ya fasa wayarta kuma ya bari zargi ya shiga zuciyarsa na tunanin ko har yanzu Al'ameen bai gama barin zuciyarta ba, don a yadda hoton nan ya fassara masa komai, gani yake mu'amarlarsu tayi k'arfin da ba lallai har a lokacin nasa kokarin yayi nasarar cire shi a zuciyarta ba, ko don kyawun fuskarsa ma.

Don haka karo na farko aka samu sab'ani tsakaninsu har na tsawon kwanaki biyu, Fadeelah tayi fushin data daina yi masa murmushi balle dariya, bata fasa yin dukkan wata d'awainiya ta gidan ba amma komai yayi duhu a idanunsa, gidan ya zama babu haske balle nutsuwa, da kansa ya gano kuskurensa ya koma ya nemi yafiyarta. Shin irin wannan kuskuren yake son sake aikatawa a yanzu? Dukkanin wata kafa ta kwakwalwarsa ta shiga kokarin hana shi abinda yake shirin tambaya amma ya kasa danne zuciyarsa.

"Leelah waye Abdoul?"

Yana kallon yadda fuskarta ta canja a lokaci guda zuwa tunani, goshinta ta takure waje d'aya.

"Abdoul? Waye shi?" Ta maido masa da tambayar.

Ya d'aga kafad'unsa kad'an.

"Mun had'u dashi ne a masallacin da la'asar bayan mun gaisa sai naji yana gayawa abokansa a bayana cewa da shine zai aure ki."

Ta d'an yi shiru kamar mai nazari, bayan wucewar wasu 'yan sakanni kuma ga mamakinsa kawai sai ta kyalkyale da dariya tana kallonsa.

"Seriously Wolfie? Shine zaka cinye ni d'anya?"

Bai san lokacin da yayi murmushi ba shima jin sunan data kira shi, zai iya rantsewa ba'a kwana biyu a duniyar nan Fadeelah bata canja masa suna ba, suna nan da yawa... Big guy, boobear, bunches, captain, cowboy, charmy, heartthrob, hoshi, habibi, Oppa, Ironman, Jaan, Ma cherie.... Ba zai iya lissafo su ba.

"Allah ya huci zuciyarka tough guy, ni wallahi yanzu in zaka shak'e ni ko kammaninsa ba zan iya ganewa ba, amma dai na tuna shi abokin yaya Salisu ne daya tab'a min magana sau d'aya, amma kafin ma a samu damar da zan bashi amsa k'addara ta d'auke ni zuwa hanyar da zan had'u da kai, so cool off kaci abincinka ka daina tunanin...."

Kafin ta k'arasa abinda zata fad'a, Adam ya jawo ta cikin jikinsa ya zagaye ta da dukan hannayensa, ya riga ya samu amsar sa kuma baya son shaid'an ya sake samun tasiri akansa, a hankali idanunsa ya sauka kan bakinta. "I miss you." Ya fad'a muryarsa k'asa-k'asa.

Nan take jinin jikinta ya sake d'aukar d'umi yana neman tafasa don jikinta da zuciyarta sunyi kewarsa kamar babu gobe, kwanansu biyu kenan da zuwa Ikara ita da Mairo, tun ranar Alhamis suka taho shi kuma sai jiya juma'a ya k'araso tare dasu Sa'id, kuma tun a jiyan waya kawai suka yi don shirye-shirye sun sha kan kowannensu, a yau kuma wayar ma bata samu ba sai hango shi kawai da ta dinga yi tare da mutane.

Ta d'ago da fuskarta kad'an yadda karan hancinsu ya had'u da juna sannan ta mik'a da hannayenta ta zagaye su a wuyansa. "I miss you too."

D'aya hannunsa ya lalubi cikin k'asan rigarta yace.

"Babyna fa?"

"Shima yayi missing d'inka like crazy."

Sai yayi wani murmushi a hankali, sautin ya fito daga can k'asan mak'oshinsa.

Fadeelah ta nutse cikin d'umin jikinsa wanda ke had'e da k'amshin sabulu da turare sannan a hankali ta rufe idanunta sanda ya sunkuyo da fuskarsa kan tata, wata wuta kamar ta lantarki ta harba tsakanin fuskarsa zuwa tata, lebbensa masu taushi da d'umi suka d'aga ta zuwa cikin gajimare.

Zuciyarta ta manta da komai ta biye masa na wani lokaci kafin kuma ta tuna inda suke, da sauri ta janye jikinta sannan ta matsa gefe.

"A mota muke fa." Tayi k'okarin tuna masa.

Sai ya jefa kansa jikin kujerar motar sannan ya zura hannu cikin gashinsa yana sauke numfashi yace.

"I'm sorry Babeğim, na manta ne." Muryarsa ta fito a shagale kamar mai jin bacci ko wanda ya tashi.

Murmushi mai taushi ya sub'uce a fuskarta sannan ta juya ta d'ebo kayan takeaway d'innan, tace.

"Bismillah, time to eat."

"Yes Babe." Ya fad'a sanda ya juyo gabad'aya saitin ta ya tankwashe k'afafunsa akan kujerar motar sannan ya sake jawota jikinsa.

Ta d'ora abincin akan cinyarta sannan ta shiga bashi a baki, yana rik'e da d'aya hannunta sannan a hankali kuma wannan lallausar muryar tasa tana mata mitar yadda yayi kewar girkinta.

Idanun Fadeelah suka ciko da wata irin kwallar farin ciki da kuma godiya ga Allah, 'yan shekaru da basu fi cikin hannu ba a baya, rayuwarta a hargitse take bata ma san wacece ita ba balle har tayi tunanin samun dad'in rayuwa haka, amma tun daga lokacin da ta fara sanin Adam a America, abubuwa suka fara bud'ewa d'aya bayan d'aya a rayuwarta.

A yau gata cikin jikinsa a matsayinsa na mijinta, gata d'auke da halittar dake shirin zama jininsu, gata a cikin garin da yake mahaifarta, cikin 'yanuwanta kuma cikin Babban gida a matsayin wani abu mai daraja.

Sai ta juya a hankali ta hango ginin k'ofar Babban gidan, kantangarsa mai tsayi na nan a tsaye kyam kamar wani gingimeman dutse, a lokaci d'aya idanunta ya dawo mata da wani zamani daban, sanda ta bud'e k'ofar wannan gidan ta fito, sanye da cukurkudadden hijabinta cikin duhun dare!

Sai kawai ta rufe idanunta a hankali kwallar dake cikinsu ta gangaro kan kumatunta.

Rayuwa.

Mece ce ita?

Tasha tambayar kanta hakan!

ALHAMDLILLAH.

KARSHE.

BAYAN NA MUTU.

©AYSHA SHAFI'EE

SHARHI

(☆_☆)

Bayan na mutu labari ne da jigonsa ya k'unshi muhimmancin dangi a rayuwar d'an Adam. Dangi wasu mutane ne da Allah ya halitta a rayuwar kowanne mutum, dangi sune ginshik'i kuma k'ashin bayan dake tafi da rayuwar duk wani mai rai.

Dangi sune mutanen da suka san ka tun lokacin da baka san kanka ba har zuwa mutuwarka, Dangi sune masu taimakonka, sune mutanen dake tare da kai a lokacin nasara da kuma fad'uwarka, sune mutanen dake k'aunarka a yadda kake ba tare da wani dalili ba, sune wad'anda ke d'orar da kai akan halayyar da zata maida kai cikakken mutum. Dangi sune mutanen dake iya fahimtar damuwarka ko baka furta ba.

Mutane da yawa zasu danganta rabi na wad'annan ma'anonin da wani zamani daya wuce ba wanda muke ciki ba, A yanzu mafi yawancin mutane zasu gaya maka ma'anar Dangi ne a matsayin K'ALUBALE kawai!

Idan muka dubi rayuwar BINTU, ita kanta zata iya bamu wannan fassarar... Amma rayuwar ADAM ta nuna mana akasin hakan, ta nuna mana cewa duk wani jin dad'in rayuwa da matsayin da mutum zai samu a duniyar nan zasu koma gefe d'aya ne su taru in har baya cikin DANGINSA, DANGI wani b'ari ne na jikin mutum ne da in har babu shi, dole ne girma da darajarsa ta ragu. Ina fatan Allah ya bamu damar rik'e zumunci a tsakanin DANGINMU ta yadda duk tsanani da k'alubalen hakan ba zai kawo rabuwar kai ba kamar yadda ya faru da al'ummar BABBAN GIDA.

Akwai mutane da yawa a duniyar nan irin ADAM da basu da masaniyar DANGINSU, wasu suna iya samun su wani kuma har ya koma ga Allah babu wanda zai iya nunawa a matsayin nasa, Ina fatan Allah ya sanya hak'uri da juriyar hakan a zukatansu ya kuma mayar musu da hakan a matsayi rahma a ranar gobe k'iyama.

Bayan Adam, rayuwar FADEELAH ma wani karatu ne mai zaman kansa, rayuwar hak'uri da juriya da kuma fuskantar k'alubale kala-kala, wanda duk daga k'arshe ke juyewa zuwa tarin alkhairi.

Ina fata Allah ya bamu irin hak'uri da juriyarta, ya kuma saka mana da fiye da alkhairin data samu, don babu wata nasara data wuce samun jin dad'in duniya da kuma na lahira.

Nagode da tarin hak'urinku da kuma lokacinku da kuka yi amfani dashi wajen karanta labarin nan. Ina fata kuma ku amfana da wani abu daga cikinsa.

MA'ANAR SUNAN LABARIN BAYAN NA MUTU.

Labarin ya fara ne ta cikin tunanin wata yarinya Bintu, wadda ke bamu labarin rayuwarta tare da kakarta bayan rasuwar iyayenta, bayan ta gudu daga gida ne tayi hatsari daga nan sai labarin ya cigaba ta b'angaren mai bayarwa ana nuna labarin Fadeelah.

A wannan hatsarin, kwakwalwar Bintu ta mutu, tunaninta ya shafe bata san wacece ita ba balle har ta cigaba da bamu labari, don haka duk wani abu daya faru bayan nan, Bintu na gaya mana cewa ne....

BAYAN NA MUTU...!

Signed.

Aysha Shafi'ee.
08067794315.































































An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment