Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hotuna na sojojin nahiyar, a cikin hotunan fursononin da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen y'akin, naga hoton Ahmad. A wannan lokacin ne kuma duk kukan rashin k'awa kuma 'yar'uwata dana tara tsawon watanni biyar ya b'alle daga idanuna, Maria taso Ahmad da zuciyarta guda kuma taso musu rayuwa mai kyau a gaba, amma hakan bai yiwu ba, ni d'in da ban tsara komai ba, ni na rayu kuma na sami tarin dukiyar da zan iya yin komai da ita a lokacin.

Naji cewa zan iya bayar da komai har kuwa da rayuwata a lokacin in da wani zai iya canja k'addarar Maria da Ahmad. Ya dawo musu da rayukansu, sannan ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsu ta yadda komai zai tafi kamar yadda Maria ta tsara a mafarkinta.

Bayan barina asibitin, na koma gidan tsohuwar nan na nemeta don in karb'e ka ka girma a wajena, amma abin mamaki babu inda ban shiga ba amma ban ga matar ba, sai a lokacin na gane gangancin da nayi, na dank'a ka a hannun wadda ban sani ba, sai dai wane zabi nake dashi a lokacin?

Shekaruna goma tsakanin birni da wannan k'arami garin ina neman bayani akan wannan tsohuwar amma ban samu ba, sai a cikin shekara ta gama sha biyu ne na sami labarin mutuwarta daga wani mutumi a cikin garin, yace min shekaru hudu baya, mota ta kad'e ta a gefen titi kuma ba wanda ya ganta da wani yaro k'arami.

Sai na shiga bin gidajen marayun dake wannan yankin ko ta kaika can ne, amma ban same ka ba saboda haka na k'addara cewa ka mutu, kuma k'uncin yayi min yawa saboda haka na tattara komai nawa na bar k'asar, na komo Ingila na bud'e wata sabuwar rayuwar da ban tab'a jin dadinta ba saboda na k'addara cewa in har na sami dad'in rayuwa ban yiwa k'awata adalci ba wadda ta mutu cikin k'unci.

A yanzu cikin kwanakin nan ne nake yawan mafarki da Maria rik'e da kai hannunta lokacin data haife ka, hakan yasa na fara tunanin cewa baka mutu ba kenan, saboda haka na cigaba da bincike akanka har zuwa yanzu da nake rubuta wasik'ar nan, na kudirta a raina cewa idan har na same ka zan shaida maka labarin iyayenka dalla-dalla fiye da yadda yake a rubuce yanzu, idan kuma bamu had'u ba, na tabbata a dunk'ule wannan zai ishe ka sanin komai, don idan har na mutu da nauyin da mahaifiyarka ta bar min, na tabbata ba ita kad'ai ba ko waye yaji labarin nan ma ba zai yafe min ba.

Idan har wasik'ar nan ta isa gareka d'an Maria, inaso ka san cewa mahaifiyarka tace in shaida maka ita bata da dangi amma ka nemi 'yanuwan Babanka a can k'asar Nigeria a wani gari mai suna IKARA! Asalin sunansa shine Ahmad Muhammad.

Adam na kaiwa daidai nan a karatunsa wata takardar check ta zamo ta fad'o gefen k'afarsa, a hankali ya mik'a hannunsa ya d'auko ta, idonsa ya gane masa zunzurutun ku'di cikin adadi na dalar k'asar ingila.

Da sauri ya sake juyawa ya karanta layi d'aya daya rage a jikin wasik'ar.

... Idan har na mutu, dukiyata gabad'aya taka ce d'an Maria, idan kuma har ba'a same ka ba, na sadaukar da komai ga gidajen marayu da tsofaffi marasa DANGI irina da mahaifiyarka.

A hankali ya ninke check d'in ya ajiye shi a gefe, abinda yake gabansa yanzu ya tabbata mutuwa ce kawai zata iya tsada shi, labarinsa bai k'are ba, hasali ma yanzu komai ya fara, a take yaji zuciyarsa tayi fiffike ta yiwa garin IKARA tsinke!

●﹏●

Ko kun tuna cewar Bintun da muka fara had'uwa da ita a farkon labarin nan daga IKARA take?

Wane k'ulli ne labarin nan ke shirin kwancewa?

Insha Allah next update zai zo kafin ranar Lahadi.


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

18

(☆_☆)

🎵🎶

Dangi anata taro...
Ko'ina d'aukacin masoya,
Aure ake na manya, lallai amaryar fa tayi dace...
... Angonki ya kasance mai hak'uri da tausasawa.
🎶🎵

Kamar yadda wak'ar ke fad'a, k'aton hall ne wajen cike da dangi na birni da k'auye, b'angaren amarya da kuma b'angaren ango, kowa yazo don shaidawa da kuma taya murnar auren Aseeyah da Angonta mai suna Idris Makama.

Duk inda ka duba mutane ne cikin kwalliya da farin ciki, gashi wajen yasha had'adden decoration tunda bayan kamu da akayi a jiya, wannan itace walima guda d'aya tilo da aka za'a gabatar sai kuma gobe Asabar a d'aura aure, ayi yini sannan a kai amarya baki d'aya.

Lokaci ne irin wanda Amarya da Ango basu dad'e da isowa ba, M.c ya rik'e su a tsakiyar fili yana tsokanarsa kala-kala sannan kuma yana kiran dangi su zo su nuna musu kara ta hanyar lik'i, adai lokacin kuma masu rabon abinci sun fara aikinsu na kawowa tebur-tebur, don haka banda hayaniya da kuma k'arar kid'a, wajen a cakud'e yake da zirga-zirgarsu da kuma ta masu gajen hakurin cewa ba'a kawo abincin wajensu ba.

Fadeelah na zaune a wani tebur daga can gefe cikin k'awayen Fatima da suke ta hirarrakinsu suna d'aukar hoto, irin ankon jikinsu shi itama ta sanya, anyi mata d'inkin doguwar riga mai simple design data zauna b'am a jikinta, telan su Fatima da bai san awonta ne ba yayi dinkin, don haka sai rigar taso ta matse ta daga sama, sai ta d'ora light pink mayafi irin kalar ashoken dake kanta. Ita bata san k'awayen Fatiman da take zaune cikinsu ba kuma ba zata iya shiga cikin hirarsu ba saboda haka tayi shiru kawai tana kallon hada-hadar mutanen wajen, a cikin zuciyarta kuma dad'i take jiwa Aseeyah sosai, yadda ta kasance 'yar cikin dangi masu yawa da k'aunarta haka, gani take Aseeyah ta riga ta gama samun rabin nasarar rayuwa irin wadda ita take nema a yanzu ido rufe.

Allah ya riga ya karrama d'an Adam da rahamomi da yawa, a ciki kuwa harda sanyashi da yayi cikin mutane masu irin jinsinsa da ake kira da DANGI, ta dad'e da fahimtar cewa duk wata d'aukaka da nasarar da mutum zai samu a duniya in har baya cikin danginsa, to wallahi ko meye zai tashi a banza ne. Shi yasa har gobe take jinjinawa Mami Safiyya yadda ta iya barin wannan tarin dangin kaf! ta tafi k'asar da bata da kowa sai miji da 'ya'ya.

A hankali ta juya ta janyo jakarta daga bayan robobin ruwa da lemon dake ajiye kan table d'insu sannan ta zaro wayarta daga ciki. Ba tare da ta kunna ba ta kalli fuskarta akan duhun screen d'in, itafa har yanzu bata yarda cewa fuskarta take kallo ba, don an fente ta ne gabad'aya da abubuwa kala-kala a inda Fatima ta jata akayi musu kwalliya, irin dai wadda ke kan fuskar duk sauran 'yanmatan wajen da kuma su Zahra da take hangowa a gefe, sai dai su in ta kalle su sai taga kammaninsu suna nan, musamman ma dai Zahra da tun da ta saba yin abarta.

Amma ita in ta kalli kanta sai taga kamar wata ce daban take kallo, don an k'ara fik'e komai na fuskar, an fito da ita d'al kamar wata 'yar tsanar da aka b'are a leda.

"Lalalala, gaskiya ya Fatima tayi kok'ari, yau kece kika yi kwalliya haka? Aunty deelah kin ganki kuwa? Kamar a sace!"

Ta tuno abinda Zahra ta fad'a sanda suka iso wajen, su kuma su Zahran sun fito zasu je taho da k'awayensu.

Ta kai hannu zata taba kan hancinta sai d'aya daga cikin k'awayen Rahma dake zagaye a teburinsu ta dakatar da ita.

"Kina tab'awa yanzu kwalliyar zata yi dabbare-dabbare, ki barshi kawai."

Tayi mata murmushi kawai ba tare da ta amsa ba, ta lura tunda suka zauna take son yi mata magana, ita kuma bata iya sabon farad d'aya ba.

Beem!

A lokaci d'aya wayarta tayi haske alamun shigowar sak'o.

Na kira Mami ban same ta ba, kun isa wajen ne?

Al'ameen ne, kuma ta tabbata bai kira Mamin ba, kalmar 'Ku' tana nufin ita kenan, so yake yaji in ita tana wajen ne kafin ya k'araso. Wannan shine sabon yaren da suka fara.

"Eh kowa yana nan. Ka iso ne?"

Beem!

"Eh nazo, zaki fito ki nuna min inda Mami take? Ba zan dad'e ba."

Tayi murmushi ita kad'ai.

"Kana ina?"

Beem!

Ina harabar wajen."

"Okay, gani nan."

Sati biyu da kwanaki, kokarin Fatima da kuma dabarunta ya juya waccan bahaguwar alak'ar data fara tsakaninta da Al'ameen a farkon zuwansa.

Hakan kuma ya dad'a tafiya ne da yawan zaman Al'ameen a gidan, don sun riga sun gama aikin daya kawo su har abokan aikin nasa sun koma, shine kawai Mami ta rik'e shi da cewar ya tsaya ayi bikin Aseeyah don yaga al'adar bikin Nigeria da bai tab'a gani ba, saboda haka ya k'ara sati biyu akan komawarsa.

Komai ya fara ne da shawarar Fatima ta farko, taje ta gayawa Mami cewa magungunan da take sha bata jin dadinsu ko zasu gwada zuwa asibiti taga likita sosai, ta san sarai Mami shi zata ce ya kaita don hidimar bikin Aseeyah tayi mata yawa, saboda haka da murnarta ta gaya masa, kuma bai ruguza komai ba yace ta shirya suje.

Ya kaita wani asibitin kud'i mai kyau ba tare da ya katbi ATM d'in Mami ba, akayi mata shigen check up d'in da ta saba da irinsa a washington aka kuma bata tulin magunguna, daga nan aka basu appointment cewa bayan kwana hudu su dawo, sai ya zama kafin cikar kwanaki hud'un nan a kullum zasu gaisasannan ya tambaye ta yadda take jin maganin a jikinta, a rana ta uku kuma ya shaidawa Mami cewa abokan aikinsa zasu zo su gaishe da ita kafin su koma.

Da shawarar Fatima, ta hutar da Mami a ranar ta shiga kitchen ta had'a musu abinci mai dadi, harda kalar na turawa da ta iyo a can. Kuma ba'yan gidan kad'ai ba, ita da kanta kanta tana juya al'amarinta a kwakwalwarta, wai Al'ameen d'in da k'iri-kiri ta yiwa kanta katanga dashi a baya shi zuciyarta kuma ke janta yanzu akansa, tana gaya mata cewa komai ba zai zama matsala ba tsakaninsu.

Sai dai wannan abun shine kusan
jigon daya fara dawo da hankalin Al'ameen kanta, don a washegari da taje yiwa Mami sallama zata tafi makaranta da kansa yace bari ya d'auko muk'ullin motar ya kaita.

"So shekara d'aya? Me kika cimma a rayuwarki so far?"

Ya tambaya sanda go-slow ya tsaresu akan hanya.

Tayi shiru kafin ta d'aga kafad'unta kad'an, idonta na kan motar dake gabansu tace.

"Abubuwa da dama kamar... na shiga university, ciwona yayi sauk'i, na saba da dangin su Mami sannan na iya hausa sosai."

Yayi guntun murmush a gefen lebb'ensa kafin yace.

"Nice! kin samu abubuwa da yawa, na miki murna."

Ta gyad'a kanta, "Nagode."

"You're welcome."

Shiru ya biyo baya, kafin ya bud'e kofar motar ya fita, yayi d'age kad'an don hango adadin motocin dake gabansu kafin yaja tsaki ya dawo.

Kamar kar tayi magana sai kuma ta kalle shi tace.

"Sai hak'uri Nigerian mu kenan."

Ya sake wani guntun murmushin da kyallinsa ya haska cikin idanunsa ya kuma sa ta jin wani iri, Ya Allah! ba wannan ne karon farko data kalle shi ba, amma tun bayan zuwansa, wannan ne karon farko da ta kalli cikin idonsa kusa da kusa haka, wai meke damunta ne?

"Waya gaya miki bana son Nigeria, zan iya dawowa nan ma baki d'aya, ina son duk k'asar da kokarin ka zai yi determining waye kai."

Sai ta kawar da kanta gefe.

"Baka san Nigeria ba, Mami tace a anan matsayinka da kuma matsayin wanda ka sani shine kawaia zai fanshi duk kokarin ka."

"Wannan kusan koina ne Fadeelah..."

Sai zuciyarta tayi tsalle ta dira gefe d'aya jin yadda harshensa ya nad'o harafan sunan nata.

"... Kawai dai na wani wajen yafi na wani yawa ne."

Bata k'ara cewa komai ba ta cigaba da kallon rayuwar mutanen waje dake faruwa a bayan windon motar, so take ta tambaye shi bayan gemunsa daya k'ara kyau me kuma ya faru dashi a shekara guda, amma harshenta yayi nauyi ya cika bakinta.

Tun daga wannan ranar sai hira ta fara shiga tsakaninsu, hira mai ma'ana ba irin wadda suke yi a shekarar baya ba, babu wasu kalamai masu taushi, sai magana kawai mai muhimmanci data danganci ra'ayin kowannensu da kuma abubuwan da suke burin cimma.

Ranar daya fara samun numberta kuma Mami ce ta kira shi cewar ya taimaka ya d'auko ta daga makaranta, su dukkaninsu basa nan don shirin bikin Aseeyah ya kankamaa lokacin.

Dole ya karbi numberta ya kira ya shaida mata cewa zai zo d'aukanta, kuma bayan ya d'auko tan maimakon ya kaita gidan Hajiya Amarya kamar yadda Mami tace, sai da suka tsaya a wani k'aton library tukunna, ya nuna mata wani abu da suka yi musu akansa game da rebe-raben k'asashen duniya.

Sanda ya sauke ta a harabar gidam Hajiya Amarya, Fatima ta d'ago mata hannu daga barandar saman benen alamun fara samun nasararsu fiye da koyaushe.

"Bafa wani abu Faty, har yanzu gaisawa muke sai kuma 'yar hira kawai."

Fatiman tayi dariya a lokacin sannan ta sauke muryarta k'asa don kar su Mami dake gefe suji tace.

"Zauna nan, ke kin san tunaninsa ne? Duk sanda kuke tare kin san me yake ji?"

Me yake ji? Fadeelah tayi tambayar a cikin kanta, don itafa har a lokacin in banda kyawun Al'ameen da kirkinsa da take gani bata san me take ji game dashi ba.

Amma shi kuma fa? Me yake ji game ita?

***

Ji yake zuciyarsa na bugawa da wani irin salo duk sanda yake tare da ita sannan ji yake kamar ita kad'ai ce abinda ke sashi annashuwa a rayuwarsa, sabon da suka yi a yanzu babu abinda yake haifar masa sai k'ara tunatar dashi cewa zuciyarsa ta k'aunace ta a baya kuma bayan wata yarinya daya tab'a kulawa a makaranta, ita kad'ai ce wadda ya taba ji cewa yana son kasancewa da ita har k'arshen rayuwarsa.

Baya gajiya ko kad'an da sauraren hirarta sannan baya taba fasa d'okin wayewar gari a kullum don ya ganta, murmushi kad'ai in tayi sai yaji zuciyarsa ta k'ara dulmiya cikin tunaninta. Ya san cewa ya rufe wannan babin a da, amma yanzu da kowacce dakika in suna tare, k'ara burge shi take, tana k'ara shiga cikin zuciyarsa sannan kuma tana raba tunaninsa gida-gida.

Kuma a cikin kowanne rabe-raben, abu d'aya ya sani shine har yanzu yana k'aunar Fadeelah kuma ba abinda zai canja hakan, sai dai zai cigaba da mafarkin zaune ne muddin cewa bai motsa ba, bai sake gwada sa'arsa a karo na biyu ba, sannan bai d'ago da kwantaccen hargitsin daya san zai faru daga b'angaren Maminsa ba.

Ya nisa a hankali ya fitar da iska ta siraran k'ofofin hancinsa, yana tsaye ne a gaban motarsa daga harabar wajen bikin, a gabansa mutane ne ke ta wucewa suna shiga ciki, har kuwa da jerin 'yanmata kala-kala kowacce cikin kwalliya, sai dai a idanunsa shi duk mata a irin wannan shekarun na 'yammatanci d'aya yake ganinsu, ba turawan da yake cikinsu ba, ba kuma wad'annan jinsin hausa-fulanin da yake gani a yanzu ba, kowaccensu kallo d'aya kawai yake musu, na Mace kawai!

Amma Fadeelah, tun daga ranar daya fara ganinta a cikin kitchen d'in nan, yaga kamar ansa wata filtila ne ta samanta an haska ta, hasken da ya shiga har cikin idanu da zuciyarsa ya haska su, yasa ya yarda cewa ita d'in daban ce da kowa, tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu kuwa. Shi yasa yake ganin lokaci yayi da zai fuskanci k'addarar dake biye dashi tsawon wannan lokacin.

A sanda Fadeelan ta ratso daga cikin wajen ta nufo wajen adana motocin da yake, zuciyarsa ta matse fiye da koyaushe ganin yadda kwalliyar fuskarta ta sake fito da tsantsareren kyawunta da bai taba gani ba, kamar yadda bai taba ganinta cikin kwalliyar ba.

Kwarai lokaci yayi da zai sake gwada sa'arsa kan Fadeelah a karo na biyu, karon da yake jin cewa ba zancen Hamida ba, a yanzu ko Maminsa bata isa tasa ya guntule farin cikinsa ba.

Abu d'aya kawai shine bai san cewa in a yanzu zata karb'e shi ba, ko kuma tarihi zai sake maimata kansa!

***

"Wai ba nan aka rubuta a jikin venue d'in ba da gaske?"

Wata 'yar kyakkyawar Matashiyar mata ta fad'a sanda take gyara hular kan yaron da take rik'e dashi a hannunta, kamar ita, yaron fari ne sosai sai dai har yaso ya zarta ta ma a kyau in akayi duba ga ya had'o da kammanin Mahaifinsa ne wanda ke zaune a gefensu yana shirin kunna had'addiyar motar da suke ciki.

"Sunan da address d'in duk iri d'aya, amma sunce wai wannan sunan Amaryar Aseeyah ba Amina ba."

"Bibty mu koma gida kawai dan Allah, kayi musu Allah ya sanya alkhairi in ka koma office, don ina jin ma Afra zazzabi ne ke shirin kamata."

Ta fad'a tana juyawa ta kalli wata 'yar yarinyar dake zaune a baya motar cikin shigar wasu pink kaya masu kyau, babu ko d'ankwali akanta sai yala-yalan gashinta da aka tufke cikin k'ananan kalba da ribbons.

"Hakan za'ayi kawai, nima na fara gajiya, don munsha yawo yau."

Mijin ya amince kai tsaye sannan ya shiga kokarin yin reverse a harabar wajen. Sai dai me? A daidai lokacin daya juya kan motar cikin saurin dake nuna lafiyar injinta, idanun matar nan suka sauka akan wata budurwa daga can nesansu, tana sanye cikin pink kaya na alamun ankon bikin sannan tana kokarin nufar wani saurayi dake jingine a gaban wata mota.

Da dare, da tazara tsakaninsu da kuma girma daya sauka akan fuskar budurwar, amma duk wad'annan ba komai bane, koda ragowar numfashi guda d'aya ne ya rage mata a rayuwarta... Ba zata tab'a kasa shaida kammannin k'anwarta jal a duniya ba.

BINTUN IKARA!

●﹏●


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

19

(☆_☆)

A lokaci guda komai ya haska tar! Cikin idanun matar, a wannan duhun safiyar data tsallake shimfid'ar 'yar k'anwar tata ta nufi k'ofa, da sanda har ta zura kafarta waje ta juyo ta sake kallonta duk'unk'une cikin zanin rufarta kasancewar lokaci ne irin na sanyi a sannan, da kuma sanda ta ciro wani zoben hannunta da Bintun ke yawan k'alatarsa ta dawo ta ajiye mata a gefen fuskarta sannan tabi duhun safiyar da idanun jama'a suka yi k'aranci cikinsa, ta tafi ga abinda take jin gwara mutuwarta da ta rasa shi a rayuwarta.

Wannan wani abu ne da ta dad'e da mantashi, baya ma cikin lissafinta kwata-kwata, don tun bayan da hakan ta faru, bata tab'a waiwayarsa ba ko a cikin kanta, amma a yanzu da tunaninsa yazo mata, sai take jin kamar a jiya ne akayi komai.

"Menene? Me ya faru?"

Mijin nata ya tambaya yana kokarin kallon inda ta juya, sai ta katse shi ta hanyar juyowa ta kalleshi da fararen idanunta k'al! wanda maik'on kwallar data fara taruwa a ciki tayi musu wani ado.

"Bibty wata na hango acan kamar..."

Maganarta ta katse, saboda a daidai wannan lokacin igiyar jikin wani mutum-mutumi da aka had'a da tarin layoyi ta sake daurewa tamau! Sannan d'igon jini guda ya d'iga a jikin k'asar kabarin da aka binne shi.

Ta d'an tsaya cak! Kamar wadda ake gogewa wani abu kafin kuma ta girgiza kanta a hankali sannan tace.

"Wata na gani kawai kamar na santa, mu tafi daga nan wajen dan Allah."

Ya gyada kansa sau d'aya sannan ya karasa juya kan motar suka nufi hanyar gate, Tarihi ya sake maimata kansa!

Sanda yazo mik'awa mai gadin wajen pass d'in hannunsa ne ya kalleta ta gefen ido, ta sunkuyar da kanta kad'an sannan da zaren hular kan d'ansu Muhammad ta d'auke 'yar k'aramar kwallar data fara taruwa a idonta.

Bai san me ta gani ba amma a take yaji zuciyarsa ta matse cikin k'irjinsa, wata irin matsewa mai rad'ad'i, irin yadda yake ji a duk lokacin daya tuno abinda yayi da kuma sanadin kasancewarta matarsa. Wani gefe a cikin tunaninsa ya shiga shaida masa abinda ya shafe tsawon lokaci yana nusar dashi, cewa lokaci yayi da zai daina bautar da ita ta hanyar dole!

Watak'ila a yanzu zata zauna dashi ko don albarkacin 'ya'yansu.

***

"Nayi zaton ka shigo ciki."

Fadeelah ta fad'a sanda takunta ya k'arasar da ita gabansa.

Sai da Al'ameen ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa jin siririyar muryarta sannan ya mike tsaye daga jiginar da yake. Tsawonsa akanta ya baiyana tazarar incinan dake tsakaninsu sosai duk da cewa ya lura takalmin k'afarta na da d'an tudu.

"Naji ance kamar biki biyu ne a wajen, shi yasa ban san ina zan shiga ba."

"A'a..." Ta girgiza kanta.

"Fatima tace bikin wata Aminah ne suka yi mistake suka saka date din yau alhali sai gobe ne nasu, shi yasa mutane ke ta zuwa suna tambaya."

"Okay, na gane."

"Baku taho tare dasu Ya Abdullahi ba?"

"A'a, su suna ciki ai ina jin, ni kai tsaye daga gida nake."

Sai ta gyad'a kanta a hankali, kwakwalwarta na gaya mata duk mutanen ita kad'ai ce ta san hanyar shigar dashi kenan, a sannan shi kuma ya tsaida idonsa akan fuskarta da kuma surarta mai shagaltar dashi na 'yan wasu sakanni kafin yace.

"Kinyi kyau 'yanmatan Mami."

Sai ta kautar da kanta gefe kadan cikin jin kunya, wanda hakan ba komai ya haifar ba sai kara tsima shi da tayi sakamakon wata mota data shawo kwana ta haske fitilarta dal akan fuskarta.

"Kaima kayi kyau, Mr. Balaraben Bature kuma Bahaushe a yau."

Ta fad'i hakan ne, tana kallon kayan jikinsa, wani yadi ne mai d'an banzan kyau da yasha fitted d'inki mara aiki irin wanda samari ke yayi a yanzu, kuma tun zuwansa k'asar, yauce rana ta farko daya fara sanya dogayen kaya, don telan Ya Abdullahi da suka fara shiri dashi a 'yar tazarar dake tsakanin gama aikinsa da yanzu ne ya bawa kwangilar yin kayan don kar ya fita daban a taron bikin.

Yasa hannu ya shafa lallausar sumar k'eyarsa sannan yace.

"Yana iya? Tunda hausawan sun rik'e ni ai dole ne in ajiye komai a gefe in shiga cikinsu."

"Kar ka damu, bikin dai daga yau sai gobe, Mami ta kusa sakinka."

Amma ke fa? Zaki taba sakin zuciyata ne Fadeelah?

"Mu shiga ciki?"

Ta tambaya jin baice komai ba, sai ya gyad'a kansa kawai tare da nuna mata hanyar. Da kowanne taku da yake bin bayanta, ji yake kamar ya fisgo hannunta ya tsaida ita, ya gaya mata dukkanin abinda zuciyarsa ke ji game da ita, cewa komai ya dawo sabo... Yana sonta kamar zaiyi hauka!

Amma ina! irin wannan kasassab'ar ita yayi a farko, ya gaya mata yana sonta ba tare da wani tsari ko shiri ba, ba tare da ya shagaltar da zuciyarta ta manta da duk wani k'alubalen da zai iya faruwa tsakaninsu ba.

Mace kamar kwai ce...

Kamaal ya tab'a gaya masa a wani lokaci.

... iya kokarinka wajen lallab'a kwan nan da kula dashi, shi zai sa har ka kai ga cinsa. Amma da zarar kace zaka rik'e shine ta duk yadda kaga dama, to a lokaci guda zai fad'i har dandaryar k'asa ya fashe.

Sanda suka k'arasa cikin hall d'in kusan kowa na cin abinci anata aikin bawa ciki ba babba ba yaro, don haka wata cool music ke tashi a wajen babu hayaniya sosai. Ance wai idan mutum na cikin damuwa a lokacin yake fahimtar me ake fad'a wak'a musamman idan wak'ar ta shafi shigen halin da kake ciki ne, don dalla-dalla Al'ameen ke jin kowacce kalma da wak'ar dake tashi take fadi a lokacin.

I wish I could go back to the very first day I saw you
Should've made my move when you looked in my eyes
'Cause by now I know that you'd feel the way that I do
And I'd whisper these words as you'd lie here by my side

I love you! please say
You love me too, these three words...
They could change our lives forever...

Duk tarin d'imbin jama'ar hall din nan suka zuk'e a idanunsa, Fadeela dake take tafiya a gabansa kawai yake gani da kuma wak'ar da yake jin kamar daga bakinsa take fitowa, da kyar ya sawa k'afarsa birki bai had'e da ita ba sanda ta tsaya daga tsakiyar hanyar tana waige-waige.

"Anan wajen fa na barta dasu Aunty iyami, ina kuma suka tafi?"

To whisper in your ear
Words that are old as time
Words only you would hear
If only you were mine...

Baitin wak'ar yayi daidai da yadda ya tsaya dab da ita kamar zai rad'a mata wani abun, a lokacin itama ta juyo ta kalle shi bakinta a bud'e kamar zata yi masa magana, sai kuma ta maida shi ta rufe sakamakon wani irin maganid'isun abu data hango daga kyawawan idanunsa.

Hasken flasher ne ya katse ya kuma janyo su daga tunanin da kowannensu ke shirin fad'awa a lokacin.

"Yawwa Hajiya, ku d'an juyo nan haka kuma

Please Login or Register in order to submit comment