Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin san ni aka nad'a caretaker."

Iman ta tab'e bakinta.

Dama ai in kina musu wannan iyayin naki dole ne a baki.

"Me kika ce?" Ta tambaya tana kallonta ta cikin mudubin.

"Cewa nayi ke ya kamata dama a bawa."

Sai tayi murmushi sannan ta cigaba da taje gashinta.

"Dama duk me suka sani sauran 'yan class d'in, ke dai bari ai za'ayi decoration d'in da ba'a taba yin irinsa ba a..."

Duk hirar da suke hankalin Fadeelah baya kansu, tunda ta idar da sallar la'asar ta nemi guri ta kwanta don ranar bata da lectures ko daya, sai dai baccin da take ganin kamar tana jinsa yak'i zuwa ko kad'an, saboda haka ta lalubo takardun lesson d'inta da Adam ta shiga bitar kowacce question d'aya data riga ta haddace ta.

A jikin wata tambaya guda d'aya idonta ya gano wasu kalmomi da suka sa kwakwalwarta tunani.

Da sauri ta mik'e zaune tana k'ara kallon rubutun kafin ta d'ago ta kalli Zahra.

"A ina mukullin store yake?"

"Yana jikin k'ofar d'azu na rufe." Ta bata amsa tana tand'e bakinta da take sawa janbaki.

"Yawwa Aunty deelah nima zan duba wani abu da nake tunanin na saka a cikin kayanki muje tare."

Iman ta fad'a sanda ta biyo bayanta ta nufi hanyar k'ofa.

Cikin k'aton kwalinta na store d'in tayi ta bincikawa har sai da ta d'auko tsohuwar jakarta ta makaranta da take amfani da ita a America. Hannunta na rawa ta zuge wani d'an k'aramin zip a gefe ta zaro wata siririyar takarda, takardar da tun daga ranar data ajiyeta bata k'ara tunawa da ita ba sai yau.

Ta warware ta da sauri sanda tsararren rubutun jiki kamar an buga shi ya baiyana.

Ya jikin naki?.

Aka rubuta daga tsakiyar paper sai daga can gefe kuma.

Mr. Hawkin's yana nemanki.

A hankali ta kara ta da rubutun Adam na paper lesson d'insu... kamar an tsaga kara, iri d'aya sak!

Kenan Adam ne ya rubuto mata paper a lokacin? a ranar data koma makaranta bayan rashin lafiyar da tayi? ya akayi ya san bata da lafiya? tun a lokacin ya san matsalarta kenan? Shi yasa ya tambayeta tun sanda zasu fara lesson d'in nan? shi yasa ya nemi jotarta don ya nuna mata ya san me take ciki?

Ta rufe idonta a hankali tana tunanin wane irin mutum ne shi daya iya mu'amala haka? waye zaiyi ta binta a hakali ta laluma haka?

"Aunty Deelah Id card d'in waye wannan?"

Muryar Iman ta fad'a a kusa da ita, ta bud'e idonta a hankali sannan ta karbi id card d'in da take nuno mata.

WASHINGTON STATE BAR
1111 East Main street, Suite 819
VA 2356-4318

Barrister Adam Steve
Status: Active
ID Number: 54217
Issued: 01/08

A gefen duk wannan bayanin, Hoton Adam ne cikin wata bak'ar suit, gashinsa da kullum yake a barbaje yanzu a kwance yake luf! cikin wani hadadden style, sannan yana da wani kwantaccen saje daya had'u ya zagaye da gashin baki wanda ya k'arawa kamaninsa mutukar kyau ba kamar yadda ta sanshi a makaranta ba, abu d'aya daya tabbatar mata da cewar Adam d'in data sani ne a hoton shine wad'annan lumsassun idanun nasa!

Bakinta ya furta sunan da kwakwalwarta ta kasa fahimta cike da rud'ani.

BARRISTER ADAM STEVE?!

Adam lauya ne?!

***
_!!!_

_Labarin dai yana ta warware wa!_

_Muna ta gangarawa!_

_Mun kusa kaiwa inda komai zai kwance gabad'aya!_😁


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

14

(☆_☆)

Ayyiryiryiriiiiii! Ayyiryiryiriiiiii!

Wata dattijuwar mata rangad'a zankad'ed'iyar gud'ar data cika kaftanin d'akin, duk kuwa da d'imbin hayaniyar matan da suka cika falon suna ta d'aga wasu tsantsara-tsantsaran kayayyaki daga cikin jerin akwatunan dake gabansu.

"Wallahi kaya sunyi mutuk'ar kyau masha Allah, Allah ya sanya alkhari nawa suka bayar kuma kud'in d'inki da cefanen?"

Wata k'awar Haj. Halima matar Baba habibu ta tambaye ta sanda suke duba akwatin kayan shafe-shafe.

"Dubu d'ari cif! ai wallahi munga kokarinsu, don da farko dubu talatin muka tanada tukuici sai da aka cika ashirin."

"Sun cancanta gaskiya, a sabon ma'aikaci ai yaron yayi bajinta ba kad'an ba, akwati goma fa."

"Goma kam! ni yanzu jigilar na Saifudden kawai nake hangowa, ba had'a lefen ba taronsa kamar wani bikin ne."

"Haba hajiya ku da abin gabad'aya na cikin gida ne, ku zaku had'a abinku fa ku karb'i kayanku."

"Ke dai bari, abinda kake rainawa shi yake zuwa ya baka tsoro."

Daga gefensu haj. Saddika matar Baba sani tace.

"Ai mu ya kamata mu fad'i haka ma ba ke ba, tunda a lokacin komawa gefe zaki yi ki bar mana hidimar."

Da dariyarta ta amsa mata.

"Ke da har yanzu baki fad'i matsayarki ba, ni dai ina gaya miki ne gwara ki zab'a tun yanzu kar abu yazo ya cakud'e miki ki rasa inda zaki yi.."

"Babu zancen cakud'ewa don zan iya, kowanne b'angare ina nan, ni ta amarya ce kuma ta ango."

Suka yi dariya gabad'aya ta cikin surutun dake tashi a d'akin, ko'ina ka duba mutane ne dai ke ta d'aga kaya daga wannan akwati zuwa wannan, yayin da daga can kitchen su Mami ne da Aunty Hadiza, matar kawu Isma'il da kuma wasu daga cikin 'yan uwansu makusanta ke hidimar raba irin snacks d'in da aka sallami dangin ango dasu ga mutanena cikin gidan.

A d'aki na k'arashe daga benen gidan, Rahma ta bud'e k'ofar band'akin da k'arfinta.

"Wallahi na dad'e banga 'yar iskar amarya irinki ba, kina nan kina waya ana k'asa ana bidirin kawo kayanki."

Aseeyah ta d'ago daga wayar da take yi ta kalle ta.

"Zuwa zanyi in taya su ko me?"

"Ai abinda ya rage baki yi ba kenan, ko ni duk rashin kunyata barin gidan zanyi wallahi."

"To sai gani ni kuma na dame ki a rashin kunyar."

"Ai baki burge ni ba, da kin sani da suka shigo zuwa zaki yi ki gaishe su, ki tsugunna kiyi godiya in sun tashi tafiya kuma ki taka musu zuwa mota."

Fadeelah dake gefe cikin kwalliyarta kamar kowa a gidan, tayi murmushi kawai tana jinsu hannunta na kan wayarta da take browsing wani assignment na makaranta.

"Kin san Allah in su Mama suka san kina gidan nan sai ranki ya b'aci."

"Toh ta yaya zasu sani, sai dai in ke ko munafakan yaran nan ne zasu gaya musu..."

Ai kuwa kafin ta rufe baki, su Sahla Sameera da Zahra suka banko cikin d'akin, da sauri Rahma ta rufe k'ofar, a yanayin kwalliyarsu wani zai zata ranar ake d'aurin auren.

"Mutane 'yan naci ne wallahi, sun k'i su matsa ma muga komai." cewar Sahla.

"Ni wallahi 'yan k'auyen nan da Hajiya ta gaiyato tsoro nake kar a samu masu sata, dan yaya Rahma baki ga yadda suke kallon kayan nan ba wallahi."

"Kowanne fa sai sun kalle shi sau uku-uku."

Zahra ta karb'ewa Sameerah.

"Dama a yanzu manya ya kamata su fara gani, ku da za'a bar abin a gidan ma ai har sai kun gaji da gani in dai kaya ne."

"Mun d'ebi na d'iba ba kuma." inji Sameerah.

"Eh dole, tunda ku za'a aura me zai hana ku d'iba.

Fatima ta shigo d'akin a lokacin hannunta rik'e da tray d'in snacks.

"Kun san me yake faruwa kuwa? Mami Hauwa ce fa tazo yanzun nan."

"Wacce?"

Rahma da Sameera suka had'a baki wajen tambaya.

"Wacce kuka sani in ba ta Kaduna ba? wallahi yanzu direba ya sauke ta gata can a falo ana gaisawa."

"Kai! wallahi Aseeya kin ciri tuta, kawo lefe ba biki ba matar nan ta tako k'afa tun daga kaduna tazo? fito-fito kiji sabon labari."

Fadeelah ta amsa sanda ta nufi inda Fatima ta dire tray d'in nan, ta d'auki samosa guda d'aya sanda su Sameera suka nufi k'ofar band'akin suna fad'in.

"Dama wai tana nan... Yaya Aseeya Mami cewa tayi fa kin fita... in gaya miki akwati set goma... kinga wani lace a cikin kayan kuwa..."

Fatima tace.

"Ku kwantar da hankalinku mana, in dai kaya ne sai kun ture, wani ma na hanya."

"Kayan wa kuma?"

Fadeelah ta tambaya.

"Wai baki san yaya Saifudden ne zai auri Rahma ba? har fa ana shirin kawo kud'i."

Mamaki ya kama Fadeelah, ashe shi yasa kwanaki da zasu je gidan Baba habibun tak'i binsu, da kuma sanda ta ganshi a kitchen ya tambaye ta Rahman, ita fa har yanzu bata iya maida hankali kan sha'aninsu, sai dai ta saurari iya abinda ta tsinta kawai don Mami ma yanzu ta rage hira da ita samun su Aunty Hadiza da Aunty iyami a kusa.

Ta jinjina kai a hankali, mamaki take yadda hali biyu mabanbanta suka had'u, shi miskili mara magana Rahma kuma wayayyiyar mace mai surutu da rawar kai, lallai wani had'in sai Allah.

"Kema Deelah kamata yayi kawai a had'a ki da Rahman ki fito mana da ango musha biki... ko ranar nan wani abokin Yaya Yusuf sai da yayi min zancenki."

Cak! tunaninta ya tsaya, don yau ne rana ta farko da wani mahaluki ya d'auko kalmar aure ya danganta ta da ita, saboda damuwar kowa a kanta na rashin lafiyarta ne da son jawo ta cikinsu, hatta Mami kuwa... tunaninta akanta kullum na samun lafiyarta ne kawai, sai taji kamar ta zama mutum kamar kowa ne da Fatiman ta fad'i hakan.

Duk da cewa kuwa har ga Allah bata son d'orar da rayuwarta a haka, bata son saka kanta a wata sabuwar rayuwa da guntulallen asalinta iya na yanzu, tafi son ace itama ta koma cikin 'yanuwanta kamar yadda su Mami suke yanzu, tana son samun irin wannan farin cikin da annushuwar da take gani a idanunsu duk sanda suka je gidan Hajiya Amarya.

Ta tauna samosan hannunta a hankali sanda hayaniyar gidan ta k'ara rud'ewa sakamakon wata dank'areriyar sark'ar gold da aka gano a cikin d'an kit d'in kayan lefen.

Sai ta mik'e ta koma kusa da jakarta, ta zaro Id card d'in Adam, ta kalli wad'annan lumsassun idanun nasa da suke kama da yana d'aukanta a hoto ne duk sanda ya kalleta, da murmushinsa dake maqalewa a gefen lebb'ensa d'aya, da kwantaccen gashinsa daya taho har ya rufe gefen idonsa, taji kamar ta mik'a hannu ta ture gashin ta kalli idon nasa sosai, idon tayi kewa tsawon shekara guda da d'oriya.

Don a yanzu ta riga ta gama lissafawa cewa kewar Adam take, shi yasa ta kasa cire shi daga ranta tsawon wannan lokacin, shi yasa komai k'ank'antar abu yake tuna mata dashi, shi yasa a ranar data rasa magazine d'in nan ranta ya sosu. Kuma ba irin binciken da bata yi a internet ba, don ganin cewa Id card d'in nan ko na bogi ne amma license number jiki da komai baiyi kama da wanda aka kirkira ba, hasalima sunan ma'aikatar dake jiki akwai bayaninta a shafin yanar gizo, abu d'aya da bata samu ba shine sunayen ma'aikatansu don ta tabbatar in harda gaske Adam lauya ne.

Saboda har yanzu kwakwalwarta bata yarda ba, a tunaninta me zai kawo shi makarantarsu tsawon wannan lokacin in har yana da aikin yi, me zaisa ma ya b'ata lokacinsa akanta? Ta duba har cikin social media amma bata ci karo da suma d'aya ma mai shigen nasa ba.

Ita dai a yanzu bata san wane hali zuciyarta take ba, domin bayan tunanin Adam akwai al'amarin Al'ameen cakud'e fal a ranta, har ga Allah a yanzu bata jin dad'in yanayin mu'amalarsu, ta san abinda tayi masa shi ya jawo komai, amma hakan ya zama dolenta ne a lokacin, don ko ita kanta bata gama sanin kanta ba, ba zai yiwu ta biye masa su fara alak'ar da zata ruguza komai ciki kuwa har da zumuncinsu Mami ba.

Sai dai duk da haka, taso ace ak'alla yanzu bayan wucewar komai da shekara guda ko gaisuwa ce na shiga tsakaninsu amma tun zuwansa gidan bata ma ganinsa sosai, kuma a iya d'an lokacin da take ganinsa yana tare da Mami ne ko Daddy suna magana don haka babu wata kofa da ko gaisawar zata shigo.

Wani lokacin sai taji kamar ta tambayi Mami game dashi amma tsoron kar ta d'ago wani abun daga b'angarenta yasa take jan bakinta tayi shiru, don ba wai shi take kewa ba, A'ah wannan lokacin data saba dashi, hirarsu, sunayen da yake lak'aba mata, dariyar da yake yawan saka ta... ko kuma a dunk'ule ace yadda mu'amalarsu take ma gabadaya.

Ta yarda cewa a yanzu matsalarta guda biyu ce, Al'ameen da Adam.

Zahiri da bad'ini!

***

"Ina kewarka sosai, yaushe zaka dawo?"

Muryar Hamida ta fad'a ta cikin wayar dake kare a kunnensa.

"Ban sani ba gaskiya amma dai mun kusa gamawa."

Al'ameen ya amsa sanda yake jera files d'in daya gama aiki dasu a ranar cikin wata chess drawer ta office d'in.

Hamida 'yar k'awar Maminsa ce wadda take son cusa kanta cikin rayuwarsa tare da taimakon mahaifiyarta da kuma ita Mamin, suna fatan zasu iya sawa ya fad'a cikin tarkonta da wannan kissa da hilar tata, shima kuma fatansa kenan... so yake ta d'auke hankalin nasa, ta janye shi ya fad'a cikin duniyarta, sai dai hakan ya gagara duk kuwa irin kokarinsa da nata.

"Na maka text da safe baka duba bane?"

"Ban fiye duba sak'onnin wayata ba shi yasa ban gani ba, amma tunda kin turo d'in ya shigo kenan, zan duba."

Lokaci ya riga ya shud'e da sanda yake damuwa da shigowar sak'o wayarsa.

"Ya wuce ma ai, nayi maka Barka da safiya ne kawai. Yanzu ka bani labarin Nigeria, na san kayi bak'i ko? don ance ranarsu tana da zafi."

Ya rufe idonsa a hankali, hirar ce baya buk'ata a lokacin.

"Kin san me? zan kira ki anjima na koma gida,yanzu ina wani aiki ne."

"Sure King, ayi aiki lafiya sai na jika."

Har ga Allah yasha mamakin tsananin hakuri irin na Hamida, don a yadda mu'amalarsu take yaci ace tun a baya ta sallami kanta, amma irin hak'urin da take yi dashi yasa shima yake d'an bata girma, matsalarsa daya da ita shine duk abinda ya faru tsakaninsu, hira wannan, to kalma bayan kalma kuwa sai ta gayawa mahaifiyarsa.

Ya bar cikin temporary office d'in da aka basu anan cikin garin Abuja da misalin k'arfe uku da'yan mintuna, sun riga sun kusa kammala komai na aikin daya kawo su saboda haka abinda suke yi yanzu bashi da yawa, ba kamar kwanaki ba da sai su kai har goman dare a waje. Da fitarsa d'an tsohon maigadin wajen ya taso da 'yar torchlight d'insa yana fad'in.

"Yallab'ai an fito, sannu da aiki... Allah ya kaika gida lafiya, Allah ya huta gajiya."

Bai fiye fahimtar zancensa gabad'aya ba amma idonsa ya kai kan torchlight d'in hannunsa, mamaki ya kamashi na tunanin me yake da fitila da rana tsaka haka, ba tare da ya tambaye shi ba ya kalli k'ofar d'akin daya taso, a d'an wani lungu yake saboda haka cikin d'akin dind'im yake duk da hasken ranar daya wadata ko'ina, ba haske ba taga sannan k'ofar ma ta karye sai kara ta da akayi. Cikin gurb'atacciyar hausarsa mai had'e da larabci da turanci yace.

"Babu haske a d'akin ka?"

Baba tsoho ya kalli k'ofar d'akin nasa sannan yace.

"Yallab'ai da yake ginin ba fuskar rana yake kallo ba kuma tun watan jiya da kwan ya mutu ne ban sake samun faragar ajiye kud'insa ba wallahi, amma ga wannan ai ina siyan batir duk sati."

Ya fad'a yana kad'a torchlight d'insa. Al'ameen bai gane duka zancen ba ya dai fahimci cewar babu d'in ne saboda haka ba tare da wani tunani ba ya zura hannunsa a aljihu ya zaro kusan rabin kud'in dake ciki ya dank'a masa.

Mamaki ya daskarar da Baba tsoho a tsaye a wajen, ya kalli kud'in sannan ya d'ago yace.

"Yallab'ai wani abu za'a siyo?"

"A'ah ka sayi fitila."

A hankali ya saki baki kawai yana kallonsa, shi mamakinsa da farko ai na me za'a siyo masa da yawa haka ne, amma ace wai shi aka bawa duk wannan kud'in? Bakinsa ya k'ulle, ya gagara cewa komai har sanda ya Al'ameen d'in ya shiga motarsa ya ja ya bar gurin, sai yabi fitilar motar da kallon mamaki kawai... ya san cewa ya bashi kud'in nan ne don yayi gyaran d'akin da zai kwana, amma ya ayyana a ransa cewa daga ranar ya bar gadi, zai je ya nemi wata sana'ar da zata rik'e shi da iyalansa fiye da sana'ar gadi.

Al'ameen ya isa gida wajen k'arfe hud'u saboda yawan motocin da kowa ke haramar komawa gida, a falon boys quarters d'in da yake zaune ya tarar da Faruk da Usman da wasu abokansu suna game d'in kwallon k'afa irin na jikin Television, suka gaisa har yana tsokanarsu cewa shima gashi nan zuwa a matsa masa wuri, kafin ya nufi cikin d'akin da yake kwana, baiyi wata-wata ba kuwa ya fad'a wanka don sauke gajiyarsa.

A lokacin da ruwan daya kunna mai d'umi daga shower yake zuba a kansa ne zuciyarsa ta shiga laluben fuskarta, fuskar Fadeelah da kullum yake son nesanta kansa daga ita, don ko giftawarta ya gani cikin gidan, sai yaji kamar dauriyar daya k'ulle zuciyarsa da ita tana barazanar kwancewa, musamnan in ta kalle shi da wad'annan idanun nata masu shek'i sai yaji kamar kar ya janye nasa har tsawon rayuwarsa, idan kuwa ya hango murmushinta daga nesa tare dasu Zahra sai yaji kamar an gaya masa ne cewa za'a amsa dukkan burikansa na duniya.

Ya sunkuya a hankali ruwan ya koma zuba a kansa ta baya.. yana nutsewa cikin gashinsa mai santsi daya manne kamar leda, ya san cewa abinda tayi masa a baya shine sanadin da yasa ya dake zuciyarsa ya karb'i ra'ayin mahaifiyarsa akanta, amma a yanzu ya fahimci nasa laifin a ciki shima. Laifin gaya mata cewa yana sonta ba tare da wani tsari ba, kuma a d'an lokacin da daga shi har ita suka fara fahimtar junansu, ya fara saka mata fatan samun mai tallafa mata tunda ya gaya mata cewa zai taimaketa ta duk hanyar da zai iya, sai yazo kuma ya lalata komai a dare d'aya... ya dagargaza zuciyar data fara yarda dashi a d'an k'ank'anin lokaci, ta yaya ma zata karbi tayinsa a wancan karon?

A lokacin daya fito daga wankan yake shiryawa, d'aya wayarsa mai rik'e da personal layin daya siya zuwansa Nigeria ta shigo ruri akan teburin durowar dake gefen gado, baya son d'aukar waya a lokacin amma ya san cewa kiran ba zai wuce daga Kamaal ba ko mahaifiyarsa saboda haka ya matsa ya d'auka, Kamal d'in ne kuwa ya shiga taya shi murnar cewa an turo da bayanan aikinsu kuma yaga irin namiji k'ok'arin da yayi kan yadda suka binciko kamfanin k'arya suke akan duk wata shaidar matsala da suka bayar.

Murmushi ya sub'uce a gefen kumatunsa jin cewa labarin aikinsa har ya k'arasa can.

"Ka bari kawai sai mun had'u zaka ji komai ma, jiya na nemeka amma baka d'aga waya ba."

"Yes, naje ganin wani case da Adam yake fighting ne akan wani tsohon mai kud'i da aka kashe."

Adam! mutumin da yake kwaikwayo kamar me, yake son samun irin nasarori da cigabansa, yake fatan sunansa ya shahara kamar nasa a cikin turawa, duk da cewa kuwa shi Corporate lawyer ne Adam d'in kuma Criminal defense lawyer!

"Anyi nisa a case d'in?"

"Zama na gaba za'a yanke hukunci, amma kar ka damu Adam ne fa... zai yi nasara akan case d'in kamar kowanne."

Kwarai kuwa! ya amsa a ransa don kowa ya kwana da sanin cewa a shekara guda data wuce, da mutuk'ar wuya ne Adam ya karb'i case baiyi nasara akansa ba.

Suka d'an tab'a hira kafin suyi sallama, daga nan ya lalubo number wayar Mahaifinsa da zai koma gida can Washington a yau bayan samun ritayarsa da yayi, amma har ta gama rurinta sau biyu ta tsinke ba'a d'aga ba, ya ajiye wayar sannan ya shirya cikin wata doguwar jallabiya kalar ruwan k'asa, kamar kullum ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ebi duka wayoyinsa ya nufi cikin gidan, inda k'aida ne a kullum abincin Mami da Fadeelah na nan yana jiransa.

"Ya Al'ameen zaka taya ni rubuta presentation d'ina na ranar abokai? (Freindship day.)"

Iman ta tare shi tun daga k'ofar Falon hannunta rik'e da takarda da kuma 'yan fensiranta harda masu kala. Ya d'an sunkuyo daidai kanta sannan yace.

"Kwarai kuwa Imani, me zai hana in..."

Bata ko jira ya k'arasa ba ta daka tsalle sannan a lokaci d'aya ta tarkata masa takardar da fensiran cikin hannunsa.

"Nagode sosai Ya Al'ameen, bari inje in bawa Trivo (Magen gidan) abinci."

Ya kalli paper da ba ko d'igo a ciki, da sauri yace.

"Na d'auka kince taya ki zanyi, ai baki fara rubuta komai a jiki ba."

"Ai abinda nake nufi kenan, ka taya ni rubutawa ka rubuta min duka."

Bata ko jira amsarsa ba ta juya da sauri tayi hanyar kicin. Ya d'an dafe kansa kad'an, daya sani bai amsa ba, don shi ya manta duk irin wad'annan abubuwan, ta yaya zai fara rubuta wani jawabi akan abokai yanzu? In dai ba shari'a zai rattaba tsakaninsu ba.

Ya d'ago da idonsa ya kalli Zahra da take tsakiyar couch d'in falon tana kallon wani indian series yace.

"Ke 'yar Aljana me yasa baki rubuta mata ba kina zaune kina kallo."

Ta cuno bakinta kad'an don bata son irin sunayen da yake saka mata, sannan ta d'ago masa wasu zungura-zunguran takardu guda biyu.

"Guda uku na rubatawa yarinyar nan, amma d'ayan ma yaga shi tayi tace wai abinda na fad'a yayi iyayi da yawa ciki, dama Aunty Fadeelah ce ke rubuta mata, yau tunda bata da lafiya kowa ya shiga uku a gidan nan daga naka wajen su Farouk zata tafi, watakila ma har ta tsallaka mak'ota."

Yadda take maganar hausarta na fita fil-fil, ba wanda zai yarda tayi zaman k'asar turai kuma a shekara guda baya bata iya hausar sosai ba, yawan zama dasu Sameera da kuma sawa kanta kar ta banbanta dasu ya taimaka mata sosai.

"Al'ameen ka dawo?"

Muryar Mami ta katse kokarin tambayar me ya sami Fadeela da yake shirin yi. Ya juyo ya kalle ta, cikin kayanta masu kyau tsaf take, sai dai da alamun damuwa kad'an a fuskarta.

"Eh na dawo Mami, na same ku lafiya?"

"Alhmdlilah, dama yanzu nake son kiran wani daga cikinku ya dawo ko kai ko Daddy."

"Lafiya dai? wani abu ya faru ne?"

Muryarsa mai taushi ta tambaya cike da damuwa saboda a yanayin muryarta kawai ya fahimci akwai wani abun.

"Fadeelah ce bata da lafiya tun safe, ko makaranta bata je ba, nayi-nayi da ita kuma muje asibiti amma tak'i yarda."

"Ya salam!" ya furta a hankali yana rik'e da hannun kujerar gefensa.

"Ya jikin nata yanzu?"

"Ba kamar da safe ba dai, amma har yanzu tana kwance."

Ya kalli k'ofar data fito daga cikinta, hanyar wani d'an k'aramin falo ne mai d'auke da kujeru uku a ciki, da alama Fadeelan tana ciki ne, don haka ba tare da yayi tunani sau biyu ba bakinsa ya furta.

"Bari in shiga in dubata."

Ya ture duk wani gargad'i da jar fitilar dake kad'awa akansa ya nufi cikin falon, ya san d'akin yana da d'an duhu kad'an amma fitilar a kunne take saboda haka a take ya hango ta akan kujera ta duk'unk'une cikin wani lallausan bargo kalar ruwan hoda, zuciyarsa ta narke gabad'aya sanda ya kalli fuskarta, idanunta a k'ank'ance suke alamun rashin bacci, da alama kuma bata yi tsammanin shigowar kowa ba, saboda tana ganinsa tayi motsi da sauri alamun gyara kwanciyarta.

"I'm sorry na tashe ki ne?"

Sai ta girgiza kanta a hankali tana k'ara gyara kwanciyar, ya k'araso ya zauna a hannun kujerar gefe.

"Mami tace baki da lafiya, ya jikin naki?"

Yaji alamun taja hanci kad'an kafin kai tsaye tace.

"Naji sauk'i."

"Kin sha magani?"

Idonsa na kanta saboda haka yaga lokacin da ta girgiza kanta a hankali.

"Saboda me?"

"Saboda naji sauk'i."

"Ta yaya kika sa.."

"Naji sauk'i Al'ameen ba sai ka tabbatar ba."

Ya Allah! ashe bata manta sunansa ba?

Ya ayyana hakan a ransa yana kallon fuskarta ta cikin hasken d'akin, ya san me take nufi sarai, don tayi maganar ne da muryar wannan Fadeelan daya sani a baya, mai k'arfin hali da dauriyar b'oye rauninta a gaban mutane.

Sai ya karkato daga kujerar da yake kai, ya k'ara fuskantar ta.

"In haka ne me yasa kike kwance tun safe?"

"Bacci ne bai gama saki na ba."

"Shi yasa idanunki suka canja?"

Sai ta lumshe idanun nata can k'asa har ya daina ganin kwayarsu sannan ta amsa.

"Har shi d'inma."

"Fadeelah rayuwa bata da adalci, ba komai d'an adam yake samun yadda yake so a cikinta ba, Allah yayi miki Rahmomin da mutane da yawa har da wanda suka fi ki a wani abin ke kwad'ayin samu, na fahimci uzirinki idan kin b'oye ciwonki a idanun jama'a, amma babu hujjar da zata sa ke da kanki ki dinga cutar kanki."

A hankali ta ware gashin idon nata ta kalle shi, Ashe har yanzu da guntuwar damuwar Al'ameen akanta? tayi zaton yayi cilli da komai na rayuwarta ne kamar yadda ya daina kulata.

Maganarsa kuma ta sata gajeren tunani, kusan abinda ya fad'a haka ne, duk da nakasarta tana da d'imbin rahamomin da yatsu baza su iya k'irga su ba, Allah ya sanyata cikin karamtacciyar zuri'ar da suka karb'eta cikinsu da

Please Login or Register in order to submit comment