Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gefe ya zauna."

"Ina tambayarki duk wannan abun ne saboda yanzu aka fara shari'ar, kuma kowa ya ganki zai san cewar kin canja mutuk'a daga yadda kika zo wajen nan tun ba'ayi zama na biyu ba, ni lauyan ki ne dole ne in damu ..."

Kamar wani ya katse shi ya tsaya bai k'arasa ba, saida ya saita kalamansa dake shirin zamewa sannan ya cigaba.

"Wannan cizon da sauro ya miki ko baki yi zazzab'i yanzu ba zaki iya gobe ko jibi, ba zan iya kawo likita nan ba amma zan iya samo miki magani ko hanyar da zaki ji saukin abubuwa, na gaya miki in kika fara rashin lafiya zai shafi dukkaninmu."

Ba wai ta yarda da zancen bane yasa tayi niyyar bashi amsa, kawai ta k'agara ya tafi ne don bata son abinda take ji a yau game dashi, maganganunsa wani a hankali kamar sai sunyi tracing kan fatar ta ne kafin su shiga kwakwalwarta, sannan ga inda ya rik'e hannunta har yanzu tana ji kamar k'ankara aka d'ora a wajen.... Saboda hakan ta bud'e baki ta gaya masa duk wasu abubuwan da take fama dasu a wajen, abubuwan da bata taba gayawa waninsa ba, sai hirar tasu ta zama kamar ta tsakanin likita da mara lafiyarsa kwata-kwata bai sako mata zancen da ya shafi shari'ar ba itama bata tambayi komai har kuwa ya tafi, don zuciyarta na cike da d'acin yadda har yanzu baya nuna wata alama ta ya san hallitarta a America.

Ba'afi awa d'aya da tafiyarsa ba, Musa mai tsaronta ya kawo mata wata madaidaiciyar leda mai d'auke da tarkacen magaunguna da kuma da kuma kayan ci ma irin na leda, sannan harda wani lotion da in mutum ya shafa sauro baya iya hawa jikinsa, bayansu sai manyan robobi na ruwa. Allah kad'ai ya san irin hanyar da yabi kafin a bar kayan nan ya iso gareta, don su Mami ba irin kokarin da basu yi ba amma aka hana su shigo mata da ko ruwa.

Akwai 'yar jotter a cikin ledar daya rubuta mata yadda zata sha magungunan, idonta ya tsirawa rubutun ido... Ta kara yarda cewa tabbas wannan Adam d'in data sani a America ne don ga rubutunsa nan kamar yadda ta haddace sh a lokacin tutorial d'insu, mamaki ya sake d'aure tunaninta game dashi, ta kasa gane dalilin da yasa yake b'oye mata kansa, kamar yadda ta kasa gane yadda akayi yazo Nigeria har cikin 'yanuwanta.

***

"Haba Hajiya, nan fa ba gidan dubiya bane, d'azu wasu suka zo suka matsa sai da suka ganta yanzu kuma kinzo? Ba fa a ma barin ziyara da yawa a kotun nan amma ku tun yaushe muke d'aga muku k'afa? Daga wannan yazo sai wani yazo, ko an gaya muku ku kad'ai ne masu 'yar uwa a koton ne?"

Wani mutumi dake zaune a teburinsa ya fad'a cikin masifa sanda Mairo da Kawu Ibrahim ke tsaye a gabansa suna rok'on abinda Mairo ke ganin a yanzu rayuwarta ta ta'allak'a akai.

Ashe har wasu sun rigata ganin Mairo a yau? Saboda su kuma ake shirin hana ta ganinsu yanzu... A cikin zuciyarta ta tsinewa lokacin data b'ata a wajen su Kawu D'anjuma da bai amfane ta da komai a yau ba, Kawu Ibrahim daya samu labarin zuwanta ne da kuma abinda ya faru a jiyan ya had'a taro na gaggawa bisa alfarmar daya nema a wajen Kawu D'anjuma.

Taron ya had'a harda wad'anda ba'a kira ba sai suka zo don jin abinda za'a tattauna, inda ba komai akayi ba sai rok'o da Kawu ibrahim d'in yayi tayi akan a taimaka a yafe mata laifin da tayi tunda har tayi hankalin dawowa cikinsu a yanzu, amma sai da aka kai ruwa rana sannan Kawu d'anjuma yasa baki a gajarce cewa shikenan taje sun yafe mata, bayan kuma ta gaya musu cewa tana da miji har da 'ya'ya biyu, sai komai ya nemi dawowa sabo...

Da yawansu suka saka baki kan cewar laifinta na raini ne da son zuciya, tunda har ta iya haihuwa biyu kafin ta neme su, su kace kar ta sake ko da wasa ta kawo 'ya'yan cikinsu balle kuma shi mijin data fifita akansu, ba irin kuka da magiyar da ba tayi musu ba cewa itama bada son ranta tayi hakan ba, amma haka aka tashi Kawu Ibrahim baici nasarar tara sun da yayi ba.

Daga nan ya kaita b'angarensa, inda matarsa Aunty Hassana ta karb'eta da mutunci, ta bata ruwa tayi wanka, sannan ta d'auko sababbin kaya a cikin nata ta bata ta sanya, ta fita daga cikin suturar data danganci Sadiq da dukiyarsa. Bayan taci abinci kuma tasa aka samo mata magani saboda zazzab'in yayen Muhammad daya fara kamata, amma duk wannan abun da ake yi zuciyarta hanqoro kawai take na son ganin 'yaruwarta.

Yayin da duk wannan abinda ake yi kuma, Sadiq na daga can gefen layin cikin motarsa yana samun bayanin abinda ke faruwa daga wajensu Saminu, don da gaske Maryam take ta yanke alak'arsa da ita, bata k'ara nemansa ba kuma bata k'ara bari ya ganta ba, gashi ba ko waya a hannunta tunda daga asibiti ta taso, ga magungunanta ma suna zube a motarsa bata ko sake waiwayarsu ba.

A safiyar ranar ne k'annwn mahaifiyarsa biyu, su Umar suka zo kamar yadda tayi alkawarin turo su, kuma bayan bayaninsa mai cike da kwana-kwana ya lallab'a su suka koma ba tare da sunga 'yanuwan Mairo ba kamar yadda ya turo su da k'udirin hakan.

Kuma da yake har yanzu Nairar jikinsa na sawa ya fad'a aji sai suka yarda ya sama musu jirgin yawon da ya tashi k'arfe d'aya na rana suka koma harda Zakkiya da Muhamnad. A yanzu yana jiran kiran mahaifiyarsa ne da kuma duk wani hukunci da zai fito daga Maryam.

"Yallab'ai don girman Allah, wannan 'yaruwarta ce shekara da shekaru basu had'u ba, bama ni saina shiga ba ka taimaka ta ganta ko na minti goma ne."

Cewar Kawu Ibrahim, mutumin ya girgiza kai baya ko kallinsu.

"Naga gobe zaku shiga kotu, meya na saurin? Ta ganta a can kawai."

Kafin Kawu Ibrahim ya sake cewa wani abun k'ofar ofishin ta bud'e, wani mai tsaro ya shigo.

"Ranka ya dad'e kira ne daga waje."

"Ahh haba dai! To gani nan."

Ya rufe file d'in gabansa da sauri kawai sannan ya fita daga office d'in ya barsu."

"Kawu dan Allah mu zauna ya dawo, mu k'ara rokonsa ko zai yarda." Cewar Mairo bayan fitar tasa.

Sanin irin yadda ta damu ne yasa Kawu Ibrahim ya amsa mata suka cigaba da zaman jira a office d'in amma ya riga ya fahimci cewa bashi da niyya.

Kusan minti biyar sai gashi ya dawo.

"Yawwa nace ku ai baku yi bayanin cewa 'yanuwa ne na kusa ba, ni tunanin da nake irin daga nesa kuke ne shi yasa, amma ba komai zaku iya shiga ku ganta yanzu, sai dai ku hanzarta don naga yamma tayi, kuje za'a fito muku da ita."

Ba Kawu Ibrahim ba, hatta Mairo dake cikin zumud'i sai da tabi mutumin nan da kallon mamakin yadda ya canja a lokaci d'aya. Sai dai ita bata yi tunanin komai ba saboda hankalinta ya tafi gabad'aya ga son ganin Bintun, amma a tunanin kawu Ibrahim zato yayi Adam ne ya bada umarnin a barsu su ganta.

Sadiq na tsaye daga cikin office d'in wani Babban ma'aikaci a wajen ya sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da ya hange su sun nufi d'akin da ake ganawa da d'aurarrun.

***

Da ace akwai inda murna zata iya yin masauki a zuciyarta, da babu abinda zai hana Fadeelah jin hakan lokacin da aka shaida mata cewa ta sake samun mai zuwa ganinta har sau biyu a rana guda.

Watakila ba'afi awanni biyu da shan maganin da Adam ya kawo mata ba, amma har taji sauk'in yanayin jikinta da kuma taimakon kayan cimar ledar nan sannan ta d'add'aki ruwan ma kamar ba gobe, don ji tayi kamar ta shekara rabonta da ruwa mai tsafta irinsa.

K'afarta bi da bi take bin bayan mai tsaron nan Musa, har zuwa wajen da a yanzu shi kad'ai ne silar samun sassaucinta, tunda a nan ne kad'ai inda zata had'u da mutanen da basa ganinta da wannan laifin.

Kawu Ibrahim idonta ya fara gane mata, sannan kuma ta tsaya cak sakamakon fuskar Mairo data ci karo da ita a gefe, Mairo dai da ta gani a Abuja, Mairo 'yaruwarta tsaye tana kallon hanyar k'ofar data shigo ta ciki idanunta a zare kamar zasu zazzago daga mazauninsu su fadi k'asa.

A lokaci d'aya taji iskar da bata san wace iri bace ta zarce cikin makogwaronta sannan d'an mitsitsin sauk'in data samu game da kulawar Adam ya murmushe yabi iska, ta sake kallon Kawu Ibrahim sosai, sannan Mairon da bata jira komai ba ta fara kokarin tahowa gare ta da sauri, sai kawai ta juya da sauri itama ta fita daga wajen, ta koma hanyar da suka biyo.

Kawu Ibrahim ya sani, ta gaya masa cewa bata son ganin Mairo bata buk'atar sake ganinta a rayuwarta, amma shine ya kawo ta har nan... Tiryan-tiryan tabi hanyar data haddace ta har cikin cell d'in da yake nata a yanzu, ba tare da wani mai tsaro ba ta shiga da kanta kuma ta janyo k'ofar ta had'e ta, yadda take ji a cikin ranta duhun wannan cell d'in ya fiye mata ganin Mairo da dukkan kasancewarta a duniya.

Ta san cewa tunaninta yafi karkata ga cewar ita Fadeelah ce a yanzu, amma tunda har tunaninta na farko a matsayin Bintu yana tare da ita, zata karbi kowanne hannu biyu ta bashi hakkinsa...

"...duk sanda Mairo ta dawo gareku kuce na yafe mata Malam, wallahi na yafe mata.

Muryar Innarta a ranar da zata mutu ta haska cikin kanta sanda ta nemi can k'arshen cell d'inta zauna, Inna Saratu ce taje ta tashe ta a safiyar ranar akan cewa tazo Inna Aminar na nemanta, kuma bayan tabi bayanta har zuwa d'akin da take ciki, ta tsinci k'arashen wannan zancen nata tana gayawa Baba dake zaune a gefe rik'e da hannunta.

A lokacin k'afafunta rik'ewa suka yi ta kasa karasawa cikin d'akin, bata kai yanzu wayo ba amma tun a sannan tayi zaton cewa irin bak'in ciki da wahalar da Mairo ta jaza musu ba wanda zai iya ko d'aga ido ya kalleta duk ranar da ta waiwaye su balle har ayi zancen 'yafiya'.

Taso a yanzu zata iya haskawa Mairo wannan lokacin da Innarsu ke kan gab'ar mutuwa amma tana fad'in cewa ta yafe mata duk da cewa kuwa itace silar ciwon nata, taso zata iya nuno mata taga irin soyayyar da ta gujewa ta tafi neman wadda bata k'unshi komai ba sai sha'awar duniya, taso zata iya nuna mata irin bak'in ciki da kuma azabar da dukkaninsa suka jure a dalilin son zuciyarta... Taso zata iya nuna mata yadda ta rasa uwa, Baba ya rasa mata, inna Saratu ta rasa 'yaruwa duk a gaban idonsu saboda ita kad'ai kawai.

Ta rufe idonta a hankali sanda ta jingina da bangon, ta dad'e da d'aukarwa ranta alkawarin cewa ba zata tab'a yafewa Mairo ba koda kuwa duniya zata nad'e da ita a cikin k'asa.

Jinginen ba dadi saboda haka ta lalubi dandaryar simintin nan ta d'ora fuskarta sanda tunaninta ya dawo mata lokacin da Baba ke biya kalmar shahada cikin kunnen Innar da kowacce gab'a ta jikinta ke girgizawa mintuna kad'an bayan shigarta d'akin.

A lokacin hawayen dake fita daga idanunta sun k'afe, tana rik'e da hannunta mai d'umi da ita Innar da kanta ta miko mata ta kama, Baba ya cigaba da furta kalmomin shahadar cikin kunnenta kafin ta iya karb'a da wata irin murya mai k'arfi data cika d'akin.

"Lailah ha ilallah, muhmad rasu..."

Shiru ne ya biyo baya bata k'arasa ba, sannan a lokaci d'aya kuma hannun da ke cikin nata yayi sanyi kalau, idanunta suka bi sama da kallo sannan numfashinta ya yanke, ya yanke tare da duk wani ragowar tunaninta a lokacin.

Tana iya tuna yadda shirun d'akin ya fallasa k'arfin kukan Inna Saratu yayin da Baba yayi k'ame kawai rike da hannun gawar kamar yadda itama take.

A duniyar nan kaf! Gwaggo lami da ta shigo d'akin daga baya, itace ta fara furta rasuwar Inna Amina.

****

Gwaggo lami ita ta fara zuwa a matsayin shaidar Kutama ranar da akayi zama na biyu, tazo ta fad'i duk wasu k'arairayin da babu ko d'igon gaskiya a ciki, amma ta rantse ta kuma kalli Alkali ta tabbatar da gaskiyar ta fad'a.

Fadeelah ta san Adam bai so yi mata tambayoyi ba amma irin maganganun data fad'a yasa shi ya mik'e, amma da yake ita d'in tsohuwar makira ce ta bashi dukkan amsoshin da suka tafi daidai da k'aryar data fad'a. Bayan ita Kutama ya kira 'yan sandan da suka je neman Bintu har garin Kano a lokacin da akace motarsu tayi hatsari, ya kira likitocin da suka tabbatar da irin gubar da aka sanya a kokon, ya kira wad'anda suka tantance shaidar hannun Bintu da ya fito a jug d'in data kai mata kokon, hatta mai markaden geron da akayi sai da ya kira kuma Alkali ya gamsu bayanansa da yawa ta yadda a cikin wata guda kawai ko makaho zai shaida inda shari'ar ta dosa.

'Yan Babban gida suka sami abinda suke so, farin ciki ya rufar musu ganin cewa suke da nasara a kowanne zama da akayi, hankalin Kawu Ibrahim ya tashi ya zama kusan kullum yana zarya tsakanin Ikara da Zaria wajen Adam, Mami ma ta k'ara rud'ewa gani take a kowanne lokaci za'a iya yankewa Fadeelah hukunci akan shari'ar nan, ita kanta Fadeelah duk sanda aka shiga zaman kotun ta kalli fuskar 'yan Babban gida taga yadda kowannensu ke murmushin jin dad'i sai zuciyarta ta sare, don hatta Habiba yanzu ta fara goge tashin hankalin kan fuskarta ganin yadda shari'ar tafi karkata gare ta a kullum.

Sai itama ta fara tunanin cewa sa'a na hannun kowa, rayuwarta tare dasu Mami zai iya kasancewa shine lokacin hutunta kawai a duniya, komai zai iya k'arewa a wannan gab'ar a yanke mata hukuncin da zai kawo k'arshen rayuwar tata.

Akwai zaman da akayi wanda Kutama ya dinga kawo hujjoji harda hotunan gawar Hajiyan ga Alkalin, hankalin mutane ya nutsu aka dinga ganin kamar a ranar za'a kawo karshen shari'ar saboda yadda komai ke fitowa fili... Amma Alkalin ya juya zaton kowa da sake d'aga k'arar zuwa wani lokacin, da alama yayi amfani da rok'on Adam na tun farko cewar kar kotu ta yanke hukunci cikin gaggawa.

Sai dai duk wannan abin da akeyi, hankalin Adam a kwance yake tsaf don shi kad'ai ke iya k'arfafawa Kawu Ibrahim gwiwar cewar ya kwantar da hankalinsa shima, Kutama yana barazana ne kawai da abinda bai sani ba.

Aunty Hadiza, Fatima dama kuma Abdullahi duk sun koma a lokacin, don haka Daddy da a dole ya nemi hutu a asibitinsa shi kad'ai ke kwantar da hankalin Mami data kafa ta tsare cewar ba zata koma Abuja ba sai an gama shari'ar nan, tana zaune a garin har lokacin kuwa da aka d'age shari'ar da hutun sati biyu, su Zahra ma sunzo amma har suka tafi basu samu ganin Fadeelah ba don an dad'a saka tsaro sosai akan ganin nata.

Abinda ya dad'a d'aid'ata rayuwar Mairo kenan wadda har a lokacin take wajen Kawu Ibrahim, kullum tana gidan bata taba fita sai ranar da za'ayi zaman kotu, ta toshe kunnenta kuma ta hakura da duk wani zagi da maganganun da ake fad'a mata a Babban gida, ta karb'i rayuwar a yadda tazo mata hannu biyu ta manta da Sadiq da wasu 'yanuwansa, 'ya'yanta ne kawai kan fad'o ranta lokaci zuwa lokaci tana jin kewarsu, amma duk da haka a ranar da Sadiq ya shafawa idonsa toka ya d'ebo 'yanuwansa har cikin Babban gida da sunan biko, bata ko kalli 'ya'yan ba balle shi.

Kawu Ibrahim kawai suka samu ya saurare su a duk fad'in gidan, kuma shima bai basu wani fata ba don yace sai abinda ita ta yankewa kanta tukunna, saboda laifin Sadiq ya riga ya fito k'arara su kansu 'yanuwan nasa a yanzu sun san ya aure ta ne bisa rashin sanin iyayenta, amma da yake da kud'insa a k'ugu sai hakan ya zama kamar ba laifi ba kowannensu ya rik'a sunkuyar da kai wajen nemar masa bikon.

Tawagar biko na biyu daya kawo ta mata ce, wadda hakan ya had'a har da yayar mahaifiyarsa, suka zo da dad'in bakinsu, don har magiya sun had'ata da ita suna gaya mata halin da 'ya'yanta ke ciki amma daga k'arshe tashi tayi kawai ta k'ulle kanta a band'aki har suka gaji suka tafi. Ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa sai ta tarwatsa rayuwar Sadiq kamar yadda ya tarwatsa tata itama.

Sai ta hargitsa shi ta raba shi da duk wani sukunin rayuwa, sai dai hakan zai zo ne a gaba don yanzu ba ta shi take yi ba ko kad'an, ta 'yar'uwarta take. Duk da har yanzu basu yi wani had'uwar kirki da ita ba amma hankalinta a tashe yake kamar kowa, kowa d'in da bai had'a da jama'ar Babban gida ba, wad'anda a gaban idonta suke kafa hira ana rahar yadda shari'ar ke kai musu, don hatta labari ya fara yawo a cikin gari cewa an kusa yankewa Bintu hukuncin kisa itama, saboda a wannan d'an tsukin Kutama ya firfito da hujjojin da ko alk'alin ya fara gamsuwa dashi.

Yadda hankalin kowa ya tashi haka ma na Fadeelah ya fara rawa ganin yadda komai ya karkata d'aya bangaren, hakan yasa ta ture komai ta tambayi Adam d'in a wata rana da yaje ganinta.

Saboda kamar k'aida ya mayar da zuwa dubata cikin kowanne sati, har ya zama itama ta kan k'irga kwanakin da zasu kai ga zuwan nasa saboda ta sami kayan amfani... Zaman cikin kurkukun bai canja daga komai ba, amma rayuwarta a cikinsa ta canja dalilin kulawar da take samu daga Adam, bata da matsalar abin ci a yanzu ko ko na abin sha, sannan bata ko ciwon kai balle zazzabin saurayen da basa damunta a yanzu, magungunan komai tana dasu hatta vitamin C wannan, Adam ya canja mata komai ya kuma sauk'ak'a mata zaman wajen, hakan ya k'ara masa matsayi sosai a idanun su Mami har ma da Kawu Ibrahim a duk ganin da zasu yi mata ranar zaman kotun, amma ita a ranta ta yarda cewa yana kyautata mata ne kawai don amfanin kansa, saboda yayi ya rabu da shari'arta kamar yadda ya fad'a.

"Kin manta me na fad'a miki?" Lallausar muryarsa ta tambaya maimakon ya bata amsar abinda ta tambaye shi d'in.

Yana zaune daga kujerar tsallaken teburin data raba su, hannunsa rik'e da wata 'yar karamar jotter da yake d'iban bayanin wani abu da ya tambayeta game da Hajiya mai rasuwa. Tun zamansa a wajen sau d'aya ta kalle shi, a yanzu wani irin kwantaccen saje ya fito a kowanne gefe na fuskarsa, hakan ya fallasa mata cewar yawan aiki ya rage masa lokacin kula da kansa, hasken d'akin kuma ya k'ara fito da bak'in wannan gashin nasa da yake a taje kullum, a lokacin taji kamar ta tasho taje tasa hannu ta barbarza shi ya koma kamar yadda yake lokacin had'uwarta dashi, sannan ta d'auko mudubi ta haska masa kansa a ciki, watakila hakan zai sa ya bud'i baki ya gaya mata cewa shine dai Adam d'in da ta sani a da.

"Tun kafin a fara komai na gaya miki cewa mutanen nan sun tara isasshiyar shaida a hannunsu, so bai kamata kema ki biyewa mutane a tunaninsu ba, wannan duk barazana ce kawai lauyansu yake yi akan abinda suka bashi, na kusa gyara masa tunaninsa."

Ya fad'i hakan ne a hankali yana lumshe idanunsa, wani irin bacci ne a idonsa tun lokacin da muryarta ta fara yi masa bayanin daya tambayeta, gajiyar da yake ciki ta salallab'o ta rufe shi don ya manta yaushe rabonsa da bacci a cikin kwana biyun nan da shari'ar ke shirin dawowa hannunsa, tsabar yawan aikin da yake yi da kuma had'e- had'en bincikensa yasa ya ture bacci daga cikin priority list d'insa.. Ya riga ya zama addicted da yawan aikin dake gabansa shi yasa rashin baccin ma baya damunsa.

Fadeelah ta cukwuikuye ledar kayayyakin da ya kawo mata, sannan tace.

"Kana tunanin za'a k'ara wata guda ana cigaba da shari'ar?"

Ya sake lumshe idonsa.

"Komai yana hannun Allah, amma a yanzu da shariar zata dawo hannuna... Ba zan ja da nisa ba, zan fito da komai a d'an k'ank'anin lokaci insha Allah."

"Me kake nufi da shari'ar zata dawo hannuka?"

"Lauyansu ya gama fito da duk shaidunsa, yanzu turn d'inmu ne, mu zamu yi leading shari'ar."

Yadda ya furta kalmar 'Mu' d'in ta fito kamar lokacin da suke tutorial d'in nan ne, sannan ya bada ma'ana kamar ita dashi sun zama team a yanzu. Ta rasa tunanin cewa Adam ne zaiyi leading shari'ar ya sata jin sassauci a zuciyarta ko kuma yadda ya had'e shi da ita cikin jimla guda ne.

Tunaninta ya shiga lalube kan wane irin shaidu zai gabatar amma muryarsa ta katse ta... Muryarsa da ta saba da ita a yanzu.

"Mu cigaba?" Ya tambaya.

Sai ta sake cukwuikuye hannun ledar sannan ta cigaba da abinda take gaya masa kafin tayi tambayar data katse su.

"Bayan haka, akwai ranar da Inna Saratu ta aike ni Babban gida in kaiwa Hajiya goro, bani da wani wayo a lokacin sosai amma ban so zuwa ba, saboda ko tare da ita muka je a gaban idonta ma masu zagina da habaici Allah yayi yawa dasu.

Mutum na farko dana fara gani kafin in kai b'angaren Hajia Aunty Sadiya ce, ta fito da tulin wankinta tana yi tana biyo wasu wak'okin hausa, tana ganina tace inzo in tayata wai ba don kar na mata jagwalgwalo bama da ta bar min gabad'aya..."

Adam saurarenta kawai yake yi amma baya fahimtar ma'anar abinda take cewa, jin muryarta yake kamar sarewar dake busawa a hankali tana kwad'aita masa baccin da yayi kewarsa tsawon kwanaki biyu.

"...Sai muka fi kusan awa guda muna yi kafin ta saka ni in shanya mata, daga nan na hadu da Aunty Saratu matar Kawu Nura kafin k'arasa wajen Hajiyar, ta aike ni can Kasuwar rana in siyo mata kayan abinci, tafiya mai nisa ce tsakanin nan da kasuwar ga rana, ga k'ank'ata ta, amma bata duba komai ba ta tura ni, na tafi na b'ata don ban gane hanyar dawowa ba sai kusan yamma, hankalin Aunty saratu ya tashi akayi ta nema na.

Masu neman nawa sun tafi ni kuma na dawo na shiga na kai mata, kuma ko a jikinta tace in ajiye nan k'ofar d'akinta. Daga nan nayi wajen Hajiya, ina ta sauri inje in kai mata goron dake k'ulle a jikina kafin wani ya sake ganina, hakan yasa naci karo da Yaya Sule a zauren shiga wajen nata, ya danno wani zagi sanda ya damk'o wuyana ya d'aga ni har sama..."

Jin yadda take ta bayani ba tare da yace komai kamar da farko ba yasa ta d'ago da kanta ta kalle shi, mamaki ya dirar mata a lokaci d'aya sannan ta zare ido tana kallonsa...

Ya jingina kansa baya kad'an da kujerar da yake zaune, ya karkata fuskarsa, ya rufe idonsa, dogwayen gashin idon sun bi sun kwanta luff akan junansu sannan numfashinsa na fita a hankali...

Bacci yake yi!

****


BAYAN NA MUTU!

©AYSHA SHAFI'EE

*33*

*(☆_☆)*

Bata san a wane irin yanayi motar ke tafiya ba don babu taga ko guda d'aya da zata nuna mata hakan, saboda haka ne ma bata san wace irin rayuwa ce ke gudana a waje ba, wannan wajen da a kodayaushe ke haskawa cikin mafarkinta.

Ta juya b'angaren hagu ta kalli sauran fasinjojin dake tare da ita, kamar yadda idanunta suka shaida mata ne tun farkon shigowarta.. Babu ko mai kamar Habiba a cikinsu balle ita kanta, ta gefenta wata Babbar mace ce mai d'aurarriyar fuska, akwai wasu mata biyu da fuskar su ke nuna tsoro da kuma tashin hankali kamar kusan duk sauran dake cikin motar.

Daga can jikin k'ofar motar idonta ya kai kan wata k'aramar yarinya bak'a mai manyan ido tana ta share hawayen dake zarya a fuskarta, a k'iyasinta baza tace yarinyar nan ta wuce shekaru sha uku ba amma ta san dole ne ta gota hakan tunda har mummunar k'addara ta jefo ta cikin wannan yanayin da take kan hanyar zuwa wajen da za'a tsareta kamar dabba.

Ko kad'an bata damu da sanin abinda ya kawo yarinyar ba balle sauran, saboda ta yarda kamar yadda k'addara ta jefo ta nan haka ma

Please Login or Register in order to submit comment