Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta d'ad'e da rashin mutane ba, ko da dandazon yaran da suka taru daga can nesa a kowanne b'angare suna hangensa, ko giftawar kawunan matan dake lek'ensa ta saman 'yan katangar gidajen su, ko kuma d'irka-d'irkan matasan da Maigarin yasa suka rako shi har k'ofar gidan tsohon da suka biyo kwatancen nemansa tun daga Ikara... Fatansa kawai ya samu abinda yazo nema ya kuma ganshi ya d'auki hanyar juyawa.

Tana can tana jiransa, tasa dukkan fatanta akansa, tana fatan Allah zai amsa addu'ointa ta hanyarsa, kamar yadda su Kawu Ibrahim da 'yan uwanta ma ke da yak'ini akansa...

Don haka dole ne yabi duk wata hanya da zata sa fatansu ya karb'u, duk wata hanya kuma da zata tabbatar da abinda
abokin karawarsa ke tsoron faruwarsa, wato samun nasararsa!

A daidai wannan lokacin Jamilu, matashin da suka d'auko a hanya kuma yake taya su fafutukar mutanen su saurare su ya fito daga cikin gidan da yake kallo, yayi saurin gyara tsayuwarsa cike da zumud'in jin abinda zai fito daga bakinsa.

"Sunce ka shiga."

Ya gyad'a kansa, alamun ya fahimta sannan yabi bayan jamilun, wad'annan matasan ma suka dafa musu baya.

Soron farko na gidan bashi da rufi in ka d'auke yalolon buhun da aka rufe k'ofa dashi kawai, na biyu kuma dogo ne mai cike da duhu saboda irin dakakkiyar azarar da akayi masa rufi da ita, daga nan sai faffad'an tsakar gida irin na kowanne gida mai iyali na k'auye... Jerin d'akuna masu baranda daga kowanne b'angare sannan k'atuwar bishiya a tsakiyar filin.

Sai dai kuma ba irin yadda gidan ya kamata ya kasance bane, don babu ko irin kajin dake kiwo a tsakar gida balle kuma mutane, k'ofar kowanne d'aki a rufe take bam! wasu ma da alama garin sauri har da labule aka had'a aka gark'ame tare, sai a lokacin yaji zuciyarsa ta fara mamakin irin tsaurin halin mutanen kamar yadda Sa'id ke fad'a.

Sa'id. Ambaton sunansa yasa ya tuna abinda ya faru d'azu a fadar Maigari.

Malam Salisu bashi da halin fitowa ya iya ganinka a yanzu, don haka zamu barka ka ganshi amma da sharad'i.

Mai garin ya fad'a bayan gwagwarmayar da aka sha kafin su iya gane hausar sa.

Ance mana ku biyu kuka zo, don haka zamu rik'e d'anuwanka har sai ka gama da Malam Salisu lafiya, sannan mu fito maka dashi.

Ya tuna yadda babu wani dogon tunani ya amince da hakan kuma har ya bada agogon hannunsa don aje a taho da Sa'id d'in, Anya kuwa baiyi kuskure ba?

"Yana cikin d'akin nan..."

"Ku, ku jira mu anan ko?" Jamil ya juya ga wad'annan matasan dake bin bayansu, kamar basu so ba amma dai suka ja suka tsaya a k'ofar d'akin. Adam ya zare k'afafunsa daga cikin takalmansa a hankali sannan ya sunkuya ya zura kai cikin 'yar k'aramar k'ofar d'akin.

Babu duhu a ciki kamar yadda yake tunani, sai rashin isashshiyar iska da hakan ya fallasa tsamin dattin d'akin, sai dai ba wannan ne ya tsayar dashi a k'ofar ba, sai ganin tarin mutane fal zaune a cikin d'akin, yabi fuskarsu da kallo d'aya bayan d'aya kafin ya tsaya akan d'an tsohon dake kishingid'e a tsakiyarsu, anan ya sami amsarsa ta farko kafin wadda yazo nema. Wad'annan mutanen 'ya'ya da kuma 'yan uwan tsohon ne, sun zo kare shi ne saboda yazo yi masa magana.

Karo na farko tun bayan wani lokaci yaji murmushi na shirin kub'uce masa, yanzu fisabilillahi zai nik'o gari ne daga can wata duniya yazo har nan don ya cutar da wannan d'an tsohon?

"Bismillah..." Jamilu ya nuna masa wajen zama, ba musu ya zauna ya tankwashe k'afafunsa akan daud'ad'iyar tabarmar.

"Maigari ya shaida mana wai kazo ne don kayi wa mahaifinmu wasu tambayoyi."

D'aya daga cikin mutanen ya fad'a. Adam ya had'iye wani guntun yawu a bakinsa sannan yayi gyaran murya a hankali, ta ina zai fara? Ta yaya zai cewa mutanen nan shi lauya ne kuma tambaya yazo yi masa game da shari'ar kisa?

"Da gaske ne daga can Ikaran kake?" Wani ya sake tambaya yana k'are masa kallo.

Ya san abinda ma'anar tambayar ke nufi, baiyi kama da mutanen da suka sani a Ikara ba don haka yayi saurin tarar tunaninsu.

"Mahaifina d'an Ikara ne, amma ba'a can na tashi ba, kuma ba'a can nake ba yanzu haka."

Wani da fuskarsa ke nuna manyanta ya ya gyad'a kai sannan yace.

"Tambayar me kazo yi masa?"

Abin yaso ya d'aurewa Adam kai? Shi tsohon baya magana ne? In su zasu yi masa maganar to ta yaya zai sami amsoshinsa? Sai ya juya ya kalli mai tambayar yace.

"In baza ku damu ba zan iya magana dashi?"

Har mutumin ya bud'e baki zai ce wani abu tsohon nan ya d'ago hannu ya dakatar dashi.

"Kar ka damu Sama'ila ai duk kuna zaune babu wani abu..." ya juyo ga Adam.

"Samari, zancen Habiba ne ke tafe da kai?"

Dammmm! Wani abu ya buga a cikin kan Adam, idanunsa suka zare a lokaci d'aya, kamar yadda idanun 'ya'yansa ma suka cika da mamaki suna kallonsa.

"Ta yaya ka sani?"

K'arin mamakinsa, sai tsohon yayi murmushi yace.

"Na san kai ba bahaushe bane d'an nan, da watak'ila ka san karin maganar dake cewa 'Alhaki kwikwiyo ne, dole ne yabi mai shi, irin wannan ranar na dad'e ina gujewa Habiba."

Adam ya gyara zamansa a hankali, kafin tsohon ya sake tambaya.

"Kai waye a wajen Habiba? Ban tab'a ganinka ba."

"Ni d'an k'anin mijinta ne, ba'a garin nake ba har ka tafi shi yasa bamu tab'a had'uwa ba."

Tsohon ya sake gyad'a kansa sannan yace.

"Ni na san shari'ar nan baza ta tab'a mutuwa ba sai anyi ta, an samu yarinyar da ta gudu ne?"

Adam ya gyad'a kansa.

"Eh ta dawo."

Tsohon ya girgiza kansa.

"Daga Habiba har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin."

Da sauri Adam ya tare shi.

".. Ban gane abinda kake nufi ba."

Tsohon ya juyo ya kalle shi sosai.

"Ko waye ya turo ka kaje ka gaya masa ba Habiba ce ta kashe Hajiya Balaraba ba."

Adam ya had'iye yawu shima yana kallonsa sannan yace.

"Zan iya sanin abinda yasa kace hakan?"

Kafin ya amsa, ya juya ga d'ansa dake gefe ya fad'i wani abu da Adam bai ji ba, d'an ya mik'e da sauri ya kama kafad'unsa, ya mik'ar dashi zaune sosai sannan ya koma ya zauna.

"Ita Habibar da ta turo ka wajena na tabbata ta gaya maka sana'ata a Ikara kafin kazo nan, don haka na saba da ita ne ta hanyar yawan siyan magungunan gargajiya da take yi a wajena.

Ana gobe za'a yi wannan rasuwar, tazo wajena da bayanin abinda kake nema yanzu, tace tana neman taimakona da in sayar mata da sassak'en wata bishiya da yake kamar guba idan mutum yaci shi, da farko bata shaida min me zata yi dashi ba sai da na matsa mata taga da gaske ba zan bata ba har sai naji dalilinta tukunna, sannan ta gaya min cewa ta yanke shawara ne kawai zata kawar da Hajiyar daga duniya don ta samu damar mik'e k'afa a gaba tayi komai yadda take so babu mai hana ta.

Ba tun a ranar ba Habiba ta saba sakin jiki ta fad'a min duk sirrinta saboda ina biye mata a dukkan ra'ayoyinta.. saboda haka na san duk irin matsalar dake tsakaninta da Hajiyar. Ta gaya min a lokacin cewa taje wajen malamai da yawa, amma dukkanin ayyukan da akayi mata babu wanda yaci akan hajiyar, don haka k'awarta ta gaya mata in har ta samu wannan sassak'en tasa mata a abin ci ko sha, to nan take zata mutu.

Sai dai a wannan ranar, ban biyewa mata kamar yadda na saba ba, na gargad'e ta da cewa abinda take shirin yi mai girma ne, kisa ba k'aramin abu bane da zata yi ya wuce kamar sauran shirinta, amma duk iya k'ok'arin da nayi wajen ganar da ita, bata saurare ni ba ta ajiye min mak'udan kud'in da basu tab'a shiga tsakanina da ita ba tace lallai in bata.

Ganin kar in rasa kud'in a wannan lokacin yasa na amsa mata sannan nayi mata alk'awarin kawo mata sassak'en har gida, washegari kuwa na sami wani sassak'en da bashi da tasiri ko kad'an naje na kai mata a matsayin wanda take nema, saboda har a lokacin zuciyata bata bani cewar in sa hannu a kisan mutum ba."

Adam ya gyad'a kai a hankali sanda tsohon ya kawo nan, bai sani ba ko a duk duniya kaf akwai sunan abinda ke faruwa a cikin kansa a lokacin, don bashi da wani kokwanto tsohon gaskiya yake fad'a, ya yarda da maganganunsa irin yardar da zai iya tsayawa a gaban ko waye ya tabbatar da hakan, amma ta yaya wannan al'amarin ya faru? In har ba Habiba ce ta kashe Hajiya ba to waye? A lokaci guda kwakwalwarsa ta shiga hasko fuskokin 'yan Babban gida d'aya bayan d'aya, kamar a sannan za'a nuna masa wanda yake nema.

"Zaka iya yi min dukkan tambayoyin da kake so yanzu."

Muryar tsohon ta katse shi, ya maido da idonsa kansa, sai a sannan ya lura cewa ashe bai ma yi masa tambaya ko guda d'aya ba amma ya sami fiye da rabin amsoshin da yake nema.

"Me yasa duk ka gaya min wannan zancen kai tsaye?" Ya yanke shawarar fara yi masa tambayar da ko 'ya'yansa dake zaune zaso sani.

Tsohon ya k'ara yin murmushi kamar mutumin dake cike da raha sannan ya kai hannunsa ya yaye bargon da ya lullub'e inda k'afafunsa suke, sai dai me? Wajen fayau yake babu k'afafun, balle cinyoyi, sai alamarsu kawai daga can k'ugunsa wanda ke nuna alamun yankewa akayi. Adam ya d'ago daga kallon wajen ya kalle shi.

"Naga ishara mai tarin yawa daga Allah d'an nan, baka labarin halin da na shiga da irin wahalar dana sha kafin in iya k'arasowa nan abu ne mai tsaho, don haka ba kai ba, ko waye a yanzu yazo neman wani bayani daga wajena, wallahi zan gaya masa abinda na sani komai munin irin rawar dana taka a ciki kuwa."

Kamar yadda sama-sama suke gane abinda yake fad'a, shima ba kasafai Adam ke gane kowacce kalma ta cikin hausar sa ba, amma yana iya fahimtar abinda yake nufi, don haka ya gyad'a kansa a hankali kafin ya sake yin wata tambayar.

"Idan har abubuwan da ka gaya min duka gaskiya ne to waye yayi kisan kenan? Tunda labari ya dad'e da fita cewar Hajiyar ta mutu ne sanadiyar gubar data ci."

Sai da ya maida bargon ya rufe jikinsa sannan yace.

"Wanda ya taki zance akan zance ya kuma taki sa'a akan sa'a."

Adam bai fahimta ba, kuma fuskarsa ta nuna alamun hakan.

"Ina nufin wanda ya san duk abubuwan da Habiba ke k'ullawa kuma yaji zancena da ita."

D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci, tsakanin shi da tsohon babu wanda ya sake magana, da alama kowannensu da irin tunanin dake faruwa akansa, tunanin Adam bai wuce na jiran tsohon ya k'arasa masa abinda yake nema ba, don ya yarda in har ya san duk wad'annan abubuwan, to abinda ya rage ma ba zai shige masa duhu ba.

.

.

.

.

.

.

.

.

Zuwa can tsohon yayi ajiyar zuciya sannan yace.

"Sule yaje wajena a wannan ranar bayan fitar Habiba."

Sule. Sule. Sule! Adam ya zana sunan a cikin kansa da manyan harafai, sai dai waye shi? A Babban gida yake? anya ya tab'a ganinsa kuwa?

"Amma bani da tabbas akansa don sai bayan awanni da fitarta sannan yazo, kuma abinda ya kawo shi ba sabon abu bane, dama yazo neman maganin ciwon mahaifiyarsa kuma nace ya dawo a ranar."

"A ina ya same ka?" Adam ya tambaya kai tsaye.

"A cikin gidan da nake zaune inda nake ganin mutane."

"Ka tashi ka barshi shi kad'ai a lokacin?"

Bai amsa ba sai da ya d'ago ya kalle shi.

"Idan kana tunanin ya d'auki sassak'en gubar ne to ba abu me mai yiwuwa ba, babu wanda ya san inda nake ajiye magunguna na balle har a gansu, sai dai in nine na fito dasu."

Adam ya girgiza kansa.

"Ba tunani nake ya d'auki gubar ba, tunani nake yaga maganin a lokacin da ka fito dashi zaka kaiwa Habiba a matsayin gubar, kuma ya gane ba gubar bace."

Sai da tsohon ya bud'e baki cike da mamaki sannan ya gyad'a kansa.

"Kwarai sanda ya shigo ina dab da fita, don magariba ta k'arato kuma so nake in shiga Babban gida a lokacin da maza suka tafi masallaci, mata kuma ke d'aki suna sallah, don haka na fito da maganin yana ajiye a gefena."

Adam ya gyad'a kansa.

"Kuma kana da tabbacin kuma babu wanda ya ganka a lokacin da ka shiga wajen Habiban?"

"Ina dashi, na tabbata babu wanda ya ganni."

"Akwai..." Adam ya bashi amsa yana kallon fuskarsa.

"... Don ba Habiba ce ta turo ni wajenka kamar yadda kake zato ba, wani ne daban wanda ya ganka a lokacin da ka shiga."

Ga mamakinsa sai kawai tsohon nan ya bushe da dariya a maimakon murmushin da yake yi.

"Na fahimci kai lauya ne tun shigowarka nan yaro, kuma ba lauyan dake kare Habiba ba, A ina wannan yarinyar ta samu gatan mai d'auko mata lauya kamar kai?"

Adam ya girgiza kansa.

"Ba shine abinda ya kawo ni ba, so nake ka gaya min da gaske babu wanda ka gani a lokacin da zaka shiga wajen Habiba?"

Tsohon ya sake girgiza kansa.

"Hanyar shiga b'angaren Habiba a can k'arshen Babban gida yake, don haka ba waje ne da mutane suka fiye yawan zuwa ba, in banda Anna dake zaune a wajen da wuya kaga wani a hanyar."

"Anna... Anna, wacece ita?"

Kalmomin har karo suke wajen fitowa daga bakin Adam. Tsohon ya sake dariyar data zame masa jiki.

"Kar kasawa kanka wani fata, Anna mahaukaciya ce, ba abinda take ganewa balle tayi maka amfani."

Ba fata kad'ai ba, Adam ji yayi zuciyarsa ta d'auki k'addarar shari'ar kacokam! Ta maida kan Anna mahaukaciya. Dukkan wannan rikicin ya fara ne daga Babban gida, an kashe Hajiyar a cikin Babban gida, An d'orawa Bintu sharrin kisan a Babban gida, an shigar da k'ara kotu daga Babban gida, ya baro Babban gidan ya taho wannan luluk'in bincike.... Ashe watak'ila AMSAR na dai cikin BABBAN GIDAN!

"Wacce hanya ce zata yi mana sauk'in fita titi?"

Ya tambayi Jamil bayan komai ya kammala tsakaninsa da mutanen Mimbiri, ya gama da tsohon nan, yayi sallama da maigari har kuma sun saki Sa'id d'in da aka tsare a fadar Maigari.

"Komawa hanyar Abuja yanzu tafiya ce mai nisa kuma hanyar bata da kyau, daga nan yafi kusa da Keffi, gwara ku fita keffin sai ku d'auki hanya ta titi ku koma yafi sauki."

Hakan suka yi kuwa, Jamil yayi sallama da wan mahaifinsa sannan yabi su har wata mararraba da ta d'auki hanyar fita k'aramar hukumar keffin daga nan shi kuma ya sami motar da zata koma k'auyensu, suka rabu bayan Adam yayi masa alkhairin da yake ganin zai koma k'auyensu ne a matsayin attajiri!

"Ba irin tunanin da ban kawo akaina ba duk da irin bayanin da suka yi min, gani nake kamar k'arya suke wani abu ya faru da kai ne, wallahi har na fara hasko yadda zan caka musu wuk'ar dake jikina don su barni in fita in nemo ka...."

Sa'id ya shiga fad'a bayan sun rabu da jamil sun d'auki hanyarsu, Adam bai katse shi ba har sai da ya kai k'arshe, idonsa na kan titin birjin da suke bi sannan yace.

"Sa'id wacece Anna?"

"Anna?" Ya tambaya cike da mamakin me ya kawo sunanta kuma a wannan halin.

"Of course, ita."

"Wani abu ya gaya maka game da ita? Cewa yayi ta san wani abu?"

Sa'id ya jero tambayoyin bi da bi, Adam ya cije lebb'ensa alamun baya son doguwar magana a lokacin, fahimtar hakan da Sa'id yayi yasa ya d'an kalli gefe hannunsa dunk'ule akan bakinsa kafin yace.

"Anna 'yar Babban gida ce itama, mahaifiyarsu d'aya da Babana, ta gamu da matsalar aljanu ne tun aurenta na farko, hakan yasa ta zama kamar bata da hankali sosai kowa yake gudunta, amma tana da nata hankalin don tana iya fahimtar wasu abubuwan."

"Wasu abubuwan kamar me?"

"Misali zata ci abinci kuma zata yi ibadar ta kamar kowa, kawai dai bata fiye tsabtace jikinta bane kuma tana saka shirme a maganganunta, amma bata da mantuwa, in har ta san abu, komai dad'ewarsa baya b'ace mata."

Adam ya gyad'a kansa yana jin kamar a lokacin ya tashi sama ya ganshi a Ikara kawai, kamar ya zuk'e duk tsawon tafiyar dake gabansu ya matseta cikin taku d'aya.

"Me ya faru? Me Malam Salisun yace maka?" Sa'id ya yanke shawarar tambayar bayanin da baiyi masa ba.

"Zan fad'a maka."

Ya fad'a cikin harshen turanci sanda yabi motar gabansu yasha wata kwana... Ya fad'i hakan ne kawai don ya rabu dashi, amma k'aidar bincikensa shi baya had'awa da kowa, baya gayawa kowa abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Har Sa'id ya bud'e baki zai sake magana wayarsa dake kan cinya ta shiga ruri, yayi saurin kallonta, Ya Allah! Ya akayi bai lura ba cewa sun shigo waje mai service ba, da sauri ya d'ago da ita cike da begen sautin kiran da yayi kewarsa tsawon kwanaki.. Bak'uwar namba ce da bai santa ba, ya d'an kalli Adam da idonsa ke kan titi kafin ya d'auka.

"Hello... Eh Sa'id ne... Eh muna tare dashi... Okay tohm."

Sai ya mik'owa Adam d'in wayar.

"Da kai ake son magana."

Kamar bai ji shi ba don da alama yayi nisa cikin tunani, sai kuma ya mik'o hannu ya karb'a sannan ya kara ta a kunnensa. Gaisuwa kawai Sa'id ya iya tsinta a cikin maganar da yayi kafin dogon bayanin da muryar ciki ke masa ya canza yanayin idanunsa zuwa wani abu da zai rantse ya kuma rantsewa bai tab'a gani tare da Adam ba, iya tsawon zamansa dashi.

Tashin hankali...

Tsantsar sa!

****

Basu sami airpot a Keffi ba, don haka dole suka k'arawa motarsu mai suka k'arasa cikin garin Abuja da kyar saboda yadda k'asan motar ya kwararrab'e da irin gurzar data sha cikin daji.

Zuwa wannan lokacin Sa'id ya fahimci me ake ciki don kiran waya ne barkatai ke ta shigowa wayarsa bi da bi na neman Adam, kasancewar shi wayarsa basu ma san inda take ba cikin tarkacen motar, kuma dukkanin kiran suna dangantuwa ne da labari d'aya, cewa bayan tafiyarsu kotu ta tura Fadeelah kurkuku wanda hakan ya faru da sa hannun lauya mai shigar da k'ara Kutama.

Sai dai abinda bai fahimta ba shine irin rud'anin dake haskawa cikin idon Adam, haushin abinda Kutaman yayi ne ko kuma me? Shi fa ya kasa gane wace irin alak'a ce tsakanin Adam da wannan case d'in, ko kuma yace Bintun ita kanta, don ba zai yiwu ace duk wannan wahalar da kashe kud'in da yake yi saboda Kawu Sulaiman bane kawai, har yaushe ya sanshi da zai ta sadaukar da kud'i da lokacinsa saboda shi haka? Yafi danganta cewa akwai wani abu tsakanin Adam d'in da Bintu.

Tunda ance ta zauna a America tare da marik'anta, zai iya yiwuwa ya santa ne tun a can, sai dai kuma kansa ya sake k'ullewa da tunanin in har su san juna me yasa daga shi har ita ba wanda yayi maganar hakan.

Ya juya ya hangi fuskar Adam d'in dake tsaye tare da wani dillalin sayar da motoci, inda suka tsaya zasu saida motar tasu bayan isarsu cikin garin Abujan, a yanzu ya fahimci cewar jinin mahaifinsa na hausawa ne kawai ke yawo a jikinsa, amma dabi'unsa kaf irin na al'adar turawan daya tashi a cikinsu ce, baya tab'a fad'in abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Bayan da kyar an samu wani makaniki ya sayi motar, suka tsaya anan gidansu na Abuja suka kintsa jikinsu kafin lokacin tashin da jirgin da Adam yayi musu booking, Sa'id yaso su huta zuwa washegari amma yaga babu niyyar hakan don haka ya rik'e ra'ayinsa. K'arfe hud'u da 'yan mintuna jirgi ya d'aga dasu daga filin tashinsa na Nnamdi Azikiwe International Airport zuwa filin saukar jirage na garin Zaria.

Sa'id ya riga ya yiwa Awwal waya kafin su taso don haka tun kafin saukarsu yana tsaye a harabar wajen rik'e da muk'ullin motar da suka bar masa anan gidansu na Zariyan.

****

".... Bayan tafiyarka da kwana biyu muka sami labari wai an d'auke ta daga nan cikin kotun zuwa wata kurkuku ta mata dake can hanyar barin gari, wallahi babu irin kokarin da ba muyi ba amma ma'aikatan kurkukun sun k'i saurararmu, sunce sai dai mu koma can kotun da aka kawo ta, daga nan ne za'a iya wani abu, kuma a can mun rasa wa zai saurare mu..."

Banda wad'annan kalaman na Kawu Ibrahim babu abinda ke maimaitawa a cikin kan Adam. Ya rufe idanunsa tsam! Ya k'ara jingina da kujerar cikin jirgin, ya kasa yarda wai Fadeelah na kurkuku a lokacin, ya kasa yarda cewa tafiyarsa ta jawo mata fad'awa mummunan halin da yafi wanda ya barta a ciki, yaya zuciyarsa ke ji ma sanda tana tsare a kotun balle yanzu kuma an gwamutsa ta cikin wata k'azamar rayuwa... kurkukun da ya sani a k'asashen da suka cigaba ma yaya suke balle kuma ta nan Nigeria?

Sannan ya kasa barin tunaninsa ya hasko yadda ta koma yanzu, musamman wad'annan idanun nata, sun d'ashe saboda wahalar rayuwar da bata saba ba? Sunyi zurfi? Sunyi fari? Ko kuwa dogwayen gashin jikinsu sun zube saboda rashin abinci mai inganci?

Ya rantse a cikin kansa ya kuma rantsewa in d'aya daga cikin wannan ya tabbata sai Kutama ya biya koda kuwa bayan shari'ar ne... Don ji yake kamar idanun nata a manne da zuciyarsa suke saboda tun daga ranar da k'addara ta had'a shi da ita, basu tab'a barinsa ba, tare dasu ya shiga duk wata gwagwarmaya ta rayuwarsa ya fito.

Fatansu Kawu Ibrahim da wannan mutumin marik'inta shine yanzu a dawowarsa yasa a fito da ita daga kurkukun a maida ta cikin kotun, amma shi ba wannan ne shirinsa ba, ya riga ya yiwa kansa alk'awari cewa daga jibi da zai kama ranar da za'a sake zaman shari'ar, k'afafun Fadeelah baza su sake takawa su koma wani k'azamin waje ba, zai k'are shari'ar a ranar ya kuma dank'a mata 'yancinta a tafin hannunta, 'yancin da zai wanke ta a idon duniya kuma 'yancin da zata zaga koina a cikin Ikara da kuma shi kansa Babban gidan ba tare da wani mai zarginta ba... Abinda ya rage masa kawai yanzu shine Allah ya tabbatar da wannan alkawarin daya d'auka.

A hanyarsu ta shiga cikin gari bayan sun sauka daga jirgin, ya kira Jabir, wannan k'aramin lauyan da kotu ta bashi a matsayin mataimaki, shi ya gaya musu sunan kurkukun da Fadeelah take da kuma kwatancenta, yana iya ganin mamaki k'arara a fuskar Sa'id lokacin da ya cewa Awwal ba gida zasu nufa ba sai yaje yaga Fadeelah tukunna.

Har saida Sa'id d'in ya tambaya, Ba sai gobe ba? ya girgiza kansa kawai, ta yaya zai iya wani bacci bai je ya ganta ba? Ta yaya zai iya runtsawa baije yaga wad'annan idanun ba...

Awwal cike da d'okin tuk'i kuwa yayi ta bin kwatancen map d'in da Jabir ya turo masa ta wayar Sa'id, don shi in za'a d'ora masa bindiga a lokacin ba zaice ga inda tasa take ba sai dai a shigar da harsashin kawai.

Zuciyarsa tayi girma kamar gingimemen gate d'in da suka tarar a k'ofar kurkukun, aka bud'e musu suka shiga bayan ya nuna I.D Card d'insa. Bayan sunyi parking kuma wani daga cikin masu gadi ya shigar dasu har wajen receiptionist inda suka tarar da wata d'irkekiyar mace zaune akan desk d'in wajen fuskarta babu ko d'igo na alamun rahma. Zuciyar Adam ta sake matsewa da tunanin har kwana nawa Fadeelah tayi tana rayuwa da irin wad'annan mutanen.

Matar ta d'auki wani kan wayar intercom bayan ya gama yi mata bayanin WAYE SHI da kuma abinda ke tafe dashi.

"Receiptioninst area. Akai Bintu Abubakar waiting room, lauyanta yazo ganinta."

Tana fad'in haka ta ajiye kan wayar sannan ta mik'a masa I.d Card d'insa da ta duba, daga nan ta umarci wata Matron a gefenta da ta kaishi shi kad'ai can waiting room d'in, su Sa'id kuma su jira shi anan.

Lauyanta. Adam ya maimaita kalmar a zuciyarsa sanda matron d'in ta jashi zuwa wata k'ofar, yaya Fadeelah zata ji in akace mata lauyanta ne yazo ganinta?

**

"Lauyanki ne yazo ganinki."

Wata Matron ta fad'a tsaye akan Fadeelah, a lokacin k'arfe shida da 'yan mintuna ne na yamma, tana zaune a harabar masallaci an idar da sallar magriba, tafin hannunta da yayi sab'a da kuma alamun kanta take bi tana d'ayewa a hankali yayin da Kenken wacce sai bayan an idar da sallar tazo ke zaune

Please Login or Register in order to submit comment