Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sau d'ari kafin na Al'ameen, don shi sai tana ganinsa tukunna sannan kyawunsa da kyautatawarsa ke narka zuciyarta ta kasa mantawa dashi amma Adam.... Har tsawon bayan shekara guda rabuwarta dashi tunaninsa bai tab'a barin ranta ba duk da cewa kuwa bata k'ara ganinsa ba.

Amma duk da haka a jiya taji tana neman k'arin bayanin wani wanda zai taimaka ya faiyace mata ma'anar abinda take ji don haka ba shiri ta lalubo waya ta kira malamarta.

"Fatee yaya ma kika ce ana ganewa idan mutum yana son wani?" Ta tambaya bayan bugu d'aya kawai da Fatiman ta d'auki wayar kasancewarta ba mai saurin bacci ba.

"La'ilaha ilallahu! tsaya mana, Deelah wa kike so da aurenki?" Muryarta ta fito da sauri.

"Babu kowa, kawai ki gaya min."

"Fadeelah kwantar da hankalinki dan Allah ki fad'a min komai a nutse yadda zan fahimta, kuma kiyi k'asa da muryarki don wannan al'amarin babba ne, amma zamu san yadda zamu yi maganin ko wane irin d'*n iska ne wannan kafin ma aje da nisa, ki gaya min waye shi? A ina kuka had'u? Bai san kina da aure bane yasa kika fara son sa?"

Da mamakin me Fatin ta d'auke ta tace.

"Fatee ba wani fa nake so ba, Adam ne."

Sai ta d'anyi shiru kafin tace.

"Adam kike so? Ban gane ba? Shine kuma kike fad'a min?"

Sai da Fatiman ta fad'i haka ne sannan ta fahimci abinda ta fad'a, sannan ta fahimci amsar da take nema, zuciyarta ta riga ta dad'e da son Adam, kawai rashin samun isashshiyar dama da kuma tarin abubuwan dake kanta a baya ne suka danne hakan, amma a yanzu da komai ya kauce rayuwarta ya zama daga shi sai ita, ba abinda ya isa ya kore hakan.

Ta bud'e idanunta a hankali tana kallon kalar kayan dake hannunta, fari da ja... Jan mai haskawa kamar an watsa masa jini. Tun a jiya ta yanke shawarar cewa itama zata fad'awa Adam gaskiyar zuciyarta, idan har zai iya ajiye duk wani matsayinsa ya gaya mata wad'annan kalaman, me zai hana ita kuma ta kasa? dole ta cire dukkan wata kunya ta fad'a masa cewa tana sonsa fiye da yadda yake tunani. A rayuwarta ta fuskanci nau'i kala-kala na ma'anar k'unci don haka bata jin a yanzu kuma tana da karfin da zata iya fuskantar wani.

Maganganun Kawu Ibrahim suka haska cikin kanta.

"Wannan auren dana yi miki Bintu, riba biyu zai zame miki a rayuwa, ina ganin abinda daga ke har shi ba kwa hangowa a yanzu sai kun zauna da juna tukunna, Allah ne shaidata ina k'okarin gyara rayuwarki ne kan tafarki mai inganci, don haka a wannan lokacin babu abinda ya dace dake sai auren, don duk dad'in rayuwar da zaki samu a gaba ba zai rufe miki wani bak'in cikin ba, amma in har kina zaune ne a k'ak'ashin inuwar aure, wannan rahamar kad'ai zata yaye miki abubuwa da dama..."

Sai yanzu take fahimtar ma'anar kowacce kalma daya fad'a, sai yanzu ta hango irin rahamar da yake fad'a, to don me yasa kuwa zata kasa ajiye komai tak'i karbar wannan rahamar?

Matsalar shine zuciyarta tace zata iya, amma bata san ta yaya bakinta zai iya bud'ewa ya fad'a masa cewa itama tana son sa ba... Don gashi tun ba'aje koina ba kayan da zata saka ma sun mata wuyar zab'a.

***

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

BABI NA K'ARSHE!

(☆_☆)

"Barka da safiya."

Muryarta ta kutsa cikin tunaninsa, d'auke da d'umin da yafi na coffee d'in da yake sha a lokacin, yana zaune ne a falo cikin lallausan carpet d'in dake tsakiya mai kalar ruwan toka yana danne-danne a computersa, ya d'ago ya kalle ta, kallon da a lokaci guda yaji zuciyarsa ta tsaya cak na wasu 'yan sakanni kafin kuma ta cigaba da bugawa da k'arfin da yayi barazanar girgiza kofin hannunsa.

Tana sanye ne cikin wata doguwar riga ta material fara k'al, amma kuma an watsa mata adon wasu jajayen fulawowi masu haske akanta! haske sosai kamar an sirka su ne da kalar jini, daga inda yake zaune kuma yana iya jiyo k'amshin nan nata dake tsima zuciyarsa.

A baiyane yake cikin idanunta cewa taci baccinta ta gode Allah, alhalin shi sam bai samu baccin ba sai wajen hud'u na dare don har yaso ya makara sallar Asuba, kuma da ace zai je wajen aiki ma da ya dad'e da makara, a yanzu haka k'okarin turawa Nasir dake jiransa ayyukan da zasu yi yau yake, ya yanke shawarar ba zai fita yau bane, don ko yaje office d'in ba lallai ne ya tab'uka wani abun azo a gani ba, hankalinsa ba zai kwanta ba sai in har yaji amsar da Fadeelah zata bashi, amsar da zata baiyana masa matsayinsa a wajenta.

Ya san ya gaya mata ne cewa tana da damar da zata yi tunani daga yanzu zuwa tsawon lokaci, amma ba zai iya ba, a yadda yake jin kansa yanzu ba zai iya jiran hakan, don a daren jiya zuciyarsa ta sake jaddada masa cewa ba zai iya cigaba da zama da ita a irin tsarin da suka d'auko ba, in ba haka ba zai aikata abinda daga ita har shi zasu zo suna nadamarsa ne, don in zuciyarsa ta fad'i abu to da gaske take hakan ne.

Maimakon ya amsa gaisuwar tata, sai ya mik'o mata hannunsa alamun ta k'araso, yana ganin yadda ta kalli hannun kamar mai shawara da zuciyarta kafin ta mik'o masa natan, kuma a take ya nutse cikin taushinsu yayin da wani abu kamar zugi ya shiga bin jijiyoyinsa.

Ya matso da ita gabansa, ta durk'ushe cikin carpet d'in idanunta a k'asa, a cikin abu guda biyu bai san wanne yafi burge shi ba, kawalliyarta ko kuma ladabinta. Ba tare da ya saki hannun nata ba yace.

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdlilah."

Sai ya d'auko plate d'in sandwich d'in da yake ci, ya saka a tsakiyarsu, rabi akan k'afarta rabi a tasa.

"Bismillah, mu ci."

Ta girgiza kanta a hankali sannan tace.

"A'a, Thank you." Ya gyad'a kansa sannan shima yace.

"Thank you too for wearing this dress."

Maganar tasa ta d'ago da idonta ta kalle shi, ya d'aga mata duk girarsa biyu yace.

"Nayi zaton 'yar godiya muke yi ne."

Sai tayi d'an guntun murmushi tana kallon gefe. Yace.

"Me yasa baza ki ci ba?"

"Bana iya cin abinci da sassafe."

Ya sake gyad'a kansa.

"Okay, ni kam tun d'azu nake ci ina jiran fitowarki kuma."

Ya lura tayi tunanin wani abu daban kafin ya d'ebe hakan da cewa.

"So nake ki fad'a min meye wannan abin don na san dai Sandwich ba haka yake da dad'i ba."

Baiyi mamaki ba sanda ta juyo da idonta ta sake kallonsa, don sun dad'e da saba irin wannan hirar, sabon abu shine yadda take zaune kusa dashi da kuma hannunta dake cikin nasa. Tace.

"Kuma sunanshi kenan, don ance ba'a canjawa tuwo suna."

Ya k'ara kaishi bakinsa sannan yace.

"Na fahimta, amma kuma meye tuwon?"

Ta d'anyi shiru alamun mamaki kafin tace.

"Oh! na manta fa kai ba bahaushe bane, amma dai duk da haka zaka san tuwon ai, tunda kana zuwa Ikara."

Ya d'age gira d'aya cike da jin dad'in sakewarta.

"Waye yace ni ba bahaushe bane, bayan jininsu na yawo a jikina?"

"Jini daban, amma a magana dai ba wanda zai kira ka bahaushe balle kuma al'ada."

Sanyin muryarta ya shiga aika masa da sak'onni kala-kala cikin kansa, bai sanda ya ajiye kofin hannunsa ba tare da ture batun Nasir dake jiransa, ya k'ara gyara zamansa a gabanta yace.

"Kin san kuwa nine top kuwa a class d'inmu?"

Girarta biyu ta had'e.

"Wane class d'in?"

"Bayan dawowata Nigeria nayi joining wani online class da ake koya hausa ne a cikin 'yan watanni kawai, kuma nine mai highest grade a class d'in"

"Kuma an koya muku komai?"

"Komai." Ya tabbatar mata.

"To shi kanshi mai koyarwar yana buk'atar guidence gaskiya, don ina jin a al'adar bahaushe tuwo yana zuwa ne a saman abubuwa da yawa."

"Na fa san tuwo leelah, kawai dai ban gane a sentence d'in da kika saka shi bane."

Ta cije gefen lebb'enta na k'asa tana kallonsa.

"Kenan ba'a koya muku komai ba tunda baku san karin magana ba."

"Na san karin magana mana, akwai littafi guda ma dana tab'a karantawa akansa."

"Zaka iya tuna d'aya?"

Ya sake gyad'a kansa.

"Inaga kamar akwai wani da ake cewa kulin kuli fita..."

Sautin dariyarta ne ya katse shi daga k'arasawa, dariyarta mai dad'in gaske da kunnensa ya saba da jinta a kwanakin nan, amma kuma zuciyarsa ta kasa karb'ar sabon, don duk sanda taji ta sai ta fitar da wani rad'ad'i dake watsuwa a k'irjinsa.

"Me ya baki dariya?"

Yana ganin yadda tayi saurin tsaida kanta ta hanyar cije lebb'enta na k'asa sannan ta girgiza kai alamun babu komai. A lokacin ne ya rasa dukkan wata dauriyarsa ya mik'a hannunsa ya rik'o d'aya natan sannan muryarsa k'asa-k'asa yace.

"Zan iya samun amsata a cikin dariyar nan?"

Murmushin fuskarta bai tafi gabad'aya ba amma kuma bata ce komai ba, me hakan yake nufi? Nasara ko akasinta? tunaninsa ya dagule zuwa wajaje daban-daban, ya rasa wanne zai tsamo ya d'auko bashi mazaunin a lokacin, sai ya k'ara sauke muryarsa can k'asa sosai kamar mai rad'a ya kira sunanta.

"Fadeelah, jiya bayan na barki ban iya barci ba ko kad'an, tunani kala-kala zuciyata ta dinga yi akan irin amsar da zan samu a wajenki, ban sani ba ko kin shirya fad'a min ita a yanzu amma ina son ki sani cewa duk abinda zaki yanke kar kiyi la'akari da rayuwarki ta baya ko kuma irin k'addarar data had'a mu, wannan duk abu ne daya riga ya wuce kuma bamu da iko akansa.

Amma a cikin zukatanmu zamu iya canja komai, Allah ya bamu damar da a yanzu zamu iya sake labarinmu ya tafi daidai da irin rayuwar da zamu shimfida a gaba, we have a whole new chance to rewrite all those sad and angry memories of our lives and create a better us that will shine the future."

Ya san ya tab'o wani abu mai girma a rayuwarta da wannan maganar, ya tab'o wani babban b'angare dake rufta zuciyarta a kullum, don a lokaci guda yanayin fuskarta ya canja zuwa na wata Fadeelan daban ba wadda ta fito da annashuwa ba. Kuma yana sane yayi hakan, don a jiya babu irin tunanin da bai yi ba na irin abubuwan da zasu sa Fadeelah ta kasa amincewa dashi, kuma a cikinsu zuciyarsa ta yarda cewa wannan dalilin yafi dukkanin sauran k'arfi, babban rauninta shine rayuwarta ta baya da take wa kallon hargitsi wanda in har zuciyarta na rik'e da hakan ba zata tab'a barinta ta cigaba ba, abubuwa zasu cigaba da rugujewa ne a duk lokacin data tuno hakan, shi yasa ya kudiri niyyar rage tasirin wannan tunanin nata don ya san ba zai tab'a iya goge shi baki d'aya ba.

Ta girgiza kanta tana k'okarin zame hannayenta amma ya sake rik'e su gam, cikin sigar rik'on da yake son ta fahimci cewa daga yanzu yana tare da ita a kowanne irin yanayi.

"Bana tunanin akwai wata rayuwa da zanyi a gaba da zata goge dukkan tabon dake rayuwata, bana jin akwai wani abu da zai mutane su manta matsayin da suka san ni dashi a baya, tabo wani abu ne da baya tab'a barin d'an Adam, don haka ko mutuwa nayi na tabbata duk wanda ya sani zai tuno ni da wad'annan tarin tabon dana riga na samu, don duk da 'yancin dana samu a yanzu bana jin zan tab'a zama wani abu mai daraja a idon duniya."

Tsawon wucewar wasu sakanni, Adam bai ko kifta idanunsa balle yayi wani motsi, zuciyarsa tana b'antarewa ne jin cewa da gaske hasashensa game da ita gaskiya ne, har a yanzu tana ganin kanta a matsayin mara daraja saboda mutane kawai.

Zuciyarsa ta matse da irin zurfin da yaji a muryarta, ya had'iye yawu a hankali sanda wani abu ya mai girma ya cika k'irjinsa.

A hankali ya mik'a hannunsa d'aya ya shafi gefen fuskarta, ta rufe idanunta amma bata motsa ba, tana k'ame a wajen kamar abunda baya numfashi, zai iya k'irga sautin bugun zuciyarta.

"Kin san wani abu lealah? We all have scars and they are an important part of our lives, sune abinda ke nuna rauni da gazawarmu a matsayin 'yan adam, I have alot of my own too, amma hakan baya nufin zan kyale su su durk'usar dani a cigaban rayuwata. Misali, a lokacin dana gama high school na gano cewa iyayen da nake tare dasu basu ne asalin mahaifana ba, abun yayi min ciwo sosai, zuciyata ta shiga zullumi da damuwa tsawon lokaci, har sai da mates d'ina suka yi joining college ina zaune a gida babu abinda nake yi.

A lokaci d'aya kuma sai tunanina yayi hankali, ya bani shawarar cewa rayuwa ba zata tsaya ba don kawai an samu tangard'ar wani abun, living with the past will only make me more vulnerable and frail, zan k'are rayuwata ne ba tare dana samu komai ba, saboda haka rana d'aya kawai na tashi na sami wani littafi da biro na rubuta sabon labari akaina, na tsara komai ya tafi daidai da mafarkina har zuwa matsayin da nake a wancan lokacin, sannan na fara kokarin cigabawa daga nan, ya zama duk sanda wani abu na kewaye na ke kokarin tuna min da zahiri sai in d'auko labarin nan in karanta in kuma cigaba da inda na tsaya."

A wannan lokacin ta bud'e idanunta ta kalle shi, akwaibkyallin hawaye a idanunta amma sai tayi dariya... Rana ta farko kenan da tayi dariya tana kallonsa, kyallin hakan kuma ya haska har cikin zuciyarsa yasa shi murmushin da bai shirya ba don abin yaso ya bashi mamaki, waye yake kuka yana dariya a lokaci d'aya?

"Ta yaya mutum yake canja labarinsa kuma ya yarda da hakan?"

"Very simple..." Ya fad'a yana cigaba da tracing gefen fuskarta cike da jin dad'in yadda bata hana shi ba yace.

"Zaki bud'e zuciyarki ne ki fito da dukkan mafarkinki na duniya, sanann ki yarda da kanki, ki bawa kanki yak'inin da ko shaid'an bai isa ya ture hakan ba balle kwakwalwarki."

Fuskarta ta juya kowanne b'angare cikin hannunsa kafin tace.

"Bana jin zan iya, don ko ina da mafarki ni ba sanshi ba."

"Kowa yana da mafarki a duniyar nan leelah, baza ki tab'a rasawa ba don ko ni na san naki da yawa, in kina so zan iya canja labarin mu a yanzu nan."

Ta d'auko da idonta ta sake kallonsa, sai ya kautar da nasa kad'an don idan ya cigaba da kallonta zai iya manta zancen wani labari ya jata cikin jikinsa.

"Ta yaya? Ta yaya zaka iya canja komai?"

A hankali ya sunkuyar da kansa sannan ya sake rik'o hannayenta, idonsa ya kai kan combination d'in fari da baki'n lallen da bai gama barin farcenta, ba zuciyarsa ta matse da tunanin cewa don shi akayi lallen. Yayi gyaran murya kad'an sannan ya sake yin k'asa da muryarsa cikin amon daya san zai ratsa zuciyarta yace.

"Let's say, shekaru goma da suka wuce baya, kina Ikara, tare da mahaifanki da kuma yayarki Maryam data gama makaranta, komai yana tafiya daidai a rayuwarku saboda kuna kusa da babban gida inda kowa ke mutuk'ar sonku dalilin kyawawan halayen mamanku...."

Fadeelah bata san lokacin data rufe idanunta ba jin hakan, lallai wannan shine mafarki, mai d'auke ka zuwa wata duniyar da babu kishiyar komai, a hankali taji wata kwalla mai d'umi na shirin taruwa a idanunta,

"... a cikin haka ne mahaifinku ya had'a Maryam aure da d'an wani amininsa, kowa yayi farin cikin hakan don Sadiq yana da hankali sosai da kuma nutsuwa. Bayan bikinsu rayuwa ta cigaba da gangara muku a hankali cikin tarin nasarori, ki gama makaranta kuma kowa ya yarda da ra'ayinki na cigaba da karatu, watakila Kawu Ibrahim ko wani daga cikin yayyenki ya samo miki makaranta kika fara zuwa daga nan gida kina dawowa, komai yana tafiya daidai a rayuwarki..."

Ya d'anyi shiru kafin ya cigaba.

"A wannan lokacin ni kuma na dawo daga America a matsayin d'aya daga cikin jikokin babban gida daya samu schoolarship na karantar aikin lauya, kowa yayi murna da kammala karatuna, kuma mahaifina ya tura ni gidajen 'yan uwa in gaishe su don na dad'e bana k'asar..."

A daidai nan kwallar da Fadeelah ke kokarin rikewa ta gangaro kan kumatunta, ta gyad'a kanta a hankali don ta hango inda labari ke dosa.

"... Watakila Sai'd yayi min jagora muka shiga bin gidajen 'yan uwa, gida na k'arshe da muka je shine gidanku, muna falo a zaune ana gaisawa kika dawo daga makaranta, ban san me ya faru ba amma a wannan lokacin kowa na wajen ya b'ace a idanuna sai ke kad'ai kawai nake iya gani kina tahowa saitina, sanye cikin doguwar rigarki mai kyau sannan da glasses na karatu a idanunki, kika k'araso kika gaishe damu amma bayan muryarki bana iya jin motsin kowa na d'akin, kika karb'i babyn yayarki daga hannun mamanki kina tayi mata wasa da dariya kina kallonta...."

Muryarsa ta d'anyi rawa kafin ya cigaba.

"... Amma ni babu abinda nake so a wannan lokacin illa in kalle ki kawai."

Ya sake yin shiru yana murza yatsunta cikin nasa, itama kuma bata cewa komai ba tsawon wucewar wani lokaci.

"Daga nan me ya faru?" Zuwa can muryarta ta tambaya a hankali alamun tana son jin cigaban.

Sai ya sunkuyo da kansa daidai satin nata ya had'a goshinsu, abinda ya fad'a na gaba ya sauka kamar ruwan sama akanta, kowacce kalma ta tab'o can k'asan ruhinta.

"May be na samu sa'ar samun numberki a wajen Sa'id, then we talk. May be kuma na fara aiki ke kuma kika cigaba da karatunki, amma muna tare da juna kodayaushe, we talked about almost everything, all those little and silly things but there never sound silly to me saboda dasu nake iya rayuwa a kullum. An then one night... Na gaya miki cewa ina sonki!"

Bata san lokacin da wani murmushi mai kama da dariya ya sub'uce mata ba, don har sai da fuskarsu ta jijjiga a tare, dama ace so samu ne...

"Zaki k'arasa?" Ya tambaya cikin husky muryarsa.

A wannan lokacin ne kuma ta kasa iya rik'e kanta, taji ba abinda take son irin itama ta fallasa mata sirrin tata zuciyar, ta fad'i kalaman da har yanzu bakinta bai gama tsara su ba, don kowacce jijiya a jikinta a matse take da zumud'in hakan. Ta d'ago da kanta a hankali ta kalle shi, shima ita yake kallo, idanunsa d'auke da wani abu daya k'ara dulmiyar da tunaninta. Ta d'aga masa kai a hankali kafin tace.

"Nima ina sonka Adam, na dad'e ina sonka... na soka tun a lokacin da nake tunanin na tsane ka, lokacin da ban ko ni wacece ba, sannan na so ka har a lokacin da rayuwarta ke cikin hargitsi, kuma insha Allah zan cigaba da sonka fiye da yadda duk wata mace zata so ka a duniyar nan, na karbi rahmar da Allah yayi min ta bani kai, insha Allah zan zama abin alfaharinka kuma ina rok'on Allah ya bani ikon da zanyi maka biyayya da dukkan iyawata."

Bata kai ga rufe bakinta ba Adam ya jata cikin jikinsa gabad'aya, ya jata zuwa wata duniya da ba san da wanzuwarta ba tsawon rayuwarta, hannayenta suka shiga rawa sannan kwakwalwarta ta rud'e, Ta dai ji sanda yayi magana amma bata iya fahimtar komai a cikin abinda yace ba sai kalamai uku kawai.

"...an bani ke!"

Bayan haka ba abinda take iya fahimtar sai yadda bakinsa ke motsawa akan nata, yana kissing d'inta kamar bazai daina ba, kamar iya wannan lokacin kad'ai suke dashi a rayuwarsu, kamar babu wata sauran magana da ta rage a duniya.

Hawaye mai d'umi ya gangaro daga idanunta sanda tattausar muryarsa ta furta akan bakinta.

"Ina sonki Fadeelah..!"

***

BAYAN NA MUTU!

BAYAN WATANNI TAKWAS!

Babban gida a cike yake da mutane fal maza da mata wanda duk wanda ka gani jini na gidan, don banda matattu hatta wad'anda ba'a fiye gani a gidan ba da wad'anda suka dade basa garin aka fara mantawa dasu kowa na nan.

Taro ne na farko irinsa da aka tab'a had'awa a gidan bisa kokarin Adam da kuma Sa'id, don sune umul'abaisin haddasa shi, kuma ba karamar wuya suka sha ba kafin hakan ya tabbata, don babu wanda aka gaiyata ta waya, da kansu ska dinga yawo gari-gari duk inda wani jinin gidan ya yada reshe har suka samu had'o kan kowa.

Babban falon Kawu Da'njuma cike yake da dattijai magidanta wad'anda sune 'ya'ya kad'ai na gidan, in ka d'ebe matansu kuma da suka taru a b'angaren gwaggi Ramatu, bayan gaka kowacce kusufa-kusufa ta gidan a cike take da jikoki da 'ya'yan jikoki har da tattab'a kunne ma suna ta wasa da tsalle-tsallensu, kowa cikin shiga yake mai kyau kamar yau take sallah. Don babu wanda zaka gani kaga fuskarsa babu annashuwa.

Filin dake harabar wajen Kawu D'anjuma shine inda aka kawata da rumfuna da kuma tausasan dardumai a matsayin inda za'a zauna, sannan ga tarin cima nan kala-kala da Adam yasa akayi ordering daga wani babban gidan abinci dake cikin garin Zariya. Abinci ne fal! Kuma kala-kala da duk yawan mutanen gidan babu hangen zasu iya tashinsa.

A wannan lokacin Fadeelah na b'angaren Aunty Hassanah ita dasu Mairo da kuma sauran wasu daga cikin sa'anni irinsu, suna ta kokarin packaging wasu 'yan souvenirs ne da suka yi shawarar a rabawa 'yan mata da kuma matan aure.

Wani maroon lace ne a jikinta da yasha adon fararen duwatsu, anyi mata d'inkin riga da skirt mai bud'ewa sosai, fatar jikinta tayi wani haske alamun hutu da nutsuwa da kuma d'an jaririn ciki.

Duk aikin da suke, Afra na mak'ale a kusa da ita don yanzu kusan ta zama 'yar gidanta. Wata Nafisa 'yar wajen Gwaggo Hajiya tana ta nacin taje wajenta amma tak'i, don haka takanas ta tura kasuwar rana aka siyo mata wata k'atuwar 'yar tsana, ai kuwa tana ganinta ta tashi da sauri har tana fad'uwa ta nufi wajenta, aka yi ta dariya.

A yanzu Fadeelah ta sake da 'yan babban gida sosai, don Adam ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ta akai akai har komai ya fara yin sauk'i a ranta, wannan fargabar da take yi akansu ta shud'e.

"Kin san Kawu sulaiman ne ya shigo yana tsokanata wai munyi wariyar 'yanuwantaka mun ture maza a gefe in ba haka su ina nasu k'ullin."

Mairo ta fad'a mata lokacin da suke k'arasa shirinsu a cikin d'akin Aunty Hassana bayan an gama aikin kayan.

"Kin san nima kwanaki da muka zo haka yayi ta jana da hira har yana ce masa wai ai zai zo ya kawo min babbar 'yarsa ta min hutu."

Mairo ta gyad'a kanta kafin tace.

"Ina ga shi da sauki ma tunda 'yan kewaye-kewayensa yake tayi, amma gwaggo Lami jiya fa bayan kun fita da Aunty Hassanah aikowa tayi wai a kai mata su Afra su gaisa, wallahi kasa rufe baki nayi saboda mamaki."

Duniyar kenan! Fadeelah ta ayyana a ranta, a da wace irin kiyayya ce mutanen nan biyu basu gwada mu ba, Kawu sulaiman yana d'aya daga cikin wad'anda suka haddasa tsanar innarsu a zukatan 'yan Babban gida, sannan takakkiya yayi har Abuja don ya d'auko ta a gurfanar da ita gaban shari'a, innarsu kuwa wace irin bak'ar wuya ce bata sha ba a wajen gwaggo lami.

Hirarsu ta katse lokacin da Ummi 'yar gidan Aunty Hassanah ta lek'o ta sanar dasu cewa an aiko cewa mata su fito.

Sanda suka isa harabar wajen da kowa ke ta hayaniyar samun wajen zama tare da makusantansa, zuciyar Fadeelah tayi mak'il da farin ciki ganin d'imbin al'umar da gabad'ayansu ke amsa sunan 'yan uwanta, ta tuno wani lokaci can baya daya wuce sanda take ganin kamar ita kad'ai Allah ya halitta a duniya bata da kowa a duniya sai su Mami kawai, Hakika dukkan wani farin cikin duniya in zaka dubi asalinsa yana komawa ne ga DANGI!

Taron ya tafi kamar yadda aka tsara komai, anyi zumuncin daya zama mak'asudi, anyi nishad'i, anyi raha kuma anci an k'oshi. Bayan nan Kawu Danjuma da wasu daga cikin dattijan gidan sunyi nasiha mai k'arfi akan muhimmanci zumunci da kuma irin k'alubalen da suka fuskanta a baya na rashin samun fahimtar juna tsawon shekaru, an yiwa wad'anda suka rasu addu'a, an yiwa Habiba fatan samun waraka, an sake jan hankali da nuna illar abinda Sule ya aikata, sannan kuma anyi fatan wannan taron zai k'ara had'in kai tsakaninsu kuma za'a yi k'okarin d'orar da hakan. Kawu Bashir kuma ya tsara cewar kafin zuwan wani taron za'a sanar da wad'anda ya kamata don kowa ya kawo gudunmawarsa ba kamar yanzu da kusan komai ya ta'allak'a akan Adam kad'ai ba.

Adam. Shi da

Please Login or Register in order to submit comment