Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sansu tun lokacin da sabuwar rayuwarta ta fara, komai daidai yake, komai yana nan kamar yadda ta san shi.

Sai dai daga can karshe ta lalubo wani sabon tunanin da bata san dashi ba, a cikinsa ta hangi wata yarinya tana tafiya cikin duhu, bata iya ganin fuskarta amma tana iya kwatanto gajiyar da take ji a lokacin don tayi tafiya mai nisa ta cikin duhun titunan dake bayanta, jikinta na rawa ta cikin cukurkudadden hijabinta.

Ta kasa gane wacece yarinyar da kuma inda ta ganta, a ina ta ganta da har zata shiga cikin tunaninta?kwakwalwarta ta shiga lalube amma tunaninta ya kasa nemo amsar hakan, ta sake tafiya wani b'angaren a cikin kanta amma sai ta daki bango.

Anan tunanin ya k'are kuma babu komai sai abinda ta wuce a baya, kamar ansa wani abu ne an goge sauransa don ta san ba nan ne k'arshe ba, kamar kwakwalwarta ta lalace ne daga nan.

Taji ranta na shirin b'aci, zuciyarta ta shi bugawa da k'arfi sannan hannayenta suka damk'e cikin tafinsu.

Monitor dake gefe ya nuna rahoton haka k'arara akan screen dinsa, a lokacin taji alamun taku na tahowa wajenta sannan muryar Dr. Florence ta kira sunata a hankali.

Fadeelah.

****

"Kina buk'atar a kashe fitulun?" Dr. Florence ta tambaya tana kallon yadda ta kasa bude idanunta sosai tun bayan lokacin da ta farka.

"A'ah a barsu, ina son hasken." Muryarta ta fito kai tsaye babu alamun wani ciwo ko rikicewa.

"Na san kinyi mamakin ganina a maimakon likitan da kika saba gani Dr. Gilbert, ba wai hakan na nufin ciwonki yafi karfinsa bane, kawai ya d'an d'auki hutu ne ni kuma zan maye gurbinsa."

K'arya take, ciwona yafi k'arfinsa ne.

Fadeelah ta ayyana a ranta, wane hutu Dr. Gilbert ya d'auka bayan yanzu ta gama jin muryarsa cike da damuwa anan? ta fadi hakan ne don kawai ta d'auke hankalinta kar ta damu akan abinda suke tunanin babban al'amari ne. Bata san cewa rikicewar data tayi na farko ya wuce ba, kuma tunda ta bud'e idonta ta ayyana cewa hakan ba zai sake faruwa ba da ita ba.

Don irin wannan ciwon kan yafi duk wanda ta taba fuskanta a baya shi yasa ta kasa tsaida rikicewarta, amma kamar yadda suka fad'a ne, a baya ta karb'i ciwonta da hannu biyu ta tallafi kanta, a yanzu kuma data fahimci ciwon nata na sake k'aruwa ne zata gayawa b'arin kwakwalwarta mai lafiya haka, ba zata sake yarda ciwon yayi galaba a kanta ba, ta daure a baya kuma zata daure ma yanzu, zata daure ta fuskanci dukkan matsalolinta a yadda rayuwa ta kawo mata, ita ba mai rauni bace!

"Na fahimta." Ta amsawa likitar tunda ta nuna alamun tana jiran amsarta ne. Sai ta gyada kanta sannan tace.

"Na san zaiyi miki wuya ki tuna abinda ya faru dake a kwanakin baya, amma..."

Kalmar kwanakin baya ta d'auki hankalinta.

"Kwana na nawa anan?" Cikin sauri ta katse ta.

"Kwananki uku kawai cikin kulawar da kwakwalwarki ke buk'ata, kuma da alama'yanuwanki na mutuk'ar sonki, don duk da mun hana kowa ganinki basu daina sintiri zuwa da kuma jero addu'oinsu ba."

Ta k'arasa tana kallon gefe, Fadeelah tabi idanunta da kallo, ganinta ya sauka akan wani d'an k'aramin table dake cike taf da tarin flowers da kuma katina masu d'auke da rubutun addu'a da fatan samun sauk'i, a gefen wani mai rubuce da sunan Iman ta hango, akwai na kawayenta ma Romilda da Melissa daga gefe, sai sauran data san bayan 'yan gidansu na tarin 'yan uwan Daddy ne.

"So muna magana..." Dr. Florence ta katse ta, ta juyo ta kalle ta.

"... In akwai wani abu da zaki iya fad'a min na abinda kika tuna zai taimaka sosai wajen bamu sanin ainihin abinda ya same ki."

Jin cewa har a lokacin basu san ainihin abinda ya same ta ba yasa ta ture tunanin 'yan uwanta a gefe.

"Bana tuna komai banda irin azababben ciwon da naji a cikin kaina."

"Na fahimci hakan, zaki iya gaya min me kike yi kafin farawar ciwon?"

Ta rufe idonta a hankali.

"Muna zaune da k'anwata ne a lokacin, tana gaya min wani labari data karanta daya dangaci k'asarmu Nigeria, ta fada min cewa sunan yarinyar ciki BINTU, a lokacin sai naji sunan kamar a irin mafarkaina yake, kamar na sanshi ne a wani wajen daban, wajen k'okarin tuna inda na san sunan sai ciwon ya fara."

"Fadeelah..." Dr. Florence Ta kira sunanta da kyar cikin murd'adden turancinta.

"Bari mu koma baya kad'an game da ciwon ki, kin samu matsalar kwakwalwa dalilin wani abu daya faru dake a baya, bamu san me ya faru ba saboda ba zaki iya tunawa ba amma muna hasashen kin samu damewar kwakwalwa ne ta hanyar buguwar kai, wanda ya haddasa miki ciwon 'Retrograde amnesia.'

Kalar Amnesia data saka kika manta rayuwar data faru dake kafin faruwar ciwon, tunaninki na baya duk ya mutu, sai sababbi kawai kike iya rik'ewa, I'm i right? kina sane da hakan?"

Fadeelah ta d'aga kanta ba tare da ta kalleta ba. Zancenta ya nuna mata ta karanci file d'inta ne tas! koma ta haddace shi.

"Kuma bayan anyi haka kwakwalwarki tana hargitsewa a wani lokacin ki manta komai na kewayenki, haka ne?"

Ta sake gyad'a kanta.

"Amma cikin shekara d'aya, sanda kika fara zuwa wajen Dr. Gilbert ciwonki yayi sauki, abubuwa sun fara daidaita har kin shiga makaranta rayuwarki ta fara tafiya cikin tsari. A watannin baya kuma sai kika fara mafarkai masu yawa da tsoratarwa, murya da siffofin mutane na binki suna maganar da ba kya iya ganewa. Haka ne?"

Maimakon ta amsa sai ta kalli yatsunta tace.

"A lokacin Dr. Gilbert yace gajiyar makaranta da kuma yawan karatun dake shiga kwakwalwata ne suka jawo min ba wani abu ba, amma daga sanda na fara mafarkan nan, kwakwalwarta da duk wani abu mai hankali a jikina ya bani alamar cewa wani babban al'amari ne ke shirin faruwa dani."

"Tabbas hakan ne." Dr. Florence ta fad'a kamar mai k'arashe mata zancen, sai kuma ta d'anyi shiru zuwa wani lokaci kafin ta sake magana.

"Yanzu ina son kiyi k'ok'arin tuna wani abu game da mafarkanki na baya, ina son ki bincika cikin muryoyin nan na mafarkinki ki gani zaki iya tsinto wani abu da suke cewa... ko meye kuwa, ko bashi da ma'ana zai zama shirme a bakinki just say it, ni zan nemo ma'anarsa."

Kin kashe ta!

Kalaman mafarkin da tayi na k'arshe suka amsa rangadadau a cikin kanta, a baya ta b'oyewa Dr. Gilbert don tana ganin hakan babban abu ne amma a yanzu da abubuwa suke cakud'ewa dole ne ta hak'ura ta yaye shi, dole ne ta fad'awa Dr. Florence don a yanzu ta yarda cewa a irin ciwonta babu wani abu wai shi Sirri.

Ta d'ago a hankali ta kalli likitar da yanayin fuskarta ya nuna alamun jiran amsa.

"Mafarkin da nayi na k'arshe akwai wata murya dana tsinci tana cewa na kashe wata a yayin da nake gudun."

Ta fad'a kamar wadda aka tursasa ta fad'i kalaman.

Dr. Florence ta kamo hannunta a hankali cikin sigar jan hankalinta.

"Fadeelah zan gaya miki wani abu da yake gaskiya kuma wani abu da kowa muke gayawa ba sai irin wad'anda suka karaso matakinki... Dr. Gilbert ya taba fad'a miki cewa ciwonki ba mai d'orewa bane koh? ya gaya miki cewa akwai lokacin da kwakwalwarki zata warke har ki iya tuna wacece ke a baya koh?

Ta gyada kanta tana saurare.

"Toh zan gaya miki gaskiya a yanzu, ciwon irin na damewar kwakwalwa bashi da wani takamaimai magani duk duniyar nan... bau wata kwaya da za'a baki ya zama rana d'aya kin tashi kin warke.

A baya sanda kika fara zuwa asibitin nan, treatment d'inki yana tafiya ne akan kokarin tallafar kwakwalwarki a saita ta ta karb'i sabuwar rayuwar dake kewayenki, kuma hankali muka samu akayi yi sa'ar hakan. A yanzu kuma da kwakwalwar take jin alamun cewa ta daidaita kanta sai wani b'angarenta ya fara kokarin tattaro abubuwan da suka faru dake a baya da ciwon naki ya k'ulle.

Don haka a yanzu kina wani mataki ne da ake kira 'Memory Retrival'. Daga yanzu kwakwalwarki zata dinga d'aukan duk wani abu da zaki ci karo dashi wanda kika sanshi a rayuwarki ta baya, kuma a matakin farko na Memory retival akwai 'Creative Reimagination, wanda shine abinda kika fara experiencing a yanzu.

Shi yana faruwa ne a lokacin da tunanin baya ya had'e dana zahiri, shine halin da kwakwalwa ke fara shiga kafin ta iya sanin yadda zata banbance abinda ya faru a bayan da kuma sabo da ya shiga cikinta, Sai abubuwa da yawa su cakud'e waje d'aya su fidda wani abu daban da zai iya shallake tunanin d'an adam.

Saboda haka wannan azababben ciwon daya fitar dake daga hankalinki Fadeelah ba komai bane face alamun warkewarki.

Yanzu kin samu abu na farko, wato suna BINTU, tunda har kwakwalwarki tayi reacting akan sunan to yana cikin rayuwarki ta baya kenan, dole akwai wanda kika sani a baya mai suna Bintu.

Zan baki d'an littafi wanda daga yanzu duk sanda kika ji ko kika ga wani abu da ya sa kwakwalwarki ta d'auke shi, walau na farin ciki ko bak'in ciki komai k'ankartarsa kuwa zaki rubata shi a ciki, kuma zaki dinga yawo da ita ne koina ki rubuta dukkan abinda ya faru dake a take ba sai kin matsa wani wajen ba."

"Hakan na nufin zan dinga fuskantar irin wannan ciwon?"

"Ba wannan ciwon kad'ai ba Fadeela, creative reimagination yana zuwa a siga da yawa, a yanzu kinji murya a cikin kanki a gobe zaki iya haduwa da jiri, jibi zaki iya suma gabadaya ko kuma ki shiga furta wasu maganganun da hankali ba zai d'auka ba."

Fadeelah ta gyada kanta a hankali alamun ta fahimci hakan, sannan tace.

"Zaki yi min wata alfarma?"

"Ina jinki Fadeelah." Ta kara kokarinta wajen furta sunan.

"Karki bari su daddy su san ciwona ya kai haka please."

"Baki da matsala, babu wanda zai sani."

Dr. Florence ta fad'a sannan ta kifta ido tana kallonta cikin wani abu mai kama da damuwa. Haka kurum taji tausayinta har cikin ranta, a 'yan shekarunta kawai da basu fi k'irgen yatsu ba rayuwarta na shirin tarwatsewa.

Don Retrival stage mataki ne da in ba mai k'arfin hali da dauriya ba, a cikinsa d'an adam na iya haukacewa gabad'aya a rasa hankalinsa!

***

"Kin tabbata kinji sauk'i sosai?" Zahra ta tambaya tsaye daga gefen gadon tana danna wayar hannunta, kusan karo na biyar kenan tana mata wannan tambayar tun bayan shigowarsu cikin d'akin da aka canja mata daga ICU.

"Na warke Zahra, wai bakya gani tun dazu nake miki murmushi ne." Ta amsa mata tana washe fararen hakoranta.

"Gwara in tabbatar ne saboda zanyi posting a handle dina, bana so daga baya inzo ina cewa kin sake komawa rashin lafiyar."

"Toh dole ne komai sai kinyi posting?"

Ta d'ago ta kalle ta da idanunta rabi a bud'e tsabar jin kai, sannan hannunta a k'age gefen fuskarta.

"Hello, a 21st century muke fa ta yaya kike tunanin zan iya..."

"Zahra taho daga nan wajen ki barta ta huta."

Aunty Nina, d'aya daga cikin 'yanuwan Daddy na b'angaren Babansa da suma suke zaune a garin ta fad'a. D'akin cike yake da duk wanda Mami Saffiya ta kira ta shaida musu cewa ana iya zuwa ganinta yanzu. Daga can gefe idonta ya sake gano mata Iman, ta mak'ure a jikin Mami tana kallo ta, ta sake mata alamar tazo da hannunta amma ta matse kafad'unta. Mami ta shaida mata cewa tun daga ranar da aka kawo ta asibiti kuka take yi tana ganin cewa labarin da ta bata ne ya tayar da ciwonta.

Pleeese!.

Bakinta ya fad'a ba tare da ta furta ba, Iman ta sake matse kafad'arta, ta san halinta sarai saboda haka tayi ta fad'a har saida taci galaba akanta ta taho.

"Kiyi hak'uri Aunty deelah..."

Ta fara tun kafin ta karaso.

"Sshhhh, waya gaya miki laifinki ne Iman? ki daina ganin hakan kinji, laifin kwakwalwata ce kawai da bata jin magana sosai, nasha gaya mata ta daina hargitsa ni amma bata fahimta."

"Amma ai ni na fad'a miki..."

"Iman." Ta sake katse ta.

"Kin san k'addara ai koh? toh ko baki bani labarin nan ba, Allah ya kaddara haka zai faru kuma babu mai iya canjawa."

Ba ta ce komai ba tayi shiru kawai tana mutsutstsuka zanin gadon a cikin 'yan hannayenta.

"Kin san me? a lokacin da nake gudun nan cartoon d'inki kawai nake tunawa, na zata nima turbo zan shiga!"

Ta fad'i maganar cikin cartoon d'in da ta san tana so, 'Wreck it ralph' hakan kuwa yasa ba shiri ta kyalkyale da dariya.

Itama tayi murmushin tana kallonta, zuciyarta cike fal da fatan ina ma a yanzu rayuwarta zata koma baya irin shekarunta, alkalamin k'addararta ya zama a hannunta.

***

BAYAN SATI GUDA.

Ta koma makaranta d'auke da tarin jotters a jakarta wad'anda zata dinga recording duk wani single abu na farin ciki da kuma bak'in ciki daya sameta a kowanne yini, yadda a kowacce ranar k'arshen mako da take da appointment da Dr. Florence zata kai mata dukkaninsu su tattauna wanda ya kamata. Fatan Fadeelah guda d'aya ne a lokacin, kar ta sake jin irin wanban ciwon kan, ko kuma wani abu da yafi ciwon yaci galaba akanta.

"Good morning class, kwanan watan yau shi ya kama daidai da ranar da aka kafa makarantar nan wanda ina girmama hakan, saboda haka na hutar daku babu karatu ko Assignments daga yau har zuwa gobe, zaku iya yin hirar ku amma cikin hankali ba da k'arfi ba, kuma banda cin abinci ko fito da waya please!"

Malaminsu na English Mr. Ryan ya fad'a lokacin da ya shigo cikin ajin. Fadeelah ta kifa kanta a table d'inta, wannan class ne da bata yinsa tare dasu Melissa, ita kad'ai ce kuma sauran 'yan ajin duk ba wani sabawa tayi dasu ba don haka bata san dawa zata yi hira ba. Sai kawai ta janyo textbook d'in English d'insu 'How to kill a mokingbird' ta fara karantawa yayin da ajin ya rud'e da surutu.

Lokacin da k'ararrawar gama period d'in ta kad'a, da sauri ta maida littafin cikin jakarta sannan ta riga kowa fita daga ajin.

Wayarta tayi k'ara a cikin aljihun doguwar rigarta lokacin da ta nufi lokarta don d'auko textbook d'in history da suke dashi, ta janyota ta kalli screen din, text ne daga Melissa.

Already @history, mun ajiye miki seat.

Ta maida ta cikin aljihunta, sanda ta k'arasa wajen lokar ta bud'e sannan ta rage litattafan jakarta a jiki, sai dai idonta ya kai kan wata 'yar siririyar paper data fad'o k'asa daga gefen lokar kamar dama an zura ta ne cikin dabara. Ta sunkuya a hankali ta d'auko ta, wani tsararren rubutu ne a jiki kamar an buga shi sab'anin ink din biron da take gani.

Ya jikin naki?.

Aka rubuta daga tsakiyar paper cikin harshen turanci, sai daga can gefe kuma.

Mr. Hawkin's yana nemanki.

Kanta ya d'an so ya d'aure, don wannan ba rubutun Mellisa bane ko Romilda, kuma ta san su kad'ai suka san da rashin lafiyarta a makarantar, sai ko principal da Daddy ya gaya masa a waya. Kamar ta yar da paper amma rubutun jiki ya sake d'aukar hankalinta sai kawai ta zuge wani d'an k'aramin zip a jikin jakarta ta ninke ta a ciki.

Bayan ta d'auki littafin, tayi tunanin ta fara zuwa wajen Mr. Hawkins kawai tunda su Romilda sun samar mata seat a kusa dasu kuma ta san ba zata makara ba.

"Shigo." Muryarsa ta bata umarni sanda ta kwankwasa k'ofar office d'in nasa.

"Na samo miki wani labari mai dadi ne.. "

Ya fad'a a lokacin data k'arasa gaban desk d'in nasa rik'e da hannun jakarta.

"Game da performance d'inki ne, na samo wanda zai dinga miki lesson a makarantar nan tunda kince baza ki iya samun malamin lesson ba. Shine best sudent da muke dashi a maths gabad'aya makarantar nan don haka in kin maida hankalinki kin saurare shi zaki yi passing sosai ki tsallake sirad'in maimaita ajin da kike kai."

Wani irin dad'i da farin ciki ya mamaye zuciyarta a lokaci d'aya, taji cewar insha Allah kamar ta tsallake masifar Maths ne don ba abinda zai hana ta sauraren wanda zai koya mata ita kadai sab'anin na aji mai gabadaya. Hannunta ya damk'o jotter ta a cikin jaka da shirin rubuta hakan kafin ta hau yiwa Mr. Hawkins godiya.

"Zaku dinga zaman awa d'aya ne kullum bayan an tashi daga makaranta, So sai ki gayawa iyayenki."

"Ba matsala, Nagoode sosai da sosai."

Bai saurareta ba ya d'auko wata paper daga cikin ma'adanin littattafanshi ya mik'o mata.

"Ga number shi nan a jiki na rubuta, ki kira shi kuga yaushe zaku fara, amma zan baki shawara, gwara ku fara da wuri don lokacin jarabawa ya k'arato."

Kamar yadda ruwa ke d'aukewa daga famfo in an kashe shi, kamar yadda tashin hankali ke samun Bawa a lokaci d'aya sannan kamar yadda mutuwa ke janye ruhi cikin kiftawar ido haka Fadeelah taji an zuk'e farin cikinta lokacin da idonta yayi arba da sunan dake jikin takardar.

Adam Steve.

Daga can cikin jakarta hannunta ya saki jotter nan data rik'o a hankali.
●﹏●


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

04

(☆_☆)

"An kori Zainab daga aiki."

Zainab, k'awar Mami ce da suka had'u tun a makaranta, kuma har a yanzu da shekaru ke gangarawa kowannensu cikin iyalai da nasarori, babu abinda ya shafi abotarsu.

Fadeelah ta juyo daga tsane plates d'in data gama wankewa a gaban sink ta kalleta, suna gyaran kitchen ne a lokacin bayan gama cin abincin dare.

"Ya salam! Mami yaushe? Me ya faru?"

"Zancen hijaab dai, in ba haka ba me zaisa deelah, abin k'aruwa yake kullum."

A farkon canjin shugaba da kuma tsare-tsaren sabuwar siyasa, sabuwar gwamnatin ta bawa european court of justice's decision goyon bayan cewa ma'aikata nada damar cire duk wani nau'i na shigar musulunci a wajajen ayyukansu. A farkon hakan Fadeelah bata tab'a tunanin cewa abun zaiyi yawa ba sai bayan an kori Mami kuma an cigaba da korar duk ire-irenta da suka ki yarda su cire Hijaabin d'in nasu kafin zuwa aikinsu.

"Naso kinga yadda last CEO d'in da nayi interview a wajensa yake saurarata, ya rufe idonsa yana d'aga kansa irin yadda mutane suke yi idan ba amsar da suke so kake basu ba d'in nan. Daga k'arshe kuma, tambayar dana san ita ta kore ni shine lokacin da yace.

“You or your parents must’ve immigrated from somewhere, right?”

(ke ko iyayenki kun zo daga wani waje ne koh?)

Ban damu da fad'awa kowa asalina ba saboda ina alfahari dashi, kai tsaye na gaya mishi ni 'yar Nigeria ce, kuma daga nan bai k'ara cewa komai ba, kawai wani kallo yayi min dana fassara da cewa.

Lady, ba zan taba d'aukan ki ba.

Ta d'anyi shiru sannan ta cigaba.

"Tun ina shekara goma nake amfani da Hijaab a rayuwata kuma ban taba tunanin cewa sai a lokacin da girma ya same ni sannan zaizo ya zame min k'alubale ba."

"Kar ki fad'i haka Mami, komai zai wuce ba zai yiwu ace kowa ne ya d'auki ak'idarsu ba, za'a samu wanda zasu fahimta insha Allah."

"Har zuwa yaushe deelah? Tambayar da nake yiwa kaina kenan kullum, naje interview masu yawan da Allah kad'ai ya san adadinsu, kuma inada tabbacin cewa ina da abinda suke so, amma a yanzu ba wanda yake son d'aukan mace mai hijaab, kamar shi d'in wani bomb ne da zai iya tarwatsa su."

"Mami ki gwada applying wani kamfanin a matsayin recruiter (Mai talla akan ayyuka) kinga kusan aikinsu gabad'aya a waya ne, kuma mutane suna kira ne da karamci tunda aiki suke nema baza suyi wani abin da bai dace ba, irin wannan aikin kuma kamar suna da religious minorities kamfanin baza su damu sosai ba."

Ta girgiza kanta ahankali.

"Haka ne tunaninki Fadeelah, amma a yanzu ko a bayan gini zaka yi aiki, sai ka bi tsarinsu."

Fadeelah ta ajiye bowl d'in hannunta akan dryer, zuciyarta ta tafi wani tunani ba tare da tace komai ba, Mami bata taba fad'a mata ba amma ita ta san dalilin da yasa ta damu sosai da samun aikin nan. Ta tsinci hirarsu ne ita da Daddy a wata rana da daddare data fito kitchen d'aukan ruwa, kowa yayi bacci a lokacin sai su biyu a falon kuma sun kashe fitila saboda haka basu kula da ita ba.

Tattaunawa suke akan yadda albashin Daddy yayi musu kad'an wajen tafi da rayuwarsu, kud'in ruwa, kud'in wuta, kudin gida, kudin siyan kayan abinci da abubuwan yau da gobe, sannan mafi girman abun kuma kudin makarantar kowannensu da yake mai d'imbin yawa, a lokacin tana jin yadda suke soke abubuwa da yawa ana hak'ura dasu don a samu a fito da kud'in makarantar kawai.

"Ya akayi kike aikin ke kad'ai? Ina Zahra?"

Mami data juyo a lokacin ta katse ta daga tunanin data tafi.

"Ta yanke hannunta da peeler ne, shine na k'arasa."

Sai ta girgiza kanta kawai tace.

"Ko kuma bata son yin aikin ba, ta yaya peeler ke yanke mutum."

Bayan ta gama goge kwanukan ta jera su a dryer, sannan tabi ta falo inda Daddy ke kallon news, su Zahra na daga can study suna homeworks d'insu itada Iman, Faruk kuma na kan dining yana danna wayarsa, ta wuce zuwa d'akinta zuciyarta d'auke da wani irin nauyi.

Shawarar data yanke tare dasu Melissa a kwana biyu da suka wuce ne ke tantama a ranta, sun yanke cewar baza ta tab'a kiran Adam da sunan lesson d'in Maths ba, don basa son kowacce irin alaqa ta had'a su dashi, kuma itama ta rantse in har ta hanyarsa zata iya sanin maths sai dai ta mutu a dak'ik'iya.

Toh amma meye amfanin rantsuwarta a yanzu? meye amfanin rantsuwar data san zata cutar dasu Mami ne, tunda suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun bata ilimin da bai zama dolensu akanta ba, ita kuma tana gefe tana shirin watsa musu k'asar kunya a ido koma abinda yafi hakan, tunda ya zasu ji a lokacin da aka gaya musu kud'in maimata aji zasu k'ara biya mata har na tsawon shekara daya?

Sai kawai ta kwanta akan gadon ta dukunkune jikinta, zuciyarta na gaya mata cewa kar ta sake ta soma bin shawarar da kwakwalwarta ke bata don baza su iya jurewa ba, ba zasu iya jurewa mu'amala da mutumin da suka tsana ba, amma sai kwakwalwarta ta hasko mata ranar da za'a kafe sunanta b'aro-b'aro a jerin masu maimaita aji, watakila ma sunanta kad'ai za'a saka... Toh taya zata iya kallon idanun Daddy a ranar? kuma ta yaya zata iya cigaba da sakewa da Mami tare da tambarin wannan laifin a fuskarta?

Sai tayi k'arfin hali ta mik'e ta jawo jakarta, a aljihun gefe ta rab'a paper da Mr. Hawkins ya bata, wani waje da ba zai rik'eta sosai ba, amma duk da haka a lokacin sai da zuciyarta ya gaya mata cewar jakar ta k'ara nauyi. A hankali ta zaro ta, idonta ya manne akan number da kuma sunan dake jiki, Sunan wanda zuciyarta ta tsana fiye da duk wata halitta mai numfashi a doron k'asa, sai gashi yanzu a cikin hankalinta tana shirin kai kanta gare shi, bisa dalilin data kira da sunan abinda yafi kaddara!

A hankali ta kwafe number cikin dial log na wayarta, sannan ta tsira mata ido kamar tana so ta tsince guda d'aya daga ciki ko hakan zaisa kiran ya tafi cikin wata lambar daban, kuma mai lambar ya amince shine mai koya matan.

Me su Romilda zasu ce in suka ji me take shirin yi? wane irin tunani zasu yi akanta? zuciyarta ta rad'a mata amma sai kwakwalwarta ta goge hakan, Ba zata iya raunana fatan su Mami akanta ba.

Bayan kusan rabin awa cikin muhawara kwakwalwarta tayi nasara. Hannunta yayi dialling number.

Sai dai kiran ba shiga ba ya katse, ta sake dannawa kusan sau uku amma ya dinga katsewa a hanya kafin ya kai ga shiga, watakila itama wayar tata bata goyon bayan wannan al'amarin ne.

Kiyi hakuri ba yadda zamu yi ne, ba zan iya b'ata ran su Mami ba.

Ta ayyana tana kallon screen d'in, kamar kuwa taji abinda tace wannan karon sai kiran ya shiga a take, kuma k'ararsa ya shiga bugawa tare dana zuciyarta, kamar a irin lokacin da dalibi ke kokarin binciko sakamakon jarabawarsa.

"Heelllooo..."

Tsigar jikinta ta mik'e yar! har zuwa tafin k'afarta, Muryarsa a lalace take kamar wanda ya amsa cikin bacci, ta kalli agogon gefen gadonta, karfe tara da rabi... ta yaya mutum zaiyi nisan bacci a wannan lokacin?

"Mhmmmm...."

Muryar ta sake fad'a a hankali jin anyi shiru, wannan karon sai da ta matsar da wayar kad'an don ji tayi kamar numfashinsa zai busa ne a cikin kunnenta.

"Naga kamar bacci kake yi, wani lokacin."

Ta daure ta fad'a sai dai bata sauke wayar k'asa ba.

"Nahh, ina jinki." Ya fad'a

Please Login or Register in order to submit comment