Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya?"

Sai ta gyad'a kanta a hankali.

"Eh zan yarda."

Ya sake gyad'a kansa kad'an.

"Nagode."

Da haka ya juya zuwa teburin zaman lauyoyi, ya kalli Kutama cikin ido yace.

"Your witness..."

Kutama ya mike, da wani faffad'an murmushi a fuskarsa ya taho wajen akwatin tsayuwar masu shaidar, gaban Fadeelah.

"Hajiya Bintu, muna yi miki barka da zuwa wannan kotun daga b'angarenmu."

Sautin muryarsa yasa Fadeelah had'iye wani k'aton abu cikin k'irjinta jin yadda muryarsa ta fito babu ko tsoron Allah kamar wannan ne ganin da yayi mata na farko. Bata ko kalle shi ba, kuma bata ce komai ba ya cigaba.

"Mun ji dukkan labarin da kika bayar kuma kinyi kokari da baki canja komai ba kamar yadda muke dashi a rubuce, sai dai kuma kin yanke wani waje a labarin baki k'arasa ba, don a yadda muka sami rahoto ance daga wannan ranar rasuwar kika gudu daga Babban gida... Haka ne?"

Ta mutsikka yatsun hannunta cikin dauriyar kar ta fad'a masa maganganun da basu dace ba a gaban kotu kafin ta d'aga kai.

"Haka ne, daga wannan ranar na bar Babban gida bisa k'arancin shekaruna da suka sa naga hakan ne kawai hanyar da zan tsira, tunda zargin kowa yana kaina ni kad'ai."

"K'arancin shekaru? Kenan dukkan tsawon shekarun da aka d'auka har zuwa sanda aka gano ki, baki yi hankalin komawa gida ba?"

Ta girgiza kanta.

"Idan har kana da rahoton komai zaka ga cewa a wannan ranar dana bar gida na gamu da hatsarin mota wanda ya haddasa min ciwon kwakwalwa, na manta komai da kowa da na sani, saboda haka wad'annan shekarun nayi su ne cikin ciwo ba wai zaman dadi ba."

Kutama ya gyad'a kansa.

"Ko zaki iya gayawa kotu waye Sule a wurinki?"

Ta gyara tsayuwarta.

"Sule d'a ne a wajen k'anin mahaifina, mahaifinsa ya rasu tun kafin rasuwar nawa mahaifin, don haka a tsari na 'yanuwantaka kamar wa yake a wajena."

"Kenan shima yana d'aya daga cikin jikokin Babban gida?"

"Haka ne."

"Ko zaki iya gaya mana adadin jikokin da suke cikin gidan?"

"Ba zan iya ba, don a wancan lokacin ma na san an doshi mutum saba'in."

"Kuma duk a cikin wannan taron kice Sule kad'ai Hajiya ta tsamo tafi k'auna a cikinsu?"

"Bance shi Hajiya tafi k'auna ba, nace tafi shiri dashi ne saboda kullum yana d'akinta saboda bashi da aikin yi kuma bai damu da fita kamar sauran maza ba."

Kutama ya sake gyad'a kansa.

"Ba kya ganin za'a iya danganta karin maganar 'idan jifa ya wuce kanka, ya fad'a kan uban kowa' game da yarda da kika yi cewa Sule zai iya cutar da Hajiya?"

Tun da Kutama ya fara tambayoyinsa har zuwa k'arshe, Adam bai katse shi ba ko sau d'aya, yayi shiru kawai yana sauraran komai, kuma cikin sa'a Fadeelah bata bashi wata k'ofa da zai d'ago wani abu ba har ya gaji ya zauna.

Shaida ta biyu da Adam ya kira Kawu Bashir ne wanda yazo ya fad'i nasa b'angaren game da rayuwar Fadeelah a Babban gida da kuma rasuwar Hajiyar, sai dai duk ba wannan ne mai amfani ba, Adam yayi masa wad'annan tambayoyin ne don a hankali su k'araso ga tambayar da tafi kowacce muhimmanci.

"Zaka iya yiwa Kotu bayanin waye Sule?"

Kawu Bashir ya gyara tsayuwarsa.

"Sule d'an wajen K'ani na ne da muka had'a uba d'aya, yana zaune ne a b'angaren mahaifinsa daya rasu tare da babarsa da k'annensa mata hud'u kafin ayi wa guda d'aya aure."

"Bayan shirin da kowa ya sani tsakaninsa da Hajiya, akwai wani abu da ka sani ya tab'a shiga tsakaninsu?"

Ya d'anyi shiru kafin ya amsa.

"Eh toh, gaskiya babu wanda ya tab'a jin kansu, don ko bayan rasuwar mahaifinsa ma da ta hana a raba musu gado shi Sulen baice komai ba, yana yi mata biyayya sosai shi yasa ma tafi yarda dashi fiye da kowa."

Sanda Kawu Bashir yake wannan bayanin, idanun Adam na kan Alk'alin nan yana son ya tsinto abinda yake fata a fuskarsa.

Bayan Kawu Bashir, Habiba ce tazo a shaidar Adam na gaba, 'yan k'alilan d'in shaidun daya tsara zai rufe shari'ar nan dasu. ta tsaya da kyar cikin akwatin, saboda ciwon k'afarta da a yanzu ya tsananta.

Kamar yadda ya fara da lallashin Fadeelah a d'azu, haka ma ya yiwa Habiba, ya k'are da cewa.

"...ki kwantar da hankalinki sosai, ki bawa kotu amsar da kika sani dalla-dalla, ba ke kika kashe Hajiya ba na sani... Don haka ina so ki bani dama mu baiyanawa kotu hakan."

Wad'annan kalaman su suka d'an kwantar da hankalin Habiba daga k'ink'inar da ta fara a farko amma duk da haka bata saki jiki sosai ba, don ta san abinda ya fad'a karya ne, ita ta kashe Hajiya ba wani ba. Bayan wasu 'yan tambayoyi da mafi yawanci gaskiya ta fad'a, Adam ya tafi ga tambayar da zata amfane shi.

"Ina so ki tabbatarwa da kotu cewa kamar yadda kowa ya sani tun daga farko akwai rashin jituwa tsakaninki da Hajiya mai rasuwa."

Idanunta a zare kuma sun zurma ta kalle shi kafin ta juya gefe kuma ta kalli Alk'alin sannan ta dawo da idonta kansa.

"Eh, eh haka ne yallabai."

Bai tsaya ba ya cigaba kai tsaye.

"Wannan rashin jituwar ita tasa tun a baya kika yi yunk'urin kawar da ita ta hanyoyi da dama amma hakan bai yiwu ba har saida kika yanke shawarar neman guba ki zuba mata a abinsha don a lokacin kina son cimma wani abu da kika san in dai tana nan to baza ta bari ki samu ba. Haka ne?"

Gaban habiba ya had'e waje d'aya sannan yayi k'undunbala ya fado daga wata sama mai nisa, ya akayi ya san wannan abin? Ya akayi ya san wannan sirrin nata? Ya akayi ya binciko abinda ta b'oye daga idon duniya? Daga ita sai aminiyarta Salame take kashewa ta binne irin wannan sirrin da ita... Salame! Sunan ya tsaya cak! Akanta, ta bar zuwa kotun nan tun kwanaki data tazo ta kawo mata ziyara ta k'arshe a inda take tsare, zuwan data kula da canji sosai a tare da ita don bata wani dad'e ba ta d'auki jakarta ta tafi da cewar ciwon k'afarta ya ishe ta da wari. Ai kuwa Tabbas! ta hanyarta ya samo wannan zancen kenan, Salame ta sayar da ita a idon duniya, tayi mata hali irin na d'an Adam, Butulu!

Sai ta had'iye yawu a mak'ogwaronta ta kuma had'iyewa sannan ta amsa.

"Haka ne yallab'ai."

Take kotun ta rud'e da hayaniyar 'yan Babban gida, a yau Habiba ta fito da zaton kowa da kuma zargin da ake mata gaban duniya ta gaskata shi. Salati da maganganu suka cika wajen ba tsayawa, kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Habiba ta kawar da kai gefe, ta yarda dole ne a yanzu ta ture komai ta amshi laifinta, don alhaki kwikwiyo ne baya tab'a daina bibiyar d'an Adam, kuma a yanzu haka ma bata hango wani dad'i nan gaba a rayuwarta, 'ya'yanta maza uku da tun farko bata jasu a jikinta ba yanzu haka duk sun yar da ita, matansu sun janye su ba mai zuwa wajenta sai autanta dashi baiyi aure ba, wanda tafi sharewa a baya da tunanin ya b'ata lokacinsa wajen neman ilimin addini maimakon ya fita kasuwa ya nemi kud'i, shi kad'ai ne a yanzu ke ta d'awainiya da ita da kuma ciwonta.

Sannan dukiyar da take tarawa ma yanzu babu ita, zuwanta Niger kwanakin baya ya cinye mata komai, ragowar kud'inta na gida yanzu baza su doshi dubu d'ari biyar ba, don a baya ma filayenta ta siyar tayi gyaran d'aki, bata da wani kwakkwaran d'an'uwa sannan bata da wani mai sonta a Babban gida, to 'ya'yanta ma sun guje ta balle wani? Dole ne a yanzu ta sauke komai ta karb'i laifinta... Lokaci yayi da Bintu zata fita daga sharrinta!

Da kyar aka samu surutun wajen ya lafa, Adam ya gyara tsayuwarsa yace.

"Kenan a yanzu kin yarda da zargin da ake miki na farko?"

Tasa hannu ta d'auke kwalla a gefen idonta sannan tace.

"Na yarda, kuma duk abinda na fad'a wancan karon dana tsaya a nan k'arya ne, waccan yarinyar Bintu bata da laifin komai, k'awata Salame ce ta bani shawarar muyi amfani da ita don kar a zarge mu, duk abinda ta fad'a gaskiya ne, ni nayi kokon a wannan ranar kuma na zuba gubar dana samo a wajen Malam Salisu a ciki, Bintu tazo ta d'auka ne bayan ta gama wankin da Hajiyar ta saka ta. Ina rok'on kotu dama duk wanda na d'auki alhakinsa ya yafe min."

Wannan karon da kyar aka samu kowa ya saurara saboda tsabar yadda wajen ya rud'e da hayaniya, har sai da Alkali yayi gargad'i ga kowannensu ya kuma karanto wasu daga cikin sharad'an karya dokar kotu sannan kowa ya shiga hankalinsa aka nutsu.

Tambayar da Adam yayi mata ta gaba shine ta baiyanawa kotu inda ta samo gubar da tayi amfani da ita. Muryarta na rawar kuka kuwa ta shiga bayani tiryan-tiryan yadda taje wajen Malam Salisu kamar yadda Adam yaji daga bakinsa a k'auyen Mimbiri, Habiba bata b'oye komai ba don har jayayyar da suka yi akan ba zai bata ba sai da ta fad'a, da kuma yadda daga baya yazo har gida ya kawo matan.

A yanzu da babu damar hayaniya, kotun ta d'auki wani irin shiru daya wuce hankali, ba abinda ke haskawa a fuskokin mutane sai mamaki da rud'ani tsantsarsu! Da mamaki kaci karo da abinda baka tab'a zatonsa ba... Da mamaki yadda wannan gaskiyar ke fitowa tar! daga bakin Habiba.

Sab'anin yadda mamakin kowa ya ta'allak'a akan Habiba, Kutama nasa akan Adam yake, yayi shiru kawai dunk'ule da hannu akan bakinsa, a iya saninsa da kuma shekarun daya d'iba akan aiki, bai tab'a ganin lauya irinsa ba... ta yaya a rana d'aya kawai da ya karb'i shari'ar zai fito da wannan bayanan? Wata nawa shi ya d'iba yana gabatar da nasa shaidun da basu tab'a tasiri irin haka ba? Wace irin hazak'a ce dashi da zai fito da komai a wannan d'an k'ankanin lokacin?

Ya had'iye wani dunk'ulen yawu a mak'ogwaronsa, fargabarsa a yanzu ba ta fad'uwa shari'ar nan bace don ya riga ya gama cin kud'insa, fargabarsa d'aya ce, in har Adam zai kasance a Nigeria, dole ne hanyar samun abincinsa zata k'aranta.

Habiba bata tsaya ba sai da ta dire gaskiyar komai har zuwa sanda ta gama had'a koko mai gubar, da sanda Bintu tazo ta d'auka ta tafi, da sanda akayi shelar mutuwar Hajiya, da sanda Bintun ta gudu aka neme ta har Kano aka rasa wanda hakan yasa shari'ar ta mutu, ita kuma ta bud'e nata babin cin duniyar daga nan.

Hannayen Kawu yahaya in banda rawa ba abinda suke yi, ji yake dama yana da ikon tashi ya fita ya kira Kawu Danjuma ya shaida masa duk abinda ke faruwa, wannan wace irin kunya ce suka jawowa kansu haka? Tuntuni suna tare da wadda ta kashe mahafiyarsu amma suke ta bulayin neman yarinyar da bata da laifi, bata da alhakin komai? suka aikata abinda ya raba kan DANGINSU alhali baren data shigo cikinsu ita ta aikata komai... Don a yanzu babu wani b'oye-b'oye komai ya fito fili cewa Habiba ce tayi kisan.

Sai dai me? Kalaman da suka fito daga bakin Adam suka sake daskarar dashi a mazauninsa. Ya d'ago da idonsa ya kalle shi, ya juya gaban alk'alin yana magana.

"Na san kotu ta saurari duk bayanan Habiba wanda babu k'arya a cikinsu, kuma na san kotu ta fara d'aukar wani b'angare na cewar Habiba tana da laifi a ciki, sai dai ina son kotu ta fahimci cewa ba haka al'amarin yake ba, gubar da Habiba take zaton ta dama kokon Hajiya da ita ba guba bace face wani sassak'en magani da bashi da tasiri ko kad'an a jikun mutum, don haka Habiba bata da alhakin kashe Hajiya, daga ita har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin."

A wannan karon kowa manta gargad'in Alkali yayi, waje ya sake rud'ewa da hayaniya wadda bata lafa ba har sanda Alk'alin ya kalli Adam yace.

"Wace shaida zaka bayar akan haka?"

Adam yace.

"Kamar yadda kotu taji a cikin bayanan Habiba, ta samo abinda take tunani guba ne a wajen wani mai sayar da magungunan gargajiya Malam Salisu, wanda a yanzu haka ya dad'e da barin garin ikara. Sai dai naje har k'auyen da ya koma a yanzu kuma na same shi mun taytauna, ya gaya min gaskiyar komai kuma na gamsu da bayanansa, naso ace ya samu halartar wannan zaman da kansa amma yana cikin rashin lafiya irin ta tsufa kuma ya rasa k'afafunsa a dalilin hatsari, amma na samuna d'auko maganganunsa a lokacin da yake min bayanin.

Yana rufe baki Jabir ya taso rik'e da wata 'yar karamar recorder, ya mik'awa wani ma'aikaci dake zaune a teburin dake k'asan zungureran teburin Alkalin, mutumin ya k'arb'a ya jona a jikin speaker da wayar AUX, tak'e muryoyi suka shiga fitowa tar a kunnen kowa dake wajen.

Ni na san shari'ar nan baza ta tab'a mutuwa ba sai anyi ta, an samu yarinyar da ta gudu ne?

Eh ta dawo. Muryar Adam ta ciki ta amsa.

Daga Habiba har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin

Ban gane abinda kake nufi ba.

Ko waye ya turo ka kaje ka gaya masa ba Habiba ce ta kashe Hajiya Balaraba ba.

Tiryan-Tiryan hirarsa da Malam, Salisu ta shiga fitowa daga speaker har zuwa iya inda ya sanya a ciki, iya inda yake so ji.

"K'orafi ya mai shari'ah!"

Kutama ya mik'e a lokaci guda da muryoyin suka k'are.

"Kotu bata da tabbaci cewa wannan muryar ta wanda aka kira da Malam Salisu ce, za'a iya amfani da muryar wani a matsayin tasa."

Alkali ya juyo ya kalli Adam.

"Me zaka iya cewa game da haka?"

Muryarsa a nutse tana sulalowa kamar tafiyar tsutsa ya amsa.

"Ya mai girma mai shari'ah, bayan 'yan cikin babban gida akwai mutanen cikin Ikara da yawa a nan, kuma na tabbata duk a cikinsu babu wanda bai san Malam Salisu ba saboda shaharar da yayi a lokacinsa, na bawa lauya Kutama dama, zai iya zab'ar ko waye ya nemi tabbaci."

Alkali ya juya ya bawa kutama dama. Mutum uku kuwa ya zab'o daga cikin 'yan kallo, biyu mutanen gari ne, d'aya kuma Saminu ne, d'an gidan gwaggo lami wa a wajen Bintu, dukkaninsu kuma suka fito suka tabbatar cewa muryar da aka kunna ta Malam Salisu ce, don haka ba wani kuzari kutama ya nemi waje ya zauna.

"Kotu ta gamsu da dukkan bayanan da aka gabatar don haka lauya zai iya kiran shaida ta gaba."

Alkalin ya fad'a cikin muryar dake nuna cewa shi kansa yana jin dad'in yadda shari'ar ke tafiya.

Habiba bata san me take ji ba har lokacin da wata mai tsaro ta taimaka ta fita da ita daga cikin akwatin wajen, ba wai an tabbatar bane amma zata shallake gaban mamaki in har akace ba ita ta kashe Hajiya ba, duk k'ok'arin da take ganin a baya wayonta ya shirya a banza ya tashi kenan... hukuncin Allah ya danne nata.

"Ya mai girma mai shari'a, zanso in gabatarwa da kotu Maryam Idris Musa, wadda aka fi sani da Anna."

Idanun kowa ya juya kan k'ofar shigowa sanda aka shigo da Anna wadda take a tsaftace sab'anin yadda 'yan babban gida suka santa, sanye cikin dogon hijabinta.

A cikin 'yan sakanni kawai Adam ya tuno irin wahalar da ya sha kafin ya samu Anna ta bishi su tafi Asibiti, daga k'arshe sai da aka had'a da matar Kawu Ibrahim da kuma yayar Bintu wanda suka rik'eta har zuwa asibitin, inda bayan an gama bincikar ta ne kuma suka kaita wajen gyaran jiki aka tsaftace ta, sai bayan nan sannan ya sami zantawa da ita, a lokacin ya dawo daga police station wajen SULE.

Jabir ya sake mik'ewa ya kawo masa wani file, shi kuma ya k'arasa ya sake bawa wannan ma'aikacin da ya tashi yaje ya mik'awa Alkalin.

"Ya mai shari'ah wannan sakamakon gwaji ne daga kwararren asibitin gwamnati, munje tare da wakilin da aka bamu daga wannan kotun inda aka auna kwakwalwar Maryam kuma aka tabbatar cewa babu ciwo a cikin kwakwalwarta kamar yadda result d'in yake nunawa.

Ta sami matalar shafar Aljanu kawai tun lokacin aurenta na farko wanda har hakan ya hana ta zaman auren, mutane suna yi mata kallon mara hankali ne sakamakon rashin kulawa data samu bayan ta dawo gida, amma kamar yadda sakamako ya nuna lafiyarta k'alau kawai tana da matsalar saka shirme a zancenta ne saboda shafar aljanun amma mun sami gamsassun bayanai daga wajenta. Idan kotu ta amince zan so ta tsaya a matsayin shaidata ta gaba."

Bayan wasu 'yan mintuna Alkalin ya gama karanta dukkan results d'in dake cikin file d'in ya d'ago ya kalle shi.

"Maryam Idris zata iya tsayawa a matsayin shaida."

Adam ya gyada kansa alamun godiya sannan ya juya ga Anna wadda aka gama rantsar da ita. Sanin halinta da yadda ya sami amsa daga wajenta a jiya yasa kai tsaye ya tambaye ta.

"Me kika sani game da shari'ar nan?"

Anna ta girgiza kai tana kallonsa.

"Ni babu abinda na sani game da shari'ar nan, babu wanda yake fad'a min me ake ciki, na gaya maka hakan tun ranar da ka tambayeni, ko ka manta ne d'an bature?"

Da yawan mazauna wajen suka murmusa jin sunan da ta kira shi, Adam ya girgiza kansa muryarsa a hankali yace.

"Ban manta ba na sake tambayarki ne kawai ko kin samu wani abin."

"Ban san komai ba..." Tana magana tana yin alama da hannayenta.

".... iya hirar Sule da mahaifiyarsa da na gaya maka tun wancan lokacin ita kawai na sani."

"Ko zaki iya yiwa kotu bayani kamar yadda kika yi min?"

Ta d'aga kanta.

"Me zai hana? Ai dole ne ma in fad'a."

Sai ta juya ta kalli Alkalin.

"Zan fad'a maka komai yanzun nan kotu, shekaru 'yan kad'an da suka wuce kafin Hajiya ta rasu ku fara wannan shari'ar, Yaya Danjuma ya bani wani d'aki a jikin katangar b'angarensu Sule, to ina nan zaune a ciki kullum, sai wani gefe na d'akin ya rufta har ina iya lek'o d'akin mahaifiyar Sule daga nan, kuma kullum ina jin zancenta dana 'ya'yanta.

Amma zancen dana fi ji shine in Sule ya shigo wajenta sai tayi ta masa fad'a tana cewa ya zama bawa a Babban gida, yana ganin kowa yana da abinyi amma shi yana zaune kawai ya kasa magana a basu gadonsu suma su sami kud'i, shi kuma yace mata ai ba zai iya bijirewa umarnin Hajiya ba, kullum-kullum suke ta yin wannan zancen har Hajiya tazo ta mutu..."

Sai ta had'e tafukan hannayenta biyu ta kwanta akansu alamun bacci. Adam ya juyo daga wajenta ya kalli Alkali yace.

"Ya mai girma mai shari'ah, Tun a farko munji daga shaida ta biyu cewa mahaifin Sule ya rasu amma Hajiya ta hana a raba musu gado kuma saboda irin biyayyar da yake mata baice komai. Idan muka yi la'akari da wannan bayanin zamu ga cewa bayan anyi hakan mahaifiyarsa ta shiga tursasa shi cewa bai kamata ya yarda da hakan ba."

Yana gama fad'in haka ya juya wajen Kutama ya bashi izinin nasa tambayoyi, amma ga mamakin kowa sai ya girgiza kansa kawai alamun bashi da tambaya akanta.

Ya yarda cewa a wannan gab'ar, babu wani abu da kokarinsa zai canja, Adam ya riga ya tunkari shari'ar baki d'ayanta ba tare da wani kewaye-kewaye ba irin nasa kuma yana baiyana komai ne a ainihin gaskiyarsa, don haka kudirin daya dauka a baya nana ganin ya toshe duk wata hanyar samun nasararsu ba zai tab'a tabbata ba, a yanzu haka ma shi ba ta wannan shari'ar yake ba, tunaninsa hange kawai yake na yadda zai kare tauraruwarsa daga dusashewa.

Adam ya d'anyi shiru sanda ya lura da rubutun da Alkalin yake yi, bai sake cewa komai ba har ya sai da ya k'arasa ya d'ago ya kalle shi sannan yayi magana.

"Ina neman kotu ta bani damar kiran shaidata ta k'arshe."

Babu shiri Kutama ya had'iye yawu cikin mak'ogwaronsa yayin da Alkalin ya zare gilashinsa ya kare masa kallo daga inda yake zaune.

"Shaida ta k'arshe? kana nufin daga wannan shaidar ka rufe shari'ar daga b'angarenka?"

Adam ya gyad'a kai gami da lumshe ido.

"Haka nake nufi ya mai shari'ah."

Sai ya maida gilashinsa sannan ya ware hannunsa a iska.

"Kotu ta baka dama."

Ya amsa hakan ta hanyar cewa.

"Zanso in kira Sulaiman Muhammad Idris a matsayin shaida ta ta k'arshe."

Babu b'ata lokaci kuwa aka shigo da Sulaiman wanda kowa yafi sani da SULE cikin wajen, biye dashi d'ansanda d'aya ne wanda ke nuna cewa a hannun hukuma yake, idanunsa sunyi zuru-zuru alamun tashin hankalin k'arara a cikinsu, kuma kamar yadda idanun suke haka ma muryarsa ke fita sanda ake rantsar dashi.

"Ina so ka yiwa kotu bayanin abinda ya faru bayan rasuwar mahaifinka."

Wannan itace tambayar da Adam yayi masa bayan ya gama amsa dukkan wasu tambayoyin da suka shaida matsayinsa a cikin zuri'ar da kuma irin alak'arsa da Hajiya Balaraba.

Sai ya kawar da kansa ga barin kallon 'yan Babban gida, tun daga ranar da mahaifiyarsa ta fad'i ta mutu yake jiran wannan ranar, ya riga ya san zata zo kamar yadda yake kwana da sanin cewa ranar mutuwarsa zata zo.

Shi yasa a baya ranar da aka fara bud'e shari'ar nan, da kyar ya yarda ya tsaya a matsayin shaidar Kutama, don sai da Kawu Danjuma yasa baki tukunna sannan ya yarda yazo, tun a lokacin gani yake kamar daya bud'e baki zai fad'i gaskiyar komai ne, amma sai talalarsa ta k'aru.. Ubangiji ya k'ara masa lokaci Adam bai zarge shi ba a sannan.

Amma a yanzu daya riga ya gama nemawa k'annensa mafita, ya yarda komai yazo k'arshe, shi yasa lokacin da 'yan sanda suka zo tafiya dashi baiyi musu ba yabi su, kuma baiyi wani musun ba a lokacin da Adam ya tsare shi da tambayoyin da kullum suke haskawa a cikin mafarkinsa. Ya bashi amsa tiryan-tiryan kamar yadda yake maimaitawa a yanzu.

"Hajiya ta hana a raba gado bayan mahaifinmu ya rasu, saboda bashi da wani kud'i ajiyayye sai gidaje kawai guda biyu wad'anda 'yan haya ke ciki, saboda haka tace baza a sayar da muhalli ba sai dai a cigaba da karb'ar kud'in hayar kawai wanda shi kuma ba wani abu ne mai yawa ba kasancewar tun farko mahaifinmu bai d'auki gidajen da muhimmanci ba yafi maida hankali kan sana'arsa. Bayan wani lokaci sai kud'ad'en dake hanunmu suka k'are ni kuma ba wata sana'a nake yi ba gashi auren k'anwata dake bina ya taso kuma babu wani tallafi da muke samu, saboda haka mahaifiyata ta matsa cewa dole ne mu samarwa kanmu mafita ba zai yiwu muyi ta zama a haka ba.

Babu irin bayanin da banyi mata ba akan girman abinda take son mu aikata amma ta tursasa ni cewa idan muka kawar da Hajiya daga duniya komai zai bud'e mana don in babu ita, ba wanda ya isa yayi magana akan gidajen muna da damar sayar da abinmu.

Ita ta tsara komai da cewar mu saka mata guba a abinci ta yadda baza a zarge mu ba, sai dai a zargi wanda ke da alhaki da abincin, babu yadda na na iya, dole na yarda da ita kuma na bada shawarar mu d'orawa Bintu hakan tunda ita ke kula da abincin safen Hajiya kuma kowa ya riga ya san yadda Hajiya bata sonta, sai ayi tunanin ta kashe ta ne saboda hakan.

Ko kad'an bamu san shirin Habiba na son kashe Hajiya itama a wannan ranar ba, don haka ban san cewa ba Bintu ce tayi kokon ba kamar yadda ta fad'a, abinda na sani kawai shine a wannan safiyar na sami filas d'in Hajiya wanda na san ana zuba mata koko a ciki, na zuba garin gubar da mahaifiyata ta bani yadda in an zuba kokon zai had'e da ita sannan naje na sami Bintu wadda ke wanki a lokacin..."

Duk wannan bayanin da yake yi, idanun Fadeelah na sunkuye tana kallon teburin gabanta, sai da yazo daidai nan sannan ta d'ago ta kalle shi, take komai na wajen ya janye daga idanunta lokaci ya d'auke ta daga cikin kotun zuwa wani zamani can baya.

"Ke!"

Wata k'atuwar murya a gefe ta janyo ta daga cikin tunaninta, ta zabura da sauri sanda atamfar rigar da take wankewa ta sub'uce cikin bokitin kafin ta d'aga idonta akan siffarsa, Yaya Sule.!

Wani mutum guda d'aya da baya tab'a barin tayi yini guda a rayuwarta ba tare da hargitsi ba, a lokuta da yawa da tunaninta ke tafiya rubutun wasik'ar jaki, tasha hasko cewa rayuwarta a cikin gidan zata fi sauk'i in har zai matsa wani wajen, don shi ba mutum

Please Login or Register in order to submit comment