Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ko don darajar fararen kayan jikinta da ta san sunfi kadarar data mallaka gaba d'aya a Ikara... A'a sai don tsaf idanun nata sula gane mata kammanin d'iyar d'anuwanta marigayi, d'iyar da ta kashe mahaifiyarta har lahira kuma ta gudo!

Bintunsu dai a matsayin amarya!

BINTUN IKARA!

***

"Kana tunanin zamu iya samun wani abu ne a wajenta?"

Mairo ta tambaya sanda suka shawo kan kwanar adireshin dake hannunta.

"Sweetum kince sanda kika ganta ankon bikin ne a jikinta, kinga kenan dole tana da kusanci dasu masu bikin, in ma basu gane ta ba ko a hotunansu za'a iya samunta."

"Haka ne." Ta fad'a tana damk'e takardar a hannunta sannan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. A hankali Sadiq ya ziro hannunsa ya d'ora akan nata.

"Komai zai tafi daidai Insha Allah Maryam."

Da sauri ta kyallo fararen idanunta ta kalle shi, a zamansu kaf! inda tana rik'ewa zata iya kirga adadin sanda daya kira sunanta kuma dukkansu a lokuta masu mutuk'ar muhimmanci ne, saboda haka maimakon taji sauki sai hakan ya k'ara nauyin ajiyar zuciyar tata, ta maida kanta jikin glass ta langwab'ar a hankali yayin da tayar ta cigaba da motsawa.

Minti biyar kawai ya isar dasu gida mai lamba d'ari uku da ashirin kamar yadda yake rubuce a hannunsu, sai dai me? K'ofar gidan cike take da motoci da kuma mutane sannan ga kid'a na tashi daga cikin gidan.

"Bibty biki suke yi." Bakinta ya furta a hankali tana kallon gate d'in gidan.

"To ko zamu koma gobe ma da...?"

Ta katse shi ta hanyar girgiza kanta.

"Inaga wannan lokacin shine daidai, in har zata je wancan bikin, wannan ma baza ta kasa zuwa ba..."

Ta juyo daga kallon gate d'in ta kalke shi.

"...zan iya ganinta ba tare dana tambayi kowa ba."

Har yanzu hannunsa tana rik'e da hannunta ya d'aga mata kai.

"Haka ne sweetum, kina shiga zaki ganta insha Allah."

Sai ta juya ta kalli su Afra dake kwance a bayan motar sunyi bacci, kafin tayi magana ya riga ta.

"Kije kawai, har ki dawo na san baza su tashi ba."

Yana iya jin yadda hannunta ke rawa kafin ta zarw shi daga cikin nasa sannan ta bud'e k'ofar motar ta fita, fitar ta dake gaya masa cewa zamansa da ita ya fara tangard'a kenan, don bai san me zai faru ba in har ta k'arasa fahimtar abinda yayi mata.

***

Sadiya ta kafe idanunta kan Bintun da take kallo babu ko k'akk'autawa, gani take kamar an sa sanda ne an ture duk sauran mutanen dake tururuwa a rumfar, fuskar dai Bintun dake ta dallarawa cikin hasken camera kawai take iya gani yayin da mamaki ke rarakarta inda take tsaye.

Me zai kawo Bintu nan? Ta yaya ta canja rayuwa ta samu duk wad'annan DANGIN? Har zata yi aure cikinsu? Ta yaya suka karb'eta? Su san ko ita wacece? Su san me tayi? Ita ta manta da nata dangin kenan? Ta manta dasu? Ta zata tayi nisan da har baza su iya ganinta ba?

"Lalle yarinya k'arshen shirinki yazo, ana yi miki bikin barin duniya ne."

Ta furta a hankali sanda ta juyawa rumfar baya sannan ta zaro wata 'yar qurqurar wayarta da niyyar kiran wad'anda zasu datse wannan al'amarin ba tare da b'ata lokaci ba.

Tayo gaba a hankali don samun wajen da zata iya jin kiranta sosai ba tare da karar kid'an dake tashi ba. Tazo daf! da hanyar gate d'in ne ta bangaji wata mace don yadda idanunta suka rufe da zumud'i da kuna rud'ani yasa bata ko ganin gabanta.

"Dan Allah yi hakuri." Muryar matar ta fad'a sai dai bata ko bi ta kanta ba tayi gaba da niyyar wucewa.

Cak! K'afafunta suka tsaya sanda muryar tace.

"Aunty Sadiya!!!!"

Sai da sunan ya fito sannan ta fahimci rawa muryar keyi, da sauri ta juyo don ta san kaf! garin Abuja ba wanda ya santa da Aunty Sadiya, wannan lak'abi ne da 'ya'yan yayye da k'annenta ke kiranta dashi a can Ikara.

Fuskar Mairo ce ta hau k'aru akan ta Bintu da ta cika tunaninta, Mairo wadda ta gudu da saurayi tsawon shekarun da suka dad'e da goge ta cikin lissafinsu a Babban gida.

Mairo dai yayar Bintu!

Mairo da Bintu 'ya'yan Amina 'yar gudun hijira.


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

24

Godiya mai tarin yawa ga yadda kuke bani sharhinku akan labarin nan, kuma kuke jimirin jiran k'ok'arina mai cin lokaci.

Ina rok"on Allah ya faranta muku da dukkan farin cikin duniya.

(☆_☆)

Sadiya ta ki'fta idanunta kusan sau ba adadi amma fuskar dai Mairon dake tsaye a gabanta bata canja ba, tana tsaye itama tana kallonta da dukkan wani ma'anar tsoro na duniya kamar bata yarda cewa ita d'in take kallo a gaske ba.

"Mairo? Ke nake gani? Dama nan kuka gudo ke da 'yaruwar taki? Ke kika zo kika d'auke ta tun wancan lokacin? A tunaninku kun tsira? Kun zata alhaki baya bibiya?"

Muryar Mairo na rawa kamar hannayenta tace.

"Aunty Sadiya wace 'yaruwar tawa? Bintu kike nufi? Tare kuke anan? Ai nima ita nazo nema."

Sadiya ta girgiza kanta.

"Ai babu sauran wata yaudarar ku kuma yanzu, tas! na gane abinda kuka shirya, bak'in cikinki ya kashe mahaifiyarki shine kika lallab'o kuka had'a baki da Bintu kuka kashe mana tamu mahaifiyar don kuna tunanin ita ta jawo muku komai ko? Sannan kika d'auketa kuka gudo nan da tunanin kun tsira kenan har abada?

Waya gaya muku laifi na kwanciya Mairo? Abuja har nisan duniya ne tsakaninta da Ikara da kuke tunanin zaku k'are rayuwarku asiri a rufe? Kunyi zaton..."

Kamar yadda dutse yake a k'ame waje d'aya babu alamun fitar iska ko numfashi a jikinsa, haka jikin Mairo ya sandare tun daga lokacin da Sadiya ta furta..

'... bak'in cikinki ya kashe mahaifiyarki..'

Komai ya d'auke cak! daga kwakwalwarta, duniyar ta tsaya mata a lokaci guda ba tare da ta fahimci sauran abinda muryar Sadiyan ta cigaba da fad'a ba balle hayaniyar wajen.

Abinda take haskowa daban ne a cikin kanta... Innarta ta rasu? Yanzu babu Innarta a duniya? Tun tsawon wane lokacin? Da gaske ne rabuwa dasu da tayi ne sanadin mutuwarta? Me yasa ta rabu dasu d'in? Me yasa ta bar iyayenta masu tsananin sonta a lokacin? Yadda Innarsu ke shan gori da tsangwamar 'yanuwan Baba musamman akansu shine har ta iya gudowa ta barta? Yadda Baba ke mutuk'ar sonta har ya dage wajen bata ilimin da ba kowacce d'iya ke samun irinsa a Ikara ba shine har ta iya gudowa ta barshi? Saboda Sadiq kawai? Wane alkhairi ta samu tare dashi ne ma tsawon lokacin nan banda 'ya'ya kawai? Da wace zuciya tayi shawarar hakan a baya? Da gaske ne Innarta Amina ta rasu..."

"Wallahi Tallahi billahil azeeem..." Muryar Sadiya tayi sa'ar dawowa cikin kanta.

"... Sai an kwatar mana hakkin Mahaifiyarmu akanku Mairo, sai an kashe ku kamar yadda kuka cire Imani itama kuka kasheta, waya sani ma ko harda had'in bakinku aka kashe Yaya shima... Wanda ya kashe Uwa meye a ciki don ya kashe Uba?"

Wace ce kuma aka kashe? Sannan waye Yaya? Babansu kenan?

Mairo ta tambaya cikin kanta, shima ya mutu? Ta yaya? Baba ya mutu...

Sai dai wannan karon Sadiya bata yarje mata dogon tunani ba taji ta finciki hannunta da k'arfi sannan ya shiga janta suna ratsawa ta cikin mutane da kuma teburan dake barbaje a wajen, bata san ina zata kaita ba don idanunta a hargitse suke bata ko iya kama siffar mutanen dake wajen balle ta san inda suke nufa!

***

Fadeelah ta had'iye yawu a makogwaronta sanda hasken camerar ya sake dallare fuskarta, kumatun ta har zafi suke yi saboda yawan murmushin k'aryar da take yi tana kallon mai hoton, wani dunk'ulen abu ne mulmulalle a k'asan mak'ogwaron nata, wanda duk sanda mutanen dake zuwa d'aukan hoton suka ce.

'Amarya Allah ya sanya alkhairi..."

Sai taji ya k'ara matsewa kamar zai iya tarwatsewa ne a lokaci d'aya, amma tsawon awa nawa kenan ana abu d'aya bai tarwatse d'in ba? sai nauyi kawai da zuciyarta ke k'ara yi.

Fatima ta sunkuyo da kanta lokacin da wasu k'awayen Mami data rako suka mik'e daga d'aukan hoton da akayi.

"Wai ban gane ba, baki gaiyaci ko k'awayenki d'aya bane? Ni banga ko Salma da kuke yawo tare a makaranta ba."

"Salma bata nan." Ta bata amsa a hankali.

"Tana Kaduna gidan yayarta, kuma ana hutu wa zan gaiyata?"

Tayi tambayar ne muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka a kowanne lokaci, don bayan abinda take ji, idonta na kan wayarta dake matse cikin hannunta, kusan awanni biyu kenan tana jiran shigowar kiran Al'ameen, tunda daga lokacin da yace mata sun taho yaci ace sun dad'e da sauka tun d'azu amma bai kira ta ba, Ya za'ayi ya kasa kiranta in har ya sauka d'in? Me zai tsare shi? Akwai abinda zai d'auke hankalinsa daga kanta ne a yanzu?

Duk hayaniyar taron da hargitsin jama'a bai sa wad'annan tambayoyin sun bar kanta ba, ba wai don ta damu dashi d'in bane a yanzu, sai don zuciyarta na gaya mata cewa rashin kiran nasa ba alkhairi bane.

"Shikenan ai." Cewar Fatima ganin yadda idanunta suka kad'a tana shirin kuka.

"Amma dai ki sani baki kyautawa kanki ba wallahi, shikenan ace duk wajen nan babu wani naki?"

Fatima ta fad'i kalmar NAKI ne da nufin k'awayenta, itama ta san hakan amma a lokacin sai kwakwalwarta ta fassara mata kalmar a baibai kuma ta karb'i hakan da hannu biyu. Ta d'ago idonta ta kalli tarin jama'ar dake gabanta bayan wucewar Fatiman... Ba karya bane duk taron wajen nan babu wani DANGINTA, kowa anan bare ne da bata had'a ko d'igon jini dashi ba, gashi auren da suka zo taya ta murnarsa ma na shirin d'auke ta ya maidata can wata nahiyar ta duniya inda zata yi nisa da su kansu wad'annan bare dangin data samu, watakila ita haka Allah ya kaddaro mata rayuwarta, watakila har ta mutu ba zata ga wani d'anuwanta na asali ba, watakila daga 'ya'yan da zata haifa a gaba ne zata fara kafa wani sabon DANGIN nata.

Ta fad'i hakan ne a rashin sanin cewa amsarta na dab! da k'arasowa inda take sannan komai na shirin canjawa kamar yadda ubangiji ya tsara. A hankali ta sunkuyar da kanta kad'an ta share kwalla sanda Mc d'in wajen data kasance mace ke fad'in.

"Ku kwantar da hankalinku ai mun gama photo session, yanzu zan fito muku da amarya kusha rawarku ku more."

Sarai! Fadeelah ta san Mc dasu Zahra take, don tun d'azu take hangosu suna faman zarya wajenta kan a saka musu wak'a suyi rawa, ita kuma tace komai nata a tsare yake lokacin rawa na nan tafe.

Sai dai me? A daidai wannan lokacin da Mc bata kai ga bawa mai kid'a umarnin ya saka wak'a ba, da kuma ita da bata kai ga d'ago kanta daga share kwallar ba, abinda ya zama sanadin canjawar duniyarta ya faru, Fadeelah taji durk'usawar wata mace gabanta da wani irin k'arfi mai kama da an hankad'o ta.

Hakan yasa ba shiri ta d'ago da idanunta da bata kai ga goge kwallar jikinsu ba, abinda ta gani, yasa kwakwalwarta ta sara sannan zuciyarta ta shiga duka cikin kirjinta kamar zata dagargaje...

Fuska ce irin tata sak! wadda d'an banbancin jikinta dake nuna ba mudubi tale kallo ba d'an kadan ne. Tayi niyyar k'ifta idonta ta sake budewa don tabbaci amma rud'ani ya hana ta motsawa, ta kasa gane komai har sanda matar ta kamo duk hannayenta biyu cikin tsananin mamaki makamancin nata tace.

"Bintu? Bintu kin gane ni? Mairo ce, Mairo yayarki ta Ikara!"

Fadeelah taji me tace, amma ma'anar kalmomin basu nutse cikin kanta ba saboda rud'ewa, kallonta kawai take da dara-daran idanunta dake nunawa tar! cewa bata cikin haiyacinta.

"Dan Allah kar kice kin manta ni Bintu, kin tuna Maironki dake miki kitso? Kin tuna mai goya ki har makarantar Allo? Mairo da take zuwa boarding ta dawo? Kin tuna ni Bintu? Mairo da kike cewa d'iyar Inna Amina ke d'iyar Aunty Saratu ce?"

Ta sake fad'a tana jijjiga hannayenta, sai dai kafin tunaninta ya iya lalubo wani abin ya d'orar, wata muryar ta shigo cikin kanta. Sanda ta d'aga idonta ta kalli matar dake tsaye akansu su duka biyun, sannan ne wannan abun na k'asan mak'ogwaronta ya fashe ya kuma tarwatse, d'acinsa ya tab'o har kan zuciyarta data buga tamakar zata doko ta fasa k'irjin nata, wannan duk bai isa ba, sai da kanta ya sara kuma ya shiga juyawa a take sannan ko'ina a jikinta ya shiga rawa.

"An gaya muku ni Sadiya kanwar lasa ce da in kun gujewa kowa zaku guje min? An gaya muku ban haifu a matsayin k'anwar mahaifinku ba? Gaku nan yanzu a hannuna gabadaya, ko kin manta ne ke BINTU? Kin manta ranar da kika kashe Hajiya na d'au alkawarin kashe ki kema? Da ace su kawu sun rabu dani da tun yaushe ban fanshi jinin mahaifiyata ba, amma aka barki kika tsallake kika gudu, kika taho wajen 'yaruwarki da tunanin kun tsira? Har wannan garin mafaka ce? Kun zata ba mai iya gano ku anan? Nace ku gaya min kun zata mutanen Ikara kifayen rijiya ne da basu iya yawo kamar tsinanniyar uwarku 'yar gudun hijira ba?"

Muryar ihu take tana magana cikin haki wanda hakan ya jawo hankalin mutane da yawa ya dawo wajen.

Da kowacce kalma d'aya da take fad'a, ba abinda Fadeelah ke iya fahimta saboda wani irin tarnik'in azaba da yake d'agowa daga cikin kanta.

Sai dai duk da haka b'arin kwakwalwarta guda da ya gama lalubensa a lokacin ya shaida mata cewa matar dake tsugunne a gabanta 'yaruwarta ce, kuma da gaske sunanta 'Mairo'. Wadda ke tsaye kuma sunanta 'Aunty Sadiya' 'yaruwar mahaifinta na ASALI, kuma su d'in duka biyu DANGINTA ne!

Bayan hakan data fahimta, kwakwalwarta ta rasa duk sauran k'arfinta kamar yadda rud'ani ya tsaida numfashinta, a hankali tunaninta ya sulale cikin wani bak'in duhu dake jiranta.

***

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

25

(☆_☆)

****

Ta fara sabuwar rayuwarta ne a tsaye, zagaye da wata irin busashiyar iska mai sanyi, sannan a cikin wani d'aki mai d'auke da gado d'aya.

Wajen da bata san ina ne ba ko kuma abinda ya kawo ta, ta zagaye cikinsa fiye da k'irgan mai tunani amma bata ga koda 'yar k'aramar k'ofar da zata iya baiyana mata abinda ke bayan katangar da ta raba tsakaninta da d'aya duniyar ba.

Tsoro ya cika zuciyarta fal, taji kamar zuciyar zata faso daga k'irjinta ne ta gudu zuwa wata mab'oyar daban! rawar da jikinta keyi yasa k'afafunta suka zame a hankali ta kai har dandaryar k'asa._

Ina ne wajen? me ya kawota? ko su waye suka kawo ta? meye dalilin kawo tan, sannan wace ce ce ita? Daga ina tazo?

Sai dai maimakon amsar d'aya da daga cikin hakan ta baiyana gareta sai ya zamo kamar an k'ara duhun bak'in hayakin daya lullub'e kwakwalwarta ne a lokacin, wanda ta kasa gane dalilin wanzuwarsa, tunda tunaninta yana aiki ba tare da tangard'a ba wajen k'ok'arin sanin ita d'in wace da kuma wajen da take ciki.

Sannan tana iya jin ilimin sanin abubuwa a cikin tunanin nata, hotuna da sunayen abubuwa da yawa, sanin halittar d'an adam da kuma yadda rayuwarsa ke tafiya.

Tana iya tuna yadda rana ke fitowa ta kwalle a sararin sama, tana iya tuna titi cike da d'imbin mutane kala-kala, tana iya tuna cin abinci, tana iya tuna yadda da dare wata kan haskaka doron duniya, tana iya tuna d'awaininyar uwa akan 'ya'yanta, tana iya tuna dariya da bak'in ciki sannan tana iya tuna komai na yadda d'an adam ke tafiyar da rayuwarshi, komai kuma yana nufin harda 'yan k'ananan abubuwa na mu'amala.

Amma duk da haka bata iya tuna wacece ita, ko daga ina tazo ko su waye iyayenta, Bata ma san meye sunanta ba. Hotunan fuskokin mutane da yawa suka cika tunaninta amma babu ilimin saninsu, ko yaya tayi yunkurin yin hakan sai fuskokin su maye gurbi da tarin hargitsin wasu kaloli marasa ma'ana.

Ta kasa tuna koda mutum d'aya da ta sani ko wani abu data tab'a furtawa a rayuwarta. Tsaya, rayuwarta? tana ma da ita ne a yanzun?

D'akin ya cigaba da zama a k'amewarsa yayin da mintoci suka yi tsawo suka juye awanni, a lokacin tayi duk dabarar fita daga d'akin har sai da tunaninta ya fara kad'ewa kamar yadda iska ke d'iban busasshen garin da aka shanya tana tarwatsi dashi.

Bayan wani zamanin guda, fatanta ya karb'u... Muryoyi suka cika kunnuwanta yayin da takunsu ke k'arasowa gare ta, Ta mik'e da gabadaya ragowar k'arfinta yayin da jikinta ya shiga rawa, tsoro ya sake matse zuciyarta.

Ba zata iya tantance ainihin abinda suke fad'a ba duk da ta fahimci wasu abubuwan don da sauri suke maganar yayin da takunsu ke k'arasowa. Idanunta suka ware cike da rarraunan zumud'i sanda k'arar bud'ewar boyayyiyar kofar wajen ya karad'e koina.

Ta k'ank'ance idanunta a hankali lokacin da wani haske mai yawa ya dallare idanunta, da farko ba abinda take iya gani sai hasken kawai, amma bayan 'yan sakanni... idon nata ya d'auko mata hoton siffofin dake tsaye a bayan hasken, siffofin dake mallakar muryoyin nan.

Ganinta ya koma tar! kamar lokacin da na'urar d'aukar hoto ta saita hankalinta akan wani abun!

A firgice ta farka daga nannauyan baccin da ta kasance cikinsa tsawon lokaci, don bata san dad'ewarta a hakan ba, amma dai ta san tasha yunkurin bud'e idanun nata bata iyawa.

Farin rufin d'aki tas ya shigo cikin ganinta mai hazo, ta kifta idanunta fiye da kirgen da zata iya kafin ta samu su saitu daidaita tar, a hankali kuma ta juya kanta b'angare d'aya na d'akin inda taci karo da wani gadon k'arfe mai d'auke da farar katifa irin wanda take kai. Daga gadon babu komai sai wata k'ofa da take hangowa a rufe, akwai sanyi a iska wanda ke nuna cewa koma daga ina ne akwai A.C a d'akin.

A lokacin kuma ta fara jin kanta na sarawa da wani irin ciwo mai rad'adi sannan ta kula an soka allurar k'arin jini cikin hannunta na hagu wanda yayi mata nauyi sosai. Da dukkan karfinta ta janyo kanta ta juya shi d'aya b'arin, anan ne idanunta suka ci karo da d'aya daga cikin tambayoyin dake shirin d'arsuwa ranta a lokacin. Mami Safiyya.

Tana zaune kan wata kujera mai zaman jinya, fuskarta nad'e take cikin katon mayafi, sannan da littafin addu'o'i a hannunta tana karantawa, nad'in kanta iri d'aya ne sak! da wanda take yi sanda suna can k'asar America, hakan yasa kwakwalwarta tayi tunanin ko tunaninta baya ya koma da ita zuwa wani lokaci can da aka kwantar da ita a asibiti a washington, amma kiran sallar la'asar da aka fara a lokacin sai ya k'aryata zarginta, America babu masallaci cikin asibiti da zaka ji kiran Sallah haka.

Hakan kuma yasa a hankali kwakwalwarta ta tuna mata da duk abinda ya faru kagin sumanta, abinda ya faru ranar kamun bikinta daki-daki har zuwa k'arshe.

Amma in haka ne ina Mairon da ta gani a wancan lokacin? Ina Aunty Sadiyar? Ina sauran 'yanuwan Mami suke zaune su kad'ai a wajen nan?

Sai ta bud'e bakinta da kyar ta kira sunanta. Da sauri kuwa Mamin ta d'ago da kanta, ganin idanunta a bud'e yasa ba shiri ta rufe littafin addu'arta ta taso, ta kamo hannunta d'aya da bashi da allurar ta rik'e cikin nata sannan tayi mata murmushi, wani murmushi da Fadeelah ta lura mai cike da taraddadi ne.

"Deelah kin farka? sannu kinji, yaya kike jin jikin naki?"

Kanta ciwo yake yi cikin azabar da take jin kamar zai dagargaje, amma maimmakon ta amsa sai tace.

"Da gaske ne naga su Mairo Mami? Da gaske ne abinda ya faru ba mafarki nayi ba?" Muryarta da kyar take fita sanda ta tambaya.

Mamin ta d'anyi shiru kamar baza ta amsa ba kafin tace.

"Su kika gani deelah ba mafarki kika yi ba, bari a kira likita ya duba ki, tun jiya ake zaton farkawarki dama."

Jiya? Fadeelah tayi tambayar cikin kanta. Tun yaushe take kwance kenan? Sai kuma ta tuna da d'aurin aurenta wanda a washegarin kamun ya kamata ya kasance, me ake ciki yanzu? An d'aura d'in? Ina Al'ameen d'in? Ina su Daddy da duk sauran suke? Ina su Mairo ma? In da gaske ne sunzo ina suka tafi kuma? Me yasa daga ita sai Mami?

Sai dai a lokacin da take wa kanta wad'annan tambayoyin, Mami ta riga ta saki hannunta ta nufi wajen wannan k'ofar data gani a rufe.

Kuma maimakon ta bud'e ta ta fita, sai taga ta kwankwasa kawai kamar mai jiran a bud'e su ta waje, bud'ewar kuwa akayi don taga sanda handle d'in ya motsa sannan k'ofar ta bud'e.

Wanda ya lek'o daga waje, ganinsa ne ya tattaro dukkan wani sauran azabar ciwo na duniya da baya faruwa a cikin kanta ya d'ora mata shi.

Wani murtuk'ek'en k'aton d'an sanda ne sanye cikin kakinsa da kuma bak'in gilashi, kalar fatarsa kad'ai ta kusa kamo ta kalar kayan jikinsa, duk da tsawon Mami amma sai ta zama kamar wata bebin roba a gabansa.

"Yallab'ai ta farka, ko zaku iya kira mana likita?"

Bakin Fadeelah ya bud'e a lokaci d'aya, gadinsu ake yi? Shi yasa bata ga kowa ba sai Mami kad'ai? To me yasa za'ayi gadinsu? Me suka yi...?

Ko kuma ita me tayi?

***

Kawu Yahya ya gyara zamansa kan kujerar da yake kai sannan ya kalli Daddy yace.

"Alhaji Ahmad, ina ga tun jiya muka gama yi maka bayanin cewa lauya zaka samo ka gaya masa duk wad'annan bayanan naka don mu duka nan manyanmu ne suka aiko mu bamu da iko akan lamarin nan, kuma, da zarar ta farka zamu tafi da ita, kuma ba jin akwai abinda zai dakatar da case d'inta shiga kotu, don haka nake ganin neman lauya shi ya kama ka a yanzu in har kuna son kare ta ne.

Daddy yayi ajiyar zuciya, sannan ya kalli inda suke zaune, cikin wani hotel da suka kama tun zuwansu garin Abuja kwanaki biyu da suka wuce, a safiyar da iyalinsa suka wayi gari a asibiti cikin tashin hankalin abinda ya faru gurin bikin Fadeelah, basu k'ara ganin matar data tada ballin a lokacin ba amma sunyi Imanin cewa ita ta kira wad'annan 'yanuwan nata da suka bada duk wata shaidar cewa Fadeelah 'yaruwarsu ce kuma suka kafa suka tsare cewar da zarar ta farka zasu wuce da ita ne can garinsu inda aka dad'e da mik'a case d'inta kotu cewar ta kashe mahaifiyarsu, wadda take kaka a gurinta.

Wai kisa!

Ta yaya Fadeelah zata iya kisa a rayuwarta? Ita d'in da ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba? Yayi musu bayani da dukkan iyawarsa akanta amma babu alamun ma suna saurarensa balle su fahimci abinda yake son nusar dasu.

Babban abinda ke bashi mamaki shine ya yarda cewa 'yanuwanta ne, 'yanuwan mahaifinta ma a tak'aice amma ta yaya zasu iya rufe idonsu su dinga fad'ar wadannan abubuwan akan 'yar d'anuwansu? Gashi sun k'i yarda su gaya masa komai akanta balle ma ya sami wani abin.

"Haka ne, Na fahimta kuma Nagode."

Ya yanke shawarar barinsu kawai don babu amfanin zaman, amma sai d'ayan daya fahimci sunansa Sulaiman ya tsaida shi.

"Idan zan baka shawara ka d'auka Alhaji Ahmad, ka rabu da case d'in yarinyar nan kawai, don kamar yadda ka fad'a ka tsince ta ne da girmanta da kuma wayonta, kuma d'an mutum a yanzu ko kai ka raine shi baka shaidarsa. Mu san Bintu tun tana tsumman goyo don haka mun fika sanin abinda zata aikata da wanda baza tayi ba."

Idan har ya d'auki wannan shawarar suka rabu da al'amarin Fadeelah, to a baiyane yake cewa rayuwar gidansa baza ta tab'a dawowa daidai ba, don ya tabbata bashi kad'ai ba, har Mami da take Uwa banbancin da take ganin Fadeelah da Zahra na haihuwa ne kawai amma sun riga sun karb'eta cikinsu, don wasiyyar mahaifiyarsa ta k'arshe a duniya zancenta ne, ta yaya kuwa zai dauki wannan shawarar su hakura da ita suna ji suna gani?

Tunda Daddy yake a rayuwarsa bai tab'a alfaharin rashin samun 'yanuwa ba sai a lokacin da Kawu Ibrahim ke wannan zancen, don ji idan har d'anuwa zai rufe idonsa ya dinga irin wannan abin akan d'iyar d'anuwansa da baya duniya a lokacin, to meye amfanin 'yanuwantakar?

Gaskiya ne da ake cewa DANGI suna suka tara!

Lokacin da ya koma cikin asibitin da a yanzu ya zama matattarar iyalinsa, ya tarar Hadiza, yayar matarsa tazo tare da su Zahra da a yanzu suke wajenta, a hannunsu kulolin abinci ne kala-kala amma 'yansandan nan uku da aka sa gadi sun hana su k'arasawa ma d'akin da Fadeelan take balle su sa ran basu.

Tun daga ranar Kamun nan taron bikin ya tashi gabad'aya, mutanen da suka zo washegari d'aurin aure haka

Please Login or Register in order to submit comment