Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gan shi ba,

Tana fita kuwa ta samu dan sahu ya kaita har ƙofar ESTATE, tana sauka taga wata luntsumemiyar mota zata shiga cikin estate ɗin har zuciyar ta taji motar ta burgeta, bayan motar ta shiga itama tabi bayanta tana mai hango yawan tafiyar da zata miƙa.

A hankali yace" Yahya tsaya yarinyar nan!' daga haka ya maida idanunsa ya kulle yana mai tambayar kanshi dalilin sawa a shigo da ita cikin motarsa,wani ɓangare na zuciyar sa yace" kawai dan ita ta kasan ce mace ne shine dalili,Yahya yayi ƙasa da glace ɗin motar tare da zura kansa waje ya ɗan ɗaga muryar sa yace"ki shigo mu ƙara sa dake!' kamar daga sama Bintu taji muryar Yahya da sauri ta juyo har zatayi gaddama sai kuma ta tuna zurfin tafiyar dan haka tayi shahada tare da addu'a A bakinta, kasancewar glace ɗin tintak ne shi yasa bata lura da oga Abdallah dake kwance A bayan motar ba,A hankali tasa hannu zata buɗe bayan motar Yahya yace" a'a shigo nan yana mai buɗe mata ƙofar,batare da tace" komai ba ta maida hannunta kan ƙofar gaba ta shiga da sallama tare da addu'ar da take ta nanatawa abakinta,tana rufe kofar wanan sanyayyan ƙamshin da ya zama hadda A hancinta yayi mata maraba, A hankali ta juyar da kanta zuwa bayanta,wani irin daram ƙirjinta ya buga dama shine A cikin motar nan to amma dai tasan bashi yace ta shigo ba dan A tunanin ta hakan baza ta taɓa faruwa ba, nutsuwa tayi sosai yayin da wannan yanayin da take kasancewa A cikin sa duk lokacin da sukayi kusanci da juna ya shiga mamayarta, ƙirjinta bugawa yake duk sakan da minti,fatanta kawai Allah ya kaisu lafiya.

Suna ƙarasowa ta fita da gudu kamar walƙiya haka ta ɓacewa idanunsu, Yahya kasa daurewa yayi sai da ya ƙyaƙyale da dariya yace" kai wannan yarinya kwai zabuwa ga yadda ta kwasa a guje kamar ance za a saceta!'shiru yayi saboda kallon takaicin da yaga ogan nasa na binsa dashi da sauri ya dauko jakarsa yabi bayansa da ita.

Dije kuwa kasuwa ta wuce tayi sayayyarta kana ta wuce gida,yayin da zuciyarta ta samu nutsuwa, damuwarta cikin kaso ɗari taji sauƙin kaso ashirin A ciki,dan haka lafiya ƙalau ta koma gida batare da tunanin wani abu ba.


Tana shiga falon da sauran gudunta inno dake zaune ita da Najib wanda yake dakon dawowar Bintu,tace" Bintu lafiyar ki kuwa? ɗan tura bakinta tayi kafin tace" wani A bu ya shigo falon cikin sallama,inno tace au ko dai tare kuke ne? Bintu cikin gunguni tace" da inno a'a daga get suka ɗaukoni!'inno tace" ashe taimakonki akayi amma kike wannan shegan taka!'bi yayi ta gefanta ya shige batare da ya tanka ba, tana ganin ya wuce ta dubi inno cikin ɗan shagwaɓe fuska tace"Allah kuwa inno tsoro yake bani shi bashi da aiki sai bawa mutane tsoro!'inno tace" ikon Allah dama mutum yana bawa mutum tsoro? A to inno shi dai kam yana bayarwa!'ta faɗa tana shigewa ɗakinta,daga inno har Najib dariyar wautar Bintu sukayi..


Yana shiga bedroom ɗinsa kai tsaye ya wuce toilet bayan ya Ajiye jakar shi,ya ɗan jima kana ya fito ya shirya cikin gaggawa saboda kiran sallar la'asar da akayi,fes ya fito cikin shigar sa ta yau da kullum wato kananan kaya sai ƙamshinsa da ya game ɗakin gaba ɗaya, yana fitowa ya wuce Pert ɗin Alhaji Baba Dan yasan yana can yana jiransa dan zuwa Masallaci dan tunda ya fara zaman gidan kwana biyu suka koma tafiya tare kamar yadda sukeyi da Asuba, amma yanzu ba Alhaji Baban ne yake zuwa ba shi yake zuwa su tafi tare wanda da ƙyar da lallashi Alhaji Baban ya yadda da haka.

Tofa yau dai kasuwar ESTATE ce take ci dan kuwa kowa da baya gida ya dawo yaran masu gida ƴan makaranta duk sun dawo ɗan gidan Alhaji Mansur saiyid da yaran Baba Ali guda biyu Sadik da lamin duk A yau suka dawo ƙasar su cikin gidansu kuma ahlin ALHAJI BALARABE,

Sai mata da suka dawo daga b.u.k kano taufiƙa da siddiƙa ƴaƴan sadiya, kasancewar ita ba A Nigeria tayi aure ba tana can ƙasar camaroo jikokin inno kenan kuma duk A sashen inno zasu zauna, dama sunce idan suka gama karatu bazasu koma camaroo ba dan haka sai da Bintu tayi gyaran ɗakinsu,

A yayi da su kuma samarin suke ɓangaren su daban A yanzu dai samarin gidan sun kai su shida, sai ƴan mata guda bakwai wanda suke rayuwa A cikin estate, Alhaji Baba ya aurar da jikoki kusan goma sha biyar maza da mata ba iya kacin na gabansa ba kawai har na sauran garuruwa.


Rahima da amna suma sun dawo ita kuwa Hauwa'u dama tunda Abdallah ya dawo estate ta daina zuwa ko ina.

A wannan rana Bintu ta aikatu iya aikatuwa, shi kuwa girkin oga Abdallah dama babu ɗaga ƙafa,ba ita tasamu zama ba sai ƙarfe tara na dare,yayin da jikinta yake A sanyaye saboda yadda ƴan matan suka dinga kyararta da nuna mata asalin matsayinta,ta fuskanci taufiƙa da siddiƙa suna da matuƙar jin kai da ɗagawa yayin da Farida take da mugun wulaƙanci kuma A kwanta da baƙar magana, itace auta A gurin babanta Alhaji Habib kuma A cikin ƴaƴan da ya haifa duka mata ita kaɗai ce bai aurar ba,Rahima da amna su kaɗai ne sukewa Bintu kallon mutum.


Washe gari dawowar su, Bintu tana kiching tana ta sauri ta haɗawa oga Abdallah kayan karin kumallo saboda yau taso ta ɗan makara kasancewar gajiyar da ta tara A jiya, siddiƙa ce ta shigo cikin kiching ɗin tana mussika ido alamu dai ya nuna yanzu ta tashi daga bacci,A lokacin kuma Bintu ta gama haɗa komai tana shirin fara ɗauka dan kaiwa ta jera masa A falonsa,dubanta siddiƙa tayi tana wani ya tsina fuska kamar taga kashi tace"ke bani break ɗin nan da yunwa na tashi safiyar yau!' cikin nutsuwa Bintu tace"wannan ai na Oga Abdallah ne kuma ba a haɗa masa abinci da kowa shi kaɗai nakewa ki bari na kai masa sai nazo yanzu na haɗa muku wani!' tunda Bintu ta fara maganar take Binta da wani matsiyacin kallo irin na ke ɗin wacece,dan haka bata bari Bintu ta haɗiyi miyau ba ta fara sauke mata kondon rashin mutunci cikin ƙasƙanci tace" ke ɗin wacece?kuma ƴar gidan uban waye da har zaki hanani Abinda ya kasance ikona? ta daka mata wata gigitacciyar tsawa mutuniyar tuni ta gigice jikinta ya shiga rawa Bintu in da Akwai abinda ta tsana A rayuwarta to bai wuce tsawa ba, babu A binda ke saurin ruɗa ta kamar tsawa shiyasa take da matuƙar jin tsoron ruwan sama,kafin wani sakon hawaye sun fara mata ambaliya,ganin hakane yasa Siddiqa tayi saurin ƙwace tiren hannunta tana ci gaba da watsa mata ba zan kallo,cikin tsoro biyu da ya haɗar mata tace"dan Allah karki tafi dashi duka ki ɗiba iya wanda zai miki wallahi shima..bata ƙarasa ba taji tas an wanke kyakykyawar fuskarta da mari,runtse idanun ta tayi kana ta buɗe su a hankali saboda nauyin da sukayi mata,taufiƙa ce tayi mata wannan marin tana tsaye a gabanta tana mata kallon gargaɗi,tace" ke har kin isa ƴaƴan masu gida su buƙaci Abu ki hanasu ke ɗin wacece idan kikayi wasa sai na lalata wan nan banzar fuskar taki,idan baki sani ba to yau kisani mu ba A takamu ko A makaranta abinda muka gadama mukeyi bare kuma A cikin gidan mu!'kallon siddiƙa tayi tace maza kwaso mana break ɗin duka bari na yiwa Farida waya da Hauwa'u su zo mu karya anan!' siddiƙa ta bata hannu suka tafa kana suka kwashe komai sukayi waje dasu.

Dur ƙushewa Bintu tayi A wajen ta saki kuka mai ban tausayi,ta yaya A cikin ɗan lokacin da Oga Abdallah yake bata ta kammala masa break zata yi ƙoƙarin sake haɗa wani, lafiya yan kunun gyaɗa tayi masa da farfesun kan saniya sai ƙosai da tayi masa wanda yaji attaruhu da albasa da kwai sai ruwan liptom data haɗa masa da kayan ƙamshi,ko ita ɗin injice ai dole ta ɓata lokaci,sauri tayi ta miƙe dan fara sarra fa kayan, wake ta kuma ɗebowa ta gyara ta zuba A blender kana ta ta ce gyaɗa ta ɗora akan gas,


Shi ko Abdallah tunda yaga ya gama shirinsa ba a kawo break ba ya samu guri ya zauna yana ci gaba da aikinsa A laptop,wani irin yunwa yaji na nuƙurƙusar hanjinsa dan haka ya miƙe ya fito falon inno ko da zai ci karo da dalilin da ya hanata kawo masa break bayan yaga alamun ta gyara ko ina na falon da ɗakin bayan dawowarsa daga motsa jiki,zama yayi yana fuskantar ƙofar kiching ɗin..


Saura ƙiris ta kammala komai, su taufiƙa suka dawo kiching ɗin hannayensu ɗauke da kwanikan abincin saurin karɓar kwanikan tayi dan har da su a fargabarta tun da a cikin saitin kayan Abdallah suke, taufiƙa ce tace yauwa kinga Farida ba sai mun jira ba ma tunda ta kusa kammala wannan sai kawai muje mu ɗora dasu!' wani irin zaro ido Bintu tayi yayin da zuciyar ta ke wani irin bugu da sauri da sauri tasa hannu ta dafe ƙirjinta..


Comments....

Vote......

Share....
💕
*KUDURAR ALLAH* 💕

*NA*


*FATIMA Y. ADAM*





_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



```Page 20 ```


Cikin tashin hankalin abinda suke san jawo mata tace" dan Allah kuyi haƙuri wallahi idan na kai masa zanyi muku wani irinsa amma dan Allah na roƙeku kar ku taɓa abincin nan!'Farida tayi mata wani kallon sama da ƙasa sannan tace" ke ƴar kwaɗayayyu ai taki taƙare tunda iyayen ki basu da zuciya suka turoki aikatau to dole ki shaƙi takaicin mu,dan haka baki isa ki hanamu ɗaukar Abincin nan A karo na biyu ba, shi wanda zaki bawa kwartankine da jikinki yake rawa dan zamu ci abincinsa? to daga yau ya daina baki abinda yake baki in baki bashi ba!' gaba ɗaya suka sheƙe da dariyar mugunta gami da ta fawa, siddiƙa tace" gaskiyar ki fa sister zan can nan haka yake babu kuskure A cikin sa!' wani irin runtse idanu Bintu tayi tanajin A rayuwarta ba'a taɓa ci mata mutunci kamar haka ba yau ita A kewa ƙazafi mafi muni A Rayuwar duk wata kamilalliyar mace, fuskarta tayi jawur saboda baƙin ciki da kuma wata azababbiyar tsana da ta taho tunda ga ƙasan zuciyar ta fararen idanunta sun juye sun koma wata kala, numfashinta da kyar yake fita saboda azabtar ɓacin rai,kafin ta ankara sun fara ɗaukar jikokin da fulas ɗin kunun gyaɗa,Farida tace" bari na kaiwa inno nata kar ayi babu ita Ana nan ana wadaƙa da hatsinta za akai wa kwarto!wani irin A zaɓaɓɓen mari mai matuƙar ƙuna da zafi taji an ɗauketaa dashi, kafin ta dawo haiyacinta ta fahimci wanda yayi mata mari ankuma sharara mata wani wanda har sai da nun fashinta ya ɗauke tare da anbaliyar jini ta hanci da baki.

Bintu da kanta ke sunkuye tana wani irin kuka mai sosa zuciya, tayi saurin ɗago kanta tare da zuba masa ido cike da tsananin mamaki da kuma tsoron hukuncin sa A kanta, siddiƙa da Taufiƙa kuwa daskarewa sukayi A tsaye tare da zuba ma sabuwar halittar da suke gani ido, wanda take suka manta da abinda sukeyi hatta marin da aka shararawa Farida bashi ne agabansu ba, kallon da ya shiga yi musu, shiyasa su kusan sakin fitsari A tsaye, siddiƙa saboda tsananin farga ba da yadda yake hukunta su da idanunsa masu tsananin kaifi,yasa ta zame ƙasa dabasss ta zauna jikinta na karkarwa.

Cikin takunsa na isa da ƙasaita ya ke takowa gabansu yayinda takun yake bada wani ɗan dadda ɗan sauti wanda ke nuni da zuwan cikakken namiji,wata irin tsayuwa yayi A gabansu, yayin da sukejin tamkar zuciyoyin su zasu faso ƙirjinsu saboda tsananin tashin hankali,Bintu ma da ba wajen ta ya tsaya ba jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari.

Tsananin kyansa da kwarjini da tarin ilhama da ƙasaitar sa da kuma shu'uman idanuwansa suka haɗu suka ƙara firgita zuciyoyinsu da gangar jikinsu,Farida kuwa tunda ta ƙame bata ƙara motsi ba dan har yanzu bata dawo daga suman Ido biyu da ta tafi ba,

Jin sautin kamilalliyar muryarsa mai cike da wani irin maganaɗisu shiya dawo dasu daga suman wucin gadin da sukayi, yace" zo nan!' kallon juna suka shigayi dan basu fahimci wadda ya kira A cikinsu ba, saida ya juya ya buga mata tsawa,kana ta fahimci da ita yake, cikin ɗaga sauti yace" ba dake nake magana ba?Bintu ta kuma rikicewa har ta rasa Abinda ya kamata tayi,wani ƙaƙƙarfan tsaki ya saki yana mai sheƙa mata wata muguwar harara wanda ta kaɗai ƴan hanjinta,saboda rikicewa har bata san lokacin da ta ganta A kusa dashi ba wanda har sai da hakan ya haifar mata da wata mummunar gullewa,runtse idanunta tayi tana shirin taji wani ta A ƙasa,shirun da taji bata kai ga kaiwa ƙasa ba, da kuma wani masifaffen ƙamshi mai kassara gaɓoɓi,da jinta A cikin wani yalwataccen ƙirji tamkar fadama shiyasa ta buɗe firgitattun idanunta masu matuƙar sheƙi da wani irin maganaɗisu,Aikuwa tana haɗa ido dashi ta kuma zarosu tamkar zasu daɗo ƙasa, tamke fuskarsa ya kumayi,ganin haka yasa da wani irin sauri ta zame daga jikinsa,kana cikin rawar murya da in ina tace" kakkayi-kayi haƙuri!' banza yayi mata tare da maida dubansa kan su Taufiƙa,kana cikin gajiyawa da yawan maganar da suka sakashi, yace"ki maresu!' da sauri ta dubeshi cikin nuna kanta da rawar murya tace" waini kake nufi na maresu?ko bazakiyi ba ya faɗa yana tsatstsareta da lulu eyes ɗinsa,girgiza kanta tayi ta juya tana fuskantar su,tana tunanin wannan shine abinda zatayi musu ta fanshe baƙin cikin da suka jefata,yadda suke taƙama da ji da kansu Ace ƴar aikin da suka raina ta sharara musu marika yaya mutum yake zaton zasuji,take taji wani ƙwarin gwiwa yazo mata dan haka batare da ɓata lokaci ba ta bude tafukan hannunta ta saita A kan fuskar Taufiƙa jikake tass kafinta dawo haiyacinta ta ɗorawa Siddiqa nata kana ta juya ta daddage ta shararawa Farida wanda yafi nasu ƙarfi da zafi, Aikuwa Farida kasa daurewa tayi kawai sai ta fashe da wani rikitaccen kuka ta fita daga ɓangaren gaba ɗaya tana kuka mai ƙarfi.

Taufiƙa da siddiƙa suma fita sukayi suna mai ɗaukar alwashi da muguwar manufa A kan Bintu,zuba mata kaifafan idanunsa yayi,yayin da yakeji kamar zaiyi dariya saboda lamarin na Bintu akwai ban dariya da kuma takaici wato ta samu dama da ƙwarin gwiwa har wani dagewa take tana zabga maruka da kuma baizo ba ko ya zatayi dasu oho,fita yayi yana cewa ki kawomin karina yanzu nan idan kuma suka dawo sukayi miki duka babu ruwana!'kafin ya kammala rufe bakinsa ta zundumi fulas ɗin kunun gyaɗa da na ƙosai har ta rigashi fita daga kiching ɗin, binta yayi da kallo cike da mamakin tsoro irin nata.


Kuka takeyi sosai wanda yake cike da san garta da kuma san ƙarawa miya gishiri,faɗawa falon nasu tayi tana mai ƙara zuzuta lamarin da shegen kukanta,Hajiya Saratu da ta fito daga kiching hannunta ɗauke da ruwan jarka,tayi turus tana kallon borin da Farida keyi cikin tsakiyar falon, cikin ɗaga murya tace"ke lafiyar ki kuwa? kamar wadda aka yiwa mutuwa!' Farida ta miƙe zaune,cikin rikici irin na auta,tace" momy wallahi garamin mutuwa da irin cin mutun cin da akayi min yau, ki duba ki gani marin ƴar aiki ne da marin ƙaton namiji A kan wannan kyakkyawar fuskar tawa!' A hankali Hajiya Saratu ta samu guri ta zauna tana bin Farida da wani irin kallon tuhuma,kawar da kanta tayi tana zunɓura baki dan tasan momin ta ba goyan bayan ta zatayi ba,aikuwa cikin ɓata fuska Hajiya Saratu tace"me kikayi mata dan nasan ruwa baya tsami banza, tabbas akwai abinda kikayi mata keda su Siddiqa, dan na tabbatar yarinyar nan baza ta mareki da gangan ba!' Dady ne ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, cike da kulawa yake duban Farida, kana yace" auta meke faruwa ne? da sauri ta isa gurinsa ta raɓa jikinsa,tace" Dady marar maka Ni Akayi,kuma nazo na faɗa wa momi ta rufeni da faɗa,ba tare da ta saurareni ba!'Alhaji Habib,ya maida dubansa kan H Saratu,yace" haba Saratu me yasa kike hakane idan baki rarrashe ta ba waye zai rarrasheta? gaskiya bana son haka!'Hajiya Saratu tayi murmushin takaici kana tace" Ni banyi mata faɗa dan wani abuba sai dan nasan bata da gaskiya,kuma kaima kasan halin ƴarka sai dai so ya rufe maka idanu,zama yayi tare da Farida kana yace" ai ban ce miki bata da laifi ba amma ai kya saurareta kiji ba'asi tunda ita aka mara!' juyawa yayi yana duban Farida yace" auta gayamin me yafaru aka mareki?nan kuwa Farida ta karkace ta shiga faɗar ƙarya da gaskiya,tana gamawa momy Sarah ta dubeta tace" yanzu ke bakiji kunyar ƙaryar da kika zauna kina sheƙa mana ba?tura baki tayi tace"nikam gaskiya na faɗa!'to munji nasu laifin ke kuma ina naki yake?shiru tayi batare da ta kula momin tata ba, Dadin Farida yace" gaskiya basu kyauta ba da suka mareki harsu biyu dan mugunta,amma kiyi haƙuri kar ki kuma shiga har karsu babu ruwan ki dasu kinji auta!' ta shi tayi ta nufi hanyar ɗakinta sai kuma ta dakata tare da juyowa fuskarta Babu alamun wasa sai tsantsan burin ɗaukar fansa tace Dady bana yafiya kuma bazan yafe musu ba har sai ranar da na ɗauki fansa na gansu suna kuka fiye da kukan da suka sani!wucewa tayi ɗakinta tayi cikin sassarfa,wani mugun kallo momi Sarah ta shiga wullawa mijin nata kallon kaga irinta ko,miƙewa tayi tabarsa nan zaune yana murmushi wanda Ni kaina ban san manufar murmushin nasaba.

A ɓangaren su Taufiƙa ma kusan hakane ya kasance,sai dai su saɓanin Farida ne ita tasamu rarrashi da ga gurin Babanta,yayin dasu kuma har kusan marinsu saida inno tayi, ta ƙare musu tatas ta ɗora musu da cewa nariga nasan halin Bintu tun kafin zuwan ku babu wanda ya taɓa kuka da ita ko ya kawomin laifin ta yarinyace sam mara shiga sabgar mutane tana da nutsuwa da hankali,kuma nasan tunda har Abdallah ya shiga lamarin lallai baƙaramin rashin mutunci kukayiwa Bintu ba, dan haka abinda yasa tayi muku yayi dai dai naji daɗi,kuma bazan hanaku ci gaba da rashin mutuncin kuba zan kyaleku dan ina da mai gyara muku zama sangar tattun banza sangar tattun wofi,kutashi ku fitamin A ɗaki!'tashi sukayi suka fita suna mai cin alwashi A kan ci gaba da ƙuntatawa rayuwar Bintu baiwar Allah.


A hankali take tafiya dan zuwa sashen Hajiya Babba,domin kai mata Masar da tayi mata alƙawarin zatayi mata saboda tana matuƙar son masa,tazo dai dai mahaɗar da zata sada ta da kori dan da zai kaita falon Hajiya Babba,sai kawai ganin mutum tayi A gabanta tamkar an jehoshi,da sauri ta ja da baya tana shirin sheƙawa da gudu,cikin hanzari Sayyid yasha gabanta yana cewa ke dalla matsoraciya mutum ne kuma ɗan uwan ki musulmi!'ɗan dakatawa tayi tana maida numfashi,kana cikin ladabi ta gaidasa,amsawa yayi yana Binta da wani shu'umin kallo,yayin da kwaɗayayyun idanunsa suke bin ko'ina najikin ta da kallo,hakan da taji ajikin tane yasa tayi ƙoƙarin zagaye shi dan wucewa, sai dai me wani irin figa taji yayi mata har yana ƙoƙarin mannata da jikinsa,A matuƙar fusace ta angijeshi tare da nuna sa da yatsa tace"kai wane ne A cikin halittu da har zakayi ƙoƙarin yin shishshigi ga halittar da tafi karfika halittar da ba ayita domin kaba kuma wadda take haramtacciya agareka? cikin cire tsoro da shirinta na fara yaƙi ga dukkanin wanda yake shirin zame mata annabo a rayuwa, taci gaba da cewa to A kul kuma A hir ɗin ka karka kuma yin wannan gangancin idan ba haka ba kuwa, hmmm,ta karkaɗa yatsan ta tare da ratsashi ta wuce ta barshi sake da baki da hanci,bashi ne ya motsa ba har sai da yaga shigarta falon Hajiya Babba kana ya jinjina kansa tare da cewa shike nan Bintu kike kowa kin jefo kanki komar Sayyid Mansur Balarabe muje zuwa muga idan zaki ci riba...


Bayan ta kaiwa Hajiya Babba Masar sai ta biyo ta can bayan ɓangaren Alhaji Mansur, inda tanan zata miƙa ya maida ita ɓangaren wannan ɗakin tana kusan ƙarasowa ta shiga ƴan dube dube ko da da wanda yake binta duk da zuciyarta cike take da matsanancin tsoro amma tariga tasa aranta sai taje wajen nan yau dan ta daɗe tana neman wannan damar saboda tasan dole sai ta cire tsoro ta kuma fara ƙoƙarin tun karar haɗarin dake gabanta,jin wayarta na zumm zumm yasa ta dakatawa daga tafiyar da takeyi,ɗagawa tayi tare da yin sallama,ta can ɓangaren Hajiya ladidi tace"Bintu ya akayi meye labarin da kika samu daga wajen Dide?cikin ƙara duba bayan ta da gefen ta Bintu tace"Hajiya ki kwantar da hankalin ki na riga na gama samun kan Dije zata dinga sanar dani duk wani abu dake shiga da fita ta ɓangaren ta,kawai dai yanzu abinda nake buƙata daga gareki shine inaso ki dinga sanar dani duk wani abu dayake tafiya wanda kike da masaniya A kansa acikin gidan nan, saboda ta hakane zan dinga binciko miki abubuwa masu mahimmanci wanda zasu kasance miki matakin nasara A kan burinki!'wata irin dariyar farin ciki Hajiya ladidi ta saki kana tace"gaskiya yarinyar nan kin burgeni ashe haka zakiyi min rana amma naso yiwa kaina sakiyar da babu ruwa,karki damu wannan ai Abune mai sauƙi ai duk ƙaruwar muce!'cikin sauri,Bintu tace"au ai nasan Anty Nafisa zataji daɗin wannan lokaci,tunda dama daga mu sai ita mukasan mai muke shiryawa A cikin gidan nan!'Hajiya ladidi tace ke fice nan ai ita kanta Nafisa bata san manufar mu ba kawai dai muna amfani da ita ne,kamar yadda ita ma take da tata manufar batare da tasan mu mun sani ba,itace dai bata san komai kanmu ba!'cikin nuna halin ko inkula Bintu tace"to ai Hajiya Ni bandamu da duk abinda kuke ciki ba Ni kawai A yanzu burina nasamu kuɗin da zan gina rayuwata,to amma kuma Hajiya wani hanzari ba gudu ba kina ganin ba sai nasan waƴanda kuke tare dasu ba saboda gudun samun matsala ta ɓangarena? Hajiya ladidi ta saki murmushin ƙeta A ganinta ta riga ta gama dulmiyar da Bintu ta gama shiga hannunta dan haka ita yanzu lokacin baccinta ne yazo,tace" Bintu babu ruwan ki da wannan Ni kaina A yanzu bana ce miki ga wanda nake haɗa hannu dashi ba sai dai natabbatar shi ɗin ahlin ALHAJI BALARABE ne kuma bandamu da nasani ba burina kawai shine A gabana!'Bintu cikin gaiyato ƙarfin hali da san kawar da halin da tashiga na ruɗani tace" tom shikenan Hajiya baki da wata matsala da Ni komai zai tafi yadda kikeso!' Hajiya ladidi tace"amma Bintu ina so maganar Nafisa ya kasance tsakanin mune baza taji wannan magana ba mu cigaba da tafiya a yadda muke!'Bintu tace" haba Hajiya ko bakiyi min gargaɗi ba bazan taɓa gayawa Aunty Nafisa komai ba,Ni na gaya miki abinda nake buƙata dan haka babu ruwana da abinda kuke shiryawa ko kukesan cinmawa,idan hakane kuwa kinga babu ruwana da tsakaninku aiki na kawai zanyi na kauce,saura na zubawa ƘUDURAR ALLAH idanu!'Hajiya ladidi tace"yauwa Bintu na gode da fahimtar ki gareni sai mun sake waya!' to shikenan sai anjima!'duk wannan wayar da Bintu takeyi tana yine cikin ta ka tsantsan da ankarewa.

da sauri ta bar gurin ta ma fasa zuwa gurin saboda yanzu tana buƙatar dogon tunani da kuma shawarar Dije,tana shiga ɗakinta tasaka mukulli ta rufe zama tayi tsakiyar ɗakin tana maida numfashin tashin hankali, kanta yayi matuƙar daurewa da wannan lamarin wato ita kanta ƴar da uwa munafuntar juna sukeyi lallai wannan al marin babbane, to yanzu yaza ayi na gano wanda suke haɗe da Hajiya?can kuma ta zabura gami da cizan yatsa A fili tace" tabbas Hajiya ladidi kin gama kashe kanki tunda kika yadda naji sirrin junanku ke da ƴarki,kuma da kanki zaki lalibo mugun da yake saki aiki!'sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya tana mamakin kanta,tare da mamakin Hajiya ladidi, dama sakarar mata ce bata da wani wayo? tana zaune jikarta tayi mata wayo ta bugi

Please Login or Register in order to submit comment