Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muk'ami a k'ungiyar makaryata.

Don zuciyarta ta damu dashi tun daga lokacin daya fara koya mata karatu har bayan shekara guda da dawowarsu Nigeria tunaninsa bai tab'a barin ranta ba, zuwan Al'amin ne kawai ya d'an d'auke hankalinta daga kansa a baya, sai kuma gashi ya sake shigowa rayuwarta da wani babban taimako... To ta yaya kuwa zata tsane shi? Matsalar kawai shine bata tab'a hasko wa kanta rayuwar aure dashi ba kuma tana ganin an bashi ita ne ta sigar da ba lallai yaga darajarta ba.

***

KARFE BIYAR DA RABI NA YAMMA.

"Kar kiyi kuka Deelah, wannan itace martabar duk wata 'ya mace, don haka kema martabarki ce kamata yayi daga mu har ke mu godewa Allah daya nuna mana wannan ranar don tsari na ubangiji babu yadda d'an adam zai yi ya canja shi, Allah ya sani daga yau zanyi bacci mai dad'i sanin cewa kina gidan aurenki lafiya, don haka ina rok'anki ki yafe min in har a zamanmu.."

"Mami dan Allah..."

Muryar Fadeelah na rawar kuka tayi saurin katse k'arashen maganar Mamin ta hanyar rungumeta, har kalmar laifi ta isa ta rab'i alak'arsu balle har ta kai ga neman gafararta? Allah ya sani in da za'a tsallake duk wannan nasihohin kowa yayi mata fatan alkhairi a kaita kawai da yafi, watak'ila in komai yazo k'arshe taje can d'in, ta duk'unk'une a waje d'aya ta fitar da nauyin kukan dake k'irjinta zata ji sauki...

Aunty Saratu ta rungumeta itama sannan ta shiga fad'in abinda kowacce mace ta haddace shi.

"Aljannarki tana hannunsa Bintu don haka biyayyarki gare shi ita zata kwato miki wannan matsayin, kiji tsoron Allah ki bishi sau da k'afa, kar ki tab'a tsallake maganarsa Bintu sai in har ta kaucewa addini ne, sannan kar ki tab'a barin rashin gaskiya ya shigo cikin zamanku..."

Mairo ta kama hannayenta duka biyu tace.

"Na san kina cikin damuwa Bintu, watakila ma zan iya kwatanta halin da zuciyarki take ciki, amma kar ki manta kowacce k'addara tana tafiya ne bisa tsarin ubangiji mu bamu isa mu yiwa kanmu komai ba, don haka kiyi kokarin kwantar da hankalinki ki fahimci sabuwar rayuwur da zaki fara yadda zaki samu farin ciki a cikinta, amma ki sani watarana b'acin rai zai iya giftawa a tsakaninku, kuma dole ne ki daure..."

Kuka take sosai a sanda Mairo ke wannan bayanin, don ta fahimci kamar wani b'ari ne na rayuwar aurenta ta d'auko take biya mata shi. Duk yadda taso a kyale ta a lokacin, babu yadda ta iya sai da ta saurari nasihar duk mutanen d'akin da Fatima ta kawo ta bayan ita dasu Rahma sun gama shirya ta cikin wata yellow laffaya mai laushi.

Bayan nan Mairo taja hannunta har cikin motar dake jira a waje, a lokacin hawayenta ya tsaya kukan zuci kawai take yi. Wata tsohuwa mai zak'in murya daga cikin 'yan aikin gidan Hajiya amarya tana ta wak'a a bakin motocin, sai dai saboda hayaniya tsakiyar wak'ar kawai Fadeelah ta iya tsinta.

...Aure martaba, darajoji mai tarin yawa...

Aure!

Wanda ke raba 'ya da Umma idan ka cire mana mutuwa.

Aure!

Ta rayu gidan mijinta su zama abokan shawara.

Aure!

Rayuwar aure da dad'i nima rana na zuwa..

.. Yadda duk na dad'e haka in nai auren sai kuga nai haske.!

Hannayenta suka shiga rawar sanyi bayan ta shiga motar, ba saboda sanyin Acn dake ciki bane, sai don a lokacin wani irin abu ya dirar mata na cewar da gaske ne ta zama matar aure kuma matar Adam, za'a tafi da ita can duniyar da daga shi sai ita sai kuma alkawarin da yayi!

Tafiyar mai tsayi ce, don ta dad'e tana sak'a abubuwa a cikin zuciyarta kafin a k'araso gidan da kowa ke kira da nata, kuma kamar dai amaryar gaske bata ga komai na cikinsa ba har aka sadata da d'akin da shima aka kira da nata, ta san dai kafin a k'arasa k'afarta tayi ta bi takan wasu tausasan carpet da taji kamar a kyaleta iya nan kawai ta nutse cikin taushinsu ta k'arasa kukan dake matse a k'irjinta.

Watakila an d'auki kusan awa guda koma fiye, kafin hayaniyar mutanen da suka rakota ta ragu a fara tafiya mota bayan mota. Su Fatima ne na k'arshen tafiya tare dasu Aunty Hassana da kuma Mairo Kuma kafin su tafin Fatima ta kasa d'aure duk wani gargad'in Mami na cewar ta kyaleta, ta jawo kunnenta ta rad'a mata.

"kin san ni malamar kice kuma na san baki manta darasinmu na baya ba lokacin zuwan Al'ameen, don haka wannan karatun shi zaki d'auko ki fad'ad'a shi a yanzu, ki ajiye duk wata kunya a gefe Deelah ki tsaya da k'afarki ki zama matar gida, mijinki bature ne bai san komai na al'adarmu ba don haka ki rik'e shi da soyayya da shagwaba irin na matan arewa har sai ya manta inda ya fito... Kiyi kwaliya, kiyi girki, ki masa hira, akwai abubuwa da yawa kuma zan dinga kiranki a waya ina kara jaddada miki su, in kika yi haka ba ke kad'ai ba, ko ni zan samu nutsuwar cewa aurenki mutu-ka-raba zai zama."

Duk yadda taso ga daurewa sai da Fatiman ta saka ta murmushi a lokacin wanda ya fito tare da ajiyar zuciya ta sheshek'ar kuka. Babu wanda kuma ya jira isowar Adam suka had'a kansu suka tafi, suka barta daga ita sai halinta.

Kuma wani abin mamaki sai ta nemi kukan da take ta tanadinsa ta rasa, saboda haka ta rungume k'afafunta ta zauna shiru kawai tana kallon d'akin da kayan cikinsa, a lokacin zuciyarta fayau take bata tunanin komai sai nazarin d'akin, komai na cikinsa kalar milk and orange ne, kuma ba wai kalar ce ta k'ayatar da ita ba, a'ah.. yadda kalolin suka kwanta cikin juna ne, yadda suke had'ewa a idon mai kallo musamman a jikin labule da kuma d'an k'aramin carpet d'in dake gefen gado da kuma k'asan stool d'in mudubi, duka furnitures d'in farare ne tas sai aka musu ratsin dogwayen layi na kalar orange d'in. A baiyane yake cewa su Mami sunyi k'ok'ari sosai wajen gwangwajeta da kaya masu kyan gaske a gidan da ba lallai zamanta ya d'ore ba.

Agogon d'akin a tsaye yake kuma bata da waya, don haka sai ta kintaci duhun da ya shigo ta cikin labule kawai ta k'addara magriba tayi don bata tunanin akwai masallaci a kusa da zata ji kiran sallah.. Ta d'auro alwala a band'aki ta fito ta bud'e wardrobe, akwatunan kayanta a tsaitsaye suke don haka ta jawo wanda taga Mairo ta saka mata dogwayen riguna da kuma hijabai ta bud'e shi, bayan ta d'auko hijabin kuma ta shiga kiciniyar maida akwatin, ta san zamanta ba mai d'orewa bane amma dole ne ta jera kayanta don d'auko su a akwati wahala zai zame mata.

Bayan ta idar da sallar, ta dad'e zaune akan carpet d'in tana jero addu'ointa, da kowacce addu'a fata take ubangiji ya zab'a mata abinda yake mafi alkhairi a rayuwar da zata fara kuma bata san tsawon wane lokaci hakan ya d'auka ba kafin ta jiyo motsi daga can hanyar da take tunanin ta falo ce. KOMAI NISAN DARE dole ne gari zai waye, ta riga ta sani dama dole ne ta fuskanci irin wannan lokacin tunda har an riga an d'aura mata aure, dole ne ta fuskanci wannan lokacin da kowa zai matsa gefe a rayuwarta ya barta daga ita sai Adam d'in kad'ai!

Al'ameen. Ta tuna rayuwarta dashi da irin mu'amalar da suka shimfida har kuwa bayan tsawon lokacin da ta yakice shi daga rayuwarta, bai yi fushi da ita ba ya sake dawowa ya karb'i soyayyarta kuma yayi duk wata fafutukar da rayuwarsu tare zata d'ore. Da ace gidansa aka kawo ta yanzu...

"Assalamu alaikum."

****

A D A M

Ya rufe idonsa a hankali game da cusa yatsunsa na hagu cikin sumar kansa, bai san me yake damunsa ba, ya gaya mata aurensu ba mai d'orewa bane don ya kwantar da hankalinta, don yayi nasarar goge wannan firgicin da ya hango a cikin idanunta sanda take zaune a gabansa, amma kuma wannan alk'awarin da yayi, ba abu ne da yake hango tabbatuwarsa ba.

An takura ta ya sani, don abinda su Kawu Ibrahim suka yi wani abu ne da bai tab'a tsammani ba, ya san cewa ya tashi ne a cikin turawa inda duk wani d'an adam ke da 'yancin kansa da zarar ya kai shekaru sha takawas, amma baya tunanin ko a al'adar hausawa koyaushe ne ake samun iyayen da zasu d'aura aure ba tare da sani ko tuntub'ar d'aya daga cikin ma'auratan ba.

....ina nemawa d'ana ADAM izinin auren 'yarka FADEELAH!!

Yana tunanin wad'annan kalaman sun jijjiga shi fiye da zazzab'in da ya fito daga cikinsa, don har aka d'aura auren bayan sallar la'asar a wannan ranar yana ganin komai ne tamkar a mafarki, abu da bai tab'a hange ba balle har ya hango faruwarsa, don daga lokacin da aka kammala shari'ar nan yayi zaton zaren daya sake had'a kaddararsa data Fadeelah ya kwance, sai gashi Kawu Ibrahim yasa hannu ya d'aure shi yadda kwancewarsa kuma zata yi wuya.

Ya hard'e hannayensa sannan ya gyara zama, a lokacin yana zaune ne a cikin mota yayin da wani ma'akacin kantin da suka yi siyayya keta loda tulin kayayyakin abinci dana amfanin da suka siyo a booth d'in motar, Sa'id na tsaye daga gefensa yana nuna masa yadda zai sa kayan. Siyayya ce irin wadda Sa'id d'in ya saba zuwa yayi musu a gidan da suke, sai dai yau da banbanci, ba gidansu zasu kai ba, gidansa da Fadeelah zasu nufa.

Yau Asabar aka yanke cewar zata tare a gidan da aka kaita, bai san abubuwa da yawa na al'adarsu ba don saida Said ya tuna masa cewar dole ne ya samu gida don ba gidan da suke za'a kawo ta ba, kuma cikin sa'a a unguwar da suke inda yayi kusa da wurin aikinsa, sai suka sami wani gida flat mai kyau, k'aton compound d'in da gidan yake dashi ne yasa ya canja shawara akan karb'arsa haya ya siye shi kawai gabad'aya, siyan da ya girgiza tattalin arzik'insa don masu shi basu yi niyyar sayarwa ba da suka ga ya dage sai suka saka masa kud'i masu yawa.

Gidan nasa ne a yanzu, kuma a yau an kai Fadeelah ciki da sunan matarsa, matar da yayi wa alkawarin cewa zai rabu da ita bayan wani lokaci, wani lokaci da ba zai tab'a zuwa ba don babu ta yadda zai iya kallon Kawu Ibrahim ko wani daga cikin 'yan babban a duniyar nan duk ranar daya rabu da Fadeelah, ya yarda da dukkan nasihohin da kowa yayi tayi masa a wannan larabar, nasihohin da ko sau nawa aka juya su cikin mabanbantan kalmomi, ma'anarsu d'aya ce dai! Cewa aurensa da Fadeelah wani babban ginshik'i ne da zai gyara zumuncin DANGINSU. To ta yaya kuwa shi zai zama sanadin b'ata wannan zumuncin?

Bayan haka kuma akwai wajen wani malami da yake zuwa d'aukar karatu bayan sallar isha'i a unguwarsu, tunda Sa'id ya shaida masa cewa yayi aure, yake ta murna da sake d'orar dashi kan hanya mai tafarki da zai bi da gidansa, yana kuma k'ara gaya masa muhimmancin aure da darajojinsa a musulunci da kuma illar rabuwarsa. To ta yaya kuwa zai so ya fara karya k'aida a matsayinsa na sabon musulmi?

Matsalar kawai guda biyu ce, Farko, ba sai wani ya tuna masa ba, Fadeelah tana da wanda take so a baya har ana shirin bikinsu wannan al'amarin ya faru, saboda haka ko da matsalar da aka samu daga wancan ne, ya san baici ace zuwa yanzu ta manta dashi ba balle har ta fara tunanin bud'e wata sabuwar rayuwar dashi d'in data tsana a baya.

Ya kai hannunsa bayan wuyansa ya shiga murza fatar wajen a hankali, har yau yana iya tuna yadda fuskarta take a lokacin daya fara ganinta, nad'e cikin mayafin dake nuna shaidar addininta, sannan kamar kullum idanunta na manne da siraran glass d'in da ya k'ara fito da ilhamarta, idanunta kyawawa masu maik'o da kyalli, suna haskawa kamar an kunna wuta ta k'asansu.

Sai dai mafi rincab'ewar al'amarin tana masa kallon tsana ne! tsana wadda ke tasowa tun daga k'asan zuciyarta, tsana wadda baya tunanin wani mahaluki ya tab'a yiwa waninsa akan abinda a lokacin bata san gaskiyarsa ba.

Abinda ya sani a yanzu shine da Fadeelah da Bintu abu d'aya ne, zuciya d'aya suke rabawa don haka in har bata sonsa a matsayin Fadeelah, don ya koya mata karatu ko ya taimake ta, babu abinda zai canja a yanzun da ya same ta a BINTUN IKARA.

Matsala ta biyu kuma itace shi da ita basu tab'a had'a wani abu daya danganci hanyar aure ba, karatu ne kawai ya had'a su kuma ya raba tuntuni, don haka shi kansa bai san me yake ji game da ita ba bayan cewar yana kewar idanunta duk sanda yayi nisa dasu saboda sun zama kamar wani b'angare ne na zuciyarsa, amma a zahiri.... Idanunta nata ne.

Sa'id ya bud'e k'ofar bayan motar aka shiga saka wasu abubuwan da basu sami waje a booth ba, sai ya lumshe idonsa kad'an sannan ya k'ara sautin k'aratun da yake ji cikin bluetooth earpice d'insa, a yanzu abinda bai sani ba shine zuwa wane lokaci zai iya fahimtar da ita cewa rabuwar aurensu ba abu ne mai yiwuwa ba? Zuwa wane lokaci zai iya gaya mata cewar alk'awarin da yayi mata k'arya ne? kafin kayan abincin nan su k'are ko kuma bayan an k'aro makamancinsu?

Idonsa ya kai kan d'an karamin mudubin gefen motar, a ciki ya hango Sa'id yana bawa wannan ma'aikacin kud'i kafin ya zagayo ya bud'e mazaunin direba ya shigo. K'arar kunnuwar motar kuma yayi daidai da k'arar shigowar kira a wayarsa, sunan Mamanshi ya fito tar akan screen d'in, Julie Walker!

Baturiyar data amsa sunan mahaifiyarsa tsawon wasu shekaru a America, tun bayan da ya dawo Nigeria kuma bata manta dashi ba kamar yadda mijinta yayi, duk bayan wani lokaci zata kira shi a waya har ma ta taka matsayinta na uwa kan harkar lafiyarsa ko rashin cin abincinsa kamar sanda yana gabanta.

Shi yasa babu yadda ya iya dole ya gaya mata zancen auren nasa kuma ta dage akan sai ya had'a ta da Fadeelan sun gaisa a waya kafin lokacin da zata zo. Ya cije lebb'ensa kad'an don abu ne a yanzu da ba zai yiwu ba. Bai fad'a mata komai ba bayan cewar yayi auren kawai, don inda zai fad'a mata abinda ya farun ba lallai ta fahimta ba... Ba lallai ta fahimci cewa a tsari na musulunci da kuma al'adar bahaushe iyaye nada damar aurawa 'ya'yansu wanda suke so ba tare da izininsu ba.

Ya bar wayar har ta gama rurinta sannan ya tura mata d'an k'aramin sak'on da ya san zata ji d'ad'insa ta kyale shi.

"Allah babu wanda zaice Ango ne kai muke ta yawo haka."

Sa'id ya fad'a sanda yake k'ok'arin tura text din, ya juyo ya kalle shi.

"Ango ba'a ganinsa?" Tambayar ta fito daga bakinsa kafin ma ya gane yayi ta.

"No, ana ganinsa mana amma ba'a ganinsa shi kad'ai haka sai tare da mutane."

Sai kawai ya juya ya kalli motar data tsaya a hold-up d'in gefensu sannan yayi murmushi a gefen kumatunsa yace.

"Tuna min ranar da kai ka tashi daga mutum."

Sa'id yayi dariya shima kafin ya sake magana.

"To bama wannan ba, da gaske ya kamata ace ka fad'a a office sun baka hutu, bai kamata ace duk wannan zirga-zirgar da kasha kuma jibi ka fita aiki ba."

Hutu ba maslaha bane a wajensa yanzu, don yafi so ya bawa Fadeelah isashshen lokacin da zata samu nutsuwa hankalinta ya kwanta tukunna kafin ya nemi fahimta daga gare ta, ya yarda in har suka bawa juna iska abubuwa suka d'an huce komai zai fi tafiya daidai. Saboda haka sai ya bagarar da zancen da wata tambayar.

"Da gaske ne wai kun kwashe duk wasu kayana a gida? Yau dana tashi fa kayan da zan saka kawai na gani a wardrobe."

"Wallahi Awwal ne, ina jin hatta chager wayarja tun jiya ya maida su gidan, haka suka dinga layi shida 'yanuwanta masu kai mata kaya. Shi yasa da sassafe ya tafi Ikaran, kuma na san kayansa gabad'aya na can zai d'ebo."

Suka yi dariya a tare, don tun sanda suka dawo daga Ikara Awwal murnarsa d'aya ce ta zai samu d'akin Adam in ya tafi, kuma bai wani jira umarni ba ana gama cinikin gidan da aka siya ya fara d'iban kayansa yana kaiwa can, shi mutum ne mai yin komai b'aro-b'aro kawai.

Sun isa gidan a lokacin da babu ko mota d'aya a waje balle su saka ran samun mutane a ciki, maigadi ya bud'e musu suka yi parking a ciki sannan suka d'ebi wasu daga cikin kayan motar ciki, masu nauyi kuma suka barsu a mota zuwa safe. Ba Sa'id kad'ai ba, hatta Adam sai da ya tsaya kalli tsarin kayan da aka jera a gidan wanda suka k'ara fito da kyan fasalinsa, daga falo, dining area har zuwa kitchen komai cikin kala biyar yake, grey, ash, white, silver da kuma zirin bak'i a wasu wajajen, bai tab'a tunanin cewa mata suna da fasahar da zasu tashi abu mai kyau irin haka ba.

Ya d'an jingina da kujerar falon yana kallon adon wasu k'ananan flowers da aka jera a saman Tv, fatansa d'aya ne a lokacin, ubagiji ya bashi damar da zai iya jan hankalin Fadeelah ta zauna dashi, don rabuwarsu ba mutanen babban gida kad'ai zata shafa ba har da nata iyayen da suka baje kokarinsu wajen gani sun kyautata gidan aurenta haka.

Idonsa ya kai zuwa hanyar shiga d'akunan kwana dake gefe, ya san dole ne Fadeelah tana d'aya daga ciki a yanzu haka, clutching the lip of her veil as his wife, his bride!

Ya lumshe idonsa a hankali, zai so ganinta kwarai amma ya san ba shawara bace yaje wajenta a lokacin.. Don ba lallai ne taso ganin fuskarsa ba a yanzun da saboda shi ta rabu da komai na rayuwarta ta baya.

Said ya fito daga hanyar kitchen a lokacin bayan ya ajiye wasu kayan, sai kawai ya juyo ya mik'a masa ledar kayan cimar daya siyo yace.

"Ka kai mata wannan tana ciki."

Daga haka bai jira amsarsa ba ya wuce shi ya nufi hanyar wajen dining, inda anan corridon shiga d'akinsa yake.

***

*NB*

_*Bani da mallaki akan wakokin dake cikin chapter nan.*_

*BAYAN NA MUTU!*

©AYSHA SHAFI'EE

42

(☆_☆)

BAYAN SATI BIYU.

Hasken rana ya shigo ta tsakanin wata siririyar hanya a jikin labulen d'akin, a k'aida kamata yayi ta zuge labulen d'umin ranar ya shigo ko ya rage azababben sanyin da tiles d'in k'asa ya d'auka, amma kuma bata son hasken ko kad'an saboda ciwon idonta dake shirin dawowa a dalilin rabuwarta da glass na tsawon lokaci.

..Muhammad ba zaka kyaleta ba? In nazo wajen nan zan zaneka fa?

Fadeelah ta d'an rufe idonta kad'an saboda yadda Mairo ke ihu ta cikin wayar da suke yi tana rabon fad'a tsakanin 'ya'yanta, ta cusa yatsanta cikin barbajajjen gashinta daya baje akan pillow, tashinta kenan a lokacin don wayar Mairon ce ta farkar da ita, ta d'aga kai ta kalli agogon d'akin k'arfe goma na safe amma har su sun tashi suna bidirinsu, ta murza idanunta da tana k'okarin saita ganinta har a lokacin Mairo na sulhu ta cikin wayar.

"Ya salam ya Allah! Ace yaro baya ko magana amma sai tsabar rashin ji... Ita kuma tayi ta masa kuka?" Ta fad'a bayan wani lokaci.

Fadeelah tayi murmushi sannan tace.

"Dan Allah yaushe zaki kawo min ita? Kinga kema sai ki huta."

"Ai ba don next week zasu koma makaranta ba tattaro miki ita zanyi wallahi, amma dai zan tambayi babanta may be tazo miki wani weekend d'in."

Ta mik'e zaune sannan tace.

"Har naji kamar inzo d'auke ta wallahi."

"Kar ki damu zata zo, kinji kuwa an yankewa Habiba k'afa d'aya?"

Maganar ta daki tunaninta, tace.

"Yaushe?"

"Shekaranjiya Aunty Hassanah take gaya min, wai tun daga cinya don ciwon yaci k'arfinta."

Bata san me zata ce ba don haka tayi shiru kawai, zuwa can kuma ta daure tace.

"Allah ya bata lafiya."

Watakila Mairo ta fahimci halin da zuciyarya ke kokarin fad'awa ne don sai tayi saurin canja zancen da cewa.

"Kin tambaye shi kuwa zuw asibitin?"

Sai ta kifa kanta akan tafin hannunta gashinta ya sunkuyo a barbaje, sannan ta girgiza shi kamar Mairon zata gani. Yau asabar ya kama sati biyu kenan da fara sabuwar rayuwarta ta aure, kuma a cikin wad'annan kwanakin, ta samu wani nutsatstsen hutu da kwanciyar hankalin da har hakan yasa zuciyarta ta fara wankuwa game da abubuwan da suka faru da ita.

Watakila don ta d'an rabu da hayaniya ne kwana biyu saboda tun sanda aka kawo ta babu wanda ya sake zuwar mata, hatta su Aunty Saratu a waya suka yi sallama, kuma ba sai wani ya gaya mata ba ta san su suka tsara hakan don ko kowa ra'ayin kansa ne k'in zuwan da taga su Zahra da suka dawo a cikin satin saboda k'arewar hutun makaranta, amma su d'in ma har yanzu sai a waya kawai take ta fama da kaud'insu.

Wayar da Mamin ta bawa Sa'id ya kawo mata sabuwa a kwalinta, kuma a ranar da suka yi waya ta gaya mata cewa akwai kud'i a account d'inta na banki... tun wannan kud'in data tura mata lokacin bikinta da Al'ameen, a yanzu da aurenta ya koma kan Adam, an samu gudunmawa sosai daga Babban gida da kuma su Aunty Saratu don haka bai fi rabin kud'in aka tab'a ba.

Shi yasa yanzu da idonta ya dame ta da ciwo take son taje asibiti a duba ta kuma ta sake glasess, tana son siyo kayan zane ma sannan tana son taje inda zata siyo wasu 'yan k'anan abubuwa da take buk'ata, amma duk hakan ba zai yiwu ba sai da izinin mijinta. Haka Mairo tace kuma itama ta san baza ta iya fitar ba sai da izininsa.

"Bintu kina jina kuwa?" Muryar Mairo daga cikin wayar ta dawo da ita daga wannan dogon tunanin.

Sai tayi saurin d'ago da kanta sannan ta amsa.

"Na gaya miki ki bari ko zuwa nan da next week ne sai ki tambaye shi tukunna, amma ko gidan Mami kika je yanzu sai ta miki magana."

Gidan Mami. Ta maimaita kalaman a cikin kanta, a da nan take kira da gida, amma yanzu saboda tasirin wasu kalamai da kuma 'yar walima, kalmar 'Gida' a wajenta ta canja daga wajen su Mami zuwa nan... Gidan Adam!

Ta shiga gyara gashinta da yatsun hannunta don Mairo bata san komai game da yadda zaman shirun nan d'in ya fara damunta bane, a yadda kowa ya sani su biyu suke rayuwa a gidan, amma a zahiri ita kad'ai take dabdalarta a cikinsa, don hatta washegarin ranar da aka kawo ta lahadi, Adam bai yini a gidan ba sai dare ta ganshi.

Ita dashi a yanzu kamar wasu makwabta ne kawai dake rayuwa a kusa da juna, ta san dai kullum zasu gaisa idan ya dawo daga aiki ko kuma wani lokacin da safe in zai fita harma ya tambayeta wani abun amma bayan nan bata fiye ganinsa sosai ba, don bata zama a inda zata ganshi d'in ko yana gida, sai dai ta jiyo motsinsa kawai daga nan cikin d'akinta.

Alkawarin daya d'auka yana nan rataye a cikin zuciyarta yana reto, don haka ta zab'i bin wannan hanyar ne saboda tana ganin itace maslaha game da irin zaman da zasu yi, ta yarda in har ta nesanta kanta dashi rabuwarsu zata zo mata sauki a duk ranar daya tsayar zai sallameta. Domin bata so tarihi ya maimaita kansa, wancan karon a makarata kawai suke had'uwa amma data bari zuciyarta ta saba dashi, ba k'aramar wahala tazo tasha ba wajen kewarsa.

Bayan haka kuma akwai wasu banzayen sak'e-sak'e da zuciyarta keyi in har tana gabansa, shi yasa ma dole ta kaucewa ganinsa tun kafin ta makara wajen ceto zuciyar tata. Dad'in da take ji d'aya ne, duk irin sak'e sak'enta bata tab'a tunanin Al'amin ba, don taji nasihar da Mami tayi mata akan hakan shi yasa ta d'auki tunaninsa ta kai zuwa can wani sak'o a zuciyarta kamar yadda take fata shima ya manta da ita ya karb'i zab'in mahaifiyarshi hannu biyu.

Bayan gaisuwa kuma abinda kad'ai ke had'a ta da Adam shine abinci, don a cikin wancan satin data gaji da kame-kamen abin ci a gidan ne tayi girki ta had'a dashi, kuma wannan ma gani tayi rashin kyautatawa ce k'iri-k'iri ace shi da gidansa da kuma kayan abincin daya kawo amma ta dafa ta barshi da

Please Login or Register in order to submit comment