Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta amince da zancen auren baya tab'a son in d'auko masa zancenta, dan Allah Mami in da wani abin ki fad'a min."

Ka san abinda mutum yake ji a lokacin da yake son nusar da k'aramin yaron da mahaifiyarsa ta mutu cewa ba zata tab'a dawowa ba? Sak haka Mami taji sanda Fadeeelah ta fad'i hakan, ta yaya zata gaya mata cewa Aunty Miryamah bata san da zancen auren nan ba kwata-kwata? Ta yaya zata gaya mata cewa Al'ammen ya roke ta ne kamar hauka kan ta taya shi boye wannan sirrin don ya sami Fadeelah a rayuwarsa? Ta yaya zata gaya mata cewa suna hasashen Aunty Miryaman zata saduda ne in taga an kai k'arshen komai?

"Mami, Mami, Umma ce ke kiranki."

Rahma ta katse komai sanda ta shigo cikin d'akin rike da wayar Mami da mahaifiyarta Aunty Hadiza ke kira, bata jira konai ba kuwa ta kara mata a kunne.

"Yaya wayar na can falo ne wallahi..." Cewar Mami cikin wayar.

"Mrs. Skeleton ya akayi ne?" Rahma ta fada sanda ta juyo ta kalle ta.

Wani murmushi ya subuce a kumatun Fadeelah, tace.

"Nice kwarangwal d'in?"

"To ba gashi nan ba..." Ta amsa tana zama a gefen gadon.

"Duk kin bi kin fita haiyacinki tun yanzu."

Ko waye a takalmina zai fita haiyacinsa Rahma.

Ta amsa hakan a cikin tanta ba tare da ta furta ba.

"Kinga deelah..." Cewar Rahman tana kamo hannunta.

"Ki kwantar da hankalinki fa, Aseeyah tace min ba wani abu wallahi mijin ma watarana in kika tashi ji zaki yi haushinsa kike ji, sannan ko ni da zan auri miskilin yaya Saifudeen ban d'aga hankalina kamar ke da kullum Al'ameen d'in nan ke tare dake yana nuna miki kulawa ba."

A daidai sanda Rahman ta fadi haka, wayarta ta zabi lokacin ta shiga ruri na alamar shigowar kira, idonta ya kai kan sunan.

Al'ameen ne.

Ta juya ta kalli Rahma dake kallonta sannan Mami dake magana tana ta had'a sarkokin nan, da Fatima ta shigo a lokacin tana nuna wa Mami atamfar data d'auko, sai ta dawo da idonta kan wayar.

A wannan lokacin ta yarda cewa ba zancen karatunta ba, ba zancen wajen zama ba, ko zancen Aunty Miryaamah mahaifiyarsa bai isa ya canja k'addararta da Al'ameen ba, sai dai wani abin kuma daban, wani abu da zai shallake tunaninta!

***

RANAR D'AYA GA FARKON WATA.

Harabar gidan Mami na d'auke da mutane tsilla-tsilla yayin da wajen yake yab'e da wani tsantsareren decoration mai d'aukan hankali, mazaunin kujeru kad'ai da zagayen teburinsu abin kallon ne, don tun kafin wajen ya fara cika da mutane akwai robobin lemu na ruwa da kuma kayan marmari fal wanda suka fi k'arfin duk mutanen da zasu zauna a kowanne tebur.

Idan ka kalli mazaunin amarya kuwa, ba zaka tab'a son d'auke idonka da wuri ba don adon al'adar gargajiyar dake jikinsa abin sha'awa da zai ka shagala wajen kallinsa, ga tsofaffi ma har hakan ya tuna musu da lokacin k'uruciyarsu a doron duniya. Daga saman rumfar kuma wani rubutu ne mai kyalli dake haska harafan...

'Barka da zuwa Kamu da Walimar Fadeelah Ahmad Malik!'

A harabar wajen ba mutane sosai sai tsilla-tsilla, amma cikin gidan dank'am yake da tarin jama'ar dake ta fafutukar shiryawa wasu kuma na k'arasa packaging kayan souvenirs d'in da za'a raba, ga 'yan aiki birjik har da na gidan Hajiya Amarya da Aunty hadiza ta tattaro sai faman aikin wanke-wanke suke da kuma d'ora abinci bayan wanda akayi ordering da za'a raba a wajen.

Mami kam! bama ka ganin inda take, don minti d'aya ne ka ganta minti d'aya kuma duk gidan sai a nemeta a rasa. Usman na ta bin Fatima yana rokon wai sun gaiyato abokansu ta taimaka in abincin yazo akai musu can boys quaters d'in Faruk, su Zahra kuwa d'akinsu guda suka cika da k'awayensu da suka fara zuwa, in banda kwalliya, hira da kuma waya da samarin da aka had'a agenda dasu ba abinda ke wanzuwa a d'akin. Fadeelah bata da dangi amma wallahi a ranar nan ba mai gane hakan, don kowa daga b'angarensa yayo gayya daidai gwargwado ta mutanensa.

Sai dai duk wannan bidirin da akeyi a cikin gidan, ita Amaryar na can band'akin dake cikin d'akin Daddy inda shi kad'ai ne ba mutane ta k'ulle kanta, ta rufe 'basin' na zama sannan ta hau ta dunk'ule jikinta akai, idonta a tsaye suke kyam! kan wayarta tana kallon zunzurutun adadin kud'in da suka shigo account d'inta na banki daga account d'in Mami.

"Fadeelah kud'in kayan d'aki ne wannan, in kinje duk abinda yayi miki ki siya kiyi amfani dashi, tunda kinga baza'a d'ebi kaya har can ba."

CAN! can yana nufin k'asar America, inda dai ta baro take murnar ta dawo tushe ta inda rayuwarta zata gyaru ta inganta watakila ma har ta samu waraka daga ciwonta, ashe wannan burin zance ne a iska kawai! Tarihi ne zai sake maimaita kansa kamar yadda ya faru ga Mami, da aure ya d'auke ta cak! ya tsame ta daga cikin 'yanuwa zuwa wata nahiya ta duniya. A baya gani take Mami tayi mutuk'ar k'ok'ari data iya zaman can d'in, sai yanzu ta gane ashe ba kokari tayi ba, abu ne da ba yadda zaka yi dashi....

Ba zaka iya sa k'afa ka ture ba ko kasa hannu ka tsige shi, manne yake cikin k'addararka da ba mai iya canja hakan sai ubangiji!

Allah ya sani ta riga ta gama fahimta a yanzu auren ne kwata-kwata bata so, shi yasa take jin kamar zata mutu, amma kuma tana son Al'ameen, irin son da take ganin tsananin kirkinsa da kuma tsananin kyawunsa, bayan haka bata jin komai a ranta game dashi amma ta yarda cewa iya wad'annan abubuwan kad'ai zasu saka taji dad'in zama dashi, sai dai inda ta baro zata koma fa? Wajen da a yanzu bata da kowa sai nasa DANGIN, wanda yake k'unshe da mahaifiyarsa da har yanzu bata san matsayinta a wajenta ba. Ya dai ce mata yau zasu taho, amma bata san 'SU' wa da wa ya k'unsa ba, abinda tafi rik'ewa kawai shine zasu zo su tafi da ita, CAN inda sabon DANGIN data samu a yanzu ma zata yi musu nisa.

Tasa bayan hannunta ta share kwalla mai d'umin data taru a idonta, ita haka ubangiji ya kaddaro mata rayuwarta, daga nan sai can, daga wuya sai dad'i daga dad'in kuma a koma wuyar, fatanta d'aya a yanzu shine ta samu farin ciki tare da Al'ameen, farin cikin da zai d'ebe mata wasu abubuwan.

K'ofar band'akin ta shiga bugawa da karfi sannan muryar Aunty Hadiza maman Rahma ta biyo baya.

"Fadeelah bud'e k'ofar mana, me kike yi? Ga mutane har sun fara zuwa baki shirya ba."

Sai ta kashe wayarta a hankali sannan ta d'ora saman sink, bata da yadda zata yi fa, bata da zab'i babu ma mai bata zab'in... Komai tafiya yake kawai kamar yadda ubangiji ya tsara, ita nata kallo ne kawai!

A hankali ta bud'e k'ofar.

"Ga mai kwalliya nan tun d'azu muke neman..."

Sai maganarta ta katse ganin hawaye shab'e-shab'e a fuskarta.

"Haba 'yanmatan Mami, kukan ne tun safe har yanzu? Girma ne fa ya hau kanki meye abin masa kuka?"

Sai ta jawota ta rungume ta a faffad'an jikinta, kamar dama hakan Fadeelah ke jira sai ta dunk'ule kanta cikin kafad'unta ta shiga rera shi a hankali, irin mai zurfin nan dake tasowa tun daga k'asan zuciya.

"Haka kowa ke ji Fadeelah, ba ke kadai ce ba kowacce mace irin wannan zafin rabuwar sai ya hau kanta, amma komai yana wucewa ne a d'an kankanin lokaci, da kanki watarana in kinzo ma zaki tashi ki tafi gidanki..."

Maganganu masu taushi da kwantar da hankali Aunty Hadiza tayi ta rad'a mata a kunne har da kyar ta samu ta shawo kanta, ta tsaida kukan nata da kyar sauran ya koma k'asan zuciyarta ya shiga jiran wani lokacin. Sannan ta saka ta ta koma band'akin ta wanke fuskarta kafin ta zauna gaban mai kwalliyar dake jiranta da k'aton akwatinta, ba yadda ta iya haka ta d'anyi mata murmushi sannan ta fuskance ta, sai daga baya kuma tayi tunanin meye amfanin ma murmushin bayan ta ganta ta gama kuka yanzu.

"Bari inje in turo miki Fatima da kayan da zaki saka."

Aunty Hadiza ta fad'a sannan ta bud'e k'ofar d'akin ta fita, da kyar ta samu Fatiman a cikin taron jama'ar gidan ta bata muk'ullin wardrobe din Mami da cewar taje ta d'auko kayan Fadeelah ta kai mata. Daga nan ta nufi masaukin k'awayenta da suka fara taruwa a lokacin, ta tarar wata Nafisa daga cikin k'awayen nata tana ta bada labarin sabuwar 'yar aikin da tayi da bata gajiya kamar inji.

"Ke nifa yanzu tiles d'in barandar wajen gidana ma fa sai ki kalli fuskarki kamar mudubi saboda tsabar yawan mopping."

Wata Jamila tace.

"Dan Allah daga ina take nima insa a samo min 'yar garinsu?"

"Daga Ikara take wai, sunanta Sadiya kuma bazawara ce wallahi ba yarinya ba."

"Ina ne Ikara?"

Aunty Hadiza ta tambaya tana zama cikinsu.

"Can wajen hanyar Zariya ne inji ta."

Daidai lokacin da Sadiyan ta k'araso rik'e da d'an matar, ta gaishe su d'aya bayan d'aya sannan ta karb'i jakar kayansa ta shiga canja masa rigar daya b'ata.

Basu cigaba da hirarta ba sai suka canja wata, amma kasancewar ita Sadiyan taji su tun farko, sai tayi kwafa a hankali sannan ta maimaita abinda ta kudirtawa ranta tun farkon zuwanta gidan.

Kaina nake gyarawa waje baiwar Allah, zamanki a gidan nan ya kusa k'arewa!

Fatima ta k'araso a daidai lokacin nan d'auke da manyan ledoji na kayan Fadeelah, ta mik'awa Aunty Hadiza muk'ullin sannan tace.

"Aunty ba mai taya ni dan Allah, wallahi kayan da nauyi."

Caraf! Nafisa ta kalli 'yar aikinta Sadiya tace.

"Bar saka masa kayan nan ki mik'o min shi, taya ta ku kai kayan nan sai ki dawo."

Sadiya ta mik'e da sauri ta mik'e ta mik'a mata yaron da jakar sannan ta kinkimi duka ledojin hannun Fatima tabi bayanta dasu zuwa d'akin da ake shirya Amarya Fadeelah!

●﹏●

😊

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

23

(☆_☆)

RANAR DAYA GA FARKON WATA.

ASOKORO, ABUJA.

Ta juya miyar dake zab'alb'ala kan gas d'in gabanta a hankali yayin da gwalantun d'anta Muhammad dake zaune a island na kitchen d'in ya cika wajen, d'aure yake cikin kujerarsa ta yara amma yana ta mik'a hannu yana k'okarin tab'o plate d'in yayarsa Afra dake zaune a gefensa tana ta kanannad'e indomie d'inta cikin fork maimakon ci.

"Mommy Muhd zai zubar min."

Yarinyar ta fad'a cikin shagwab'a tana ture yala-yalan kitson kalabarta daga fuska, sai dai mahaifiyar tasu bata ko juyo ba balle ta nuna alamun taji me tace, cigaba da juya miyarta kawai take yi a hankali idanunta na tsaye kyam akan taswirar siffarta dake nunawa a jikin murfin gas d'in.

Watak'ila ruhinta yayi nisa ya bar doron duniya ma a lokacin, don tunani take yi mai zurfi, irin tunanin da tsawon shekaru bata tab'a yin irinsa ba, bai tab'a zuwa kanta ba don a kwakwalwarta kaf babu muhallin irinsa, Tun bayan lokacin da idanunta suka gano mata k'anwarta Bintu a wajen bikin nan, bata sake tunawa da ita ba sai a yanzu, a yanzun da take jin ba iya tunanin k'anwar tata ba ma, abubuwa ne da yawa ke ta taruwa suna kwancewa a cikin kanta, kamar a da an k'ulle su ne can wani wuri guda, sai yanzu suka sami 'yancinsu na fitowa.

A hankali taji hannu ya ziro ta gefen k'ugunta ya kashe wutar gas d'in dake shirin k'one miyar, sannan ya zuro kansa cikin wuyanta ya rad'a a cikin kunnenta.

"Tunanin me kike yi?"

Mairo ta rufe idanunta a hankali sannan ta kwance hannayensa daya nad'e a jikinta ta juyo ta kalle shi, ta kalli fuskar da tun a kwanaki biyu ta canja mata zuwa wani iri duk da cewa kammaninsa basu canja ba don shine dai mijinta, wannan Sadiq d'in da take so fiye da komai a rayuwarta, wanda har ta baro gida saboda shi, d'an kyakkyawan bafulatanin nan da tun gani na farko da tayi masa a bakin rijiyar da suke zuwa d'ebo ruwa taji zuciyarta ta fad'a duniyarsa. To me yasa a yanzu take ganinsa wani iri?

"Me ya same ki?" Ya tambaya hankalinsa kwance yana maida wani dogon gashinta daya fito cikin hular kanta.

Ta san yana yin hakan ne saboda miyar bayanta dake bud'e, yana son gashi amma baya sonsa a harkar abinci. Sai ta zame hannayenta daga cikin nasa daya rik'e sannan ta kalle shi sosai.

"Bibty akwai maganar da nake son na fad'a maka wadda ni kaina ban tabbatar da ita ba."

Watakila ba'a idanunta kad'ai ba, har a wajen wasu ma fuskarsa zata nuna cewa hankalinsa a kwance yake, amma daga shi sai ubangijinsa suka san irin rud'ani da kuma tashin hankalin da yake ciki tun dawowarsa daga k'auyen 'Talfa'.

Ya san cewa a baya ya shigo da Maryam cikin rayuwarsa ne saboda burinsa da yake son cimma, amma tun kafin ma ya kammala samun burin nasa kyautatawarta a gareshi tasa ya kamu da son ta, bayan samun burin nasa kuma sai ya yarda cewa rayuwarsa baza ta tab'a tafiya daidai ba in har babu ita, ta riga ta zama kamar wani b'angare na jikinsa da ba zai iya yankewa ya yar ba, saboda haka sai ya ajiye komai shima ya biyewa wannan hasashen da shi da ita suka d'ora iyayensa cewa bata da DANGI, sai iya wata mata kad'ai daya kaita wajenta bayan sun gudo daga garinsu, inda yasa iyayensa suka nema masa aurenta a gurinta.

Hankalinsa a kwance yake da hakan tsawon shekaru, amma daga lokacin da tazo haihuwar d'ansu na biyu tasha wata irin wahala kamar zata mutu, daga wannan lokacin nadamar abinda yayi mata ta fara kama shi, don kusan kwananta biyu cikin matsananciyar nak'uda kafin ta iya haihuwa saboda likitocin sunce gwara ta haihu da kanta, a sannan ne kuma daya duba yaga wata yayar mahaifiyarsa ce kad'ai tare da ita a asibitin sai tausayinta ya kamashi, ya ayyano da mutuwa zata yi kenan haka zata tafi babu kowa nata a kusa, saboda yasa an hana ta tuna duk wasu DANGINTA a duniya.

Nadamar abinda yayi ta fara kama shi har zuwa ranar da suka tsaya wajen bikin nan yaga alamun kwalla a idanunta, tunaninsa ya bashi cewa watakila taga wani ne data sani a baya kuma ta kasa gaya masa saboda ya riga yasa an k'ulle kwakwalwarta daga son tuna 'yanuwanta.

Amma a yanzu ya shiryawa komai, ya shirya masa da dukkan dauriya da kuma k'arfin hali, zai amsa tambayoyinta ya kuma karb'i laifinsa hannu biyu... abu d'aya da har yanzu bai shirya masa ba shine rabuwarsa da ita.

"Daddyn Afra ranar da muka tsaya a wajen bikin nan bayan mun dawo daga park..."

"Mommy Muhd ya zubar."

Muryar Afra ta katse ta sanda k'arar plate d'in abincinta ya tarwatse a k'asa.

Shikenan! Sadiq ya ayyana a ransa sanda ta janye idanunta daga nasa ta tafi wajen yaran, daga yanzu komai zai fara, zai fara girbar k'addarar abinda ya shuka. Yana kallonta ta kwashe abincin ta zuba a shara sannan ta bud'e k'asan fridge inda ba sanyi sosai ta d'auko madarar kwali, ta zubawa Afra a kofi sannan ta zubawa Muhd a feedersa mai straw, ta bawa kowannensu sannan ta sake dawowa ta d'ora idanunta akan nasa.

"Bibty ka tuna ranar? Har na juya ka tambayeni me nake kallo?"

Bata bari ya amsa ba ta cigaba.

"Wata na gani kamar k'anwata Bintu ta can Ikara kuma tun daga lokacin sai na kasa mantawa da ita, kullum sai na tuna fuskarta don na tabbata ita d'in na gani."

Tirk'ashi! Gabad'aya abin yazo kenan, wato k'anwarta ma ta gani ba wai wani na nesa ba, k'anwarta da ya san ita kad'ai take da ita a duniya, to amma ta yaya hakan ta kasance? Aikatau ne ya kawo ta Abuja ko me? Don zai iya tuna yarinyar k'arama ce sosai a wancan lokacin da yake zuwa Ikara, don samun Maryam kawai!

"Ka tuna ta?" Muryarta ta katse tunaninsa, sai ya kamo duka hannayenta biyu ya matso da ita gabansa sosai.

"Ta yaya zan manta 'yaruwarki Sweetum, na gane Bintu sosai."

Ta shiga motsi da yatsun nata cikin hannunsa a hankali.

"Ban san ina zamu same ta yanzu ba, amma da gaske ina son ganinta Daddy, jikina yana bani cewa bayan duk wad'annan shekarun 'yanuwana zasu manta da komai."

Da gaske ne yaje Talfa, da gaske ne ya tone kabarin nan kuma da gaske ne ya k'ona layar mutum-mutumin data zama silar arzikinsa, in ba haka ba tsawon shekarun nan yaushe Maryam ta tab'a zancen 'yanuwanta, yaushe ma ta iya tuna su balle har tayi tunanin komawarta wajensu? Sai dai godiyarsa d'aya a lokacin shine bata yi tunanin ya akayi ta manta su a baya ba, ya akayi shima bai tab'a yi mata zancensu ba sannan ya akayi ma har ta iya gudowa daga gare su... Don wad'annan tambayoyin su zasu canja akalar rayuwarsa.

"Kin shirya a yanzu kina son komawa wajensu kenan?"

Yayi tambayar ne da ma'ana biyu, farko in har da gaske ta shirya tunkarar k'alubalen da daga ita har shi zasu fuskanta, sannan na biyu don ya maida abun kamar itace a baya bata neme su ba.

Ta d'aga kanta a hankali.

"Na shirya Daddy, ina ganin lokaci yayi da zan neme su... Ko don su Afra."

Ya gyad'a kansa a hankali shima sannan ya fad'i abinda ya shirya masa tun farkon bayaninta.

"Kije ki shirya yanzu mu fara da neman Bintunki Maryam."

Idanunta suka zare a lokaci guda.

"Yanzu? Yau?"

"Ko zamu bari sai gobe?"

Sai ta saki hannunsa sannan ta shiga girgiza kai.

"Da gaske kake?"

"Da gaske nake, kije ki shirya."

"To amma ina zamu ganta? ranar ma.."

"Ssshhh..."

Ya matso a lokaci d'aya ya d'ora yatsansa akan lebb'enta.

"Kar kice komai, kije ki shirya mu fara gwadawa."

Mamaki ya kusa had'iye ta inda take a tsaye, anya daidai komai yake faruwa kuwa? Ta yaya zai yarda da ita a lokaci d'aya haka? Ta bud'e baki kamar zata sake yin magana kuma sai ta fasa ta d'auki Muhammad da sauri tayi hanyar d'aki da niyyar shiryawar tun kafin ma ya canja shawara. Ya bi bayanta da kallo tare da godewa Allah data fasa maganar data yi niyya, don ya san in har godiya zata yi masa, daga baya zata zo tayi dana sanin hakan fiye da tunaninta.

****

"Alhaji kace ranar shida ga wata ko?"

Habibu, mai kula da harkar wajen biki ya fad'a yana fitowa daga wani d'aki mai cike da takardu a cikin office d'insa.

"Kwarai ranar shida ga wata ne."

Sadiq ya amsa daga kan kujerar tsallaken teburin da yake zaune.

"To ai ba'a ma tafi da nisa ba, shi yasa da nayi tunanin sai mun duba sannan ka dawo, amma wata biyu ai record d'in yana kusa."

Ya karaso ya zauna akan kujerarsa sannan ya d'ora yatsansa d'aya kan wani layi a cikin littafin.

"Gashi nan bikin wata Aseeyah akayi daga yamma har zuwa Magariba."

"Washe gari fa?" Ya tambaya kai tsaye.

"Bikin wata Aminah Salihu Mu'azzam."

Kwarai! Itace 'yar shugabansu a office da aka gaiyace shi suka zo bayan fitar da suka yi a ranar akace ba ranar ne bikin ba.

"Ranar bikin Aseeyan, an samu wad'anda suke zuwa neman bikin Amina?"

Habibu ya danyi murmushi sannan yace.

"Yallab'ai ai ni harkata ta masu zuwa neman hayar wajen ne da kuma biya kud'i, wannan sai dai a kira securities din wajen su zasu san wannan."

"A'a barshi kawai, yanzu zaka iya bani address din wadanda suka nemi hayar wajen?"

"Na bikin Aminan?" Habibu ya tambaya.

"A'a na ita Aseeya d'in."

"Eh to yallab'ai, ai ka san irin wannan abin ne da d'an matsala, kazo ka bada bayanin mutum kuma wani abu ya faru ace..."

"Kaga..." Sadiq ya tsaida shi.

"Babu wani abu da zai faru, bayani kawai nake nema daga wajensu ba wani abu ba, ko kaga nayi maka kama da wanda zai aikata wani abu mara kyau ne?"

Fatan Sadiq a lokacin, Habibu ya amsa da 'Eh' don da gaske ne shi mai aikata abu mara kyau d'in ne, banbancin kawai, a bad'ini ba zahiri ba.

"Shikenan to, Allah ya kare bari na samo takarda na rubata maka address d'in matar da ta karbi hayar wajen."

Sanda Sadiq ya tashi fita daga office d'in, ya ajiye masa rafa na takardun 'yan d'ari biyu sababbi.

"Bibty address d'in waye wannan?"

Mairo ta tambaya sanda ya fita ya same ta tsaye a jikin motar daya barta a cikinta, da alama ta kasa zaman ciki ne saboda d'okin dawowarsa.

"Mutanen dacsuka karbi hayar wajen."

Sai ta d'ago ta kalle shi da wani sabon mamakin a fuskarta.

"Me address d'in zaiyi mana?"

Bai amsa ba Muhd ya fara kuka daga cikin motar saboda haka ta bud'e ta d'auko shi, a take shima ya matso ya karb'e shi ya shiga jijijiga shi.

"Ina jin kwarewa yayi, shi yasa bana son tsotson hannunsa, ta fada tana shafa bayansa sanda yake jijjiga shin.

Daga can gefensu wata budurwa na zaune a cikin mota tana jiran yayanta ta hango su, a lokaci d'aya taji zuciyarta ta murmushe da sha'awarsu, taji dama itace Mairo da wannan kyakkyawan mijin da kuma kyawawan yaran don tana iya hango Afra dake dukan glass na windon motar alamun tana son fitowa, gani take Mairo ta gama samun sa'ar duniya, bata san cewa itace take cikin sa'a ba da take cikin DANGINTA, da mahaifiyarta bata mutu da bak'in cikinta ba, da bata kasance matar mutum dake rayuwa cikin haramun ba, da kuma bata had'a zuri'a da wanda yake cutar da ita tsawon lokaci ba.

D'an Adam baya taba kallon wani yace 'yayi sa'a', kowanne mutum da irin damuwarsa a duniya.

****

🎶

K'amshi k'amshi yana tashi... 'Yan mata zamu je kamun amarya!



🎵

Wak'ar dake ta tashi a wajen kenan yayin da mutane suka dabaibaye rumfar zaman amarya da ake gudanar da kamun amarya Fadeelah.

Sadiya dake gefe taja tsaki a k'asan ranta, ita tun d'azu taso ganin amaryar, amma wadda ta d'aukarwa kayan nan ta hana ta fon suna zuwa k'ofar d'akin ta juyo ta karb'i kayan sannan ta sallameta, yanzu kuma an shigo da ita fuska a rufe wai sai anyi kamun za'a yaye tukunna.

"Wannan fa duk shirme ne walkahi ba haka ake ainihin Kamu ba, a garinmu ranar kamu amarya ko kwalli bata sawa balle tayi kwalliya."

Wata a gefen Sadiya ta fad'a a inda suke zaune, daga can gefen filin ne inda kusan tawagar 'yan aiki ne da kuma wasu 'yanuwan masu gidan na k'auye da basu da wayewa sosai.

"Ai kin san abin al'ada-al'ada ne, mu a namu b'angaren ruwan turare ma ake wanke amaryar dashi."

Cewar wata kuma a gefe. Wata daga can hausarta cakud'e da yare tace.

"Mu namu duk wanda yazo kudi zai je ya dank'a a hannun amaryar kafin ma ya nemi wurin zama."

Suka kyalkyale da dariya, wata tace.

"Ashe duk amarya kud'i take yi da bikinta."

"Ko kad'an ake bata kuwa ai ta tara."

Haka suka yi tayi Sadiya na jinsu bata ko ce uffan ba, don ita tunaninta na can wajen hangen abinci da kuma son ganin amaryar, tana son ta tashi amma ta san da hajiyarta ta ganta zata dank'a mata wannan fitinannen d'an nata, a cikin ranta ta kudirce cewa duk randa ta kori mahaifiyarsa daga gidan shi zai fi kowa shan azabarta kamar yadda ta bauta masa fiye da kowa.

"Yawwa kinga zo ki taya ni dan Allah."

Muryar wannan yarinyar data taya d'aukan kaya d'azu ta yafito ta daga gefe, Fatima take ko wa? Da saurinta kuwa ta mik'e tayi wajenta don daman neman hanyar tashi daga wajen take. Buhu ne na jakunkuna masu d'auke kayan amfani kitchen dama na gida kala-kala a ciki.

Lallai kud'i na inda suke! Ta ayyana hakan a ranta sanda ta hango rayuwarta ta Ikara shekara da shekaru, musamman a gidan mijin ta na biyu data sha mutuk'ar wahala. Amma ba komai ita zata yi abinda yafi haka ma ranar da ta tashi aurar da 'yar da zasu haifa da Alhajin hajiyarta da take shirin aura.

Can gefen rumfar amaryar yarinyar tasa ta ajiye buhun, ashe da sauran wasu ma don sai da suka koma ta d'ebo kai uku banda wasu ma da suka taya ta d'ebowar.

Mutane sun ragu sosai a rumfar saboda haka sanda ta ajiye na k'arshe ta juyo ne idonta ya hango mata abinda take nema tun farkon zuwanta wajen... Cikin rumfar amaryar da mutane suka ragu a yanzu sannan amaryar dake zaune fuskarta shab'e-shab'e da hawaye.

Yadda tsawa ke fad'owa kan wani abu walau tsirrai ko dutse ta tarwatsa shi ya tashi daga kammanninsa, haka Sadiya taji a lokacin da kammanin fuskarta suka juya take cikin tsananin mamaki da rud'ewa sanda fuskar amaryar ta haska cikin idonta, ba wai don tsananin kyan da tayi

Please Login or Register in order to submit comment