Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku gaisa yarinyar da Nafisa ta samo min dan debe kewa, sai dai kuma marainiya ce..shigowar Bintu ne ya katse mata zancen, sallama Bintu tayi cikin sassan yar muryarta me tsananin daɗin sauraro,A lokaci ɗaya kuma tana tsugunawa A gaban inno tare da rissinawa ta gaida Ammi,Ammi ta zubawa Bintu ido, kana cikin sanyin murya itama ta amsa gaisuwar, ta dubi inno tace masha Allah inno yarinyar ko kyakkyawa, ko itace'Rahima ta dameni da zancen ta?inno ta washe haƙora cikin jin daɗi tace" itace ai naga jininsu ya haɗu da Rahima tana sonta! Ammi tace"kinsan Rahima da son Abu mai kyau!'ta kare maganar da mikewa tsaye,tace" inno ni bari na wuce zan shiga wajen Hajjah!'to madalla Allah ya ƙara sauƙi!'ahankali Bintu tace"ki gaida gida Allah ya ƙaro sauƙi!'cikin ƙure bintun da kallo ta amsa ta da Amin na gode!'tare da barin falon gaba daya,


Tafe take zuciyarta cike da da tarin tunaninnika, bata ga komai A game da yarinyar ba,haka nan kallon da tayi mata ta gano babu komai cikin idanunta sai tsananin kunya da gaskiya,tanajin wani ɓangare na zuciyar ta nasan amincewa da Bintu, to amma kuma me yasa takejin wani irin tsoro A kan yariyar? tanaji kamar da wata maƙarƙashiya A kan zuwan yarinyar duk da bata da wani zargi A kan Nafisa sai dai can ƙarƙashin zuciyarta tanajin wani Abu daban, amma dai komeye zan sakawa yarinyar ido,dan kaf gidan nan ba abin yadda bane dole ne na gano komeye Ake shiryawa.


Yau ne ya kama, kamun Amare wanda yayi daidai da kwanan Bintu biyu A estate, ƴan matan Amare sai shirye-shirye suke, wasun su da yawa suna sashen inno,yayin da Bintu sai shiga da fita take, itace wancan itace wannan ko Abincin daren Abdallah sun hanata ta ɗaura, gashi yau A time table ɗin sa sakwara zata yi masa da miyar egusi,

karma hauwa'u da amna suji labari, sun takurawa Bintu, kuma bakomai ne yake ɗawainiya dasu ba face kishi da hassada, duk da suma ba munana bane amma suna jin suna raina kansu A duk lokacin da bintu ta kasance A waje, shiyasa suka ɗauki karan tsana suka ɗora mata, hakan baƙamin faranta wa Anty nafisa rai yake ba,duk da har yanzu basu kuma haɗuwa ba tunda ta kawota.


Saida duk ta sallamesu kana ta fara aikinta shima saida Inno ta fito ta tsawatar musu,cikin sauri take sarrafa duk abinda.yazo hannunta,duk da cewa basu taba haɗuwa ba har yau, amma tana ƙoƙarin kiyaye duk wasu ƙa'idojinsa da Aka lissafo mata,kai wannan mutum da shegen fi'ili yake komai bayaso,A haka ta gama aikinta lokacin babu kowa duk sun tafi wajen da Ake kamu shima A cikin estate ɗin yake,sai da ta gama jera masa komai kana cikin sauri ta nufi ƙofa dan fita, sam bataso su haɗu da wannan murɗaɗɗen mutumin, gashi yau har ta shiga lokacin dawowarsa shiyasa take sauri ta fice kar ya tarar da ita.


Tana buɗe kofar tayi wani irin gware da wani irin faffaɗan ƙirji, duk da ita bata gama tan-tance da abinda tayi karon ba, runtse manyan idanunsa yayi dan haƙiƙa yaji zafi har cikin ƙahon zuciyarsa,

Buɗe Manyan idanunsa yayi, A daidai lokacin ita kuma Bintu ta gama murza goshinta, ta ɗago dan ganin mugun da yai mata wannan aika-aikar, zaro manyan fararen idanun ta tayi tare da dagewa iya ƙarfinta ta kurma wani uban ihu, tare da komawa cikin falon da gudu tana neman gurin ɓuya,kira take wayyo inno yau nayi gamo, wa innahu sulaimanu, fafina yau nayi gamo, kuka takeyi sosai tamkar zata fitar da numfashinta,

Mamaki haushi ta kaici duk sune suka cushe zuciyar Abdallah,yana nan tsaye ya kasa ko da motsawa, balle sanin abinda zaiyi, ga ƙararta da duk ta cika masa kunne har ya rasa me ya kamata yayi, kaji yarinya da rashin hankali, amma shi bai ce mata Aljana ba sai shi zata cewa Aljani,tsuka yayi kana yaja ƙafafuwan sa ya ƙarasa shiga cikin falon,ɗago idanunta tayi da suka fito waje kamar na preter, cak ya tsaya yana kallonta dan shi dai ba ma'abocin kallo bane amma sosai yaga kamar su da preter har zaro idon da yanayin tsoronsu amma azahirance bintu tafi preter kyau,hannu yasa ya finciko ta ransa A matuƙar ɓace, ya daɗe bai ji ɓacin rai makaman cin na yau ba,idanunta, ta kuma zarowa kamar zasu faɗo ƙasa saboda firgita da tsoro,ji tayi kawai yaja ta har bakin ƙofa ya turata waje,ya maida ƙofar da matuƙar ƙarfi ya rufe,

Tsuru tayi A bakin ƙofar zuciyarta cike da fargaba,yanzu hankalin ta ya riga ya dawo jikinta,sai yanzu ta fahimci waye, A fili tace kai waini wace irin matsoraciyace? mutum da falonsa amma na kirashi da Aljani?cikin irin muryarta da ta saba yiwa fafi tace me yasa nake hakane? gashi najawo zai karya min hannu,to koma kurma ne ? kai inno dama tace sai ya kwana biyu baiyi magana ba, to kuma bakinshi baya yin komai? hannunta ta kalla taga har yayi ja ga shi sai raɗaɗi yake mata,kallon ƙofar tayi tana zabga mata harara tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta, tace kuma ban yafe ba mugu!'ta arta A guje kamar wadda zai kama.



Yana shiga bathroom ya sakarwa kansa shaya,yanayi yana sakin tsaki, kai wannan yarinya A kwai bagidajiya kawai tazo ta ƙaran ciwon kai,
sai da yagama shirinsa tsaf, kana ya fito falon, wajen cin abincin ya nufa kai tsaye dan shi Abdallah yana cin binci sam baya wasa da cikinsa, shiyasa ma yasa a samo masa mai girkin, gashi kuma bai iya bin gidajen abinci ba saboda tsantsani, zama yayi ya zuba sakwarar yaci sosai dan sosai ɗanɗanon abincin yayi masa ɗari bisa ɗari, har ya shiga mamakin wannan ƴar yarinyar ce ta iya sarrafa abinci haka ga nau'in lemuka masu inganci da'A cikin kwana biyun suka kama zuciyar sa, A hankali ya miƙe ya koma cikin falon tare da zama cikin kushin, hannu ya miƙa ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinsa, wadda take ta buruntun neman agaji, cikin hakimtacciyar muryar shi yayi sallama bayan ya dannata A amsa kuwa, muryar Dady ce ta ratso ta cikin wayar, bayan ya amsa sallamar tare da gaisuwar da Abdallah yayi masa,yace" Abdallah ina fata ko mai lafiya, batare da ya jira amsarsa ba ya cigaba da cewa anya kuwa Abdallah kanayin wani ƙoƙari kuwa dan najika shiru babu wani motsi,ina tsoron kar mutanen nan su sham mace mu,dan na lura A kwai mutanen da suke bin diddigina, amma bansan ko suwaye ba ban san kuma daga ina suke ba amma ga dukkanin alamu mutane ne mabanbanta shiyasa nakeso naji kai ta wajenka babu wani Abu?

Cikin nutsuwa Abdallah yace" dady ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai sameni da ikon Allah, kuma ina yin komai ne cikin lura, dady bamu ne zamu fara kai farmaki ba dole yanzu nasan bazasu zauna ba, da farmakin su zamu fara gano su kar ka damu babu wanda baza musawa ido ba insha Allah ko mai zai tafi dai dai!'hamdala dady yayi ya kuma tabbatar Abdallah yana yin komai da hangen nesa.


Anyi biki angama cikin kwanciyar hankali, an kuma kai Amare gidajensu, an bawa ragowar ƴan matan inno fili suna zuba sha anin su, yayin da masu shiri suka fara shiri masu makirci suka fara shirin ƙulla makircinsu,


Aɓangaren su Hajiya ladidi kuwa, yau Anty nafisa tayi sammakon zuwa gidan nasu,A yayin da suka ƙule A ɗaki suna ƙulla tsiyarsu, Anty nafisa tace"yanzu Hajiya taya zamu dinga isar da saƙonmu wajen wannan banzar yarinyar? kinga idan nace zan dinga kiranta muna keɓewa A kwai babbar matsala, kinsan gidan namu makiran suna da yawa, kuma baka ganesu kowa munafuncinsa yana cikinsa!'Hajiya ladidi tace" mafita ɗaya ce shine mubata waya!'to amma tayaya zamuyi hakan shima A kwai haɗari!'duk shiru sukayi suna tunanin mafita, can Anty nafisa tace yauwa na samo hanya!' Hajiya ladidi ta zuba mata ido tare da yi mata nuni da cewar tana sauraren ta,Anty nafisa tace" me zai hana nayiwa inno dabara na nuna mata ya kamata A bawa Zahra waya saboda ko wani uzurin zai taso na buƙatarta a kusa yayin da bata kusa!'tana direwa Hajiya ladidi tayi mata wani kallon bakya cikin haiyacinki,kana tace"nafisa A she baki da wayo so kike inno tayi wani tunani A kan haka?wannan ai ba dabara bace sam ki canza tunani!'Anty nafisa tace to Hajiya meye mafita?kinsan dai bazai yiwu mu bata waya A ɓoye ba,dan inno zata iya ganowa kuma kinsan bagidajiyar nan tsaf zata gayawa inno wanda ya bata!Hajiya ladidi taja iska ta furzar kana tace"mu bar wannan zancen nasan yadda zanyi!Anty nafisa tace dan Allah kigayamin me zakiyi kinji Hajiyata? Hajiya ladidi tace" Alhaji zan gayawa ya kamata ya kira Alhaji Baba yaji ya Zahra take, daga nan zai dinga kira akai akai danjin lafiyar yariyar, kinsan daga ƙarshe me zai faru? Anty nafisa ta girgiza kai, taci gaba da cewa daga nan zansa Alhaji ya siyo ƙaramar waya, zan sashi yaje gidan da kansa dan kaiwa Zahra wayar, wannan shirinane kuma zai tafi daidai da tsarina cikin sauƙi batare da zargin kowa A kanmu ba!wata shegiyar dariya Anty nafisa ta saki, tare da cewa, gaskiya Hajiyata kina da basira, wannan shirin yayi bari nayi sauri na koma dan gabatar da shirin mu na farko.


Dije inaso ki kasance cikin shiri dan muna gab da kutsawa cikin lamarin!'daga haka ta kashe wayar tare da jan motar ta bar gurin cikin shigar ta ta kullum.


A daidai wan nan lokacin, shi kuma Abokin aikin Hajiya ladidi bayan sun gama waya da'ita, ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya, yana mai cewa ladidi kin gama yawo tunda kika haɗa kai dani bayan Ni ɗin ma bani bane kin tabka babban kuskure kin kai kanki ga halaka, dan nasan yana gama samun Abinda yake so daga gareki sunanki sorry, Ni dai ana biyana zan canza sheƙa dama mu haka aikinmu ya gada, Hajiya ladidi kina ruwa, yayin da yakuma.sheƙewa da wata muguwar dariya, tabbas kinyi kuskure haɗa hanya da ƴan ƙungiyar jack masiface babba.


A hankali take ta kawa cikin sanɗa da kiyaye wa dan kar wani ya ganta,kuka mara sauti ta farayi yayin da taga hanyar ta ɓace mata, guduwa take sanyi dan tunda tayi mafarki da fafinta yana ƙara jaddada mata abinda ta manta wato sunan kakanta yana kuma sanar da'ita ba bacci ya kamata tayi ba, domin gaba ɗayan ta A ɗaure take A tsakanin makiya, haka kuma babban yaki ne A gabanta wanda ya tun karota da zafinsa.

Wannan shine dalilin da yasa take neman hanyar tserewa, domin zuwa ta fuskanci manyan ƙaddarorinta, sai kuma gashi kanta ya juye ta rasa hanyar tserewa.

Tana cikin wannan zagaye ne tazo ta wajen wani ɗaki, sai lokacin kuma shegen tsoronta ya dawo, dan lokacin wajen misalin ɗaya da rabi na dare ne,juyawa tayi da niyar komawa,sai dai me wani irin jijjiga taji gaba ɗaya gurin nayi da sauri ta juya dan ganin meyake faruwa, dan saboda tsananin tsoro ji tayi ta kasa guduwa,wani irin razanannen ihu ta saki wanda A tunanin ta cikin mintuna zataga an kewaye ta, sai dai ga mamakinta ko kare baiyi haushi ba, zuciyar ta ce ta shiga wani irin bugu da sauri da sauri yayin da tayi arba da ɗakin nan yana wani irin juyi tare da fitar da wani irin hayaƙi, cikin kiɗimewa ta tattara dukkanin ƙarfinta ta sheƙa da wani irin A zababben gudu na fitar hankali wanda kawai tsintar kanta tayi A cikin ɗakinta......
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 15 ```



Tamkar A mafarki haka yake ganin Al'amarin,ihun da Bintun take har cikin tsakiyar kansa, juyi kawai yake tsakiyar tattausan gadon,bakinsa ɗauke da addu'o'i, lokaci ɗaya kuma komai ya tsaya cak tamkar ɗauke war nefa, A hankali ya tashi zaune hannun sa dafe da kansa, wannan Al'amari bakaramin hautsina masa tunani yayi ba, to me hakan yake nufi?me ya kawo wannan yarinyar cikin mafarkinsa?meye haɗin ta da wannan ɗakin? meye kuma A cikin ɗakin?Anya kuwa ba abinda yake zargi A kan yarinyar bane Allah ya nuna masa? tabbas hakan yana nuna masa turo ta A kayi, to amma waye ya turota? me aka turota ta aikata masa? komawa yayi da baya ya jingina da fuskar gadon tare da tattaro bedsheet ɗin ya ciku kuyeshi ya watsa shi ƙasa, miƙewa yayi ya fara zagaye ɗakin yana furzar da wani irin zazzafan huci daga bakinsa, idanunsa har sun sauya kala saboda tsananin zafin zuciya, lailai dolene ya binciki yarinyar nan,A sannu zai kamata da lefi dumu-dumu, bathroom ya faɗa ya ɗauro Alwala ya kama jera na filfilu.



Tunawa da Abinda ta gani yasa ta kuma rikicewa jikinta ya shiga wata iriyar kakkarwa, cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi ya rufeta, A matuƙar tsora ce take da gidan nan, wannan wane irin gidane suka kawoni? ta faɗa cikin kakkarwar jiki da tashin hankalin da yaƙi barinta, raɓewa tayi can ƙarshen ɗakin tanajin kamar A lokacin abun yake faruwa, runtse idanun ta tayi, cikin tashin hankali tace"wayyo Allah katemakeni ka kuɓutar dani daga hannun waɗan nan mutane, ya Allah katemakeni ka tsareni daga shiga haɗarin gidan nan, ka kawo min mafita cikin gaggawa!'kuka tasaki me matuƙar bantausai da karya zuciyar mai imani,A hankali cikin jin tsoro da ɗar-ɗar take takawa har zuwa cikin bathroom,Alwala tayi ta fito ta shinfiɗa sallaya ta tada kabbara domin miƙa Al'Amuranta gurin sarki Allah buwayi gagara misali.


Garau ta tashi washe gari tayi aikinta kamar yadda ta saba, ta haɗa karinsa ta nufi falonsa da tunanin ya fita motsa jiki kamar yadda ta saba zuwa ta tarar ya tafi, shi yasa basu fiya haɗuwa ba,tana shiga falon ta ɗan yi jim, kana kuma ta wuce ta jera kayan karin,juyowa tayi bayan ta A jiye da nufin ƙara Sachin ɗin falon dan ganin inda bai gyaruba ta kuma kimtsawa, saboda tun kan ya farka take shigowa ta gyara falon idan ya fita motsa jiki kuma sai ta gyara ɗakin da wankin toilet, dafe ƙirjinta tayi tare da saurin ja da baya ganin mutum kwance yayi luf cikin kushin, A kimtse yake cikin kayan motsa jiki damtsensa sai glowing yake idanunsa A rufe tamkar mai bacci, murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da motsashi A hankali tace"haka kawai sai mutum ya dinga bani tsoro kuma bani da damar yin ihu ko kuka sai A fizgeni a wulla waje,mutum sai kace kurma ba abinda ya iya sai ɗacin rai!

A hankali ya shiga buɗe lumsassun idanunsa masu dawo da mutum cikin nutsuwar sa, ya ɗora su Akan kyakkyawar fuskar Bintu,tsaf yaji duk abinda tace, saboda shi Abdullah ya kasance daga cikin mutane masu tsananin ji, dan haka bai sha wahalar jin duk abinda take faɗa ba.

Cikin rikecewar da kaifafan idanunsa masu tsananin maiƙo da sheƙi suka sakata,cikin yanayin fargaba da matsanancin tsoro da ya saukar mata A lokaci ɗaya, cikin sanɗa ta taka dan tsira daga waɗan nan shu'uman idanuwan nasa da suke neman kassara duk wata gaɓar da ke gudanar da jini A cikin jikinta,

Wata tsadaddiyar murya taji tamkar amsa sarewa acikin kunnuwanta,wadda ta saka gaba ɗaya ragowar kuzarin dake tare da ita ya ƙarasa malalewa,cak ta tsaya A inda take batare da ta ƙara wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba, cikin yanayin maganarsa na fitar da magana ɗai ɗaya tamkar wanda akasashi yi dole,yace"karki sake ganina ki tsorata,numfashinta bai gama dai dai tuwa ba ya kuma rigirgizo mata tambayar da ta motsa ƴan hanjin cikinta, tare da wata iriyar juyowa sosai tana fuskantar sa, yayin da idanuwan nan suka kuma fitowa cikin firgici da tsoro,sai da ya gama karantar yanayin ta tsaf kana ya kuma mai maita mata tambayar,yace" dake nake jiya misalin ƙarfe biyu me ya fita dake waje har kina neman fasawa mutane kunnuwa da shegen ƙaranki,me kikeso kishiga kiyi A wannan ɗakin? hantar cikinta ya kuma kaɗawa, to ma wai miyene na jin tsoron bayan nasan ban yi komai ba,wata ƙila ma shine yake wani mugun abun A cikin ɗakin, idan ba haka ba me yasa da yaji ihun nawa baizo ya tai makeni ba?kuma ya akai yasan na fita? kai wannan mutumin A kwai baƙin mugu!' gigitacciyar tsawar da ya buga mata ne yasa ta dawo haiyacinta,ya nunata da yatsa yana cewa duk ranar da na tabbatar da rashin gaskiyar ki to ki tabbatar da cewa sai nayi gutsi-gutsi da namanki A cikin gidan nan,wuce ki fitamin A falo!tun kan ma ya gama rufe bakinsa ta arta da wani shegen gudu,bata tsaya A ko'ina ba sai tsakiyar gadonta tana maida numfashi me cike da razanar da tayi da Abdallah, Allah kafitar dani daga cikin wannan gida na mutane marasa tsoron ka, kowa munafiki ne A wannan gidan, duk basu da gaskiya, duba Irin kallon da wannan Ammin Rahiman takeyi min dagani itama so take tasani wani mugun aikin!'


Ammi ta dubi Rahima tace" auta ina ƙawarki kuwa zahra?Rahima ta saki dariya tare da miƙewa zaune tana cewa" wai ta gidan inno? ni wallahi ma banje ba tun washegarin da Aka kai Amare, faɗa mukayi da inno! ta ƙarasa maganar tare da ɗan turo baki, Ammi tace"to ai ba da ƙawar taki kukai faɗa ba ya kamata dai ki dinga zuwa kina ɗebe mata kewa!'to Ammi amma sai na huta sosai zan koma zuwa!' Ammi tayi murmushi kawai A ranta tanajin haɗa kusanci tsakanin Rahima da Zahra shine kawai hanyar da zata 'iya bi dan fahimtar abinda take so ta sani A game da Zahra,tasan ko bata tambayi Rahima ba zata dinga bata labarin Zahra,ita kuma zata dinga hankalta da inda yarinyar ta sa gaba idan A kwai wani Abu maka mancin na rashin gaskiya zata sani.


Duk tsarin da Hajiya ladidi tayi shine ya kasan ce, sau biyu ne tasa Alhaji munir ya kira Alhaji Baba,ba tare da wani shan wahala ba tsarinta ya tafi yadda take so koma fiye da haka tunda A cikin kwana biyu Alhaji Baba yaji san sha'awar ya mallaka wa Bintu waya,ko dan sudinga gaisawa da bawan Allah Alhaji munir, tabbas yana jin daɗin yadda Alhaji munir ɗin yake nuna kulawarsa A kan ƴar marainiyar Allah Bintu,shi yasa yaji A ransa gwara ya bata waya dan shi Alhaji munir ɗin yasamu damar kiranta kai tsaye,

Alhaji Baba da kansa ya kira Alhajin Nafisa, yasanar dashi ya bawa Bintu waya kuma layin da yaƙi rasa dashi shine layin Bintun, dan haka zai'iya kiranta kai tsaye, godiya Alhajin Nafisa yayi masa kana sukayi sallama, A lokacin suna tare da Hajiya ladidi ya kuma sanar da ita yadda sukayi da Alhaji Baba,yadda Hajiya ladidi ta nuna farin cikinta,har saida ya tsaya yana dubanta cike da mamaki,ganin haka yasa ta waske tare da cewa, kai masha Allah gaskiya Alhaji Baba ya kyauta,tare da ɗaukar wayarta ta bar falon.


Ita dai Bintu kawai ganin inno tayi da ƙaramar waya ta bata,duban inno tayi tace"inno wannan wayar fa ta waye?inno tace nakine Alhaji ne ya baki saboda kurinƙa gaisawa da Alhajin Nafisa!'to inno kiyi masa godiya, yanzu zan ƙarasa aiki sai naje nayi masa godiya nima!'inno tace"aiko yace" karki sake kije da niyar yi masa godiya,yace kiyi masa addu'a kawai ita yake buƙata!'cikin sanyin jiki Bintu tace"inno ai addu'a tsakanina daku ba mai yanke wa bace, Allah Ubangiji yaja kwana me amfani!'inno ta amsa da Amin Batula,kana ta juya ta fita daga kiching ɗin.


Tunda inno ta fita ta kasa ci gaba da aiyukan ta, gaba ɗaya ji takeyi mutanen nan suna ɗaureta, wai yaya ita da take neman hanyar tserewa suke ƙara yi mata da baibayi da zaman gidan,anya kuwa zata iya ci gaba da zama A gidan tana cin karo da shaiɗanun mutane da kuma Aljanu?


Lokacin da Anty Nafisa ta shigo falon inno bata tarar da kowa ba,dan haka kai tsaye kiching tanufa, dan anan takesa ran ganin Bintu, cikin Sa'a kuwa tana shiga ta sameta tana kan tunanin mafita wa matsalar datake ta tun karo rayuwar ta,

Tana ganin Anty Nafisa jikinta ya fara rawa, cikin sauri ta durƙusa ƙasa dan gaidata, batare da ta amsa ba ta ɗora mata da tambayar, ina inno? Bintu tace"ta tafi wajen Hajiya Babba,zata dubata da jiki!'saurin kamo Hannun Bintu tayi sukayi can cikin kiching ɗin,hannu ta mikawa Bintu tare da cewa ina wayar da inno ta baki?cikin sauri tace gata can, tanayi mata nuni da kan prezer,da sauri Anty Nafisa ta ɗauki wayar tare da buɗe ta tasaka mata wani layin A ciki, kana tasata A babiratin, sai da ta gama sannan ta dubi Bintu tace"ki kula da kyau, baki wayar nan yana daga cikin shirin mu dan haka ki kula da'ita tamkar yadda zaki kula da rayuwar ki,kuma duk wani shiri da kike na guduwa muna sane da hakan,zaro manyan idanunta tayi wanda idan tayi hakan baƙaramin kyau yake ƙara mata ba, Anty Nafisa tayi murmushin mugunta,kana tace" kina mamaki ko? to inaso kisani duk yadda kika zacemu mun wuce haka, mun zarta tunanin babban kaima barantana wannan ƙaramin kan naki, inaso kuma ki dinga sarrafa wannan shegen tsoron naki dan watarana zai iya hhhh gaiyato mana matsala cikin aikin mu, inaso kuma ki iya bakin ki A cikin gidan nan dan duk wanda kika gani ba Abin yadda bane ESTATE ƊIN ALHAJI BALARABE YA WUCE TUNANIN MAI TUNANI munanan munajira muga yadda ƘUDURAR ALLAH zata tarwatsa mugayen zukata da ɓara gurbin IYALEN ALHAJI BALARABE dan nasan namu ba komai bane shiyasa bana tunanin yin na dama akan abinda nake aikatawa ko kuma nace na aikata,A da har na fara karaya, na fara tunanin makomata sai Hajiyata ta nusar dani tare da ɗorani bisa hanya mai ɓullewa.


Babu abinda zuciyar Bintu take sai wani irin bugu mai tsanani, Anty Nafisa idon ta ya rufe ko lura da yadda yanayin Bintu ya koma batayi ba,dan tana gama zantukanta ta juya ta fita da sauri tabar kiching ɗin,yayin da ta bar Bintu tamkar butun butumi A daskare, tuni ƙwaƙwalwar ta tafi hutun wuccin gadi,ji tayi an jijjigata da ƙarfi,wata Irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tayi tare da fashewa da wani kiɗimam man kuka mai razanar da zuciyar mai imani, dije ta zuba mata ido cike da mamakin meye yasa ta kuka kuma? ko dai irin matsalar su ɗaya? tabbas ta daɗe A laɓe tanajin Anty Nafisa sai dai bataji komai ba, tunda bata daɗe da shigowa ba Nafisan tafita,tsoron irin kukan da Bintun takeyi shiya kama dije,tsoron biyune ya haɗe mata na farko kukan Bintu wanda har yi take kamar zata shiɗe, na biyu tsoron kar A zo akamata ace ita tayiwa Bintun wani abu, wannan tunani da tayine yasa tayi saurin juyawa zatabar kiching ɗin, Amma kuma sai taji ta kasa wani irin tausayin yarinyar ne ya dinga kewayawa har cikin ɓargonta wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata, cikin sauri ta durƙusa inda Bintu take ta kama hannun ta tare da miƙar da ita tsaye,A hankali ta jawota jikinta ta shiga bub buga bayanta tana shafa kanta tana bata baki cikin taushin murya,tace" haba ɗiyata ko mai yayi zafi fa maganin shi Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan kowa kika ganshi yana da matsalarsa, wannan kukan da kikeyi ai sai ya cutar dake ki dena ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah shine zai yaye miki kinji!'Bintu da yanzu ta riga tayi shiru sai ajiyar zuciyar da take fitarwa ajejjere,sai da dije ta tabbatar Bintu ta samu nutsuwa kana ta janye ta daga jikinta tace maza jeki ɗaki ki wanke fuskar ki kar inno tazo ta ganki A haka baza taji daɗi ba!'A hankali Bintu ta fara takawa sai da ta kusan barin kiching ɗin kana ta juyo cikin muryar ta da ta dashe tace" mama na gode Allah ya biya ki dukkanin buƙatunki na Alkhairi ya kareki daga sharrin maƙiya!' da sauri ta ƙarasa fita daga kiching ɗin saboda wani kukan dayake ƙoƙarin kufce mata,

Da ido dije ta bita tana ta nanata faɗin Amin akan harshen ta,haƙiƙa idan tace bata ji daɗin addu'ar da Bintu tayi mata ba tabbas tayi ƙarya, itama fita tayi jikinta A sanyaye, zuciyar ta kuma cike da tunanika iri-iri.


Tana shiga ɗakin ta waɗa

Please Login or Register in order to submit comment