Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kira waya kana neman Magareth ne da zummar son sanin wani abu game da iyayenka, to a farkon watan da ya wuce ne d'aya daga cikin ma'aikatanmu ta binciko wata tsohuwar wasika a cikin kayan marigayiyar, wadda aka buga ta da sunanka tun shekaru goma da suka wuce.

Muna fatan cewa zaka sami amsar da kake nema a cikin wasik'ar, don haka tana nan a wajenmu cikin kyakkyawar ajiya, duk sanda ka sami dama kazo ka karb'a.

Sa hannu,

Gidan kula da tsofaffi na garin leicester, k'asar Ingila.

●﹏●

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

*18

Assalamu Alaikum, ina gaishe ku sosai tare da fatan alkhairi.

Daga wannan zuwa update na gaba zamu saurari labarin Adam ne. So yake yi ku san asalinsa kafin ya sake dannowa cikin shafukanku a karo na biyu.

Shi yasa zamu d'an dakata da b'angaren Fadeelah da Al'ameen na d'an lokaci kafin mu sake waiwayarsu.

Kar ku manta tattare da kowanne labari na duniyar nan akwai kunci da kuma tarin fad'i-tashi, don haka a labarin Adam ma wad'annan abubuwan baza su b'ace ba.

(☆_☆)

Karfe biyu da rabi na ranar litinin, jirgin 'virgin america' ya dira a harabar babban filin saukar jirage na garin leicester dake k'asar Ingila, kamar kowacce rana, wajen cike yake da mutane da kuma d'imbin ma'aikatan dake ta zirga-zirga a kowanne b'angare, sannan ga jirage a zube wanda da alama wasu basu dad'e da sauka ba yayin da wasu kuma ke shirin tashi.

Ta cikin jerin fasinjojin da suka fara biyo matattakalar saukar jirgin, Adam ya sanyo k'afarsa sanye cikin wani dogon takalmin Boot kalar ruwan k'asa, gashin kansa a taje cikin wani style mai kyau, sannan idonsa na b'oye cikin bak'in gilashi.

Ya tsaya daga inda yake ya kalli yanayin garin da kuma hada-hadar mutane, murmushi ya b'alle a bakinsa, wani murmushi mai zurfi daya manta yaushe rabon da yayi irinsa sai a yanzu da komai na kewayensa ke nuna masa cewar ya iso inda zai gyara rayuwarsa.

Yanayin fuskarsa yayi kyau cikin siririn hasken ranar daya b'ullo ta tsakanin hazon daya mamaye garin bakid'aya, yana sanye cikin wata doguwar coat k'irar kamfanin 'London fog' rik'e da 'yar karamar jaka a hannunsa.

"Idan zaka iya matsawa kad'an zamu wuce."

Muryar wani dattijo daga bayansa ta fad'a, sai a lokacin ya tuna akwai mutanen dake tsaye a bayansa zasu fito, cikin nutsuwa ya biyo jikin matattakalar ya sauka a k'asar garin dake rik'e da sirrinsa tsawon shekaru.

Bayan ya karbi 'yar k'aramar jakar daya sanyo kayansa a ciki, ya fita waje inda ya hayi taxi zuwa hotel d'in da yayi booking d'aki tun kafin zuwansa, babu wani b'ata lokaci ya karb'i muk'ullin daki na d'ari biyu da uku (203) ya shiga, komai a tsare yake k'al kamar kowanne hotel, bai b'ata lokaci ba ya fad'a band'aki yayi wanka sannan ya shirya cikin wasu kaya kalar ruwan k'asa, a samansu ya dora doguwar jacket mai kyau data zarce har k'asan gwiwarsa.

K'ararrawar d'akin ta amsa sanda yake taje kansa a gaban wani dogon mudubi, d'aya daga cikin masu aikin hotel d'in ne d'auke da wani faranti mai cike da tarin cima kala-kala, a layi d'aya ya gaya masa cewa shi bai nemi abinci ba, amma sai ya shaida masa cewa wannan kyauta ce daga garesu kamar yadda suke yiwa duk wani sabon bak'o, ba yadda ya iya haka ya bud'e masa k'ofar ya shigo ya ajiye, bai ko bi ta kan abincin ba ya juya ya cigaba da shirinsa, abinda yake gabansa a yanzu yafi k'arfin cimar kwanaki biyu ma.

Lokacin daya fita harabar hotel d'in, agogon 'Brew Watches' dake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya shaida masa cewa k'arfe hud'u da rabi ne na ranar, babu wahalar taxi a wajen don haka take ya samu mai motar daya nunawa address d'in hannunsa suka nufi inda zuciyarsa ta dad'e tana mafarkin zuwa tsawon shekaru biyu... Gidan kula da tsofaffi na garin leicestar!

Sanda suka isa wajen, mai motar ya wuce doguwar harabar wajen mai cike da bishiyu da kwantacciyar ciyawa har zuwa daidai barandar shiga cikin ginin take, wani security ya k'araso da sauri ya bud'e masa k'ofar ya fito.

"Barka da zuwa yallab'ai."

Da alama hakan wata hanyar girmama bak'insu ce, ya amsa masa da murmushi kafin ya juya ya sallami mai taxin.

Yadda yake tunanin da hasashen wajen, haka kuwa ciki ya kasance, d'an banbancin kad'an ne da nasa tunanin.

Cike da d'oki yabi gajeren layin mutanen dake ganin receiptionist d'in wajen, idonsa na kan yadda take karb'ar kowanne mutum da murmushi iri d'aya kafin ta bashi damar ganin wanda yazo ya nema, ya matsa gaban desk d'in nata sanda matar gabansa ta kauce.

"Barkanka da zuwa gidan kula da tsofaffi da masu rauni na garin Leicester, wajen wa kazo?"

Sai yaji guntun murmushi ya sauka a kumatunsa jin muryar matar da ya saba ji a waya, yau gashi a gabanta IDO DA IDO.

"Barkanki da aiki, sunana Adam steve..."

"Ohh Adam!" Ta katse shi da k'arin wani murmushin a fuskarta, Da alama yawan wayar da ya dinga damunsu dashi a shekarun baya baisa sun manta da sunansa ba.

"Barka da zuwa Mr. Steve, fatan ka iso lafiya?"

"Lafiya kalau."

"Naji dad'in haduwa da kai a zahiri, sannan ina maka ta'aziyyar mutuwar Magareth."

Ya gyad'a kansa sau d'aya. "Nagode."

"Tun jiya muke saka ran ganinka, gashi yau Manager baya nan, da kun gaisa."

Ya sake gyad'a kansa a hankali da wani murmushin sannan yace.

"Ba komai, ina fatan abinda nazo karb'a yana nan."

"Kwarai kuwa, minti d'aya ka zauna a can wajen yanzu za'a kawo maka."

Ta fad'a tana nuna masa wajen wasu kujeru dake can gefe, ya k'arasa ya zauna a bayan inda wata tsohuwa ke zaune tare da 'yarta da jikanta da suka kawo mata ziyara.

Watakila suna amfani da agogo mai kad'awa ne a jikinsu, don baya jin minti d'ayan ta wuce sanda wata ma'aikaciyar ta iso wajensa tallafe da bayanin asalin wanzuwarsa a duniya.

"Barka da zuwa Mr. Steve, munji dadi zuwa da kanka da kayi ba sak'o ba, sannan muna k'ara gode maka akan kare dukiyar Magareth da kayi baka karb'a ba."

Ta fad'a da fad'ed'en murmushi a fuskarta irin wanda suke yiwa dukkan bak'insu kafin ta mik'o masa wani tsohon envelop mai girma, da sauri ya d'ago da hannunsa ya karb'a, tudu da kaurinsa ya shaida masa cewa koma meye a ciki to yana da d'imbin yawa ba kad'an ba. A hankali ya shiga juya shi cikin hannunsa, babu b'angare ko guda d'aya da aka zana digo balle sunansa kamar yadda suka fad'a a cikin wasik'ar da suka aiko masa...

... d'aya daga cikin ma'aikatanmu ta binciko wata tsohuwar wasika a cikin kayan marigayiya Magareth, wadda aka buga ta da sunanka tun shekaru goma da suka wuce.

Sai ya d'ago ya kalleta yace.

"Nayi zaton kun ce wasik'ar tana d'auke da sunana, amma yanzu banga inda aka rubuta a jiki ba?"

Har a lokacin da murmushin a fuskarta tace.

"Wannan wasik'ar ita ta bamu amsar da muka shafe tsawon shekara guda muna neman akan 'yan'uwan Magareth mr. Steve, ita kuma ta tabbatar mana cewa kai ba jininta bane kamar yadda ka fad'a a baya, Magareth bata sanka ba bama ta tab'a ganinka ba amma ta rubuta wasik'ar ne da sunanka, sunanka na asali data sani ba wanda kake amfani dashi yanzu ba, in ka karanta zaka fahimci komai."

Kamar ya sake tambayarta wani abu yaga meye amfanin hakan alhali ga amsar komai yanzu a hannunsa saboda haka ya karb'i takardun d'aya hannunta yayi signing akai kamar yadda tace, sannan yayi musu sallama ya fita, abu da'ya daya zauna a kansa shine itama ya san muryarta kamar yadda ya gane ta receiptionist d'in farko.

****

Bayan ya koma masaukinsa, ya kashe wayoyinsa baki d'aya, ya rufe tagogin d'akin bakid'aya, ya rufe k'ofa ya kange kansa da duk wani abu da zai katse shi sannan ya b'are ebvelop d'in ya zaro doguwar wasik'ar da tayi kusan tsawon wani d'an adam din.

Kwanan watan dake rubuce a farko ya shaida masa cewa an rubuta wasik'ar ne kusan shekara goma da wasu watanni baya. A hankali idanunsa suka shiga bin rubutun da aka yi shi da zubi irin na typewriter d'aya bayan d'aya.

*_~_*

Ban sani ba ko wasik'ar nan zata tab'a isa gareka d'an Maria, don ganina da kai na k'arshe a cikin jinin haihuwar da Mahaifiyarka ta mutu ta barka ne, watakila bayan rabuwarmu kaima ka mutu a wannan daren, watakila kuma ka rayu ka zama mai kishin kai kamar mahaifinka har ka lalubo inda zan ajiye maka wannan wasik'ar a doron k'asa.

Naso ace baki da baki zan shaida maka labarin iyayenka don ba komai ne zai saku cikin wannan gajeriyar wasik'ar ba, amma a kullum tsufa dad'a cinye ni yake gashi ban san lokacin da zan yi nasarar nemoka ba, kuma bana son in mutu ban cika alkawarin dana d'aukarwa mahaifiyarka a daren da zata bar duniya cewa in har ni da kai munyi tsawon rai zan gaya maka asalinka ba, zan fad'a maka asalin mahaifinka don kaje ka nemi 'yanuwanka kar ka k'are rayuwarka a garari kamar yadda dukkaninmu muka yi.

Ba sai mun je da nisa ba d'an Maria... Yak'i! Shine mafarin samar da halittarka a duniya.

SHEKARAR 1987

A wannan lokacin, ni da mahaifiyarka muna d'aya daga cikin k'ananan ma'aikata masu goge-goge a sansanin sojojin dake yak'i da wata k'asa akan iyakar America.

Maria k'awata ce da muka taso tare a gidan marayu, kamar ni itama ta tsinci kanta a can ne bayan yak'in daya faru a yankinmu aka kashe danginmu bakid'aya. Saboda yawan da ire-irenmu suka yi, sai aka dinga d'ibanmu zuwa wajaje da dama inda ake neman k'ananun ma'aikata, sanadin haka ni da mahaifiyarka muka tsinci kanmu a yankin sojoji inda muke aikin dafa musu abinci da duk wani aiki daya kama k'ark'ashin gadin wasu sojojin mata.

Rayuwa wannan yankin rayuwa ce mai cike da k'unci da kuma tashin hankali, duk da cewa ba'a dab da makwantar sojin muke ba, amma a kullum ba abinda ke tashi a wajen sai k'arar fitar harsashi da kuma tashin bamabai, rana ta farko da aka kaimu kusan kurumcewa muka yi, bama iya magana da junamu sai daga baya muka koyi magana da ihu kamar yadda kowa a wajen yake, ba wani abu ne daban ba a kullum ka samu labarin mutuwar wani, koda kuwa a cikin mu ne 'yan aiki, harsashi kan iya tashi goron zabi ya sameka a koina sannan za'a iya jefo bom d'in da zai tashi waje guda a lokaci d'aya.

Ba ranar da zata fito ta fad'i ba'a binne gawa wajen ba, har sai da ta kai saboda k'arancin waje sai an tara gawarwaki da yawa sannan a binne su a rami d'aya, kuma kamar yadda ake k'aro sojojin a kodayaushe haka muma 'yan aikin ake k'aro mu da zarar adadin yayi k'asa. Tun zuwanmu wajen babu abinda muke yi sai aiki, aiki irin wanda lokacin magana da na kusa da kai ma babu shi, gashi kusan kullum ruwa ake yi amma ba ga mu 'yan aikin ba hatta sojojin nan duk k'arfin ruwa baya tsaida al'amura.

Bamu dad'e a wajen ba muka fahimci cewa kusan rabin sojojin wajen da wanda ake k'arowa asalinsu ba 'yan k'asar america bane, wasu sojojin haya ne daga wasu k'asashen, wasu kuma masu laifi ne daga gidan yari irin wanda aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai, daga baya aka basu zabin shiga aikin sojan ko kuma su k'are rayuwarsu a d'aure.

A cikin irin wad'annan fursunonin Mahaifinka yake, Sunansa AHMAD, musulmi ne, dan wata k'asa mai suna NIGERIA. Bamu san laifin da yayi yazo nan ba, amma kowa a wajen ya sanshi akan mutum mara magana da hayaniya wanda koda yak'i ya tsagaita a wasu ranakun, baya tab'a sakin jikinsa kamar yadda sauran su kanyi, abu na farko daya fara jan ra'ayin Maria akansa kenan.

Hanya guda d'aya da muke ganin sojojin nan shine, a ranakun da yaki yayi sauki suka dawo nan cikin sansanin su ci abinci, mu kuma zamu je mu kwashe kwanukansu mu wanke, sai dai hakan ba sosai yake faruwa ba don wani lokacin sai a fi k'arfin kwanaki arba'in babu irin wannan ranar, amma duk da k'arancin hakan Maria ta fara lura da Ahmad a irin wannan lokacin. Sai tace dani.

"Gashi can yau ma zaune, ba tare da kowa ba."

Tun ina biye mata muna yin hirarsa lokaci-lokaci, har na fahimci abin nata yayi yawa na rabu da ita. Amma Maria bata daina ba, ta cigaba da bibiyar al'amuran Ahmad har ya kai duk sanda aka samu irin wannan ranar in zamu je kwashe kwanuka, da wuri zata fita don ta riga kowa d'auke na gabansa, ta wannan hanyar ya fara lura da ita har suka karya dokar da ake jaddada mana a kullum cewar kar mu yadda wata alak'a ta had'a mu da sojojin, don bana mantawa bamu fi wata d'aya da zuwanmu wajen ba aka kashe wani soja tare da wata 'yar aiki da ya yiwa fyad'e, basu ko duba cewa babu laifinta a ciki ba aka harbeta da harsashi d'aya a zuciya kamar yadda aka yiwa sojan.

Maria tana da hikimar zance, watakila maganar harshenta ce yasa ta ja hankalin Ahmad har ya san sunanta, don a watarana mun je don kwashe kwanukan, sai ya taso ya tsaya a gabanmu ya miko mata nasa kwanon kuma ya kirata da mai sunan 'yan garinsu, watakila ba don na janye hannunta mun bar wajen ba, tun a wannan lokacin k'addara zata datse komai tsakaninsu ba tare da an samar da kai ba.

Na san cewa Maria kyakkyawa ce 'yar k'abilar mutanen turkiya, amma a wannan halin da muke ciki kullum jage-jage ban san abinda yaja ra'ayin Ahmad ya fara sonta ba, Na fahimci hakan ne ta yadda duk ranar da aka samu sauk'in yak'i, Maria ke cika da mutuk'ar d'okin tafiya kwasar kwanuka don kawai ta ganshi, sannan idan mun je shi kuma baya tab'a iya janye idonsa daga kanta har mu gama komai mu tafi, na dad'a tabbatar da abinda ke tsakaninsu ne ranar da Maria ta sulale da duhun Asuba ta bar aikin da muke yi ta fita ta baya, ana kwara matsanancin ruwa wannan lokacin saboda haka mamakin abinda zata yi yasa nabi bayanta.

Daga can nesa na hangeta tsaye ita dashi, sunyi kusa da juna sosai sannan ya rik'e hannayenta duka biyu kamar yana mata sallama don a lokacin koina ya cika da k'arar takun sojojin dake ta fita suna tafiya gab'ar yak'in. Nabi duk wasu hanyoyi da na sani don in nusar da ita ta daina shiga al'amarin Ahmad amma bata fahimce ni ba Saboda a wannan komawar da suka yi ne yak'i ya rincab'e, aka kashe mutanen cikinsu masu d'imbin yawa, ya zamana kullum cikin dawo da gawarwaki ake ana binnewa, wasu ma ance a can ake barinsu kawai.

A lokacin Maria ta daina bacci ta daina komai, kullum idonta na kan 'yar k'aramar tagar dake kallon hanyar da ake shigo da gawarwakin, tun ban damu ba har nima nazo na fara fatan dawowarsa, don daga yadda naga yanayin k'awata a wannan lokacin na tabbata zata iya kashe kanta a duk ranar da aka shigo da gawar Ahmad.

●﹏●


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

17

(☆_☆)

Fatanmu mu duka ya karb'u a ranar da yak'in ya tsagaita, duk da anyi musu mummunar ta'asa amma sun taho da murnar cewa abinda suka yiwa wad'ancan yafi nasu muni, don har mu 'yan aiki a wannan ranar munyi farin ciki. Ahmad ya dawo shima, a cikin cincirindon sojojin dake dawowa a wahalce kuma Maria bata yi wani tunani sau biyu a kwakwalwarta ba ta tafi ta rungumeshi!

Ubangiji yaso kowa yana ta kansa ne a lokacin saboda haka ba'a sami wad'anda suka lura dasu ba, a sannan ne kuma na fahimci cewa duk wani bayanina ba zai tab'a tasiri akan Maria ba, ta riga ta had'e zuciyarta da ta Ahmad kuma ban isa in raba su ba, saboda haka na zura ido kawai na kalli abinda k'addara ta tanadar tsakaninsu.

Don kamar had'in baki a wannan lokacin sai sojojin suka shafe kusan kwanaki ashirin basu koma fagen yak'i ba, saboda haka alak'ar Maria da Ahmad sai ta samu bigiren yad'uwa, har ta kai nima na sauko daga tunanina ina jin dad'in kasancewarta dashi, saboda wata irin tsantsar kulawa da yake bata ta hanyoyi da dama, har saida ta kai yanayinta dama shigarta sun fara banbanta da namu, duk da cewar albarkacinta nima na canja sutura a irin kayayyakin da yake bata wanda yake yin aike ga masu gadin wajen su siyo mata. Kuma cikin ikon ubangiji babu wanda ya tab'a zargin komai daga gare ta balle har alak'arsu ta tonu.

A wannan lokacin ne kuma Maria ta same ni da zancen cewa ta canja addini ta koma na Ahmad, kuma ya gaya mata zai aure ta su koma can k'asar su bayan an gama yak'in, bance mata komai ba don bana iya hanata komai d'in daya dangance shi.

Sai dai Ahmad bai samu damar koya mata komai game da addinin ba yak'i ya sake dawowa suka tafi barmu cikin jiran tsammani, kuma a cikin wannan jiran ne wani babban al'amari ya faru.

Wanda shine samun cikinka, yazo a lokacin da muka shekara d'aya da rabi a sansanin, lokacin da muka riga muka saba da rayuwar wajen muka zama mutanen daji na k'arfi da yaji, har a sannan kuma su Ahmad basu dawo daga gab'ar yak'in ba. Ni na fara ganewa Maria tana da ciki kafin ma ita, kuma bayan mun tabbatar da hakan na shiga bata shawarar hanyar da zamu bi mu gudu tunda muna d'aya daga cikin manya da ba'a takura musu sosai amma Maria tak'i yarda, tace min baza ta tafi ta bar Ahmad ba alhali baima san da cikinta ba.

Kamar yadda na sani, itama ta san a wannan lokacin in sojojin dake gadinmu suka fahimci ciki ne da ita ba abinda zai hana su kashe ta amma soyayyar da take wa Ahmad ya rufe idonta gam da hangen hakan, saboda haka na rabu da ita muka cigaba da zaman jiran tsammanin da muke ciki a kodayaushe.

Wanda k'arshensa ya haifar da abubuwa da dama, na farko dawowar sojojin nan ba tare da Ahmad ba ko gawarsa, gashi ba wanda zamu je mu tambaya ace meye alak'armu dashi? Nayi iya kokarina in nusar da Maria ta hak'aura cewa Ahmad ya mutu amma ta kasa fahimtata, tace ai ba dukkaninsu ne suka dawo ba mu dai zauna zamu ganshi.

Na biyu komawar sojojin da sake dawowarsu bayan watanni biyu babu Ahmad, na uku sauran ma'aikatan da muke tare suka fahimta cewar Maria na da ciki, na hudu, ganewar d'aya daga cikin sojoji matan dake gadinmu da k'ulleta da suka yi a wani d'aki wanda kowa ya san duk aka saka a ciki to baya wuce kwanaki biyu ba'a harbe shi ba, na biyar... Fito da ita nayi da kuma guduwarmu!

Na samu taimakon wata abokiyar aikunmu ne muka sato muk'ullin d'akin da aka kulle Maria cikin dare, daga nan muka bi ta wata hanya ta cikin k'arkashin k'asa da suka yi inda shima muka samo mukullinsa, matar nan ita ta taimake mu ta kulle k'ofar daga waje bayan mun shiga, amma duk da abinda ya faru da kyar na samu Maria ta yarda ta bini muka gadu daga wajen, tunaninta gabad'aya ya ta'allak'a ne cewa zamu tafi mu bar inda Ahmad zai dawo nemanta, don bata yarda cewa ya mutu ba har a sannan.

Allah ya taimake mu har muka yi kwanaki biyu muna tafiya cikin dajin da bamu san kansa ba sannan sojojin suka farga da guduwarmu suka bazama neman mu, mun gane hakan ne ta yawan harbin bindiga da muke ji a kusa damu da kuma hango motocinsu da muka fara yi a can nesa damu, a lokacin tunanimu ya tafi kan me yasa zasu tada hankalinsu don mu 'yan aiki biyu sun gudu kawai, amma muka kasa sanin dalili.

Bama taba tsayawa a waje d'aya kullum cikin tafiya muke sai idan mun samu ruwa a waje ne kawai muke d'an tsayawa mu huta gajiyarmu, ubangiji ya sani daga ni har Maria bamu yi tunanin zamu tsallake dajin nan ba tare da an kama mu ba, amma cikin sa'a sai gashi har muka isa wani k'aramin gari basu ganmu ba, anan muka zauna tsawon wata guda muna aiki a wani k'aramin gidan cin abinci, inda da kyar suka bamu wajen kwana cikin sitonsu.

A wannan lokacin alak'ata da Maria kawai shine duk abinda nace mata muyi zata yi, amma ta daina min magana da kuma sani a harkokinta, laifina take gani cewar na rabota da wajen da Ahmad yake, nima kuma ban damu ba saboda hankalina na kan yadda zamu daidaita rayuwarmu kawai, sai dai hakan bai yiwu ba saboda rashin lafiyar da muka fara a lokacin, Maria ce ta fara fama da wasu irin kuraje k'anana masu k'aik'ayi da suka feso a bayanta kafin daga baya su fara bin kowanne b'angare na jikinta, daga nan nima suka fito min a fuska sannan hannaye da duka jikina.

Ba tare da wani b'ata lokaci ba kuwa mai gidan cin abincin ya kore mu, muka je asibiti anan aka shaida mana cewar basu tab'a ganin cuta irin wannan ba, babu wanda yayi mana zancen biyan kud'in magani suka ce dole mu zauna don a bamu taimakon gaggawa, nayi tunanin da zuciya d'aya suka yi hakan, ashe tun kafin zuwanmu an riga an sanar da kowanne asibiti a kewayen cewa da zarar mun zo a kama mu.

Maria ce ta binciko wata takarda a d'akin da aka zaunar damu, wadda aka buga ta da sunanmu cewa mun gudo daga sansanin sojoji ne d'auke da wata cuta ta annoba da zamu iya shafawa mutane ko a iska ne don haka a sanar da hukuma da zarar an ganmu, anan muka fahimci dalilin da yasa sojojin nan suka damu da nemanmu.

Mun gudo daga asibitin cikin sa'a kuma mun sha wuyar b'oyewa mutane kafin mu had'u da wata tsohuwa wadda ta tausayawa Maria saboda tsohon cikinta ta sauke mu a gidanta, cikin 'yan kwanaki kuwa ciwonta yayi tsanani sosai har nakud'ar haihuwarka ta kamata, a cikin wannan ciwon Maria ta rik'e hannuna ta rok'e ni da in kula da abinda zata haifa kuma in shaida masa asalin mahaifinsa don kar ya k'are rayuwarsa irin tamu. Kwananta biyu cikin tsananin ciwon kafin ka fito duniya, a ranar kuma hukumar asibitin nan suka gano inda muke aka shaidawa sojojin dake nemanmu.

Maria bata ko shura ba bayan fitowarka ta mutu saboda tsananin wahalar da tasha, Na san cewa idan har na gudu a lokacin nan to neman mu ba zai tab'a k'arewa ba, amma idan har suka ganni tare da gawar Maria, kai zaka iya tsira daga nemansu, hakan yasa na rok'i tsohuwar nan data d'auke ka ta gudu don mu d'auke hankalinsu daga kanka. Ganina da kai na k'arshe kenan, sanda tsohuwar ta lullub'e ka cikin wani zani ta fita da kai ta k'ofar baya, ba tare ko anyi maka wanka na farko a duniya ba.

Wani abu dana tabbatar in cewa ko ka rayu a wannan lokacin dole hakan ya haddasa maka wani ciwon, don kazo duniya ne cikin wani irin hargitsattsen yanayi.

Ba wai hawaye ba, kuka ne sosai ya taho cikin idanun Adam, amma sai ya girgiza kansa alamun A'ah, komai ya riga ya wuce, ya shud'e tare da lokaci mai dad'ewa, don haka koya zubar da hawayen babu amfani a yanzu, yasa yatsansa guda d'aya ya d'auke guntuwar kwallar da taru a gefen idonsa... Ashe asalin ciwon kwakwalwarsa kenan, shi yasa iyayensa na can suka kasa gaya masa dalilin da ya haddasa masa shi, tunda sun same shi ne tare da ciwonsa. Tsaya, ta yaya ma suka same d'in?

A hankali ya maida idanunsa kan guntun rubutun daya rage ya cigaba.

Bayan sojojin nan sun kama ni an kuma binne gawar Maria, sai na fahimce cewa ashe suna neman mu ne don kar mu shiga cikin mutane mu yad'a musu ciwon ba wai don su kashe mu ba, aka kaini wani babban asibitin sojoji inda ake warkar da sauran 'yan sansanin namu, wanda kowannensu ya girgiza jin mutuwar Maria, sai dai ba wanda na bud'i baki na shaidawa cewa ta haihu kafin ta mutu, watanmu biyar a asibitin cikin kulawa kafin a sallami kowannenmu da d'imbin kud'i a matsayin ladan wahalar da muka yi a sansanin yaki.

Ranar da zan bar cikin asibitin nan, na ziyarci d'akin adana

Please Login or Register in order to submit comment