Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman na siyarwa, don hatta Awwal d'in da yazo yayi mata siyayya ma shi ya turo shi, saboda haka sai ta k'udirce a ranta cewa zata yi ko don ta samarwa kanta lada kafin damar ta sub'uce mata, tunda Allah ba ruwansa da tsarinsu, a wajensa shi mijinta ne da in ta kyautata masa zata samu ladanta. Kuma taji dad'i da shima ya karb'i hakan a matsayin kyautatawa kawai, baiyi tunanin cewa tana neman cusa kanta ne wajensa ba.

Watak'ila kuma wannan yanayin zaman nasu yana d'aya daga cikin abinda ya dad'a kwantar da hankalinta ta samu nutsuwa a cikin 'yan kwanakin nan. amma kuma yanzu kad'aicin ya fara so ya dameta don haka take son ta d'an fita, kuma ta san in dai ta tambaye shi zai barta, matsalarta kawai shine kowa sai yayi magana in yaji ta fitan, don ga Mairo nan ma ta fara.

Sai ta koma da baya ta sake kwanciya akan gadon sanda Mairo ta cigaba da cewa.

"Bintu abinda nake so ki fahimta shine daga ke har shi wannan shine aurenku na farko, kuma kowa ya san a yadda auren yazo don haka ki bari hankalin mutane ya d'an d'auke daga kanku tukunna, zuwa wani lokaci ba wanda zaice wani abu don kin fita."

Zuwa wani lokaci. shima haka yace mata, zuwa wani lokaci zai rabu da ita, to ta yaya kuwa zata yi ta zama babu abinyi har 'Zuwa wani lokaci?'

Sai dai har ta bud'e baki zata yi magana, ta tsinci k'arar knocking a jikin k'ofar d'akin, babu shiri ta mik'e zaune idanunta d'auke da mamaki.

"Waye?" Tambayar ta fito daga bakinta tun kafin ma ta san ta ma ta fad'a, kuma a take taga wautarta k'arara, waye zai mata knocking da safe in ba wanda suka kwana suka tashi tare ba? To bai tafi aiki ba dama? Sai ta juyo da fuskar wayarta ta kalla, a lokacin wayar da suke yi da Mairo ta katse... Abinda ta gani ya k'ara sawa ta zare idanu, yau asabar! Hutun k'arshen sati! yana gida! Ya salam kwata-kwata ta manta don a wancan k'arshen satin yayi tafiya Katsina ne tsawon kwanaki uku wanda ya had'a har da litinin.

Ba shiri tayi wulli da wayar ta lalubi ribbon akan gadon ta d'aure gashinta, sannan ta jawo hijabin sallarta ta zura, ta kalli fuskarta a mudubi kafin ta wuce bud'e k'ofar, babu kwantsa a idonta amma ta sake murje shi sannan ta kwantar da gashin girarta.

Yana tsaye kuwa sanda ta bud'e k'ofar, sanye cikin farar T-shirt da wando 3-quater, sannan gashin kansa a barbaje, zuciyarta ta matse don rabon da ta ganshi a haka tun lokacin da suna America, wai baya jin sanyi ne? Shima ita d'in yake kallo, sai dai shi ba kallon nazari yake mata ba, kallo ne kamar na wanda ya kama mai laifi, taji zuciyarta ta matso cikin mak'ogwaronta sannan iska tayi mata wuyar shak'a, ko dai tayi masa laifin ne?

"Kin tashi lafiya?" Muryarsa mai zurfi ta gaisheta kafin ta gama tunanin, nata hankalin gaisuwar yazo.

Kunya ta ratsa ta, sai tayi saurin sakin hannun k'ofar sannan ta gaishe shi.

"I'm sorry na tashe ki ne?" Ya furta a hankali cikin sigar damuwa wanda ya cakud'e da taushin muryarsa. Watakila d'azu ta manta bata fad'i cewar muryarsa ma na d'aya daga cikin abinda yasa take k'ok'arin kauce masa ba, don har yanzu duk sanda zai mata magana ji take kamar yana rad'a mata ne a kunne, bata san kuma yaya zata ji ba in har da zai lalubi kunnen nata ne ya rad'a mata. Wata murya a cikin kanta ta rafka salati, kina da hankali kuwa Fadeelah? wane irin tunani kike yi haka alhali yana tsaye a gabanki? amma wata muryar ta kare ta da cewa to meye? Ai ba haramun bane don kinyi wannan tunanin akansa.

A wajen kanta kuma, lallausar muryarsa ta sake maimata mata tambayar da yayi.

"Na tashe ki daga bacci ko?"

Sai tayi saurin girgiza kanta cikin riba biyu, ta bashi amsa kuma ta kad'e wad'ancan muryoyin biyu.

"A'a na tashi dama, kawai dai ban fito bane."

Ta k'ara da cewar.

"Na manta yau saturday, ban san kana gida ba."

"Nima banso na fito dake yanzu ba, wasu ne suka zo wai bak'in ki ne daga mak'ota."

Da turanci yayi maganar, watakila bai san yadda zai fad'i kalmar 'mak'otan' bane don har yanzu hausarsa bata zauna sosai ba don ma dai yana kokari ne, amma wad'anne irin mak'ota ne zasu shigo mata da safe haka? Ta san dai mata biyu dake mak'otaka dasu a gefen gidan sun shigo mata kwanakin baya, amma yanzu kuma bata san waye ba... Bari dai taje ta gani koma su waye d'in, bari ta fincike kanta daga wannan yanayin mara kyau da take shirin fad'awa, saboda haka ta gyad'a kanta kawai tace bari taje su gaisa, amma maimakon ya bata hanya, sai ya k'ara matsowa dab da ita ya tsaya, hannayensa sunk'e cikin aljihun wandonsa.

"I want to ask you something. (Ina so in tambaye ki wani abu)"

Bata kalle shi ba, amma tana iya jin tsawonsa kamar na dutsen zuma a gabanta, don haka ba shiri zuciyarta ta shiga tsere, me kuma zai ce mata bayan yace bak'i suna jiranta? wani abu yayi girma a cikin mak'ogwaronta saboda tana iya jin tasirin kallon da yake mata a jikinta, hakan yasa ta dunk'ule yatsun k'afarta.

"Me yasa kike guduna?"

Bata san lokacin data saki k'afar tata ba sannan ta d'ago da idonta ta zare su akansa,

Me? Ta ina ina wannan tambayar ta taho? Ya akayi ya gane? Waye ya bashi shawarar ya tambaye ta? Saboda me ma zai tambaye tan?

Sai ta girgiza kanta.

"Ni ba gudunka nake yi ba, ina ganinka kullum, ta yaya zan guje ka."

Kusan gaskiya ta fad'a, don tana da hujjar kare kanta, shi kansa ya sani babu ranar da ba zasu ba kuma inda zai bata dama ma, tsaf zata lissafo masa kowanne kaya daya saka tun bayan tarewarta gidan, a jere ba tare da tsallaken koda rana guda ba. Ta had'iye yawu kad'an tana aikawa zuciyarta kallon mamaki, don ko ita kanta bata san ta rik'e hakan ba sai yanzu.

Ga mamakinta sai yayi murmushi sannan ya gyad'a kansa kamar ya fahimta ko ya yarda da ita kafin yace.

"In kin gama da bak'in naki, akwai maganar da nake son muyi."

Ya k'ara jefa mata wani kallon kafin ya juya ya tafi. Tabi bayansa da kallo sannan ta rufe idanunta alamun Allah ya kawo mata agaji, don bata san wane irin yak'i zata yi da zuciyarta ba in har suka zauna yin maganar.

***

Adam ya lumshe idanunsa sanda yake zaune a wani side falo dake hanyar zuwa kitchen, waya ya gama yi yanzu da abokin aikinsa Nasir akan wani case da suke yi tare, Nasir d'in ya nemi daya shigo ne don su fitar da sakamakon wani sauti da aka tace musu game da shari'ar da suke yi ta wani saurayi daya kashe k'anin mahaifinsa, amma kai tsaye ya shaida masa cewa ba zai iya fitowa ba, don a ko k'ofar gida baya son fita, hutu yake buk'ata irin wanda ya dad'e rabonsa dashi.

Ya kurb'i coffe d'in daya had'a a hankali sannan ya koma da baya ya jingina da kujerar, yau sati biyu kenan da tarewarsu a gidan, kuma a cikin wad'annan kwanakin yana tunanin ya cimma tsarinsa na bawa Fadeelah isashshen lokacin da hankalinta zai kwanta, don a yanzu ya lura fatarta tayi haske kamar yadda take a baya sannan idanunta sun washe kamar madara, babu wannan d'ashewar, babu firgici a cikinsu balle kuma wani tunani.

Shi yasa a yanzu yake ganin kamar lokaci yayi dashi da ita zasu zauna suyi magana ta fahimta, don ya fara shiga damuwa game da yadda ta kasa sakin jikinta dashi har yanzu, ba abinda ke had'a su sai gaisuwa kawai, daga nan kuma ba zata k'ara cewa komai ba sai in har shi ya tambayeta wani abun, sannan in ba ma gaisuwar ba baya ganinta kwata-kwata, in ta shige d'akinta shi da ita sai gobe kuma. Da farko shima ya taya ta gudar masan ne don kar ya takurata, amma yanzu kuma abin ya fara damunsa.

Gani yake abinda take yi laifinsa ne, tun farko shi ya saka mata wani fatan da yasa har yanzu ta kasa karb'arsa a matsayin mijinta, watak'ila da baiyi mata wannan alkawarin ba da yanzu abubuwa sun fara tafiya daidai tsakaninsu wanda hakan ne fatansa, don baya son a samu b'ullar wata matsala ko yaya take da zata kai ga sanin su Kawu Ibrahim, Shi yasa dole ne ya kawo k'arshen duk wata diramar dake faruwa a zuciyarta kafin ya rasa ta inda zai fara.

Bayan wani lokaci yaji k'arar motsi daga kitchen, hakan ya tabbatar masa cewa bak'in nata sun tafi kenan don haka ya mik'e ya ajiye kofin hannunsa ya nufi can.

A tsaye ya same ta, ta juya baya tana aikinta yayin da kitchen d'in ya gauraye da k'amshi kala-kala, ta canja kayan jikinta zuwa wata doguwar riga kalar yellow mai haske, bai sani ba ko telan da yayi d'inkin bai san awonta bane amma anyi kasan rigar ne yana ja har k'asa wanda ya dad'a fito da kyawun d'inkin, wani abu ya wuce cikin mak'ogwaronsa don tayi masa kyau gaskiya, musamman kalar kayan da suka fito tar a cikin kalolin baki da ruwan toka na kitchen d'in, sai ya zama kamar an saka kala ne akanta ita kad'ai.

Allah ya sani duk da ba wani sabo suka yi ba har yanzu, amma yana jin dad'in zama da ita don ya saba da rayuwa a gidansa yanzu, ya yarda da duk maganar da malaminsa ya gaya masa a ranar da Sa'id ya fara shaida masa cewa yayi aure.

"... aure rahma ne Adam, yana da darajoji mai tarin yawa, kai kanka a yanzu zaka fi jin kanka ka zama mutum kuma zaka sami nutsuwa fiye da kowanne lokaci, sannan ko a idanun Al'umma girmanka sai ya ninku akan da..."

Ya yarda da hakan saboda yanzu ko su Sa'id girman da suke bashi daban ne, sannan shi kansa ya kwana biyu rabonsa da zuwa wajensu, a kullum ya tashi daga aiki tunaninsa na kan hanyar komawa gidansa ne kawai, inda zai dawo ya tarar da ita kuma ya kwanta da tunanin cewa wad'annan idanun da yake bacci dasu kullum, a yanzu suna 'yan taku nesa dashi ne kawai.

Gashi kuma ya fara sabawa da cin abincinta, kalolin girkinta dake had'ewa tsakanin American dishes da kuma na nan Nigeria, watakila kuma zuciyarsa na d'okin ganinta ma a kullum, ganin simple shigarta mai kyau kamar yanayin kayan gidan, watarana ya kanji kamar ya gaya mata cewa tayi kyau! Amma in ya fad'i hakan, bai san wani irin kallo zai tsinta a idanunta ba.

Fadeelah ta juyo ta kalle shi a lokacin, yana tsaye a jikin doguwar k'ofar kitchen d'in, hasken ranar dake shigowata ta blinds d'in kitchen din ya haska a fuskarsa, hakan yasa taga abinda bata kula dashi a d'azu ba, yayi gyaran fuska da kuma na saje wanda ya sake fik'e kammanin fuskarsa, bakinsa ya motsa cikin wani guntun murmushi da taji har tafin kafarta, sai tayi saurin juyawa ta cigaba da had'a biredin sandwich d'in da take yi.

"Bak'in naki sun tafi?"

Ta tsinci muryarsa tana k'arasowa ciki.

"Eh sun tafi, tace ma in baka hak'uri ko sun tashe ka da wuri, zasu yi tafiya lagos ne yanzu shine tazo min sallama."

Bai amsa hakan ba sai yace.

"Ashe kin fara sabawa da mutane?"

A cikin kanta ta lalubo wani magogi ta shiga goge abinda muryarsa ke k'ok'arin yi a zuciyarta kafin ta bashi amsa.

"Sun dai shigo ne wancan satin mun gaisa kawai, shi yasa tazo min sallama kar naji shiru don tace zasu dad'e basu dawo ba."

Ya gyad'a kansa sanda ya tsaya 'yan taku kad'an da ita inda ta ajiye wani farantin tumatir da take yankawa, k'amshin turarenta wanda ya had'e da na sabulun wanka ya ratsa cikin kwanyarsa, amma a yanzu da yake kusa da ita ba wannan ne yafi d'aukan hankalinsa ba, idanunta... A yau ta saka musu wani zirin bak'i da ya k'ara fito da girma da kuma kyallinsu, hakan ya shiga tsima zuciyarsa sai kawai ya juya ya d'auki wuk'a gefe sannan ya shiga k'arasa yanka tumatir d'in cikin kwarewa kamar wani shahararren chef, abinda ya bawa Fadeelah mamaki kenan, bata san sanda ta kalli yadda hannunsa ke sarrafa wuk'ar ba sannan kuma fuskarsa.

Sai ya girgiza kansa yace. "Idan kina shirin tambaya ko nayi aikin girki ne to A'a."

Muryarsa a sake take kamar mafi yawan lokuta da yake mata magana, saboda haka ta had'iye yawu da kyar sannan ta juya ta cigaba da abinda take yi.

"Ko dai tunani kike ba haka bane?"

Bata ji me yace ba don haka ta d'an tsaya da abinda take yi. "Na'am?"

"Ko kina tunanin ba gaskiya na fad'a ba?"

Ya maimaita mata, sai tayi saurin girgiza kanta ba tare da ta kalle shi ba tace.

"Ta yaya zance ba haka bane, bayan ban san rayuwarka ta baya ba."

Yana cigaba da yankawar yace.

"Tunda baki san komai akaina ba kenan idan na ce miki nayi rawar circus a baya zaki yarda?"

Ta d'an tsaya da abinda take yi sannan ta saki murmushi, maganar ta bata dariya sosai amma sai ta gintse ta hanyar girgiza kanta.

"A'a, banda irin wannan."

"Saboda me?" Ya tambaya.

Ta sake cije lebb'enta don kaucewa yin dariyar da bata san ya akayi ta iya tsallake komai na zuciyarta ta taho ba sannan ta shiga jera biredin akan plate d'in wainar data soya kafin ta amsa.

"Ai baka yi kama da irin wad'annan mutanen ba."

A lokacin ya gama yanka tumatir d'in sannan ya mik'o mata, sai dai ya lura kamar dariya take yi don haka ya fasa bata plate d'in sanda ta mik'o hannu, yace.

"Ba dai wai hango ni kike ina rawar circus d'in ba ko?"

Fadeelah bata san ya akayi ta tsinci kanta a wannan yanayin ba, ta dai ji kawai komai ya kwance mata ne don haka bata san sanda ta juya masa baya ba sannan ta rufe fuskarta da tafin hannayenta shiga yin dariya.

Mamaki ya kama Adam sosai don zai iya rantsewa bai tab'a ganin dariyarta irin haka ba ko lokacin da suna America saboda sautin dariyar na gaske ne dake fitowa a zallarsa, Ba kallon fuskarta yake ba amma ya san dariyar tayi mata kyau sosai, shima kuma tayi masa kyau... Ashe dai samun had'in kanta ba abu ne mai wahala ba? Ashe zai iya shawo kanta cikin d'an k'ank'anin lokaci kamar yadda yake iya janyo hankalin Alkali a kotu? Watakila da gaske ne da mutane ke cewa yana da wata baiwa ta iya yin tasiri a zuciyar mutane.

Ya lumshe idonsa a hankali yana fatan Abubuwa su tafi masa daidai, kuma cikin sa'a sai addu'arsa ta karb'u don a tsakanin wannan asabar da lahadin yayi nasarar sawa Fadeelah ta fara sakin jikinta dashi, don bai je koina ba a weekend d'in kuma bai fasa janta da hira kala-kala ba. A cikin hirar tasu ne kuma ya samu damar bata labarin rayuwarsa ta baya da kuma labarin iyayensa da yadda yadda akayi har yazo Nigeria.

Kuma in har baiyi kuskure ba, ya hangi wani abu kamar tausayawa a idonta sanda yake bata labarin, daga baya ma sai ya fahimci bayan tausayin watakila labarin ya tuno mata da wani abu mara dad'i ne a tata rayuwar, don kallo ta dinga yi masa irin na wanda ke tausayawa wani ba tare da ya san hanyar da zai bi ya gyara al'amarin nasa ba, kuma bata k'ara cewa komai ba daga nan, ta tsirawa kofin hannunta ido ne kawai tana juya shi ba tare da shan abinda ke ciki ba.

Saboda haka ya matso ya zare shi daga hannunta ya ajiye akan d'an k'aramin table d'in dake gefen kujera... Abubuwan da suka faru dasu a baya sun riga sun shud'e kuma damuwa dasu ba abinda zai canja, don haka kamar yadda ta tab'a fad'a masa a baya ne, kamata yayi su fuskanci abinda ke gabansu kawai. Yace.

"Ki gaya min wani abu game da ke, me kika yi a Nigeria bayan kun dawo?"

Ta gaya mishi cewa ta zana jarabawar shiga jami'a har ma ta sami gurbin karatu a nan jami'ar Abujan, sai dai saboda abinda ya faru a yanzu haka an koma hutu kuma har anci semester guda babu ita.

"Kina ganin zaki koma ne ko kuma zaki canja makaranta?" Ya tambaye ta bayan ta kai k'arshe.

Sai ta juyo ta kalle shi, wanan kyallin idanun nata ya k'ara tsima shi, sai ya d'auke kansa tun kafin zuciyarsa ta bashi shawarar wani abu daban. Da gaske yake in har bata son komawa waccan makarantar zai nemo mata private university mai kyau wadda za'a iya samu su shiga sabon session a yanzu.

"A'a, na yanke shawarar ajiye semester ne kawai sai in koma wani session d'in, bana jin Daddy zaiji dad'i in har na canja."

"Kinyi reporting hakan?"

"A'a, amma munyi maganar da Mami tace zata je."

Mami, Mami. Bai san sau nawa ta ambaci sunan matar nan ba tun sanda suka fara magana, babu ta yadda wani zai ce ba mahaifiyarta ce ba in har bai sani ba, ta riga ta bata wani matsayi mai girma a zuciyarta, kuma bai sani ba ko akwai ragowar irin wannan matsayin a zuciyarta yanzu, daga nan inda yake zaune yana iya jiyo sassanyan k'amshin dake tashi daga jikinta wanda ke kokarin haddasa masa tunani kala-kala a cikin ransa, ya had'iye yawu da kyar yana tunanin watakila watarana zai duba d'akinta yaga sunan wannan turaren.

"Ina so in fad'a maka wani abu." Muryarta ta shiga kunnensa kai tsaye ba tare da zato ba, kuma kafin ya amsa ta cigaba da cewa.

"Lokacin da aka kaini kurkuku, Kutama yaje ya same ni a can."

Ba shiri ya juyo ya kalleta da tsantsar mamaki, Kutama? Me yaje yi wajenta? Me yayi mata?

"Na san komai ya wuce amma a wajenka irin wannan shari'ar kana yinta ne kullum, shi yasa nake so na fad'a maka koda wata shari'ar zata sake had'a ka dashi."

So yake ta tsallake duk wannan bayanin na gabatarwa ta fad'a masa abinda ya faru kai tsaye kawai, amma saboda tsabar abinda ya fara ji a zuciyarsa game da sunan Kutaman data ambata sai ya kasa tsinto muryarsa.

"Yaje ne da zancen cewa mu sayi wasu shaidu a wajensa in har ina son in samu 'yancina, don wai da wad'annan shaidun biyu kad'ai kotu zata iya yanke min hukuncin kisa ko na d'aurin rai da rai a kurkukun, amma in har muka siya, to zai tattaro komai ya bamu shi kuma ya fasa gabatar dasu a kotun yadda zamu yi nasara, yace min kaima ya same ka da zancen amma baka yarda ba, sai dai na san ba haka bane shi yasa na fad'a maka."

Sanda ta fad'i hakan, Fadeelah taji kwalla na neman cika mata idanu kamar yadda yake faruwa duk ranar da ta tuna rayuwar cikin kurkukun nan da hargitsin cikinta, wutar Nepa ta d'auke a daidai wannan lokacin, watakila kuma a sannan ma maigadi ya zab'i lokacin wajen yin zagaye a unguwa don ba'a kunnan metre solar a take ba kamar yadda ya saba.

Saboda haka duhu ya mamaye koina, kuma manya- manyan labulayen falon suka taimaka wajen hana hasken farin wata shigowa, d'akin yayi dind'im bata iya ganin komai kuma bata iya ganinsa, amma tana iya shak'ar wannan k'amshin da ta dad'e da yiwa tambari da NASA.

"Bayan haka me ya faru?"

"Ban yi niyyar saurarensa ba da farko, amma ya tsayar dani cewar ya san inda ka tafi a lokacin."

"Ya fad'a miki kuma?"

"A'a, yayi amfani da wannan damar ne kawai don in saurare shi."

"Kuma kin yarda dashi a lokacin?"

Muryoyinsu a hankali suke fita suna kanannad'ewa da junansu ta cikin duhun d'akin, kuma tasirin duhun yasa Fadeelah taji kwallar idonta na k'aruwa, saboda haka muryarta na rawa tace.

"Ba zan tab'a yarda da mutum irinsa ba a rayuwata."

Ta yaya kuwa zata yarda dashi? Bayan tana ganin yadda yake dagewa a kotu wajen ganin an hukunta ta saboda wasu 'kud'ad'e kawai da duk yawansu ba zai shafe dogon lokaci yana ganinsu ba, zuciyarta ta matse da tunanin mutane nawa Kutama yasa aka kashe a baya ko kuma aka datsewa rayuwar 'yanci akan gaskiyarsu, wanda itama ba don taimakon Allah ba da tuni ta shiga jerin lissafinsu.

Muryarta ta shaida masa cewa kuka ne ke shirin kwace mata kuma ya san tunanin halin data shiga a baya ne yasa hakan. Bayan gama shari'ar nan, yasa an tsoratar da kutama tsawon sati biyu da wata takadar bogi ta cewa za'a kore shi daga aiki, don ya riga rantse cewar sai nasa idanun suma sun shiga irin firgici da tashin hakalin da yasa idanun Fadeelah a baya, sai dai da ace bayan ya san wannan maganar ne, da sai yabi duk hanyar da zai iya a maida takardar nan ta gaske yadda zai shima shafe rabin rayuwarsa yana jin zafin hakan.

Duk da duhun d'akin, yana iya ganin yadda take kai hannunta tana goge hawaye a fuskarta, sannan yana iya jin sautin ajiyar zuciyar da take yi ma, zuciyarsa ta had'e waje d'aya, yana son ya rarrasheta amma kuma yana tsoron kar hakan yaja shi ga yin wani abun daban.

Sai dai bayan wani lokaci ya kasa daurewa zuciyar tasa, kuma bai san sanda ya kai hannu ya kamo nata cikin nasa ba, yaji sanda hannun nata yayi rawa kad'an amma kuma daga nan bai k'ara jin komai ba don taushinsa kamar na wani sabon pillow ne mai laushin gaske.

"Nasha wuya sosai a wajen nan..." Bai zata ba amma muryarta ta sake fitowa cikin kuka, a shirye don fitar da d'acin dake damunta.

"... 'yan kwanaki ne kad'an amma naji kamar an canja ni zuwa wata duniyar ne, duk irin wahalar dana sha a babban gida ba d'aya bace da wannan wajen, shi yasa ya nemi ya tsorata ni da hakan don in yarda dashi, ban san kuma yaya zanyi ba da ace..."

D'aya hannunsa ya samo kuncinta a lokacin, ya shiga share hawayenta da babban yatsansa yayin da sassanyan k'amshinta mai dad'i ke juya masa kwakwalwa, sannan a hankali ya sunkuya daidai kunnenta ya rad'a mata,

"Komai ya wuce lealah, insha Allah daga yanzu ba abinda zai k'ara shigowa rayuwarki sai alkhairi..!"

A wannan lokacin Fadeelah bata san ko kuka take yi ko kuma k'ok'arin nemo hanyar da iska zata shiga kirjinta ba.

***

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

43

(☆_☆)

Komai yana tafiya ne daidai a cikin wannan satin, a yanzu shi da ita sun sami fahimtar juna sosai, don a cikin 'yan kwanaki kawai Adam yayi nasarar zabge fiye da kashi saba'in na waccan rayuwar da suka fara a cikin sati biyu.

Yana mutukar k'okarin ganin cewa yayi duk abinda zai ja hankalinta don ta fahimce shi duk sanda ya tashi sanar da ita cewa wancan alkawarin da yayi mata ba mai faruwa bane, ba don komai sai don su raya fatan su Kawu Ibrahim akansu kuma watakila don a yanzu ya fahimci cewa yana son matarsa kuma baya son rabuwa da ita. He just kept falling for her, one of the few things he think gravity can't explain.

Fadeelah ta zama duniyarsa a yanzu, ya gane cewa zuciyarsa ta karb'eta tun daga ranar daya fara tozali da idanunta, abinda ya hana shi gane hakan tun a baya shine, saboda abubuwa sun danne zuciyarsa bai maida hankalinsa kanta sosai ba, amma a yanzu da komai ya lafa ya zama daga ita sai shi... Ya fahimci ya dad'e da k'aunarta, don abinda yake ji game da ita yana tasowa ne tun daga k'asan zuciyarsa, musamman in ta kalle shi da wad'annan idanun nata dake karya duk wani kuzarinsa.

Tana k'ara shiga cikin zuciyarsa a duk sanda yake tare da ita, tana k'ara burge shi da calm personality d'inta wanda ke mannewa a zuciya da ruhin duk wanda ke tare da ita, bata da magana can sosai, amma duk sanda take magana muryar nan tata na fita a hankali, mantawa yake da komai na duniyar nan sai ita kawai, ita dashi da kuma gidansu.

Tsawon rayuwarsa a baya, bai tab'a saka aure cikin lissafinsa ba balle har ya dinga hango kansa a ciki, amma a yanzu da k'addara ta kawo shi cikinsa kuma ya saba da matar tasa, baya jin zai iya wata rayuwa mai kyau a gaba in har ba tare da ita ba, shi yasa ba abinda zuciyarsa ke fata irin ya k'are rayuwarsa da ita har ma su

Please Login or Register in order to submit comment