Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne mai yawan fita ba, saboda haka kusan kullum yana gefen Hajiya yana k'ara b'antare ragowar rusashshiyar alak'ar dake tsakaninsu.

"Me kike yi anan?"

Ya tambaya yana kallon bokitin dake gabanta.

Me? na zata kana zaune a wajen lokacin da Hajiya ta jefo min tarin kayan wankinta da sanyin safiyar da ba kowa ya gama tashi ba taje inje in wanke.

Taso ace zata iya gaya masa hakan ba tare da ta jawowa kanta wani abun ba.

"Kayan Hajiya nake wankewa." Ba yadda ta iya, ta amsa a hankali.

"Toh tana jiran kokonta in kin gama."

Ashe wannan lokacin shine MAFARIN HARGITSIN RAYUWARTA! ashe sai da ya riga ya gama zuba gubar sannan yazo ya same ta, ashe daga ita har Habiba dake nata shirin sun fad'a tarkonsa ne cikin rashin sani... Sai ta janye idonta hankali ta maida k'asa, wata kwalla mai d'umi ta taru a cikinsu, karo na farko taji kuka na shirin kwace mata a cikin kotun...

Ashe ba tsakaninta da Hajiya kawai Sule ya rusa a baya ba, rayuwarta gabad'aya ya ture daga tubali, ya barta tana reto a gefe, wani reto mai ciwo da wuya... Idonta ya dinga hasko mata duk irin wuyar da ta sha tunda daga lokacin da tayi hatsarin nan ta farka kwakwalwarta a mace, kowanne k'alubale data fuskanta BAYAN TA MUTU.... duk akan wannan gaskiyar da bata fi tsakanin minti biyar a fad'e ta ba!

Sai ta kasa rik'e kukan da take dannewa a k'irjinta, kawai ta kifa kanta akan teburin gabanta sannan sautinsa ya shiga fita cikin siririyar muryarta da wani irin amo mai k'arfi, kuka ne irin wanda bata tab'a yi ba a wannan sabuwar rayuwar tata, kuka ne da Bintu kawai ta sanshi ba Fadeelah ba... Kuka ne irin wanda Bintu kawai ta tab'a yinsa a wasu keb'abb'un lokuta...

Sanda aka nemi Mairo aka rasa...

Sanda Innarta ta rasu...

Sanda Babanta ya rasu...

Da sanda aka raba ta da Inna Saratu!

Kuka ne dake fitowa tun daga k'asan zuciyarta, tana iya jin yadda k'arfinsa ke jijjiga kowanne k'ashi na jikinta tamkar zasu b'alle su rabu da junansu, tana iya jin yadda jijiyoyin jikinta ke nannad'ewa kamar ana k'ulle su... Sannan tana iya jin yadda bangwayen kotun ke amsawa da sautinsa tamkar zata iya zama silar tsagewarsu!

BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

40

(☆_☆)

Zaune akan kujerarsa, Alk'ali yace.

"Bayan dukkan bayanai da kuma hujjoji da kotu taji daga kowanne b'angare, Kotu ta yanke hukunci cewa yarinyar da ake zargi bata da laifi, haka ma duk sauran wad'anda ake zargi daga baya sakamakon gano ainihin wanda ke bayan kisan Hajiya Balaraba, sannan kuma kotu ta yankewa Sule wanda aka samu da laifin kisan hukuncin d'aurin rai da rai tare da aiki mai tsanani a gidan yari. Da wannan hukuncin kuma, kotu ta kawo k'arshen shari'ar da Iyalan Malam Idris Musa suka shigar watanni biyu da suka wuce."

Adam ya rufe file d'in gabansa a lokacin da wajen ya rud'e da hayaniya bayan tashin Alk'alin.

Ya mik'e tsaye shima jikinsa babu kwari, *It's over!* komai ya k'are... Ubangiji ya amsa addu'arsa ya kawo k'arshen shari'ar nan a yau, Fadeelah zata cigaba da rayuwarta sannan zumuncin Babban gida kuma zai gyaru!

Kawu Ibrahim yace dashi.

"Ban san ta yaya zan gode maka ba Adamu, ban san me ma ya kamata ince ba."

"Nima ban cancanci godiya ba Baba, nayi abinda ya dace ne kawai." Ya fad'a a hankali kamar mai rad'a.

Sai yasa hannu ya rik'o kafad'unsa duka biyun yace.

"Ina alfahari da kai Adamu, ina alfahari da kai irin alfaharin da mahaifinka ya mutu yana burin samu, A yau ka shigo cikinmu ka tabbatar masa da mafarkinsa, kayi abinda ba wanda zai tab'a irinsa, ba a wajenmu kad'ai ba Adamu, wallahi duniya kaf zata shaida cewa kai tauraro ne daban a cikin taura..."

Bai k'arasa ba Adam ya rungume shi kawai, don shi kansa a wannan lokacin ji yake tsakaninsa da magana akwai tazara mai nisa.

Alh. Ahmad, marik'in Fadeelah yace dashi.

"Kayi aiki mai kyau Adam, kayi namijin k'okarin da ba kowa ne zai iya shi ba, mun gode kwarai da gaske kuma na tabbata wannan case d'in zai jawo maka muhimmiyar d'aukaka a Nigeria, you did a brilliant job!"

Sauran mutanen Babban gida suka yanyame shi da murnar Allah ya sanya alkhairi da kuma jinjina ga k'ok'arinsa. Sa'id ya mik'o masa hannu suka gaisa sannan yace.

"Ba sai ka gaya min komai ba, na riga naga dukkan abinda na dad'e ina jiran amsarsu daga wajenka yau. Kayi k'ok'ari sosai yaya, Allah ya k'ara k'arfin basira."

Bayan mazan, mata ma birjik suka yi ta taruwa a gabansa da irin tasu murnar, ba 'yan Babban gidan kad'ai ba, har da mutanen waje na Ikaran da kuma jama'ar gari wad'anda suka zo kallo, sai dai duk a cikinsu wadda yafi rik'ewa itace marik'iyar Fadeelah, matar Alh. Ahmad.

Da hawaye a kowanne idonta ta kamo hannunsa d'aya da duka nata biyun, ta dinga jero masa wasu tarin addu'o'i da bai tab'a samun irinsu ba a rayuwarsa, don addu'o'i ne irin na uwa kuma bahaushiya wadda bai tab'a samu ba.

Har yaje kwanciya a wannan ranar bayan tarin hayaniya da kuma cike-cike na rufe case d'in kafin a baza shi ga Media, abu biyu ne basu gushe daga ransa ba, farko addu'o'in matar da yaji kowa na kira da Mami Saffiya, sannan kuma kamar koyaushe a rayuwarsa... Idanun Fadeelah, sanda ta tafi ta rungume yayarta da yaji ana kira da Mairo bayan awanni hud'u da gama shari'ar kafin a kammala komai kotun ta sallameta, Mairon ce farkon wadda ta fara zuwa ta rungume sanda ta fito wajen tarin jama'ar dake jiranta, yana iya tuna yadda dukkan jikinsu ke jijjigawa da wani irin kuka da yafi k'arfin a kira shi da na murna, kuka ne da su kad'ai kawai suka san abinda suke fitarwa daga cikinsa.

Fitarwa. Kalmar ta d'auki hankalinsa, ya lumshe idonsa kad'an sannan ya k'ara lumewa cikin filon dake k'asan kansa, fatansa a lokacin shine Fadeelah ta gama fitar da dukkan wani bak'in ciki yau cikin kukan da ta sha, kukan da ya hana shi samun magana ma da ita, don ba zai so ace ta cigaba da wahalar da kanta da irin wannan kukan ba... Ta cigaba da wahalar da idanunta!

Ya rufe idanunsa a hankali tare da hoton nata a cikinsu sanda azababbiyar gajiyar dake nukurkusar sa taci galaba akan kowanne b'angare na jikinsa.

Sai a lokacin ya fahimci abinda Sa'id yaji lokacin da suka dawo daga Mimbiri, don sai a sannan ya shiga biyan bashin kowacce gwagwarmaya da yayi tun sanda ya karb'i shari'ar Fadeelah. Burinsa a wannan lokacin bai wuce ace ya samu kamar kwanaki uku ba abinda yake sai bacci ba.

Sai dai me? Washegari ya tashi da abubuwa guda biyu, farko wani irin matsanancin zazzab'i mai zafi daya rufe shi, na biyu kuma labarin rasuwar SADIYA daga Babban gida!

***

Sadiya ta rasu ne a dalilin hatsarin mota data samu a hanyarta ta komawa Abuja tsakanin garin Zariya da Kaduna, cikin matsanancin gudun da mai motarsu keyi yaci karo da wani mai irin nasa gudun ya bangaje shi, abin da ya haddasa motar ta shiga wul-wuli kenan akan titi tana wullar da mutanen dake cikinta, Sadiya ta booth ta fito kanta ya bugu da kwaltar titi ya tsage ta mutu a take, kuma har aka kawo ta gida bayan su Kawu Yahya da aka kira ta wayarta sunje sun d'auko gawarta, akayi mata wanka da sutura, jini bai bar zuba daga kan nata ba, haka akayi mata sallah aka kaita kabarinta.

Ba wai alhinin rashin Sadiya ne ya girgiza 'yan Babban gida ba, a'a yanayin mutuwarta ne da basu kad'ai ba hatta jama'a da yawa daga cikin Ikaran basu tab'a gani ba, don da farko ma da aka kawo ta rasa mai yi mata wanka aka yi, saboda yadda kowa ya tsorata da ganin gawarta kai a rabe, sai daga baya aka samu su Kawu Ibrahim da Kawu Nazifi da kuma limamin unguwarsu suka yi mata wankan sannan aka sallace ta.

Don haka babu laifi a jajantawa Sadiya kuma anyi zaman makoki na gaske, don ko Fadeelah wadda tun bayan sallamarta take b'angaren Kawu Ibrahim tare da Mairo, ta ture komai ta jawo wannan dangantakar ta cewa ko ba komai Sadiya k'anwar mahaifinta ce, Dangin ta ce ta hanyar da baza a rasa irin jininta a nata jikin ba, saboda haka ta bud'e zuciyarta tayi mata addu'a da fatan Allah yayi mata rahma.

A yau ake sadakar uku don haka gidan ya cika fiye da koyaushe, kusan kowanne b'angare da mutane ana karb'ar gaisuwa, suma suna zaune a falon Aunty Hassanah tare da wasu daga cikin danginta. Ta juya kanta gefe kad'an inda Aunty saratu da Mami Saffiya ke zaune waje d'aya, duniyarta guda biyu had'e a waje d'aya!

Mami ta koma Abuja tun washegarin ranar da aka sallameta daga kotu, amma yau ta sake biyo jirgi ita da Faruk suka zo addu'ar ukun wadda daga ita za'a share makoki... A tsakaninta da Aunty Saratu bata san soyayyar wa zata fifita sama da ta d'aya ba.

Aunty saratu ta sota tsakani da Allah kuma ta kula da ita tun a lokacin da mahaifiyarta take raye, sannan bayan ta rasa jigon iyaye duka biyun, ta kula da ita har bayan sanda aka raba su, sanda take zaune a gaban Hajiya, wani lokaci da ya zama a duniya kaf! itace kad'ai wadda zata gani taji dad'i.... Ga Mami Safiyya kuma, wadda ta tsince ta rana tsaka ta hanyar dangin karere, amma tun daga wannan lokacin bata tab'a banbanta ta da 'yayan cikinta ba, tana yi mata soyayya ne irin wadda Allah yake halattawa uwa ga d'anta.

Kuma cikin wani ikon na Allah sai su biyun suka had'a kansu tun sanda suka had'u a zama na k'arshe a kotu, to mai hali iri d'aya ne ya had'u da d'anuwansa. Ta lumshe idanunta a hankali sanda muryar Mami wadda ke waya ta shiga kunnenta.

"To ai ban gane bane Abdullahi, wai fingerprint d'in Samiran ne yak'i hawa?"

Bata san sanda ta dakatar da duk wani tunani ba ta tsaida hankalinta akanta.

"To me yasa tun jiyan baka d'auke ta daga islamiyya ba kuje a sake yi mata?"

Ta sake tambaya tana k'okarin nemo wani abu cikin jakar gabanta, jin haka sai Fadeelah ta juyar kanta d'aya b'agaren d'akin, ta sauke ganinta akan mutanen dake zaune sannan zuciyarta ta shiga bugawa da sauri.

Tsawon wani lokaci Mami ta dad'e da daina yi mata zancen Al'ameen, amma shekaranjiya bayan sun dawo gida, sanda ta samu kad'aicewa da Kawu Ibrahim ya gaya mata cewa su Daddy sun zo masa da zancen an fasa aurenta da Al'ameen saboda mahaifiyarsa ta zab'a masa wata a can zai aura. Kwata-kwata ta manta da hakan don a lokacin ta k'okarin farfad'owa take, sai kuma rasuwar Sadiya da zancen rashin lafiyar Adam tazo ta danne maganar a zuciyarta.

Saboda haka yanzu ta fahimci zancen na Mami, k'okarin shirya tafiyar su Zahra can Washington take yi saboda bikin nasa yazo.

A lokaci guda taji kwarin jikinta na neman guduwa kamar an zare mata laka, amma bata ga dalilin da zai sa taji hakan ba don ana shirin bikin Al'ameen... mutumin daya yaudareta, ya kuma tilastawa Mami akan ta taya shi b'oye cewa zai aure ta ne ba da izinin mahaifiyarsa ba, Allah ya sani bata ji haushin Mami na yin hakan ba ko kad'an, saboda ta san irin yadda ta d'auki Al'ameen kuma watak'ila a lokacin ta fahimci itama tana son shi. Sai ta mik'e daga wajen gabada'ya ta koma cikin d'akin Aunty Hassanan ta kwanta.

Tunaninta ya gangara kan maganar da ta tab'a gayawa Al'ameen a America, lokacin daya fara cewa yana sonta.

Zuciyarka ta gaya maka tana sona, saboda haka kana k'okarin bata abinda kake so ne kawai ba tare da tunanin halin da ni zan shiga ba.

Na gaya miki...

Baka gaya min komai ba Al'ameen sai son zuciyarka kuma na fahimce ka sarai saboda haka nima ka fahimce ni ka fita daga rayuwata, na fad'a maka bana sonka kuma bana sonka a cikin rayuwata.

A yanzu ta kuma yarda Al'ameen son zuciyarsa kawai ya sani, baya tab'a duba halin da waninsa zai shiga illa tabbatuwar abinda yake so kawai, sanda ake shirin bikinsu, bai damu da yaya mahaifiyarsa zata ji ba in har ya aureta ko kuma ita kanta ta yaya zata iya rayuwa a inuwar wadda bata k'aunarta.

Duk abinda ta gaya masa a wancan karon gaskiya ne, abu d'aya kawai da tayi k'aryarsa shine da tace bata sonsa, wannan k'arya ne, ta so shi a wancan karon kuma ta so shi a lokaci baya kad'an saboda iya mu'amala da kuma kyawunsa, amma banda yanzu... Yanzu data shiga duk wani nau'i na kalar rayuwa ta fito harda kuwa wanda ya sata a ciki.

Ta ja guntun tsaki kafin ta janyo hijabin Mairo dake gefe ta rufe fuskarta dashi.

Alak'arta da yayarta ta gyaru tun daga ranar da aka sallame ta daga kotu, a ranar data fahimci cewa ba wai abinda kake dashi ne a rayuwa mai muhimmanci ba, illa wanda kake dashi a rayuwarka.

Don haka a yanzu kullum tare suke kwana suke tashi cikin tarin labaran da basa yankewa akan abubuwan da kowannensu ya shiga bayan zamanin da suka rabu, sai dai hirar bata tab'a gangarawa kan shari'ar da aka gama da kuma d'an zaman kurkukun da tayi, ta fahimci Mairo na k'ok'arin tallafota ne don ganin ta farfad'o ta saki jikinta sosai, saboda ko zancen fasa aurenta sau d'aya ta tab'a yi mata shi da fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ya kuma bata wanda yafi shi. Sannan itama bata fiye yi mata zancen mijinta ba illa na 'ya'yanta kawai, kuma hakan ya taimaka sosai wajen wanke zuciyar kowannensu daga uk'ubar da suka fito.

Kawu Ibrahim yace zata koma wajensu Mami in al'amura sun natsa amma ita gani take yanzu ba zata iya tafiya tayi nisa da Mairo ba. Aunty Hassanah ta gaya mata dukkan irin abinda ya faru da mijinta da kuma irin zirga-zirgar wahalar da yake yi na ganin ta koma, wanda har yanzu bai samu kwakwakwaran mutum d'aya da zai tunkara a Babban gida ba hatta kuwa shi Kawu Ibrahim d'in, daga shi sai su Saminu masu taimaka masa ke ta bulayinsu har yanzu.

Ita kanta bata son Mairo ta koma wajen mutumin daya cuce ta, amma Aunty Hassanah tace komawar tata shi yafi ko don k'ananan 'ya'yanta da ba'a san hannun wa zasu fad'a ba in har ta dage dole sai ta rabu dashi. Zuciyarta ta cigaba da sak'e-sake cikin duhun hijabin da yayi mata dad'i a fuska kafin a yaye shi.

"Tunanin me kike yi?"

Mairo ta tambaya tana zama a gefen gadon.

Ta d'ago da idonta ta kalle ta daga kwancen, bata san yaushe tayi wanka ba amma ta canja hijabin jikinta zuwa wani sea green daya k'ara haskata, Allah ya sani dole ne mijinta ya nace da bibiyar ta koma gidansa don Mairo tana da kyau, irin kyawun da ta tabbata koina zata shiga a fad'in duniya babu wanda zaiyi mata kallon daban, saboda irin wannan kyan ne da d'aid'aikun mutane kawai Allah ke zab'a cikin jinsi ya azurta su dashi..

"Wai nace tunanin me kike yi?"

Ta sake katse ta da alamun damuwa a fuskarta.

"Ba komai..." Ta amsa tana k'ok'arin cire wani guntun farce a yatsanta na hagu.

"... Kawai tunaninsu Afran ki nake, ina son in gansu ko suna kama dake."

Da jin haka sai ta janyo hijabin da ta cire a fuskarta ta shiga ninkewa.

"Kar ki wani damu kanki da wannan tunanin, d'azu Saminu yazo yake ce min Babansu yace zasu zo tare da 'yanuwansu suyi gaisuwa."

Sai ta tsaya daga k'ok'arin cire farcen.

"Da gaske? Yaushe zasu zo?"

"Ban sani ba gaskiya, zancen da nazo gaya miki ma daban ne, Saminun yace min wai an sallami Adam daga asibiti, an maida shi gida yanzu."

Adam. Asibiti. Kalaman suka yi nauyi a cikin zuciyar Fadeelah, yau kwanaki uku kenan, tun ranar da aka sami labarin rasuwar Sadiya, Sa'id yayi waya cewar Adam ma ya tashi da wani irin zazzab'i har asibitin da suka je sun rik'e shi, don haka tun wannan ranar mutane ke zarya daga wajen makokin zuwa cikin Zariyan dubo shi. Bata samu tayi magana dashi a ranar da aka sallame ta ba don bata ma k'ara ganinsa ba tun bayan da aka gama zaman kotun, tayi tunanin zuwa dubo shi itama amma ta san Kawu Ibrahim ba zai bari ba.

Don tun sanda suka shigo b'angaren Aunty Hassana a daren da k'afarta ta tako cikin Babban gida bayan tsawon wasu shekaru, bata lek'a koina ba, ko mutanen dake zuwa ganinta ma kad'an ne saboda rasuwar Sadiya data d'auke hankalin kowa, kuma hatta manyan babu wanda yayi wata magana har yanzu.

"Ya warke kenan?" Ta tambaya a hankali tana kallon Mairon wadda ta girgiza kanta.

"Saminu yace a yadda ya ganshi jiya dai yana jin jiki, watakila saboda zirga-zirgar dubo shin da ake yi ne ya matsa sai ya koma gida. Kin san wanda ba bahaushe ba ba lallai yaso wannan jelan na mutane ba."

Sai ta gyad'a kanta a hankali tana k'ara tuno gutsirarrun labarin Adam wanda Mairo ta tsinta itama ta gaya mata. Komai ya bada ma'ana a cikin labarin, abinda kawai bai bada ma'ana a cikin kanta ba shine me yasa daya ganta yak'i nuna ya santa? Don ko sama da k'asa zata had'e baza ta tab'a yarda cewa ba shine Adam d'in data sani a America ba.

"Wallahi da Kawu zai yarda, da gobe Saminun ya kaimu munje mun dubo shi, mutumin da yayi maka babban taimako ai ya wuce irin wannan uzurin ya hana ka dubo shi."

Cewar Mairo, ta cigaba da cewa.

"Bawan Allan nan yana da kirki Bintu, d'an zamana a gidan nan baki gayadda yake hidima da mutane ba, yanzu haka fa komai na d'awainiyar b'angaren nan shi yake yi, sannan Aunty Hassana tace min yanzu duk mai wata buk'ata a Babban gida Sa'id kawai ake samu a fad'awa, da ya gaya masa shikenan wallahi ko nawa ne zai bada, shi kansa Kawu D'anjuman ba k'aramin sauk'in abubuwa ya samu ba da zuwansa, bashi da kyashi ko kad'an irin na al'adarmu."

Tana rufe baki Mami ta shigo d'akin.

"Har kin fito daga wankan? Banga wucewarki ba." Ta tambayi Mairo kafin ta sami bakin gadon itama ta zauna.

"Na fito Mami, kuna ta magana da Aunty Saratu na wuce."

Mairo ta amsa da murmushi.

"Sannu Fadeelah, ya gajiyar jikin naki?"

"Da sauki sosai, Aunty Saratu tayi min gashi jiya naji dad'in jikina."

"Toh Allah ya sawwak'e, d'azu dana shigo Kawu Ibrahim yake ce min ya kira Daddy a waya cewar muzo wani satin akwai zama da za'ayi, ya gaya muku?"

Mairo ta girgiza kai.

"Wallahi bamu sani ba, kuma jiyan nan ma muke zancen komawar tata."

"To watakila sai ranar in munzo zamu tafi tare, Deelah na d'ebo miki wasu kayan sakawar, Hassanah ta tura yaranta su karb'o miki daga wajen Farouk."

"Toh Mami, Madallah."

"Yanzu zamu tafi kuma, Farouk yace jirgin da zamu bi k'arfe uku zai tashi, kina ganin zaki iya fitowa soro ku gaisa dashi? Nayi nayi ya shigo yace wai mutane sunyi yawa."

A Babban soron shigowa cikin gidan suka sami Farouk bayan Aunty Hassanah da Aunty Saratu duk sun amince cewa taje d'in, Fadeelah ta cika da mamakin ganin yadda ya fara ajiye k'asumba a 'yan watanni kawai da ta rabu da ganinsa. Taso ta tambayeshi su Usman da harkar makaranta amma ta lura kallon da yake mata na tsantsar tausayawa ne don haka ta bar zancen sai ta koma gida tukunna.

Motar da suka d'auko ta kawo su Ikara daga airpot d'in Kaduna na tsaye a gefen hagu na k'ofar gidan kasancewar rumfunan zaman makokin daga dama suke, don haka ita da Mairon data rako ta suka lek'a kad'an har zuwa tashinsu.

Sai dai me? Motar tasu na tashi wata k'erarriyar mota k'irar Ford ta maye gurbinta, kuma kafin tayoyin motar su kai ga gama tsayawa ko kuma kafin su Fadeelan su kai ga juyawa cikin gida.. Wanda ke zaune a mazaunin direba ya bud'e k'ofarsa da wani irin sauri ya fito.

Wucewar 'yan sakanni kawai kafin idanun Mairo su daukar mata siffar Sadiq tsaye yana kallonta, bata k'ara ganinsa ba tun bayan ranar daya kawo ta saboda a haka kamar yadda yake kallonta da mamaki itama mamakin ne ya tsayar da k'afafunta daga juyawa ta koma ciki, sai da sauran k'ofofin motar suka shiga bud'ewa ne sannan komai ya tarwatse, ta juya da sauri tayi cikin gidan.

Fadeelah ta bita da kallo kafin ta dawo ta sake kallon mutumin dake tsaye a gefen bud'add'iyar k'ofar motarsa, da farko bata gane shi ba sai a yanzu data juya sannan taga kamar an saka wani abu daya zabge shekarun fuskarsa ya hasko mata shi a sanda ta sanshi... Sanda take raka Mairo bayan gari ta had'u dashi, da sanda Mairo bata fahimtar komai in ba kalamansa ba... ta gane shi sarai da sunan mutumin daya zama farkon hargitsa rayuwarsu.

Daga cikin sauran k'ofofin motar da suka bud'e, mata uku da maza biyu suka fito, a hannun d'aya daga cikin matan wani abu ne daya zuk'e duk fushin dake shirin tasiri a zuciyarta, wani d'an farin yaro tas! da kammaninsa ke baiyana cewa jinin Mairo ne sannan rik'e a hannun d'aya daga cikin mazan, yarinyar da bata wuce shekaru biyar ba sanye cikin wasu milk kaya masu kyau!

Fadeelah taji kwalla ta cika idanunta a take, taji dama tana da iko da lokaci a sannan, da ta dawo da rayuwar baya lokacin da innarsu ke raye, ta hasko mata wannan lokacin don taga 'ya'yan Mairo, 'ya'yan da rabo ya rantse akansu ya zama dole ta tsallake mahaifarta a wancan lokacin don su zo duniya, sai kawai ta k'arasa gurin matar dake rik'e da Muhammad ta karb'e shi.

Mairo tayi zaman dirshan kan gadon Aunty Hassanah tana sak'e-sake a ranta, ta san cewa a wata guda daya wuce zuciyarta ta yanke mata cewa bata damu da mijinta ba, ta d'auki kudirin yanke duk wata alak'a dake tsakaninsu ta kuma yi alk'awarin cewa zata yi nesa da duk wani abu daya dangance shi, amma ganinsa kawai da tayi yanzu ya tuna mata da cewa Sadiq ne fa!

Wannan Sadiq d'in da taso fiye da komai a rayuwarta, d'an bafulatanin nan da tun gani na farko da tayi masa a bakin rijiyar da suke zuwa d'ebo ruwa taji zuciyarta ta fad'a duniyarsa... Ta rufe idanunta a hankali tana tuna banbancin yadda ta barshi da yadda yake a yanzu, kammaninsa sak! suke dana mutumin da yayi nesa da kwanciyar hankali.

Ya tara gemu har da gashin baki, gashin kansa babu taza sannan daga takalmi har hular kansa basu dace da dogwayen kayan daya sanya ba... A baiyane yake cewa rashinta ya tab'a shi ta kowanne b'angare don kammanin fuskarsa ma kad'ai sunfi kama dana mara lafiya. Sai dai duk da haka, ta san ko kad'an halin da yake ciki bai kamo k'afar irin halin da ita ya sakata a ciki ba.

Sallamar Mairo ta katse tunaninta, tana d'ago ido kuwa zuciyarta dake da rauni ta sake karyewa ganin Muhammad rik'e a hannunta, shima ya rame kad'an sannan yayi d'an wuya.

"Afrah tana wajen sauran, gasu nan sun shigo falo."

Fadeelah ta fad'a tana k'ok'arin mik'a mata Muhammad d'in, sai dai me yana had'a ido da ita ya juya kansa sanann ya fara kuka alamun ba zai je ba.

"Kaga fa, mominka ce." Cewar Fadeelah, amma maimakon ya fahimce hakan sai ma k'ara tsallara kukan da yayi ya shiga zillewa yana k'ara k'ank'ame jikin Fadeelan, sai kawai itama ta juyar da kanta gefe ta fara hawaye, dama ta sani cewa alhakin Muhammad ba zai barta ba, ta yakice shi daga jikinta a sanda lokacinsa bai kai ba, don haka dole ne yayi zuciya da ita.

Tayi saurin goge hawayenta sanda Aunty Saratu tayi sallama, biye da ita Zakkiyya ce da k'annen mahaifiyarsu su biyu, ta zamo daga kan gadon sanda su suka zauna akai. Afrah na ganinta kuwa ta janye hannunta daga cikin na Zakkiya ta fad'a jikinta tana fad'in.

"Mommy Oyoyo, mommy oyoyo!"

Karo na farko tun bayan rabuwarta dasu itama ta rungume 'yarta sannan ta cusa kanta cikin wuyanta ta shiga gaishe su.

"Lafiya k'alau Maryam, ya hakuri kuma?" Suka had'a baki wajen amsa mata.

"Alhamdulilah." Muryarta ta fito a hankali.

Aunty Saratu ta nuna Fadeelah tace.

"Ga k'anwarta nan, wadda aka sallama daga kotu."

Mairo tayi shiru tana saurarar rad'ar da Afrah ke mata yayin da suke barka da kuma yiwa Fadeelah jaje.

"Mommy kullum sai nace Daddy ya kawo ni wajenki amma sai yayi tace min sai gobe, kuma nace masa ya

Please Login or Register in order to submit comment